IN SO YAKI NE CHAPTER 15 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

IN SO YAKI NE CHAPTER 15

IN SO YAKI NE CHAPTER 15

- - Post a Comment
IN SO YAKI NE CHAPTER 15

  D'aki ne wanda ya kasance mai duhu haken da ya haska d'akin haske ne wanda ya shigo daga ƙaramar taga wanda tsayin ta yafi ƙarfin tsayin mutum ya kai shi, ya jima kwance yana nazarin yanda haƙar sa zata cimma ruwa, jira kawai yake lokaci yayi a fitar dashi daga wannan d'akin da marabar sa da qabari qalilan ne, bai aune ba kuwa yaki ƙarar takun ƙafafu hakan ya tabbatar masa cewa time yayi, da sauri ya mik'e ya doso k'ofar wanda duk dabarar mutum bazai kai ga girgiza ta ba ballantana ya bud'e ta shi kaɗai in de ba da makullin ta ba, wata y'ar k'ofa ce wanda iya hannun sa kaɗai zai iya zira wa ta nan ne aka jeho masa wata y'ar leda, murmushi kawai yayi ya duk'a ya ɗauki ledar ya ware ya ɗauko abunda ke ciki, shaving stick ne mai blade d'aya don haka ya kad'a kai yana murmushi "Just what i needed to execute my plan! And this time around i will not be the looser! Coz i will hurt you somewhere you did not even expect SURAAAAJ!"...+ Ƙarfe tara na safe aka buɗe masa k'ofa kamar yadda aka saba, bai b'ata lokaci ba ya fito idanuwan sa cikin na mutumin wanda ke riƙe da bindiga ya kame waje guda jira kawai yake SA'EED ya gama fito wa su tafi, kamar kullum wajen cin abinci suka nufa, waje ne mai cike da dogayen tebur masu kama da bench haka kowa in ya karbi abinci sai ya nemi wajen zama, duk da ma wasu idan ka zauna kusa da su ka yanki tikitin tashin hankali don basa tsoron ko ta kwana, Sa'eed na karbar abinci ba tsaya ko ina ba se ɓangaren crooks Daf da wani ƙato ya zauna duk da cewa magana suke ba kowa ne zai fahimci hakan ba, daga ƙasan bench d'in Sa'eed ya mik'a wa k'aton blade d'in da ya cire daga jikin shaving stick d'in sannan ya kalle shi a sace yace "I've waited so long for this! Remember idan kayi kuskure sai na kashe ka and i mean it, idan yaso nima se a kashe ni! K'aton ya ɗan jinjina kai yana wasa da rezar a hannun shi yana k'are wa prison warders d'in kallo kowa yana post ɗin shi komai yana tafiya daidai sai ya yi magana da Sa'eed ta gefe gefe yace "Punch me now! Ka naushe ni a duk inda kaga dama dole mu sa su yarda cewa faɗa muke yi in the process zan yi amfani da wannan rezar na yanka jijiyar hannun ka ta yanda babu kayan aikin dake prison d'in nan da zai iya taimaka maka ta haka kaga basu da wani zaɓi da ya wuce su fitar da kai zuwa asibiti daga nan kuma dabara ta rage wa mai shiga rijiya da baya. Amma sedai abunda zamu aikata maka akwai hatsari idan kuma aka samu akasi ka mutu fa????" Wata dariya ce ta kufce wa Sa'eed ya dubi k'aton ido cikin ido yace "kaga nayi kama da wanda ke tsoron mutuwa?" Yana k'arashe maganar ya dunk'ule hannun sa ya kai wa k'aton nan naushi har saida hancinsa ya fitar da jini ganin haka yasa warders d'in suka nufo su da gudu take wajen ya hargitse prisoners sai bubbuga kwanuka suke suna ihu hakan ya raba hankalin warders d'in gida biyu daidai lokacin ƙaton nan ya haye ruwan cikin Sa'eed cikin sauk'i ya kama hannun sa ya yanka da blade d'in kafin su ankara sai jini suka gani yana kwarara, da gudu masu tsaro suka k'aru a wajen aka janye ƙaton nan ana duka nan da nan masu kula da lafiya suka shigo, burin Sa'eed ya cika domin dama chan buƙatar sa kenan a fita dashi daga prison ɗin daga nan kuma sauran ya rage masa........ Da gudu likitoci suka yo kanshi basu wani b'ata lokaci ba sai Emergency operation room, wajen was heavy guarded ta yanda likitocin ma wasu basu da hurumin bin sa. Bayan an gama masa aikin ne aka yi moving nashi zuwa ICU lokacin bai farfaɗo ba amma babu wata matsala wanda ya wuce jini da ya rasa da yawa wannan ma kuma an kula da lamarin tun da wuri, hakan kuma yana nufin komai ya tafi a kan tsarin Sa'eed....... ******. ******* Ta dad'e zaune tun shigowar ta d'akin ta rik'e shafal cikin ta tana shafa shi a hankali hawaye na bin kumatun ta ɗaya bayan ɗaya, sallamar su Mubeenah ta sa Laylah tayi saurin goge fuskar ta tana sakin murmushin da bata yi niyya ba, kwarai sun fahimci yanayin ta hakan ne ma yasa Mubeenah tace "I know how tough it is for a mother to loose her unborn child, because hakan ta faru a kai na, I'm sure by the way you look nasan hawayen ki bazasu rasa nasaba da hakan ba, it hurts ka buɗe ido kana muradin ganin abunda kake so kuma ya kasance babu shi, Laylah duk abunda ya faru a rayuwar mu ita ce ƙaddarar mu kuma kamata yayi mu rungume ta mu bar wa Allah komai , kukan da kike yi will only affect your health, afterall baki wani jima ba da farfaɗo wa." Murmushi Laylah tayi ta jinjjiga kai tace "kin yi gaskiya Oum Iman ni kaina mamakin dalilin kukan nan nake yi, komai ya wuce but memories d'in suna farautar ƙwaƙwalwa na ta kowanne fanni, barcin ma kasa yi nake yi, idan na tariyo rayuwa na tun ina ƙaramar yarinya har zuwa yanzu sai inga babu moment guda ɗaya tak da nayi living life d'ina for myself, i wasn't the selfish type of girl, i only wanted to live for others to be happy se yanzu na fahimta cewa i have to be happy to give others happiness. Na fuskanci abubuwa na kunci da takaici a rayuwa waɗanda ko a mafarki bana son sake ganin su. Kai Khadijah ta jinjina tana cewa "All that was in the past Laylah, you are not alone anymore, ga Tasleem, and Suraj is there for you sannan muma muna tare da ke na san zai dauki lokaci but komai zai dawo daidai, duk abin da ya faru is in the past. Yanzu lokaci ne da zaku yi adjusting rayuwar ku daga ke har Suraj besides you are not married to Muhseen anymore". Zaro idanuwa Laylah tayi da mamaki ƙarara a fuskar ta lokacin da taji Khadijah tana cewa bata da aure A hankali ta d'ago idanuwan ta da suka k'ank'ance saboda kuka tana kallon su baki a sake Ajiyar numfashi Mubeenah tayi sannan ta rik'e hannun Laylah tace "Look Laylah....tun jiya da kika yi wurgi da Papern divorce naki Suraj ya gani, though bai ce komai ba bisa kuskure ya faɗi daga hannun sa hakan yasa muka gani, ina tunanin apart from Meenah kowa ya san zancen nan, Laylah i know it's embarrassing but still it's better to tell you all we know mun zama d'aya yanzu babu amfanin b'oye b'oye. Kai Laylah ta jinjina duk taji jikin ta yayi sanyi kamar ta nutse. Murmushi kawai ta saka wanda ya k'ara mata kyau tana goge hancin ta da yai jajir, su ma murmushi suka maida mata sannan suka mik'e "Ki yi wanka ki fito muna downstairs zamu jira ki for breakfast" Kai ta girgiza su kuma suka fice daga d'akin, sai da ta ɗauki lokaci tukuna ta mik'e zuwa bathroom bata dad'e ba ta fito d'aure da towel ta tsaya gaban madubi tana kallon kanta. Haka kawai ta tsinci kanta da sakar murmushi musamman da ta tuna encountern ta na d'azu da Suraj "He's still the same... Funny and cheerful" ta fad'a a ranta kafin ta kad'a kanta gami da runtse idanuwan ta tana bubbuga fuskar ta "Ki farka Laylah! Stop dreaming he belongs to someone else now!" Ta fad'a a fili kafin ta buɗe wardrobe tana neman ɗan kayan da zata ɗan mak'ala tunda de tasan cewa nan ba gidan ta bane amma ga mamakin ta sai taga kaya a ciki har wajen kala biyar ɗinkin atamfa ga kuma abaya's waɗanda suka fi rinjaye ma kenan, idanuwan ta ne suka sauk'a kan wata jar atamfa ɗinkin doguwar riga don dama ita ba ma'abociyar d'aura zani bace don haka ta janyo shi, a jikinta take ji don ita aka ajiye su, kai ko ma ba nata bane zata saka domin sune kaɗai kayan da ta gani a wajen kuma bazai yiwu ta maimaita wanda ta cire ba, zira rigar tayi sannan ta kama gashin kanta ta d'aure shi in a bun sai ta yafa baƙin mayafi, turarrukan dake gaban mirror ɗin tabi da kallo kafin ta kai hannu ta ɗauki wani arabian ta fesa kamar wanda take tsoro fuskar ta ko kwalli babu se farar powder da ta shafa haka ta ɗauki wayarta ta nufi k'ofar fita....... Tun da ya shirya ya fito living room ya kafe TV da ido alamar news yake gani jifa jifa yakan d'aga wayar shi ya ɗan duba sai ya ajiye, a nan Habeeb ma ya iske shi. "Gud morning". Suraj ya fad'a a tak'aice ba tare da ya ɗauke duban sa daga Tv ba. Shima Habeeb d'in bai kalle shi ba ya amsa da "Morning brother". Har Habeeb zai k'ara magana sai mai aiki ta katse su "Sir! breakfast is ready." Kai kawai Suraj ya gyad'a mata sannan yayi nuni da hannu zuwa upstairs yace "kice su fito da wuri tare da yaran nan nasan rigiman boboh bai wuce yunwa yake ji ba na faɗa hurry!" Da sauri ta nufi upstairs don aiwatar da umarnin da aka bata, yayinda Suraj ya mik'e ya nufi dining table ya ja kujera........... A hankali taje sauk'owa jiki babu kwari don yanda suka k'ura mata ido abun har ya gundure ta ji take kamar ba a kan k'afafun ta take ba, Suraj da ya riƙe sliced bread shi bai kai baki ba shi bai ajiye ba hakan yasa Ameer ya kwace bread d'in ya ajiye yana dariya sai lokacin Suraj ya dawo daga duniyar da ya shiga ya ɗan yi gyaran murya sannan ya saki karamin murmushi yana sunkuyar da kai. Shima Habeeb couldn't help but smile ganin yanayin ɗan uwan nasa. Duk abunda ke wakana Meenah tsabar takaici ta kasa haɗiye dankalin da ta tura a baki don ji tayi duk dadi'n shi ya sauya zuwa d'aci. Hannun ta kuwa ta damk'e Fork ɗin kamar zata b'alla shi sarai Mubeenah ta lura da haka amma sai ta basar. Laylah na k'araso wa wajen ya fara bada daddad'an k'amshi wanda ya sa Ameer lumshe ido cikin zolaya yace "hmmmm! " Bugan hannun shi Mubeenah tayi tana masa nuni da Meenah haka yasa shi gimtse maganar da zai furta don haka ya saki murmushi kawai ita de Laylah fuskar ta a sake take amma na ciki kuma ita ta san yanda take ji. Tana zama kuwa Meenah ta ajiye fork ɗin ta hanyar buga shi da table Suraj har razana yayi ya bi ta da kallo yayinda ta mik'e ta nufi stairs......... Da kallo ta bi Meenah sosai jikin ta yayi sanyi ta san tabbas barin wajen da Meenah tayi yana da nasaba da zuwan ta wurin, a hankali ta dawo da duban ta kan fuskokin su sai ta lura ko alamar damuwa basu yi ba Suraj kam murmushin sa ma yake yana taunar abincin tamkar babu abunda ya faru, rai a b'ace Laylah ta ƙi zama tace "You think this is funny?" A wannan karon ne duk suka d'ago kai suka aza idanuwan su ga fuskar Laylah wanda cikin sa babu alamar wasa. nan da nan Suraj ya ajiye sandwich d'in hannun sa bisa plate ba tare da ɗauke duban shi a kan Laylah ba "How can you be so dumb? Mace d'auke da juna biyu cikin fushi ta bar cin abinci maimakon ku lallab'a ta sai hakan ya zama abun dariya a wajen ku...... Like seriously!? A irin yanayin ta lallab'a ta ya kamata ku yi anything can happen, bai kamata ta shiga damuwa ba coz a slight b'acin rai might prove to be fatal for her but instead kun maida abun wasa. Anyways forget it! Saboda it seems i am talking to a bunch of headless bodies" Tana kai nan a maganarta Laylah ta juya ta koma upstairs zuwa d'akin ta. Duk da jikin su a sanyaye yake Suraj ya yi ajiyar zuci yace+ "A kullum Ameer da Habeeb kuna tambaya na meyasa Laylah ta kasance special? I think yau kun fara samun amsar ku, Meenah was jealousy and envious of how we looked at Laylah and on the other side Laylah..... Duk da ta san cewa don ita Meenah ta bar wajen she is fighting for her, that's Laylah for me she is never selfish hakan yana daya daga cikin dalilan da yasa soyayyar ta ke ƙara girma a zuciya na, ban bar k'aunar ta ba lokacin da na fahimci tana da aure kuma yanzu ma da bata da shi ba zan bar k'aunar ta ba ko da kuwa soyayyar Laylah zata sa in rasa raina Murmushi Habeeb yayi yana dafa kafad'ar Suraj kafin yace "Bros in that case i think you have aiki a gaban ka coz you have two ladies to comfort! Dayar matar ka ce ɗaya kuma Beb ɗin ka oya gooo!!" Habeeb ya mik'e tsaye yana fad'in "bye guys nidai kunga tafiya ta Suraj sai ka hanzarta don yau zan yi presentation d'in" sunkuya wa yayi ya sumbaci Khadijah yana murmushi "bye sweetie" ita ma hakan tayi mishi sannan tace "bye Habeeby" Suraj ya kafe shi da ido har ya fita sannan ya dubi Ameer yace "yau nikam se yadda ta yiwu na san zan iya shawo kan Meenah but Laylah??? She's the tough type" Dariya suka sa kawai shima bai ƙara magana ba ya nufi stairs, sai a lokacin ummin Habeeb suka fito "Ah ah! Ya naga table d'in ya rame haka, ko dai har sun fita? Kai Ameer ya gyad'a yace Habeeb ya fita Suraj ya koma ciki bai gama shiri ba. Kai ummi ta jinjina tace "Muma mun shirya zamu koma Kaduna anjima, amma sapna zata zauna tunda naga ta ɗan warware a nan ɗin ba kamar kwanakin baya ba. Haɗe rai Boboh yayi yace "no granny please don't go! Dariya suka yi kawai shi ko yaci gaba da cin abincin shi..... "Tunda ya shiga d'akin yake ƙoƙarin lallab'a ta amma se take tirje wa, hakan ba ƙaramin b'acin rai yasa Suraj ba yayi zuciya ma ya fice daga gidan ko ta kan Laylah ma bai bi ba. Su kansu yanda yayi sallama da su sun san ba'a kare ta da dad'i ba. Meenah na zaune a d'akin b'acin ran shi bai girgiza ta ba ko qiris, mik'ewa tayi ta fita daga d'akin tana masifa har ta isa inda d'akin Laylah yake sai ta kasa d'aga k'afa, bayan ta ya rik'e, ta zaci abun wasa ne da taga go _no_ go kawai sai ta saki ihu..... Tun shigar ta d'akin Laylah ta zube kan gado ta kifa fuskar ta cikin pillow har barci ya fara ɗaukar ta. Kamar daga sama ta jiyo ihu, babu shiri ta yi firgigit ta mik'e, ihun da taji a karo na biyu ne yasa ta fita da gudu don kamar muryar Meenah taji, ai kuwa tabbas Meenah ce durk'ushe kan gwiwa tana riƙe da k'ugu. "Meenah!!!" Laylah ta fad'a tana k'ok'arin kama ta. Amma tsabar kishi ta sa hannu ta hankad'a Laylah ita ma dake bata da ƙarfin kirki sai ta zube ƙasa. Aka yi sa'a Su Mubeenah sun ji ihun nata suka taho daidai lokacin Laylah ta fad'i. Da taimakon Khadijah ta mik'e tana gyara mayafin ta yayinda Mubeenah ke k'ok'arin d'aga Meenah "Ummi ina ga nak'uda take mu kaita asibiti kai ummi ta gyad'a sapna sai lokacin ta fito daga sashen ta, ganin abunda ke faruwa yasa ta taimaka suka sauk'a da Meenah downstairs, babu wani b'ata lokaci suka garzaya da ita zuwa asibiti. Suraj kuwa ko da ya fita ma ba office ya nufa ba sannan babu wayar shi ɗaya da take a kunne don shi duk Meenah ta bashi haushi, though ya san cewa tana da juna but it doesn't mean she should act like a child. B'angaren Laylah kuwa ganin yanda Meenah tayi mata yasa ta gwammace ta zauna a gidan ita kaɗai da yaran in yaso sauran su tafi da ita......... STORY CONTINUES BELOW ******. ****** Ya dad'e da farka wa duk illahirin motsin da ake yi a kansa duk yana ji amma sai ya k'ame tamkar mai barci, duk numfashi ɗaya da ya ja yana k'ara masa ƙarfin gwiwa na aiwatar da qudurin da ke ran shi ko kaɗan zuciyar Sa'eed a bushe take, saida yaji k'afa ta ɗauke ya tabbatar shi kad'ai ne a d'akin sai ya tashi zaune yana k'are wa ventilator kallo kafin ya saki murmushi, hannu ya sa ya danna wasu madannai kafin kace me ƙarar na'ura da kayan aikin duk suka baibaye wajen shi kuma ya koma ya kwanta yana jira a buɗe k'ofa ya fara acting kamar yanda ya tsara. Bai ɗauki kwararan mintina biyu ba likitoci da Nurses suka garzayo kansa kowa na nasa ƙoƙarin babu wanda hankalin sa ke jikin shi shi kuwa she mustukuku yake irin na Wanda ya kasa shak'ar numfashi a lokaci guda kuma hannun sa yana masa aiki domin kuwa da hannun ya zaro wayar doctor daga aljihun sa ya cusa ta karkashin cinyar sa ta yanda babu yanda za'a yi a gani daga nan ne kuma sai ya lumshe ido tamkar mai barci hakan yasa suka gyara masha kwanciyar sa suka fita,. Saida ya tabbatar sun fita ɗin yayi sauri ya ɗauko wayar ya saka ta a silent sannan ya danna wasu lambobi yayi dialing "Kai kana ina ne? Na fito kamar yanda aka tsara get me out of this fucking hospital! Duk yanda za'a yi ina so in fita a yau ɗin nan, ban damu ba in cikin dare zaku zo ko yanzu but make sure kun shirya tsari mai kyau!. Kar ka kira ni da wannan layin ko me zai faru. Ku tabbatar kun sama min wajen hutu mai inganci da kuma motar hawa everything should be according to my taste ina fatan ka gane...." Nan ya katse wayar yana murmushi kafin ya danne kan lambar yayi deleting d'in ta kuma ya cire ta a silent ya wurgar a k'asa sannan ya koma ya kwanta........ ______the same hospital______ Da sauri aka shiga da ita labour room duk iya ƙoƙarin Ameer don samun wayar Suraj a banza don basa shiga ummi ma tayi ta gwada wa a kashe don haka ta k'ira Habeeb "Wai kam ina Suraj ya shiga ne? Tun d'azu wayoyin sa baya tafiya gashi muna asibiti Meenah tana labour ward yanzu haka idan ana buƙatar sa a nan kuma fa?". Ummi yanzu haka nima neman sa nake ta yi don bai iso wajen aiki ba har yanzu infact nayi zaton ma har yanzu yana gida..." Kai ta girgiza sannan ta katse wayar "Chan office d'in ma bai je ba ina ganin wani abun ne ya taso mai muhimmanci. Abba ya kad'a kai yace Allah shi kyauta..." Ba'a jima ba doctor ta fito tace "Aammm.....waye mijin Meenah? Da sauri suka mik'e sai kuma suka yi turus saboda sun tuna Suraj baya nan Abba yace "Doctor....mu familin ta ne unfortunately mijin ta baya nan something urgent came up bai ma san an kawo ta nan ba I'm sure da yanzu haka mun ganshi a nan idan akwai abunda ake buƙata Please zamu yi on his behalf." Kai ta girgiza tace "ba zai yiwu ta haihu da kanta ba dole sai anyi CS due to........ Bata k'arashe maganar ba Aunty fatima ta katse ta da sauri gudun kar ta fad'i cutar da Meenah ke da ita don tabbas mace mai brain Cancer ga nak'uda it will only trigger the pain in her. Cs shine mafita domin haka ta ce "Muna sane da matsalar ta doctor, just kiyi abunda ya dace zamu sa hannu a kan papers d'in na tabbata idan Suraj yana nan ma he will do the sam. Kai doctor ta jinjina sannan suka tafi da Aunty fatima lokacin ne aka fita da Meenah zuwa( OR ) Operation room......... _______________ Ya dad'e zaune a coffee shop d'in a hankali Yana siping black coffee kamar wanda aka tsikara ya mik'e da sauri ya ajiye kud'in bisa table ya fita da saurin shi ya shiga mota ya koma gida, yana tuk'in ne amma hankalin shi tunano masa rayuwar sa take a baya, komai yana tafiya bisa tsari saboda akwai soyayyar mahaifiyar sa a tartare da shi, da tana nan she would have shown him the right way to tackle every situation but Allah baya barin wani don wani yaji daɗi. "Maybe i should call Dad" Ya fad'a a fili sannan yayi parking motar a gefe ya cire wayar daga Flight mood sai ya yi dialing numbar Dad d'in shi, layin sa na Cairo ya k'ira yayi ta ringing har ya kusa katse wa sai Dad ya d'auka, ya kai mintina uku Suraj bai ce komai ba, Dad na jin haka yasan akwai matsala don haka sai ya kashe wayar don yasan a wannan shirun na Suraj bazai ce komai ba shima wurgi yayi da wayar tashi ya bugi sitiyarin motar shi yana ƙoƙarin hana hawayen da suka cicciko masa a ido zubowa. Daga bisani de ya tada motar kawai ya nufi gida . Tun da ya shigo living room yaga fayau babu kowa mamaki ya kama shi dom ya sani cewa yawanci sukan yi hirar su war haka a nan, mak'e kafad'a yayi sannan ya haura stairs nan ma babu alamar suna nan saida ya jiyo dariyar yara a d'akin Laylah sai yayi tunanin a chan suke don haka ya shiga da sallamar sa. Cartoon suke kallo sai dariya suke ita kuwa Laylah ta jingina da gadon ta takure yayinda iman ke barcin ta cikin kwanciyar hankali, sallamar Suraj ce ta sa suka d'ago da sauri ita ma Laylah ta kai duban ta ga K'ofa. Tana ganin shi ta mik'e ta nufo shi "Suraj.....yaya jikin Meenah? Is she alright? Kun dawo ne ina su Mubeenah?" Nan ne wani ƙararrawa ya kad'a a kan shi cewar shirun da yaki a gidan ba lafiya ba. "Me ya faru da Meenah! ? Ina suke ki min bayani Laylah ban fahimci tambayoyin ki ba". Nan ta kwashe abunda ya faru ta sanar da shi ai kuwa bai yi wata wata ba ya yi saurin juyawa zuwa motar sa ita de Laylah bata yi wani yunk'uri ba ta koma d'akin suka cigaba da harkokinsu da yaran............. Har zai shiga mota ya hango Ameer yana waya, da sauri ya doshi inda yake zaune bisa resting bench ya mik'e k'afar sa d'aya a saman bench d'in.. "Prince!! Prince Laylah just told me what happened a wanne asibitin suke??" A hankali ya d'ago ido yana kallon Suraj d'in sai kuma ya maida wayar sa a kunne yace "Habeeb ga Suraj d'in ya dawo, i told you kana tada hankalin ka ne for no reason gashi ku yi magana.." Ya ƙarashe maganar yana miƙa wa Suraj waya, bai wata wata ba ya amshe wayar ya kara ta ga kunne. "Ina ka shiga ne Suraj? You got us worried sick! Ka kashe wayoyin ka sannan baka ma je wajen aiki ba what has gotten in to you? A yanzu zancen da nake maka Meenah tana O-R maka bayani ma ni bazan iya ba koma me kake yi just come to the hospital!" Kashe wayar yayi bayan ya sanar da shi asibitin da suke. Bai bi ta kan Ameer ba ya juya ya tafi ya ma manta wayan Ameer ne a hannun shi, shima Ameer bai tsayar shi ba don yasan yanzu haka a rud'e yake don haka ya mik'e ya koma cikin gida da har zai shiga d'akin ya fasa yayi kwanciyar sa a falo........ Suraj na isa asibitin lokacin suma suka shigo, haka kawai jikinsa ya bashi ba su da gaskiya ta yanayin idanuwan su, amma sai ya basar, yayi tambaya a reception aka faɗa masa inda Meenah take daidai lokacin likitan ke congratulating d'in su Habeeb. Sosai yaji K'irjin shi na bugawa babu wani kwakkwaran dalili, ji yayi jiri na d'iban shi yayi gaggawan riƙe Habeeb su kansu saida suka tsorita da yanayin nashi, saida ya ɗan daidaita tukuna ya d'ago kai yace "How's Meenah? And the baby......?" Ummi ta ɗan yi murmushi tace "both baby da maman ta suna lafiya, bata farka ba......." Nurse ne ta katse su duk suka juya suna kallon ta "Congratulations Mr Maleek your little princess looks just like a photocopy of Meenah she only has your nose" sosai Suraj yayi dariya duk da har yanzu jikin sa a sanyaye yake is like something bad will happen amma sai ya sa a ransa cewa koma de menene Allah yana nan. Ya dubi nurse yace "zamu iya ganin baby?" Kai ta gyad'a ta ce "of course you can.....come this way." Nan suka bi bayan ta zuwa wata k'ofa, d'aki ne wawakeke mai kyau daga Wajen da suke suna iya kallon jerin jarirai dake cikin kananan gadon yara kowanne da tag wato shaidar sunan iyayen a k'afar sa gwanin ban sha'awa Khadijah ji take kamar ta ɗauke ɗaya ta gudu. Suraj de na tsaye har nurse ta fito riƙe da babyn tana murmushi A lokacin ne Suraj ya sa hannu ya amshe ta. Hawayen da ya ƙi bari su zubo babu shiri suka fara kwaranyo wa. Waje ya nema ya zauna yana k'are ma ƙaramar fuskar ta kallo, indeed nurse tayi gaskiya tamkar photocopy d'in Meenah ce, little version of Meenah! Addu'a yayi mata sannan yayi kissing goshin ta. Habeeb yayi gyaran murya yace "I hope baka manta da mutane a nan ba, nima de Dad ɗin ta ne lemme welcome my sweet little princess". Wani dariya Suraj yayi yana shanye kukan nashi da sauri ya mik'a ta Habeeb ya karb'a shi kuma ya juya yana k'are ma wajen kallo kamar gizo haka yaga giftawar Sa'eed, kad'a kansa yayi ya ɗan saki murmushi a ranshi yace "Me yasa nake tunanin abunda bazai faru ba? Na tabbata kawai idanuwa na ne ke min gizo." Nan ya juya ya cigaba da harkokin sa sai lokacin ne ya kula da wayar Ameer a aljihun shi kawai se ya dafe goshin sa yana dariya se ya mik'a wa Mubeenah, tana karb'a kuwa ta saka a purse...... ________ Mintina goma da suka wuce...... Su uku suka shigo asibitin kusan a tare da Suraj sedai basu lura da shi ba suka wuce shima duk da cewar ya gansu ya basar, hanyar d'akin Sa'eed suka nufa amma sai suka lura da tsauraran matakan tsaro dake wajen don haka suka ja da baya suka sake shiri, wannan karon murd'e wuyan wasu Nurses biyu suka yi suka saka kayan su dayansu kuma wanda ya kasance jagoran ya ƙare ma wajen kallo sannan a sace ya shiga office d'in wani doctor inda ya haɗa kan shi da bango cikin sauk'i ya ɗauki tag ɗin shi da kuma coat nashi ya saka, gudun kar a gane shi ya sa face mask sannan ya ɗora siririn gilashi. Janye likitan yayi ya saka shi a banɗaki ya rufe sannan ya fito inda ya bar sauran biyun suna taka masa baya, cikin sauk'i suka shige d'akin ba tare da wani kwakkwaran bincike ba. Suna shiga suka rufe k'ofar shi kuma babban nasu ya zare mask da gilashin yace "We are here Boss!". Wani firgigit Sa'eed yayi ya mik'e yana dariya ya ware hannuwan sa biyu suka rungume juna "MAYEEE!!! I know i can count on you.. .... " Ya fad'a yana janye jikin sa daga hug d'in "Welcome back Boss!" Cewar wanda Sa'eed ya k'ira da mayee. Kai kawai Sa'eed ya jinjina yana murmushi sannan yace "i hope my escape route is cleared and safe?" Kai suka gyad'a masa hakan yasa shi murmushi yana shafa kasumbar sa da tayi duguzuzu da ita. Taku da suka ji yasa dukan su uku suka nemi wajen fake wa suka buɗe k'ofar, saida likitan ya gama shigowa ya na ta dube dube da alama shine wanda ya rasa wayar sa ko ince wanda Sa'eed ya ɗauke wayar sa, bai ankara ba yaji an doki kanshi da abu mai nauyin gaske daka nan bai san inda yake ba, kayan sa Sa'eed ya saka duk da ma sun so suyi kaɗan haka ya saka su, sannan ya toshe fuskar sa da glass ya sa mask kamar yanda wancan yayi, shi kuma likitan suka aza shi kan gadon suka lullub'e tamkar mara lafiya sannan suka fice ba tare da fargaba ba , ana cikin haka ne Suraj yaga giftawar su amma sedai gani yake tamkar gizo ne idanuwan sa ke masa don haka ya watsar da lamarin......... Fitan su ke da wuya wata Ambulance ce a ajiye suka shiga hakan zai hana ko kuma rufe duk wata kafa ta suspicion saida suka yi nisa da asibitin sannan suka sauya kayayyakin su suka zubar da na asibitin a nan ne wata bak'ar mota k'irar Mercedes ta k'araso suka shiga. Babu abunda Sa'eed yake sai dariya kasancewar abunda ya shirya ya tafi a daidai.... "Ina zamu fara zuwa Boss?" Mayee ya tambaya. "Hmmm! Da nayi tunanin kawai in wuce in huta, but na tabbata nan da wasu awanni labarin escape d'ina zai karad'e ko ina, hakan zai sa su ankare kuma idan hakan ta faru komai da na tsara zai ruguje, how about this? Let's give my loving brothers a surprise visit I'm sure they will love it!" Bai k'arasa maganar bama driver'n ya juya akalar motar zuwa maitama district sai sheqa ayar su suke tayi. A bakin gate d'in suka tsaya driver'n ya buga horn kai kace masu gidan ne mai gadi jiki na rawa ya hau buɗe k'ofa ba tare da ya duba ko waye ba, basu jira ya gama buɗe k'ofar ba ma suka danna kan motar ciki hakan yayi sanadiyyar faduwar gateman ɗin ƙasa wanwar, guda biyu daga cikinsu suka fito suka rufe gare ɗin sannan suka tisa k'eyar gateman suka rufe shi cikin daki bayan sun tamke masa hannu. Sa'eed kuwa ko sauraraon su bai ba shi da Mayee suka kutsa kai cikin gidan. Tunda Ameer ya kwanta a falon barci yayi awon gaba da shi kamar a mafarki yake jin takun ƙafa amma sai ya gyara kwanciyar sa, kasa barcin yayi yana ji tamkar bakwai wani tsaye a kansa,a hankali ya buɗe idanuwan shi masu cike da nauyin barci, abunda ya gani ne yasa shi sake runtse idon sa ya ɗan buɗe su karo na biyu, a nan ne ya tabbatar wa kansa abunde da ya gani a farkon shi ne, wani irin zabura yayi ya zauna baki a sake fuskar sa cike taf da mamaki "S....Sa'eeed..h....hhow is this possible?? You can't be here!" Wani murmushi Sa'eed yayi ya sa hannu ya janyo Centre table daf gaban Ameer sannan ya zauna "What is it Bro? Yaya dai naga ka tsorita? Nine fa!! Sa'eed !!! Your one and only brother! Shin baka yi farin cikin gani na bane? Ko kuma de kana mamaki ne? Kar fa ka manta with Sa'eed anything can happen it's not a big deal" Ya gama maganar yana dariya harda hawaye kafin ya tsare lokaci guda ya chafko wutan rigar Ameer ya shak'e idanuwan sa suka sauya launi "Zan baka zaɓi! It's either you join hands with me or die ina fad'a maka wannan ne saboda akwai guntun b'arb'ashin son ka cikin raina, idan kayi haka toh Lallai ka tsira, abunda zaka yi ba wani mai yawa bane just stay out of my business zan yi abunda ya kawoni in tafi i won't hurt you". Hankad'a hannun sa Ameer yayi a zuciye sannan yace " me kake tunani? That i will decieve my own brother saboda kai? Idan baka sani ba Sa'eed na dad'e da cire ka daga layin yan uwana tunda kai ka nuna cewa baka da imani baka da tausayi, i will never join hands with a person like you! Ka jira ka gani by the time aka gane ka gudu daga prison sai ka raina kanka kum.......". Bai gama maganar ba Sa'eed ya ɗauki glass d'in juice dake gefen sa ya watsa a fuskar Ameer sannan yace " Ka farka bro stop dreaming, nayi nisa bana jin k'ira! Kana tunanin plan d'in da na shirya tsawon watanni takwas zai tafi a banza ne? Noooo Ameer Nooo!!! Zan baka wani ɗan labari, everything was planned even before in shiga prison saboda na san zan kamu, it was just a matter of time, na saba da crooks d'in gidan, na karanci halayen masu tsaron wajen, and then i used them as my baits!!! Simple as that, na san cewa prison d'in da nake basu da wasu updated facilities da zasu yi maganin matsala ta domin kuwa idan suka tsaya wasa zan iya rasa raina, just as i expected sun yi referring d'ina zuwa specialist hospital, thanks to their professional doctors i was saved, sannan da taimakon mutane na i am here face to face with my stubborn little brother, what a pitty.... Har yanzu baka warke ba daga wancan raunin, kayi tunanin matar ka da yar ka idan kayi abunda nace i will spare them if not i will not have mercy on anyone who dare come in my way! So tell me ina mutanen gidan suke???? Wani mahaukacin dariya Ameer yayi sannan yace "ina tunanin wannan karon ka yi rashin Sa'a don babu wani wanda yake cikin gidan nan duk sun fita, ka iya tafiya try your luck another time!" Mari Sa'eed ya gaura mar har saida kunnen shi yayi wani dum, har Ameer zai yi magana ya hango Laylah zata fito, hankalin shi ya tashi da ido yayi mata magana ita kanta saida taji wani fitsari ya cika marar ta nan take gumi ya karyo mata, da hannu Ameer yayi nuni alamar ta koma ciki , kai ta girgiza masa alamar bazata koma ba saida Sa'eed ya lura akwai wani al'amari da yake faruwa amma kafin ya waiga ta juya da gudu zuwa d'aki ta rufe k'ofa da key sannan ta yi saurin kashe Tv ta dubi yaran tace "Kuji! Kowa yayi shiru bad guys are here duk wanda yayi magana zasu kama shi" zaro ido Boboh yayi yace "I don't like bad guys let's hide" Rungume shi Laylah tayi tace "yes idan baku yi magana ba bazasu zo ba but if you make noise they will come and take us away" da wannan tayi dabarar hana yaran surutu amma a ranta take ji dole ne ta taimaki Ameer duk runtsi ko da kuwa zata rasa ranta ne a wani ɓangaren kuma dole ta kare yaran daga sharrin Sa'eed, ta dubi Iman dake wasan ta kan gado ta san tabbas ba yanda zata yi ta rufe bakin Iman saboda haka ta buɗe bathroom ta saka su a ciki ta tara wa iman toys d'in ta a gaban ta sannan ta ja k'ofar bayan ta ce Tasleem ta kula da su.........

Post a Comment for "IN SO YAKI NE CHAPTER 15"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...