IN SO YAKI NE CHAPTER 14 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

IN SO YAKI NE CHAPTER 14

IN SO YAKI NE CHAPTER 14

- - Post a Comment

IN SO YAKI NE CHAPTER 14 Satikai sun shige, Laylah tana nan yanda take babu improvement. Tasleem na tare da Dad nata Suraj cikin walwala da jin dadi babu abunda ya ragar mata na gata Ameer kam Alhamdulillah don yanzu da crutches yake tafiya his wounds seems to be healing faster, b'angaren Muhseen kuwa kulawarsa na hannun jami'an tsaro kasancewar sa mai laifi, d'akin da yake kwance a asibiti ma an sa tsaro sosai gudun kar yayi escaping duk da ma de he seems calm for the time being. As for Sa'eed, anyi sentencing nashi a prison under watching trial har sai Laylah ta tashi ta bada statement nata. Yayinda Suraj ke k'ok'arin balancing rayiwar shi da professional life nashi Meenah on the other hand is proving to be dangerous for both Laylah and Tasleem, tun tana yi a b'oye har ya fara bayyana babu abunda taki jini kamar taga Suraj a kusa da Laylah a asibiti sau da dama tana yunkurin ta kawar da Laylah amma somehow plans nata suke failing haka ba k'aramin hargitsa mata lamari yake ba don ji take kamar ita ta kashe kanta kawai ta huta. Ba tare da tayi la'akari da cutar da take d'auke da shi ba infact fama take da kanta in those few weeks amma abun se k'aruwa yake. Doctors dake duba case na Laylah sun duba sunga cewa watakila environment da Laylah take shi yake slowing process na recovery nata sai aka yi deciding akan za'a tafi da ita gida a chan za'a cigaba da kula da lafiyar ta watakila chanjin wajen zai sa ta fara responding wa treatment da ake mata, Suraj yayi signing papers d'in suka, tare da Nurses biyu aka maida ta gida. Ameer ma already yana gida duk da yana facing difficulties na yin wasu daily activities d'in amma yafi jin daɗin kasancewar shi a gida cikin y'an uwansa. A nan ne kuma inda matar ta kada mijin domin hankalin Suraj ya riga ya karkata ga Laylah domin ko karyawa baya iya yi sai ya ga fuskar ta, ba wai baya bai wa Meenah hakkin ta ba infact soyayyar da yake nuna mata ma har ya ci uban na da he was trying hard to balance the differences tsakanin shi da ita but Meenah doesn't seems to appreciate all shi Suraj har rasa ma yanda zai yi da ranshi yake yi tun su Mubeenah suna shiru har suka fara tanka wa Meenah coz ta sauya wasu lokutan gani suke kamar ta haukace don yanzu sai ta tafka maka baƙin ciki yanzu kuma kuyi daɗi gani suke iya shege ne kawai, yayinda Suraj ke ganin kawai cikin ne ke saka ta masifa...... #8 MONTHs LATER............ Ita kad'ai tana zaune she hura hanci take tana cika shikam Suraj ganin haka sai ya mik'e ya ɗauki wayar shi zai fita gashi de ƙarfe biyar ne yamma yayi sosai amma ya gwammace ya fice ma ya bar gidan don shi duk ta ishe shi ji yake kamar ya duk'unk'une ta ya cusa a wardrobe ya rufe. Ko ta kanshi bata bi ba ta mik'e da kyar ta riga shi fita daga d'akin. Ihun Tasleem yaji ko wayar ma jefar da ita yayi ya fice da gudu "Tasleem! Tasleem!!......" Kwance ya hango ta a k'asa ta kasa d'aga hannun ta gefe guda bowl na ruwa da towel shima a dungure ruwan ya malale a wajen ita kanta Tasleem ɗin jik'e take ihu kuwa bata daina ba saboda ita kaɗai tasan yanda take ji. Ko da Suraj ya k'arasa gurin sai yaga Meenah tsaye ta haɗe rai wannan ya tabbatar mishi cewa tana da hannu a lamarin a fusace ya durk'ushe ya d'ago ta ya juya zuwa d'akin shi Khadijah ce ta sa aka gyara wajen, da Sauri Habeeb ya iso fuskar sa da alamar tambaya yace "What....what happened? Naji kamar Muryar Tasleem ina take?" Khadijah ta kad'a kai tace "fad'uwa tayi i think she hurt her hand tana d'akin Ya Suraj" Khadijah ta k'arashe maganar rai a dakile don ta fahimci cewa somehow Meenah tana da hannu a abunda ya faru. A tare suka shigo d'akin Suraj na zaune ya ma rasa ta inda zai fara tunda ko Hannun Tasleem ta ƙi bari ya taɓa se waya ya d'aga ya k'ira doctor Allah ya sa ba karaya bane kawai sprain ne, doctor ya yi mata necessary treatment sannan ya bata pain killer sannan ya tafi hannu de kam an nannad'e shi da Ortho crape bandage tsabar wahala ita kam har tayi barci, Suraj bai bi ta kan su Habeeb ba ma ya mik'e a fusace ya fita daga d'akin Allah Allah yake ya haɗe da Meenah coz babu shakka ita ce. Har zai yi coner Ameer ya rik'e rigar sa kaɗan ya rage ya wafce sai kuma ya tuna Ameer d'in ma crutches ne suke supporting d'in shi kar ya ji masa ciwo don haka ya tsaya chak yace "What kind of a woman would do such heartless thing to a seven year old kid? Ameer ka kyale ni in same ta, ta fara wuce gona da iri kuma! Idan ma Laifi Tasleem tayi atleast she should punish her the right way, dubi halin da ta sa min y'a ta i won't let it slide!!!." "Suraaaaj..... I know abunda tayi bata kyauta ba but kar ka manta condition nata, ka kyale ta tukunna for now watakila cikin ne yasa take behaving so wild so........" Gimtse maganar Ameer yayi jin ƙarar fad'uwar abu jigib! A ƙasa. Zaro ido Suraj yayi yace "LAYLAH! Ai kuwa bai tsaya b'ata ko da dak'ik'a ba ya ruga a guje zuwa d'akin. Turus yayi a lokacin da ya bud'e k'ofa bakin shi na b'ari yana kokarin furta sunan ta.......LAYLAH!!!" Suraj ya k'ira sunan ta cike da mamakin ganin ta da yayi kwance a k'asan floor tana ta yunkurin tashi amma ta kasa, for the first time in 8 months suraj ya yarda da maganar doctor da yace Laylah tana improving.... Da gudu ya k'arasa cikin d'akin yayi kokarin maida ta bisa gado yana kallon yanda bakin ta ke karkarwa hannuwan ta suna b'ari daidai lokacin Su Habeeb suka iso Mubeenah ta zuba ruwa kaɗan a glass ta bata, tamkar bata taɓa shan ruwa ba jaka ta kurba sannan ta fara kokarin magana "Ta..... Tasleem...ina.... Suraj bai bari ta k'arashe maganar ba yayi saurin katse ta yana cewa "Tasleem tana nan....barci take yi ki kwantar da hankalin ki Please we all are here for you" Kai Laylah ta fara girgiza wa cikin sanyin murya wanda ke sarkafe wa tace "I heard her crying! Ban san yanda aka yi ba amma tamkar a mafarki naji kukan ta, she must be hurt please Suraj ku fad'a min inda take....." Ajiyar numfashi Suraj yayi kafin ya duk'ad da kai k'asa yace "Am sorry..... Fad'uwa tayi d'azu ta gurd'a hannun ta, but all is well doctor ya duba ta she's now sleeping so there's no need to worry kar ki tada hankalin ki "+ Blanket d'in da ya rufa mata tayi saurin yayewa sannan ta mik'e a daddafe tana k'ok'arin fita daga d'akin, ko sauraraon Suraj bata tsaya yi ba iya ƙarfin da ya rage mata ta sa kai tsaye ta nufi d'akin ɗakunan dake wajen tana wangale su kamar zararriya Suraj bai yi ƙoƙarin hana ta ba duk da cewa ya lura da yanda take tafiyar tamkar ɗan shekaru biyu se gauraye wurin take. Tana buɗe d'akin Suraj ta hango Tasleem kwance sai shan barci take yi, k'arisawa tayi gaban gado ta durk'ushe tana shafa fuskar ta tana murmushi, Suraj ma sai ya tsinci kanshi da yin murmushin tun yana yi a zuci har ta koma dariya yana mai rungume Habeeb "Did you just saw what happened? Laylah ta tashi! She's awake and healthy! I can't believe this! I will have to call the doctor!!!" Kai Habeeb ya jinjina ya ɗan yi murmushi sai lokacin ya yi magana "Suraaaaj.......wayan naka yana down stairs." Ganin yanda Suraj ke laluma aljihun shi tamkar wawa yasa Habeeb faɗin hakan. Wata y'ar dariya yayi yana shafa kai sannan ya fice da sauri domin d'auko wayar shi. Sosai action nashi ya baiwa Habeeb dariya kawai duk suka bishi da kallo har ya fice. Ƙaran rufe k'ofa da Suraj yayi shine ya razana Laylah sai a lokacin ta fara tunano abunda ya faru wannan daren, tamkar flashes haka take ganin su before you know it ta rik'e kanta da hannu bibbiyu tana girgiza kai sai kuma ta zube ƙasa. Abun ya d'aure musu kai sosai Nurses d'in da wuri suka maida Laylah d'aki aka kwantar, ko da Suraj ya dawo shima sai hankalinsa ya tashi, har doctor ya k'araso ya d'an yi wasu gwaje-gwaje ya gama, bata farfaɗo ba. "Don't worry Suraj it is bound to happen, tunanin ta ne ke dawowa,and since abunda ya faru 8 months ago wasn't a pleasant one dole hakan ya faru, for now let her rest she'll be fine, idan akwai matsala do not hesitate to call me." Kai Suraj ya jinjina suka yi sallama da doctor Habeeb ya taka masa shi kuwa ko motsa wa bai yi ba daga inda yake zaune saida yaji k'iran sallar magariba sannan ya tashi....... Duk dramar da ake yi Meenah bata ma sani ba domin bata ma cikin gidan tana chan garden tana zaune bata damu da sauron da ke shawagi ba tsabar masifa shima Suraj bayan abunda ta aikata wa Tasleem bai nemeta ba infact farin ciki ne ma ya lullub'e shi tunda Laylah ta farka. Wajen ƙarfe takwas na dare ya shigo d'akin da sallamar sa, wannan karon Laylah da kanta ta amsa sallamar tana jingine bisa gado ba tare da ta dubi idanuwan sa ba ko ɓangaren da yake Yana ƙaraso wa ya zauna daga bakin gadon yana kallon ta, har lokacin bata d'ago kai ba. "Hey.....yaya jiki?." Iya kalmar da Suraj ya iya furta wa kenan domin kalaman yi mata magana ma sun b'ace daga kwanyar sa. A takaice ta amsa masa "Alhamdulillah" Shima kawai kai ya jinjina ba sake cewa komai ba na about 2 minutes sai kuma yayi gyaran murya yana satar kallon ta daidai lokacin ta d'ago kai suka yi ido huɗu se kuma ta juya, Tasleem ce ta shigo da murnar ta tana rungume Suraj "You are right Daddy! See!... My hand is not hurting anymore" Rungume ta yayi yana dariya sannan ya sake ta ya ɗan ja hancin ta yace "i told you it won't hurt daddy's gal!...... Ganin wannan connection d'in tsakanin su ya burge Laylah tuni idanuwan ta suka cicciko bata ankara ba taji Tasleem ta fad'o jikin ta "Mommy! Kin tashi!!" Murmushi tayi sannan ta rungume Tasleem sosai a jikin ta tana sakin kwalla masu d'umi shidai kallon ta kawai yake kamar zai yi hauka especially idan ya tuna cewa irin wannan warm hugs d'in bazai samu ba daga Laylah no matter how bad he needs it. Mik'e wa yayi zai fita, gam gam yaji Tasleem ta rik'e hannun shi "Ka zauna a nan, mommy will feel better if you are here" Ba tare da ya juyo ba ya tsaya chak ya lumshe ido tamkar mai yin nazari, a hankali ya juyo ya shafa kan Tasleem yace "talk to your mommy I'll be back." Kai ta jinjina ya koma gun Laylah tana dariya "Mommy Daddy Muhseen ya bani wani takarda in baki harda phone nashi. Bin ta Laylah tayi da kallo cike da mamaki har ta fice daga d'akin, bata wani ɗauki lokaci ba ta dawo riƙe da wata envelope ta mik'a ma Laylah, hannun ta na b'ari ta anshe envelope d'in ta yaga bakin sa sannan ta ciro Papern da kuma waya ta ɗan nisa sannan ta buɗe Papern. Tun tana zaune bisa gado bata san lokacin da ta mik'e tsaye ba hawaye na tsere kan kumatun ta, tana gama karantawa ta duk'unk'une takardar a hannun ta sannan tayi wurgi dashi, paper dai bata tashi fad'uwa ba sai gaban Suraj wanda isowar sa kenan ɗauke da plate na abinci, durk'usawa yayi ya ɗauki Papern sannan ya ajiye plate d'in ya bud'e don ya karanta. Sedai saɓanin Laylah shi dariya ce ta kufce masa irin sosai ɗin nan. Jin dariya yasa Laylah ta juyo shi kuma sai yayi saurin saka Papern cikin aljihun shi ya gimtse dariyar. Share hawayen ta tayi ta dube shi with a fit of rage tace "Please Suraj......i want to be alone" ko musu bai yi ba infact da murmushi ya jinjina kai yace "As you wish darling, idan kin huta ga abinci ki ci bazan so ki zauna da yunwa ba ko kaɗan". Mamakin yanayin sa tayi amma sai ta basar tacigaba da kukan ta, Tasleem na share mata hawaye.....Duk wannan wahalar, duk gwagwarmayar da na sha, all the sufferings you cost me.......is this the end of it? Muhseen you don't even have the courage to face me...... I wish you gave this to me youself wallahy da sai na fanshe duk azabtarwan da kayi min, i would have chopped you up into pieces ta hanyar da babu mai iya maida ka. Because of your selfish intrest you......."+ Bata k'arashe maganar ba tsabar takaici da kuma jin haushin kanta, tsawon lokaci ta ɗauki laifin ta d'aura wa Suraj ashe dai komai cikin duhu aka yi shi, but wanda yafi kowa laifi shine mahaifin ta da ya kasance babban kobo, da har za'a yi blackmailing nashi da kalamai ya ƙi gaskiya ya d'aura d'amarar tarwatsa farin cikin y'ar sa. "What kind of a father could do that?" Laylah ta k'arashe maganar tana hawaye. Juyawa tayi ta dubi gadon Tasleem na zaune tayi shiru tana kallon ta, murmushi Laylah ta sakar mata sannan ta dawo kan gadon ta zauna tana mai jan d'iyar tata a jiki "Me ya samu hannun ki? Yaushe kika ji ciwo" Tab'e baki Tasleem tayi ta ce "Ba Aunt Meenah bace ta bangaje ni na fad'i.....kuma ita ne ta tsaya a hanya na......." Rufe bakin Tasleem Laylah tayi da murmushi tace "it's ok baby, ya kamata ki dinga kallon hanya in kina tafiya" kai Tasleem ta girgiza ta langabar hakan ya bata dariya ta ce "i missed that kinda look" washe hak'ora Tasleem tayi ta kwanta kan cinyar Laylah tace "i missed you too mommy"..... Yana fita ya shiga d'akin sa infact bai da wani tak'amammen dalilin shigar sa d'akin se zagaye zagaye yake yana dariya, zama ma ya gagara a gun Suraj haka yayi ta busy na k'arya kusan 30 minutes lokaci zuwa lokaci yakan buɗe Papern ya sake karantawa. Mik'e wa yayi daga coffee chair d'in da yake zaune ya nufi terrace. Rufe ido yayi yana shak'ar sassanyar iskan dake busawa kafin yace "At long last! Finally i have another opportunity to make you mine for ever and ever! Ban damu ba ko me zai faru I don't give a damn!!! LAYLAAAH!! LAYLAAAH!! LAYLAH!". Ƙaran taku da yaji ne yasa shi gimtse maganar ya juya at once, ganin Khadijah da Mubeenah yasa shi sauk'e nannauyan ajiyar zuci. K'arasa wa suka yi inda yake Mubeenah ta rufe k'ofar da ta sada d'akin da terrace sannan suka juyo suna kallon shi. Wani ɗan iskan dariya Suraj yayi irin na rashin gaskiya yana sosa kai "Hey ladies! What brings you here? Akwai matsala ne?" Murmushi suka yi a tare Khadijah ta ɗan gyara murya sannan ta ware tafin hannun ta wanda ke ɗauke da churarren paper. "i guess this belongs to you?.." Ta fad'a yayinda ta tsare shi da ido. Zaro idanuwa yayi waje ya dafe goshi sannan yace "ta yaya kika samu wannan Papern? How!!" Khadija ta yi dariya tace "hmmmm.....now that you have asked! Ba mu ne muka samu Papern ba shi Papern shi ya same mu ai" Kai Mubeenah ta girgiza tace "Yess! Kuma mun karanta especially ma wajen da Muhseen ya ce "I'm sorry Laylah, na sake ki saki Uku".. Mubeenah ta dubi Khadijah tace "ina ganin ban yi mistake ba a abunda na furta ko kuwa"?? Kai Khadijah ta jinjina alamar "Ehh". Zaro ido Suraj yayi yana kallon su baki a sake sai kuma yace "You ladies are something else! Even after knowing sakamakon da takardar ta bayar i can see you are smiling...... Does this mean that we are on the same team???". Tab'e baki Khadijah tayi Mubeenah ta haɗa gira ta mik'a masa Papern sai kuma suka juya, shidai Suraj har jikin sa yayi sanyi saida suka isa k'ofa sai suka bushe da dariya shima da yaji hakan sai ya ɗan saki ransa Mubeenah tace "Idan bamu yi supporting d'in ka ba who will? Of course we are hundred percent on your side Suraj bro, because we are team Laylah_Suraj!!" Suna kai nan suka fice suna dariya shi kuwa tsabar daɗi ji yayi tamkar yayi ihu kowa ya ji. Ta kai rabin awa zaune har Tasleem tayi barci, sai wani ƙara da cikin ta ke yi. Ji take tamkar bata ci abinci ba na sati guda, har ta kai ta ga riƙe cikin tana yamutsa fuska, sai lokacin ta tuna da abincin da Suraj ya kawo d'azu ai kuwa jiki na rawa ta janyo plate ta yi Bismillah sannan ta fara afka lauma, a wannan lokacin d'and'anon abincin ko rashin sa duk bata bi ta kai ba infact saida ta d'auki lomar k'arshe sannan ta fahimci sakwara ce bisa plate da miyar ganye. Kwarewa tayi nan take ta fara tari, sai lokacin Suraj da ya jima tsaye a k'ofa ya shigo da sauri ya zuba ruwa a cup ya mik'a mata, babu shiri ta karb'a ta kafa a baki ba tare da lura da wanda ya mik'a ba. "Sannu.... " Ya furta a tak'aice yana gyara zaman sa bisa bedside drawer yana wasa da kofin da ya bata ruwan, "Nagode." Ta amsa masa ba tare da ta d'ago ba ta ce "Dare yayi, meyasa kazo nan a wannan lokacin? Kasan bai kamata ba your wife might feel bad about this".. Murmushi yayi kawai ya mik'e ya nufi k'ofa zai fita. Chan k'asan mak'oshin ta tace "What the...... How mean! Dubi daga magana kawai se ya wani kama hanya ya tafi without even a heart soothing word! Coward!!!" Ta k'arashe maganar da rolling idanuwan ta tana bin shi da kallo. Sarai ya ji abubuwan da ta fad'a kawai de ya basar ne ya cigaba da tafiya cikin ranshi kuwa wani sanyi yaji da daɗin kalaman nata. Turus yayi a k'ofar don ganin su Mubeenah tsaye tamkar shi suke jira. Gira Mubeenah ta d'aga masa alamar tambaya hannuwan ta nad'e a K'irji "Naga kana murmushi......what exactly were you doing in there a wannan lokacin? Dare yayi, go take care of your pregnant wife ka barmu mu kula da y'ar uwar mu a nan, come on!! Leave!!" Wangale baki Suraj yayi da mamaki yace "Oh! So abun haka ne? Fine then.....i will surely go and look after my pregnant wifeee carry on...sai da safen ku." Yana kai nan ya ratsa su ya wuce yana dariya suma dariyar suke kafin suka shiga d'akin da Layla take........ Washegari...... Dawowarsa kenan daga morning jogg duk yayi zufa, wurgi yayi da water bottle na hannun shi bisa kujera ya nufi stairs, cikin sauri yake tafiyar bai ankara ba yaji sun ci karo kaɗan ya rage ta zame tayi baya amma sai yayi saurin figo ta jikin shi hakan yasa yayi loosing balance suka zube ƙasa tsabar yanda ya bugu har saida ya saki ƙara "Aahh!!! Aahshh! Ya ilahy!! K'are wa jikin sa kallo tayi da ta dubi manyan damatsan hannun sa dake shek'i saboda zufa da sauri ta dafe su da hannayen ta zata tashi amma santsin zufan ya ja hannun ta sake fad'o wa kanshi, tsabar kunya sai ta k'ank'ame idanuwan ta tana tunanin yanda zata yi, kallon fuskar nata yayi na wasu dak'ik'a kafin ya sa hannu ya tura ta gefe, da sauri ta mik'e tsaye K'irjin ta na dukan uku uku. "What on Earth!!....... Me kike ci haka? Ko dai mutum biyu ne suka fad'o kaina??" Ya k'arashe maganar yana duba bayan ta ko da wata wanda ke tsaye. Ita de kallon sa take baki sake bata ce komai ba... Dafe bakin sa yayi da tafin hannun shi alamar mamaki ya nuna ta da ɗan yatsa "it's really only you! Ke.....kke...ke kaɗai ce!! Unbelievable!! Nauyin da naji a kaina yafi ƙarfin haka, saida na kusa sumewa..." Haɗe rai tayi ta kumbura baki kafin tace "Ai bani nace ka taimaka min ba kai ka ga dama, kaga da ace baka riƙe ni ba da baza ka tsinci kanka a wahalallen yanayi ba..." Tana kai nan ta wuce ta barshi a wajen, shi kuwa dariya yayi yana sosa k'eya.........

Post a Comment for "IN SO YAKI NE CHAPTER 14"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...