IN SO YAKI NE CHAPTER 11 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

IN SO YAKI NE CHAPTER 11

IN SO YAKI NE CHAPTER 11

- - Post a Comment
IN SO YAKI NE CHAPTER 11


  K'ara speed d'in motar Ameer yayi su ma sai suka k'ara gudun nasu, maimakon ya tsaya se ya d'au hanyar fita daga garin, dad'in hakan suka ji domin kuwa a nan ma aikin su zai fi tafiya smoothly. Ai kuwa bai ankare ba ya hangi wasu manyan motoci biyu sun nufo shi gadan gadan, duk iya k'ok'arin shi na yaga ya kauce musu ya ci tura ko da ya juya bayan sa ma wasu bak'ak'en jeeps ne guda biyu kafin ya juyo yaji motar da yake ciki wuntsila se glasses dake tarwatse wa luckily ma ya d'aura seat belt, karaf d'aya Ameer yaji tamkar ba a duniyar yake ba ko ido baya bud'ewa ga jini dake bin kan sa yana k'ok'arin wanke masa fuska, upside down yake kallon d'aya daga cikin babbar motar ta sake yin kanshi, shidai ya san tashi ta k'are amma se ya saki murmushi ya rufe ido don ko bu'de baki ya kasa, K'ara kawai kake ji se juyi da motar take yi kan titi tana tumbling kafin tayi gefe ta bugi da bishiya, upside down take se tires da suke ta juya wa... Biyu daga cikin mutanen ne suka fito suna lek'a motar da Ameer d'in yake "DAMN!!" Cewar babban nasu "Ba Suraj bane wannan yanzu yaya zamu yi?" D'ayan yace "Kamata yayi mu bar nan! Ko yaushe daga yanzu zamu iya shiga cikin matsala kawai ka buga wa boss ka sanar da shi aikin shi ya kammala tunda mun riga mun karb'i kud'in mu full cash kawai mu ware" "kuma fa ka zo da shawara bari kaga na k'ira shi Boss d'in" cewar babban "Boss! Komai ya tafi yanda ake so Suraj ko da ya fito a raye toh bazai kai labari ba! Aikin ka ya kammala!" Wani wurgi Sa'eed yayi da wayar bisa gado ya bushe da dariya sannan ya juya ya dubi Muhseen dake zaune kan resting couch yace "k'urunk'us kan d'an b'era! This is what you deserve Suraj! Ai ina ganin nayi maka ma da sauk'i it would have been better idan nine na murk'ushe ka da hannu nah! " Muhseen! Your job is done! Ga kud'in ka chan... All you have to do is ka sake min kurciya ta, ina fatan ka fahimci abunda nake nufi? Divorce Laylah and send her here to me safe and sound like a bride! I will show her how a real man should be! Seven years later Suraj lays his hand on me because of that village bitch so barin rama tsiya da alkairi. I will have her on my bed tomorrow night! Anything goes wrong then u are a dead meat Muhseen!".. Kai Muhseen ya girgiza a d'an tsorace yace "tabbas zan kawo maka ita, i won't let you down, amma what about her daughter?". Sa'eed yayi dariya yace "atleast har yanzu yarinya ce ita, so ya kamata Suraj ya samu mai yi masa addu'a! A kaita tayi kallon farko kuma na k'arshe wa mahaifin ta".... Bushewa Sa'eed yayi da dariya ya kwanta shame shame kan gado yana wak'a for his victory ya kunna Tv yana jiran BREAKING NEWS....... Driving yake yana ta surutu da Boboh se dariya yake, Traffic light ne ya sa red don haka ya ja birki mik'ewa Boboh yayi ya tsallaka back seat yana lek'a waje ya rik'e glass d'in motar da k'ananan hannuwan shi se dariya yake. Gefe Suraj ya duba don yaga dalilin dariyar Boboh, karaf suka had'a ido baki sake yake dariya ita ma dariyar Laylah take yi ta d'ago masa hannu, ido ya kashe mata yana murmushi sannan ya maida duban shi ga green light da ya bayyana a trafic post din haka ya take motar yacigaba da tuk'i Tasleem na ta making funny faces wa Little Suraj (Boboh) har suka wuce sannan ya maido da kanshi cikin motar yana surutai...... BREAKING NEWS.... "Hello i am Sandy Gabriel and welcome to business ethics here with me is Mr Sufyan k. "Mr Sufyan speaking of business, about twenty five minutes ago we've recieved a very shocking news that one of your friend in Business Mr Suraj Abdoul-maleek was involved in a tragic accident though uptill now there was no news of whether he is alive or death, what do you have to say about that?" Sufyan: it was indeed a shocking event i still can't get through it tun lokacin da aka sanar da ni, let's just hope Suraj is safe and sound........" Paper cups d'in hannun shi dake cike da coffee Habeeb ya sake duk suka malale a k'asa jiki na b'ari idanuwan shi sun sauya launi da gudu ya koma inda ya bar Khadijah zaune, ita ma ganin yanayin shi yasa ta tsorita ta mik'e "What happened? Ina ka shiga tun d'azun? Saura about ten minutes jirgi ya tashi and you.......... Habeeb wai me ya faru ne? "It's Suraj!...... He.....He had an accident...i just saw it on Tv mu koma gida please, i just hope he is alright." Zaro ido khadijah tayi tana fad'in Innalillahi wa inna ilayhir-raji'uun!" Jakarta ta rataya sannan ya fisgi hannun ta suka fita, kasancewar driver ya koma da mota sai suka shiga taxi, tun suna Hanya yake dialling numban Ameer bata shiga, don haka yayi dialing numban Mubeenah "Ya Habeeb.....i just saw the news, ban san ya zanyi ba, Meenah is devastated kuma har yanzu ko magana bata yi, i have been trying Ameers number bata shiga what do i do? Ki bari gani nan zuwa, ni ban ma san location na accident d'in ba ballantana asibitin da aka kai shi just brief naga news d'in na rasa ta inda zan fara "Specialist Hospital muke yanzu shigowan mu but bamu samu ganin shi ba Habeeb pls hurry i can't handle Meenah alone". "da Sauri Habeeb ya umarci driver da su nufi specialist hosptl Suraj har ya kai Boboh school ya kuma samu admission d'in sannan ita ma Laylah tayi enrolling Tasleem a tare suka fito daga offishin principal d'in tana bin shi a baya tana murmushi "Why are you smiling?" Ya tambaya ba tare da ya juyo ba Da sauri ta dake tace "Ni? No!....m...mme zai sa ni murmushi? I am not smiling at all" ta k'are maganar tana girgiza kai harda mak'e kafad'a cikin ranta kuwa tace "Jinnu ne kai? Ko magician?" Murmushi yayi yace "Babu ko d'aya," Zaro ido tayi waje ta shige gaban shi ta tsaya tana kallon shi "Yaya akayi kasan me nake fad'a?" Kashe mata ido yayi yace "be careful when you are around me coz i can read minds" Ya k'arashe maganar yana ture d'an yatsar ta da ta nuna shi sannan yacigaba da tafiya... A harabar makarantar daidai inda suka yi parking ta dubeta yace "So...." Itama kallon shi tayi da sigar tambaya tace "Sooo??" Chocking smile yayi yace "Are you free? I mean now that i have met my daughter i would like to buy something special for her, in bazaki damu ba accompany me lets go shopping". Tab'e baki Laylah tayi tace "Why me?" "Because you know her better than me, i need hints about her hobby, favourite colour, what makes her happy da sauran su... I hope kin gane?" Murmushi tayi tace "shikenan muje, but zan baka first and important hint! Tasleem is just a photocopy of you. Son jiki gareta, ga tsoro kuma kamar de kai she is allergic to cinnamon" Seatbelt ya d'aura yana murmushi a ranshi yace " Wato nine matsoracin ko? I'll show you!". Random shopping ne tunda babu specific abunda yaje siya haka ya dinga tarkata ma Tasleem tun Laylah na shiru har ta fara complain da kyar tayi convincing nashi a kan ya isa haka, ya ciro debit card ya mik'a kenan karaf idanuwan sa suka sauk'a kan Tv dake aiki. Tabbas motar sa ce don ga number plate d'in Da sauri ya dubi receptionist d'in ya ciro residential card nashi ya mik'a mata "Pls in kun yi parking send it to this address" Bai tsaya wata wata ba ya fice Laylah na biye da shi duk ta rud'e saboda ganin yanayin shi... Tana shiga motar Suraj ya tada motar se lokacin yace "Ameer......Ameer! Laylah Ameer had an accident! Kuma an d'auka ni ne! Ya Allah protect my brother...." ya k'arashe maganar yana hawaye Seven years kenan rabon da Laylah taga Suraj so desperate haka, kasa d'age ido tayi daga fuskar shi cike da tausaya wa..... Wani wahalallan parking yayi wa motar wanda ya janyo hankalin gangamin press dake jira a bakin asibitin domin su ji state na lafiyar sa Da mamaki duk suka juyo kowa tambayar dake kansa shine "Idan wannan Suraj Maleek ne toh wanda yake ciki kuma waye kenan?, kanshi suka yo kowa da nashi tambayar babu ko sassauta wa, ji yayi duk duniyar tayi masa zafi bai bi ta kansu ba ya kutsa ta cikin su ganin haka yasa Laylah ta yi saurin rik'e rigar shi don idan ta tsaya zasu murk'ushe ta, juyo wa yayi yana kallon ta kafin ya kamo damtsen ta ya figo ta saida suka shige entrance na asibitin sannan ya sake ta "Sorry......" ya furta chan k'asan mak'oshin sa ita ma da murmuring tace "it's okay".+ Su ma wanda suke reception da mamaki suke kallon Suraj kafin yayi magana ma suka ce "Ka bi Hallway na dama O.T (operation theater) yana......." Bai jira ta k'arashe maganar ba ya sa gudu ya nufi inda ta kwatanta masa Habeeb ya hango tsaye ya jingina da bango Mubeenah na zaune ta had'e kai da gwiwa, ita kad'ai ya fara ji a zuciyar shi because irin shak'uwar ta da Ameer baya misaltuwa "Habeeb!". Suraj ya k'ira shi cikin rawar murya Duk kusan tare suka juyo jin muryar wanda basu yi zato ba, zaro ido Mubeenah tayi ta dubi k'ofar OT d'in sannan ta juyo ta dubi Suraj labb'an ta har suna vibration tace "Ssu.....su....SURAJ??!........ It's really you? You are perfectly alright!" Sai kuma ta dubi Habeeb ta sake kallon Suraj tace "WAIT! WAIT!......Idan wannan Suraj ne and he is safe and sound then who is.......? Who is in the operation room?" Ta k'arasa maganar tana sauk'e numfashi da kyar tamkar wanda aka shak'e Kasa magana Suraj yayi se kuka se lokacin Habeeb ya fahimci inda Suraj ya dosa "No! No no .... Suraj you must be joking it can't be Ameer right?" Sai lokacin Suraj ya girgiza kai ya rungume Habeeb yace "It's him Habeeb it's Ameer, ban san me ya faru ba, all i know is lokacin ina wanka Ameer took my car keys, ban san me yasa yayi hakan ba it would have been me but now....." Kai Mubeenah ta girgiza tace "hah! Oh come on Suraj kar ka min wannan wasan! Ameer fa lafiyar sa lau yaje karb'an sak'o a gun wani friend nashi, it can't be him........ I'm sure yanzu haka ya koma office lemme call him!" Wayar ta ta d'auka ta fara dialing numbar Ameer su kam se suka saki baki suna kallon ta musamman Suraj da yafi kowa feeling guilty saboda a motar sa Ameer yayi hatsari Daidai lokacin aka fito da Ameer, turus Mubeenah tayi ta k'ura wa stretcher d'in ido tana kallon fuskar Ameer, karkarwa hannun ta ya fara wayar ma da ta kara a kunne sulale wa tayi se fad'i take ta tarwatse Ita ma gwiwa ta zuba a k'asa tana kuka da sauri Laylah ta rik'e ta khadijah ta d'ebo mata ruwa a dispenser ta bata da kyar ta karb'a Ko da ta d'ago ma bata ga Suraj da Habeeb ba don haka ta mik'e da Sauri ta bi hanyar da aka yi da Ameer Khadijah da Laylah suka bi bayan ta cikin sauri "Doctor please...... Do your very best and save my brother!" Suraj ke maganar cikin gigita ganin haka yasa doctor yace "Calm down Mr Maleek..... Your Brother is out of danger, he had a narrow escape from death i don't know how but let's say Ikon Allah ne! There are about four fractures in his body , including two left rib bones and that is why we recommended immediate surgery, and it was successful! hannun shi na dama ma a karye sannan ya samu karaya a cinya Se kuma buguwa da yayi a kai, akwai specialised neurologist yanzu zai duba shi sannan idan an babu matsala we'll let you know for now please let's pray and hope he will be perfectly alright". Likita na rufe baki Mubeenah dake tsaye bakin k'ofa ta yanki jiki ta fad'i da sauri wasu nurses suka yo kanta domin bata taimakon gaggawa hankalin Suraj ya tashi ya ma rasa inda zai yi guda d'aya. "Suraj.....khadijah zata kula da Mubeenah for now let's go to Ameer". Ya kai kusan Mintina biyu da yin maganar Suraj na tsaye tamkar wanda aka dasa. "SURAJ!" Da sauri ya d'ago kai saboda yanda Habeeb ya k'ira shi se cewa yayi "Ok.." Kai Habeeb ya girgiza yana tunanin kar Bp na Suraj ya tashi don abun zai yi masa yawa don haka yace "ka san me? I think you should go home, Meenah ita kad'ai ce kuma i'm sure bata samu labarin cewa ba kaine kayi accident ba go and cheer her up, by now nasan an tashi su Boboh daga school zan jira a nan zan yi duk abunda ya dace i'm sure yanzu haka ma su oummi sun iso please control yourself you know better that kai ma ba isasshen lafiya ne gareka ba just go home and rest a bit se ka tura driver ya d'auko Boboh...... Laylah ce ta iso inda suke ta tsaya, suna had'a ido da Habeeb ya kawar da kai gefe "Sorry to interrupt, Suraj zan je in d'auko Tasleem a school in bazaka damu ba se in taho da Boboh" ta k'arashe maganar tana kallon Habeeb "No thank you! We don't need your sympathy Laylah we can handle our family problems so stay out! We apperciate your care and concern but that's enough now! Please leave and don't go any where near my son". STORY CONTINUES BELOW Kalaman Habeeb ba k'aramin ciwo ya ji wa Laylah ba a zuciya tuni idanuwan ta suka cicciko, jiki a sanyaye ta juya ta bar wajen. Suraj cike da mamaki ya juyo yana kallon Habeeb "Why? Why Habeeb? Yaya zaka yi mata irin wannan maganan? How could you be so mean?" Dafa kafad'ar Suraj Habeeb yayi yace "No Suraj i am not being rude i am trying to show her her rightful place, matar aure ce ita yanzun, kuma na tabbata tun safe kana tare da ita, baka tunanin hakan zai iya jawo mata matsala? Don't misunderstand me na san abunda nake yi, already i saw it at the party Muhseen was just playing cool amma he looks suspicious, let her go Suraj ". Yana kai nan ya juya ya bar wajen Suraj ya fita da sauri yana neman inda zai ga Laylah amma ya rasa ta, mota ya shiga a fusace ya fisge ta har tires suna k'ara ya fice daga harabar asibitin, gida direct ya nufa ko kwak'waran parking bai yi ba ya fito ya nufi cikin gida, yana sa k'afa a living room ya hango ta zaune bisa carpet ta had'e kai da gwiwa, jin motsin shi yasa ta d'ago kai tana kallon shi, da farko tayi zatan gizau yake mata amma da ta fahimci shi d'in ne sai ta mik'e da gudu ta d'afe jikin sa ta rungume tamkar zata shige cikin shi "Suraj you scared me! I know you will be fine, na sha fad'a wa Mubeenah it wasn't you but she didn't believe me, Alhamdulillah Allah ya dawomin da kai safe and sound".... Zame jikin shi yayi daga nata ya barta tsaye a wajen ya haura stairs ba tare da ya kula ta ba ko furta kalma. Bin shi tayi da kallo tana share hawayenta ta ce "ban damu ba duk abunda zaka yi, all i want is for you to be safe wannan kad'ai ya ishe ni Suraj"... ***** ***** ***** A fusace ya mik'e yana kallon TV idanuwan shi sun kad'a sai cije baki yake, wata room service ce ta shigo da food trolley daga trolley d'in har abincin da ya sa aka shirya ya sa hannu ya mangare se k'aran fashewan tangaran kake ji , a tsorace matar ta rakab'e jikin bango tana k'ank'ame jikin ta "Get lost!..." Ya daka mata tsawa ba shiri ta ruga waje da gudu "Suraj! U had a narrow escape today but i'll get you next time! Now zan je in ji da wad'ancan k'ananan kwarin! Ni zasu cuta su yi min k'arya? They said Suraj ne a motar how comes he's totally safe?" Wayar sa ya d'auka da makullin motar shi ya fice yana k'iran numban Muhseen...... "Million goma na biya su domin suyi min aiki, i paid them full cash but they betrayed me! Duk inda suka shiga ina so nan da 24 hours a gurfanar da su a gaba na, ka same ni a bar and make aure you come with Laylah this time i won't go easy on Suraj! I will hurt him to the core....." Kashe wayar yayi ya shige motar shi yayi gaba. Muhseen na kashe wayar ita kuma Laylah tana shigo wa hannun Tasleem cikin nata, Murmushi ya saka harda sa nannu ya shafa fuskar Tasleem Abun wani banbarakwai suke ganin shi don basu saba da kindness ba daga Muhseen, ture hannun shi Tasleem tayi daga fuskar ta tana kallon cikin idon shi da fararen idanuwan ta kafin ta murgud'a masa baki ta ruga da gudu zuwa upstairs. Cije leb'e yayi yana k'ok'arin b'oye b'acin ran shi se ya saki murmushi ya dubi Laylah yace "It's ok yarinya ce, i know it will take long for her to trust me or even like me but don't worry komai zai dawo daidai" yana rufe bakin shi ya matso daf da Laylah ya fara kissing nata ita de tayi gaho tana ganin ikon Allah ba ta motsa ba sannan babu wani shauk'i da ya d'ebe ta se ma dunk'ule hannuwan ta da tayi don ji take tamkar ta murd'e wuyan shi, don kan shi ya d'auke bakin shi daga nata sannan ya ce "Na shirya special dinner gobe, ki shirya around 8:00pm it will be super romantic, just na fad'a miki ne so that you should get ready" Yana kai nan ya wuce yana shu'umin Murmushi ta bi shi da kallo har Ya fice sannan ta sa hannu tana goge lips d'in ta "I don't trust you Muhseen! You must be upto something! Ko ma minene zan gano ai!" tana kai nan ta haura upstairs zuwa d'aki duk taku d'aya idan ta d'auka maganar Habeeb ke haunting d'in ta ga kuma ta wani b'angaren wannan sabon salon na Muhseen yana bata mamaki ta rasa ma me ke damun ta kwata kwata....... Oummin Habeeb, Sapna da Abba a lokaci d'aya suka shigo, daidai lokacin Habeeb zai fita "Oummi sannun ku da zuwa, Da yanzu zan je in d'auko ku diga airport" Murmushi tayi tace "No need son tunda gashi Allah ya kawo mu! Ya ya jikin Ameer d'in? " Ummi har suna had'a baki da Abbah wajen tambayar. "da sauk'i" Habeeb ya amsa musu idanuwan shi kan Sapna dake rakab'e a gefen Oummi ya kad'a kai yacigaba da cewa Yanzu haka yana ICU, Mubeenah yanzu ta farfad'o shine zan siyo wad'annan magungunan don tana buk'atar su" Kai Abbah ya girgiza sannan yace "Inaaa....shi Suraj d'in? "Suraj na ce ya koma gida, daman shima baida lafiya likita yayi recommending cewa yayi avoiding stress da kuma damuwa, idan yana nan kuma he will be more than stressed". "Gaskiya ne, you did the right thing, Allah ya muku albarka baki d'aya, bari muga Ameer d'in idan zasu bari in yaso se mu duba Mubeenah" Dad ya k'arashe maganar yana tafiya su oummi na biye da shi "Eh zasu bari but da d'add'aya not all at once" Cewar Habeeb sannan ya wuce ya nufi pharmacy don siyan maganin Mubeenah....... Ta dad'e tsaye tana knocking k'ofa Suraj bai bud'e ba, gajiya yayi da disturbance d'in ya mik'e a fusace daga shi sai boxer ya bud'e mata k'ofar, k'are wa juna kallo suke yana kallon tray d'in hannun ta dake d'auke da lafiyayyen pounded yam da egusi soup a gefe guda kuma power horse ne mai sanyi har yana naso se water bottle, juya wa yayi ya koma kan resting couch ya zauna ya bar ta tsaye a gurin, kai ta kad'a da murmushi ta k'arisa cikin d'akin, abincin ta ajiye saman side table sannan ta zauna kan couch d'in ta fuskance shi "Suraj i know you are sad and worried about Ameer but in the process kar ka manta da lafiyar ka, atleast eat something don't......" Bata k'arashe maganar ba Suraj ya yi murmushi yace "You need the food more, na tabbata baki ci komai ba tun breakfast gashi har yamma tayi come on.....eat." Ya k'arashe maganar yana sa mata loma a baki babu yanda ta iya se ta karb'a saida ta had'iye tace, "Idan baka ci ba yanzu i promise you ni da baby bazamu ci komai ba zamu fara food strike" dariya yayi yana kallon ta se yace "Fine then..... I will eat but on one condition..... Sedai idan tare zamu cinye don wannan yayi min yawa ni kad'ai" "Hah! Look who is talking!! Wannan d'an abincin ne yayi maka yawa? Na yarda a hakan ma inde zaka ci Bismillah". Haka ta ja hankalin shi saida suka cinye abincin sannan ta tattare plates d'in ta fitar. Wayar ta dake gefen sink ne ya fara ringing da sauri ta d'aga ganin Habeeb ne ke k'iran ta "Meenah how's Suraj? Is he alright?" "I don't know Habeeb......na de yi managing na sa shi ya ci abinci but he seems dull, i am afraid i can't handle him for long ya rufe kanshi a d'aki da kyar na samu ya bud'e." "Don't worry babu abunda zai faru i'll call him" Nan suka yi sallama ta ajiye wayar juyawan da zata yi se ta hango shi yana sauk'o wa daga stairs har ya sauya kaya ya shirya tsaf cikin jar t-shirt da bak'in jeans yana kad'a key d'in motar shi. Boboh ya hango zaune tsakiyar falon se birkita takardu yake Iman na ta rarrafe tana zagaye falon ga toys nan ko ta ina, murmushi yayi ya k'arasa cikin falon ya d'auke Iman yana mata wasa Boboh na ganin shi ya mik'e da gudu ya rungume shi "Daddy zan bika" Hannun Boboh ya rik'e ya zauna bisa cushion yana jan kumatun shi iman ko tayi lamo a jikin shi da alama barci take ji "Zaka bi ni? " ya tambayi Boboh da sigar zolaya, kai ya gyad'a yace "Eh" "Alright je ka Mommy Meenah ta shirya ka duk ka b'ata kayan ka da chocolate" Da gudu ya nufi hanyar kitchen bai ma yi magana ba Meenah ta kama hannun shi zuwa d'akin Suraj don yawancin kayan shi suna nan saboda sometimes idan rigimar shi ta tashi nan yake kwana. Basu d'au lokaci ba ya fito da gudu yana dariya ya fad'a jikin Suraj "I'm readyy........" ya fad'a yana washe hak'ora, mik'e wa Suraj yayi yana kallon Meenah yace "zaki je ne?" Kamar daman jira take ta kad'a masa kai tana murmushi "Oya go get your mayafi ki same mu a mota" da sauri ta tafi d'aukan mayafin shi kuma ya kama hannun Boboh suka fita "Wannan motan daddy prince (Ameer) ne ina motan ka daddy?" "Mota na ya b'aci Boboh yau a motan Daddy prince zamu tafi Mak'e kafad'a bobo yayi yace "Oh oh ni bana so this car is too shmool" Dariya Suraj yayi yace "Toh babban mutum wanne motan kake so? Juyawa yayi ya dubi jerin motocin dake parking Lot ya nuna wata farar Royce Royce dake ajiye, shi kanshi Suraj tunda ya siyo ta sau d'aya ya hau don de kawai kullum masu aiki sukan goge motocin in sun samu free time shi yasa babu k'ura a jiki. Rufe motar yayi ya nufi wajen da farar motar ke ajiye se ya k'ira wani d'an saurayi dake kula da motocin ya ce "Bani key d'in motar nan" Da sauri ya mik'a masa key d'in Suraj ya amsa sannan ya shiga ya tada motar yana rungume da iman har saida Meenah ta shiga sannan ta amshe ta Boboh na ta tsalle a baya yana surutai... Yana ajiye su k'ofar aibitin suka shige shi kuma ya tsaya gyara parking. A reception ya iske su tsaye sai suka k'arasa ciki, Sallaman Meenah yasa suka d'ago kai Mubeenah dake jingine a gado ta dubi Islam dake barcinta a jikin Meenah tace "Sorry Meenah na barki da rigimar Iman......." Kai Meenah ta girgiza tace "Meye haka kike fad'i ? Babu komai Mubee Iman is also my responsibility besides babu wani rigimar da tayi mini, yaya jikin naki?"+ "Da sauk'i, please tell them su bar ni naga Ameer ni babu abunda ke damu na i just want to see him" Murmushi Meenah tayi tace "Mubee i know how exactly you are feeling, ki d'an k'ara hak'uri idan drip naki ya k'are se ki gan shi" Kai ta girgiza alamar "toh" kawai. Shi dai Suraj kallon su kawai yake yi kafin daga bisani ya juya ya fita Boboh na biye da shi har k'ofan ICU bai ma sani ba har suka shiga ciki tare shiru d'akin babu sautin komai se beeping sounds na computers dake aiki se sautin numfashin Ameer da yake sauk'a sama sama, k'arasa wa yayi daf da Ameer ya ja stool ya zauna yana k'are masa kallo, ya dubi k'afan da ya karye sannan ya d'aura hannun shi kan hannun Ameer a hankali yace "Hey......" Ga mamakin shi sai yaga Ameer ya juyo a hankali da kyar yake bud'e ido yace "S......s.suraaajj....., my brother...." Hawayen shi Suraj ya goge yace "I'm sorry Bro! Ban san meya sa ba but i feel guilty because it was my car that put you to this whole mess" Kai Ameer ya kad'a yace N.....noo Suuraj....it wasn.....It wasn't your fault! And i have no regret ko da ace ban rayu ba i would be glad! Da ace ban yi hakan ba it would have been you lying here! And i can't handle that, don't worry Suraj i am perfectly fine! Cike da takaici Suraj yace "what are you saying! How could you be perfectly fine a wannan condition d'in how can you pretend to be alright? Na tabbata ciwon da kake ji mara misaltuwa ne. Kuma me kake nufi da you have no regret?" Tari Ameer yayi yace "Your life is in danger Suraj! So also Laylah........... Ahhh!" K'ara ya saki saboda ciwon da yaji a k'irjin shi, da sauri Suraj ya mik'e yace "Be quiet Ameer kar ka fama ciwon ka just relax we'll talk later" Suraj ya mik'e zai fita Ameer ya rik'e hannun shi "ka saurare ni........Sa...Saa...SA'EED! SA'EED....." Jin kalmar da Ameer ya furta yasa Suraj ya juyo yana zare ido "what?....which Sa'eed? Ameer Sa'eed ne ya sa ka cikin wannan halin?" Kai Ameer ya kad'a yana hawaye da kyar ya bud'e baki yace "Shirin kashe ka yake yi, he was together with Muhseen in this.......Aarrh ..... Suraj Laylah ba ita ne tayi silar rabuwar ku ba Sa'eed shi ya shirya komai in the first place it was a conspiracy...." Nan Ameer ya kwashe labarin tattaunawar Sa'eed da Muhseen a daren party ya sanar da shi, nan take Suraj ya ji duniyar ta mishi d'aurin minti ji yayi kanshi na sara wa, kafin kace me Suraj ya dena ganin komai se duhu, Ameer babu daman motsi gashi yana gani a kan idon shi Suraj yana sulale wa k'asa da sauri ya dubi bobo yace "Boboh .....ahsh.. Hurry je ka k'ira daddy," Shi da bai san me yake faruwa ba ya fita yana wasan shi yana tafe har d'akin da Mubeenah take ya tura ya dubi Habeeb yace "Daddy prince yace kazo".... Da sauri duk suka mik'e suna mamakin Mubeenah tace "Boboh Daddy prince d'in ka ya tashi ne?" Kai ya gyad'a mata yace "Eh......suna magana da Daddy kuma Daddyn ya fad'i a k'asa......" Ai Habeeb bai jira k'arshen zancen ba ya ruga, ita ma Meenah tabi bayan shi. Wangale k'ofar yayi nan ya iske Suraj zube a k'asa, baki a sake ya dubi Ameer dake kallon shi sedai babu halin motsa wa, zaro ido Meenah tayi a tsorace ta zube gaban shi tana jijjiga wa, gashi kuma ICU suke babu daman d'aga murya, khadija ta juya da sauri ta k'ira likita, aka wuce da shi, admitting nashi aka yi Habeeb bai bar wajen ba saida Suraj ya farfad'o, yana bud'e ido ya fiffisge igiyoyin da aka manna masa na stimulation ta zuba sannan ya mik'e ya d'auki rigar shi yana saka wa, duk yanda Habeeb yayi ya hana shi fita Suraj ya tirje ya fice a fusace yana fad'in "Enough now Sa'eed! Ya isa haka! I can't take it anymore, you destroyed my whole life a lokaci d'an k'ank'ani now is my turn, i will make you pay!" Turus Habeeb yayi da jin kalaman Suraj ya ce "Sa'eed kuma?" wanne Sa'eed d'in?" Nan Suraj ya juyo ya kwashe duk yanda suka yi da Ameer ya sanar da shi, ji yayi kamar an murd'e masa zuciya se ya tsinci kansa da kasa hana Suraj fita hasali ma shi kanshi se ya bi bayan Suraj d'in da sauri suka shiga mota, garin ma yamma tayi don an riga da anyi sallar la'asar, tuk'i Suraj yake baya ma sauraron duk wani mota dake gaban shi don kawai overtaking nasu yake ba tare da bin k'a'i'dojin tuk'i ba.........

Post a Comment for "IN SO YAKI NE CHAPTER 11"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...