IN SO YAKI NE CHAPTER 10 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

IN SO YAKI NE CHAPTER 10

IN SO YAKI NE CHAPTER 10

- - Post a Comment
IN SO YAKI NE CHAPTER 10


  Da sauri yake tafiyar yana tafe yana juye juye Ameer kuwa yana rakab'e yana kallon shi "I am sure Muhseen is up to something, i don't like that guy, definately there's something fishy in ba haka ba me zai sa ya dinga acting suspicious? Ko ma menene i will find out" A zuciyar shi Ameer ke sak'e sak'en nan, sannan yacigaba da bin Muhseen har inda ya zauna kan wani resting chair, b'uya bai yi wa Ameer wahala ba saboda flowers da suka kare shi. Waya Muhseen ya fitar yayi dialing wata number wanda tayi kama da na k'asar waje, da alama video call ne, Ameer saida ya ja da baya da ya ga wanda yayi appearing a screen d'in wayar Muhseen baki na b'ari yace a ranshi "SA'EED??? It's really him! It.....it's Sa'eed? Miye alak'ar shi da Muhseen kuma? I will have to find out!"+ Wani Shu'umin murmushi Sa'eed d'in yayi sannan yace "Idan Muhseen ya k'ira ni a wannan lokacin am sure babban dalili ne! Tell me why have you called?" Murmushi Muhseen yayi yace "Tarkon ka ya kamu! Kamar yanda kayi predicting Suraj couldn't hold himself back when he saw Laylah infact saida yayi abunda yasa suka keb'e upstairs, amma ni sam ban fahimci me yasa kake aikata hakan ba aboki na. Da farko kayi brainwashing d'in mahaifin ta hakan yayi sanadiyyar rabuwar Laylah da Suraj and now you want them to come closer to each other again ban gane wannan chemistry d'in naka ba." Wani mugun dariya Sa'eed ya sa kafin yace "Saboda wannan y'ar Makiyayan da Suraj my life went through hell! Na tsawon shekaru bakwai na sa sun d'and'ana d'acin da nima naji now its time for me to play my games with them! Zan sa musu zuma a baki kuma in hana su lasa, it's going to be an intresting game! Just keep calm for now!" Muhseen ya yi dariya yace "Gobe Monday! Suraj will sign the papers finally zaka samu abunda kake buk'ata, da signature d'aya Suraj zai dawo fanko ko da allura bazai mallaka ba..." Kai Sa'eed ya girgiza yace "Kana tunanin Suraj mahaukaci ne? He is a highly intelligent person ba zai yi signing wad'annan papers d'in ba har sai mun tursasa shi, ba dai gobe zai fita aiki ba? Kasa mutanen mu kan hanya, i know how to get what i want from him kai de kawai kayi abunda zan fad'a maka zan turo maka text d'in abunda ya kamata kayi, enjoy the party for now". Wani Shu'umin murmushi Muhseen yayi ya mik'e yana dube dube sannan ya gyara jacket nashi sannan ya koma ciki tamkar babu abunda ya faru... Motsi na kwarai Ameer ya kasa yi, sai hawaye da ya wanke masa fuska, hankalin shi ya kasa d'auka cewa Sa'eed zai aikata duk abubuwan da yaji "I know my brother can stoop to any level but ban tab'a tsammanin zai aikata haka ba.... How can Sa'eed be so selfish? So shine ma yayi sanadiyyar rabuwar Suraj da Laylah! Kuma yanzu he is trying to harm Suraj again, he is conspiring against Suraj and Laylah!! In dai ina raye bazan bari wani abu ya same su ba i will not let you harm them!...... Da takun isa ya k'arasa table d'in, kujerar dake gefen ta ya ja ya zauna yana murmushi, suna had'a ido da Habeeb, Habeeb ya kawar da kai don shi ko kallon Muhseen baya son yi, Gefen Muhseen Ameer ya zauna kuma da gangan yayi hakan don ta gefen ne Muhseen ya ajiye wayar shi, Ameer ya ja plate ya d'iba abinci yana ci a hankali yana tsintar veggies d'in ciki amma a zahiri idanuwan shi kan wayar Muhseen take ai kuwa bai d'auki lokaci ba wayar tayi haske, karaf Ameer ya kwashe message d'in da kallo d'aya abunka da genius😉. Kawar da kanshi yayi kamar bai ga komai ba yacigaba da cin abincin. Isowar Suraj kan table d'in ne yasa Laylah ta d'ago kai, daidai lokacin kuma Meenah tayi pecking kumatun shi, har saida taji wani d'aci a bakin ta tsabar takaici ji take kamar ta fisge Meenah daga jikin Suraj, a garin takaici ta saki chokalin hannun ta ya fad'i k'asa , kafin kace me kowa ya maida duban shi ga Laylah Idanuwan ta suka cicciko tace "I......i'm S...sorry" Muhseen ji yayi ta yarfa shi gaban su dan haka ya saki murmushin dole sannan ya rik'o hannun ta ya matse gam sannan ya lankwasa, babu wanda ya gane abunda ke faruwa a lokacin, matso wa yayi daf da kunnen ta yace "Stupid woman! Spoon ma ya zama miki big deal? Can't you just for once do anything right?" Tsabar rad'ad'in da take ji saida taji tamkar ta saki fitsari a wajen, kamar an ce d'ago kanka Suraj ya sauk'e idanuwan shi kan glass credenza dake bayan su Muhseen, nan yaga abunda Muhseen ke aikata wa, Karkarwa hannun Suraj ya fara har ya kasa controlling wutar emotion dake ruruwa a k'irjin shi, Meenah ta lura da inda yake kallo sosai ta ga juriyar Laylah amma dole tayi controlling Suraj kar ya birkice musu a wajen, don haka ta damk'e hannun shi da nata sannan ta mik'e ta ja shi tana murmushi, duk su ma suka sakar mata murmushi.. Kitchen ta nufa sannan ta manna shi da jikin fridge tace "Control yourself Suraj! Please calm down!!" "Calm down? How did you expect me to calm down? Bakiga abunda ke faruwa bane? He was torturing her just saboda ta jefar da spoon! I might not be her husband Meenah but I respect Laylah bazan b'ari yayi insulting d'in ta haka ba because she is the mother of my Child! ". Zaro ido Meenah tayi amma sai ta b'oye mamakin ta tace "It's OK Suraj at least not now, zan kula da komai just relax". Tana Kai nan ta juya zata fita tana cewa "don't come out har sai kayi controlling anger d'in Ka please" Kai kawai ya jinjina Meenah ta fice, ya d'au lokaci Shima kafin daga bisani ya fito........ Da k'yar ta samu ta wafce hannun ta daga rik'on da ya mata ta mik'e tsaye tana murza hannun a hankali kafin ta had'iye miyau tana k'irk'iro murmushi ta dubi Muhseen tace "I am done eating.......na bar purse d'ina upstairs i'll go fetch it right away....." Kai ya jinjina shima yana murmushi, da sauri ta nufi upstairs tana kwalla, ta damk'e hannun wanda duk yayi jajir da shi. A fusace Suraj yabi bayan ta bai damu da mutanen da ke wajen ba Muhseen kuwa ko kai bai d'aga ba sai murmushi yake ya cigaba da cin abincin a tsanake. D'akin Suraj ta shiga ko purse d'in dake kan gado bata d'auka ba ta tsaya duba hannun ya shigo, banke k'ofar yayi ya rufe, k'aran ne yasa ta juya cikin sauri, suna had'a ido ta juya tana share hawaye sannan ta zari purse d'in zata fice, gown d'in ta ya rik'e yana kallon ta, chak ta tsaya ba tare da ta juyo ba saboda yanda taji idanuwan ta sun cicciko "I am sorry Laylah.......but i have to do this" Ya idar da maganar yana mai rik'o hannun nata a hankali. Bata ce komai ba sannan bata hana shi ba, stool ya janyo sannan ya umarce ta da ta zauna nan ma babu musu tayi biyayya... Kallon shi kawai take tana ganin yanda yake ta bincike daga drawer zuwa drawer da alama abu yake nema sannan ya nufi hanyar bathroom bai jima ba nan ma ya fito rik'e da wani ointment, durk'usa wa yayi gabanta yana bud'e wa ba tare da kallon fuskar ta ba ya kama hannun a hankali ya fara shafa mata ointment d'in, ita kuwa kallon sa take tana murmushi had'e da kwalla. Saida ya kammala shafa mata tukunna ya d'ago kai suka had'a ido, handkerchief ya mik'a mata ta karb'a tana share hawayen ta. "Suraj....i ......i have to go now.....thank you for applying the ointment and for your care but i have to leave before Muhseen gets suspicious. Murmushi yayi sai lokacin ya sakar mata hannun. Mik'ewa tayi zata fice Suraj baki na b'ari ya ce "F..Fulanii......" Wani bugu k'irjin ta yayi da jin sunan da ya k'ira ta dashi har saida ta lumshe idanuwan ta sannan ta juyo tana kallon shi.. Suraj ya d'an gyara murya yace "Amm........you cant go out like that. Ni zan fita, ki d'an yi freshening fuskar ki you look so pale and weary at least ki gyara make-up naki ... Uummm........ What do you call that black thing? Yess! Mascara! I think your Mascara is draping, yayi ruining idanuwan ki"... Ya k'are maganar da sakin wani chocking smile hakan yasa Laylah ta zaro ido ta juya tana kallon madubi, tamkar wata y'ar madabo haka ta zama, tsabar takaicin dariyar da yake mata sai ta wurga masa purse d'in nata tana murgud'a baki da sauri ta shige washroom d'in domin gyara fuskar ta. Dariya yayi ya ajiye purse d'in bisa gado sannan ya nufi k'ofa yana fad'in "She's still the same Nutty as always.......+ Around 10:30 duk aka watse, kowa ya gaji especially matan. Mubeenah, Khadijah, Meenah duk d'akin Meenah suka kwanta kamar an musu duka, tun suna hira har barci yayi awon gaba da su, babu wanda ma ya damu da sauya kaya ko makeup , ko su Habeeb da Suka ga hakan saida suka yi ta dariya sosai.... Suraj ma yana shigowa d'akin da sauri ya kashe musu wuta yana dariya sannan ya lek'a d'akin da boboh da Iman ke barci nan ma yayi addua ya shafa musu sannan ya fita ya umarci nanny da ta rufe k'ofar. Downstairs ya nufa inda har lokacin Ameer da Habeeb ke hirar su, duk da cewa sun fahimci akwai damuwa tattare da Ameer shi kuwa sai denying yake yana cewa babu komai.. Wayar Habeeb ne ya fara ringing da sauri ya d'aga ganin sunan Oummin sa ne ya bayyana a screen d'in, bayan sun gama gaisa wa tace "Habeeb please gobe in Allah ya kaimu ka taho Kaduna. "Lafiya kuwa Ummi? You sound disturbed" ya tambaya da sauri "Lafiya Habeeb, it's about Sapna, tun jiya ta zo gida, she has not been herself since , bata magana da kowa ballantana ta fad'i damuwar ta, balle kuma uwa uba cin abinci, ni da Abban ka mun yi iya k'ok'arin mu, maybe idan ta ganka zata fad'a maka damuwar ta, besides banda kai da Suraj bata yarda da kowa ba, i am afraid kar ta illata kanta in the process. Shiru Habeeb yayi bayan ya saurari bayanin Ummin sa sai daga bisani ya shaida mata cewa In shaa Allah zai kamo hanya goben zuwa KD. Nan suka yi sallama Habeeb ya ajiye wayar yana sauk'e numfashi . Falon shiru yayi tamkar babu rai a cikin sa, gajiya Suraj yayi da shirun ya juya ya dubi Ameer da ya jingina bayan shi a kujera ya lumshe ido sannan ya dubi Habeeb da yayi shiru yana kwance rigingine ya d'aga kai kamar mai k'irga ceiling sai ya Mik'e tsaye yana Mik'a "Aahh.......guys ni na tafi zan kwanta idan kun gama tunanin sai ku taho" Tashi Habeeb yayi ya zauna yace "You carry on Suraj Gud nyt, bana jin barci i'll join you later." Shima Ameer hakan ya fad'a. Kai Suraj ya jinjina yana kwafa, da gangan ya kashe wutar falon ya nufi kitchen da sand'a, babban roban ruwa ya d'auko mai uban sanyi basu ankara ba suka ji sauk'ar ruwa , a firgice duk suka mik'e Ameer har yana neman dungure "Ahhh! Suraj!!.. What the f**k ........." Habeeb ne ke maganar yana dunk'ulewa waje guda, Ameer ya mik'e da sauri ya amshe robar ya kwarara wa Suraj ruwan tas a jiki haka suka dinga masa dariya ganin yanda ya fi su birkice wa.. Da wannan dabarar ya ja hankalin su ya mayar da damuwar su ta koma dariya, upstairs suka nufa don already dare yayi gashi gobe monday. Tamkar d'akin samari haka suka maida d'akin suraj karaf d'aya duk sun zubar da jik'akk'un kayan nasu ranan kam closet d'in Suraj ya sha binkice don kowanne saida ya zari pyjama suka kwanta ..... Halin Suraj ne idan ya gan su cikin damuwa ya nemi hanyar kawar da ita don haka yayi murmushi ya kashe wutar d'akin shima ya kwanta,...K'iran sallar asubah na fari Suraj ya bud'e ido, cikin magagin barci ya lalumi wayar shi ya duba time k'arfe hud'u, k'afar Habeeb da ya loda masa ya ture duk jiki na ciwo ya mik'e tsaye yana stretching bathroom ya wuce direct ya d'auro alwala ya dawo, yana bud'e closet nashi ya dubi kan gadon yace "Wai baza ku tashi bane? Tsaki Ameer yayi cikin magagin barci yace "ta yaya zan yi in tashi bayan dannau ya danne ni?" yana maganar yana ture d'ayan k'afar Habeeb shi kuwa Habeeb sai ya saki murmushi ba tare da bud'e ido ba ya sake loda masa k'afar. Nad'e hannu Suraj yayi yana dariya yace kai fa Ameer baka ji komai ba naka wasa ne ni Habeeb har k'asa ya tureni cikin dare i wonder how khadija is managing don wollah nasan ta sha k'afafu kam. Tashi Habeeb yayi da sauri ya d'auki pillow ya wurga ma Suraj, shima yana chafe wa ya wurga masa Habeeb yayi dodging yana dariya. Ameer kuwa k'ara lume fuskar shi yayi cikin pillow ya ja blanket da hannun sa d'aya ya rufa kanshi a kasalance yace "Oh God! Habeeb... Irin wannan luguden k'afafun da ka min i'm sure sai an min tausa, please i will advice you idan zaka yi barci khadija kam ya zama mata dole amma keep Boboh away from your bed don wataran zaka murk'ushe min yaro" Suraj tsabar dariya har yana zama a k'asa, a fusace Habeeb ya danne Ameer "kafin na murk'usa Boboh kai bari na fara koya ma hankali tukunna!" da kyar Ameer ya ja jikin shi ya nufi bathroom yana rik'e kunkumi, Suraj dake gefe ma saida ya samu rabon sa don ruwan pillows da Habeeb yayi masa.... Tare suka wuce masallaci, suka d'an yi nafilfilu sannan suka suka gabatar da Sallar Asubah. Saida gari ya waye sannan suka bar masjid tamkar yara Haka Habeeb ya rako Ameer a guje don ya ishe shi da tsokana. Mubeenah na tsaye tana neman wajen zama taji an damk'o ta, ba shiri ta jefar da water bottle d'in hannun ta don da alama zasu fita jogging ne "Save me baby.....!!" Turus Habeeb yayi ganin Mubeenah da yayi, khadija tayi murmushi kawai tacigaba da rolling mayafin ta. Kwafa Habeeb yayi ya harari Ameer sannan ya dubeta yace "Smile all you want zan had'u dake!" Da Sauri Suraj ya k'araso yana kallon agogo "Mubeenah...... Na mance da paper works d'in nan kwata kwata barin k'arasa, ina da wasu ayyukan sosai a office" D'aki ya nufa bai jima ba ya fito da Laptop nashi da takardu nan ya zauna dining section yana ta fama, har takwas bashi da aiki se shan hot coffee milk, lokacin da ya kammala Habeeb har ya kimtsa cikin farar shadda d'inkin 3qtr ga hula brown ya kafa, sosai yayi kyau. Lokacin da ya shigo ma har an saita breakfast don haka suka had'u tare suka ci abincin gwanin sha'awa da burgewa+ "ina zuwa haka naga ka shirya da wuri?" Ameer ya tambaya, mik'ewa Habeeb yayi yana kurb'e ragowar tea d'in shi yace " Kaduna... Oummi ta k'ira ni jiya, it's about Sapna so zan tafi in naga kammala maybe in juyo da dare ko gobe in shaa Allah" kai Ameer ya jinjina yace "Toh Allah ya sa de lpy, please ka gaida Oummi" "Zataji" ya amsa a tak'aice ya dubi Khadijah ya kalla sai fuskanci ta b'ata rai, Murmushi yayi ya koma ya zauna gefen ta yace "what now? You are not little Boboh da zan zauna ina rarrashin ki, pls saki fuskan ki kin sani cewa ba don yau ne zaki yi enrolling Suraj a school ba da zan tafi da ke i'm sorry Love" Ko kallo bai ishe ta ba don ji take tamkar zai yi tafiyan watanni, Suraj ya lura da ranta ya b'aci don haka yayi charaf yace "Don't worry Habeeb, ba gani nan ba? Zan kai Boboh makarantan. D'auki matar ka ku tafi, Sapna ma zata ji dad'in ganin ta since ita kad'ai ce a chan" "What about your meeting Suraj?" Habeeb yayi tambayar yana kallon idon Suraj "Don't worry Ameer zai kula da komai sannan Mubeenah is here daman ina neman excuse ma ina so in fita in d'an sha iska in ga gari saboda haka carry ur wife waka....." Duk saida ya basu dariya da last statement d'in shi da sauri khadija ta nufi sashen su ta shirya tsaf cikin doguwar riga ta atamfa tayi mata kyau se jakar ta data rataya babba, Hannun ta Habeeb ya kama suka yi sallama suka fice. Ameer ya dubi Mubeenah yace "Idan kin je just carry on with the meeting tunda nayi hinting naki a kan komai akwai sak'on da zan karb'a a gun wani friend" kai Mubeenah ta jinjina da Murmushi ta kwashi papers d'in da Suraj ya yi reviewing sannan ta wuce sashen su, itama bata jima ba ta fice a motar ta. Ameer saida ya jira Suraj ya shiga wanka ya d'auke key d'in motar Suraj se ya ajiye masa nashi a wajen yayi sauri ya fice, a gurguje ya watsa ruwa ya shirya ya fito sanye da farar shirt da blue jeans da sauri ya bud'e bak'ar SUV d'in Suraj yayi mata gear, bai yi wata wata ba ya bar harabar gidan..... Ko da Suraj ya kammala shiryawa yayi ta neman key d'in sa bai samu ba se na Ameer don haka kawai ya zari key d'in ya fito kan sa a k'asa yake tafe yana d'aura strap d'in agogon shi, karo suka yi da sauri ya rik'o ta yace "Ya Ilahy! Sorry Bebs ina ta sauri ban kula ba". Murmushi tayi kawai ta k'arasa d'aura masa agogon tace "No it's my fault, tun da nayi breakfast nake jin kasala barci ne sosai a ido na, zan taka maka zuwa k'ofa se in dawo". Kai ya girgiza ya d'an mata peck a kumatu yace "Na yafe, kije ki ja rest madam kar ki wahalar min da baby". Yana kai nan ya wuce yana mata murmushi ita ma kallon sa take tana murmushin har ya shige..... Tun fitar shi ya lura akwai motar dake bin sa a baya amma se ya cigaba da tuk'i calmly.... Wani daga cikin motar dake bin Ameer ne ya d'aga waya ya kara a kunne yana fad'in "Boss.. Gashi nan ya fito.. Eh na tabbata Suraj ne motar shi ne.......ok Boss kawai kayi mana umarni yanzun nan zamu bi ta kanshi .........

Post a Comment for "IN SO YAKI NE CHAPTER 10"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...