FETTA CHAPTER 28 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

FETTA CHAPTER 28

FETTA CHAPTER 28

- - Post a Comment
FETTA CHAPTER 28

  Fetta sun dawo garin Agadez cike da kewar mutanen Niamey, sun so ta k'ara musu ko sati d'aya, Amanukal ya nuna yana buk'atar dawowar ta, da alk'awarin zata rik'a zuwa musu akai akai, Tasha alkharai mai yawa wurin dangin mahaifiyar ta, Sanah ma ba k'aramin alkhairi suka mata ba.+ Azagas tasa an shirya musu abinci kala kala, kai kace wata babbar bak'uwa ce, Fuska d'auke da murmushi tace "Tanti wannan abinci haka ai da kala d'aya ma ya isa", Hararar ta tayi tace "Ba a gidan sarauta ba, kuma yar gatan masarautar", Tayi dariya tace "Bara nayi wanka da sallah", Sanah tace "Nikam sai na fara cin abinci", Azagas tace "Ke ai dama acici ce", Suka yi dariya. Suraj kwanaki bakwai yayi su ne cikin damuwa da rashin kwanciyar hankali, baccin sa ragagge ne, ya rasa meke masa dad'i, Kullum aikin sa ya d'auki hoton Mimi da Fetta yayi ta kallo, Ya rasa dalilin da yake son kallon na Fetta, gashi tunanin ta ya kasa barin k'wakw'alwa da zuciyar sa, Kwance yake d'akin sa shiru, ya lumshe idon sa, cikin sa na masa kukan yunwa but baya jin zai iya saka wani abu a ciki, Wayar sa ya lalubo ya kunna karatun Qur'ani yana saurare ko zai samu natsuwa a zuciyar sa. Tasleem tasha ado cikin wata arniyar gown, hannun ta da k'afafun ta sun sha adon k'unshi ja da bak'i, kallo d'aya zaka mata kasan Amarya ce, Tsaki taja a karo na ba adadi, Ta kalli Sophy ta dake gefe "Ni fah na soma gajiya da jiran sa, wane irin ango ne zai bar Amarya na jira", "Kiyi hak'uri maybe wani uzuri ya tare sa", Ta sake jan tsaki tana hard'e hannayen ta a k'irji tare da jingina jikin motar dake harabar gidansu Sophy, Anan ta shirya mai makeup tazo ta sameta kasancewar gidan su mutane sunyi yawa, Tsinkayo motar ango ta k'ara b'ata rai, ita a dole sai yaga fushin ta, Abokin sa ne ya fito daga motar yace "Tuba muke Amarya, tela ne ya mana wulak'anci bai kammala d'inkin ango ba", Ta sauke ajiyar zuciya da yin murmushi tace "Har nayi fushi", "Ayi mana hak'uri", Ta jawo hannun Sophy tace "Mu tafi" Sophy ta shiga gaban mota, Tasleem ta shiga baya, Bello yana zaune fuskar sam ba annuri kamar ba ango ba, Kallo d'aya ya mata yayi faking smile, ya juya ya cigaba da danna wayar sa, Kwata kwata baya farin ciki, babu telan da ya b'ata musu lokaci, shine baya ra'ayin zuwa, sai da Kawu Lamid'o yaci masa mutunci, Ya shirya yazo. Gagarumin kamu aka yi a ranar, Bello murmushin dole kawai yake, but idan ka mishi kallon tsaf zaka fahimci babu walwala a tare dashi. Feena gyaran jiki sosai ta shiga yi, Da kanta tacewa Hajiya ta samu mai mata gyaran jiki, Hajiya mamakin rawar kai irin na Feena take, Komai sai tace da kanta zata yi, tun tana mata fad'a har ta zuba mata ido. "Umma sati d'aya fah kenan amma shiru kake ji, daga Hajiya har Suraj babu wanda ya nemi mu", Cewar Bilkisu fuska d'auke da damuwa, "Me kike ci na baka na zuba, zasu nemi mu", "Ni dai gaskiya ba zan iya jira ba, zan fara neman sa da kaina", "Toh ai shikenan" Ta mik'e ta nufi d'akin ta, Wayarta ta d'auka, ta kai kan number Suraj, ba tare da wani tunani ba ta danna kira, shigowar kiran ya katse karatun Qur'anin da yake saurare wanda yake jin natsuwa a hankali na saukar masa, ya bud'e idon sa dake masa yaji tsabar rashin isasshen bacci, Ganin bak'uwar number ya danna reject, wani kiran ya sake shigowa, rai a b'ace ya d'aga, "Hello Ya Suraj ina wuni?" ta fad'a tana kashe murya, "Lafiya", "Dama na kira ne na maka jajen abunda ya faru Allah ya kyauta gaba", "Amin" bai jira ta sake cewa komai ba, ya kashe wayar, STORY CONTINUES BELOW Wayar hannun ta tabi da kallo cike da takaici, "Wallahi sai na koma gidan ka Ya Suraj, soyayyar ka tama zuciyata mummunan kamu" Ta fad'a k'walla na cika mata ido. "Mutanen da suka rik'e ki tun bayan rasuwar Gabdullahi, bakya ganin ya kamata ki neme su, ki saka musu da alkhairi, nima ina so na musu alkhairi mai yawa", Cewar Azagas, Fetta ta numfasa tace "Lokaci na zuwa da zan neme su, har abada bazan manta alherin su da muhimmiyar rayuwar da suka taka a rayuwata ba", Azagas ta jinjina kai, sau da yawa tana tunanin akwai wani dangane da rayuwar ta, da take b'oyewa but bata tab'a yunk'urin tambayar ta ba, Ta katse tunanin tace "Allah ya kaimu", "Amin", Adnan ya shigo sanye da earpiece, yana wak'e wak'e, Su'ad dake zaune ta zubawa tv ido kamar ba kallo, a zahirin gaskiya kwata kwata hankalinta baya kai, tayi nisa wurin tunani, Ta d'ago kai ta kalle sa tace "Uhmm ina son magana da kai", Kunnen d'aya ya zare yace "Ina ji", "Bikin Feena ya matso Dan Allah ina so naje", Kafad'a ya d'age yace "Ina ruwana, you are free, please daga yau kada ki sake tambayata duk inda zaki je kije", "Sanin hakk'in ka ne shiy.....", Hannu ya d'aga mata alamar ya isa, ya mayar da earpiece ya wuce ciki abun sa, Girgiza kai tayi tana mayar da k'wallar dake shirin zubo mata. Suraj bayan ya idar da sallar la'asar yaji zaman gidan da kad'aici ya ishe sa, Ya d'auki mukullin motar sa, ya fita zuwa wurin shak'atawa, Wurin swimming ya nufa, Ya tub'e kayan sa ya shiga ko zai rage damuwa, Kusan awa d'aya ya d'auka kafin ya fito, fitowar sa yayi daidai da soma rurin wayar sa, Ganin sunan Munir kan screen, ya d'auka, "SS kana ina ne gani gidan gonar ka", "Ok ka jira ni, on my way", Yana buk'atar wanda zai sanar da damuwar sa ko zai rage nauyin da k'irjin sa ya masa, Ya tsane jikin sa, ya mayar da kayan sa, Mintuna kad'an suka kawo shi gidan gonar sa, A tsaye bakin office d'in sa ya tarar da Munir, Suka yi shaking hannu, "Yaushe ka shigo garin?", "Jiya fah", Ya bud'e suka shiga ciki tare da zama kan kujera, "Suraj meke damun ka ne, you are looking dull", "Ina cikin damuwa Munir", Da mamaki yabi sa da kallo, karon farko tun bayan kud'in Suraj da yaji ya ambaci damuwa yace "Meke damun ka?", Bai b'oye masa komai ba, ya sanar dashi, "Abunda na dad'e ina gudar maka kenan shiyasa nake yawan baka shawara ka daina sana'ar fashi da makami, babu macen da tasan ciwon kanta da zata zauna da kai sanin sana'ar ka, yaran ka bara su tab'a alfahari da kai ba, haka Hajiya duk ranar data gane ba zata yi alfahari da kai ba", Idonsa suka rine suka yi jajir, zuciyar sa na tsananin bugawa "Meyasa bai yi tunanin haka ba kafin ya jefa kansa a sana'ar?" Ya tambayi kansa, "Suraj ka fad'a tarkon son Fetta, gashi soyayyarta ta maka kamu a k'urarren lokaci, lokacin da ta sub'uce maka, kuma bana tunanin zata tab'a dawowa gare ka, sanin kana d'aya daga cikin yan fashin da suka kashe mahaifin ta" "Ban kashe shi ba Munir, ban tab'a kisan kai ba, ban zama silar kashe shi ba" Ya fad'a cikin karaji, tare da buga hannayen sa kan teburin dake gaban sa, "Baka da hanyar kare ka Suraj, tunda kaje gidan kuma kaine ogan su", Lips d'in sa na k'asa ya cije, fuskar sa tayi jajir, har jijiyoyin kansa sun fito, Ya kasa gaskata soyayyar Fetta ce ta kama sa, bai tab'a sanin so ba balle yasan kalar sa da yanayin sa, yasan yana jin damuwa a kanta, yana yawan tunanin ta, abubuwa da dama game da ita na burge sa, yana son kyautata mata, yakan so jin ta a kusa dashi, baya gajiya da kallon ta, kwanakin nan da yayi ba tare da ita ba, yana jin tsananin kewar ta, "Shin hakan na nufin soyayyarta ce ta kamani ko shak'uwa", Ya furta maganar a fili, "Soyayya da shak'uwa", Ya tsinkayo muryar Munir cikin tsakiyar kansa, "No Munir Noo bana sonta, shak'uwa ce", Munir yayi murmushi gefen baki yace "Ba da jimawa zaka gaskata soyayyarta ta maka mugun kamu, ina fatan Allah ya daidaita al'amuran ka, zanje wurin Abba tun d'azu nake ganin kiran sa", Ya kasa ce masa komai har ya fice. A daren ranar tunanin maganganun Munir suka hana zuciyar Suraj sukuni, yana k'aryata baya son Fetta, shak'uwa ce. Yau ta kama ranar asabar, a ranar aka d'aura auren Bello da Tasleem, Ranar tazo d'aya da na Feena, an d'aura auren ta da Fahad, sai washe baki take, murna fal zuciyar ta, Gidan Hajiya cike yake da jama'a, Suraj tunda aka d'aura aure babu wanda ya sake ganin sa, ko wurin reception bai je ba, gidan gonar sa ya nufa. Su'ad tazo, duk wanda ya ganta sai yayi maganar ta rame, amsa d'aya take basu rashin lafiya tayi, da yawa suna zaton ciki ne yazo mata da laulayi mai wuya. Gidan Alhaji Tambari ya cika da al'ummar Annabi, kasancewar sa dan' siyasa kuma auren yar' sa tilo d'aya ba k'aramin gayya yayi ba, Kawu Lamid'o baki ya kasa rufawa ya zama surikin Alhaji Tambari, Gwaggo har wani hura hanci take a dole dan' ta ya auri yar' masu hannu da shuni. Bello daga wurin reception, gida ya dawo ya shige d'akin sa, Ya saka key, kan katifar sa ya kwanta, ya jawo wayarsa ya kira rabin ransa Karima, magana da ita kad'ai zai sa ya samu natsuwa, Tana kwance bata jin dad'in jikinta da zuciyar ta, sanin an d'aura wa mijinta da take tsananin k'auna aure, Kiran sa ya shigo, Ta d'auka tare da fad'in "Ango Ango", "Amarya" Murmushi mai ciwo tayi tace "Ya gajiyar hidima?", "Alhamdulillah", "Allah ya sanya alkhairi", Ba tare da ya amsa ba yace "Ina kewar ki sosai ina ji kamar na ganni a gabanki", "Bada jimawa ba In Shaa Allah zamu kasance tare" Ta fad'a zuciya a raunane, "Allah ya tabbatar da hakan", "Amin", Sun dad'e suna hira, kafin ya kashe wayar. Bayan sallar la'asar motocin kai Amarya daga b'anagaren Fahad suka zo, mota biyu, Mutum biyar ne suka zo, duka tsofaffi, Dangin Hajiya da dangin Marigayi suka d'unguma aka tafi kai ta, Gidan ta dake unguwar rijiyar zaki, yayi kyau sosai, gida d'aya suke da surukan ta sai dai kowa da b'angaren sa, sashen iyayen sa aka fara kai ta, Mahaifiyar sa ba yabo ba fallasa ta tarbe su, Aka nufi b'angaren ta da ita, yayi kyau sosai, kowa na tofa albarkacin bakin sa, kafin magrib kowa ya watse aka bar Amarya ita kad'ai. Tasleem an kaita hadadd'en gidan da Mahaifinta ya basu, an zuba kaya tsadaddu a ciki, babu abunda ya burge Bello a gidan, kwanciyar hankali da farin cikin sa ya fiye masa komai, Nama da lemo kad'ai ya kai mata, ya koma d'ayan d'akin yayi kwanciyar sa, Tasleem haushi kamar ya kashe ta, a ranta ta k'udiri maganin sa, bai isa ya wulak'anta ta ba. *Bayan wata d'aya* Fetta so, k'auna da kulawa take samu daga dangin ta, a ko da yaushe burin su, su faranta mata, a cikin wata d'aya taga gata ba na wasa ba, Ta k'ara haske da kyau, Fatar ta ta k'ara shek'i, ta koma sak buzuwar ta, jinin sarauta, Shak'uwa mai k'arfi ta shiga tsakanin su da Abutalib, idan basa b'angaren Azagas tare, toh suna b'angaren Amanukal, yana d'ebe mata kewa sosai da hana ta tunanin da zai iya haifar mata da matsala, Mimi ta k'ara girma da wayo, Fetta sai ta wuni bata saka ta a ido ba, Nono kad'ai ake kawota ta bata shima can ba'a rasa ba. Ta b'angaren Suraj damuwa da rashin kwanciyar hankali sun kasa barin sa, Ya rame sosai tamkar mai cuta, kallo d'aya zaka masa kasan yana cikin tsananin damuwa, Hajiya ta soma tausayin sa, yanzu tana sake masa da tilasta masa yaci abinci, hakanan yake turawa ba dan yana jin dad'in sa ba, Bai sake zuwa fashi ba, gaba d'aya yaji ya fita ransa, Maganganun Fetta yake tunawa a kowane lokaci, Harkokin kasuwancin sa ma baya maida hankali sosai, komai a sanyaye yake yin sa, Abun na damun yaran sa basu da hurumin tambayar sa, Harkokin sa na lagos ma sam baya waiwayar su, Yau ma zaune yake shi kad'ai a d'akin Mimi, hoton Fetta yake kallo, duk yadda yaso k'aryata zuciyar sa kan bata son ta abun ya faskara, Duk iya k'ok'arin sa wurin yakice ta ya kasa, sau tari ya kan ji haushin kansa, ya kan ji tamkar ya musaya zuciyar sa, A kullum da kalar yadda yake jin ta a ransa, ga masifar kewar ta dake damun sa, ba abunda yake son jin kamar k'amshin turaren ta, sau da yawa wadrobe d'in ta yake bud'ewa ya d'auki kayanta ya rungume a jikin sa, ta haka yake samun sassaucin abunda yake ji a zuciya, Ya gama gaskata soyayyar Fetta ta dad'e da masa mugun kamu ba tare da ya ankara ba. "Me yasa abubuwa suka zo a haka?, meyasa zata barni a lokacin da zuciya, ruhi da gangar jikina ke muradin ta, meyasa ban fahimci ina k'aunarta ba kafin na rubuta mata saki? Ya Rabbi a ina zan ga Fetta na dawo da ita rayuwata, na nemi gafarar ta, na bayyana mata tsananin k'aunar da nake mata" Ya k'arasa hawaye masu d'umi na wanke fuskar sa, ya manne hoton ta a k'irjin sa yana matsewa. Mamakin zubar hawayen sa yake, ba zai iya tuna lokaci na k'arshe da ya zubar dasu ba, Kusan minti talatin yana durk'ushe a wurin, manne da hoton ta a k'irjin sa, bugun zuciyar sa na tsananta, tunanin sa a ina zai ganta? babu wanda ta sani bayan su Aliya balle yayi tunanin taje can, "Yasmeen" zuciyar sa ta fad'a, "Ba zata rasa masaniya akan Fetta ba" Ya cewa kansa yana mik'ewa tamkar wanda aka zungura, Hoton ya ajiye a ma'ajiyar sa, ba tare da ya tsaya ya gyara kan sa ba, Ya d'auki mukullin mota ya fita a gaggauce.+ Minti 30 ya kawo shi gidan su Yasmeen, gidan yake bi da kallo yana ganin yadda ya lalace, fetin sa duk ya tsufa, harabar gidan tamkar ba mutane ke rayuwa ba, sab'anin wasu lokuta a baya, "Kai ka zama silar rugujewar gidan nan" Yaji zuciyar sa ta fad'a, nadama da rauni yaji sun dababaiye sa lokaci d'aya, D'akin mai gadi ya lek'a ko zai gansa, yace ya mishi sallama da Yasmeen, ba kowa a ciki, k'wakwalwar sa ke haska masa daren ranar da ta kasancewar ranar da yake tsananin nadamar faruwar komai, Mahaifin Fetta yake hangowa a idon su, da Fetta a lokacin da tayi k'ara da aka harbi mahaifin ta, idon sa ya runtse yana dafe kansa dake sara masa had'e da juyawa, "Ya Rabbi" Bakin sa dake karkarwa ya furta, ya jingina da bango, ina ma zai iya mayar da hannun agogo baya ya goge ranar cikin tarihin rayuwar sa, Yasmeen ta fito da shirin zuwa makaranta, ganin Suraj yasa tayi turus, tana mamakin zuwan sa da yanayin sa, yayin da zuciyarta ke harbawa da tsananin k'arfi, daren data rasa iyayenta take tunawa, tana jin tamkar ta shak'ura sa ya fad'a mata dalilin su na raba su da farin cikin su, K'ok'arin tattaro natsuwar sa yayi ta hanyar cewa "Wurin ki nazo Yasmeen", Mamakin yadda yake magana a sanyaye take sab'anin cikin isa da tak'ama, Maganganun Fetta yasa tayi k'ok'arin danne zuciyart tace "Toh" tana nufar veranda dake harabar gidan, yabi bayan ta, Kujerun roba dake wurin suka zauna, Ya numfasa yace "Alak'ar dake tsakanin ku da Fatima, nasan baza ta tab'a tafiya tsawon lokaci ba tare da ta neme ki ba", Yasmeen ta sauke ajiyar zuciya tace "Meyasa kake tunanin ta sanar dani? Ko kad'an bansan inda Fetta take ba, tun ranar data bar gidan ka ban sake jin wani abu da ya dangancen ta ba", "Hakan ba abu mai yiyu bane", Ya fad'a yana tsare ta da ido, wanda yake hango rashin gaskiya a tare da ita, Agogon dake sak'ale a hannun ta, ta kalla tace "Zan makara ina da test", Ta mik'e ba tare da ta jira cewar sa ba, ta nufi motar ta, Kallo mai cike da mamaki yabi ta dashi, Yau shi ake fad'awa magana a wuce ba tare da an jira cewar sa ba, b'acin rai yaji na taso masa, yana jin yafi k'arfin haka, Jin alamun tashin motar ta, Zuciyar sa tace "Ita kad'ai ce hanyar had'uwar ka da Fetta, don't let ur anger control you ka rasa ta na har abada", Ya mik'e da sauri ya nufi motar, Knocking glass ya mata ta bud'e, A raunane yace "Meyasa ba zaki sanar dani ina Fetta take ba? ", Murmushin gefen baki tayi tace "Bani da masaniya", Tana jan motar ta tayi gaba, hakan ba k'aramin b'ata mishi rai yayi ba, yayi feeling humialated, Cike da zafin zuciya ya nufi motar sa yaja, bai san ina zasa shi, bai san ina zai nufa ba, yawo yake cikin gari ko hakan zai rage masa damuwa but ko kaso biyar na damuwar sa bai bar sa ba. "Bazan tab'a sanar da kai ina Fetta take ba" Cewar Yasmeen dake driving, kallo d'aya zaka masa kasan yana cikin tsananin damuwa, ko shakka babu rashin Fetta ya tab'a sa, but bata yi deserving mutum kamar Suraj ba, a da tana ganin tsantsar dacewar su, sab'anin yanzu da take ganin had'uwar su tamkar kifi da kaska, shin me ya kaishi ga aikata fashi da makami?, K'arar wayarta ya katse mata tunani, "Kina ina?, gashi har za'a shiga test", Cewar k'awarta dake suke tare makaranta, "Gani nan zuwa", Ta fad'a tana k'ara gudun motar, STORY CONTINUES BELOW Fitowar ta wanka kenan tana tsane gashin ta da k'aramin towel dake hannun ta, Sanah ta shigo rungume da Mimi, "Allah yasa ba rigima take ba" Cewar Fetta, "A'ah kaya nazo na chanza mata zamu fita, Tanti tace ki shirya tare zamu je", "Kuje dai, nikam bana jin fita", Sanah ta jinjina kai tace "Tab ai fitar saboda kece, Addani(Haka suke kiran Elhidir) yace zamu je shak'atawa, Allah Tumuqqartin ke yar' gata ce, mun sha rok'on Addani muje shak'atawa tare sai yace ayyuka sunyi yawa, amma saboda ke zai je", Fetta tayi murmushi har cikin ranta tana jin dad'i da k'aunar Elhidir, soyayyar da yake nuna mata yakan sa taji tamkar Addani d'in ta, tabbas da tun tasowar ta tana tare dasu, ko kad'an ba zata yi maraici ba. Cikin mintuna kad'an ta shirya cikin lace mai masifar kyau da tsada, ba k'aramin haska ta yayi ba, ta saka yan kunni, sark'a da awarwaro na zinari, wanda yanzu dasu take ado, Tayi kyau sosai, Sanah nata yaba kyan da tayi. Feena a cikin wata d'aya na auren ta, ta soma fahimtar halayyar Mahaifiyar Fahad da K'annen sa, sam basa k'aunar ta, kullum kyara da hantara ce tsakanin su, ko gaishe da Mahaifiyar sa tayi ba yabo ba fallasa take amsa ta, wani lokacin ma bata amsawa ba, abun na damun ta, babu yadda zata yi ko ta fad'awa Fahad kalmar d'aya ce "Tayi hak'uri", yana nuna mata soyayya sosai kuma zaman lafiya suke, matsalar d'aya ce dangin sa. "Yau kinje kin gaishe da Mum kuwa" Cewar Fahad, Feena dake zaune gefen sa tace "A'ah", "Me kike nufi da a'ah", "Kasan halin mahaifiy..." Dakatar da ita yayi "Kinga Feena bana son yawan k'orafe k'orafe tashi muje ki gaishe ta", Jiki a sanyaye ta mik'e, ta d'auko mayafin ta, suka nufi sashen mahaifiyar sa, Zaune take falo tana shan kayan marmari, kallo d'aya zaka mata kasan yar' boko ce mai ji da isa had'i da tak'ama, Cike da ladabi tace "Mummy ina wuni?", Yatsina fuska tayi tace "Sai yanzu zaki zo gaishe ni", Fahad ne yayi saurin cewa "Bata jin dad'i ne", "Kaine bakin ta, sallamamme daga gani yarinyar nan ba'a banza ta barka ba, yadda kake rawar k'afa a kanta", Feena murya a sanyaye tace "Kiyi hak'uri Mummy tun safe kaina ke ciwo", Tab'e baki tayi tace "Uhmm", Ta juya kan yar'ta wacce zasu yi kusan sa'a da Feena tace "Ke bani remote", Ta mik'a mata, suna had'a ido da Feena, ta galla mata harara, Mummy channel ta canza tare da maida hankalin ta kan kallon, taba banza ajiyar su, Ganin haka Fahad yace "Mum sai da safe", Ta juyo tana kai dubanta kan Feena "Tashi ki tafi, ina so magana da da'na", Jiki a sanyaye ta mik'e ta fita, hawaye na bin kuncin ta. Suraj kusan awanni biyu yana yawo cikin gari, hakan bai sa ya samu natsuwar da yake son samu ba, Ya nufi gida zuciya cunkuse da tsantsar damuwa, K'amshin turaren Fetta kamar ko da yaushe ya ziyarci k'ofofin hancin sa, "Ya Ilaihi" Ya furta yana jin yadda idon sa ke sun tozali da ita, gangar jikinsa na son jinta a kusa dashi, Kujerun falon ya zauna, tare da jingina yana lumshe ido, tunani da kewar ta na dabaibaye shi. Yamma lik'is Fetta suka dawo masarautar, ta gaji sosai wurare daban daban suka je, Elhidir ya mata siyayya bata wasa ba, duk da cewa tana da komai na buk'ata, Ruwa ta watsa ko zata ji k'arfin jikin ta, tabi lafiyar gado tana huce gajiya, Tunanin Aliya ne yazo mata, tana kewar su sosai, Wayarta k'irar Iphone 11pro max ta jawo, ta danna kiran Aliya, Bugu d'aya ta d'auka, ta dad'e tana jiran kiran Fetta, ganin number da bata 9ja ba, ya tabbatar mata itace, "Fetta ina fatan kina lafiya?" Cewar Aliya cike da zumud'i, "Lafiya lau Umma, Ya Mallam dasu Hajar?", "Ya fita kasuwa, Hajar sun tafi k'ok'i", "Ina gaishe su", "Dan Allah ina kika shiga Fetta, kuma meye dalilin tafiyar ki", Ta sauke ajiyar zuciya tace "Ba komai Umma, In Shaa Allah zan dawo gare ku, sai anjima", Ta kashe ba tare da ta jira cewar ta ba, Aliya tabi wayar da kallo tana sak'a abubuwa da dama a ranta. Ajiye wayar tayi, ta nufi toilet jin kiran sallar magrib. Tasleem ce rik'e da k'ugu gaban Bello, Cike da masifa tace "Na gaji da halayyar ka, aure wata d'aya babu wani cigaba, toh wallahi baka isa ka wulak'anta ni ba, kana ci k'ark'ashin mahaifina", Wani banzan kallo ya watsa mata yace "Na buk'aci tallafin mahaifin ki, ban tab'a sha'awar auren ki ba Tasleem, baki da tarbiya da nagartar matar aure", "Kutumar ni zaka zagar wa iyaye", Tsaki yayi ya fice ya bar mata d'akin, Wayarta ta d'auka, ta danna kiran mahaifin ta, bugu d'aya ya d'auka, ta fashe da kuka tana fad'in "Daddy wallahi na gaji, kullum sai ya zageni yau ma cewa yayi bani da tarbiya, wai baku bani tarbiya ba, ban fito gidan mutunci ba", "Shi Bellon yace haka", "Eh Daddy", Ta sake fashewa da kuka, Ya kashe wayar cikin tsananin b'acin rai, Yana danna kiran Kawu Lamid'o, tijara da rashin mutunci ya zuba masa wanda sai da Kawu lamid'o yaji ya soma nadamar had'a auren, tun kafin ayi aure yake fuskantar cin mutunci daga wurin Alhaji Tambari, babu girmawawa ko kunyar surukai tsakanin su, Ya numfasa ya kira Bello, yace cikin minti ashiri yana son ganin sa. K'arfe uku na dare, but tamkar bakwai na dare a wurin Suraj yadda ko alamar bacci babu a idon sa, rungume yake da bargo yana shak'ar k'amshin ta, yayin da yake jin tsananin kewar ta na zagaye dukkan gabb'an jikin sa, ba zai iya jure rashin ta ba, ya zama dole ya koma wurin Yasmeen ita kad'ai ce hope d'in sa na sake tozali da Fetta. Bilkisu wacce ta mayar da kiran Suraj al'adar ta, kullum sai ta kira sa, baya k'in d'aukar kiran ta, wanda ya rasa dalilin hakan, idan sau biyar zata kira sa a rana baya fashin d'auka, Wani mugun asiri Aunty Jummai ta karb'o wajan bokan ta, wanda aka had'a da fatar maciji, harshe kare da bak'ar cab'a, aka binne a mak'abarta, asiri ne da sai cusawa Suraj soyayyar Bilkisu, ya fitar masa da Fetta a rai, yaji ya tsane ta, sai dai kash hakan bata kasance ba, wayarta ce baya iya tsallakewa ko yayi yunk'urin shuka mata rashin mutunci sai ya kasa. Kiran sallar farko ta danna masa kira, ya danna receive, yana saka speaker, "Hello Ya Suraj ina kwana?", "Lafiya lau", "Dama nace pls ina son ganin ka anjima, akwai wata magana da zamu yi", "Ok" Ya fad'a yana kashe wayar, Tsalle ta duka ta kalli Aunty Jummai dake gefenta tace "Zai zo Umma", "Ya zama dole ki kawo kud'i a k'arawa boka dan aikin sa yayi", "Dole ne Umma, bara na tashi na fara shirin tarbar sa", "Kada ki manta ki barbad'a garin nan a lemo, ki tabbatar ya sha", Tayi nodding kai, K'arfe bakwai na safe Suraj ya nufi gidan su Yasmeen, yaci sa'a yaran gidan sun fito sanye da uniform wanda ke nuna makaranta zasu, D'aya daga cikin su ya aika, ya kira masa Yasmeen. Tashin ta bacci kenan, Nu'aym ya shigo yace "Wani na kiran ta", "Ok" Tace masa tana kallon agogo, bakwai da minti ashirin, "Waye da safiya haka", Brush tayi, ta wanke fuska, ta zura hijab ta fito, Ganin Suraj mamaki ya kamata, "Me kuma ya dawo yi?" Ta tambayi kanta tana k'arasawa veranda, sama sama suka gaisa, Duk wani girman kai, isa da tak'ama ya nemi su ya rasa, cikin k'ask'antar da murya yace "Ki dubi girman Allah kiji tausayina ki sanar dani ina Fetta take", "Na fad'a maka bani da masaniya", "Bacci ya k'auracewa idona a dalilin ta, na rasa natsuwa da kwanciyar hankali tun ranar da ta bar rayuwata, plss Yasmeen ki sanar dani ko zan samu sassauci a rayuwata", Ya k'arasa yana dafe kansa dake tsananin sara masa tamkar zai rabe biyu. Yasmeen da kallo tabi sa, yayin da zuciyarta ta raunana, Jin tayi shiru ya d'ago idonsa da suka soma ja yace "A shirye nake na karb'i duk wani hukunci da zata yanke a kaina, but bazan iya jure rashin ta ba", Tausayin sa taji ya kamata, wani b'angare na zuciyarta na sanar da ita watak'ila had'uwarsa da Fetta ya zama silar shiryuwar sa ko da ace ba zata koma gare sa ba, a yadda taga soyayyar Fetta ta kamasa ko shakka babu komai zai iya dan ganin ta dawo gare sa, Tsintar kanta tayi da furta "Masarautar Agadez", A razane yace "Kina nufin Fetta na masarautar Agadez", Kai ta gyad'a masa, "Meye had'in ta can?", "Shine kad'ai abunda zan iya sanar da kai", Godiya ya shiga yi mata tamkar ba Suraj mai ji da kai, da isa, Murmushi tayi ta mik'e ta shige cikin gida.+ Wayarsa ya fiddo a aljihu, ya shiga kiran Rabi'u, bugu biyu ya d'auka, "Ranka ya dad'e ina kwana?", Bai amsa gaisuwar ba yace "Ina so kamun booking flight na Agadez, if possible jirgin yau nake so", "Ok Sir", Ya kashe wayar, Rabi'u murna yake ogan nasa ya kira sa, ya jima bai ga kiran sa ba, ko ya kira ma baya d'auka, har ya soma zargin ko wani laifin suka masa duba da yadda ya canza musu gaba d'aya. Cike da tunanin meye had'in ta da Masarautar Agadez ya dawo gida, k'aramar jaka ya d'auka ya saka kayansa kala biyu da abubuwan da yake tunanin zai buk'ata, Hotan ta da ya mayar d'akin, ya masa ma'ajiya gefen gado, Ya d'auka ya kalla yace "Am coming to you and My little angel", Ya sumbaci hoton yana jin sanyi a ransa, da jin tamkar ya bud'e idon sa ya gansa a gaban su, Kiran Rabi'u ya katse masa tunani, Yayi receiving yana fatan an samu, "Ranka ya dad'e an samu gobe da safe k'arfe bakwai", Ya kashe wayar cike da haushin rashin samu yau, yayin da wani b'angare na zuciyar sa ke nuna masa farin ciki ya dace yayi, Ya sauke ajiyar zuciya, ya kwanta kan gado tare da saka wayoyin sa flight mode, baya son damuwa. "Am sorry Fetta na karya alk'awarin da na d'aukar miki, ina ganin sanar dashi shine alkhairi" cewar Yasmeen dake zaune a d'aki, hankalin ta ya kasa kwanciya tunda ta sanar dashi, She is feeling guilty. Bilkisu shiri sosai take na zuwan Suraj, gidan ta gyara tsaf, tayi cefane wanda bata tab'a yi ba, ko taba Aunty Jummai ayi, Kaji biyu ta siyo tayi pepper chicken, tayi fried rice da coleslaw, ta had'a ginger drink wanda tayi barbad'en magani a ciki, Bayan sallar la'asar tayi wanka ta chab'a ado cikin fitted gown na atamfa, tabi jikinta da turaruka ta feshe, "Yau dole Suraj ya bada kai bori ya hau, wannan kyau haka tamkar lu'u-lu'u" Cewar Aunty Jummai, Bilkisu tayi fari ido tana jin tamkar tafi kowa a yau, Tana karairaya ta nufi d'akin ta, ta d'auki waya ta danna kiran Suraj, jin ta a kashe, zuciyarta ta buga, ta sake kira, kusan sau biyar tana kira amsar d'aya ce a kashe, zama tayi gefen gado, ta rafsa tagumi tana addu'ar Allah yasa ba ruining ranar ta zai yi ba. Suraj sam ya manta da zancen had'uwar sa da Bilkisu, zumud'in zuwa yaga Fetta yasa ya manta duka schedules d'in sa na ranar, Bayan ya idar da sallar la'asar a masallacin dake had'e da gidan, Ya nufi b'angaren Hajiya, bai sameta a falo ba, ya shiga cikin d'aki, Kwance take da charbi a hannu tana lazimi, ya kalleta yana jinjina k'ok'arin mahaifiyar tasa wurin ibada, shi kam bazai iya tuna when last ya d'auki charbi yayi lazimi ba, ko karatun Qur'ani baya samun lokaci ya zauna yayi, a ko da yaushe busy yake kan neman duniya da burin tara arzik'i mai yawa, Tunanin sa ya katse yace "Mama ina wuni?", "Lafiya lau", ta fad'a tana tashi zaune, "Uhmm dama nace zanyi tafiya gobe", "Toh Allah ya kai ka lafiya ya bada sa'a", Ya amsa da "Amin", "Ga abinci can kan dining ka d'auka kaci, naga ko an kai b'angaren ka haka ake dawowa dashi", Ya d'an sosa k'eya yace "Mura ce ke damuna, so nayi losing appetite", "Allah ya sawwak'e" Ta fad'a ba dan ta yarda ba, tasan sarai rashin Fetta ke damun sa, Ya amsa da "Amin" Yana mik'ewa ya fita, tabi bayansa da kallo, ta girgiza kai ta sake kwanciya tana cigaba da lazimi. Su'ad na kitchen na k'ok'arin dafa indomie ta saka ma cikin ta, yunwa sosai take ji, Taji k'arar wayarta, ta fito da sauri zuwa falo ta d'auka, Ganin Adnan ne mai kiran tayi mamaki, sanin baya kiranta idan ya fita tun safe sai dare yake dawowa ko abincin ta baya ci, tana gab da tsinkewa ta danna receive, "Wane irin iskanci ne ina kira sai ta kusa tsinkewa zaki d'auka", Shiru tayi tana tuna kafin auren su ko sau goma zai kira bata d'auka ba, baya tab'a nuna fushin sa, sai ma fatan ba laifi yayi mata ba, lallai maza basu da tabbas, "Ko baki ji bane" Ya fad'a cikin tsawa, "Uhmm ina kitchen ne wayar na falo", Yaja tsaki yace "Ki had'a kayan ki, zan turo mota yanzu za'a kwashe hadda gadaje", Ya kashe ba tare da ya jira cewar ta ba, wayar tabi da kallo tana jin tsananin tashin hankali, ba dai sakinta zai yi ba, watanni kad'an da auren ta ace ya mutu, ba k'aramin kunya da abun fad'a zata sha ba, zama tayi ta kasa wani motsi balle tayi yunk'urin had'a kayanta, Kusan minti ashirin tana haka, jin k'auri a kitchen tayi saurin mik'ewa, sam ta manta da indomie da ta d'aura, ta k'one k'urmus, Fitowar ta kitchen yayi daidai da sallamar mai gadin ta, yake sanar da ita masu kwasar kaya ne, jiki a sanyaye ta had'a kayan sawar ta, a akwatun nan lefe, ta had'a nasa, Masu kwasar kaya suka shigo suna kwashewa. Bilkisu ganin har bayan isha'i babu Suraj ba alamar sa, wayoyin sa har lokacin a kashe, Hankalinta ya soma tashi, kar dai watsa mata k'asa zai yi a ido, duk shirinta ya zama na banza, Aunty Jummai ta sama a falo tace "Umma kinji sa shiru, wayoyin sa a kashe", Ta k'arasa hawaye na wanke fuskar ta, "Bashi nan zuwa anjima mu gani, ina tunanin wani uzurin ya rik'e sa", "Allah yasa" Ta fad'a tana share hawayen ta. Adnan sai kusan sha d'aya ya shigo gidan, ya dawo da wuri kenan, Su'ad dake zaune tsakar gida kan kujerar roba, ta kalle sa tace "Sannu da Zuwa", "Tashi mu tafi, ina fatan ba komai naki a cikin gida", Kai ta girgiza masa, mayafi ne sanye a jikinta sai wayar dake hannun ta, Motar data gani bakin gate ta bata mamaki, Civic ce one door(Mai k'ofa d'aya), "Dama Adnan na hawa irin motar nan?", Ta tambayi kanta, "Zaki wuce mu tafi ko kuwa", Ya fad'a cikin d'aga murya, ta bud'e murfin motar ta shiga, Ghetto area taga sun nufa, irin unguwar yan k'auye, cab'ali da kwata k'oina, ga yara na yawo ba kaya, awakai da raguna had'i da kaji nata yawo, Gidajen masu tsarin ginin da ne kewaye da unguwar, babu ginin zamani ko d'aya, Unguwa ce ta talakawa, Mamaki fal ranta bata da damar tambaya, mamakin ta bai k'aru ba, sai da taga sunyi parking bakin wani k'aramin gida, mai k'ofa babu gate, Yace ta fito, babu musu tabi bayan sa har cikin gida, Gida ne k'arami mai d'akuna biyu a jere, d'aya ciki da falo, d'ayan kuma falle d'aya, kitchen da band'aki, sai tsakar gida, "Anan zamu cigaba da zama", Ya fad'a hankali kwance, A razane ta kalle sa tace "Me kake fad'a Adnan", "Abunda kunnen ki suka jiye miki", Ya juya ya fice abun sa, Zama tayi dirshan kn sementin dake shimfid'e tsakar gida, ta d'aura hannu ta fashe da kuka. Bilkisu ranta ya kai k'ololuwa wurin b'aci da rashin zuwan Suraj, taci kuka ba kad'an ba, Aunty Jummai ta dinga lallashin ta, itama ranta ya b'aci sosai, ta d'auki alwashin ko zatayi yawo tsirara sai Bilkisu ta koma gidan Suraj, asiri ko wane iri duk tsaurin sa ta d'auki alwashin aiwatar dashi, Ta gaji da jiran tsammani, abu yak'i ci yak'i cinyewa. Suraj daren yau gani yake tamkar an k'ara masa tsawo yadda ya k'osa gari ya waye, yayi tozali da muradin ran sa, sai faman juyi yake kan gado, yana duba agogo akai akai. Kiran sallar farko a kunnen sa, yayi wanka had'i da brush, ya d'auro alwala yana jiran a tada ik'ama. Fetta tunda ta tashi sallar asuba bata koma ba, kayanta take had'awa, jirgin safe zasu bi zuwa Niamey, waccan karan ma ita ta buk'aci tafiya a mota dan taga k'asar Nijar, Bikin yar' k'anwar Mummy ake, sati d'aya zata yi a can, Sanah taso bin su but suna zuwa makaranta, *7:30am* Jirginsu Suraj ya lola dasu sama zuwa k'asar Nijar, zaune yake ya lumshe ido, yana tunanin Fetta, da farin cikin cikin awanni kad'ai zai yo tozali da ita, yaga little angel d'in sa yana tsananin k'aunar gudan jinin tasa. "Ba zaki tsaya kici abinci ba", Cewar Azagas, Fetta tace "A'ah Tanti, idan na tsaya zamu iya rasa jirgin mu", "Toh Shikenan Allah ya tsare ya kai ku lafiya, a gaishe da mutanen can", "Zasu ji", Ta fito harabar masarautar rungume da Mimi, da sauri dogari ya taso ya bud'e mata k'ofa, ta shiga suka nufi airport, suna zuwa ba b'ata lokaci jirginsu ya d'aga zuwa garin Niamey.

Post a Comment for "FETTA CHAPTER 28"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...