Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

FETTA CHAPTER 26

FETTA CHAPTER 26

- - Post a Comment
FETTA CHAPTER 26
Zuciyarta ke ingiza ta ta bud'e, wani courage taji yazo mata, Ta murd'a handle d'in tare da tura k'ofar d'akin da k'arfi, Tsaye tayi bakin k'ofa tana bin d'akin da kallo, babu gado balle katifa a cikin sa, akwatuna ne na k'arfe a k'alla zasu kai biyar, gefe kuma wani k'aramin safe ne, jallabiyar da ya cire ta gani ajiye gefe, A hankali take taka k'afarta cikin d'aki, har ta kai bakin akwatunan, Safe dake gefe takai hannunta ta bud'ewa taji a rufe, Kamar ance kalli gefe, ta hango wata yar' k'aramar jaka a sak'ale, ta jawo ta bud'e, keys ne da yawa a ciki, Ta d'auki d'aya wanda take kyautata zaton shine na safe d'in, Tana sawa ya bud'e, Takardu ne masu yawa a ciki, ta fiddo su, kowacce takarda tana d'auke da sunayen mutane wanda daga title na sunan, zaka san manyan mutane ne, hamshak'an masu kud'i, sauran takardun bayanai ne na kowane, address d'in su, shigowar su gari, wuraren da suka je, kud'ad'en da ake tunanin suna da a gida, Kud'in da suka yi withdrwaing, "Meye had'in sa da haka?, meyasa duka mutanen dake rubuce hamshak'an masu kid'i ne? Meye alak'ar shi dasu?", Ta jefawa kanta tambayoyin, "Dan' fashi yana buk'atar bayanai akan mutum kafin ya shiga gidan sa fashi", Zuciyarta ta bata amsa, K'irjin ta ya doka, takardun ta mayar ta rufe safe d'in, Akwatin farko ta bud'e, kayan sawa ne a ciki, wanda duka bak'ake ne, sai p-caps a kalla zasu kai biyar, da facemasks irin wanda ba'a ganin komai a fuskar mutum sai idonsa, a k'alla zasu kai goma, "Meya had'in sa da wannan kaya?", "Kaya ne irin wanda yan fashi ke sawa su b'atar da kama", Zuciyarta ta bata amsa, gefen kanta taji ya sara, "Ya Allah", Ta furta tana jin karaya da sarewa, A hankali ta mayar da akwatin ta rufe, Abunda ta gani a d'ayar akwatin ya matuk'ar d'aga hankalinta, bindigogi ne kala kala da bullets, kanta ke juyowa mata tana ganin dishi dishi, Jikinta ya shiga kyarma, Zama tayi a wurin dirshan ta kasa koda k'wakk'waran motsi, Ta kasa wani tunani, komai nata ya tsaya, banda zuciyarta dake bugawa da tsananin k'arfi, Sunayen Allah take ambata, a hankali taji k'arfi da sassauci na saukar mata, Hannun ta na rawa ta rufe akwatin, Ta fito d'akin tana jin kanta na juyawa mata, Ta rufe ta mayar da mukullin wurin da yake. Da k'yar ta kai d'akin da suke, ta fad'a kan gado, Ta rasa tunanin me zata yi, "Suraj Dan' fashi", Tayi saurin kwab'ar kanta "Baki tabbatar ba", "Wacce hujja nake nema bayan wannan?", "Still kina neman k'wak'kwara", wani sashe na zuciyarta ya fad'a mata, "Ya Rabbi ka taimakeni Ya Allah ka fahimtar dani Ya Allah ka fitar dani a duhu, Ya Allah ni baiwar ce mai rauni kada ka d'aura mun abunda ba zan iya ba", Ta fad'a da k'arashewa da kuka mai tsuma zuciya, Kuka take zuciyarta na zafi tamkar ana hura mata garwashi, Kusan minti talatin tana kuka, kafin ta mik'e ta shiga toilet, ta d'auro alwala ta fara gabatar da nafilfili. Wuraren k'arfe hud'u na dare Suraj ya shigo d'akin sanye da jallabiya, a zaton sa tana bacci, ganin ta tana sallah, ya d'an tsorata, Allah yasa bata gane ya fita ba, Kan gado ya nufa ya kwanta, ya sumbaci Mimi dake ta bacci abun ta, Fetta sam bata ji shigowar sa ba, ta mik'a dukkan hankalinta wurin bautar ubangijin ta da kai masa kukan ta, shi kad'ai zai mata magani. Har aka kira sallar asuba, ta gabatar da sallar asuba, ta zauna tana karatun Qur'ani, Suraj tunda ya kwanta bacci mai nauyi ya d'auke sa, Kukan Mimi yasa ta tsaya da karatun, Ta juya ta d'auke ta, Ganin sa kwance yasa zuciyarta bugawa, ta kalli kayan dake jikin sa, "Mayaudariya mai fuska biyu", Ta tsinci kanta da furtawa, Haushin sa lokaci d'aya taji ya lullub'eta, Ta d'auki Mimi tana breastfeeding, tausayinta na ratsa ta, "Idan Suraj ya kasance dan' fashi, wacce rayuwa Mimi zata yi, ya zata taso taji Mahaifinta Dan' fashi ne", tana fatan kada hakan ya kasance, Yayin da zuciyarta ke son gaskata mata, STORY CONTINUES BELOW A hannun ta ta koma bacci, bata yi yunk'urin mayar da ita kan gadon ba, sai rungumeta tsam da tayi a k'irjinta, tana hango duk wasu abubuwa suspicious da ta gani a tare dashi. Suraj ya farka da sunan Allah a baki, ya kai dubansa ga Fetta, wacce idonta ke rufe ta jingina da gado, zaka d'auka bacci take, but damuwa da tunani ne suka had'u suka dabaibayeta, ga kanta dake masifar sara mata, Toilet ya shiga yayi alwala, Praying mat d'aya ce a d'akin wacce Fetta ke zaune a kai, hannu yasa yayi tapping kafad'ar ta, Ta bud'e ido tana sauke su kan tafin k'afar sa, "Koma kan gado, zanyi sallah", Muryar sa kad'ai tada mata hankali take, ba tare da ta kalle sa ba, ta koma kan gado ta kwanta, ta kwantar da Mimi gefe, taja bargo ta rufe dukkan jikin ta har kan ta, "Jirgin mu sha biyu na rana, zamu koma kano", Ta jiyo muryar sa saman kanta, Ba tare da ta bud'e kan ta ba tace "Ok", Kano take buk'atar komawa, tana son zuwa gidan gonar sa, da guest house d'in sa(Ta tab'a jin sa yana waya akan wani ya same shi a can), Tana son sanin meye had'in sa da Mahaifin Yasmeen, zuciyarta na tabbatar mata yana da hannu a kisan sa, bindigogin data gani yasa ta karaya, zuciyarta ta raunana, Jin cewa zasu koma hakan ya mata dad'i duk da zuciyarta cunkushe take da fargaba had'i da damuwa. Sai da ta tabbatar ta daina jin motsin sa a d'akin, Ta mik'e ta had'a kayanta da na Mimi, Tayi wanka, tama Mimi suka shirya tsaf, Jin shigowar sa, yasa tayi saurin d'aukar wayarta tana dannawa, "Ki taso muyi breakfast", "Ina azumi", "Da izinin wa?", "Nayi ta jiran ka dawo, baka dawo ba har bacci ya d'auke ni", Jin haka ya fice d'akin ba tare da yace komai ba. Bai wani ci abincin ba, ya buk'aci su fito su tafi, Fetta sam tak'i sakin jiki dashi, ko kallon sa bata yi ba, A cikin jirgi ma runtse ido tayi tamkar mai bacci, Suraj a zaton sa bacci take, but duk bayan mintuna yana juyawa ya kalle ta, Sai da taji annoucement na sun sauka, Ta bud'e idon ta, Suraj na gaba tana baya suka fita daga jirgin, Dukkansu bayan mota suka shiga, Fetta har lokacin tak'i yarda ta kalle sa, har suka isa gida babu wanda yayi magana. Ita ta fara bud'e murfin motar ta fita d'auke da Mimi, Suraj ya fito yana bin bayan ta zuwa b'angaren Hajiya, A falo suka same ta tana breakfast, "Ahh Mutanen Lagos saukar safiya kuka yi", Fetta da murmushi d'auke a fuskar ta tace "Ina kwana?", "Lafiya Lau, sannun ku da zuwa", "Yawwa", Suraj ma ya gaishe ta, kafin ya mik'e yace "Zan je na shirya na fita", "Toh Allah ya bada nasara", Ya amsa da "Amin" Ta juya kan Fetta tace "Tashi kije ku huta", Ta amsa da "Toh" Tana mik'ewa, Zuciyarta cike da tausayin Hajiya idan Suraj ya kasance Dan' fashi ya zata ji, Dan' da take tsananin so, take alfahari dashi a ko da yaushe, Da tunanin ta shigo b'angaren su, Lugagge d'insu da ma'aikatan gidan suka shigo dasu, taja zuwa d'aki, Ya fito wanka d'aure da towel, yana tsane jikin sa, Akwatin da ajiye gefe, ta shimfid'e Mimi kan gado, "Fitar mun da kaya", Magana kawai yake so ya mata, ya rasa me zai ce, Shirun da take ya soma damun sa, Wadrobe na kayan sa ta bud'e ta fitar masa da kaftan, had'e da hula da ta shiga da kayan, Ta ajiye masa kan gado ta fice d'akin, Falo ta zauna ta kunna kallo, but hankalin ta sam baya kai, ta lula duniyar tunani. K'amshin turaren sa ya sanar mata da fitowar sa, Saitin ta ya tsaya yana zuba mata idon sa, tak'i d'ago kan ta balle su had'a ido, abunda yake so, "Zan fita", "Allah ya bada sa'a", Ta fad'a ba tare da kalle shi ba, Murya a sanyaye tace "Ina son zuwa gidan gonar ka please, ban tab'a zuwa ba", Yayi mamakin jin haka, but bai kawo tunanin komai ba, sai da dad'i da yaji ta fara damuwa da al'amuran sa, "Idan anyi azahar driver ya kai ki", "Nagode", "You take care", Tayi nodding kai. "Ga kayan na had'a maka", Karima ta fad'a tana ajiye k'aramar akwati a gaban sa, Bello sam bai ji ta ba, yayi nisa a tunani, Ta dafa kafad'ar sa, Yayi firgigit, Kusa dashi ta zauna ta kamu hannun sa, "Dear Dan Allah ka fad'a mun damuwar ka?", "Babu komai, ina tunanin duniya ne kawai", Hannun sa ta d'an matsa tace "Ina hango damuwa a k'wayar idon ka, rashin sanar dani zai jefani a damuwa fiye da taka, Dan Allah Mijina ka gaya mun meye matsalar ka?", Bello ya numfasa yace "Rashin sanin ina ganin shine alkhairi, ko kad'an bana son damuwar ki balle tashin hankalin ki", "In Shaa Allah ko d'aya ba zaka gani ba, kaima da kake cikin damuwar zanyi k'ok'arin fitar da kai, da izinin Allah" Ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya ya sanar da ita duk abunda ke faruwa, Ba k'aramin girgiza tayi ba, hankalinta ya tashi, K'ok'arin b'oye damuwar ta tayi, tare da d'aura murmushi kan fuskar ta tace "Shine ka tada hankalin ka, ka hana ma kanka natsuwa da walwala, Ka bi umarnin iyayen ka baza ka tab'a tab'ewa, idan ni kake ji, kada ka damu, zan jure duk tsawon lokacin da zaka d'auka, In Shaa Allah watarana komai zai wuce, zamu yi rayuwa mai dad'i tamkar hakan bata faru ba", Rungumeta yayi yana jin k'aunar ta na ratsa shi, Karima mace ce ta gari, Ya gode ma Allah da ya ceto rayuwar ta daga halaka, ta zama abokin rayuwar sa. Suraj shago nan sa na electronics yaje, yana duba yadda al'amura ke tafiya, Ya jima bai je ba, sai Manager sa ne ke tafiyar da harkokin wurin. Fetta tana shirin zuwa gidan gona, Kiran Yasmeen ya shigo wayar ta, "Hello Mutanen lagos", "Mun dawo kano d'azu", "Babu sanarwa", "Afuwan idan na kammala komai zan kira ki", Yasmeen tace "Toh", Bata sake cewa komai ba, Ta kashe wayar ta jefa cikin handbag, Ta gyara hijabinta ta fito, Mimi na b'angaren Hajiya, bata tsaya karb'ar ta ba, Tana so ta kawo k'arshen komai, bata son duk wani abu da zai tsayar da ita. Tun daga bakin gate take mamakin girma irin na gidan gonar, Bata k'ara mamaki ba sai da ta shiga ciki, makeken wurin da girman sa ba zai misaltu ba, Ma'aikatan wurin nata gaisheta cike da girmawawa, Rabi'u ya shiga zagayawa da ita kamar yadda Suraj ya kira ya umarce sa, Kusan minti 30 suna zagayawa bata ga alamun zasu kai k'arshe ba, Tace "Wash na gaji, ko zaka bud'e mun office d'in sa na d'an huta", Ba musu yace "Toh Hajiya", Suraj bai ce masa ya hana mata shiga ko'ina ba, sanin kuma matar sa ce yasa zai bud'e mata, but babu wani mahaluki dake shiga office d'in, sai Suraj dasu amintattun yaran sa. Ya bud'e mata ta shiga, "Idan kin gamawa hutawa, sai ki kirani mu cigaba da zagayawa", Tace "Ok", Ya fita tare da ja mata k'ofa, Mukulli tasa ta rufe, Tana bin office d'in da kallo ya had'u iya had'uwa, Kamar na wani governor, Drawer dake jikin centre table d'in sa ta bud'e, Files ne a ciki, ta d'auko su, tana fiddo takardun dake ciki, Kamar na lagos wannan ma sunayen mutane ne, wanda tana jin su a garin, da gidajen radio, Ta karanta duka sunayen babu na Mahaifin Yasmeen, zata mayar ta hango wani tsohon file, ta d'auko tana duba takardan ciki, Idonta ya kai kan Sunan Alhaji Adamu bebeji da bayanai a kan sa, Zuciyarta ta harba da k'arfin gaske, wasu ruwa taji a cikin kunnen ta, kanta ya shiga juyawa mata, rubutun ya koma mata dishi dishi, Kanta na bugawa tamkar ana buga mata guduma, jikinta na kyarma tamkar wacce aka sawa electric shocking Knocking k'ofar ake, ta kasa ko da k'wakk'waran motsi balle tayi yunk'urin bud'ewa, jikinta ke kyarma, bugun k'ofar ya tsananta, "Ya Hayyu Ya Qayyum" Ta furta tana mik'ewa, Da k'yar ta kai bakin k'ofa, ta murd'a mukulli, tamkar jira ake, aka turo k'ofar da k'arfi, Ganin Suraj tayi saurin ja baya kamar taga dodo, tana runtse ido, Office d'in yabi da kallo, yaga yadda ta fito masa da takardu, K'irjin sa ya doka, "Meye dalilin ta na mun bincike?" Ya tambayi kansa cike da mamaki,+ "Waye kai? Meye sana'ar ka?, Ina son sanin ainihin d'abi'ar ka", Ta fad'a cikin karaji ba tare da bud'e idon ta ba, Da kallo yabi ta yana jin yadda zuciyar shi ke bugawa, "Baki da right na personal life d'ina and wa ma yace ki shigo office d'ina ki mun bincike", Idonta da suka yi jajir ta bud'e, tana kallon sa babu alamar tsoro ko shakku a tare da ita, "Ban damu da rayuwar ka da duk abunda zaka aikata ba, rayuwar ya'ta nake dubawa, mutuncina nake dubawa, kamar yadda bana fatan rayuwa da dan' fashi wanda yayi silar kashe Mahaifina", Kalamanta yaji sun daki dodon kunnen sa, but sam ya kasa fahimtar inda ta dosa da zancen kashe mahaifin ta, "Suraj Sa'id ka fad'a mun wanene kai?, Meye had'in ka da mugayen makamai, meye had'in ka manyan mutanen da naga sunayen su?", Duk da ya girgiza da jin kalamanta ya dake yace "Ina ruwanki da rayuwata da abunda nake aikatawa, sake miki da nayi bashi zai sa ki saka kan ki cikin al'amura na ba, you should stay out", Murmushin takaici tayi tace "Ina fatan zargin da nake a kan ka kada ya tabbata, idan kuwa ya tabbata wallahi tallahi sai na mik'a ka kotun addinin musulunci inda za'a yanke maka hukunci daidai da abunda ka aikata" "Idan kin shigo rayuwata ne dan ki tarwatsa ta kinyi kad'an, Suraj Sa'id ba zai tab'a bari kiyi nasara ba", Kallon takaici tabi sa dashi tace "Idan kana ja, ka sanar dani wanene kai?", Cikin d'aga murya yace "Dan' fashi da makami, sana'ar fashi nake, da ita na zama abunda na zama, itace sana'ar da na tara tarin dukiya, itace silar da kowa ke sha'awa ta, yake burin kasancewa tare dani, abunda kike son ji kenan, toh kinji kije ki fad'awa duniya, goo" Ya k'arasa cikin d'aga murya yana nuna mata hanyar fita, "Dan' fashi da makami", Ke yawo a k'wa'kwalwar kan ta, Office d'in na juya mata, komai double take ganin sa, Kalaman sa tamkar saukar aradu haka taji su a dodon kunnen ta, zuciyarta na tsananta bugawa, zafi take ji a jikin ta tamkar ana hura mata garwashin wuta, hak'oran ta na karkarwa, tun daga ranar da Yasmeen ta sanar da ita, bata tab'a jin tashin hankali da firgici kamar yau da taji daga bakin sa, idonta taji suna lumshewa a hankali ta fad'i bata numfashi, A gigice Suraj yayi kanta, yana jijjigata, Harshe shi tamkar an datse shi ya kasa furta komai, d'aukarta yayi cak ya fito office d'in a rud'e, Ma'aikatan wurin suka yi kansa, suna tambayar lafiya, bai bi ta kansu ba, Ya sakata bayan mota, Shima ya shiga, Driver da sauri ya shiga yaja mota, ko ba'a fad'a masa ba yasan asibiti zasu je, Asibitin International ya nufa dasu, babu b'ata lokaci aka shiga da ita, Likitoci suka shiga bata taimakon gaggawa, Yaso shiga d'akin da ake treating d'in ta likitocin suka hana, Ya kasa zaune ya kasa tsaye sai zirga zirga yake, yana addu'ar samun lafiyar ta, ya rasa tunanin me zai yi, kansa gaba d'aya ya k'ulle, kallo d'aya zaka masa kasan yana cikin tsananin damuwa da tashin hankali. Bello ya iso garin kano cike da k'udirin bin umarnin iyayen sa, maganun Karima sun yi tasiri a kan sa, kaso d'ari na damuwar sa, hamsin ya rage, Bai samu wata tarba daga wurin iyayen sa ba, Kawu Lamid'o ya kai duban sa gare sa yace "Maza ka shirya yanzu ka tafi wurin Tasleem, kar na sake naji ka mata abunda ba daidai ba", Cike da ladabi ya amsa da "Toh" yana nufar d'akin sa, Ruwa kad'ai ya watsa, ya canza kaya, Ya fesa turare shima dan yana so, ba dan zai je wurin ta, baya k'aunar sake ganin ta, dole ce kawai zata sa, Shigowar text d'in Karima ya katse masa tunani "Ina fatan Mijina ya sauka lafiya, kuma ina fatan baya tare da wata damuwa, ba zai bari wani abu ya b'ata masa rai ba", Yayi murmushi yana jin k'aunar ta na ratsa shi, Ya mata reply mai cike da kalaman soyayya. Tasleem ta fito tana yanga, Bello dake zaune kan kujera a falon, ko kallo bata ishe sa ba, har ta zauna, "Sannu ko", Ta fad'a, "Yawwa, ya mutanen gidan?", "Lafiya", Ta fad'a tana tsare sa da ido, kyawun sa take gani duk da bai kai Suraj ba, kyan ya mata, Lemo ta tsiyaya a kofi ta mik'a masa, sip d'aya yayi ya ajiye, Tana ta jan sa da hira, bai jima ba yace zai koma akwai wurin da zai je, Ya karb'i number ta, ta masa rakiya har bakin motar sa, Ya tafi yana tunanin yadda zai yi rayuwar aure da yarinyar da baya jin ko d'igon son ta. Dalelliyar mota ta sauke Bilkisu bakin gidan su, ta bud'e murfin seat na baya ta fito, Hajiya Rabi tasa a maidota gida bayan sun gama shek'e ayar su, "Kin dad'e Bilkisu, tun d'azu nake jiran ki, kizo muje yima Hajiya Allah sanya alkhairi an sa ranar Feena", Cewar Aunty Jummai, Ta tab'e baki tace "Ba sai munje ba Umma, dan kawai ansa mata rana", "Ke dalla mara wayo kissa ce ai, hakan zai sa taji dad'i", Bilkisu mamakin makirci da kissa irin na mahaifiyar ta take, Gyale ta cire, ta kasa hijab, Aunty Jummai dama da shirin ta, Suka nufi gidan Hajiya. A falo suka sameta ita da Feena suna lissafin abubuwan da za'a siyo, Aunty Jummai tana washe baki ta shiga zuba addu'a da nuna farin cikin ta, Bilkisu ma tayi addu'ar Allah ya sanya alkhairi, Hajiya ta amsa su da sakin fuska, Feena kam sama sama ta amsa su, Hajiya tace "Bilkisu yaushe za'a k'ara yin aure?", Aunty Jummai tayi saurin cewa "Kowa yazo sai tace bata so, ita dai Suraj", "Allah sarki", Hajiya ta fad'a tana d'auko wani zancen, Aunty Jummai ba haka taso ba, dan Boka ya fad'a mata Hajiya ta kanta zata ce Bilkisu ta koma gidan Suraj. Idonta ta bud'e a hankali, tana jin yadda kanta ya mata nauyi, da kallo tabi d'akin, hakan ya tabbatar mata asibiti ne, drip dake sak'ale a hannun ta, ta fisge, Bata buk'atar kulawar kowa a yanzu, Ciwon dake zuciyarta ya girmi asibiti, idan zata shekara anan baza su mata maganin komai ba, Saukowa tayi daga kan gado, ta d'auki hijabin ta dake gefe ta saka, Ta fito d'akin tana jin jiri na d'ibar ta, tamkar zata fad'i, Suraj dake bakin k'ofa yayi saurin tasowa ya nufo ta, Da hannu ta dakatar dashi, "Kada ka kuskura kazo kusa dani", Ya sake matso ta yana fad'in "Ina zaki je baki da lafiya, ki koma kada ki jawowa kan ki wani ciwo", Bata saurare sa ba, ta rab'a gafen sa zata wuce, yayi saurin shan gabanta, yana k'ok'arin rik'e ta, Taja baya tana fad'in "Kada ka tabani, kada ka sake yunk'urin hana ni fita daga asibitin nan", Ganin idan ya tsaya jayayya zaat tara musu mutane, yaja gefe, Taka k'afarta take ba tare da tasan ina take nufa ba, natsuwa sam baya tare da ita, Har ta kai bakin gate, tsintar kanta tayi da tarar napep ta masa kwatancen gidan Suraj, Suraj tana fitowa yabi bayanta, ganin ta shiga napep, ya shiga mota yabi bayan su, Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke ganin gida aka sauke ta, Tana shigowa, Samee ta fito daga b'angaren Hajiya rik'e da Mimi nata kuka, "Tun d'azu take ta kuka, an bata madara tak'i dainawa", Karb'ar ta tayi ba tace komai ba, Ta rungume ta, Mimi shiru tayi kamar ba itace ke kuka ba, ta nufi b'angaren Suraj tana jin tsana da k'yamatar gidan da duk abunda ke cikin sa, Tana ganin kiran Yasmeen tak'i d'auka har ya tsinke, Bata buk'atar magana da kowa a halin yanzu, bata buk'atar shawara kowa, zuciyarta zata bi, bata son duk wani da zai hana mata aiwatar da kud'urin ta, Suraj babu natsuwa a tare dashi ya shigo, ganin ta falo tsaye rungume da Mimi, ya sauke ajiyar zuciya a zaton sa tana b'angaren Hajiya, ta sanar da ita waye shi, baya k'aunar abunda zai d'aga hankalin Hajiya ya jefata a damuwa, meyasa ya bari Fetta ta shigo rayuwar shi, da yasan haka zata kasance ba zai tab'a sake mata ba, ta yadda zata yi bincike a kansa, Fetta ta katse masa tunani, takarda da biro ta ajiye a gaban sa, "Ka rubuta mun takardar ta", Ta fad'a tana masa kallo mai cike da tsana. Kallon ta yake a razane, yana son tabbatar da abunda kunnen sa suka jiye masa, "Kai nake jira, saki uku nake buk'ata", Wani banzan kallo ya watsa mata yace "Are you out of ur sense, kinsan me kike fad'a?", "K'warai kuwa Suraj takardata nace ina buk'ata", Mamaki ya cika sa ganin yadda take masa magana gatsau,+ "Taya kake tsamannin na cigaba da zama da Dan' fashi wanda cin sa, tufafin sa, muhallin sa duka daga haramun ne, har nima ya ciyar dani ta wannan hanyar, taya kake tunanin na cigaba da zama da mutumin da ya bada umarnin a kashe mahaifina" Ta k'arasa hawaye masu d'umi na wanke fuskar ta, "Sam ban gane ina maganganun ki suka dosa ba, Ni Dan' fashi ne amma taya na sama silar kashe mahaifin ki?", "Gidan Alhaji Adamu da kaje fashi, mai gadin sa shine mahaifina, Ka cuce ni Suraj, Allah ya isa tsakanina da kai, ina fatan wannan ta zama rana ta k'arshe da zan saka a idona, bana fatan sake ganin ka a rayuwata" Ta zauna k'asa tare da k'ank'ame Mimi a jikinta tana kuka mai tsuma zuciya, zuciyarta na d'aci wanda ke kawo mata har cikin mak'oshin ta zuwa bakin ta, Suraj tashin hankalin da bai tab'a ji a rayuwar sa ba yaji ya dabaibaye sa, ko rasuwar mahaifin sa bai ji irin sa ba, zufa ta shigo karyo masa, zuciyar sa na dokawa da tsananin k'arfi, yana jin ina ma mafarki yake ya farka, har cikin ransa yake jin kukan ta, wanda ke k'ara d'aga hankalin sa da dagula masa lissafi, Cikin karyewar zuciya ya gurfana gaban ta, yana k'ok'arin kai hannun sa ya tallabo fuskar ta, Tayi saurin ja da baya tana fad'in "Kada ka sake ka tab'a ni, bana buk'atar komai daga gare ka sai takarda ta", Yawun bakin sa ya kafe, ya kasa furta komai, ya rasa da wacce kalma zai fara bata hak'uri ya tausasa zuciyar ta, mutuwar mahaifin ta shine babban laifin da yake ganin ya aikata mata, zaman shi dan' fashi bai shafi rayuwar ta ba, Ta katse mishi tunani "Ka bani takarda ta ko naje na sanar da Hajiya komai da sani game da kai", Jin haka ya girgiza, baya son tashin hankalin Hajiya, haka baya jin zai iya sakin ta, bai tab'a jin rashin son rabuwa da ita kamar yau ba, Cikin karyewar zuciya yace "Dan Allah Fatima ki.....", "Bana son jin komai, bana buk'atar jin wata kalma da zata fito daga bakin ka", "Ki duba Mimi, kina so ta taso babu uwa a tare da ita, kina so tayi rayuwar maraici", Sai a lokacin ta d'ago tana bin sa da kallo mai cike da tsana tace "Kana tunanin zan tab'a barin ya'ta ta taso cikin k'azamar haramtacciyar rayuwar ka, har abada bazan bari tasan waye Mahaifin ta ba, dan bara ta tab'a alfahari da kai ba, daga yau mahaifin Mimi ya rasu, na shafe tarihin shi a cikin rayuwa ta da na ya'ta, bana fatan mu sake ko da awa d'aya a k'ark'ashin inuwar ka" Zuciyar shi ke tafarsasa, maganun ta sun b'akanta ran sa da zuciyar sa, babu mahalukin da ya tab'a fad'a masa magangun da suka sosa zuciyar sa kamar yau, lips d'in sa na k'asa ya cije cikin tsananin b'acin rai, har sai da ya jini ya fito, Zuciyar sa na ingiza sa da hasassa masa ya sake ta, Takardar ya jawo tamkar zai yi k'wace a hannun wani, ya d'auki biro cikin zafin nama, ya rubuta mata saki biyu, Ya jefa mata takardar yana ficewa daga falon, Takardar ta d'auko ta karanta, zuciyarta ta harba da k'arfi wanda ta rasa dalili, mik'ewa tayi, Ta goya Mimi, ta saka hijab da nik'ab, K'aramin littafi mai d'auke da asalin ta kad'ai ta d'auka, Ta fice daga gidan ba tare da kalli b'angaren Hajiya ba, bata son duk wani abu da zai tsayar da ita, Zuciyarta take bi, ba abunda take buk'ata kamar tayi nisa da Suraj da duk wani abu da ya dangance shi, Gidan Waheeda ta nufa, Ta same ta ita kad'ai mijin ta baya nan, Kallo d'aya Waheeda ta mata ta hango rashin natsuwa a tare da ita, "Lafiyar ki kuwa Fetta?", "Jikina ne baya mun dad'i", Ba dan ta yarda ba tace "Allah ya baki lafiya", "Amin Dan Allah aron dubu goma nazo ki bani", Karon farko a rayuwar ta da ta rok'i abu wurin wani, shima babu yadda zata yi ne, duk kud'in da ta samu ta hanyar Suraj, ta ajiye masa, hatta ATM d'in ta bata d'auko ba, Waheeda tayi mamakin jin haka sanin irin dukiya ta Suraj, ba tare da tace komai ba, Ta shiga d'aki ta d'auko ta bata, tace "Kyauta na baki", Fetta ta amsa ta mata godiya. STORY CONTINUES BELOW Daga gidan Waheeda ta tari napep tace ya kai ta inda zata samu motar Nijar, Tasha ya kai ta, ta shiga motar agadez, tazo a sa'a mintuna kad'an motar ta cika suka d'aga, Shiru tayi ta jingina da window, duniyar sam bata mata dad'i, banda rad'ad'i babu abunda zuciyarta ke yi, Tsantsar nadamar auren Suraj fal a zuciyar ta, babban bak'in cikin ta had'a zuri'a dashi, ina ma zata iya maida hannun agogo baya, ta goge duk wani abu da ya danganci Suraj cikin rayuwar ta, Meyasa ta amince da auren shi, "K'addara" Wani b'angare na zuciyar ta ya fad'a, Wani zafi taji na ratsa jikin ta, gefen kanta na sarawa, Sunayen Allah ta shiga ambato, Suraj yana fita, motar sa ya shiga yaja, sam baya cikin natsuwar sa, maganganun Fetta ke yawo a k'wak'walwar kan sa, Driving yake kamar mai sabon hauka, saura k'iris ya bige wani mai mashin, Allah ne kad'ai ya kawo sa guest house d'in sa lafiya, Mai gadi a sukwane ya bud'e gate jin irin horn da yake, Ya danno motar ciki da matsiyacin gudu, Da sauri mai gadi ya kauce, Rough parking yayi ya fito, ya shiga ciki, Kan kujera ya fad'a yasa hannayen sa biyu yana dafe gefen sa dake tsananin sara masa, "Kina da labarin Fetta kwana biyu ban ji kin ce tana gaishe ni ba", Cewar Mallam dake kishingid'e kan tabarma a tsakar gida, Aliya dake wanke wanke tace "Wallahi shiru ban ji ta ba, wayar ta idan na kira bata shiga, ina tunanin unguwar da suke a can babu network", "Toh Allah yasa hakan, amma anjima kije gidan ko sunyi waya da ita", "Toh In Shaa Allahu da yamma zan lek'a", Ya k'ara sautin radio dake gefen sa yana saurare, Yasmeen ta duba wayar ta a karo na ba adadi ko zata ga kiran Fetta, Kan number ta takai tayi dialing, bata shiga, Ta kira ya kai sau biyar amsar d'aya ce, "Lafiya wayar ta bata shiga yau", Ta fad'a cike da fargaba da addu'ar Allah yasa lafiya. Hajiya hidimar bikin Feena ta d'auki hankalin ta, duk da ba shagalin biki za'a yi ba, Siyayyar kayan d'aki kullum cikin yawon kasuwa da shopping malls suke, Shigowar su kenan gida, Aliya ta shigo, "Yanzu nake ganin shigowar ku, ashe da nazo tun d'azu bazan tarar daku ba" Cewar Aliya, "Wallahi tun azahar sai yanzu muke dawowa" Cewar Hajiya tana zama kan kujera, Feena ciki ta wuce ba tare da tabi ta kan Aliya ba, "Sannu Allah ya nuna mana lokaci lafiya", "Amin", Jim kad'an tace "Kuna da labarin mutanen lagos, tun tafiyar su bamu yi waya ba", Hajiya tace "Sun dawo d'azu da safe ai", "Au na d'auka suna can, idan na kira wayar ta bata shiga", "Tana nan b'angaren ta", "Bara naje" Aliya ta fad'a tana mik'ewa, A bud'e taga k'ofar falon, ta shiga da yin sallama, Shiru ba'a amsa ba, kusan sau uku tana yi shiru, "Toh ko bacci take", Muryarta ta d'aga sosai tana sallama, Jin shiru tace "Ina ga sun fita", Ta koma sashen Hajiya take sanar da ita basa nan, "Ina jin sun fita, da yake nima bana gidan", "Bara na koma, na bar su Hajar su kad'ai a gida", "Toh ki gaishe su", "Zasu ji" 9:00pm na dare Har lokacin Hajiya bata ji dawowar su Suraj ba, Wayarta ta lalubo, ta danna kiran sa, Suraj wanda tunda kwanciyar sa a wurin, bai tashi ba, kansa ya masa masifar nauyi, yana masa ciwon da bai tab'a ji ba, jikinsa na hucin zafi, Sallar magrib da isha'i yana ji ana kira but ya kasa ko da k'wakk'waran motsi, balle yayi yunk'urin yi, yana jin wayar sa na k'ara, ya kasa d'auka, har ta tsinke, kira kusan biyar na shigowa babu wanda ya d'auka, Hajiya hankalin ta ya fara tashi, bata tab'a masa kira haka bai d'auka ba, wayar Fetta ta shiga kira sam bata shiga, "Ya Allah kasa yaran nan lafiya suke", Ta fad'a fuske d'auke da damuwa. Tafiyar awa goma sha d'aya ta kawo su garin Agadez, duk tsawon tafiyar, bata yi ko gyangyad'i ba, tana ganin yadda abokan tafiyar ta ke bacci a natse, tana jin ina ma itace bata d'auke da wata damuwa, Tashar garin aka sauke su, kowa ya shiga d'aukar kayan sa, Fetta bata zo da komai ba sai kayan jikin ta, mai taxi ta tara tace ya kaita masarautar Agadez, Garin take bi da kallo, tana jin sanyi sanyi a ranta na zuwa asalin ta da mahaifar ta, Mamakin girma da tsaruwar masarautar take, tana fatan samun natsuwa da kwanciyar hankali mai d'aurewa a garin Agadez cikin dangin ta, "Nan zan ajiye ki, ba'a bari mu k'arasa ciki", Ya fad'a da yaren buzaye, Kud'in sa ta tambaye sa, Yace "Sefa" bata san kud'in nijar ba, kuma bata yi chanji ba, Ta zaro dubu d'aya ta bashi tace "Kayi hak'uri kayi chanji, shigowata daga nigeria kenan", Babu musu ya karb'a ganin ta ninka masa kud'in, yaja motar sa ya tafi. Tunani take ina zata dosa, bata san hanyar da zata sada ta da b'angaren Azagas ba, bata san had'uwa da kowa, sai ta fara ganin ta. Hajiya hankalin ta ya tashi sosai ganin har safiya babu Suraj da Fetta babu alamar su, duka wayoyin su a kashe, Ta kira Aliya ta sanar da ita, kofin da ta d'auko ta zuba kunu ta saki ya fad'i, tana rafsa salati, Mallam yayi kanta yana tambayar lafiya, ta sanar dashi, Salati yayi ya sanar da ubangiji. Yasmeen ganin har safiya bata ji daga Fetta ba, ta kira wayar ta kashe, Ta shirya zuwa gidan taga lafiya, labarin da ta tarar ya d'aga hankalin ta matuk'a. Suraj daren jiya da k'yar ya samu ya gabatar da sallar magrib da isha'i, bacci ya k'auracewa idonsa, sam bai runtsa ba ciwon da kansa ke yi, ya hana masa yayi tunanin komai, har ya fara jin kiraye kirayen sallar asuba, ya mik'e ya d'auro alwala ya gabatar da sallah, Abubuwan da suka faru tsakanin sa da Fetta ke dawo masa har zuwa sakin ta da yayi, K'ara yayi yana dafe kansa da fad'in " No ban sake ta ba", Mukullin motar sa ya shiga nema, can ya hango sa k'asan carpet, ya d'auka yana fita babu natsuwa a tare dashi.

Post a Comment for "FETTA CHAPTER 26"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...