DR SALEEM CHAPTER 7 KARSHE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

DR SALEEM CHAPTER 7 KARSHE

DR SALEEM CHAPTER 7 KARSHE

- - Post a Comment
DR SALEEM CHAPTER 7 KARSHE s

Saleem dagowa yayi ya kalleta irin kallon dayake mata yasa jikinta yayi sanyi amma a haka takarasa shigowa cikin office din jawo kujera tayi ta zauna tana sakar mishi murmushi . + magana yakeson yi amma yasaka sakamakon kamshin turaren dayaji yi yayi kamar an buga mishi guduma akai ita kuma safiyya ganin yanayinshi yasa ta saki wani shu'umin murmushi. sannan ta matsa kusa dashi nan ma yakara shakan kamshin cewa yayi ki wuce kibani wuri banason kamshin nan ki fitanmin daga office . kara matsowa tayi yace i said get out! ai dagudu ta fita . sai data bar asibitin sannan ta tsaya tana sauke ajiyan zuciya. taxi ta tare ta nufa gidansu surry. tana isa taga surry na shirin fita. a kofar gida sukai clashing . surry tace lph naganki haka . safiyya cewa tayi hmmm mushiga kyaji komai . surayya cemata tayi gaskiya sauri take yi sugar daddy dinta na jiranta. safiyya tace haba kawas dan Allah ki tsaya muyi mgn mana kinsan ba wanda nake kaima kuka na sai ke. toh shikenan mu shiga amma gaskiya minti biyar na baki. suna shiga dakin safiyya tagayama surayya yanda sukai da saleem. tsaki tayi tace ai kema kin bata kin manta abinda boka yace ne. ai cewa yayi yana cikin wannan halin zakiyi ta ambatan sunanshi sau uku . safiyya durkushewa tayi a kasa tace nashiga uku dan Allah kizo mukoma wurinshi. surayya wani kallo ta watsa mata tace aikinsan hanyan wllhy bazan raka kiba ke gaba daya kin rikece akan wani saleem shi kadai ne namiji nafada miki akwai hot guys dasuke sonki kinki kibada hadin kai. kin nace ma wani saleem . kewai nan Aure kikeso kiyi. bayan saleem dinnan ba sonki yakeba yanada mata amma kinbi kindamu kanki. ga Abokin sugar daddy dina yanata min magananki tun randa ya ganmu amma kinki ki amince mishi wanda wllhy saleem ko taka kafanshi beyiba ina dai wurin naira ne. safiyya kallon bnza ta watsa mata tace nifa ba iskanci nakeso nayiba aure nakeso nayi kuma duk wa'innan yan iska ne . suma din ai da Aure suke sanki dan haka kibada kai bori ya hau kimanta da saleem in kuma zakiyita kashe kudinki a banza toh shikenan Allah ya taimaka. safiyya zama tayi tai shiru sannan tace kai no way bazan taba bari ba saleem nawane bazan taba barin ma husna shiba. domin in na bar mata tamkar tayi nasara kenan. surayya tace nasara kuma ta nawa ai tariga tayi nasar tunda ta rigaki Aurenshi. tsaki surayya tayi tace ke nikinga tafiyata Alh nakirana. safiyya tace toh shikenan ni zan koma wurin boka . surayya tace okay toh duk yanda kukayi naji. tare suka fita kowa yayi hanyarshi. saleem kuwa ganin kanshi ya matsa mishi da ciwo yasa ya nufa gida. yana shiga ya tadda husna a falo ganin yadda ya hade rai yasa itama ta shareshi sallamarshj kawai ta amsa . wucewa yayi kawai ya shiga dakinshi direct toilet ya shiga yayi wanka ya fito yayi sallah. tsintar kanshi yayi dason karanta Alqur'ani daukowa yayi ya karanta A hankali yakejin zuciyarshi tana sanyi . A haka har ya kammala iya yanda ya sawwaka sannan ya tashi ya fito falo koda ya fito bega husna ba dan haka direct yaje dinning yaci abinci ya koshi sannan ya nufa dakin husna. a kishingidw yaganta akan sofa tana waya tana murmushi . karasowa yayi ya tsaya a kanta jin kamshin turaren shi besata ta dagoba kuma besa ta ajiye wayan ba har saidatagama wayan sannan ta tashi zatabar dakin dan ko kallon inda yake batayiba bata ma nuna tasan yana dakinba. shikuwa gaba daya ya shaka . cin fushi da tsawa yakira sunanta. bata juyoba amma dai ta tsaya chak. karasowa yayi ya fincikota. yace mekike nufi danine ? kinawaninshareni nidaya kamata nayi fushi dake banyiba saike ce zaki fushi dani. kallonshi tayi tace ni ka sakeni dan Allah u are hurting me kara matse ta yayi. yace oh really !so u r feeling hurt. kai ta daga mishi kawai . saketa yayi yace husna me akamiki kike fushi . menene abin fushi menene abin damuwa keda kikacena karo mata . ni yanzu nadaina matsa miki ni nariga nasan bazaki iya daukan lalurata ba shiyas anga gwamma nabi shawaranki dan haka kika ranki a inuwa kidaina bata ma kanki rai ki sa farinciki a zuciyanki domin kuwa burinki zai cika . insha Allahu in the next 2 weeks Amaryata zatazo. yana gama fada ya wuce yabarta a tsaye kamar statue . husna jitayi kamar ta fasa ihu ko zataji sauki. safiyya kuwa wurin boka ta koma ta mishi bayani kan matsalan da akasamu. boka kuwa wani irin ihu yayi yace hakika kinyi kuskure domin yanzu ba wacce zai tsana samadake. safiyya kuka ta rushe dashi race nashiga uku🙆🏼‍♀️ dan Allah boka . bata karasaba boka ya daka mata tsawa yace ke ba'a hadamu da Allah. a rikice tace toh dan Aljani samiri ka taimakeni. boka kecewa yayi dawani irin dariya sannan ya hade rai kamar betaba dariya sannan ya buka kasa ya gige ya sake bugawa yayi zane zananshi sannan yace afita daya ce kiba bakin aljani jikinki na kwana biyu toh da haka ne zaki mallaki saleem zaki kuma juya shi tamkar rakumi da akala . safiyya rikicewa tayi tace nidai boka wannan yayi tsauri achanza wani bukatan. wani irin tsawa ya daka mata yace fice kibamu wuri kafin bakin aljani ya batar dake . safiyya durkusawa tayi tace...... Safiyya cewa tayi to boka na amince zanyi duk yanda kace indai zan mallaki saleem kuma na raba shi da matarshi,+ Boka kecewa yayi da wata matsanancin dariya yace tunda kin Amince toh ga daki chan kije ki cire kaya kayanki ki kwanta baki aljani zaizo yayi abinda zaiyi dake. Safiyya tashi tayi tana tunanin abinda zata aikata wata zuciyar ta haneta wta zuciyar ta ingizata zabin dayan zuciyanta tabi wanda take nuna mata cewa ai ba wani abu bane dan kinyi domin kuwa salee sai yanda kikai dashi zaki juyashi sannan sai abinda kikace mishi zaiyi da wannan tasamin. kwarin guiwar shiga dakin da boka ya umarceta tana shiga ganin yanayin dakin sai da hanjin cikinta ya murda domin kuwa dakin gaba daya duhune sai dan haske kadan wanda yake bayyana kwarangwal din dske dakin kayan tsafine a dakin. juyowa tayi dan ta koma waje amma bata ganin hanyan komwa dariya kawai taji an kece dashi ance la'ananniya ina zaki ai bake ba fita domin kin riga dakinshigo keda fita dakin nan kuma sai bayan kwana uku lokacin bakin aljani yagama biyan bukatanshin dake. safiyya kuwa jitayi fitsari na binmata jiki domin gaba daya ta rude ta rikice ihun da aka mata shiyadawo da ita hayyacinta. boka cewa yayi kwanata la'ananniya kicire kayanki kuma idan ba haka ba kika kara minti biyar sai dai ki haukace. safiiyya taji maganar hauka dagudu ta fara cire kayanta ta kwanta akan gado . nan boka yazo yagama abinda zaiyi da ita sannan ya fice safiyya ko gaba daya ta galabaita domin yafi awa uku yana abu daya gashi shine yafara saninta ya mace ai tasha a zaba. tana cikin tunanin rayuwar dat a tsinci kanta da tunanin yanda zata gayra kanta domin har yanzu dakin duhu ne ba abinda take hangowa. sai kwarangwal tana zuane tana hawaye sai kwai taga dan haske ta wani kofa tashi tayi tabi hanyan lekawa tayi taga bandaki ne amma gaba daya wani irin doyi bayin yakeyi a haka ta daure tashiga tai wankan tsarki domin ko ruwan zafin dazata gasa jikinta babu ruwansanyi kawai ta samu ta dauraye jikinta tafito ta kwanta ta kwanta ba jimawa taji an danneta an kara afka mata. a takaice. dai safiyya sai datayi kwana uku tana ganin bakar izaya a cikin gidan bangaren iyayenta kuwa ba irin tashin hankalin da basu shiga ba domin kullum cikin nemanta akeyi ba dare ba rana. bangaren surry bby kuwa tasa tsoron gaya ma iyayenta inda tace zata karshe domin tasan kila tana chan dan ita boka sai datai mishi kwana uku sannan yayi mata aiki akan alhajinta amma sai dai tai shiru tace bari dai in ta wuce kwana uku tafada musu inda taje . bayan kwana bakwai amma shiru ba labarin safiyyadangi ba wanda be saniba na kusa dana nesa an bazama sai addu'a akeyi Allah ya bayyanata surayya ma hankalinta atashe yake domin takanas taje wurin boka amma yace mata bata wurinshi hade da zagi yamata ya kuma ce inta kara dawowa sai ya haukatata STORY CONTINUES BELOW shiyasa surayya taaama kanta lafiya taja bakinta tai shiru boka kuwa bayan tafiyanta yace ai shi tunda yaie betaaba jin dadin wata mace ba kaar safiyya dan haka shi yama aureta ta zama matarshi annan zata rinka rayuwa bawanda ya isa ya rabasu bangaren safiyya kuwa danasani ne fal acikin ranta ta rame ta jeme tayi baki don bokan koda yaushe cikin kawo mata kanshi yake tun tana kuka har ta daina kuka sai dai na zuci takeyi yana kawo mata abinci da ruwa kullum safe rana dare. itakam yanzu ba komai a gabanta sai istigfari datake yawaita yi sannan tana addu'a Allah yafitar da ita daga gidan nan na ukuba bangaren husna da saleem kuwa ba wani sauyi husna na zaune a falo taga ana shigowa da akwatina gaba daya jitayi gabanta ya fadi sannan cikinta ya juya sagudu ta nufa toilet dan jim kadan sai ta fito ta koma falo lokacin saleem na zaune a falo dagowa yayi ya kalleta yaga gaba daya tashin hankali a idonta dariya ce taso subce mishi amma yayi maza ya gimtseta . yace ga kayan fadan kishiya nan na miki kuma duk abinda kike bukata ki sanar dani dangane da bikin da wani shirye shirye da zakiyi. daurewa kawai tayi ta daga kanta . shikuwa ganin tana shirin yin kuka yasashi tashi yabar mata falo. husna da sauri taje daki ta dauki wayanta ta kira yasmeen tana dagawa yasmeen tace uwargida ran gida ya akayi ne? husna kuka kawai ta fashe dashi tace dama da gaskene yasmeen tace mene? husna tace aure mana yaya saleem aure zaiyi yasmeen tace eh mana aure zaiyi yau sauran one week ma husna kam ihu ta kurma na shiga uku naja ma kaina wayyo Allah mutuwa zanyi rayuwata tazo karshe yaya saleem ya ksheni. yasmeen tace da akayi me husna kefa kikace yayi aure nikuma yazo ya sameni yace nasamo miahi budurwa aikuwa na hadashi da kanwar kawata suka daidaita kansu. husna wani kukan ta saka tace Allah ya isa tsakanina dake yasmeen wato dake za a hada kai a cuceni ko toh wllhy daga yau bani bake kit ta kashe w wayan jefar da wayan tayi sai kuma chan ta dauko ta fara dialling numbern mummy mummy ringing biyu ta daga tace my daughter yadai kuka hussna tasa tace mummy wai yaya saleem aure zaiyi mummy tace eh mana husna yazo ya samemu yace zaiyi aure da farko dai naki yarda tunda naga dudu du yaushe akai aurenku amma kuma dayana bani hujjijinshi sai naga tabbas ya cancanta da yayi aure kuma kema kanki husna ai kinga cancantan haka tunda kw kanki kin bashi shawaran yayi auren. wayyo Allah husna jitayi kaar zuciyarta ta fashw kit ta kashe wayan bata ma mummy sallama ba. jefar da wayan tayi ta nufa dakin saleem a tsaye taganshi ya kara waya a kunnenanshi yana murmushi juyowa yayi ya kalleta sai kuma ya juya baya yace kedai bari bbyna na kusa kishigo gidana domin nasan ke bazaki taba gajiya dani ba kuma na yarda dason da kikemin dari bisa dari. domin kuwa so abaki bashi bane so a aikace ne kuma ni na yarda dacewa duk abinda nakeso shi kikeso. kai bby i wish kena fara aura amma ba matsala better late than never. bari na barki haka domin ni jin muryanki gaba daya mantar dani yake inajin yunwa balle kuma ganinki in kina gabana bana son kallan ko wata ace gani nake duk ba mata bane a gabana. husna kuwa jitake kamar ta shakeshi domin zuciyanta jitake kamar ya fashe saleem sai daya gama soyayyarshi sannan ya juyo yace uwargidana yaushe kikazo nan. husna da gudu ta nufeshi tafara dukan shi a kirji tace ni sai ka sakeni yau wllhy saleem baka sona ka tsaneni so kake ka kasheni kaga bayana ko kuma kasamin ciwon xuciya na mutu ka huta dama yanzu batani kakeyi ba ta amaryarka kakeyi tunda ni kagama dani dama na san ba sona kakeyi ba jikina kakeso ai na dade da sani tana magana tana dukanshi. saleem tureta yayi yace ai abinda kikeso shina miki da bakinki kikace na karo aure toh meye laifina nabi abinda matata takeso ai ba laifi bane ni duk abinda kikace nayi shi nayi turehi tayi tace wllhy karyane ai ni dawasa nake mak shine kaje ka na neman wata wai har zakayi aure juri ne raji yana dibanta rike kanta tayi zata fadi da sauri saleem ya tarota tureshi tayi tace nika rabu dani eyasa baka barni na na fadiba in ma mutuwane nayi wllhy baka sona ka tsaneni kuma yanzu zan bar maka gidanka zan tafi inda bazaku sake ganina ba da kai da kowa ma har da mummy dama nasan yanzu an daina sona tana gama fadan maganan ta tashi ta nufa dakinta ta dauka trolley ta harhada kayanta aciki saleem kuwa ya fara fargaba domin yaga dagaske takeyi. yana fitowa falo yaganta da trolley da sauri ya matso kusa da ita yace ina zaki tace zanshiga dunya yace amma badai da cikina ba sai kibari idan kinhaihu kya tafi duk inda zaki hararanshi tayi tace nibani dawani ciki kuma ko inadashi sai na zubar da shi. saleem ji yayi kamar anbuga mishi abu akanshi cike da bacin rai ya isa gaban husna ya shaketa yace wllhy kika zubar min da gudan jinina sai na miki abinda baki taba tunanin ba in kuma kince karya ki gwada kigani ga hanya nan bazan hanaki fita ba.tureta yayi ita kuwa tashi tayi cike da azaban da takejin na shaketan dayayi ta tashi ta fara jan trolley dinta ganin da gasketa take dasauri saleem yaje ya dagota chak sai dakinshi ya kaita. kwantar da ita yayi akan gado ya kow ya rufe kofa dawowa yayi ya zauana a kusa da ita yace yanzu mekikeso tace takardana ko kuma ka fasa aure tace hade da turo baki kama bakin yayi yace bako daya daza a yi kuka ta fashe da shi ta kwanata a kasa har da birguma ganin da gaske takeyi yace toh tsaya kiji shikenan za a daga bikin ai sai ta kuma sa wani ihun yace kai bby kincika damuwa kefa kikace nayi aure yanzu kuma kinxo kina fushi. tace ai wasa nakeyi ama DAN Allah kace ka fasa auren wllhy duk abin da kakeso zan maka in ma zaka iya nemana sau hansin a rana zan iya indai bazaka kara aureba kaji ps kace ka fasa. shiru yayi ya juya idonshi sannan yac gaskiya nidai........... toh fans kuna ganin saleem zaifasa auren nan kuwa ko kuwa dai zaiyi auren??uya ido saleem yayi sannan yace gaskiya nidai ba zan fasa auren nan ba sannan kuma bazan rbi dake ba husna najin haka ta fara sakin kukan shagwaba tace nidai Allah kazabi daya yace nidai naki ya kwaikwayi mgananta dukan wasa ta kai mishi. Kirjinshi sannan tace nidai dan Allah yaya kafasa auren nan yace in nafasa me kikeso naje nace ma amaryata sannan me zance ma su daddy da mummy sannan kuma ai kinga b dadi ba wanda zaiji dadi ace ankusa bikinshi kuma ace anfasa koke nama haka bazakiji dadiba kuma nima bazanso na haihu ama yata hakaba. Husna daurewa kawai tayi ta mishi murmushi tace shikenan yaya bakomai Allah ya tabbatar da Alheri ya baku zaman lph. Tana gama fadin haka ta tashi ta wuce dakinta sakamakon kukan dayake neman kufce mata. Tana shiga daki kuka ta fashe dashi tace saleem bazan taba iya rayuwa dakai sannan da wata ba wllhy kishinka zai iya kasheni gwamma kawai nafita daga rayuwarka natafi chan nayi nesa dakai wanda watakila kamanta dani haka dai taita. Kuka tana sambatu. Bangaren saleem kuwa tana fita yasha fa kanshi yana sakin murmushi me hade da fassarori iri iri. A ranan saleem ne kawai yayi bacci cike da nishadi ita kuwa husna tana zaune kawai tana saka da warwara chan kuma sai naga ta dauki waya ta kira abbanta ringing biyu yayi ya daga yace my baby tace ummm daddy yace yau kintuna da daddynki kenan tace aidama kullum kana raina kuma ina tunawa dakai yace Okay ya gida ya mijin naki tace lph lau yace yasu daddynki da mummynki tace daddy kowa lph yace madallah. Ganin tayi shiru yace bby yadai tace daddy dama inaso nazo wurinka me cike da jin dadi yace yaushe tace kamar in d next three days nakeso nazo Daddy yace Okay toh Allahya kaimu. Keda megidan naki zakuzo shiru tayi tana tunanin toh ba a gaya m daddy bikin ba kenan daddy ne ya katse shirun ta hanyar cewa Okay dear Allah ya kawoki lph zamuyi magana. Bayan kwana uku Da sassafe husnah ta tashi ta shirya ta bar gida a lokacin saleem yana bacci direct airport ta tunda flight dinta by 8 zai tashi . By 8 kuwa jirginsu ya daga sai uk Saleem kuwa be farkaba sai karfe goma na safe ya na tashi yayi wanka ya fito koda ya iso falo began taba sannan kuma bega anshirya komai akan dinning ba da sauri ya ajiye briefcase dinshi ya nufa dakin husnah y duba yaga ko lph yana shiga yaga begantaba toilet ya duba nan ma shirun. Hankalinshi a tashe ya duba wardrobe dinta nan yaga ta kwashe wasu kayanta daga kanshi sama yayi nan yaga ba trolley dinta guda daya wani irin gumi ne yake karto mishi da sauri ya fito falo ya dauka key din mota ya nufa gidan mummy ko zai ganta koda yaje a falo ya iske mummy zata shiga kitchen nan dai ya fara kalle kalle ko zaiganta mummy ta katse mishi tunani tace son lph ka shigo ko sallama babu kuma ka tsaya kana kalle kalle me kake nema ? shiru yayi sannan yace babu komai mummy gani nayi kamar nayi mantuwa ne okay kawai tace ta shiga kitchen taje ta dauko warmers ta jera a dinning tagama shirya komai zataje kiran daddy sai gashi yana sakkowa bayan ya sakko ne saleem yake gaidasu hade da mummy . daddy ne ya amsa mishi hade da murmushi mummy ko hararanshi tayi tace sai yanzu zaka gaida ni yace y hakuri mummy a rikice na shigo ne mummy tace kaji dashi dai. daddy yace ina daughter na? shiru yayi yace ashe ma banan tazoba daddy yace me kace ? yace a'a tana lph daddy tashi yyi yace bari natafi office mummy tace bazaka tsaya kayi breakfast ba yace a'a mummy nayi a gida yana gama fada ya fito ya figi mota ya nufa office koda ya isa office dinshi safa da marwa kawai yakeyi yan tunanin inda husnah t tafi. chan kuma sai y dauki wayanshil ya kira yasmeeen tana dagawa yace banason wasa husnah tazo gidanki da sauri tace yya husnah? kuma wllhy batazoba meyafaru ne? kit! ya kashe wayan be bata amsa ba. da sauri ya dauko mukullin mota ya fito daukan mota yayi wnda shi kanshi be san ina zaije ba. yinin ranan dai haka saleem yayishi yana neman husnah dakaganshi kaga wanda yake cike da tashin hankali. husnah kuwa ta sauka lph inda abbanta dakanshi yazo ya dauketa . direct gidan dayake suka sauka husnah kuw bakaramin yabama gidan tayi ba dan ko lokacin dat taba zuwa ba a wannan gidan yake ba dan wannan gida yafi girma da komai da komai . dakinta daddynta ya nuna mata tana shiga kuwa gaba daya dakin hotunantane a ciki harda wnda take karama batafi shekara hudu ba. bakaramin kyau dakin yamata ba. da sauri ta tashi ta nufa toilet tayi wanka ta fito ta rama sallolin da ake binta . bayan ta idar tana zaune jitayi ana knocking tace yes come in. wata baturiyace tashigo tace weldone madam! husnah tace thank you. tace madam food is ready. husnah tace okay am come in. tace okay. husnah kuwa cire hijabin tayi sannan ta nufa dinning table gaba daya kallon abincin tajeyi dan gaba daya bawanda taga zata iyaci tsaki kawai tayi . daki tawuce kawai taje ta hada tea tasha ta kwanta aikuwa nan da nan bacci ya dauketa abinka dame karamin ciki🤪 Bayan kwana biyu gaba daya saleem ya fita hayyacinshi dan kullum bashi da aiki sai na tunanin husna kuma kullum sai yafita yana zaga gari ko zaiganta amma babu ita bbu dalilinta gashi befada ma su mummy ba. bngaren husna itama kanta hnklinta yana waurin mijinta dan it kanta tasan tana azabtuw da rashin shi amma yata iya hakanan zataita hakuri har ta manta dashi. ita anata lissafin gobe ne bikin saleem shiyasa gb daya takara rikicewa hankalinta ya kara tashi gashi ma shiknshi saleem din ko nemanta beyiba saboda yana rawn jiki da amaryarshi. ita ya daina sonta. gaba daya ynzu bta da aiki sai na tunanin saleem gashi daddy in yafita baya dawowa sai dare ba wanda take samu tayi hira dashi da safe kawai take haduwa da daddy . saleem kuwa ganin gashi yau kwana uku ba labarun husnah shiyasa ya shirya yaje gida ya sanar da mummy da daddy halin da ake ciki. daddy da mummy bakarmin tashin hankali suka shigaba . inda taita ma saleem fada akan meyasa be sanar dasu ba tuntuni sai yanzu. sannan tace ita wllhy tayi data sanin sata dayayi cikin plan dinshi. gashi nan sanadin haka ta tafi wanda ba musan inda take ba ynzu. daddy kuwa kanshi a daure yace wane plan kike magana? da sauri saleem yace daddy bakomai. daddy a tsawace yace bakai na tambaya ba kamin shiru. idonshi ya juya wurin mummy yace wane plan ina tambayanki. mummy tace dama umm ummm. daddy yace dama me? tace...... mummy tace dama saleem ne suke samun matsala da husnah to shine har ta furta mishi yayi aure shikuma saleem yace bashi da niyyar kara aure so yake kawai ta gyara shine muka hada plan dani dashi da yasmeen . + toh kwana shida da suka wuce takirani dan taji maganar auren kuma na tabbtar mata da maganan hka ma ta kira yasmeen. toh nikuma ..... dadddy cewa yayi yimin shiru ya za'ayi kibiyewa yara kudinga sakarci wannan ai shirmen bnxa ne toh inma wani abun ne baki iya kiranta kimta fada ai ke tamkar mahaifiya kike gareta amma dayake son yaranki ya rufe miki ido sai kika aikata abinda kikaga sunfi so. mummy da sauri ta dago ido ta kalli daddy tace haba abban saleem me kakeso kace kana nufin kace na nuna banbanci kenan kome? dukanninsu jini nane daga saleem din har husna nayi haka ne domin su daidaita kansu kana nufin kace zaki husna naso saleem ne. bakomai bari zan fita neman husna. daddy cewa yayi yadai fi miki domin kuwa daga ke har saleem kuke da alhakon batan yarinyar nan kuma wllhy duk abinda yasameta ku kukaja yan gama fdin haka ya ficewrshi. saleem matsowa yayi kusa da mummy yace dan Allah mummy kiyi hakuri nina ja miki amma insha Allahu za'a ga husna zan nemota zan dawo da matata. bangaren husnah kuwa daren jiya batai bacci ba kuka taci sosai domin ita a tunaninta yau saleen yashiga dakin amaryarshi . tana kwnce tanata raya abubuw da dama gaba daya jitayi zuciyanta na mata zafi wani irin kishi takeji wanda baza'a iya misalta shiba. daddy da safe ganin bega husna tazo gaisheshi b yasa y shiga dakin dubota ko lph . koda yashiga jinta yayi a toilet tanata kwarara amai zama yayi a cushion din dake cikin dakinta. koda t fito a galabaice ta fito sannu daddy yamata sannan yace ta shirya ta sameshi a falo suje asibiti . falo y koma ya jirata itama ba jimawa sai gata tafito mukullin mota ya dauka ita kum tana binshi a baya. koda suka isa asibitin akai abinda y dace sannan suka je office din dr tambayoyi yamata tabashi amsa nan yayi rubuce rubuce yace suje lab . koda suka je lab blood test akamata. sai dasuka jira result din yafito sannan suka koma office din dr inda dr ya tabbatar musu tana dauke da ciki sannan kuma yace ta rage tunani . daddy kuwa baki yaki rufuwa sai murna yakeyi husna kuwa kunya gaba daya ta kamata. daga nan sukaje pharmacy suka amsa magani . daddy sai daya bari sunzo gida sannnan ya tamabayi husna meyake damunta me tasaka a ranta. husna kuw taki ba daddy amsa sai kuka data fshe mishi dashi. cewa yayi taje ta huta kawai. dakinshi ya koma ya dauko wayanshi ya shiga dialling numbern saleem . saleem kuwa ganin numbern bbn husna ne yasa shi faduwar gaba. yna ganon kiran yaki dagawa. har 3 missed calls ya mishi amma yana gani bedaga ba. chan dai kome ya tuna sai kuma yyi sauri ya kira daddy ringing biyu yayi daddy ya dauka saleem kuwa cike da faduwar gaba ya amsa sallamar daddy . nan dai suka gaisa . sai kuma saleem yayi shiru daddy yace saleem inaso idan da hali kazo cikin satin nan inason ganinka. saleem yace toh daddy insha aAllahu nan da kwana biyu zakaganni daddy. daddy yace toh Allah ya kaimu. bayan kwana biyu saleem ya gama shirye shiryensh na tafiya inda yaje yama mummy da daddy sallama daddy kuwa already ya riga dayagama daddyn saleem halin da akeciki imda yake sanar mishi husna na chan wurinshi amma yaki fada ma mummy kuma yahana mummy kiran bbn husna taji ko tana chan mummy kuwa jikinta ya bata husna nachan shiyasa daddy ya hanata kiran babbn husna domin yasan tana chan. gashi kuma yace saleem yaje yasameshi wnnan ne ya kara tabbatar ma da mummy husna na chan amma koma dai menene in yaje taji. daddy kuwa cewa saleem yayi ya tabbatar in yadawo daga tafiyan ya nemo inda husna take. mummy kuwa sai da ta rakoshi har inda ya driver dinshi ya parker mota sannan tce saleem kanganin kuwa anya husna bata chan . saleem yce wllhy mummy nima haka nake tunani kamr tana chan. mummy tace toh Allah yasa tana chan. duk yanda ake ciki mayi magana inka isa chan. yace toh mummy. mummy tace safe trip son. yace thank u mummy. saleem kuwa daga gidansu direct airport driver ya kaishi ya isa ba jimawa suka daga zuwa uk. koda ya isa uk dama yariga yagayama dinning tym din da zasu sauka. aiko suna sauka ya hango daddy yana jiranshi dan daddy dakanshi yaje ya dauko sirikinshi. koda suka iso daddy yakai saleem guest room yace ya kimtsa sai yazo ya sameshi. hakan kuwa akayi saleem sai da ya shirya yayi wanka yayi sallah ya shiga cikin gidan. a lokacin husna na falo a zaune tana kallo kamar a mafarki taji sallaman saleem . shikuwa saleem be lura da itaba sai da ya shigo gaba dayansu kallon mamaki suke ma juna saleem kuwa jiyake kamar yaje ya rungumeta amma sai ya basar ya karasa shigowa....... saleem basarwa yayi ya shigo yana shigowa daddy na fitowa nan ya karaso ya tsugunna har kasa ya gaida daddy .+ daddy kuwa cike da farinciki yace haba my son ka tashi mana nibanaso kana tsugunna min nama fiso ka rungumeni. saleem kuwa kallonshi yayi daddy kuma murmushi ya sakar mishi ya bude mishi hannu alama ya rungumeshi saleem kuwa sose kai yayi yana murmushi a ranshi yace oh daddy zaman turai ya maidashi bature . ganin saleem na murmushi daddy yace is alright let's eat the dinnig is set. saleem kuwa karasawa yayi ya zauna a kan dinning table daddy ne ya kalli inda husna take yace daughter are you not hungry? shagwabe fuska tayi tace daddy am not hungry . tashi ma tayi ta wuce daki saleem ko da ido ya bita domin bakaramin missing dinta yayi ba gaba daya jiyake kamar yaje ya rungumeta a jikinshi. sai dayaga ta bace mishi sannan ya maida hankalinshi kan abincin kadan yaci yace ya koshi. komawa falo yayi ya zauna yana jiran daddy ya gama bayan daddy ya gama dakanshi yaje dakin husna ya kirata. daddy falon ya fito ya zauna sannan ba jimawa husna ta fito itama. daddy sai da ya bude taro da addua sannan ya fara magana kamar haka . daddy yace saleem inaso nasan meyake faruwa ne tsakaninka da husna? saleem shiru yayi be amsaba . daddy sake tambayanshi yayi saleem yace bakomai daddy. daddy yace toh kasan da zuwanta kassan nan ? saleem yace a gaskiya daddy bansaniba domin nima na wayi gari bangantaba kuma kullum cikin nemanta nakeyi. daddy kuwa maida kallonshi yayi ga husna yace haka akayi? shiru tayi yace magana nake miki fa ? tace eh daddy hakane daddy yace toh a wane dalili kika taho ba tare da sanin mijinki ba tace daddy nifa nagaji da zama dashi ne saleem kuwa da sauri ya dago ya kalleta suna hada ido harara ta galla mishi harara shikuwa gaba daya mamakin husn yakeyi. daddy yace toh yanzu mekikeso ayi tunda kin gaji da zaman dashi. tace nidai daddy kawai ya tafi yaje yayi rayuwa da amaryanshi. daddy murmushi yayi domin ya gane kishi ne kedamun husna shima saleem murmushi yayi husna kuwa ganin saleem na murmushi ta cika tai fam a ranta tace toh kenan ma dadi yakeji nace yaje ya zauna da matanshi. daddy yace toh yanzu so kike a raba auren? da sauri ta dago ta kalli daddy taga shima ita yake kallo . tace a'a kar a raba kawai nidai zan zauna a nan shikuma yaje yayi rayuwa da amaryanshi. daddy yace a'a bazai yiwuba dole ki zabi daya koki koma gidan saleem ko kuma a raba airen. aiko nan fa husna tasa kuka tace ita baza'a raba auren ba kuma bazata koma ba. daddy ganin ta rikice mishi gashi dr yace ta rage damuwa da tunani. yasa yace mata ta wuce daki . tashi tayi ta tafi . daddy nan yama saleem bayanin halin datake ciki da abinda dr yace. daganan daddy yace amma saleem sai kai aure banda labari STORY CONTINUES BELOW saleem dan sosa kai yayi nan shima yama daddy bayanin abinda zai iya fada mishi. daddy murmushi yayi yace toh shikenan yaushe zaka tafi ne? saleem yace one week xanyi kawai daddy yace okay in zaka tafi sai ka wuce da matarka. ai nan saleem ya tsugunna har kasa ya rinka ma daddy godiya. daddy cemishi yayi ya isa haka jeka huta my son. bahaka yasoba yaso daddy yace yaje wurin matarshi amma bayanda zaiyi haka ya tashi ya wuce masaukinsa. washegari husna na tashi tayi wanka ta shirya cikin robber gown red kayan ko bakaramin amsanta yayi ba abinka da faran mace gashi takara haske abinka da me karamin ciki fuskan nan tata tayi fayau although ba wani kwalliya tayi ba amma tayi kyau sosai. fitowa falo tayi taga daddy da saleem suna zauna kan dinnig table suna breakfast tssaki tayi sannan ta karasa kusa da su tace daddy gudmorning? yace morning my bby. hw was ur nyt? tace fyn.hade da jan kujera ta zauna . ganin bata gaida da saleem ba yasa daddy cewa bazaki gaida yayan naki ba . sai data murguda baki sannan tace ina kwana? saleem murmushi kawai yayi sannan ya amsa mata. daddy kuwa ya riga kowa gamawa tashi yayi ya musu sallama yace ya tafi office. a tare suka mishi sai ya dawo. yan fita saleem ya tashi ya koma kujeran dake kusa da husna. husna kuwa kar daure fuska tayi amma batace mishi kala ba har tagama cin abincinta. tashi tayi zata tafi sai jitayi an sunkuceta gabadaya ihu tasaka wanda yasa daya daga cikin ma'aikatan ya fito abinda ya gani ne yasa ya koma. shikuwa saleem bedireta ba sai akan bed dinta. kwantar da ita yayi sannan shima ya kwanto yayi mata rumfa tureshi tayi tace ni dan Allah ka kyaleni yace naki. kokarin tashi takeyi amma shikuma ya kara bake bake . tace wai meye hakane ? yace SO ne? tace so wane irin so ai ninasan bakasona dan Allah kafita daga dakin nan banson ganinka. bece komai ba ya tashi yazo daidai bakin kofa ya rufe kofa ya xare key din sannan ya dawo inda take. yana zama ya jawota jikinshi ta fado . kallon juna sukayi namintoci sannan ta kawar da kanta gefe shikuwa saleem kara jawota yayi kamar zai shige jikinta. husna baki ta murguda mishi tace wai meye hakane? be kulataba illa cigabada da abin da yakeyi kokari yake ya rabata da rigan jikinta. da saurinta riki mishi hannu tace kabari banao nidai takardana zaka bani dan bazan koma gidankaba . yace okay karkidamu zan baki takardanki yanzu. da zafi zafi ya fara romancng dinta ganin tana hawaye ne ya sassauta mata. sai daya rabata da kayan jikinta sannan ya tabbatar daya kashe mata jiki da salonshi sannan ya fara kokarin shiga jikinta husna kuwa da jikinta gaba daya a mace yake sannan kuma tayi missing megidan nata taba da kai bori ya hau. nan suka lula duniyar ma'aurata . saleem kuwa banda sambatu ba abinda yakeyi domin dama tunda yaganta yakejin wani muguwar sha'awa . be sarara mata ba sai da ya gamsu. rungumeta yayi yace bbyna karki gujeni wllhy inasonki idan na rasaki bansan yadda yazanyiba Dan Allah matata karki gujeni . tureshi tayi sannan ta fashe da kuka tace nidai banasonka kaje chan wurin amaryanka kasan kana sona amma ka iya yimin kishiya wllhy na tsaneta kaima na tsaneka. saleem kuwa ji yayi kamar an buga mishi abu a kanshi. tashi yayi yasa kayanshi ya wuce guest room yana zuwa ya shiga toilet yayi wanka sannan ya zauna domin kuwa gaba daya ranshi a bace yake ya rasa yadda zai bullo ma husna gashi yana matukar sonta so yake su zauna ba tare da wani matsala su gina rayuwa me cike da so ds kauna. toh amma yaushe hakan zai faru domin kullum husna bata da magana sai na ya saketa bazata zauna dashi ba . gashi yau har tana cewa ta tsaneshi. yanzu ya zaiyi. STORY CONTINUES BELOW husna bata sake sa saleem a idonta ba shima kuma be kara shiga harkantaba, yau da safe ya samu daddy yace ma daddy yanaso zaiyi magana da mummy yanaso ya kira mishi mummy aikuwa mummy na zaune tayi tagumi domin tunda saleem ya tafi hankalinta a tashe yake domin be kirataba. ganin kiran daddyn husna ne yasa a sauke ajiyan zuciya sannan ta daga bayan ta dga waya saleem yace mummy ina kwana tace ah saleem kaine ai inata jiran kiranka baka kiraniba . yace am sorry mummy . tace toh yanzu ya ake ciki ina husna? yace tana dakinta . ajiyan zuciya mummy ta sauke tace alhamdulillah tunda chan tayi. yanzu tare zaku dawo . yace eh mummy amma yar takice sai taurin kai . mummy tace toh kai mata wayan zanyi magana da ita. kallon daddy yayi daddy kuwa kai kawai ya daga mishi yayi murmushi yana zuwa dakin husna yayi knocking tace yes come in. yana shiga yaganta a kwance tana game a wayanta. kamshin shi kawai taji ta dago tana kallonshi tace me ka shigo kamin a dakina? waya ya mika mata . tace mexanyi dashi ? yace ki amsa kisa a kunne . amsa tayi . jin muryan mummy tayi. da ssuri ta cire wayan a kunne. sannan ta mayar tace mummy ina kwana? mummy tace haba daughter yanzu kin kyautamin kenan? ace wai har zaki bar kasan nan batare da kin fada min ba. meyayi zafi haka? ko duba halin da zan shiga bakiyi ba. ai ko baki fada ma kowa ba kya fadamin husna dai shiru tayi batace komai ba mummy tace toh yanzu dai yaushe zaki dawo? shiru tayi bata ba mummy amsa ba mummy tace magana nake miki fa . tace mummy ni bazan dawo ba . mummy tace ba saleem wayan . mika mishi tayi . mummy tace mishi bani guri zanyi magana da husna. kabar kusa da ita. okay kawai yace ya mika ma husna wayan tare da barin dakin. husna amsa tayi hade da cewa helo" mummy tace kina jina tace eh inajinki mummy tace husna inaso kibani hankalinki sannan maganan dazan miki zan miki a matsayinki na yata. husna abinda nakeso dake shine ki rike mijinki sannan kada kiyi sakaci kibari wata ta kwacemiki miji. sannan mezaisa ki gujewa mijinki saboda kishiya toh kenan kin nuna ke karamar mace sannan ke ba jarumar mace bace tunda dai har baxaki iya taran kowane matsalaba sannan kuma bazaki fuskanci matsalar data taso miki ba. kina tunanin in kon bar gidan saleem bazaki kara aure ba. kuma kina tunanin in kin sake aure mijinki bazai miki kishiya ba. banda maganan kishiya baki san mexaki tarar ba achan sai kiga matsalar dakika bari anan ta chan tafi . dan haka nakeso kafin kiyanke hukunci ki tsaya kiyi tunani. bawai kuma ina miki magana bane dan ki koma gidsn saleem dan yana 'dana a'a ina miki fada ne a matsayinki na 'yata wacce na rike na kuma bata tarbiyan da ya dace . dan haka bari na barki duk hukuncin da kika yanke yayi daidai. husna kuwa banda kuka ba abinda takeyi domin tasan ta tafka babban kuskure hakika mummy ta wayar mata da kai dan haka yanzu zatazage dantsen zama da mijinta sannan zata bashi kulawar da bata bashi ba da sannan zata zauna da kishiyarta ko wacece domin bazata taba bari a kwacemata miji ba. sai data wanke fuskanta sannan ta mayar ma da daddy wayanshi daddy koda yaga yanayinta bece mata komai ba illa gaisuwa da sukayi yayi musu sallama ya tafi office. bayan kwana biyu, duk yanda taso su hadu da saleem hakan be yiwuba gashi kuma sauran kwana biyu ya tafi tanaso taje tasameshi tace mishi zata bishi su tafi . amma yanzu taga ko fitowa bayayi. shikuwa saleem bakaramin missing dinta yakeyi ba amma tunds tace ta tsaneshi yaja jikinshi daga gareta saidai da safe yaje ya gaida daddy a daki yake wuni ko abinci sai dai ma'aikata sukawo mishi. shiyasa basa haduwa da husna. husna kuwa tana zaune abin duniya ya isheta dan sotake taga saleem wta zuciyar nace mata taje wurinshi wata zuciyar na hanata. amm data tuna hudubar mummy yasa ta shirya tayi kwalliya ta nufa guest room. koda ta isa door bell ta danna. saleem na kwance yaji kara tashi yayi yaje ya bude kofa ganin husna yayi a bakin kofa. gb daya ta tafi dashi domin rigar datasa ta kamata daga sama ga boobs dinta suncika sunyi fam sannan daga kasa kuma ya bude . karamin veil kawai tasa ta yana kanta. saleem kuwa jawota yayi ciki ya tura kofan. yace a haka kika taho baki sa hijab ba . turo baki tayi gaba sannan tace toh ai bawanda yaganni kuma ma ko an ganni menene. juyowa yayi ya mata wani irin kallo. juyawa tayi tace tunda bakai farinciki dazuwana b toh shikenan na tafi. da sauri yaje ya tarota yace haba bby kema kinsan nayi missing dink kawai dai kishi nakeyi ace kon fito a haka sai dan wannan veil din da kika yafa dadai kinsa hijab in kika shigo nan sai k cire tunda ni aka ma kwalliyan yace hade da kashe mata ido daya . turo baki tayi tace niba kai nama waba kaina nanawa. yace okay. wuri ta samu ta zauna . saleem yace bby yadai? tace dama nazo nace maka yaushe zaka tafi zan baka sako ka kaima mummy. saleem kuwa wani kallo yabita dashi yace mekike nufi? tace kamarya? yace okay kina nufin ba tare zamu tafi ba kenan? tace ai baka bani hakuri ba sannan kuma bakace nabika ba ai ba biko kazo ba. saleem kuwa dariya yayi yace toh shikenan matata ya tsugunna ya kama kunnenshinyace am sorry na miki laifi kiyi hakuri . sannan ina neman izininki kizo kibini mu koma gidanmu mu gina sabuwar rayuwa me cike da farinciki sannan kuma inaso na raina cikina yace hade da shafa cikin . ture hannunshi tayi tace nibanda komai. nan fa suka fara wasa daga nan koma wasa ya chanza salo ka fada duniyar masoya. bayan komai ya lafa sun tsarkake jikinsu . husna kuwa tana kwance jikin saleem . saleemm yace bby kinsan bakaramin tada min da hankali kikayi kawai na tashi na nemeki na rasa tace am sorry i will not do it again. shiru ne ya ratss sai chan kuma husna tace yaya ina kanwata banj kce komai ba akanta . yace eh i want to suprise you sai mun koma zaki ganta. kirjinta taji yayi dam. amma ta daure ta kirkiro murmushi . kwantawa tayi lum a jikinshi abinka dame karamin ciki nan danan bacci ya dauketa shikuwa saleem ganin tayi bacci ya kara gyara mata kwanciyanta. shima ba jimawa bacci yayi gaba dashi STORY CONTINUES BELOW an gobe zasu tafi daddy yakirasu ya musu nasiha sosai . washegari da safe suka daga nigeria. koda suka iso sai da sukaje suka gaida daddy da mummy sannan suma suka musu fada hade da nasiha daganan suka tafi gida. koda sukaje gida husna tayi mamakin ganin an chanza mata komai na dakinta. amma kuma data tuna saleem yayi aure sau ta basar kawai ta wuce dakinta tayi wanka ta kwanta dan dama sunci abinci gidan mummy. tana kwance taji ana shafata bude ido tayi tace yaya amma kasan hakn bedace ba ko. kwananka nawa baka nan sai kuma kazo dakina ai barayin amaryanka zaka. saleem yace zo muje kiga amarya mana. dama abinda ya kawoni kenan kuma naa kina bacci. tsaki tayi tace ba inda zani ni bacci nakeji. gobe ma hadu. daukanta kawai yayi chak ya nifa da ita dakinshi ai suna shiga taga gaba daya anyi decorating dakin da flowers da candles . gba daya dakin yayi mata kyau sosai ga hotonsu ita dashi a jikin bango . dayan gefen kuma hotunan tane da akai framing dinshi duk ya sakala a bango . saukowa tayi daga jikinshi. ta fara kallon ko ina tace waw yayi kyau. yace sure? tace sure. wuce wa yayi yaje ya dauko wani karamin box da kuma wani abu anyi wrapping dinshi da wrapping sheet. miko mata yayi yace oya go and get ready. amss tayi tana kallonshi yace gira ya daga mata tashi tayi ta nufa bthroom tana budewa taga wani irin sexy nyt gown wanda dashi da babu duk daya ne . gaba daya jiknshi net ne gashi iya cinyrta ya tsaya. sawa tayi ta fito. tana fitowa yaje ya rungumeta yace waw bby you look fyn. shinshinata ya shiga yi wani irin kamshi takeyi mishi kamar me wani sihirtaccen kamshi take fitarwa. jawota yayi ya zaunar da ita a jikinshi ya bude box din y dako wani diamond ring ya samata aikuwa cip cip ya mata a hannunta . ai ganin kyan ring din yasa batason lokacin data mishi kiss ba. shikuwa unexpected yaji kiss ai kuwa dasauri ya juyo da ita ya shiga shafa jikinta nan dai aka fada duniyar masoya. washegari take tambayanshi maganan amarya yace bawata amarya dama plan ne nan yake sanar da ita ynda abin yake . aikuwa yasha duka da pillow. nan ma takira yasmeen tamata ta tas tace wato da ita za'a hada baki ko. nan dai yasmeen tace ai gyara sukeso so take ta chanza kafin ayi mata na gaske, dariya sukasa gabayansu . nan kuma aka koma bata shawarwari ynda zata kama saleem a hannu. bangaren safiyya kuwa anata addu'a inda daga karshe Allah ya taimaketa tasamu hanya ta fito a lokacin yana chan yana badala da wata ya manta be kulle kofan ba tan turawa taji ya budu haka taita gudu har ta fito cikin gari tasamu tasamu abin hawa ya kawota gida . tana shiga barayinsu ihu ammy tasa domin yanda taga safiyya kamar mahaukaci banda ita ta haifeta da bazata ganetaba. nan dai aka dauketa aka kaita asibiti bayan kwana biyu aka sallamota inda ta fada musu abinda ya faru nan dai aka jajanta mata . kuma aka mata nasiha daga baya ta koma islamiyya inda ynzu ta shiryu. ruky kuwa chan hanyar yawonta mota ta bigeta wanda ko shurawa bata yiba ta mutu. nan tsoron Allah ya kara shigan safiyya . bayan wasu wattanni ta samu miji wanda yasan labarinta kuma ya amince zai aureta nan dai akasa rana sukai aure. bangaren husna anata fama da ciki domin yanzu cikin ta ya tsufa saleem kuwa kullum sai ya tsokaneta. husna na bacci cikin dare taji kamar an mintsineta da sauri ta tashi chan taji bayanta ya rike mara ta fara ciwo . a wani irn murdewa da maranta yayi yasa ta daki kara saleem kuwa a rikice ya tashi yana ganinta yasan haihuwane daukanta yayi yakaita dskin daya shirya komai idan labour ya tashin mata. da kanshi ya karb haihuwanta wanda bakaramin namijin kokari yayi ba . a haka ta santalo bby girl . nan fa saleem ya gyarata sai daga baya ya kira mummy ya gaya mata . yan uwa da abokanan arzik haka akaita zuwa saleem kuwa da kyar ya bari aka tafi da husna gidan mummy amma sa safe da rana yake zuwa. akwana a tashi ba wuya inda har anyi suna yarinya tce sunan mummy. ama za' a rinka kiranta da ammy. bayan 40days saleem yaji shiru beji ance husna zata koma ba aikuwa washe gari ya kasance sunyi 41 days yaje gidan yasamu mummy rai a hade ya gaida ta itama hade rai tayi sannan ta amsa mishi tashi yayi ya wuce dakin husna . inda yaganta a zaune tana ba ammy nono zama yayi kusa da ita yayi tagumi yace . tace abban ammy ya akayi meyake damunka? yace aikin fi kowa sanin abinda ke damuna haba ance sai kinyi 40days zaki dawo gashi yau har 41 days tace haba abban ammy ai nakusa dawowa nasan bazan wuce nan da 14 days ba tinda dai zan zaga dangi yan uwa da abokan arz... wani kallo ya mata wanda yasa ta ksa karasa maganan datakeyi. yace okay naganoki wato ke baki damu da damuwata ba ko ? ko duba halin dazan shiga ba kya yi ko. tace yaya kayi hakuri kwana nawa zan dawo yace nibawani hakurin da zanyi kawai ki tashi mutafi gida. zaro ido tayi tace kayi hakuri yaya gaskiya bazan iya binka ba ai wannan abin kunya ne. yace okay fyn. kiyita zama amma kisani duk abinda ya faru dani kekika ja. yana gama fadin haka ya wuce ko sallama beyi da mummy ba. husna kuwa ganin har an kwana biyu saleem baya dsukan wayanta yasa ta shiga tashin hankali ga text messages ta tura mishi amma ba rply . gaba daya yanayinta ya chnza tasani mijinta irin mazan nan ne masu karfin sha'awa amma ya zatayi dole tayi hakuri har lokacin da xa'a maidata. husna ganin kwana hudu kenan saleem bezoba sannan kuma baya kiranta a waya kuma kota kira be dauka yasa ta zauna ta fashe ma da mummy kuka ita amaida ita dakinta. mummy kuwa mamaki husna tabata domin husna macece me kunya ganin haka mummy ta lallasheta tace gobe ta koma tace ma mummy ita dai yau zata koma mummy tace toh shikenan. husna txt tama saleem tace yazo ya dauketa ai saleem nganin txt dama yana kwancene yana tunaninta yasashi taka rawa da tsalle da sauri ya dauka key din mota ya nufa gidan mummy yana shiga yagaida mummy bata amsa mishi ba illa harara data sakar mishi. da sauri ya wuce dakin da husna take a tsaye ya ganta ga akwatina a gabanta . yanashiga ta rungumeshi ta sakar mishi kuka hakuri yabata yace ta rike shagwabnta sai sunje gida dukan wasa ta kai mishi yayi sauri ya kauce. jawo akwatin yayi y fitar dashi inda suka ma mummy sallama suka tafi itadai batace komai ba da ido ta bisu kawai tana musu addu'a Allah ya kara dankon so da kaunan junansu. daddy kuwa koda mummy tagaya mishi cewa yayi sun mishi daidai. dariya tayi tace ai dayake kai da dan naka halin ku daya bayan sun koma saleem kam ansha amarci domin kukan dadi ba'a magana hade dasa mata albarka. washegari yake tambayanta ya akayi mummy tabari ta dawo nan ta lbarta mishi yanda akayi. dariya yayi yace aidama nasan plan dina zaiyi aiki duk danima daurewa nayi n rashin jin muryanki da ganinko. dariya tayi hade da rungume mijinta tanajin wani sonshi na karuwa a cikin zuciyanta wnda shima hakan ne daga bangaranshi. Alhamdulillah anan na kawo karshen littfina me suna dr saleem kuskuren danayi aciki ina nema Allah ya gafar tamin.

Post a Comment for "DR SALEEM CHAPTER 7 KARSHE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...