DR SALEEM CHAPTER 2 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

DR SALEEM CHAPTER 2

DR SALEEM CHAPTER 2

- - Post a Comment
DR SALEEM CHAPTER 2


  washegari ranan daddy zai dawo dan haka mummy da husna tun safe suke aiki girki kala kala aka ma daddy .+ bayan sungama komai mummy tace husna taje ta kira saleem yazo su tafi airport din dan by jirginsu ya kusa sauka. husna tace um mummy da kin kirashi a waya kawai. mummy zatai magana saleem yace saboda bata isa dakeba. husna dai batace komai ba. mummy tace a'a nibanason haka tunda kazo shikenan kawuce mutafi. fitowa sukayi mummy tashiga motan saleem itakuma husna ta shiga motanta. tana bayansu har suka nufa airport din. koda sukaje jirginsu be sauka ba dan haka suka samu wuri suka zauna. dama husnah tunda ta fito daga motarta taga wani yanata kallonta . amma haka ta kauda kanta har ta karaso inda su mummy suke. shikuwa ganin ta zauna yasa ya bita har inda yaga ta zauna . yana zuwa ya musu sallama . mummy fuska a sake ta amsa mishi. saleem kuwa ya bashi hannu suka gaisa. sai jitayi yace Asma'u dan Allah kozaki ban minti biyar. gabanta ne yafadi ya akayi ma yasan sunanta domin ita bata sonshiba kuma ma bata taba ganinshiba. ganin taki motsawa mummy tace tashi kije mana jiki ba kwari ta tashi ta nufa inda yake a tsaye. saleem kuwa banda harara ba abinda yake aika musu. shikuwa ganin yanda saleem ke hararansu yasa yace su matsa daga chan gaba. bayan sun matsa ne yake cemata . da farko dai sunana Abubakr sadiq, ni badan garin nan bane aiki ne yakawo ni garin kano. ina aiki ne a saudi airline. dazu naganki toh tunda naganki naji gaskiya kin burgeni domin bazan iya barin wannan daman ta wuce ni ba. ina fatan za'a bani dama nima na shigo cikin sahun manemanki dan na san baza'a rasasu ba. ita dariya abin ya bata wanda yasata tayi dariya. shikuma ba karamin kara burgeshi tayi ba. yace toh wannan murmushin ma amsa ce. itadai husnah batace dashi komai ba dan ita bata kula kowa ko da an mata magana bata sauraransu dan ta riga ta mallaka ma wani zuciyanta. ganin tayi shiru yace toh ga katina zan saurara kiranki. Asma'ul husnah. tace wai ya akayi kasan sunana yace haba ai sanin sunan abinda kakeso bashi da wahala zuciyata ta riga ta baki sunan sai kuma nayi dace sunan nakine. tace gaskiya banyarda ba kafadamin kawai yace toh in kinaso nafada miki sai kin kirani anjima zan fada miki yanda akayi nasan sunanki. STORY CONTINUES BELOW zaiyi magana sukaji saukan jirgi. tace bari naje daddyna ya iso. yace nikuma dan uwana ya iso. murmushi sukayi a lokaci daya. tare suka taho har wurinsu mummy suna tsaye mutane suka fara firfitowa. ai husna na hango daddy da gudu ta tafi ta rungumeshi. dan husna ta bala'in shakiwa da daddy kuma yajata ajiki sosai dan yanda yake mata ko su nusaiba baya musu haka. saleem kuwa banda tsaki ba abinda yayi . yace wai yarinyan nan bazata girma bane. mummy kuwa murmushi taita sakar ma daddy. nan fa suka shiga gaisheshi suna mishi sannu da zuwa. daganan kuma suka dunguma inda sukai parking mota. daddy yace shi motar daughter dinshi zai hau mummy ma tace inda mijinta yake nan itama nan take. saleem kuwa ya shaka yace haka zamuyi daku. husna tai charaf tace ai nima ni kadai nazo. har da gwalo tayi mishi. shikuwa shigewa motarshi yayi ya figeta da gudu. husna kuwa a hankali cike da nutsuwa take driving har suka iso gida. a falo suka tarar da saleem a zaune. murmushi daddy yayi yace kai son baka girma yanzu dan abin nan kake ma baccin rai. kafa namiji ne ita kuwa husna macece kuma fa kanwarkace . ya shagwabe fuska yace toh ai daddy nifa ni naso na daukeka a motata shiyasa kaga ko asibiti banje ba. daddy yace toh shikenan my son kayi hakuri kasan duk dawowa kai kake daukoni . wannan karan kanwarka ta daukoni. amma next tym kai zaka daukoni. mummy tace hmm nidai kubar min mijina ya huta . ai saleem bazaka girma da shagwaba ba amma Aure yakamata amaka domin muma mu huta. kunkuni ya fara yace haba mummy aure kuma duka guda nawa nake. husna kuwa kallonshi tayi a ranta tace wai wannan ne yake cewa guda nawa yake. ganin kallon da husna ke mishi yasa ya harareta . ita kuma ta mishi gwalo. ya nuna kanshi wai shi? tace eh . kai kawai ya kada. mummy kam tana kallonsu amma batace komai ba. murmushi kawai tayi. husna kuwa dinning ta nufa inda daddy yake zaune ta shiga serving dinshi . daddy kuwa yace kai wannan kamshin daban ne dan nasan daughter tace tamin wannan abinci. mummy tace aiko kamar kasani . yace haba ai nasan daughter naji dani. saleem kuwa tsaki yayi yace daddy wannan ce tayi abincin lallai za'aci jagwalgwalo . husna murguda mishi baki tayi tace toh so nawa kake cin abincin nawa kuma katada plate din. daddy yace a toh daughter rabu dashi ni nasan ko matarshi bazata iya wannan girkin ba. dan daughter ta daban take. saleem cewa yayi daddy wallhy kai kake kara shagwaba yarinyar nan har take ma mutane rashin kunya . idan taganka har wani sabon raini take min amma in baka nan ko bakinta bakaji. dadday yace daughter zauna kici abinci kinji. toh tace hade da karasa tsiyaya ma daddy juice a cup. tana zama saleem yace waye zaiyi serving dina . tace ai kanada hannu . mummy tace kwarai kuwa. saleem tashi kawai yayi yabar side din. mummy da daddy dariya kawai sukayi. bayan sungama husna taga saleem bezoba tace bari ta zuba mishi takai mishi. mummy tace toh . STORY CONTINUES BELOW hade komai tayi a tray ta nufa side dinshi . tana isa ta fara knocking sannnan tayi sallama . shikuwa jin muryanta yaji dadi dan dama da muguntan daya shirya mata. shigo taji yace tura kofan tayi a hankali tare dakara yin sallama tace yaya saleem ga abincinka mummy tace na kawo maka tafada bakinta na rawa dan yanda taga yana kallonta. tsugunnawa tayi ta aje abincin kan stool . shikuwa rankwashi ya buga mata akai. da sauri ta tajuyo ta kalleshi tare da dafa kanta. shikuwa ya hade rai kamar bashiba. tace yaya saleem menamaka. bakinta ya kama ya murde yace har tambayana ma kikeyi duk wannan rashin kunyan dakike min harda murguda baki dankinga daddy yadawo ko. sake bakin yayi ya kama kunnen ya murde itakuwa dan azaba hawaye kawai takeyi. chan ya sake kunnen yace oya fara tsallan kwado . zaro ido tayi. yace bazakiyi ba kenan yana kokarin cire belt din jinkinshi da sauri tace zanyi dan tasan bakaramin aikin saleem bane ya zaneta. tsugunnawa tayi tafarayi tana zuwa bakin kofa ta arce da gudu. kamar daga sama mummy taji mutum ya fado. tace ke lafiyanki kuwa . tace mummy yaya saleem nefa wai sai nayi tsallan kwado. daddy yace wane irin tsallan kwado kuma sai kace karamar yarinya. ai husna kara shagwabewa tayi tace daddy kumafa har murdemin kunne yayi sannan ya rinka rankwashina wai ina mishi rashin kunya daddy kuwa ranshi ya baci . wayanshi ya dauka yakira saleem a lokacin saleem zai kai loman abincin kenan yaji wayanshi na kara. daddy kuwa rai a abace yace kazo ka sameni! tashi kawai yayi ya aje spoon din ya nufa side din mummy. a falo ya tadda daddy husna nazaune kusa dashi tana hawaye. sallama yayi sannan ya karaso. daddy yace wannan wane irin muguntane ya kamar husna zakace tayi tsallan kwado baya ga rankwashi ga kuma murdemata kunne da kayi. banasan shashancin banza idan bakaso mu bata dakai toh wllhy kafita daga harkanta. yarinyar nan tuntana karama kake mata mugunta yanzu ta girma bazata huta ba. toh bazan dauka ba . yarinya ta damu dakai abinci ta dauka takai maka ganin katashi baka ciba . amma dan mugunta ka ritsa ta wai tayi tsallan kwado toh wllhy daidai da rana daya tace min ko kallon banza kamata sai kaga yanda zanyi dakai. saleem kuwa dan baccin rai idonshi harja yayi gaba daya jijiyoyin jikinshi sun bayyana. yace daddy kayi hakuri bazan karaba. daddy be kalleshiba yace daughter muje sama nabaki tsarabanki. nan suka tashi suka bar saleem da mummy a zaune. mummy ma tashi tayi tabi bayansu. saleem kuwa jiki a sanyaye yai side dinshi yana zuwa yayi fatali da abincin . da daddare ma yana zuwa ya gaida du mummy ya wuce dakinshi. husna gaba daya bataji dadi ba tayi dana sanin gaya ma daddy datayi gashi nan yama saleem fada. a daki tazauna taita kuka. mummy ce tashiga ta duba ta ganin tana share hawaye mummy tace lph? cikin kuka tace mummy dan Allah kiba daddy hakuri da yaya saleem wllhy banji dadi ba niban fada dan ya mishi fada ba dan Allah mummy kiba yaya saleem hakuri. mummy murmushi kawai tayi tace ki kwantar da hankalinki komai ya wuce. mummy kuwa mamaki takeyi dan duk abinda saleem zai ma husna idan taga ranshi ya baci hankalinta tashi yakeyi. mummy da daddy ne acikin daki suna kwance mummy take fada mishi ciwon husna da abinda doctor yace. daddy shiru yayi sannan yace toh tana da wani tsayayyene? mummy shiru tayi sai chan tace gaskiya bansaniba . yace toh ya kamata ki tambayeta kotanada wanda takeso muji. mummy tace nida a tunanina mezai hana a hadasu Aure da saleem . daddy yace what! saleem fa kikace so kike ya kashe yar mutane a gida ma ya aka kare balle a barsu su biyu. gaskiya bazai yiwuba. mummy tace haba dai ai auren shine zai kara hada kansu kuma nifa yanda na lura kamar husna nason saleem . daddy yace haka kike gani nidai bazan mata doleba ki tambayeta kiji ta bakinta duk abinda tace miki kya fada min. sannan yace toh shi saleem din kina ganin yana sonta. mummy tace maganar saleem kabarni dashi kawai. 🤔🤔🤔 kara kara qaqa yau fa akeyinta shin ko saleem zai amince ya auri husna? washegari mummy na tashi bayan ta gama hada breakfast tayi komai .+ ta nufa dakin husna domin tajita shiru husna kuwa bata samu tayi bacci ba sai cikin dare shiyasa ta makara sallah asubah ma da kyar tasamu ta tashi tayi. mummy na shiga ta isketa a kwance akan sallaya tana bacci. juyawa kawai tayi tabar dakin. a lokacin shima daddy har ya sauko saleem ma shima ba jimawa sai gashi ya shigo. gaishe dasu mummy yayi sannan yaja kujeran dinning ya zauna . daddy kam ganin husna bata saukoba shiru yace wai ina daughter ne? mummy tace naje na sameta tana bacci shiyasa na kyaleta inaga bata samu bacci da wuri bane . daddy yace toh abarta ta huta. saleem kuwa abincinshi ya cigaba daci bece komai ba. bayan sungama daddy ya hau sama yace bari yaje ya huta. mummy kuma daga ita sai saleem tace son idan ka dawo daga aiki zamuyi magana dakai. yace okay mummy . sannan itama ta tashi tabi daddy. tana shiga ta iske daddy a tsaye bude mata hannunshi yayi alamar tazo aikuwa da sauri taje ya rungumeta z nace oh su daddy ashe basu tsufa ba. bangaren husna kuwa sai 10:am ta tashi tana tashi tashiga toilet tayi brush sannan tayi wanka tafito ta shirya cikin riga mara nauyi sannan ta sauko kasa koda ta sauko lantana kawai tagani me aikin mummy gaisheta tayi sannan ta nufa dinning tayi breakfast. bayan tagama ta koma daki ta dauko wayanta tafara chatting dayake yau bata da lectures. tana zaune mummy tashigo hade da sallama. gaidata tayi sannan mummy tace daughter kinsha bacci. murmushi tayi sannan tace mummy jiya banyi bacci bane da daddare da wuri inata research. mummy tace yayi kyau daughter. shiru ne ya ratsa kafin mummy tafara magana tace daughter kibani hankalinki magana nakeso nayi dake . husna murmushi tayi tace mummy inajinki . tace daughter zaki iya Auran Saleem? husna kuwa wani dadi ne ya ratsa ta dan bata dawani buri daya wuce ta Auri saleem . shiru tayi bata ba mummy amsa ba . mummy tace ba shiru zakiyi ba Amsa nakeso . Amma banaso kiduba saleem dan yana dana. kice zaki Aureshi dan wllhy husna bazan miki dole ba inda Akwai wanda kikeso kifada min. sai ya turo kawai ai maganan Aure. husna kanta a sunkuyw tace a'a mummy. A'a mene bazaki iya Auran saleem ba ko kuwa.. bata karasa husna tace zan iya wllhy mummy. mummy dariya ce ta kamata amma ta gimtse dan dama ta lura husna nason saleem. mummy tace kin tabbata ? kai kawai ta daga ma mummy dan gaba daya kunyace ta kamata. mummy tace toh Allah ya miki Albarka daughter Allah yasa nag jikokina. husna ai sai ta cusa kanta cikin pillow. tashi mummy tayi ta barta. ai tanajin mummy tafita ta tashi ta kama rawa tana juyi tana Alhamdulillah burina ya cika . Allah nagode maka. mummy kuwa tana labe tana jinta dariya kawai mummy tayi tace Allah yasa saleem yasoki fiye da yadda kike sonshi. datagaji da rawan kawarta ta kira kuma Aminiyarta tace sis Allah ya amshi addu'a na burina ya kusa cika na auran saleem. ihu akayi ta dayan bangaren tace waw amma na tayaki murna Allah ya tabbatar da Alheri sai nazo. husna kuwa da sauri ta shiga bayi tayi alwala ta yi sallah raka'a biyu ta gode ma Allah sannan tayi addu'a zabin Alheri. koda saleem ya dawo har daki yaje ya samu mmmy a lokacin tana zaune ta idar da sallah. saleem ya duka ya gaida ta sannan ya jawo stool ya zauna . mummy sai datayi gyaran murya sannan tace saleem nasan ka da biyayya na tabbata bazaka taba watsa mana kasa a ido ba kamar yadda husna bata watsaman kasa a ido ba. ai yanaji an ambata husna gabanshi ya fadi. bakinshi na rawa yace insha Allahu mummy bazan watsa muku a kasa a ido ba kome kuka umarcenj zanyi. mummy tace gud nasan haka . kuma nasan ka tabbata bazamu cuceka . yace kwarai kuwa. mummy tace mun yanke hukunci zamu hadaku Aure da husna. ai da sauri yace what!!!! hade da zaro ido. mummy tace haba son yanzu fa kagama min alkawari zakayi mana biyayya. bantaba tsammanin haka daga gareka ba son. yace danAllah mummy kiyi hakuri maganan ce tazomun bazata. Amma na Amince mummy . mummy tace yauwa yaran Albarka insha Allahu bazaka taba danasani ba nasan watarana sai kayi Alfahari da wannan Auran. tashi kaje Allah ya maka Albarka. Amin kawai yace ya tashi dan jinkanshi yake kamar zai rabe biyu gaba daya ya shiga tashin hankali bayan fitanshi kuwa mummy tayi farinciki amma tawani barayin kuma tausayin husna takeji. Amma ba abinda yafi karfin addu'a zata cigaba dayi musu addu'a. saleem da kyar ya karasa dakinshi dan har wani jiri yakeji. yana isa ya fada gado ya kwanta yayi rub da ciki. a wannan dare saleem beyi baccin kirki ba. shi gaba daya tunani yakeyi wai husna zai aura karamar yarinya da ita . yaushe ma tagirma toh meye abin aure a jikinta. shi gaba daya ancuceshi dan bazai iya nunata ba a matsayin matarshi.. ita kuwa husna bacci tasha mecike da farinciki.... mummy kuwa tana shiga dakin daddy ta iske shi shima har yayi wanka yana zaune yana karanta newspaper.+ da murmushi ta karasa kusa dashi. yana kallonta yace wannan bakin naki akwai magana yanda yaki rufuwa . murmushi tayi tace kwarai kuwa nazo maka da Albishir me dadi . daddy kuwa ajiye jaridan yayi a gefe yace uhnmm ina jinki uwargidana. tace toh yara dai sun yadda sun Amince da magana Auren. daddy sai dayayi gyaran murya sannan yace inafata bazuwa kikayi kika tilasta musu ba. mummy tace haba ya kake magana haka mezaisa na tilasta musu husna tana son saleem a yanda na lura shikuma saleem koda na mishi magana be musa ba kasan shi saleem ba'a taba gane mishi . ba'a sanin inda ya dosa ko yana son abi bazaka ganeba. daddy yace hakane Allah ya tabbatar da Alheri amma zanyi musu magana kowa naji ta bakinshi. sannan zan kira ita mahaifin husna muyi magana dashi. mummy tace toh hakan ma yayi. sannan ta tashi ta koma gefe ta samu wuri ta kwanta. daddy shima kashe hasken wutan dakin sannan ya kwanta ya jawo mummy jikinshi. washegari saleem daya tashi da wani matsanancin ciwon kai ya tashi da kyar ya samu yayi sallah asubah ko masallaci be iya zuwa ba yana idar da sallah ya koma ya kwanta. husna kuwa da wuri ta tashi ta shirya ta taya mummy hada breakfast bayan sungama ta nufa daki tayi wanka sannan ta fito a lokacin data sauko ta iske mummy da daddy zaune akan dinning table. da fara'a ta karasa tace daddy gud morning yace morning my daughter. sannan ta samu wuri ta zauna . tace daddy shine bakajirani nayi serving dinka ba. mummy tace na lura kedai bakya so na samu ladan mijina ni kadai. ni gwamma ma kiyi aure kije chan gidan mijinki. husna kuwa rufe ido tayi tace kai mummy . daddy kuwa cewa yayi a'a a kyale min daughter ta haka. daddy yace ah wai saleem befito bane haryanzu . mummy tace nima maganan dazanyi kenan shida yake fita da wuri amma kuma ace har yanzu shiru. itadai husna batace komai ba . bayan tagama ta tashi ta hau sama ta dauko jakanta da key din mota ta sauko. sallama ta musu sannan ta nufa skul. bayan sungama breakfast daddy shima daki ya koma. mummy kuwa dakin saleem ta nufa. buga kofan tayi taji shiru dataji shiru ne ta tura kofan taji shi bude. tana shiga ta iske shi a kwance ya rufe da bargo. da sauri ta karasa ta taba kanshi wani zafi taji sosai. tashinshi ta shiga yi da kyar ya buede idanunshi ya sauke shi akan nata. yace mummy. tace son meyake damunka haka. naji jikinka yayi zafi . yace kaina ke ciwo tace kasha magani kuwa? a'a yace. tace toh ka tashi kayi brush bari na kawo maka breakfast dinka nan. kai kawai ya daga mata. da kyar ya tashi yayi brush ya fito kenan ita ma mummy tashigo rike da tray a hannunta. tea din ta mika mishi sannan ta jawo stool ta ajiye plate wanda yake shake da soyayyen dankali da kwai sannan a gefe kuma ga liver sauce. da kyar yake kurban tea din. sai da mummy ta takura mishi sannan yaci dankalin. sannan ta dauko first aid box ta bashi magani. sai datagama sannan tace haba son kana dr amma bazaka kula da kanka ba. sannan tace nasan ba komi ya jawo maka ciwon kai ba illa damuwa dakasa a ranka akan maganan Auren nan saleem inaso kaciire komai a ranka ka mika ma Allah lamarinka ka kuma maba biyayya insha Allah zakaji dadi nan gaba. karka manta husna yar uwarka ce kuma anan gida ta taso tarbiyan daka samu shi ta samu. kuma yarinyan tanada biyyaya na tabbata bazaka taba dana saniba . nan dai taita mishi nasiha sannan ta tashi ta fita. ba laifi ya danji sanyi amma duk da haka ranshi a jagule yake. daddy da daddare yatarasu gaba dayansu dan yaji ta bakinsu bayan ya bude taro da addu'a. sannan yace duk da dai naji maganar a abakin mummynku toh kuma inaso naji ta bakinku. inaso naji shin kun yarda kun Amince da a kulla Aure a tsakaninku. shiru sukayi bawanda yace kala. sai da daddy ya maimaita sau uku sanna kowa ya daga kai. daddy yace ba daga kai zakuyi ba amsa zaki bani da bakinku. A tare sukace eh mun Amince. daddy yace Allah ya muku Albarka. ya kuma tabbatar da Alheri. nan ya zauna ya musu nashiha daganan yace zaku iya tafiya. kowa tashi yayi ya nufa dakinshi. daddg kuwa waya ya ciro yakira bbn husna ya shaida mishi komai. bakaramin farinciki bbn husna yayi ba nan yayita musu addu'a hade da Allah ya tabbatar da Alheri. sannan yace ma daddy aikune iyayan husna nabar muku komai a hannunku. daddy kuwa dadi yaji. kafin suyi sallama sai da daddy ya tsokaneshi akan yaki aure toh ga husna nan zatayi aure. dariya kawai yayi sannan yace ai loakcine. daddy yace kullum haka kakecewa. toh Allah ya nuna mana lokacin Amin yace sannan sukai sallama. nan kuma yakira dan uwanshi ya shaida mishi gobe yana nanzuwa . sannan yayi albishir akan ya shaidawa innah jikanta dai ya kusa Aure. dayake innah a gidan Alh suleiman take . tana zaune ne a barayi daban kuma tana da masu aikinta dake mata komai. innah bata dawani buri daya wuce taga saleem yayi Aure. washegari kuwa Alh tahir ya nufa gidan dan uwanshi. sai da yafara zuwa ya gaida mahaifiyarshi sannan ya kira suleiman yace mishi yana barayin innah. nan fa ya iso suka zauna suka dan taba hira kafi kuma sufara magana akan abinda ya tarasu. nan dai sukaita shawarwari inda aka sa rana wata uku masu zuwa. innah bakaramin farinciki tayi ba dan innah nason husna ta yaba kuma da hankalinta.

Post a Comment for "DR SALEEM CHAPTER 2"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...