Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

DAN ADAM CHAPTER 34

DAN ADAM CHAPTER 34

- - Post a Comment
DAN ADAM CHAPTER 34
Idan kaga Ango Faruk da Ummi sai ka ji tamkar ka sacesu tsabar kyan da suka yi. Gaba daya shigar fari sukayi, shi shadda ita kuwa wani arnen leshi ta sanya, akayi mata nadi da silver, ta yi kyau har ta gaji da yinsa, gaba Angon kusan susucewa ya yi da ya ga Amaryarsa, dauriya ce kawai ya yi gudun 6atamata kwalliya. Wajen ya hadu, har iyaye suma sun je har kuwa Ihsan wacce ke faman dagawa. Shigowar Ango da Amaryarsa yasa su Fati zaro ido suna dubansu, Husna ta hau dariyar mugunta. "Ya akayi ne Fati? Ga Yayanmu nan fa da matarsa." Ta rad'amata saitin kunnenta alokacin da ta ke daukar bidiyon Amarya da Angonta. Fati banda Umm babu abinda ya fito daga bakinta don ita har kunyar Ummin ta ji, ashe shine wanda zata aura amman basu sani ba ta kyalesu suke faman zuzutashi? Sai bayan an zazzauna ne Husna ke labartamusu cewa tun alokacin ma mijinta ne kawai dai ta 6oye ne. Suka yi ta mamaki, can kuma suka hau yiwa kansu dariya na rashin hankalin da suka yi. Ummi ta maida hankali ga duban dubban mutanen da suka taru dominsu, ta sauke kanta tana mai jin nauyi, tasan fa dakyar idan rabin wadannan mutanen basu san tarihinta ba, don da yawansu matan sukan zo siyayya ko zumunci wajen Hajiya Babba, wasu suna ganinta matsayin yar aiki wasu kuwa basu san ta ba saidai jikinta na bata cewar zasu ji labarinta. Jin hannun Faruk cikin nata ne yasa ta dago kai gami da dubansa. Kallo ya ke mata, ba irin kallon da zata iya watsarwa ba ne, kallo ne mai nuni da tsantsar soyayya. Ya dan rankwafo saitin kunnenta. "Tunanin daren ki ke? Gidana fa za mu wuce daga nan." Ta turo baki tana ji kamar ta saki kuka don haushi da kunyar da ya bata, ta lura yau tsokana ya ke ji da shi don tun a mota ya ke faman tsokanarta. Dariya ya yi wacce ta bawa dumbin yan uwansa mamaki musamman yan Adamawa da basu saba ganin miskili Faruk na dariya haka ba. "Lallai yau ango ya ke." Acewarsu. Taro ya yi kyau, Ango da Amarya sun sha lik'i da hotuna, hakanan sun yanka kek (cake) har sun ciyar da juna, abinda ya burge mutane bai wuce dan russunawar da Ummi ta yi ba, da kuma shi din da ya bata cike da kulawa. Ikram ta yi ta cilla idanunta, ta kasa daukesu daga kan Gidado wanda a yau ya yi shigar kufta bak'i wacce ta haskaka shi ta kara fiddo tsantsar kyawunsa. A sace ta ke daukarsa a hoto duk Intisar na lura da ita, ita a nata ganin me zai hana ta nemi Ummi ta sanarmata cewar tana son dan uwanta ko da taimakon da zata iya yi gareta? A ganinta wannan ce damar da zata iya cin galaba ta samu ya saurareta. Amma abun ne da daure kai ace mace har mace kamar Ikram ta 6uge a soyayyar wanda ke zaune a kauyen Jar Kwami, anya wannan zata haifar mata da d'a mai ido? Hankalin Intisar ya dauke sa'ilin da mijinta ya kirata a waya akan ta je gareshi. Bayan an tashi da taro kalilan cikin iyaye suka raka Amarya gidanta, sai kuwa kawayen Amarya wadanda suka ce sukam komin dare sai sun tsaya siyan baki, nan iyayen suka tafi suka barsu ganin sha biyu ta wuce, suna fita Angwayen suka shigo, nan fa suka ce sai an basu kudin siyan baki, abin sai ma ya bawa su Haidar dariya, basu tsaya ja in ja ba Ango ya ajiyemusu bandir na d'ari-d'ari guda biyu, suka ce sam basu amince ba tunda sun san Angon ma'aikacin Banki ne to kudin su fi haka. "Wai kuwa ba ku ganin hadarin da ke a garinnan?" Cewar wani cikin tawagar da dariya. Murmushi Faruk ya yi, Haidar yasa hannu ya ciro yan dubu-dubu saidai ba rafa ba, ya mik'awa Husna wacce ta fi kowa daga murya. Nan suka sanya shewa gami da basu hanya su shiga, wani cikin abokan ya yi takaitacciyar nasiha sannan suka yi addua aka shafa, daga nan suka titsa keyar yan matan suka fice, Abubakar na fadin. "A kularmin da Innota, ko k'uda banaso ya takura rayuwarta fa." Dariya kawai Faruk ya yi sadda ya yi musu rakiya. Ya daga kai ya dubi sararin samaniya ganin yanda ake walkiya akai-akai da kuma cida ga kuma iska mai dadi da karfi, ya juya ya koma ciki bayan ya rufe kofar gam! Kai tsaye dakin Amaryarsa abar so da kaunarsa ya nufa, a zaune ta ke kamar yanda suka barta, wannan karon kukanta ya yi karfi fiye da baya, ya karasa ya hau saman gadon ya cire lullu6in fuskarta gami da d'ago ha6anta. "Ummin." Wannan murya ba ta koyaushe bace, ita kadai tasan zak'in da muryar ke yi mata, ita kadai kuma tasan yanda ta ke ji a jiki da zuciyarta aduk sadda ta ji. Kasa amsawa ta yi, saidai kuma dif kukanta ya tsaya sai hawayen. "Kukan ya isa haka, ko kina so na kasa cika alkawarin da na daukarmiki cewar ni Faruk bazan bari Ummina ta shiga kuncin rayuwa ba da iznin Allah? In sha Allah Ummina kuka ya k'are miki saidai ko na dadi muddin kina tare da Sadaukin Hajiya." Ta lumshe idanu kawai sa'ilin da labulen dakin da ke kadawa da karfi ya soma feso musu ruwa da aka soma sakamakon windon dakin dake a bude. Ya runtse ido yana murmushi yayinda ya dan ja yatsun kafarta har ta danyi k'ara kadan. "Na ta6a sanarmiki cewa inason lokacin ruwa?" Ta girgiza kai a hankali tana mai lumshe ido sakamakon ruwan dake dan fesowa fuskarta. Ya dora yatsansa saman idonta na hagu yana wasa da shi. "Kinsan dalili?" Yana maganar tamkar ba ya so. Zuciyarta na bugu da karfi-karfi ta k'ara girgiza kai. Ya dan bugi bakin kadan. "Magana fa za ki yi, yau hira zamu yi." Ta dan turo bakin kadan batare da ta ce uffan ba. Saitin kunnenta ya matsa ya yi mata rad'a. "Zuciyata na nishadantuwa aduk sadda ake ruwa, ina jin wani farin ciki." Ta hade jikinta wuri daya. "Um." Shine abinda ta iya furtawa adalilin sanyin da ta soma ji sakamakon ruwan da ke dan shigowa. Ganin haka ya mike ya rufe windon ya koma gareta. "Tashi ki watsa ruwa ko kya ji dadin jikinki, daga nan ki yi alwala, ko kina bukatar taimakona?" Ta girgiza kai cikin sauri, ya shafi fuskarta yana 'yar dariya daga haka ya fice daga dakin, ta mike tana mai bin bayan mijinta da kallo, ta daga hannu sama gami da yiwa Allah godiya da Ya bata miji har miji irin Umarul-Faruk, fatanta zamantakewarsu ta yi kyau su shimfida rayuwa tsabtatacciya. Kafin yazo ta hau k'arewa dakin kallo wanda yasha adon fari da ruwan hoda, har ya gaji da haduwa. Nan ma bandakin ya yi mata kyau don gaba dayansa farin tiles aka shimfida har jikin bango. Da ruwan dumi ta yi wanka sannan ta dora alwala, bayan fitowarta ta sanya doguwar riga fari k'al mai ru6i biyu ta bacci sabuwa dal wacce aka sanyamata a akwati, Abida ta jaddadamata ta sanyashi yafi sau uku, ya hadu iya haduwa, na k'asan iyakarsa gwuiwa, sai kuwa na saman wanda ya ke dogo. Ta dora zani a sama sai hula mai taushi da suka sanyamata mahad'in kayan. 'Ina zan iya yawo haka gaban Yaya Faruk banda abin Anti Abida?' Ta yi maganar a zuci. Tana cikin ninke wadanda ta cire ne wayarta ta shiga k'ara. Ta yi saurin cirota daga yar fos din da ta halarci Dinner party. Gogannata ne, saida gabanta ya fadi, ta yi addua kafin ta amsa. "Ummina zo gareni." Ta hau dube-duben hanyar shigowa da dakin. "Kana ina?" Ta fada a sanyaye. Murmushi ya yi mai sauti kafin ya amsa. "D'akina." Shiru ya biyo baya, kamar ta ce ina ne dakinnaka saidai ta fasa. "Toh." Ta furta a hankali kafin kuma ya ajiye wayar. Hijabinta fari k'al ta ciro cikin karamar akwatin da Anti Abida ta had'amata sai kamshin turare ya ke yi ta zura ajikinta. Silifas ta sanya ta fito falon, saida numfashinta ya kusa dauke don kyau da tsaruwar falon, ba tarkacen kaya saidai komai mai tsada ne acan gefe kuma wajen dinning ne. Labulenta lemon green ne mai surkin bak'i haka suma kujerunta. Ta numfasa tana mai kara yiwa Daddy adduar fatan alheri a zuciyarta. Kai tsaye ta nufi wata kofa ta bude, nan ma daki ne amman gado ne kawai madaidaici sai bandaki. Ta rufe ta bi dan corridor da ke a gefe, nan kofa daya ce ke fuskantarka. Ta murda ta shiga, wani sanyi ya ratsata yayinda kafafunta suka nutsa cikin wani lallausan kafet na bakin kofar, fitilu a kashe hakazalika an bude baranda sai iska kawai ka ke ji ta ko'ina, ba ka ganin komai sai hasken katuwar talabijin dake jikin bango, sallama ta yi saidai babu alamun yana falon. Sai kuma ta ji ya amsa yana fitowa daga dakinsa rike da darduma. Sanye ya ke cikin doguwar jallabiya shima, ya kunna fitila yana fadin. "K'araso mana." Ta karaso gabanta na dukan tara-tara ta kasa kallonsa. Bayan ya shimfida ya ja su sallah raka'a biyu bisa sunnah, sannan ya yi musu adduoi daga haka kuma ya janyo ledar gefensa, da kansa ya fita ya dauko filet ya dawo. Da kansa ya ciyar da Umminsa tana taunawa kamar bata so, bayan sun kammala ta taimaka mishi da kwashewa ta kai kicin, a karshe ta zarce dakinta ta wanko baki. Gaba daya ta kasa komawa sashensa, to ta koma ta ce mishi me? Kawai sai ta kashe fitila ta haye gado saidai kafin ta kai ga runtsawa wayarta ta dauki k'ara. Ta daga don tasan shi ne. "Ummina zo ki amshi wani abu." Ta danyi shiru sai kuma ta bishi da toh. Dole ta mike ta maida hijabinta ta fito. Koda ta shiga wannan karon ya kashe komai sai hasken walkiya da ke dan haska dakin. Kafin ta kai ga wani yunkurin ta ji mutum ta bayanta har saida ta firgita. "Haka akeyi kuma daga kai kaya kicin sai ki gudu ko?" Ya yi maganar k'asa-k'asa, a hankali ya kunce daurinta kafin ya cire hijabin. "Wannan duk sanyin ne? Zo mu je ki ji." Ita dai ba bakin magana sai uban tsoro da ya mamaye zuciyarta. Tana a jikinsa har suka shiga dakinsa wanda ya fi nata girma da haduwa, can wata kurya ta hango gadon nashi wanda baifi na kwanciyar mutum biyu kacal ba an sanya labule an rufeshi ruf ta yacce ba ka hango cikinsa. 'Shi kuwa yana son kalar blue a rayuwarsa.' Ta fad'i a zuciyarta ganin nan din ma fari da bulu ne kalar dakinsa. Dif ta ji ya kashe fitila sadda ya karasa da ita ga makwancinsa. Kamar ta tambayeshi ko baya jin sanyin gari ganin yanda ya bude winduna yabar net ga iska na kadawa sai kuwa hasken walkiya da ake yi akai-akai saidai ko me zaayi yau kam bazata iya magana ba, to ina bakin maganar? Ko daga rikon da Faruk ya yi gareta tasan yau sai a hankali, gabanta sai safa da marwa ya ke yi saidai ta yi alkawarin faranta ranshi a wannan rana...! "Welcome to your love Asiya... I love you and i will show you...!!! ( Barka da zuwa ga masoyin ki Asiya. Ina sonki kuma zan muna maki...!)" Bai damu da ko ta fahimci yaren nasa ba ko a'a, saidai wannan Faruk sak ne haihuwar Ahmadu da Fatima, ba wani can da boko da gayu ya ratsashi ba. Daga wannan babu wanda ya kara doguwar maganar da hankali zai dauka acikinsu...!!! ASUBA TA GARI FAR HAS....!!! Murmushi ta yi ta k'ara muskutawa gami da k'ara k'ank'ame lallausan bargo wanda ya hade da tsadadden kamshin turarenta da na Faruk, saidai kasancewar nashi yafi nata karfi yasa ya rinjayi nata, mafarki ta ke yi mai dadi wanda gaba daya cikin baccin ta ke yinsa har tana murmusawa gami da k'ara rukunkume bargon, wai ga ta ga Faruk yana kara jadaddamata irin mugun son da ya ke yi gareta. Ta yi nisa a mafarkinta ta ji ana zagaye kunnenta da yatsa, firgigit ta farka, Faruk ta gani zaune sanye da jallabiya wacce ta manne jikinsa kasancewar daga wanka ya fito sai kuwa fuskarsa da ta nuna hakan don jik'e ta ke da ruwa har kuwa sumar kansa. Ai da gudu ta tura kanta cikin bargon tana jin kamar ta nutse awajen ga wani radadi da ta ke d'an ji a jikinta. "Morning Ummina, tashi ki yi wanka kada lokacin sallah ya wuce ko na yi miki?" Da sauri ta girgiza kai, murmushi ya yi kafin yasa hannu ya lalubo nata, wani sanyi ya ratsata. Ya soma kokarin taimakamata ta mike saidai ita gaba daya nauyi ta ke ji ya ganta a yanayin da ta ke duk kuwa da cewar a daren ya fadamata kunya tsakaninsu yanzu ta kau. Mikewa ya yi ya bar mata dakin ganin yanda ta ke d'ari-d'ari da shi. Yana fita ta yi wuf ta dauki abinda zata dauka ta fad'a bandaki. Saidata yi wanka da ruwan dumin da ya tara mata kafin ta fito. Nan kuma ta maida hijabinta ta d'ora zani a samansa, zata tayar da sallah ya shigo dakin. "Zo mu yi jam'i mana." Ba musu ta bi bayansa ya tada kabbara ya ja su sallah, bayan sun idar ya yi musu addua suka shafa. Ta karasa ta durkusa gabansa kanta a k'asa. "Barka da Asuba." Ya sumbaci goshinta. "Kin tashi lafiya? Ya gajiyarki?" Murmushi ta yi a kunyace saidai bata iya amsawa ba. Ta mike zata fita ya dakatar da ita. "Ina za ki kuma?" Ta dubeshi a sanyaye. "Shida naga ta kusa kada ka makara a ofis zan dora maka kari ne." Ya taso ya zagayeta da hannuwansa. "Kar ki takura kanki, yau babu inda zanje ina nan tare da ke koyaushe." Ta lumshe ido tana murmushi ya ja ta suka koma daki nan ya kwantar da ita bayan ya rage mata kayan jiki ya barta daga ita sai fingilar rigar baccinta, hakan shima ya rage sannan ya hau suna fuskantar juna, ya kuramata idanu ya matse hannuwanta cikin nasa. "Allah Ya albarkaci rayuwarki Ummina, Allah Ubangiji Ya bani ikon kyautatamiki har abada, Allah kada Ya kawo kaddarar da zata gifta tsakaninmu har ta rabamu. Ina sonki ina kaunarki, bayan Hajiyata da Daddy, bani da wacce nakeso nan duniya kamarki, bazan gaji da gayamiki kin mamaye ko wane sak'o na zuciyata ba Ummina, bazan gaji da gayamaki yanda nake sonki ba, da ace akwai kalmar da ta fi I love you nuna tsantsar so da kulawa da na fadamiki, saidai fatana bai wuce na Allah Ya bani ikon nunamiki a zahiri ba a kuma kowace rana. Matso nan." Ya karashe gami da janyota ta kwanta saman lallausan kirjinsa, ta lumshe idanunta tana jin so da tsananin kaunarsa na k'ara zagaye jini da jikinta. "Kinji yanda bugun da zuciyata ya k'aru?" A hankali ta gyada kanta. Ya shafi kanta. "Haka ya ke yi tun farkon ganin da na yi miki a gidan Modibbo (Ranar meeting), haka ya cigaba da yi har zuwa ranar daurin auren Haidar, bai tsananta ba sai a daren da na daukoki daga wajen party zuwa gidan Mami, kinga kuwa Faruk ya jima cikin mayen son Asiya. Ki rike Faruk da amana, ki guji yi mishi hali irin na DAN ADAM na butulci, in sha Allah za ki ji dadin zama da shi." So kenan, don kuwa Ummi batasan sadda ta matse Mijinta a jikinta ba. "Ina sonka Yaya Faruk, kai ne hasken rayuwata, da kai nake tunk'aho, kai ne ka soma nunawa duniya nima mutum ce kamar kowa, ina da tawa darajar, zan iya mallaka maka dukkan abinda na mallaka ba ma jikina kawai ba, ina sonka ina kaunarka, bana fatan Allah Ya nunamin ranar da zan yi butulci agareka." Baisan lokacin da ya dagota ba, ruf ta rufe idanunta yayinda kirjinta ki matsanancin bugu, ya zubamata idanunsa masu nuni da tsantsar kauna kafin yasa hannu ya ja abin rufa....! Sai wajen takwas na safe suka farka daga baccin da ya kwashesu, ta rigashi farkawa hakan yasa ta zare jikinta a hankali daga nasa, ta zubamishi ido tana murmushi, komai na shi abin sha'awa ne, a sannu ta dauki abinda zata dauka ta fice zuwa dakinta. Kai tsaye wanka ta yi ta shirya cikin wani jan yadi ta yi kwalliya. Har wani ajiyar zuciya ta saki ganin yanda ta fito ta yi kyal da ita. Murmushi ta yi ta murza daurin dankwali kamar yanda Husna ta koyar da ita bayan bidiyo kala-kala da ta aikomata na daurin dankwali. Saida ta kammala ta feshe jikinta da turaruka masu dadin kamshi kafin ta fita zuwa kicin ta soma kiciniyar hada musu karin kumallo, tana cikin yi ta ji mutum a bayanta. Har saida ta firgita ta juyo, ganinsa yasa ta sunkuyar da kai tana murmushi. "Bana ce karki wahalar da kanki ba?" Ya fada a shagwabance. Ita kam batasan ita da shi wa zai rarrashi wani ba... Ka yi hakuri gani na yi..." Sai kuma ta yi shiru. Murmushi ya yi ya ja hannunta zuwa dinning table ya zaunar, ta dubeshi ya sanya yatsansa a baki alamu na ta yi shiru. "Shii! Yau aikina ne ba na ki ba." Daga haka ya yi hanyar kicin yana murza hannuwansa. Ta bishi da kallo kamar ta yi dariya, yana sanye da riga tshirt marar nauyi sai kuwa wandonsa 3 quarter. Tunaninta ko zai iya tace ruwan shayin, sam batasan ma akwai kayan abinci ba da ta soyamusu kwai. Shi kuwa sanin akwai din yasa shi tsayawa gami da rike k'ugu bayan ya ciro kwai guda bakwai a firij. Toh ya zaiyi? Me da me ake sanyawa acikin kwai idan za'a soya? Ya ta6e baki don yasan bai wuce maggi kawai ba sai a yanka albasa. Nan ya tace ruwan shayin ya sanya a filas kafin ya koma ya dauko (bowl) ya soma fasa kwan, ya bi wata kofa dake cikin kicin din wanda ya kasance store, ya dauko albasa guda daya. Haka ya na gyarata yana hawaye, idanunsa a rufe ruf, ji ya yi an rike hannuwansa. Ya bude idanun dakyar ya na duban Ummi wacce jin shiru ta biyo baya, ta hadiye dariyarta. "Kawo zan karasa don..." Ai bata karasa maganar ba ya sakarmata albasa da wukar ya fita da sauri-sauri yana fadin. "Ina sonki fa." Saida ta tabbatar ya yi nisa kafin ta tuntsire da dariya ta yi mai isarta sannan ta soma aikin. Shi kuwa gogan yana bandaki ya na fama da wanke idanunsa, saida ya wanke hannunsa tas da handwash kafin ya soma da fuskarsa, bayan ya kammala ya goge da karamin tawul, sai kuma ya tunano da Umminsa wacce ya ce ba zata shiga kicin ba, ya dan daga gira. Toh ya zai yi? Daman fa ba ta6a shiga kicin din ya yi ba, shawarar Haidar ya bi wanda ya ce a ranar farko ya yi mata karin kumallo da kansa. Alokacin dubansa ya yi ya yamutse fuska. "Kasan dai ba shiga kicin na ta6a yi ba ko?" Haidar ya yi dariya ya daki kafadarsa. "Koya za ka yi for the sake of love." Alokacin murmushi kawai ya yi. Sauke ajiyar zuciya ya yi gami da ajiye tawul din a ma'ajiyarsa, kai tsaye ya fito falon, kamshin suyar kwai ya cika falon, k'arar kwankwasa kofar da akayi ne yasa shi fasa shiga kicin din ya nufi wajen kofar. Malam Ado direban Hajiya Babba ne rike da kwando. Ya gaisheshi da girmanawa, Faruk ya amsa kafin yasa hannu ya kar6i kwandon da ya ke mik'o mishi. "Gashinan, Hajiya ta aikoni na kawo." Murmushi Faruk ya yi, da yasan zata aiko ai da bai wahalar da Umminsa ba, ya mishi godiya sannan ya sallameshi. Ummi da ta ke jera kayan kari a saman tebur ta soma bin hannun Faruk da kallo ganinsa rike da kwando. Ta karasa bayan ta ajiye tiren hannunta, ta kar6i kwandon alokacin da ya ke fad'in. "Kinga Hajiya ta aikomana da abin kari kuma." Murmushi kawai ta yi. Farfesun kaza ne sai kuwa ruwan shayi a filas, farfesun ta zubamusu, suka yi zaman sha. Yanda ya ke tarairayarta tamkar wata bebi abin har ya soma daina bata kunya don ta lura kamar halinsa kenan idan zata tsaya kunyarnan sai ta cuceshi kamar yanda ya sha fadamata kenan, ba ya son kunyarnan idan sun yi aure. Karfe sha daya da mintuna suna zaune a falo ya sanyata jikinsa suna hira inda ya ke k'ara yi mata albishir da zai nemamata Malamar da zata dunga zuwa har gida domin koyar da ita, wannan albishir da ya ke yawan yi gareta yafi komai sanyata cikin farinciki. Hon da aka yi ne yasa hankalinsu ya koma ga waje, maigadin ya bude aka shigo, hakan yasa shi mikewa gami da lek'e ta windo. Murmushi ya yi sannan ya dubi Ummi. "Yan uwanmu ne fa 'yan Gombe." Jin haka batasan sadda ta mike tsaye ba tsabar d'oki ta nufi hanya don budemusu. "Tsaya mana." Muryarsa ta katseta. Dankwalinta ya mik'omata ta yafa a kanta suka sakarwa juna tattausan murmushi kafin ta nufi kofar da ake kwankwasawa don ta bude shi kuwa ya koma sashensa. Anti Halima ce ta soma shigowa sai kuwa Hajiya Salma a bayanta da sauransu. Ta rasa ina zata sa kanta don farinciki, wannan ya rungumeta wannan ya shafa kanta, duk sai ta ji kunya ta cikata. Abu ta yi mata rada a kunne. "Har kin chanja." Ta harareta, ta tuntsire da dariya. Haka suka shiga suka zauna. Nan wadanda basu samu zuwa ganin gida ba suka hau zagaye, Faruk ya fito wannan karon sanye da dogon wando maimakon gajere ya durkusa yana gaidasu. Ummi ta dan dubeshi. 'Ashe yasan kunya.' Ta fada a ranta. Bayan gaishe-gaishe ne ya fita jin cewar da Gidado suke. Hajiya Salma ta ja Ummi har d'aka, wasu kayayyakin ta kara damk'amata sannan ta bita da nasihu masu ratsa jiki da jini. Karshe ta rungumo kafadarta yayinda kwalla suka cicciko mata har saida suka zubo. "Ina ganinki tamkar Zahra Innon Abubakar, ina kaunarki har cikin zuciyata Ummi. Ki rikeni matsayin uwa kamar yanda na rikeki nake miki kallon diyata kinji?" Ummi dake hawayen farinciki itama ta gyada kai tana murmushi mai bayyana hakora. "In sha Allahu Mama (Kamar yanda ta ji Abubakar da kowa ma suna fad'a) za ki sameni mai yin biyayya gareki irinta d'a da uwa." Hajiya Salma ta share fuskarta yayinda ta ke ji kamar da Zahra ta ke magana, ta rike hannun Ummi. "Allah Ya albarkaci rayuwarki Ummi. Tashi ki adana wadannan kafin wani ya shigo." Ta amsa da to sannan ta mike ta bude sif ta bude dirowar dake cikinta daga tsakiya ta zubasu. Sun jima suna hira da mutan Gombe sannan sukayi shirin tafiya.+ *** *** *** Ikram kwance saman gado bayan dawowarta daga makaranta ta yi shiru tana jin takaicin rashin sallamar da basu yi ba da Gidado hakanan bata samu ta kar6i lambarsa ba har ya tafi. A haka Ihsan ta shigo tana sanye da riga da siket yan kanti, su sai gobe zasu wuce. Ta dubeta duban kurilla kafin ta zaune gefen gadon cike da damuwa. "Na tsani na ganki cikin wannan yanayin wallahi 'yar uwa, ji na nake yi kamar zazza6i. Ke kuma ga shi nayi-nayi ki fad'amin damuwarki kin k'i, karki manta a baya kece mai bani shawara kan na cire damuwar komai cikin raina game da Yaya Faruk, yanzu kuma da Allah Ya yayemin sai ke ki ke neman jefa kanki cikin damuwa wacce jikina ke bani kamar damuwar irin tawa ce." Ikram ta dubeta da mamakin yanda akayi ta d'agota da sauri haka. Ta numfasa kafin ta mike zaune ta matso gareta jiki a sanyaye. "Ki yi hakuri Ihsan, banaso sanyaki damuwa shiyasa ban fadamiki ba, wallahi son..." Sai kuma ta yi shiru tana mai jin nauyin furucin. Ihsan ta dubeta cikin zak'uwa. "Inajinki ki yi magana." Ikram ta sadda kanta. "Wallahi Soyayyar Gidado yayan Ummi ne ya maidani haka, bansan..." "What?!" Cewar Ihsan hankali a tashe cikin daga murya, wannan yasa Ikram kasa cewa komai ta yi shiru kawai. Ko me Ihsan ta tuna sai kuma jikinta ya yi sanyi ta buga tagumi ta yi shiru. Batasan sadda ta soma hawayen bakin ciki ba. "Mun shiga uku Ikram, mun shiga uku, ya akayi muka k'are a fadawa tarkon jinin Ummi? Kin kamu da son Gidado wanda bai fiki da komai ba, asalima kin ketareshi a aji, ga shi ina shirin auren Abubakar wanda a baya nake hura hanci nake tunk'aho nake kuma gani kamar na yi miji na nunawa sa'a wanda yafi Yaya Faruk komai na jin dadin rayuwa, ashe tunk'aho nake yi da dangin Ummi, yarinyar da tun farkon ganina da ita ban ta6a jin digon kaunarta ba, yarinyar da nake kishi a kanta. Saidai zuwa wannan lokacin na makaro don ban isa na tunkari Abba nace bana son Abubakar ba, ban kuma isa na ce hakan ba koda a karon kaina ne don yanzu inason Abubakar Ikram, ina jinsa a raina sai nake ganin abin tamkar a mafarki duk da cewar jinin Ummi ne, kinsan kuwa Abubakar koyaushe mukayi waya ba shi da hira sai ta Ummi? Sai ince miki wallahi ko matarsa Badiyya, ba ya yimin maganarta kamar yanda ya ke min ta Ummi a yanzun, koyaushe cikin kwatantamin yanayinta da Innonsa ya ke yi, ya na yawan cemin ya na jinta kamar Innonsa, sai ince miki tun jiya da na 6ata ransa a wajen fatin Yaya Faruk akan Ummi har yanzu ya k'i kiran wayata balle na samu damar ba shi hakuri, ni kuma gani nakeyi zubda aji ne na dauki waya na kirashi akan wata Ummi. Don Allah Ikram kada ki sa mu ji kunya, ki barmu ma da wannan da muke sha sanadiyyata, kuma naga kin soma shigewa Ummi, don Allah ki fita hanyarta." "Kuskure babba da ku ka tafka a rayuwarku." Suka tsinci murya daga bakin kofa, gaba daya suka juya ga kallonta. Intisar ta karasa shigowa ta rufe kofar don kuwa a dazun Ihsan bata karasa rufeta ba. Ta tako a sannu sakamakon kumburin da kafafunta sukayi ta isa garesu ta janyo kujerar gaban madubi ta zauna kafin ta dubesu a tsanake fuskarta a daure sannan ta soma magana....

Post a Comment for "DAN ADAM CHAPTER 34"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...