DAN ADAM CHAPTER 30 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

DAN ADAM CHAPTER 30

DAN ADAM CHAPTER 30

- - Post a Comment
DAN ADAM 

CHAPTER 30Suna zaune a falo da Hajiya dake lissafe-lissafenta na kaya hannunta rike da biro da dan(Memo) na lissafi, yayinda Ummi ke gefe tana karyawa, zuwa yanzu ta soma sakin jiki da Hajiyar. Sallama ya yi ciki-ciki, suka amsa, Hajiya bata dubeshi ba dalilin batason 6ata a k'irgenta. Ummi ta saci kallonsa, fuskar babu digon walwala, ta daure ta gaisheshi, ya amsa ganin Hajiya na wurin. Ta mike ta janyo tebur gabansa da niyyar hadamishi kari.
"No barshi, sai anjima zan karya."
Ta kada kai kawai ta koma mazauninta, Hajiya ba tare da ta dubeshi ba ta ce.
"A'a, kodai ba ka tare da yunwa ne? Wannan lokacin nasan kana karyawa Sadaukina, maza Ummi gama ki hadomishi."
  Ta amsa da toh. Ya yamutse fuska yana duban Hajiya.
"Wai kwanab biyun nan wa ke gyaramin daki ne? Toilet dina k'arni. Ko kusa gyaran bai yi."
"Samira ce." Cewar Hajiya tana dubanshi. Ya dan muskuta. 
"Daga yau ta daina bana bukata, sam bata iya aiki yanda ya kamata ba."
Hajiya ta dubi Ummi, kamar ta ce wani abu sai kawai ta share da fadin
"Allah Ya kyauta." Daga haka ta bi bayan wayar da aka kirata har ta yanke bata daga ba. Shi kuwa kwantar da kanshi ya yi jikin kujera ya lumshe idanunsa, shi kadai yasan me ya ke ji a zuciyarsa. Har Ummi ta gama ta hadamishi abin kari bai dago ba balle ya kalleta, itama dauriya kawai ta ke yi hakanan tana jin kunyar kanta bata son Hajiya ta fahimci akwai abinda ya hadasu, saidai tuni ta dagosu shiru kawai ta yi ta zubamusu ido. 
    Kai tsaye kicin ta sauka ta maida kofi da filet sannan ta yi hanyar sashensa, gyara ta hau yi, saida ta kammala ta tabbatar komai ya yi kyau sannan ta koma ga bandaki ta hau wankewa, saida ta kammala ta goge sannan ta fito rike da tsummokaran a bokiti, ta dubi ko'ina ta ga ya yi kyau sannan ta rufe kofar. Allah Ya taimaketa har ta zagaya wajen garden basu hadu ba, zama ta yi da niyyar wanke tsummokaran, sai kuma ta dakata cikin tunani, Allah Sarkin bayinSa kenan, kamar bata taka matsayin 'yar aiki ba kafin zuwan wannan lokaci da ta ke matsayi na Matar Dan Gida.  
  Acan kuwa Faruk koda ya hau samansa ya tarar da komai tsaf ya yi mamaki sosai da sosai, kamshi daddad'a kawai ke tashi, da sauri ya karasa ga dakinsa, nan ma an gyare tas hakanan bandaki wanda ke kamshi babu wannan k'arnin. 
"To wa ya gyara?" Ya tambayi kansa, ya fito ya nufi barandarsa don ganin nan dinma ko an gyara, shima(tiles) din kamar ba'a ta6a takawa ba.
Kamar ance ya dubi ciki garden, ya hangota tana faman wanke tsummokarai, ya kasa gaskata idanunsa, sai kuma ya ga ta mike tana matsewa gami da shanyawa. Ji ya yi kamar ana k'ara kwararo mishi sonta, ga wani tausayinta da ya ji ya dirar masa, ina laifin ma ta yi gyaran kawai banda wannan wanke-wanken? Ya soma ja baya yana girgiza kai.
"No Ummina, matsayinki ya zarce haka gareni."
   Kawai sai ya juya ya fita zuciyarsa na yi mishi babu dadi, ganinta ya ke yi kamar Ummin baya, wacce ta ke yiwa kanta kallon wata marar gata.  
   Ita kuwa tana tunane-tunanenta akan rayuwa har ta gama shanya, ta sanya hannu da zummar zubar da ruwan, sai ganin mutum ta yi tsaye, ta dubeshi shima din ita ya ke duba, ya kar6e bokitin ya ajiye, a kunyace ta sunkuyar da kanta. Ta kasa cewa uffan.
  "Kinyi min gyara, na gani kuma na ji dadi, Allah Ya yi miki albarka."
"Amin, nagode." Ta amsa jiki a sanyaye ganin ba digon walwala a fuskarsa har lokacin.
  "Don Allah Yaya Faruk ka yafemin na..."
  "Ki dunga barwa ita Samirar ta dunga wanke wadannan." Ya yi nuni da tsummokaran, fuskarsa a daure ya juya ya tafi. Ta bishi da kallo idanunta cike da kwalla, wannan fushinnasa yana cin ranta kwarai, saidai me za ta yi mishi ya huce?
  Misalin karfe sha daya Dakta da iyalinsa suka diro gidan, Jidda har daki ta biyota lokacin tana goge kayan Islamiyyarta, ta dan yi yak'e sadda gabanta ke bugu da sauri-sauri, tasan yau kam zaman gidan zai mata zafi saboda su da basu kaunar su bud'i ido su ganta. 
  "Anti Jidda sannu da zuwa, ina kwana."
Jidda wacce ta yi sakato tana dubanta da mamakin chanjawarta ta hau jinjina kai.
"Lallai kan mage ya waye, Ummin ce kuwa?" Ba kunya ba tsoron Allah ta furta a fili. 
Ummi ta na murmushi ta maida kanta ga gugarta batare da ta ce komai ba. 
Jidda ta ta6e baki sannan ta karewa dakin kallo kafin ta fice. Rufe kofarta ne yasa ta duban kofar, ga mamaki sai ta ji ta daure don ko kwallar bata yi ba, inda sabo kuma ai ta soma sabawa da wannan cin fuskar nasu. Fatanta lokacin makaranta ya yi ta wuce tun kafin su taru gaba dayansu abin ya zame mata da yawa, ga fushin Faruk gareta, sannan ga cin fuska daga su Jidda. 
    Faruk ya dubi Jidda, kwarai ya ji furucinta saidai ya basar ya cigaba da hirarsa da Dakta. 
   Ta iso garesu ta zauna gefen mijinta.
"Matarka ta yi k'iba ta kara kyau."
Ta fada tana duban Faruk, idan dutse zaiyi magana to ya yi gareta, ya cigaba da jan Dakta da hira. Jidda ta yi dariya kawai don tasan halin Faruk, koda zata wuni tana magana tunda kamar ransa a 6ace ya ke to fa bazai amsa mata ba. 
   Wajen karfe biyu saura sai ga Haidar da Intisar banda Ikram wacce daga can zata wuce makaranta, kamar hadin baki shima Babban Yaya ya iso alokacin da Fadila, Ummi na jin hayaniyarsu saidai bata ko lek'o falon ba, asalima alwala ta yi sannan ta shiga shirin tafiya makaranta. Turo kofar da akayi ne yasa ta waigowa, Intisar ce, ta shigo da murmushi saman fuskarta.
"Aa, Amarya Ummi sannu."
Ta gaisheta itama fuska a dan sake ganin ita dinma ba wani sabo suka yi ba amman bata bita da kallon banza ba irin na wadancan. 
   Ta karasa shigowa ciki tana fama da cikinta wanda ya doshi wata biyar saidai yana da girma. 
  "Makaranta za ki kenan? Ikram ma can muka barota a gida zata wuce, tare za ku yo nan."
"Toh." Ta fada cikin rashin sabo. 
Daga haka ta fita itama ta cigaba da shirinta, saida ta yi sallar Azhar sannan ta dauki jakarta ta fito. Duk suna falon, yaransu suna gida saboda Islamiyya sai an tashi zasu yo nan. 
   Duk suka dubeta, ta yi kasa da kanta tana karanto adduoi cikin ranta, haka ta karasa ta durkusa ta gaishesu, duk suka amsa.
"Amaryar Lil, Allah Yasa alheri." Cewar Dakta, bata amsa ba banda kasa da ta yi da kanta tana murmushi kadan. Hajiya ta dubeta.
"Ki tsaya fa ki ci abinci kan ki wuce."
"Toh."
Sannan ta mike daga durkuson da ta yi ta nufi kasa, Jidda kallon kafafunta ta ke yi da suka sha kunshi wanda ya kara haskakata, ta ta6e baki gami da yin kus-kus da Fadila suka dara gami da tafawa.
  Mazan suka dubesu kawai suka kauda kai. Faruk kuwa tsam ya mike. Ya dubi yayyunsa.
"Ina zuwa."
Daga haka ya sanya takalmi ya bi bayan Ummi, dariya sukayi, Hajiya kuwa murmushi kawai ta yi. Ta gama gaskatawa Ummi ce farincikin dan nata. 
   Ita kuwa baiwar Allah, a tsaitsaye ta ci fried rice din loma uku kawai ta yi, Binta na cewa ta k'ara, fadi ta ke a'a saita dawo. Ruwa ta sha sannan ta fito, har zata fita ta ji maganarsa.
"Ki jira na kaiki."
Ta tsaya cak batare da ta waiga ba, ya yi hanyar dakinsa, mukulli ya dauko, tana tsaye sai jin hon dinsa ta yi hakan ya fahimtar da ita cewar ta kofar baya ya zagaya. Ko a motar baice mata uffan ba, suna isa bayan ya tsaya ya dubeta.
"Yau me ya hanaki sanya safa?"
Cikin soma gajiya da wannan fushin na Faruk ta amsa cikin rawar murya.
"Na manta ne wallahi." Ya sa hannu gefensa ya bata wacce ya fito da shi ta sanya sannan ya cire lock ta fita. 
"Nagode." Shine abinda ta ce cikin rawar murya sannan ta rufe kofar ta fice. 
   Tana shiga su Shukra suka tareta.
"Anti Hasiya yau ma Yayanmu ne ya kawoki?"
Tsaki ta ja wanda batasan sadda ya fita ba, ta giftasu ta wuce, suka bita da kallo kawai. 
Husna ta lura kamar tana cikin damuwa, ta bi bayanta har kusa da kujerarta ta zauna gami da dafata.
"Lafiya kuwa Hasiya?"
Kamar jira ta ke yi kawai sai ta soma kuka, Husna ta rike kafadarta, ta duba ta ga ana kallonsu.
"Ki yi hakurin danne damuwarki, kinga idanuwa duk a kanki fa."
Jin haka yasa ta share idanunnata, ta daure ta nutsu, ayau ta ji kewar Antinta Amina kwarai, saidai itama Husna ta yarda da ita, tana da hankali, watakil ta samu shawarar da zata iya bata. .....
Saida aka tashi ne suka samu damar ke6ewa. Anan Husna ta yi shiru tana kallon Ummi, ganin haka yasa Ummi soma magana.
"Wata shawara nake nema agareki."
Husna ta gyada kai cike da k'osawa don sau wajen biyar kenan tana furta hakan amman ta kasa magana.
"Ina jinki."
Dakyar ta samu ta labarta mata kadan cikin labarinta wasu abubuwan kuwa ta sakayasu, ta nuna mata kawai dai tana fuskantar matsala yanzu da saurayinnata da aka daura aurensu aka bar biki daga baya. Ta karanto mata matsalar a sakaye sannan ta k'ara da fadin.
"Husna kin ganni ko? Ban budi ido naga mahaifiyata ba, sannan ban samu wata kulawa daga kishiyarta ba, har zuwa yanzu da aka zo batun aurennan, sannan ni duka-duka ma a Islamiyyar Kano da na ke fadamiki ban jima ina zuwa ba, wani sa'in idan wata fita ta zo shikenan bana zuwa. Ina cikin tsaka mai wuya Husna, ina 6atawa mijin aurena rai, ki taimakamin da iya abinda ki ka sani, yarda dake ne yasa na sanarmiki abinda ban ta6a fadawa kowa ba a makarantar nan."
Husna wacce ta cika da mamakin wai Hasiya yanzu matar aure ce, ta numfasa bayan kalamanta na karshe wanda yasa ta jin tausayinta.Murmushi ta sakarmata.
"Ki sha kuruminki k'awata, in sha Allah daga gobe zamu soma. Saidai abinda nakeson ki sanyawa ranki, shi fa mijinnan wajibi ne gareki ki bishi sau da k'afa, karki bari damarki ta wuce, idan ance biyayya ciki har da ba shi hakkinsa na aure idan ya nema tunda dai ansan da igiyarsa akanki, wannan zamanin ba'a sakaci Hasiya, mata da yawa neman mai aurensu su ke yi, wasu kuwa kamar su jawo namijin ya kwanta da su su ke ji, ballantana kuma idan mijinki wani hadadden ne, tuni za ki yi sake. A baya ne za ki ji duk iyayenmu na irin wannan kunya-kunyar, ansan tana da kyau saidai bisa shawara ki rageta, ki rungumi mijinki hannu bibbiyu. Karki damu, yanzu kinga dai anzo daukata, bari zuwa gobe zan taho miki da wani littafi SIRRINMU na wata tsohuwar marubuciya sai kuma wani Sinadarin Rayuwa shima marubuciyar ta yi kokari matuka wajen koyawa mata salon kula da miji da gida, zan kuma k'ara miki a kai. Duk fa litattafan Antina ne matar Yayana da nake hannunta, zan rufa miki sirrinki Hasiya koda baki nemi hakan ba."
Ummi ta dan ji sanyi, ta yi mata godiya sannan suka zagayo farfajiyar makarantar, anan suka yi kici6us da Fati.
"Yauwa, anzo daukarki fa tun dazu Anti Hasiya."
Ummi na jin haka ta daure fuska.
"Nikam karki kara kirana Anti banaso wallahi."
Fati ta rike ha6a.
"Ah, ai sai na kiraki da fin haka, kin kai wallahi. Sai ma idan kin hadani da yayannaki."
Dariya Husna ke yi ita kuwa Ummi tsaki ta ja kafin a fusace kuma ta bar wajen. Ganin haka Husna ta sha jinin jikinta, ta biyota da sauri gami da dafe kafadarta.
"Wai Hasiya kodai shine mijinnaki?"
Ummi ta juya, ganin Fati bata biyosu ba sai ma dagomata hannu da ta yi alamun (bye-bye) ta juyo ga Husna, kai kawai ta gyada mata a sanyaye.
"Innalillahi! Kai Hasiya wallahi ban ta6a ganin irinki ba, kina da kamar wannan me zai hanani zage damtse wajen ba shi kulawa ta musamman? Kodayake..."
Sai kuma ta yi shiru don ta tuna kalaman Hasiyar a dazu ta kuma fahimci cewa ko karatun litattafai ba ta yi, ita kuwa har na yanar gizo yi ta ke yi, tana kuma cin karo da abubuwan karuwa na Matan Aure, wasu kuma idan sunfi karfinta bata karantawa kasancewar yayanta kusan kullum sai ya bincika wayarta yasa ta ke takatsantsan.
Ummi babu abinda ta ce saima haushin kanta da ta k'ara ji, lallai kam ta yi babban kuskure a rayuwarta.
Suka rabu Ummi ta nufi motar, direban gidansu Haidar ne, Ikram na zaune ciki sai faman cika ta ke yi da batsewa.
Ummi ta shigo sannan ta gaida Direban, ta kara da fadin.
"Ku yi hakuri don Allah, bansan ya zo ba."
Tsaki kawai Ikram ta ja sai direban ke amsawa da babu komai.
Earpiece Ikram ta sanya a kunnenta tana jin wak'a , ita kuwa sai ta maida hankalinta ga kallon hanya cike da tunanin maganganun Husna, kwarai ta yi ganganci, tasan har da hudubar su Anti Abida da Halima ya taimaka wajen k'in sakarwa Faruk. Wanda sam bai cancanci haka ba, sai ta ji tana zuci-zucin gobe ta yi ko don Husna ta damk'a mata litattafan.
Har suka isa ba wanda ya cewa wani uffan, koda suka shiga kai tsaye sama kowannensu ya nufa. Nan suka iske daga Babban Yaya sai ko Faruk da Hajiya sai su Jidda kowanne na kawo raayinsa, lefe Babban Yaya da Hajiya ne zasu hada, na Faruk bai wuce kawai gani ba, kudin ma sunce ya barshi, sai batun dinner party da suke yi da kuma fiddo anko wanda Babban Yaya ya ce su fadi irin wanda zasu yi zai kawo musu su za6a. Duk wannan za su yi shi ne a cikin sati biyu, saboda zuwa Adamawa da zasu yi su kwana uku su dawo don Modibbo ya matsa akan lallai sai an tafi saboda wadanda tsoffinsu basu sani ba.
Shigowar su Ikram dinne ya katse su, Faruk idanunsa akan Ummi ya kasa daukesu, haka kawai ya ke jin kewarta ainun, wannan karon fuskarsa a dan sake, suka gaishesu sannan Ummi ta yi ciki ta bar Ikram anan, itama tana jin batun da akeyi ta mike zuwa nata dakin inda ciki ta riski Intisar kwance saman darduma ta idar da sallah.
Wajejan biyar na yamma, Haidar da Ridwan wadanda suka je daukar yara daga makaranta suka shigo ciki, don daman direban suka hutar da sanyashi dauko su Ummi kawai. Nan gidan ya k'are kacamewa, Ummi duk ta takura har saida suka wuce, koda aka kirata cin abinci ta ce ta ci, akan haka har fad'a Hajiya ta yi mata gami da nunamata kada ta sake irin hakan ta dunga ci tare da su. Daddy yana dawowa daga Kano inda ya je ta'aziyya matasan suka koma wajensa har Hajiya, nan ya ke jin dukkan shirye-shiryensu, ya yi na'am da hakan, ya kuma ji dadin yanda kansu ke a hade har kowanne ya dauki nauyin abinda zai yi. Haidar na buga I.v da rabo ya dauka, shi kuwa Ridwan na dinner party, yayinda Babban Yaya da Hajiya zasu yi lefe, karshe Daddy ya dauki alkawarin yiwa Ummi kayan daki da komai na mata, acewarsa ko don zaman da ta yi da su ta cancanta, bai dace su bar iyayenta da nauyi ba, ta zama tamkar jininsu. Faruk ya ji dadi matuka, bakinsa ya kasa rufuwa, bawai don wani abin ba sai don ganin kowannensu ke nuna kaunarsa da wannan auren, hakazalika hadin kansu ya fi komai faranta ransa, fatansa har mutuwa su kasance tare haka.
Washegari sam basu hadu da Ummi ba, sai ta waya ta kirashi, wannan karon bai gwanyata ba don ya amsa, ta gaisheshi ya amsa ba kamar jiya ba, a karshe ta rasa abin cewa kawai ta yi mishi adduar sa'a sannan suka yi sallama. Daga lokacin kullum sai ta gyara mishi daki tas.
Koda ta je makaranta Husna ta damk'a mata litattafan, shikenan kuwa ta samu abin karatu, koyaushe cikin karatu ta ke yi har ta soma gano kuskurenta kwarai, har sai gashi tun tana kunyar wanke mishi undies har ta gwada yi na rana daya sai ta kasa shanyawa kawai ta matsar da labulen dake wajen kwamin wanka ta shanyasu a karfensa.
Ranar Alhamis ta yi wannan aikin, yana dawowa ya ganewa idanunsa, ido ya fiddo yana kallo da mamaki, sun wanku tas, saidai anya Umminsa ce za ta yi? Ya kasa gaskatawa har ya gama wanka ya shirya cikin doguwar jallabiya fara ya nufo cikin gidan.
Hajiya na sashen mijinta, Ikram kuwa wacce ta dawo kenan, tana dakinta tana aikin makaranta. Wannan ya ba shi damar shigewa dakin Ummin. Sallamarsa ce ta sanya ta mikewa zaune da sauri gami da tura littafin kasan filo ta riko wayarta kamar ita take dannawa, ya dubeta sannan ya dubi hannunnata, ta yi kasa da kanta.
'Ya Allah, Ka bani ikon dauriya ga dukkan abinda Yaya Faruk zai zo min da shi.' Ta yi furucin a zuciyarta, a fili kuwa dan zamowa ta yi gami da mishi barka da zuwa, ya amsa sannan ya zauna gefenta, hannu yasa ya kar6i wayarta, ya gama bincikensa har open apps ya duba saidai ba abinda ta bude, ya ajiye wayar saman kafafunta yana dubanta fuskarsa cike da damuwa.
"Ki yi hakuri Ummina."
Ta dubeshi ido waje.
"Hakurin me?"
Ya lumshe ido ya bude.
"Na 6ata miki rai kwana biyunnan, na yi miki laifi, ki gafarceni."
Ta girgiza kai da sauri.
"Wallahi ni ce mai laifi Yaya Faruk, don Allah ka yi hakuri, in sha Allah na daina yi maki abinda ba ka so..."
Ta karashe a dan kunyace, ya yi murmushi wanda ya jima baiyi gareta ba gami da riko hannunta ya dan murza.
"Is ok, share wannan, ni yanzu dai ki gayamin, daman an iya wankin undies aka bar Faruk nata wahala?"
Ya fada a shagwa6ance, ji ta yi kamar ta nutse a wajen, ai fa kunyarnan sai a sannu zai saketa gaba daya. Ta hau sussunne kai tana murmushi, ya yi dariya yasa hannu ya karkato fuskarta gareshi, ganin haka ta lumshe idanunta batason su hada ido. Ya yi mata k'uru da nasa idanuwan. Can kuma ya numfasa ya sanyata jikinsa ya matse.
"Ummina idan addua ki ke min ki rage yinta, don idan Faruk ne kin gama mamaye zuciyarsa, please ki ragwanta kinji? Ina jin kamar zuciyata zata fashe da sonki."
Ta bude idanunta tana numfarfashi, tausayinsa ta ji, ta yi amannar cewa son da Faruk ke yi mata bai kai wanda ta ke mishi ba, kuma ba hakan na nufin ita din bata son nashi bane. Tana ji bata iya hanawa ba, tana gani bata iya ta kwa6a ba, haka sakonnin suka yita shigarta, duk inda ya biyo bata ko tureshi, har abin ya kai ga fin karfin tunaninsu, sai kuma don kansa ya kyaleta yana dubanta.
"Za ki tayani kwana yau? Tsoro nake ji."
Batasan sadda ta dan harareshi ba sannan ta kauda kai gami da dan turo baki, ji ta ke kamar ta nutse saidai batason 6ata ranshi, batason ya k'ara nisantarta. A kwana biyun nan ta wahala da shariyar da ya ke mata.
Ya hau gyara mata sutura yana fadin.
"Kinji? Please."
Shiru ta yi, kamar ta ture hannunshi don tasan ba a iya gyaran zai tsaya ba, ai kuwa ta ji ya sumbaci hannunta.
"Lallen nan naki ya burgeni Ummina, ki dunga yimin please."
Ta gyada kai kawai, sallamar Hajiya yasa ta ja baya da sauri gami da rufe kanta, shi kuwa baya ya ja kadan ya gyara zamansa sannan ya amsa. Hajiya jin muryarsa ta yi mamaki, hakan yasa ta fasa shigowa don kuwa wani hadin ne ta kawowa Ummin na mayuka masu gyara jiki don ance in kana da kyau ka k'ara da wanka.
Ganin ta maida kofar ta rufe bata ko shigo ba yasa Faruk duban Ummi yana murmushi mai bayyana hakora.
"Kinji Hajiyata fa?"
A rude ta ke kallonsa. Ta karya wuya.
"Don Allah Yaya Faruk ka tafi kada ta dauka wani..."
Sai kuma ta yi shiru don gudun 6ata ransa, ya dan ja jelar gashinta da ya lek'o.
"Kada ta dauka me? To naji zan fita, amma kirani da wani suna banason wannan."
"To Sadauki." Ta fada da sauri.
Ya yi 'yar dariya.
"Aa, wannan Hajiyata kadai ke fada."
Ta marairaice fuska can kuma ta ce.
"Yalla6ai."
Ya ta6e baki ya girgiza kai.
"Chanja."
Kamar zata yi kuka ta yi shiru can kuma ta dubeshi, ko ajikinsa asalima dariya ya ke mata.
"Um..um...toh Yaya Umar."
Dariya kawai ya yi ya mike gami da sumbatar le66anta sannan ya ce cikin rada.
"Ina sonki kamar na mutu." Daga haka ya juya ya fita, ta bishi da kallo tana murmushi har ya fice.
Daga ranar masoyan suka shirya....!!!
*** *** ***

        .          ***   ***    ***
   GYARA
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
    
107

Mutanen gidan hankulansu gaba daya ya tafi ga shirye-shiryensu,  Cikin sati guda Hajiya da Babban Yaya sun had'a kusan rabin lefe, abinda ya ragemusu kalilan ne, Hajiya ta kar6i size din Ummi na dukkan abinda zasu bukata. Acan kuwa Daddy ya fidda makudan kudi ya bada odar kayan daki, kayan kicin ma, Babban Yaya ne ya jagoranci had'awa don ya sanarmishi akwai wadanda suke hada kayan kicin na aure saidai kawai a biya kudaden. Ai kuwa a kwana biyar aka hada komai aka ajiyesu acan gidan Faruk din zuwa lokacin da jera zai zo. 
    Ummi duk batasan budurin da akeyi ba sai bayan Hajiya ta nemi size dinta, kullum sai ta yi waya da mahaifinta. 
  Husna tana iyakar kokarinta wajen koyamata abubuwan da bata gane ba. Har wata rana suna zaune ta dubeta.
"Wai ni kuwa Hasiya me zai hana Yaya Faruk ya sanyaki makarantar boko? Ko kuma ya daukar miki Malamin da zai koyardake ko a gida ne kafin zuwan ya sanyaki?"
  Ummi ta murmusa.
"Ya ce sai na tare zai daukarmin, don bakisan yanda ya ke son karatun ba wallahi, ni kaina ina mafarkin na ganni na yi, bani da burin da ya wuce na neman ilimi, yanzu kam Alhamdulillah ina fahimtar na Addini na sosai."
Husna ta gyada kai, in sha Allah za ki yi ilimi Hasiya, kina da kokarin daukar karatu wallahi abin har burgeni ya ke yi. Ina da wani bidiyo kusan kala uku na A B C D da wani na 1 2 3, Zeenat kanwata nake kunnawa ta kalla duk sadda ta dameni da na kunna mata(Game) gobe ki yi kokarin zuwa da wayarki sai na tura miki ta (Play store), na tabbatar shima zai amfaneki. Ki dage Hasiya, ilimi shine gata a wannan zamanin. Sannan tunda kina(whatsapp) zan sanyaki wani group na girke-girke, akwai ma wani na kwalliya, komai aikowa sukeyi har yanda ake d'aura dankwali amma shi sai an biya ake shiga, idan har ki ka maida hankali In sha Allahu za ki fi haka a wajen Yaya Faruk."
    Ummi ta ji dadi matuka, Husna iyayen gayu daman ba daga nan ba, tun haduwarta da Ummi ta ji jininta ya hadu da nata ainun, duk da ansha zugata akan ita din ba ajin kawancenta bace, don ba abinda suka sani game da Ummin saidai kuma sun rainata a hakan. 
    Batasan sadda ta rungume Husna ba don dadi, Husna na dariya ta kai mata duka.
"Malama za fa ki 6allani, kina son ragemin farashi."
Dariya sukayi. 
          Washegari ta zo da wayarta Husna ta dura mata bidiyoyi don har (data) ta kare ta yi connecting da hotspot dinta. Haka har games ta sanya mata na k'irge da A B C.
  Ummi fa an samu abinyi, daga neman haddar makaranta sai kuwa game da kallon bidiyo. Faruk ya yaba kwarai da wannan taimako da Husna ta yi mishi, har lambarta ya kar6a ya yi mata godiya. 
  Koda aka tashi tafiya Adamawa banda Ummi ciki don daga Hajiya da kannenta (Mami da Hajiya Mama) sai kuwa yaransu su dinma ba duka ba kasancewar ba lokaci ne na hutu ba, Ummi kuma alokacin ne zata wuce Gombe. Ta shirya komai nata sai d'oki ta ke yi, yau ma suna hanyarsu ta dawowa daga islamiyya inda suka yi bankwana da Husna da wasu cikin yan ajinsu, tana kokarin mayar da littafi jaka, ya fad'i gefen Ikram. 
  "Wayyo yi hakuri." Cewar Ummi sannan ta kai hannu ta dauka, idanun Ikram ya kai ga hoton da ya fado cikin littafin, gabanta ta ji ya yi mugun faduwa, na ganin wani kyakkyawan matashi sanye cikin farar shadda, duk da cewar bai yi wani yanayi na masu kudi ba saidai ya hadu babu k'arya, batasan lokacin da ta taimakawa Ummi da dauko hoton ba, ita Ummi kuwa sam hankalinta na ga littafin tana bud'ashi don duba ko hoton na nan, ta ji Ikram na mik'amata. Cikin dan yamutse fuska ta ce. "Waye wannan?"
   Ummi ta kar6a gami da dan dubanta, bata fahimci komai a yanayinta ba, hoton GIDADO ne da ya bata alokacin da zata baro Jar Kwami, yanzun ma Husna ta  dauko don ta nuna mata, harma da wasu na su Abu, murmushi ta danyi.
  "Dan uwana ne."
  Daga haka Ikram ba ta ce uffan ba, sai ma ta kauda kanta, ta kasa mance fuskar. 
'Na shiga uku ni Ikram, meke shirin faruwa?'

Post a Comment for "DAN ADAM CHAPTER 30"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...