DAN ADAM CHAPTER 28 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

DAN ADAM CHAPTER 28

DAN ADAM CHAPTER 28

- - Post a Comment
DAN ADAM CHAPTER 28 
A
Ta runtse ido gami da dan mak'e wuya kamar wacce ake shirin kaiwa mari, ba ta ce komai ba. Ya kasa rike dariyarsa saida ya dara kadan. "Ummina kenan, ki rikeshi na bar miki." Ta zaro ido kawai saita kashe wayar don kunya, ashe daman ya ganta? Ya k'ara kira bata daga ba, karshe ma ta kashe wayar. Washegari misalin takwas na safe, tana zaune tana shirin karyawa suna waya da Amina wacce ke labartamata cewar itama za su je Nijar dangin mahaifinsu su dawo, ta tayata murna a karshe ta sanarmata Faruk yana nan. Amina ta yi dariya kwarai. "Oh wannan soyayya ta ku? Kedai ki yi ta godiya ga Allah da wannan babbar kyautar." Murmushi kawai Ummi ta yi mai bayyana hakora. Sun sha hira sannan su ka yi sallama. Kwanan Faruk biyu ya soma shirin komawa bayan zuwan Malam Balarabe garin an zauna an tattauna inda ya yi musu bayanin karatun da Ummin ta soma a Abuja, sun ji dadi matuka saidai basu aminta da komawarta gidan surukai ba, haka dai ba don ya so ba ya hakura da raayinsa, yasan idan ya turo su Daddy to watakil su amince ta koma can. A zaure suka tsaya suna sallama, Faruk ya dubi Ummi gaba daya ji ya ke kamar ya zubda hawaye, ita kuwa kanta a k'asa, ya fiddo wayarsa ya kara daukarta hoto, sautin camera yasa ta fahimci abinda ya ke. Ta ja hijabinta tana fadin. "Kai Yaya Faruk na kusan goma kenan fa." "Ke an fadamiki ina gajiya da kallon hotunanki?" Murmushi kawai ta yi mai bayyana hakora kafin su yi sallama, a sanyaye ta mishi adduar isa lafiya suka yi sallama ran kowannensu cike da jin kewa. Saida Ummi ta yi sati biyu a Jar Kwami, kawarta ta islamiyya, Husna A Rashid har ta gaji da tambayar ranar dawowarta makaranta ganin lokaci ya ja bata dawo ba. A wannan sati biyun har Kwami ta je ta ga dangin kakarta wadanda wasu da yawa sun rasu, kwananta biyu ta dawo sannan ta wuce birnin Gombe gidan su mahaifinta. Kwanakinta uku da zuwa ta lura da sauyin da aka samu tsakanin mahaifinta da Dada don zuwa yanzun ta sake da shi ta nunamishi komai ya wuce abin ya bata mamaki ya kuma yi mata dadi don har hira sosai suna yi. Kamar yau juma'a da yamma, sun hadu gaba daya tsakar gida ana hira, wayar Malam ta yi kara. Ya saki fuska sosai ganin Malam Yahuza ne. Fadi ya ke. "Yau Yahuza ne ya tuna da ni?" Ya dauka da sallama, bayan gaishe-gaishe Malam Yahuza ya soma ba shi labarin bayan rabuwa, ya sanarmishi ya samu ya shirya da yan uwansa ya nemi gafararsu, ya gangara kan labarin da ya ba shi mamaki da al'ajabi har saida ya tashi ya bar wajen yana fadin. "Innalillahi." Suka bishi da kallo musamman Ummi da ta ji wata irin faduwar gaba don tsoronta ya kasance ko Habiba ce ta gudu daga gidan yari. Bayan ya gama wayar ne ya dawo, anan Haruna ke tambayarshi ko lafiya. Ya dubesu. "Diyar Malam Yahuza, Dije, 'yar Baba kin santa ko?" Ta gyada kai don hankalinta ya dan kwanta. "To itace mijin ya turowa mahaifinta takardar sakinta, aciki ya ke shaidawa mahaifin ya kamata tana mu'amala da yar uwarta mace, ya yi mata duka ya korota tun washegarin faruwar lamarin saidai an tabbatar mishi bata zo wannan yasa yanke turomishi takarda. Bayan haka kuma da kwana biyu labari ya riskeshi cewar an ganta can gidan wata Bokanya ta je tare da abokiyar shaidancinnata har an samu wasu sun k'ona gidan kurmus. Dakyar ita Dijen ta samu arcewa, fitarta kuma ta hau titi da zummar tsallakawa mota ta bi ta kanta." Kowa a wajen ya dauki salati. "Duniya abar tsoro, wannan masifa da me ta yi kama?" Cewar Baffa kenan, Dada ta ca6e. "Karshen duk wani mai aikata mummunan aiki kenan matukar bai tuba ba, Allah Ya karemu da al'ummar musulmi ga fadawa halaka irin wannan." Ummi girgiza kai kawai ta ke yi tana salati, lamarin mutane abin tsoro, wani abin kamar a mafarki, ba don na kusa da kai bane idan ka ji a wani wajen kana iya cewa ba gaskiya bane. "Allah Ka sa mu cika da imani." Cewar Malam Balarabe, suka amsa da amin. Washegari misalin karfe uku na rana, Ummi kwance a dakin Antinta Abida matar Baffa tana karanta wani littafi na Ahlari da ta taho da shi, ta tsinci muryar Baffa na tambayar Abida ta ba shi tabarma anyi bak'i daga Abuja. Batasan sadda ta mike tsaye ba tana lek'ensu ta windo. "Su waye?" Cewar Abida tana mai mik'amishi tabarmar. "Maneman auren Ummi." Ai batasan sadda ta dafe kirji ba gami da komawa saman kujera ta zauna. "Su Daddy ne?" Shine tambayar da ta jefi kanta da shi a fili. "Ina ki ke 'yar nema? Fito nan ki ji labari mai dadi." Cewar Abida tana kokarin shigowa dakin, a guje Ummi ta mike ta 6uya bayan labule tana dariya ciki-ciki. "Au 6uya ki ka yi? Kya ma fito, ai ni tun ganin da na yi wannan saurayin ya kasa hakuri ya biyoki har nan, nasan ba lallai ya iya hakurin barinki ba." Ta daga labulen da Ummi ke 6oye, ganin haka ta durkusa tana mai rufe fuskarta da hannu tana dariya. "Kai don Allah Anti." Abida ta dara. "Za ki san Anti, bari mu zo mu soma gyaraki yarinya." Daga haka ta saki labulen ta koma duba sanwarta. Ummi ta fito ta zauna da saman kujera tana dariya, karatun dai bai samu shiga ba. Gen. Ahmad Danzaki ne, sai kaninsa Alhaji Aminu Danzaki da babban Abokin Gen. Ahmad Danzaki, wato Major Yusuf Bashir mahaifi ga Sa'ad miji ga Baraka. Sai ko Babban Yaya wanda shi ne ya tuk'osu daga Abuja, bayan shigowarsu da tambaya suka iso unguwar sannan suka yi kiran Malam Balarabe kamar yanda suka tsara ya tura aka taho da su. Har la'asar, Ummi na mak'ale wajen Abida ta kasa fitowa. Tana cikin sallah ya shigo, tana ji suna magana k'asa-k'asa da Abida, sai kuma ta ji Abida ta soma bud'a wanda ya sa Ummi gabanta ya fadi adaidai lokacin da ta sallame. Furucin da Abida ta yi ne yasa ta durkuso a wajen tana salati....! "Alhamdulillah, Allah Shi ne abin godiya, amma ya akayi haka ta kasance?" Cewar Abida kenan. "Wallahi abu na Alllah, da kansu suka buk'aci hakan sai kuma Malam bai musa ba don a farko sun bukaci komawarta Abujan saboda karatun da ta soma amman bamu amince ba, sai suka yanke shawarar kan a daure auren kawai, to shine fa aka daura, tarewa kuma aka barshi nan da wata daya." Duk wannan bayanin da Baffa ke yi a kunnen Ummi, ta ji jikinta ya yi mugun sanyi, take ta ji ruwan hawaye na kwaranyo mata, wai shikenan ta zama MATAR AURE? Ta zama mata wajen Umarul-Faruk Danzaki? Allah mai Iko, yanzu komai za ta yi saida izninsa? Tana nan durkushe saman darduma tana hawaye, Abida ta shigo bayan fitar maigidanta. Ta rik'ota. "Haba Ummi, kukan menene? Godiya za ki yiwa Allah, wannan ikon naSa ne anzo da zummar a sanya rana aka daura aure gaba daya kinga kuwa babu mai yin hakan sai Allah." Haka ta ja ta har suka isa dakin Dada, nan sauran jama'ar gidan suka yi mata caa, ita kuwa jikin Dada ta shige tana kuka, kukan da batasan dalilinsa ba. Hakanan ba zata iya tantance yanayin da ta ke ciki ba, farin ciki ko akasinsa. Kiran da Malam ya aiko ayimata ne yasa ta dan nutsu. Har lokacin daman hijab dinne jikinta, tana tafe kanta a k'asa har ta shiga rumfar Malam inda anan su Daddy ke zaune, sun yi sallah sun ci abinci. Bata iya kallon kowa ba ta durkusa ta gaishesu, suka amsa. Daddy ya ce. "Ke kuma daga mun bawa Balarabe aronki shikenan sai ki mak'ale ki gujemana?" Ya karashe da dariya, su dinma dariyar su ka yi ita dai murmushin yak'e ta yi don har lokacin jikin ba dadi. Ta mike ta tafi bayan sun sallameta, a ranar su Daddy suka koma. Bayan tafiyarsu Malam ya kara kiranta. Zaune ta samesu su uku, da Baffanta Haruna sai Babanta da kuma Malam din. Malam ne ya soma magana. "To Hasiya, kinga dai yanda Allah Ya yi lamarinsa ko? To inaso ki yarda da hakan a matsayin kaddararSa, Allah Ya yi yau din ita ta kama ranar daurin aurenki ba baiko ba. Sadakinki dubu hamsin muka kar6a don neman albarka cikin aure. Yanda su ka ce, gobe litinin zasu turo direbansu idan yaso a wuce da ke can, sun buk'aci komawarki zuwa zuwa lokacin bikin ba don komai ba sai domin karatun da ki ka soma kada ayi miki nisa. Ina fatan ba za ki bamu kunua ba Hasiya?" Shiru ta yi cike da jin nauyi yayinda hawaye ya zubomata don babu abinda ya fado ranta sai matan su Babban Yaya da kuma Ikram da abokiyarta Ihsan wadanda a rayuwa basu kaunarta, a gefe kuma wane irin kallo Mami za ta yi gareta? Malam ya cigaba da nasiharsa, a karshe shima Baffa Haruna ya tofa nasa sannan ta suka sallameta ta koma ciki. Da Magriba tana kwance saman gadon Dada duk jiki babu kwari ta luluk'a cikin duniyar tunani wayarta ta yi k'ara wanda har saida ta firgita, salati ta yi sanya a hankali sannan ta janyo wayar, gabanta daman tuni ya ke bugu da sauri-sauri, ta sauke ajiyar zuciya ganin ba wanda ta zata bane. Ganin sunan Antinta Amina yasa ta dagawa da sallama. Dariya Amina ta yi bayan ta amsa tana mai rangad'a bud'a. Ummi ta runtse ido tana murmushi kawai. "Kai Ummi, wato maimakon ma ya kasance ni ce farkon ji shikenan saidai na ji a wajen su Hajiya Mama? Ba ki bugomin waya ba?" Ita dai Ummi shiru kawai ta yi mata, dariya Amina ta yi, ai nasan daman babu abinda za ki ce. To Ummi, Allah Ya sanya alheri, hakika na tayaki farinciki sosai. Nima gobe za mu wuce Nijar yanzu haka ma ina tare da Inna. Sai lokacin ta yi magana. "Allah Ya kaiku lafiya Anti, ban ita mu gaisa." Amina ta mik'awa Inna. Bayan sun gaisa Inna ta yi mata fatan alheri, murmushi kawai ta yi a kunyace ba tare da ta amsa ba, Inna ta dan yi mata nasiha kadan sannan ta mik'awa Amina wayar suka yi sallama. Ta ajiye wayar tana shirin komawa ta kwanta Dada ta shigo. "Wai ke ba zaki tashi haka ba ki sanya wani abu a cikinki?" Ta dan tur6une fuska. "Dada bana jin yunwa fa." Dada ta zauna gefenta tana murmushi. "Ina fa za ki ji? Farinciki ya cika miki ciki kinmin kwacen miji kin ji dadi ko?" Batasan sadda ta 6oye kanta a saman cinyar Dadan ba, kamar za ta yi kuka ta ce. "Kai don Allah Dada." Murmushi Dada ta yi gami da dafa kanta. "Allah Ya yi miki albarka Hasiya, Yasa ki gado mahaifiyarki wajen hakuri a zamantakewar aure duk kuwa a hakan ma na fahimci kema mao hakurin ce. Wannan aure, auren gata ne, bazan 6oyemiki ba, a dan zaman da yaronnan ya yi tare da mu na fahimci da yawa cikin kyawawan halayensa, kwarai yana sonki don banajin ko Abdullahi mahaifinki yana miki son da Umar ke yi miki. Ki yi biyayya ga dukkanin umarninsa, ki dage ainun ki bawa marar d'a kunya wajen neman ilimi Hasiya, wannan shine babban gatan da ki ka rasa a baya, kada ki sake ki yi wasa da ita. A kulkum ina k'ara ganin daraja da k'imar Hajiya Madina, wacce a labarin da ki ka bani itace farkon wacce ta soma yi miki gatan sanyaki neman ilimin addininki. Allah Ya sakamata da alheri, Ya jik'an Hasiya." Kuka ciki-ciki Ummi ke yi, da gaskiyar Dada, Mami ta taimaketa a rayuwa, babu abinda za ta iya yi ta biyata ita da Abba face addua. Haka Dada ta yi ta rarrashinta sannan ta mike ta shiga hadamata kaya bayan ta lalla6ata ta zubamata abinci. Anan Ummin ke jin ashe ba ita kadai za ta wuce ba, har da rakiyar Abida da mijinta Baffa wadanda zasu kawai don ganin waje bisa umarnin Malam. Ta ji dadin hakan. Karfe tara na dare, Anti Halima da Anti Abida suka sanyata tsakiya sunata yi mata nasiha. Ita dai ta kumbura ta yi fum don bata ga amfanin nasihar ba tunda ba tarewa za ta yi ba. "Yauwa, kuma karki sake ki zubda ajinki, karki ba shi fuskar da wani abu zai shiga tsakaninku, zai fi d'okin ki, wallahi ki kiyaye. Duk abinda zai je ya zo karki bari wannan kunuar taki ta yi saurin tafiya kinji ko? Idan ku ka yi hakuri wata daya kamar yau ne." Cewar Anti Halima kenan. 'Wayyo Allah.' Cewar Ummi a zuciyarta kafin ta yi soma kwalla, wadannan me su ka maidata ne? Ganin hakan yasa suka yi dariya don su ganin Ummi suke yi kamar kanwarsu ba diyarsu ba. Ta mike a guje ta bar musu saman tabarmar ta koma cikin daki wajen Dada. "Au ki ka gudu ko? Ai yanzu aka soma." Cewar Abida kenan cikin daga murya. Dada wacce har ta kwanta ta dubeta saidai ba ta ce komai ba. Kamar jira akeyi ta shigo dakin, wayarta ta soma k'ara, ita kam yanzu duk sadda ta ji k'arar wayar ma sai gabanta ya fadi. Adnan ne, ta ji kamar kada ta daga, shikenan fa labari ya zagaya ga kowa. Ta dan dubi Dada wacce idanunta ke rufe kafin ta d'aga da sallama. Bud'ar da ta ji ya yi ne, yasa ta dariyar da bata shiryamata ba ga kuma kunya da ta ji, yau kuma namiji ne da bud'a? Wannan abu lallai ya bata dariya. "Kai Yaya Adnan." Ta fada tana dan marairaice murya. Ya yi dariya. "Da girman kujerarki Antina Matar Best, tuba nake ranki ya dade nasan na yi lattin tayaki murna, abubuwan ne sai a hankali, sannan don Allah ki daina kirana da Yayan nan, yanzun ma kina fad'a kamar na nutse don kunya." Dariya ta k'ara yi tana mai sa hannu ta rufe fuskarta, ba zata iya rike dariyar ba, shi dai Adnan ba dai iya tsokana ba. Shima cikin dariyar ya ce. "Atoh, ai gaskiyane, yanzu idan My Best ya ji ai sai ya dauki fushi da ni. To Allah Ya sanya alheri, Ya nunamana ranar aurenku, abin dai zai min takaici don inaga watan zamu soma jarrabawa kinga ba lallai na zo ba." Ta gyada kai tamkar yana ganinta. "Allah Ya baku sa'a." "Amin, ina Amarena? Kakanninmu." Ba ta yi mamakin Adnan ba, daman ai Shi Allah babu ruwansa, idan Yaso sai ya yi daya mai kyakkyawan zuciya acikin dubu, to ballantana kuma suma su Ihsan din rashin fahimta ne yasa suke mata hakan. Tana dariya ta amsa da duk lafiya. Sun dan ta6a hira yana jifanta da tambayoyi akan Gombe tana amsawa a karshe suka yi sallama. Babu jimawa kuma ta ji wani kiran alokacin da ta ke kokarin kwanciya, shi ne dai wanda ta ke gujewa kirannasa. BABBAN GORO, UBAN GAYYA...!!! Ta zubawa wayar ido kamar ba zata amsa ba, sai faman safa da marwa numfashinta ke yi, har dai ta kusa yankewa sannan ta yi bismillah ta amsa. Shiru ba ta ce komai ba shima baice ba, can kuma ta ji ya sauke ajiyar zuciya ya yi sallama cikin sanyin murya. Ta amsa itama kamar wacce aka shak'ewa wuya don dakyar muryar ta fita. "Kema hawayen ki ke yi kamar ni?" Ya fada a shagwa6ance, ta rufe bakinta da hannu don dariyar da ta so su6uce mata. Ya cigaba da magana. "Dagaske nake fa, wannan idan zan rabu da Hajiyata sai yaya? Kawai kina shirin rabani da gidanmu ko? Dazunnan Haidar ya gama yimin dariyar mugunta ya tafi." Ta hadiye dariyarta ta maidashi murmushi mai bayyana hakora. "Um." Shine kawai abinda ta ce sa'ilin da ta saci kallon Dada, minsharin da ta ji ne ya tabbatar mata cewar yanzun ta yi nisa da bacci. "Tashi Ummi, tashi mu yi salla mu mik'a godiyarmu ga Allah, zan k'ara kira karki kashe wayar kinji?" Ta gyada kai kawai, saida ya kara maimatawa. "Kinji?" Alokacin ta amsa da to, bai jira cewarta ba ya katse kiran. Ta bi wayar da kallo tana murmushi, soyayarsa na k'ara ratsa dukkan sassan jikinta, fita ta yi, babu kowa a tsakar gidan duk an shiga makwanci, alwala ta dora bayan ta kama ruwa sannan ta koma dakin ta tada sallah, ta jima tana adduo'i har da hawayenta kafin ta shafa ta mike. Mintuna biyar bayan haka, har ta fidda ran zai kira don lokacin sha daya ta kusa sai ga kirannasa. Ta daga da sallama, ya amsa kafin ya tambaya ko ta yi? Ta amsa da eh. "Alhamdulillah." Ya maimaita sau uku sannan ya cigaba da fadin. "Matata." Ta ji sunan har cikin jini da jikinta, ta lumshe ido tana murmushi ga kirjintata dake lugude da sauri-sauri, saidai ta kasa amsawa, ganin abin ta ke yi tamkar a mafarki. "Matata Hasiya, ko ba ita bace? Kina jin mijinki na kira ki ka yi shiru ko?" Ya karashe a shagwa6ance, ai daman tasan ko wata macen ba fa zata nunawa Faruk shagwa6a ba, don ko ita ba zata iya yanda ya ke yi ba. "Um." Ta fada kanta na k'asa tana wasa da kasan t-shirt din dake jikinta na bacci. "Kin zama matata yau, shikenan na girma, haka Hajiya ta ce." Har lokacin murmushin ne dai ta yi. "Gobe za ki zo gareni Hasiya, ina fatan kin shirya tarbata?" Ta zaro ido a tsorace. "Kamar ya?" "Au ba ki sani ba? Shikenan sai kinzo din." Ta tsorata, ta tunano maganganun su Anti Halima, ya zama dole ta yi takatsantsan don kuwa dagaske ba fa za ta bari ajinnata ya zube ba. Ya cigaba da janta da hira, hirar da ba zata iya dauka ba, ganin dai dagaske ba zata bude baki ta ce wani abin ba yasa shi yi mata sallamar dole ba don yaso ba. Daga nan suka kwanta kowanne zuciyarsa cike da begen dan uwansa....! Washegari...!!! Bayan Ummi ta kammala karyawa, ko mikewa daga wajen ba ta yi ba, Dada ta mik'omata wani abu a kofi, ta dubi kofin, tasan daman tun zuwanta tana bata nonon saniya tana sha, saidai wannan karon wani abu ta gani cikinsa mai kama da lalle, ta dago kai tana dan yamutse fuska ta dubeta. "Menene wannan Dada?" "Kar6i ki shanye sai na gayamaki." Ba musu ta kar6a ta shanye tas gami da saurin korawa da ruwa don dacin bakinta ya kau. Murmushi Dada ta yi sannan ta mik'amata wani kullin itatuwa a farar leda. Ummi ta kar6a tana dubanta. "Maganin sanyi ne, da zarar kin dawo kafin biki, za ki dunga sha kina tsarki da shi, mahadinshi jar kanwa, wannan da ki ke gani ba'a wasa da shi, sakacin iyayenku kenan, sai a yita dabkawa mata kayan gyara amma ba a basu maganin sanyi. Sai ki ga bayan aure anzo anata faman zaryar zuwa asibiti." Ita dai Ummi a kunyace ta ajiye ledar a gefe, Dada ta dauka tana cigaba da fadin. "Ki dage wajen kula da jikinki, ko yanzu ai ke kanki kin ji chanji ba kamar yanda ki ka zo garinnan ba." Ummi ta yi shiru, kwarai kuwa da gaskiyar Dada, don kuwa tun zuwanta kullum da abinda za ta bata ta sha, daga ta ce maganin basir sai kuwa na ciwon jiki. Ita dai hakanan ta ke sha batare da tasan wani abu na maganin ba. Misalin bakwai na safe, Faruk ya yi mata text ya shaidamata tahowar direban tun biyar na Asuba, alokacin tana zaune Dada ta kira wata makwafciyarsu tana tsantsara mata kananun kitso, ga kunshi ana yi mata. Sun kwashi awanni uku suna yi kafin a kammala kitson, sannan ta wanke lallen, kowa ya ga kitson da kafarta sai ya tanka, wannan yasa ta rufe gashinta mai laushi da bak'i. Kafar kuwa ta makamishi safa. Ta yi wanka ta hade cikin wata doguwar rigar abaya mai ru6i biyu, bak'i da ruwan k'asa, wanda ya fiddo (shape) dinta, daga gefen hannuwan kuma sai aka yi shi mai fadi kamar buba. Ta yane kanta da mayafinsa. Wajen karfe goma sha biyu da mintuna, Babanta ya kirawota, ya yi mata nasiha sosai akan ta kula ta kuma bi mijinta sau da k'afa a karshe ya sallameta bayan ya sanarmata cewa an damk'awa Dada sadakinta zata bata, nauyi ya hana Ummi cewa komai ta tashi ta wuce. Shigarta ciki babu jimawa ta ji yaran gidan na ihun mota ta zo. Gabanta ta ji ya soma bugu, haka kawai ta ji kamar za ta kara yin nesa da yan uwanta. "To Hasiya, tashi ki yi sallah za ku kama hanya. Shiru ta yi domin yau da asuba jini yazo mata. Shirunta ya fahimtar da Dada, kawai sai wuce ta dauki jakar kayanta ta mikawa Aliyu d'a na biyu wajen Baffa Haruna wanda baifi sa'an Adnan ba. Ummi ta soma sharar hawaye, tana nan zaune har zuwa lokacin da aka ce ta fito su wuce. Nan ta rike Dada tana hawaye, Dada dakyar ta iya daurewa ta cireta daga jikinta. "To mene na kukan kuma? Kiyi hakuri kinji, ai ba'a rabu ba. Rike wannan, sadakinki ne." Ta girgiza kai. "Ki yimin abinda ki ka ga ya dace." Daga haka ta zira takalminta mai tudu ta janyo jakarta bak'a wacce da ita ta zo sannan ta fito Dada na rike da ita. Haka dai da kuka Ummi ta rabu da gidannan, mahaifinta shi kansa saida ya ji kamar ya yi kukan, Baffa na gaba ita da Abida suna baya. Wayar direban ta yi kara, nan ya ke sanarwa da mai kiran cewa sun taho, ya yi musu adduar isowa lafiya sannan sukayi sallama. Ya dubi Baffa yana dan dariya. "Yalla6ai ne." Baffa ya yi murmushi kawai. Direban kuwa dan surutu, sai ya hadu da Baffa shima ba kanwar lasa ba, tun Ummi na jinsu har ta yi matashi da cinyar Abida bacci mai nauyi ya dauketa. Basu suka isa Abuja ba sai karfe bakwai da wasu mintuna, shima don sun yi tsaye-tsaye ne yin sallah da sauransu. Tunda aka shigi garin Abuja Ummi ta ji kamar ta ruga aguje ta koma Gombe, da wane ido zata kalli Hajiya? Wai shikenan fa itama ta zama suruka a gidan. Bayan isarsu kofar gidan, ya yi hon, da sauri Maigadi ya budemusu suka shiga yana dagamusu hannu. Ta rike hannun Abida. Abida wacce ta suma a kallon gida, ta dubeta, ganin yanda duk ta firgice yasa ta fadin. "Ki yi ta addua." Sai lokacin ta tuna ta shiga yi, a harabar gidan babu kowa har zuwa lokacin da suka fito sai lokacin kuma suka Gen. Ahmad ya shigo dawowarsa kenan daga masallaci, a bayansa kuwa Haidar Danzaki ne sai ko Faruk Danzaki. Ummi sai sunne kanta ta ke yi, Baffa ya karasa ya mikawa Daddy hannu suka yi musabaha, yana tambayar yanda suka iso. Su Ummi suka russuna suka gaishesu, sannan suka shiga ciki. Faruk ya tsunduma a kallonta baya ko kifta idanu, saida Haidar ya dan mintsileshi a kafada sannan ya dafa wajen yana 'yar kara kadan. Dariya suka yi. "Control yourself mana." Murmushi kawai ya yi kafin ya russuna yana gaida Baffa, sannan sukayi ciki. Da Binta Ummi ta soma karo, suka rungume juna suna murna, harda hawayenta don Ummi kam akwai arhar kuka. Binta ta dubeta. "Kinga yanda ki ka koma kuwa? Ranki ya dade." Dariya sukayi, lokacin da ta share hawayenta. Saukowar Hajiya daga sama ne yasa ta sunkuyar da kai a kunyace. Hajiya wacce ta kasa 6oye farincikinta ta karaso tana duban Abida. "Sannunku da zuwa, diyata kunya ta shiga tsakaninmu kuma?" Ta karashe tana mai rikota, dariya Abida da Binta sukayi. Ta ja su zuwa sama, dakin Ummi suka sauka, saida sukayi wanka suka chanja kaya sannan Abida dake zaune saman darduma ta idar da sallah ta dubeta. "Kai Ummi ki godewa Allah, na tayaki murna wallahi. Irin wannan karramakin da su ke yi? Ga uwa uba kuma suna da arziki? Kinyi sa'a sosai, sai naga ma haduwar gidan ta zarce yanda nake kissimawa." Murmushi kawai Ummi ke yi lokacin da ta ke kokarin jona matacciyar wayarta a chaji. Tana sanye da doguwar riga(cotton) wacce da kadan ta wuce gwuiwa tana da botila a gaban rigar mai dogon hannu sai ta dora zani akai. Kanta rufe da hula, aka kwankwasa kofar da sallama, suka amsa sannan Binta ta shigo. Suka kara gaisawa da Abida kafin ta fadi sakon Hajiya na su fito su ci abinci. Kamar ta tambayi Binta ina Ikram, sai kawai ta share. Ta yafa mayafi suka fita itama Abida da lullu6inta. A saman katuwar ledar cin abinci aka jera komai, Hajiya Babba ta yi musu bismillah, Ummi da kanta ta zuzzubamusu a ranta ta ji sanyin rashin ganin Faruk awajen don kunya ta ke ji. Bayan sun kammala ta tattara, Hajiya na fadin ta barshi saidai bata saurara ba, ta yi k'asa, Abida ke fadin. "To Hajiya ai an zama daya." Saukarta yasa ta gwammace bata sauko din ba don kuwa Haidar ne da gogan zaune suna cin abinci. Dole ba yanda ta iya ta karasa saukowa, ta dan durkusa ta gaida Haidar, ya amsa fuska a sake. "Sannu Amarya ya hanya?" Ta kasa dubansu, ciki-ciki ta amsa da Alhamdulillah. Faruk ya bi le66anta da kallo don kuwa maganar bata fito sosai ba, murmushi ya yi sannan ya kauda kansa ya cigaba da cin abincinsa hankali kwance. Ta mike ta karasa kicin, suka fito tare da Binta suka koma sama, nan suka iske Hajiya Babba da Abida suna ta hira, suka tattara suka koma kasa. A kicin dinne Ummi ta samu danar tambayar Binta dake faman binta da kallo. "Wai ina Ikram?" Dariya Binta ta yi. "Wallahi tana dawowa daga makaranta ta hada jaka ta gudu gidan Yaya Haidar, saidai fakewa ta yi da cewa zata taimakawa Intisar da ayyuka tunda cikinta ya soma tsufa, har shi Yaya Haidar din ke cewa ta barshi tunda ba tun yau ba yaso zuwannata ta k'i. Yanzu dai ta tafi can, nasan kuma karya ta ke yi wallahi saboda bakin cikin za ki zo matsayin matar Yalla6ai ne." Murmushi mai ciwo Ummi ta yi, tasan daman da wuya Ikram ta chanja. Saida ta lek'a ta ga sun bar falon sannan ta fito daga kicin ta haye sama. Babu kowa a falon wannan karon, Hajiya Babba ta yi wurin mijinta, Abida kuwa ta shiga daki, tana shirin murda kofa ta shige daki ta ji sallamar Faruk a bayanta. A rude ta juyo ta tabbatar shi dinne. Ya zubamata idanu yana sanye da riga da wando fari da ja. "Waalaikumussalam." Ta amsa a hankali. Ya karaso daf da ita gami da sanya hannu ya dago ha6anta. "Ki sameni wajen pool...please." Ya karashe a tausashe. Ta gyada kai cikin rawar jiki, ya saketa sannan ya juya ya fice, ta bishi da kallo. Bata koma ciki ba sai kawai ta bi bayansa jiki ba kwari. Haidar ya wuce, ta gama waige-waigenta kamar mara gaskiya kafin ta murda kofar ta shiga. Kofar na waje baya ganin na ciki saidai na ciki ya ga na waje. Yana zaune yana duban ruwan, shigowarta yasa shi dago kai yana dubanta. Ta yi kasa da kanta tana mai kara gyara zaman mayafinta. Tana kokarin zama a kujerar gefensa ya janyota ta fada saman kafafunsa ba da niyya ba. Ji ta yi gaba daya ta rude, ta shiga kokarin mikewa saidai ya tare dukkan hanya. Take kuka ya tahomata. "Don Allah ka yi hakuri." Ya lumshe ido yana shak'ar kamshin turarenta. Ganin haka ta fisge da karfi ta mike gami da ja baya. Jingina kansa ya yi jikin kujera yana dubanta fuska dauke da murmushi. "Come to me please Ummi." Ko gezau ba ta yi, come dai ai ko dan kauyen yau da gobe zai san me kalmar ke nufi. "Ka yi hakuri ka kyaleni na tafi." Har lokacin bai motsa ba, saida ya kusan mintuna biyu yana dubanta sannan ya janyo kujera ya nunamata. "Zo ki zauna." Saida ta tabbatar dagaske ya ke sannan ta karasa ta zauna. "Kun iso lafiya?" Kai ta gyada don har lokacin cike ta ke da fargaba. "Idan ba ki yi magana ba zan sanyaki yin ta dole fa." "Alhamdulillah." Ta fada da sauri har muryar na hardewa, abin yaso ba shi dariya. "Na so mu yi hira saidai na lura kamar kina tare da gajiya ko? Tafi ki kwanta, saidai Antinmu na tafiya za ki had'a kayanki ki komo dakina." Ta zaro ido tana dubansa, shi kuwa ya hade fuska kamar gaske. Kawai sai ta sunkuyar da kanta ta soma hawaye. Karamin tsaki ya ja ya durkusa gabanta. "Why? Komai kuka awajenki ko Ummina?" Ya fada a sanyaye, bata ankara ba ta ji ya soma lashe hawayen, ta soma girgiza kai kafin ta yi yunkurin tureshi tana fadin. "Don Allah Yaya Faruk..." Yasa hannu akan le66anta kafin ya girgiza mata kai. "Karki hanani please. Idan bakyaso ki daina kuka. Bakisan suna da tsada wurina ba?" Ya karashe da murmushi saman fuskarsa. Sannan ya mike yana dubanta. "Tashi na rakaki." Ta mike da sauri don daman abinda ta ke zuci-zucin ta ji kenan. Saida suka kai kofa ya riko kugunta ya kai bakinsa daf da kunnenta. "I LOVE YOU." Ta lumshe ido, abinda tunda suke bai ta6a furtamata kenan ba, jikinta ya dauki rawa, zata murda kofar, ya kai hannunsa kan nata suka murda tare. Da sauri ta fice. "Hey!" Ya fada yanda yasan za ta ji, ta tsaya cak batare da ta juyo ba. "Ba ki ban amsa ba." Da sauri ta cigaba da tafiya har da gudu-gudunta. Ya bita da kallo yana murmushi sannan ya juya ya nufi samansa yana dan rera waka cike da nishadi.

Post a Comment for "DAN ADAM CHAPTER 28"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...