DAN ADAM CHAPTER 24 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

DAN ADAM CHAPTER 24

DAN ADAM CHAPTER 24

- - Post a Comment
DAN ADAM CHAPTER 24

  aramar tafiya. Modibbo ya yi ta jan Ummi da wasa yana kiranta da amaryarsa. Ita kam kanta na kasa kawai tana dan murmushi har suka gama shiga mota. A mota wannan karon ita da su Amal suka zauna don har rige-rigen zama kusa da ita suke, shi kam Ma'aruf har lokacin bai sake da ita ba ya rike abinda Mominsa ta ce masa akanta. Itama ta maida hankalinta ga yaran, duk a takure ta ke don duk dagowar da zata yi sukan hada ido da Faruk wanda ya saita madubi yanda zai dunga ganinta har Haidar na mishi dariya. Ita kuwa damuwa ta yi jin yanda ya ke atishawa, tabbas mura ta kamashi. Garin ya danyi duhu, sunyi nisa aka soma yayyafi kafin kuma a soma ruwan ba mai karfi sosai ba, duk aka daga gilasai, abokan hirar nata duk sunyi bacci, wayarta ta yi karar shigowar sako, ta duba duk a nata zaton kamfani ne saidai Faruk dinne. "Ko na dawo nan?" Ta dan dago suka hada ido cikin madubi, ya narkar da ido, da hanzari ta kauda kanta. Shi Faruk bai kunyar ma a dagosu? Bata kara kallon madubin ba, shi dinma murmushi ya yi kafin ya soma lumshe ido maganin mura na son sakashi bacci, can kuwa ya shimfida hankicif saman fuskarsa bacci ya yi awon gaba da shi. Itama tun tana kalle-kalle har nata baccin ya iso. Haka dai har suka isa garin Abuja inda suka tarar ana ruwa kamar da bakin kwarya. Koda suka isa gidan Dakta ne ya yi amfani da lemar bayan motar ta kai yaran ciki, su Ikram kuwa iyayen son ruwa haka aka shiga a guje. Ummi duk hankalinta na ga Faruk wanda ta ga yana shirin shiga ruwan shima, tana son ta haneshi saidai da kunya ainun, to ta ce masa me? Wata lemar Ikram ta daukomusu a ciki Binta na bin bayanta da guda uku, Hajiya ta shige tare da su Jidda, itama Binta ta mikamata tana dariyar murnar ganinta. Ta kar6a gami da fitowa. "Ni fa?" Ya fada yana dubanta da dan daga murya don karar ruwa. Binta ta dubeshi, Haidar ne kadai ke wajen yana bada umarni ga maaikatan masu shirin kwasar kaya cewa abar kayan har ruwa ya tsagaita. Sai kawai ta mikawa Binta lemar da sauri gudu-gudu ta yi ciki rike da takalman su Amal wanda suka cire a mota. Faruk ya na murmushi ya kar6i lemar daga hannun Binta, itama ciki ta yi cike da shaawar yanda suke tafiyar da soyayyarsu. Kai tsaye itama falon ta shiga. "Aa, garin yaya kika shige? Kema biyewa Ikram ki ka yi kenan, maza tafi ki chanja kayannan." Fadin Hajiya Babba kenan, ta ajiye takalman kafin ta nufi sama. Babu k'ura ko kadan a gidan don su Binta sun gyara tsaf, Binta ce ta gyara kuryar Hajiya. Ita dai ta yi mamakin ganin dakinta tas, ta jinjina kai, tasan aikin su Binta ne, wai kenan har ita keda wannan matsayin. Yana zaune yana shan(coffee) alokaci guda kuma ya lula duniyar tunani har Alhaji Kabir na mishi magana sam bai ji ba. Ya dan ta6o shi. "Abubakar." Ya dan dubeshi sannan ya sauke ajiyar zuciya. "Naam Baffa." "Tunanin me ka ke yi ne har ina magana ba ka ji ba? Me kuma ya faru? Ko akwai wata matsala?" Ya girgiza kai. "Aa, saidai Baffa jiya naga wata yarinya mai kama da Inno sak, na yi mamaki." Alhaji Kabir ya dan yi shiru kafin kuma cikin rashin fahimta ya ce. "Ikon Allah, watakil kawai kamanni ne. Kasan ana samun haka sosai." Abubakar ya girgiza kai. "Wannan kamar har ta so ta 6aci, ba don sanin da na yi cewar Inno bata raye ba da sai na ce itace, anya wannan itama ba daga Gombe ta fito ba?" Shi dai Alhaji Kabir abin mamaki kawai ya ke ba shi, wacece wannan da har ya ke had'ata da danginsu na Gombe? Har suka bar Kano Abubakar bai kara sanyata a idanu ba wanda ba haka yaso ba. Yaso ko hotonta ne ya daukarwa mahaifinnasa ya ganta. *** *** *** A satin Ummi ta soma zuwa islamiyya yare da Ikram duk kuwa da cewar Ikram din bata so hakan ba, saidai dadinta daya, ita tana aji na karshe na yan hadda ita kuwa Ummi aji biyu aka sanyata. Ta hadu da wata daliba mai kokari, Husna, wacce a kwana biyu kacal jininsu ya hadu da ita. Ita din diyar wani mai kudi ce don kuwa makarantar ta masu da shi ce, wayayyiya ce amma ba irin wayewar nan ta banza ba. Har musayar lambar waya sukayi. Ranar juma'a Yaha ta dira a Abuja, Hajiya Babba har tasha ta sanya direba ya daukota. Wannan ne zuwanta na farko gidan Hajiya Babba, lallai Mami ba cikin gida take ba, ga inda gida ya ke. Bayan gama cin abincinta ta shiga dakin Ummi inda anan ne zata kwana. Yaha baki ta saki tana mai karewa ko'ina kallo har sadda Ummi ta shigo dakin ta ajiye mata robar ruwa a gefen gado. Ta bi Ummin da kallo. "Ummi, wannan dukiya har haka?" Ummi murmushi kawai ta yi ba tare da ta san abin cewa ba. "Kinsan fa ban sanar da Saude batun zuwanki ba don kuwa sam bata kaunar ki je." Tasan hakan daman ba wani sabon abu bane, matar da ta yi mata mummunan rik'o ina za ta amince da k'ara sanyata a ido? "Ina Minna ta kirani ta jaddada min cewar kada na yarda ki je Ringim, acewarta ko nawa nake so zata dunga bani cikin albashinki, ita dai fatanta kada ta budi ido ta ganki a Ringim, ta ce na yi mata wannan taimakon har zuwa sadda wani buri nata a kanki zai cika." Gaban Ummi ya fad'i, wannan tsana har haka? Yanzu ko me zuwan nata zai haifar? Ta sauke ajiyar zuciya cike da damuwa. "Idan ma wani mugun abun ne ki kwantar da hankalinki, Allah zai kareki." *** *** *** RINGIM "Wayyo Allah!!" Ta yi furucin da karfi tana mai mikewa zaune a firgice. Malam Balarabe ya tashi a tsorace yana duban Saude. Sai uban gumi ta ke had'awa duk kuwa da cewar garin ya danyi sanyi. "Lafiya Saude?" Ya tambaya cike da fargaba. Saude dake dafe da kirjinta tana numfarfashi, ta dubeshi, sai lokacin ta dawo hayyacinta. Ta yi tsai da ido tana dubansa domin kuwa tsoro ya ke bata, gani ta ke yi kamar mafarkinta gaskiya ne, wai Malam Balarabe ne da daukarta ya jefa a rijiya bayan ya bata kyakkyawan mari har biyu a gefensa kuwa Hasiya kishiyarta ce tsaye tana faman kyakyatar dariya. "Addua ya kamata ki dunga yi idan kinyi mafarki ba wai ihu ba. Duk kin tsorata ni." Daga haka ya ja guntun tsaki ya juyamata baya, ta bishi da kallo cikin zubda ruwan hawaye sannan itama ta kwanta rigingine tana goge fuska. 'Meke shirin faruwa? Kada fa asirinmu ya tonu.' Ta ke maganar a zuciyarta, ta kudurta komawa wajen Bokanya gobe don ta k'ara bincika mata lamarin. Dakyar ta samu ta koma bacci a wannan daren. *** *** *** ABUJA Mutan Abuja da karfe biyu suka kama hanyar Ringim, wannan zuwa na musamman ne, Hajiya da Gen. Ahmad ne sai ko Babban Yaya da Ridwan sai kuma uban gayyar Faruk da Ummi da Yaha wacce suna shigowa Ringim ta soma rarraba ido na son nuna inda za su sha kwana. Haidar kadai ne bai samu zuwa ba. Ummi gabanta sai bugu ya ke da sauri-sauri, ga mararta da ta k'ulle, tana cike da tsoron irin cin kashin da za'a yiwa bayin Allahn da suka san daraja ta dan Adam. Wane irin tarba zata samu daga mahaifinnata? Sam, bata da masaniya. Hajiya Babba ta lura da yanayin da ta shiga, ta ji ta bata tausayi don kuwa ta ji daga bakin Yaha irin wahalar da ta sha a hannun ubannata da matarsa, ta dan dafa hannunta, wannan yasa Ummin dubanta. Murmushi na karfafa gwuiwa ta sakarmata. "Ki kwantar da hankalinki Ummi, ki yi ta addu'a, babu abinda yafi karfin Ubangijinmu." Ta jinjina kai tana dan murmushi. Daga haka ta cigaba da addu'o'inta har Yaha ta nuna layin da zasu shiga.+ Saude ce tsaye rik'e da k'ugu tana faman jan tsaki, a zaune saman kujerar falon, Habiba ce tana faman kai lomar dan wake. Mariya na waje suna wasa da yara. "Ki yiwa Allah ki taso mu wuce, wai menene haka?" Habiba ta dauki dunkulen dan wake guda ta jefa a bakinta tana mai dubanta cikin yanayi na santi. "Ai kwarankwatsa sai na gama, wa ya ce ki yi dan wake alhalin kinsan bana ganinsa na kyale balle kuma da yanzun ma babu abinda na saka a cikina, na fadamiki fa daga kasuwa na fito." Ta k'ara sud'e man wanda ya hade da yaji sannan ta cigaba da magana. "Na fadamiki ki saka ranki a inuwa, ko makamancin tunaninki bazai afku ba, idan yar banza ta takura mana sai ma mu saka Yaha ta maido diyarta ta mu kasheta mu kashe banza." Saude wacce ta gaji da tsayuwa ta zauna sai lokacin ta dan numfasa. "Anya hakan ma bai fi ba?" Kafin Habiba ta samu abin cewa, sallamar Malam Balarabe ta karad'e kunnuwansu. Suka dubi juna da mamaki kafin kuma Saude ta yi wuf ta fito. Ya ajiye ledar hannunsa a gefe. "Malam lafiya yau ka dawo da wuri?" Ya dauki buta jikinsa duk a sanyaye ya nufi hanyar bandaki yana fadin. "Ina zuwa." Ganin yanda ya ke magana a sanyaye ya kad'a yan hanjin cikinta duk kuwa da cewa tasan halittarsa can daman ba mai zafi bane, idan har kaga bacin ransa to ba karamin kai shi bango ka yi ba. Habiba ta fito rike da kwanon dan wake a hannunta, cikin muryar rad'a ta ce. "To bari na koma na cigaba da bawa cikina hakkinsa kafin nan kun kammala." Ta karashe da dariyar shakiyanci Saude na harararta. "Malama yanzu zan shigo." Ita dai Habiba ta sa kai ta fice. Bayan fitowar Malam Balarabe ya ja kujera yar tsugunno ya zauna gami da zabga uban tagumi. Cikin fargaba ta ce. "Wai menene? Ko babu kasuwar balangun ne yau naga ko rana bata ida faduwa ba ka taho." Ya numfasa. "Haruna(yaronsa) na bari a can na taho, jikin nawa duk babu dadi, haka kawai na tsinci kaina da jin wani sanyin jiki, fatana Allah Yasa alheri ne." Saude ta yi tsuru da idanu, yau kuma meke shirin faruwa? Shigowar Mariya a guje ne ya katse tunanin kowannensu. "Umma! Umma!!" Suka maida hankali gareta jin yanda ta ke ihun kira, babu wanda gabansa bai fad'i ba acikinsu. Malam Balarabe ne ya riko hannunta. "Menene 'yar Baba?" Tana haki tana nuna kofar waje da yatsa, bakinta a washe ta ke fadin. "Wasu ne suka zo da katuwar mota suna..." Kafin ta karasa magana suka tsinci sallama mutane, Yaha ce a gaba Hajiya Babba na biye da ita. Saude ta zaro ido. "Yaha?" Malam Balarabe ya mike yana mai amsa sallamarsu yana dubansu duban rashin sani don daidai da Yahar bai rike kamanninta ba. Kafin kuma wani cikinsu ya kara cewa komai, Ummi itama ta sanyo kai da sallamarta wanda dakyar ta iya daurewa ta yi shi don a matukar tsorace take. Ganinta yasa Malam Balarabe zaro ido ya nunota da yatsa. "Ha...ha..si..daman ba ki mutu ba?!" Kawai sai ya zube anan, ihu da salatin Ummi ne ya ankarar da Saude cewa lallai yau ABINDA AKE GUDU ya afku! Ta kasa koda kwakkwarar motsi tana ganin Ummi ta yi kanshi tana jijjigawa. Faruk da suke waje, yana jin ihun Ummi baisan sadda ya sanya kai cikin gidan ba su Babban Yaya na biye da shi. Hajiya Babba ta hangi buta, da sauri ta nufi butar ta dauko, Faruk ne cikin zafin nama ya kar6a ya soma yayyafa mishi, aka ci sa'a ya farfado. Saude jikinta sai kadawa ya ke yi tamkar mazari, ana haka itama Habiba ta shigo don kuwa ta ji hayaniya saidai bata gask'ata ba hakan yasa ta zo ganewa idanunta. Wata budurwa ta gani sanye da tsadaddun kaya durkushe tana kuka sai mazan dake tsaye a wajen. Malam Balarabe aka kamashi ya zauna gami da jingina da bango. "Sannu Baba." Cewar su Babban Yaya, bai amsa ba sai binsu da ya ke yi da kallo kafin ya sauke idanunsa akan Ummi, da sauri ya runtse ido ya soma salati. Duk sai ya basu mamaki, babu kamar Ummi, mamakinta bai wuce na ganin wai mahaifinta ke tsoranta ba. "Wai Malam lafiya?" Saude ta yi maganar cikin rawar murya tana mai fatan ace Malam Balarabe ya koresu daga gidan matsayin ya ga fatalwa matarsa. Ya nuna Ummi. "Wai Hasiya ce dai ta dawo? Daman ba ta mutu ba?" Tambayar da ya yi ne yasa hankalin su ya dan kwanta banda na Saude da Habiba wacce jin hakan yasa ta sulale ta koma gidanta, bata yi wata-wata ba ta dauki mayafi sai gidan Bokanya har jikinta na rawa tsabar firgici. Acan kuwa, Yaha ta amsawa Malam. "Aa Malam, wannan Hasiyar Ummi ce diyarka diyar marigayiya." Ya kurawa Ummi idanu kamar yau ya soma ganinta, Ummi! Ummi!! Shi kuwa ina ta shiga kwana biyu ba ya ganinta?

Post a Comment for "DAN ADAM CHAPTER 24"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...