DAN ADAM CHAPTER 23 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

DAN ADAM CHAPTER 23

DAN ADAM CHAPTER 23

- - Post a Comment
DAN ADAM CHAPTER 23

  Washegari da misalin karfe sha biyu na rana, Hajiya Mama da iyalanta suka dira a gidan Modibbo. Ummi tun gaishesu da ta yi ta sauko. Ido hudu sukayi da Antinta Amina dake tsaye a kofar kicin suna gaisawa da Larai. Da sauri Amina ta juya ta fita, itama Ummi cikin saurin ta karasa sauka daga bene ta fita, tsaye ta ganta a baranda ta sunkuyar da kai. Cikin sanyin jiki ta karasa gareta ta dafa kafadarta fuskarta dauke da matsanancin farinciki. "Anti." Koda Amina ta dubeta ta razana da ganin hawayen dake saman fuskarta. Hankalinta ya tashi. "Anti ki yi hakuri don Allah, ban.." "Meyasa haka Ummi? Meyasa bakya tausayawa kanki da rayuwarki? Anya kuwa kinsan hatsarin da ki ka jefa kanki? Kina sane cewar a sanadinki zumuncin dake tsakanin Mami, Hajiya Babba da Hajiya Mama ya raunana?" Gabanta ya fadi, Amina ta koramata bayanin duk abinda ke faruwa ta dora da fadin. "Ina jiyemiki tsoron abinda zai je ya zo. Karki dauki maganganu a baibai, ni mai kaunarki ce, ba kuma zan so wani abu ya sameki ba sanadin auren Yaya Faruk, saidai kishi tsakaninki da Ihsan?" Ta yi shiru tana mai girgiza kai kafin ta share fuskarta. Bata kara komai akai ba ta yi gaba, Ummi hankalinta ya yi mugun tashi, duk wannan abun ya faru ne sanadinta? Ya akayi bata da masaniya? To wa zai fadamata, bata ji daga bakin kowa ba, ta tuno dai sadda Hajiya Babba ke kokarin yi mata magnar Faruk ya shigo wanda hakan yasa Hajiya katse maganar da ta yi niyya alokacin. Durkushewa ta yi awajen sai kuma ta ji kuka mai karfi ya tahomata, da sauri ta zagaya dan lungun gidan ta durkushe ta soma shek'asa, duk a sanadinta hakan ya faru, anya bata zama mai son kai ba? Tana ina akayi hakan? Meyasa babu wanda ya sanarmata? Sai gaba daya ta ji kunyar kanta ya mamayeta, ya za ta yi da wannan abu? Da wane ido zata kalli Mami a yanzu? Don ita sam Ihsan bata gabanta kamar Mami, Mami ta fi ji. Acan kasan zuciyarta kuwa tana ji kamar ba zata iya rabuwa da Faruk ba. Ta jima anan har saida ta ji Amina na cigiyarta sannan ta taso ta zo tana mai amsawa. Ganin yanayinta ne yasa Amina jin wani mugun tausayinta, ta janyo hannunta suka zauna a baranda. "Anti wallahi ba ni da wannan labarin, bansan da shi ba da babu abinda zai kaini ga amincewa hakan." Amina ta yi murmushi cike da tausayawa Ummi, tana kaunar yarinyar ko don hakurinta. Ita kanta ta yi mamakin yanda aka ce Ummi ta yarda da batun auren Faruk batare da wani tunani ba. "Karki damu kanki Ummi, Ubangiji Ya fi kowa sanin dalilin hakan, idan kuma Ya kaddaro aurenki da Yaya Faruk to babu makawa sai an yishi. Kawai dai ni na yi mamaki ne daman yanda akayi ki ka amince har haka." Ummi ta dubeta sai kuma ta shiga bata labarin dukkan abubuwan da suka faru bayan tafiyarta, Amina tana murmushi ta tsaida idanunta kawai tana duban Ummin. Har saida Ummin ta shiga damuwa, ga wani gumi da ta ke yi sakamakon iska mai zafin dake kadawa haka kuma garin hadari ne kwance. "Ki godewa Allah da Ya hadaki da mutum mai matukar kaunarki irin Yaya Faruk, lallai kin yi sa'a." Kunya ta kama Ummi, ta sunkuyar da kanta don har lokacin hankalinta bai kwanta ba. Kiran da Larai ta yi musu ne ya katse hirarsu, abinci ne. Ta dubi Ummi sadda ta mik'awa Amina filet din abinci. "Sama za ki hau ai, kya ci a anan?" Cewar Larai. Ta ji babu dadi. "Kai Larai, to ni wacece da ba zan ci da yar uwata ba? Larai zata yi magana Amina ta rigata. "Ai nasan halin kanwata ko wane matsayi ta taka ba zata wulakanta DAN ADAM ba." Larai ta jinjina kai tana mai kya6e baki. 'Inama ni na samu damarki.' Ta yi furucin a ranta, a fili kuwa hannu ta mik'awa Amina. "To kawo na k'ara muku." Bayan ta k'ara Ummi ta kar6a suka koma falon dake k'asa suna ci suna 'yar hira anan ne Ummi ke jin batun saka ranar Amina wanda aka daga sai bayan azumi don lokacin watanni biyu ya rage azumin. Misalin karfe uku kusan kowa ya iso har Mami. Ummi kasa zuwa ta yi gaida Mami, wajen Amina ta wuce har lokacin da aka bude taro da addua suka soma abinsu. Ummi da Amina na nan zaune suka ji sallama, suka dubi kofar suna mai amsawa. Wani saurayi ne dan dogo bak'i saidai kana kallon sumarsa Kaga bafulatanin mutum(lol) yana sanye da shadda fara k'al sai hula da ya dora a kansa. Shima idanunsa a kansu musamman ma Ummi wacce ya k'urawa ido har ta tsargu da hakan ta sunkuyar da kanta. Suka shiga gaisheshi, ya amsa, kafin su yi wani yunkurin Abba da amininsa Alhaji Kabir Jimeta sun shigo, kai a kasa Ummi ta gaishesu don kuwa tana tsoron kallon da zata samu daga Abban wanda bata mance irin rabuwar da ta yi da gidansa ba duk kuwa da ance komai ya wuce. Kafin su kai ga cewa komai sai ga Babban Yaya da Dakta sun sauko daga sama, su suka jagorancesu zuwa saman. Abubakar Kabir Jimeta har ya soma taka benen bai bar waigen Ummi ba shi fa kallon sani ya ke yiwa fuskarta saidai ya kasa tuna ko a ina yasan fuskar! Zai so Baffansa ya gani saidai kuma sam bata k'ara dago kanta ba. Acan sama kuwa bayan an zauna aka gaggaisa, Modibbo cikin harshen fulatanci ya ke tambayar Alhaji Kabir Jimeta mutan gida. Bayan gama gaisuwa Abba ya gabatar da Abubakar matsayin wanda ke son Ihsan da aure. Banda Hajiya Babba da ta riga tasan zancen da kuma Faruk da shima ya riga da ya sani a bakin Hajiyarsa, babu wanda bai girgiza da jin wannan batu ba sai ko Hajiya Mama dake murmushi kawai. Washegari da misalin karfe sha biyu na rana, Hajiya Mama da iyalanta suka dira a gidan Modibbo. Ummi tun gaishesu da ta yi ta sauko. Ido hudu sukayi da Antinta Amina dake tsaye a kofar kicin suna gaisawa da Larai. Da sauri Amina ta juya ta fita, itama Ummi cikin saurin ta karasa sauka daga bene ta fita, tsaye ta ganta a baranda ta sunkuyar da kai. Cikin sanyin jiki ta karasa gareta ta dafa kafadarta fuskarta dauke da matsanancin farinciki. "Anti." Koda Amina ta dubeta ta razana da ganin hawayen dake saman fuskarta. Hankalinta ya tashi. "Anti ki yi hakuri don Allah, ban.." "Meyasa haka Ummi? Meyasa bakya tausayawa kanki da rayuwarki? Anya kuwa kinsan hatsarin da ki ka jefa kanki? Kina sane cewar a sanadinki zumuncin dake tsakanin Mami, Hajiya Babba da Hajiya Mama ya raunana?" Gabanta ya fadi, Amina ta koramata bayanin duk abinda ke faruwa ta dora da fadin. "Ina jiyemiki tsoron abinda zai je ya zo. Karki dauki maganganu a baibai, ni mai kaunarki ce, ba kuma zan so wani abu ya sameki ba sanadin auren Yaya Faruk, saidai kishi tsakaninki da Ihsan?" Ta yi shiru tana mai girgiza kai kafin ta share fuskarta. Bata kara komai akai ba ta yi gaba, Ummi hankalinta ya yi mugun tashi, duk wannan abun ya faru ne sanadinta? Ya akayi bata da masaniya? To wa zai fadamata, bata ji daga bakin kowa ba, ta tuno dai sadda Hajiya Babba ke kokarin yi mata magnar Faruk ya shigo wanda hakan yasa Hajiya katse maganar da ta yi niyya alokacin. Durkushewa ta yi awajen sai kuma ta ji kuka mai karfi ya tahomata, da sauri ta zagaya dan lungun gidan ta durkushe ta soma shek'asa, duk a sanadinta hakan ya faru, anya bata zama mai son kai ba? Tana ina akayi hakan? Meyasa babu wanda ya sanarmata? Sai gaba daya ta ji kunyar kanta ya mamayeta, ya za ta yi da wannan abu? Da wane ido zata kalli Mami a yanzu? Don ita sam Ihsan bata gabanta kamar Mami, Mami ta fi ji. Acan kasan zuciyarta kuwa tana ji kamar ba zata iya rabuwa da Faruk ba. Ta jima anan har saida ta ji Amina na cigiyarta sannan ta taso ta zo tana mai amsawa. Ganin yanayinta ne yasa Amina jin wani mugun tausayinta, ta janyo hannunta suka zauna a baranda. "Anti wallahi ba ni da wannan labarin, bansan da shi ba da babu abinda zai kaini ga amincewa hakan." Amina ta yi murmushi cike da tausayawa Ummi, tana kaunar yarinyar ko don hakurinta. Ita kanta ta yi mamakin yanda aka ce Ummi ta yarda da batun auren Faruk batare da wani tunani ba. "Karki damu kanki Ummi, Ubangiji Ya fi kowa sanin dalilin hakan, idan kuma Ya kaddaro aurenki da Yaya Faruk to babu makawa sai an yishi. Kawai dai ni na yi mamaki ne daman yanda akayi ki ka amince har haka." Ummi ta dubeta sai kuma ta shiga bata labarin dukkan abubuwan da suka faru bayan tafiyarta, Amina tana murmushi ta tsaida idanunta kawai tana duban Ummin. Har saida Ummin ta shiga damuwa, ga wani gumi da ta ke yi sakamakon iska mai zafin dake kadawa haka kuma garin hadari ne kwance. "Ki godewa Allah da Ya hadaki da mutum mai matukar kaunarki irin Yaya Faruk, lallai kin yi sa'a." Kunya ta kama Ummi, ta sunkuyar da kanta don har lokacin hankalinta bai kwanta ba. Kiran da Larai ta yi musu ne ya katse hirarsu, abinci ne. Ta dubi Ummi sadda ta mik'awa Amina filet din abinci. "Sama za ki hau ai, kya ci a anan?" Cewar Larai. Ta ji babu dadi. "Kai Larai, to ni wacece da ba zan ci da yar uwata ba? Larai zata yi magana Amina ta rigata. "Ai nasan halin kanwata ko wane matsayi ta taka ba zata wulakanta DAN ADAM ba." Larai ta jinjina kai tana mai kya6e baki. 'Inama ni na samu damarki.' Ta yi furucin a ranta, a fili kuwa hannu ta mik'awa Amina. "To kawo na k'ara muku." Bayan ta k'ara Ummi ta kar6a suka koma falon dake k'asa suna ci suna 'yar hira anan ne Ummi ke jin batun saka ranar Amina wanda aka daga sai bayan azumi don lokacin watanni biyu ya rage azumin. Misalin karfe uku kusan kowa ya iso har Mami. Ummi kasa zuwa ta yi gaida Mami, wajen Amina ta wuce har lokacin da aka bude taro da addua suka soma abinsu. Ummi da Amina na nan zaune suka ji sallama, suka dubi kofar suna mai amsawa. Wani saurayi ne dan dogo bak'i saidai kana kallon sumarsa Kaga bafulatanin mutum(lol) yana sanye da shadda fara k'al sai hula da ya dora a kansa. Shima idanunsa a kansu musamman ma Ummi wacce ya k'urawa ido har ta tsargu da hakan ta sunkuyar da kanta. Suka shiga gaisheshi, ya amsa, kafin su yi wani yunkurin Abba da amininsa Alhaji Kabir Jimeta sun shigo, kai a kasa Ummi ta gaishesu don kuwa tana tsoron kallon da zata samu daga Abban wanda bata mance irin rabuwar da ta yi da gidansa ba duk kuwa da ance komai ya wuce. Kafin su kai ga cewa komai sai ga Babban Yaya da Dakta sun sauko daga sama, su suka jagorancesu zuwa saman. Abubakar Kabir Jimeta har ya soma taka benen bai bar waigen Ummi ba shi fa kallon sani ya ke yiwa fuskarta saidai ya kasa tuna ko a ina yasan fuskar! Zai so Baffansa ya gani saidai kuma sam bata k'ara dago kanta ba. Acan sama kuwa bayan an zauna aka gaggaisa, Modibbo cikin harshen fulatanci ya ke tambayar Alhaji Kabir Jimeta mutan gida. Bayan gama gaisuwa Abba ya gabatar da Abubakar matsayin wanda ke son Ihsan da aure. Banda Hajiya Babba da ta riga tasan zancen da kuma Faruk da shima ya riga da ya sani a bakin Hajiyarsa, babu wanda bai girgiza da jin wannan batu ba sai ko Hajiya Mama dake murmushi kawai.Allah Mai Iko, abu ya yi kyau." Cewar Modibbo a sanyaye yana dan murmushi, tabbas yaso kwarai Faruk da Ihsan su yi aure, saidai kuma ba yanda zaiyi tunda Muhammad Modibbo ya daureshi da jijiyon jikinsa, ba zai kira Alhaji Kabir da bare ba don kuwa zumunta mai karfi ta auratayya ta shiga tsakani. (Za ku ji idan an shiga tuna baya) Saidai a ganinsa wata kusan ai tafi wata, haka dai ya sanya alheri a lamarin. Alhaji Kabir ya dubi matasan yaran Hajiya Babba yana mai fad'ad'a fara'arsa. "Yanzu Hajiya Fatima wadannan duk iyalinki ne? Masha Allah duk sun girma." Hajiya Babba ta yi murmushi, zai iya mantasu kuwa a fuska don rabonta da shi tun tana goyon Faruk da ta je Adamawa, ko su Ikram bai sani ba. Hajiya Mama ce ta soma nunamishi yarannata. "Wannan shi ne Usman, ga Ridwan nan babban likita, sai Haidar da karaminsu a maza Faruk." Yana mamaki yana binsu da kallo da murmushi, idan kaga Alhaji Kabir ba za ka ce shi ya haifo Abubakar ba don kuwa shi farin bafulatani ne tas, dogo ne kuma siriri. "Ai na dan gane Usman da Ridwan tun shigowata, wadannan ne dai bansani ba." Ya nuna Haidar da Faruk. Akayi dariya, gaba dayansu yaran saida Modibbo ya yi mishi bayani akansu. "Kenan dai Faruk kai ba ka yi aure ba? Me ka ke jira?" "Ai shima yana niyyar yin, akwai wacce zai aura. Ina ta ke ne ma?" Cewar Modibbo yana waige-waige. Ihsan ta ja tsaki a ranta. Haka kawai za'a dunga tsoma wata can cikin abin zuri'arsu, daidai da Faruk din haushinsa ta ke ji yanda duk ya gama lalacewa akan wacce bata ketare ta a komai ba. Wata hirar da aka sanyo ce yasa Ikram wacce aka tura kiran Ummi ta yi mursusi ta gyara zama bata tafi ba, anan kuma Modibbo ya sanarmusu da batun zuwa Adamawa, aka bari sai idan anyi hutun makaranta. Daga nan aka yi zaman cin abinci, Abubakar hankalinsa ya kasu biyu, ga tunanin yarinyar da ya gani mai kama da Inno, sannan ga kallon Ihsan wacce ya ke jin kamar ya sanyata a aljihu ya fice da ita ko babu komai irin kalarsa ce. Mami na tare da yan uwanta wadanda Modibbo ya hadasu ya musu nasiha sosai, duk da har lokacin takan ji zafinsu saidai ganin irin mijin da diyarta ta samu na nunawa duniya kadai yasa ta sassauto aganinta ko babu komai ta burge. Wayarta ce ta yi kara wanda ya yi sanadin katsewar lomar da ta ke shirin kaiwa bakinta. Ta duba ta ga Yaha ce, ta dauka, bayan sun gaisa ne Yaha ke sanarmata cewar ta iso gidanta bata sameta ba. Mami ta yi murmushi. "Kinsan gidanmu na Sharada ko?" "Kayya Hajiya, na kwan biyu banje ba koda na shiga layin ba lallai na gane gidan ba." "Karki damu ki taho sai ki kirani idan kin shigo." Daga haka ta ajiye wayar, Hajiya Babba wacce sam bata da fushi sosai ta dubeta fuska a sake. "Wacece zata zo?" Mami ta amsa. "Yaha ce wacce ta kawo Ummi, ta bukaci ganinta ne da kar6ar kudin wata na sanarmata bata wajena yanzu." "Don bata wajenki idan kin fidda kudinki kin bayar sai cibi ya zama k'ari?" Cewar Hajiya Mama a kufule don daman har lokacin bata gama hucewa ba. Mami ko kallonta bata yi ba, Hajiya Babba ce ta danyi dariya. "Ke kuma menene abin daukar zafi to? Kefa haka ki ke ba dai zuciya ba Sadiya." Ta maida abin wasa hakan yasa Hajiya Mama ta dan sake itama. "Ai Madinar ce sai a hankali." Mami itama dan murmushin ta yi kada ta bada su agaban surukai (Jidda da Fadila). Ummi tana tare da Amina suna hira anan kicin tare da su Larai har sadda Larai suka tafi kai abinci. Alokacin Amina ta dubeta. "Wallahi kar ki so kiga yanda fatarki ta kara kyau saidai kin rame don har gwara kafin zuwanki Abuja." Ummi ta ta6a wuyanta tana murmushi. "To Anti ba dole ba, nifa koyaushe cikin tunani na ke na wannan abu wallahi." "Ya za ki yi to?" Alokacin da Larai suka dawo ne ta dubesu. "Wai kuwa kunsan cewa wannan saurayin da ya zo shi zai auri Ihsan?" Amina da Ummi suka dubi juna ido waje kafin su dubeta. "Anya kuwa?" Cewar Amina.+ "Wallahi kuwa, sunansa Abubakar nima zan fito na ji su Rahila na zancen wai sun dace kuwa." Ummi ta yi shiru kawai batare da ta tantance yanayin da ta ke ciki ba, Amina zuciyarta fal murna, hankalinta ya kwanta Ummi ba zata hada kishi da Ihsan ba kenan. "Lallai, Allah Ya tabbatar da alheri." "Ameen dai, ai daga gani dan hutu ne, wannan baisan talauci ba." Suka danyi dariya. "Kai Larai." Fad'in Amina kenan. Nan suka shantake don gaba daya Ummi nauyin fita ta ke ji, ko kusa batason wani ya ganta, tana ganin Faruk na faman dokomata kira saidai ta kasa dagawa har ya gaji ya daina. Har lokacin bata bar tuna kallon da wanda aka kira da Abubakar ke jifanta da shi ba, ta rasa ko na menene. Sai bayan sallar Magriba su Abba suka tafi banda Abubakar da ya tsaya hira da Ihsan ya ce zai taho, gaba daya suka yo musu rakiya. Shigowar Mami kicin dinne yasa Ummi kallonta cikin rudewa. Ta durkusa ta gaisheta murya na rawa. Daga kallo daya bata k'ara duban inda ta ke ba ta soma magana. "Amina ki je ki taho da Yaha tana nan bakin titi wajen kantin Nura." "Toh." Amina ta amsa, daga haka Mamin ta fice. Ita kuwa Ummi ta shiga tashin hankali matsananci, Yaha kuma? Shikenan yau zata koma garinsu, tasan abinda Mami ke shirin aikatawa kenan. "Muje ki rakani." Ta bi bayanta jiki a matukar sanyaye, a falon kasa, su Rahila ne da su Jidda gaba daya sun hadu hankalinsu ya tafi a kallon (Swaragini) a tashar Bollywood, sam hankalinsu ya tafi a kallo. Suka fito, a farfajiyar gidan su Faruk ne tsaye, lokacin walkiya ake yi da cida na alamun saukar ruwa duk sadda Allah Yaso. Idanunsa ya kai kanta, ya yi tsai yana dubanta da tunanin inda za ta je a daren nan, kasa jurewa ya yi ya kira sunanta. Ta juyo tana mai amsawa. Ya karaso. "Ina za ku je?" Amina ta sanarmishi aiken da Mami ta yi musu. Ya gyada kai kafin ya dubi Ummi. "Ina wayarki?" Ta dago mishi ita ta mik'a batare da ta yarda da kallonsa ba. Ya kar6a duk da ya so kallon kwayar idanunta ko zata fahimci 6ata mishi ran da ta yi na k'in daukar wayarsa saidai hakan ya gagara. Suka wuce wayar na hannunsa. Abubakar dake can gefe saman kujera tare da Ihsan suna hira ya yi tsai yana k'ara duban Ummi. 'Kamar ta yi yawa.' Ya fad'a a ransa. Ya kai duba ga Ihsan wacce gaba daya ta gama k'uluwa da wannan kallon da Abubakar ke yiwa Ummi, kada ace shi dinma ya fad'a tarkonta ne? "Honey, wacece wannan please?" Ranta ya 6aci. "Bansanta ba nima." Ganin yanda ta yi maganar a fusace ya sanyaya mishi jiki, ya sassauta murya yana mai dan dafa cinyarta. "Sorry i don't mean to hurt you." Ta dan janye cinyarta gami da jan guntun tsaki. "Please Abbakar babu kyau fa abinda ka ke yi, kada ka k'ara ta6ani." Ya numfasa. "Ki yi hakuri zan kiyaye, ke dince kin hadu ne Ihsan samun irinki sai an tona." Ta dan ji sanyin abinda ya ce har cikin ranta, wannan yasa ta dan sassauto, shima ya ajiye maganar Ummi gefe ya cigaba da shigar da kansa wajen mutuniyartasa. *** *** *** Ummi sun danyi tafiya kafin su ga Yaha. Koda suka isa gareta, baki bude kawai ta ke kallon Ummi, wani arnen material ne a jikinta dinkin riga da siket, ta kara wani kyau sosai, duk da ramar da ta yi, dirin jikinta yana yanda ya ke bai girgiza ba. "Ummi ke ce?" Ummi da har lokacin bata bar shakka-shakkar Yahar ba ta yi dan murmushin yak'e. Gaisuwar da Amina ta yi mata ne ya katse tunaninta tana mai amsawa sannan suka soma tafiya. Yaha ta dubi Ummi. "Na ji abin arzikin da ya sameki ai jiya a bakin Hajiya." Furucin da ta yi yasa suja dubi juna ita da Amina fargabarsu ta dan kau jin ta kira hakan da abin arziki. "Um." Shine kawai abinda ya fito daga bakin Ummi. "Allah Mai Iko kenan, in sha Allahu babu abinda zai hana wannan aure naki sai ikonSa, yarinya kin yi goshi. Na gano kuskurena Ummi, ki gafarceni kinji 'yarnan, bana so hakkinki ya kamani alhalin ba kiyi min laifin komai ba haka siddan na biyewa makiran nan(Saude da Habiba) na tsaneki." Ta k'arashe kamar zata yi kuka, wanda hakan ya basu tabbacin da zuciya daya ta ke maganar. Farin ciki yasa Ummi soma zubar da ruwan hawaye ba tare da ta ankara ba, tana kuka tana dariya don murna, ta daga kai ta dubi sararin samaniya yanda ake faman walkiya. Yau ta kira wata babbar rana da ba zata ta6a mancewa ba. (Wani abun na gaba Ummi), Yau ita Yaha ke yiwa magana cike da nuna kulawa da nadama? Amina ta dafa kafadarta. "To sarkin kuka, akan hanya ki ke fa, kada a dauka sato ki mukayi." Suka yi dariya har Yaha, ta yi kasa da kanta tana share fuskarta da mayafin jikinta kalar yadin. Banda hamdala babu abinda ta ke yi har suka karasa Yaha na basu labarin auren cin amanar da Dije diyar Habiba ta yi da mijin yar uwarta. Tabbas Ummi tasan wacece Dija don kuwa kusan bata da iyaka da gidansu, duk sadda ta so shiga ta ke yi, itama ba dai mugunta ba kodayake ba a k'asa ta dauka ba. "Ina Babana?" Yanda ta yi tambayar cikin sanyin jiki ne yasa suka ji tausayinta musamman Yaha wacce tasan ko sau daya bai ta6a tambayarta ba, saidai batason ta karyamata zuciya ta yi dan yak'e. "Babanki yana nan cikin koshin lafiya." Har suka k'arasa hirar Ringim sukeyi, Yaha na bata labarin irin abubuwan da suka faru. Koda suka isa gidan Amina ce ta karasa da ita wajen Mami don kuwa ita Faruk ne ya tsaidata, duk yanda ta so k'i hakan bai samu ba don Yaha sun ce ta dakata. Sai anan ma Yaha ta ganshi, shakka babu Ummi ta yi katari da babban goro. Can gefe suka tsaya k'asan bishiyar dogon yaro. Haidar da Dakta sun fita kai Abubakar masaukinsu. Ya dubeta fuska ba walwala. "Shi ne ki ka k'i daukar wayata ko?" Tana wasa da gyalenta ta ce. "Ka yi hakuri ina cikin mutane ne." Ya dan ta6e baki. "Don kina cikin mutane kuma shikenan sai ki kasa amsa wayata Ummi? Kinsan yanda na ji kuwa?" Shiru ya biyo baya kafin ta furta kalmar hakuri. "Da abinda ki ke kwarata kenan, kinsan duk girman laifin mutum matukar zai ban hakuri to nakan hakura, amma idan ya k'ureni za'a ji kanmu fa." Murmushi kawai ta yi. Iskar da aka soma mai zafi yasa suka dan rufe idanu. "Kwanakin nan ana zafi Alhamdulillah, gwara ruwan ya sauka ko an dan ji sanyi." Fadin Faruk kenan. Ita dai 'Um' kawai tace. Saida iskar ya lafa ya dubeta. "Ko ki tambayi albishir da nace zan miki ko?" "Ina shirin tambaya ne." "Aa Ummina banda karya fa, shikenan ma na fasa sai aurenmu ya tashi. Ga wannan." Ya mik'omata wani k'aramin gida na zobe, ta dubeshi ya dan daga mata gira. "Kar6i mana, ko na sakamaki?" Ta girgiza kai sannan ta kar6a. "Oya bude ki saka na gani." Ta bude a hankali, wani kyakkyawan zobe ta gani mai kyau ruwan gwal, watakil ma na gwal dinne bata sani ba. Ta sanya a yatsanta na kusa da karamin, ya zauna das sai daukar ido ya ke. Ya zubawa yatsun idanu tamkar ya sumbata ya ke ji, sauke ajiyar zuciya ya yi yana mai dubanta. "Ya miki kyau sosai." Ta dan russuna kadan. "Nagode Yaya Faruk, Allah Ya k'ara arziki." Har cikin ransa ya ji dadin adduarta. Ya amsa da murmushi. Ganin an soma yayyafi ne yasa dole suka yi sallama ta nufi ciki rike da gidan zoben. *** *** *** Acan kuwa Yaha na tare da su Hajiya Babba suna magana akan Ummi, Hajja da Mami suna zaune babu damar aibata abin don kuwa Modibbo na zaune a gefe don kusan anan falon ya ke wuni. Hajiya Mama ce ta sanarwa Yaha dukkan abinda ake ciki, Hajja sai kallon banza take watsawa Yaha ganin yanda ta wani washe baki kamar gonar auduga. "Daman dole ta yi murna tunda an gama tsafe miki d'a kin kasa ganewa." Ta yi furucin a hankali cikin harshen fulatanci, babu wanda ya tanka saidai Yaha ta tsargu don ta lura kamar tsohuwar bata farinciki da hakan. Nan dai aka gama tattaunawa Yaha ta tabbatarmusu ba'a yiwa Ummi miji ba, karshe aka tsaida magana inda bayan shawara da Modibbo da kuma Gen. Ahmad (ta waya) cewar Asabar mai zuwa za'a je can Ringim bisa jagorancin Yaha a tsaida magana da mahaifin Ummin sannan a saka rana. Da haka aka rufe tattaunawar, Yaha ta so tafiya anin an soma ruwa suka tsaidata sai ta ci abinci, idan yaso sai su fita tare da su Hajiya Mama. A dakin su Larai Ummi ta zauna tare da Yaha. Yaha na cin abinci ta dubeta. "Amma sai naga kamar mutanen nan ba suyi marhaba dake ba Ummi, kinga yanda tsohuwar nan ke dubana kuwa?" Ta dan yi yak'e ba tace komai ba. Yaha ta kai loma. "Um, Allah dai Ya fiddamu daga zargin mutane, kada a dauka wani mugun abin muka k'ullo." Fadin hakan yasa idanun Ummi cika da kwalla, ai hakan ma ake zargi. Ta yi nasarar sharesu bata ko bari Yaha ta lura ba. Saida wajen takwas suka yi shirin tafiya, suma su Ummin gobe da safe zasu wuce Abuja. Ta kar6i lambar Antinta Amina da Yaha don a dazun Faruk ya bata wayarta. Da hawaye ta rabu da Antinnata. "Ki gaishemin da su Anti Hauwa da Inna." Amina ta amsa itama idanunta cike da ruwan kwalla. "Za su ji Ummi, nasan har ku wuce Ringim ba lallai mu hadu ba, saidai ko waya, ki dage sosai da addua karki gaji, in sha Allahu Allah zai taimakemu." Da wannan suka rabu zuciyar kowannensu babu dadi. Itama Mami alokacin suka fice. *** *** ***

Post a Comment for "DAN ADAM CHAPTER 23"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...