DAN ADAM CHAPTER 22 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

DAN ADAM CHAPTER 22

DAN ADAM CHAPTER 22

- - Post a Comment
DAN ADAM CHAPTER 22


  ABUJA+ "Allah Mai Iko." Shine abinda Gen. Ahmad ya fad'a sa'ilin da ya ajiye waya da Alhaji Atiku inda suka tattauna a mutunce. Hajiya Babba da ke kokarin zuba mishi abinci babi abinda ta ce, tamkar duk bata ji abinda suke tattaunawa akai ba. Shima Daddy ita ya yi shiru yana duba. "Meyasa ki ka 6oyemin wannan batu? Na yi tsammanin don shi ki ka je Kanon?" Hajiya ta ajiye (serving spoon) tana mai duban mijinnata cike da kulawa. "Me fa?" "Ai shi Alhaji Muhammad ya riga da ya yiwa diyartasa miji, d'an abokinsa, Alhaji Kabir Jimeta." Hajiya Babba ta yi wani murmushi. 'Madina kenan.' Ta fada a zuci, a fili kuwa ta nuna rashin damuwarta. "Allah Yasa alheri, ni sai yanzu da ka fada na sani daman iyakar tattaunawarmu da ni da Madinar ce, watakil sai bayan ta sanarmishi itama ta ji hakan don da ace ta san da haka ba zata 6oyemin ba." Ta fad'i hakan ne don batason ta nunawa mijinta basu dadi da yar uwarta. Ganin fuskarsa ta cika da damuwa ta ce. "Ba wani abu fa, kasan babu mai aurar matar wani, watakil ba rabo tsakaninsu, idan akwai sai kaga lamarin ya juye." Ya jinjina kai cike da gamsuwa da maganganunta. "Hakane kuma, to Allah Ya za6amusu abinda yafi alheri. Ita wannan ya ake ciki?" "Ga dukkan alamu lokacin zuwan matar da ta kawota ya k'arato inaga tunda ga watan saura kwana biyu ya mutu, ( family meeting) din namu shima ina tunanin jibi ne zaayi." Cewar Hajiya kafin kuma ta cigaba da zubamishi abinci. Kwance a saman lallausan katifa a saman gado, Ummi ce tana faman duba wasu litattafan addini da Hajiya ta had'ata da su, ta ji dadin hakan kwarai, Hajiya ta k'ara da batun sanyata Islamiyyar da Ikram ke zuwa don zuwa lokacin hatta form an kar6omata, hakanan an bada a dinka mata (Uniform). Ga shi kuma gogan ya nuna yana mata sha'awar karatun boko, acewarsa neman ilimi ko gemunka na ja a k'as ba ka yi latti ba. Wannan shine kyakkyawan albishir gareta. Wayarta ta yi k'ara alokacin da ta tsunduma cikin karatu, ta sanya hannu ta janyota. Tsai ta yi da ido tana duban lambar wacce ta ta ganta banbarakwai, har ta katse bata iya ta d'aga ba, sai a karo na biyu ne ta d'aga da sallama. Daga can Adnan ya amsa yana dariya. "Kaga sabon shiga kin tsoraci kada a gudu da ke ne?" Ta so gane muryar saidai bata da tabbacin shi dinne ko aa, ta dan saki fuska. "Ba haka bane." "To ina My Best?" Kalmarnan babu a bakin wanda ta santa sai Adnan, ta washe hakora gami da mikewa zaune. "Lah, Yaya Adnan?" Sai kuma ta yi dariya shima darawar ya yi. "Ni ne nan kanin Angonki." "Kai Yaya Adnan." "Ai gaskiya ne, yanzu ko kin yi tsada karki so ki ji kashedun da aka yimin kafin a bani lambarki." Ta yi murmushi. "Ina wuni." Ta fada cikin basar da wancan maganar. "Ba zan amsa ba tunda kin yi waya amma ba ki nemi a ba ki lambata ba." "Ka yi hakuri to, ya su Mami?" "Suna k'asarku, ni ina nan Dubai." Ta dan bude ido kadan. "Au na manta, Yaya Faruk ya gayamin kwanaki wai za ka karatu ko?" "Inye! Abu ya yi nisa haka ashe?" Ya karashe yana dariya, ita kuwa murmushi kawai ta yi, ita sai lokacin ta tuna da ashe fa da yaya Ihsan ta ke magana, sam halinsu ya bambanta. Adnan ya sake da ita suka shiga kwasar hira sosai yana bata labarin Dubai tamkar wata abokiyarsa, duk da tana jin wani dan kara(din-din) ta cikin wayar bata fahimci ko na menene ba. Bayan sun kammala wayar ne ta ajiye, nan ta fahimci Faruk ke kira. Kafin ta kai ga yunkurin kiransa sai ga shi ya kara kira. Bai ko amsa sallamarta ba. "Da wa ki ke waya?" "Yaya Adnan ne." Ya sauke ajiyar zuciyar da har ta ji. "Ok, amman kun jima kuna waya, me ya ke fadamiki haka?" Ta yi murmushi kadan. "Hira ce ta makarantarsu ya ke min." "Ok, kina da labarin tafiyarmu Kano gobe?" Gabanta ya fadi. "Har da ni?" "Au, Hajiya bata sanarmiki kenan? Watakil sai zuwa anjima, family meeting zaayi, kusan wannan karon ni da ke ne masu muhimmanci a gurin, akwai wani ma albishir din amman ba yanzu zan yi miki shi ba." Ita kam duk ta tsorata, ta lura shi gogan ma bai gane hakan ba. Suka dan ta6a hira kafin su yi sallama. Ai kuwa a daren Hajiya ke sanarmata cewa ta shirya kaya ko kala uku ne. Washegari gaba daya da misalin biyu na rana suka kama hanya har yayyun Faruk da matansu, a motar can lungu ta zauna don gujewa wani abin da zai je ya zo, tana ji Intisar, Baraka da Ikram suka juye harshe zuwa fulatanci suna hirarsu, duk ta bi ta tsargu duk da basu ko kallon inda ta ke. *** *** *** KANO Acan kuwa gidan Mami, da misalin karfe uku Yaha ta diro. Mami ta dubeta bayan ta zauna. "Aa Yaha sai yau ki ke tafe?" "Wallahi kuwa Hajiya, Minna na je shiyasa na kwan biyu ba ki ganni ba, su ma can gidan su Ummin suna min waya wai sun ji shiru." Murmushi Mami ta yi na takaici. "Ai kuwa Ummi bata gidannan yanzu." Yaha ta karkato gami da yin sakato da baki. Mami ta koramata bayani. "Jar Uba!" Shine kawai abinda Yaha ta ambata....! Yaha ta yi furucin cike da tsananin mamaki, ba don Mami da kanta ke sanarmata ba da kai tsaye zata kira hakan da shaci fad'i. Mami ta cigaba da magana. "Ba abin mamaki bane, shi DAN ADAM idan ya samu guri fin haka zai iya aikatawa, banda haka ki duba irin yanda na dauki yarinyarnan, tunda nake yin yan aiki ban ta6a yin wacce na kyautatawa ba kamar ita, har wai yar aiki ta samu matsayin da zan zauna na dan yi hira da ita. Anan menene bai faru ba.." Sai kuma ta yi shiru tana mai jin zafi a ranta. Yaha ta yi shiru cikin nazari, to ita fa Saude kudi ta ke nema, ita dai acewarta ko karuwanci yarinyar zata fad'a to ta fad'a matukar zata samu abin duniya sanadin haka, ga kuma yanzu a karshe da suka yi waya ta sanarmata kada ta kuskura yarinyar ta k'ara koda kallon hanyar garinsu ne ballantana wai ta kawota ganin gida. Yanzu ya za ta yi? "Ki ka yi shiru? Idan za ki iya komawa gobe ki dawo to, idan kuwa za ki yi zaman jiran zuwansu daga Abuja yau din to babu laifi."(Ta sani ne ta hanyar Ihsan wacce su ka yi maganar da Ikram.) Sai lokacin Yaha ta dawo cikin hayyacinta, lallai kam tana bukatar nazarin. "Bakomai ranki ya dad'e, zan iya tafiya na dawo goben." Mami bata ko kara kallonta ba, daga haka itama ta mike ta bar gidan ba tare da ta samu ko na mota daga Hajiyar ba kamar yanda ta saba yi mata duk zuwanta. Bata zarce ko'ina ba sai gidan 'yar yayarta Abida wanda anan ne ta saba sauka duk sadda ta shigo garin Kano. Abida ta yi mata kyakkyawar tarba yanda ta saba. Yaha ta sauke mayafinta. "Su Abu sun wuce makaranta ne?" "Eh sun dan jima." Sai bayan ta ci abinci ta yi sakato tana tunani, Abida da ke gefe tana kokaarin zuba kananzir cikin risho tana mata hira amman shiru hakan yasa ta dubanta. "To Inna meke faruwa ne haka?" Yaha ta hau lashe kwana kafin ta tureshi gefe ta dubeta. "Bani shawara Abida, kaina ya cushe na rasa ma menene abin yi." Abida ta maida risho ta gyara sannan ta karkato tana dubanta. "Ina jinki Inna." Ta karanto mata tun kai Ummi aikatau da kuma ire-iren abinda Saude ke sanarmata akan yanda ta ke son ganin Ummi har ma da yanda suka yi da Mami. Ta karashe da fadin. "Yanzu wallahi gaba daya jikina jinsa nake a sanyaye, ni tunda nake kai yan aiki ban ta6a haduwa da mai hakuri irin Ummin nan ba wallahi, zan iya ce miki tun tashinta a hannun Saude bata huta ba, ga kuma tsangwama da tsanar da ubanta ke nunamata tamkar ba jininsa ba." Abida ita kam mamakin Innarta ne ya cikata, ashe daman zata iya mugun abu har irin haka? A haka idan ka ganta tamkar ba zata aikata ba. "Allah Mai Iko!" Ta fada a fili kafin ta cigaba da magana. "Inna a farko ina mai baki shawara kan ki ji tsoran Allah, ki kuma sani cewar dukkan wani abu da muke aikatawa za'a tashemu gobe kiyama a kuma tambayemu. Wannan sam ba daidai bane a hada baki dake wajen cutar da rayuwar baiwar Allah wacce bata ji ba, kuma bata gani ba, ki sanya Rahma (diyar Yahan) a matsayinta ki auna ki gani, za ki ji dadi ace yau babu ranki Kulu(kishiyarta tun mijinsu na raye) ta aikata hakan agareta? Kada hakkin Ummi ya kamaki anan gaba Inna, don Allah ki yi tunani wannan ba daidai bane ko kadan." Daga haka Abida ta juya ta cigaba da aikinta zuciyarta cike da dumbin tausayin Ummi duk kuwa da cewa labarinta kadai ta ji. Yaha wacce ta yo shiru tana nazarin maganganun Abida ne, jikinta ya yi sanyi, babu abinda ke yawo a kwakwalwarta face irin zagi da hantara da ta dunga yiwa Ummi a hanya da kuma zuwansu Kano, harma da zaginta da suka yi zaman yi da su Saude duk akan abim duniya wanda ba wani mai yawan azo a gani bane. Ta sauke ajiyar zuciya kawai. Mutanen Abuja sai Magriba suka shigo garin Kano, Ummi sai rarraba idani ta ke har suka shiga gidan Modibbo. Sai lokacin ta soma jin kamar ta saki fitsari a wando tsabar rud'ewa. Adduo'i kawai ta soma karantowa. Bayan sun isa ne aka soma fitowa, kusan itace karshen fitowa daga motar, tana saukowa suka hada ido da Faruk wanda ke sanye da yadi fari k'al da aka yiwa aiki da bak'in zare, murmushi ya sakarmata ta kauda kanta ganin ba su kadai bane. Bayan shigarsu ne aka hau gaggaisawa, Ummi ta tsorata da kallon banzan da ta samu daga Hajja wanda a baya ba haka ta ke amsa mata ba. Haka har dai aka basu wajen kwana, abinda ta tsorata ne ya faru don kuwa daki daya aka basu su uku, wato ita, Ikram da kuma Baraka, Intisar na tare da su Jidda. Baiwar Allah duk da a matse ta ke da shiga bandaki saida ta tsaya suka gama uzurirrikansu sannan ta shiga, lokacin an yi sallar isha'i. Wanka ta yi ta chanja auduga sannan ta fito sanye da mayafi saman daura kirjinta, basu dakin duk sun fita, ta karasa ga yar jakar kayanta ta ciro doguwar riga ta jallabiya ta sanya sakamakon zafin da ake yi sosai. Ta tsaya shafa mai tana kallon fuskarta a madubi yanda duk ta chanja ta yi wani haske mai kyau hakanan fatarta ta murzu. K'arar da ta ji wayarta ta yi ne yasa ta mikewa ta dauka. Da sallama ta amsa wayar. "Dear ya gajiyarki? Kin yi sallah?" Kunya ta kamata, wato bai lura koda aka tsaya sallah ba ita bata yi ba? "Gajiya ta bi lafiya, ya naka gajiyar?" "Ta ya zan gaji alhalin ina ganinki?" Murmushi kawai ta yi tana duban madubi jin an murda kofar, mikewa ta daga wajen gami da komawa gefen gado ta zauna. Ikram ta ta6e baki kafin ta dauki wayarta (don daman abinda ya shigo da ita kenan) ta fice. "Ba za ki fito cin abinci bane?" Ta girgiza kai. Gaba daya bata saba da shiga cikinsu ba, ta saba rayywa da su matsayin yar aiki mai kai musu su ci sannan a kwashe, anya zata iya ci tare da su? "Kinyi shiru? Ki fito ga shi fa duk an hadu." "Toh." Shine kawai abinda ta ce sannan suka yi sallama. Faruk kuwa yana ajiye wayar suka hada ido da Haidar, dariya ya yi. "Wannan kashem muryar fa?" Cewar Haidar. Murmushi kawai ya yi. "Ya wuce ace yana waya da Juliet dinsa." Cewar Fadila cikin gatse. Ya dubeta kamar ya tanka sai kuma ya share kawai. Hajja ta so tofa nata saidai kuma tana gudun idanun Modibbo wanda ba karamin gargadi ta sha daga wajensa ba tun kafin zuwansu. Har zaa soma cin abinci babu ita ba dalilinta, ya dan rausaya kai suka yi ido hudu da Hajiyarsa. Murmushi ta yi mishi, ta riga tasan damuwar dannata, ta kai dubanta ga Ikram. "Ikram maza tashi ki je ki kiramin Ummi ta zo ta ci abinci." Ba'a son ranta ba ta mike ta nufi dakin nasu. Ummi na zaune har lokacin ta zubawa wayarta idanu tana tunani ta ji an kara shigowa dakin ba sallama. Ikram ta watsamata harara. "Ki zo." Daga haka ta fice abinta, gaban Ummi na faduwa ta mike ta dauki mayafi ta yafa a saman jallabiyar dake jikinta sannan ta mara mata baya. A falon dai da ta sani na Modibbo anan suke, ta dan dubi hanyar kofar, kamar ba'ayi sadda ta kasa shiga ba don kunya ta ce Amina ta taimaka ta soma shiga su kai musu abinci, wai yau itace zata shiga cikinsu su ci su sha tare? Idanunta ya ciko da kwalla, ta daure cikin rawar murya ta yi sallama, suka amsa mata, kamshin turaruka da na abinci ne ya soma dukan hancinta ga kuma sanyi na (Ac) mai ratsa jiki, tana tafe kanta a kasa tamkar zata fad'i haka ta ke ji x durkusawa ta yi a gefe yanda yan aiki suka saba. Ya lumshe ido gami da yin k'asa da kansa, ji ya ke kamar ya tashi ya rungumeta cikin jikinsa, ya fahimtar da ita cewa yanzun matsayinta ya wuce zatonta, ya nunamata itama mai daraja ce da k'ima, saidai doka ta addininsa bata ba shi wannan damar ba. Ya tsinkayi muryar Hajiyarsa na fadin. "Dawo nan mana Ummi, ke kadai ake jira aci abinci." Ta mike jiki a sanyaye Modibbo na kallonta cikin yaba nutsuwa da hankalinta, ya ji yarinyar ta burgeshi, haka ta karasa ta zauna a gefen Jidda can bakin kujera. Hajiya ta umarci Jidda da ta zubamata, shinkafa ce da miya sai farfesun kifi ta nuna shinkafar ma ta isa. Nan ta yi bismillah ta dan soma ci, idanu ta dan dago kadan, karaf a cikin na gogannata wanda ke shirin kai loma, ya yi wanka yana sanye da wando (3 quarter) sai riga marar hannu don shi din bai fiye son yanayin zafi ba. Ta yi saurin kauda kanta, duk bata saki jiki ta ci sosai ba har aka soma kammalawa, kusan ta riga dukkansu ja baya. Hajiya ta dubeta "Kada dai kin k'oshi? Haba, me ki ka ci?" "Na koshi ne." Ta fada a hankali, Modibbo ne ya yi magana cikin harshen fulatanci sannan Hajiya ta dubeta. "Tashi dauki filet din ki wuce daki ki ci." Ta nuna ta koshi, karshe dai ganin Hajiya ta dage yasa dole ta mike ta dauka tana jin Modibbo na fadin. "Lallai Amaryar tawa mai kunya ce kamar bafulatanar itama." Kalilan ne suka dara banda masu jin haushin lamarin. Kai tsaye k'asa ta sauka zuwa kicin, Larai mai aikin na ganinta ta saki baki. "Ummi, ashe idanuna ba gizo sukamin ba dazu ke dince ki ka koma haka?" Ummi ta dan yi murmushi cikin jin nauyi tana mai fatan kada a yi mata wani mugun zargin ganin irin kallon da wata dake tare da Laran ke mata, da alama sabuwar yar aiki ce. "Ni ce Larai, ina wuni." "Allah kenan, Mai maida talaka sarki, Mai maida sarki kuma talaka. Ashe kuma autan hajiya za ki aura?" Shine abinda kawai Larai ta ce batare da ta amsa gaisuwarta ba. Ta ajiye farantin tana murmushin dai saidai ta kasa amsawa. Zata fice ta ji Larai na fadawa dayar. "Allah dai Ya kwato musu dansu, wasu mutanen ba tsoron Allah, daga sun samu wuri sai kuma a asirce dan masu gida." Ta yi maganar a hankali wanda karaf a kunnen Ummi, ta fice da sauri.....Kasa komawa saman ta yi ta fita nan wajen barandar tsakar gidan ta tsaya cike da tunani. Tasan ba Larai kadai ce mai irin wannan tunanin a kanta ba, ba'a rasa mutane da dama da zasu kawo hakan a ransu game da ita ba. Ta yi shiru tana nazarin wajen alokacin da ta tunano ranar daurin auren Haidar inda anan ne ta soma ganin murmushin Faruk agareta, sai ta ji rabin damuwarta ta kau, ta shagala a tunani ne ta soma jin hirarrakin mazan suna fitowa. Da sauri ta yi baya, Babban Yaya ne ya soma ankara da ita. "A'a, Ummi me ki ke yi anan? Ko duk zafin ne?" Ta girgiza kai saidai ta kasa magana. "Ka sani ko plan din da suka shirya kenan da mutumin nata? Su hadu a nan?" Abin ya basu dariya, ita kuwa kunya duk ta bi ta isheta ga babu bakin magana. Jin sun cigaba da tafiya ne yasa ta saurin juyawa zata koma ciki. "Tsaya mana." Ta tsinci muryar Faruk, dole ta dago kanta ta ganshi tsaye bai tafi ba, hakan yasa ta kalli yayyunnasa, ko waige basu yi suna nufar kofar gidan suna hirarrakinsu. Ya tako har gefenta ya tsaya. "Ummi." Jin yanda ya kira sunanta a sanyaye ne yasa ta amsawa a hankali tamkar bata so. "Ki yi hakuri." Ta dubeshi, fuskarsa cike da damuwa. "Hakurin me kuma?" Ya dan jinjina kai. "Nasan zamanki cikin yarannan ba zai miki dadi ba, saidai idan ki ka k'ara hakuri kan wanda na sanki da shi, na dan lokaci ne zai wuce kinji?" Ta yi dan murmushi, tana son Faruk kusan fiye da yanda ya ke sonta. (A ganinta) don acewarta ya cancanci komai daga gareta, matashi irinsa da ya ketare ta amman bai ko damu da wadannan bambance-bambancen da jama'a ke gani ba ya aminta da ita har ya furta yana sonta da aure, ita kuwa me za ta ce ga Allah banda godiya? "Na ta6a fad'amiki kina da kyau?" Ya yi furucin a hankali cikin murya mai kama da ta rad'a bayan ya soke hannuwa cikin aljihun wando gami da kwantar da kansa jikin bango. Ta dan dago idanunta a hankali tana dubansa, saida ta ji cikinta ya kad'a hakanan gabanta ya cigaba da dukan tara-tara, ba ta k'ara marmarin kallon idanunsa ba, kusan tunda ta ke da Faruk bata ta6a ganin irin wannan kallon daga gareshi ba. Shi dinma ya fahimci razanar da ta yi, ya runtse ido kafin ya budesu. 'Ya Salam' Ya yi furucin a ransa kafin ya tsaya sosai. "Sai munyi waya, ki koma ciki." Bai jira cewarta ba ya juya da sauri, maimakon ya bi bayan yan uwansa sai ya wuce dakin da aka saukesu. Ita dinma da sauri ta yi ciki, yau wani Faruk din ta gani ba wanda ta sani ba, wannan Faruk din ya tsorata ta. Koda ta koma sama, a falon daga Hajja sai Hajiya Babba zaune suna hira sai kuwa Modibbo dake gefe yana jan carbi. Ta wuce a sannu ta yi dakin da aka basu don kwana. Gaba daya masu kwana tare da ita basu nan sai Baba karami(mai sunan daddy), Amal da Yasmeen. (Yaran Babban Yaya) da kuma Ma'aruf da Ahmad (Yaran Dakta) suna wasansu saman gado. A dakin kusa masaukin su Jidda ne ta jiyo shewa da hirarrakinsu. Zata zauna saman gadon ne ta ji Ma'aruf na fadin. "Ke! Karki zauna a gadon nan, wari ki ke yi." Ta yi shiru tana kallonsa, ba laifi bane don ya yi mata, ya danganta da abinda aka fadamasa a kanta. "Lala lala, sai na fadawa Grandma, ka manta abinda ta ce mana? Ita fa Uncle Faruk zai aura." Cewar Baba Karami kenan. Ta dubi fuskar Ma'aruf ganin yanda ya ke yamutsa fuska. "Ai Momi ta ce mana 'yar aiki ce, ko boko ba ta yi ba ko?" Ya fada yana duban kaninsa Ahmad wanda ke yin doki da filo, Ahmad ya gyada kai. "Eh, Momi ta ce kuma kada mu dunga kulata." Amal a guje ta yi hanyar waje tana fadin. "Sai naje na gayawa Grandma." Da sauri Ummi ta rikota tana murmushin yak'e. "Dawo kinji, rabu da su." Amal cikin kalar tausayi ta ce. "Gashinan sun sanyaki kuka." Ummi a wayance ta share fuskarta. "Ba kuka nake ba abu ne ya shiga idona." "Lah Uncle fa ya ce mu daina k'arya kuma kin yi." Cewar Amal, yarinyar ta burgeta, ta yi murmishi har cikin ranta. "To na daina, jeki ku yi wasanku bazan zauna saman gadon ba." Gefe ta zauna tana danna waya saidai zuciyarta cike fal da damuwa, Amal ta matso. "Lah Anti kina da game?" Ta yi murmushi kadan. "Akwai, za kiyi ne?" "Eh." Nan ta kunna mata, suma yaran duk suka matso zasu yi, Ma"aruf yana gefe yana kallo, yana son ya ce zaiyi saidai ba dama, sai kuma ya mike ya nufi waje yana fadin. "Ai nima Momina tana da game bari na amso wayarta." Murmushi kawai ta bishi da shi har ya fice. Haka sukayita jagwalgwala wayar tana kallonsu har chaji ya kusan k'arewa sannan ta kar6a ta jona ta. Tana jin bacci saidai batason hawa gadon ace ta yi laifi, haka ta kwanta nan saman darduma. Har ta soma bacci ta ji wayarta ta dauki k'ara, mikewa ta yi tana salati, har lokacin basu shigo ba, yaran ma sun gaji da wasa sun kwanta. Ganin Faruk yasa ta yin murmushi kafin ta dauka duk a gajiye don muryarta ma ta nuna. "Bacci ki ke yi wai?" "Eh." "Shikenan bari na kyaleki saida safe." Ya fada cikin dauriya don shi kam tunaninta ya so ta6a nasa baccin, suka yi sallama daidai lokacin su Ikram suka shigo. "Wai yarannan bacci suka yi anan? Lallai ma, ke kuma kina kallonsu idan suka yi mana fitsari fa?" Fadin Ikram kenan. Baraka ta dubi Ummi don ita sam bata ko lura da ita ba ma. "Tashesu su wuce dakinsu." Bata ji ko darr a ranta ba, don ita bata jin kanta a wata har yanzu ballantana ta musa musu, haka ta tashesu ta mik'asu wajen iyayensu inda akayi musu shimfida a k'asa, saidai ta sanyasu fitsari kafin ta kwantar da su, tuni Intisar ta yi baccin don ga gajiya ga kuma ciki. "Saida safenku." Ta fada bata ko saka ran zasu amsa ba sai kuma ta ji sun amsa din sannan ta rufemusu kofa ta koma dakinnasu. Nan ta kwanta k'asa gami da yin filo da hannunta, babu wanda ya ce mata uffan, tana ji suna yara fulatancinsu suna dariya, sai ta juyamusu baya don duk ta tsargu. Basu jima da hakan ba sai ga Hajiya Babba ta shigo. Suka amsa sallamarta, ta shigo ciki sosai. Daman tasan hakan zai iya faruwa, ta daure fuska. "Ke kuma mene na kwanciya a k'asa? Tashi ki hau gado. Ku kuma kuna ganinta ku ka kyale?" "Ita ta za6i nan fa." Cewar Baraka. Harara kawai ta samu daga Hajiya Babba wanda yasa ta jan baki ta yi shirun dole. Ba ita ta bar dakin ba saida ta tabbatar Ummi ta hau gadon, kafin ta juya harshe ta gargadesu sosai sannan ta fice. Ummi dai tun tana jin hirarsu har mijin Baraka, Sa'ad ya kirata suka hau hira, sama-sama ta ke jinsu har bacci ya yi awon gaba da ita. Washegari....

Post a Comment for "DAN ADAM CHAPTER 22"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...