DAN ADAM CHAPTER 13 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

DAN ADAM CHAPTER 13

DAN ADAM CHAPTER 13

- - Post a Comment
DAN ADAM CHAPTER 13  KADUNA+ Dija tuni ta kammala dukkan abinda aka sanyata, zaman jiran sakamakon kawai takeyi wanda hakan ya soma faruwa domin a yanzun koda bata fito ta karya ba, Deen da kansa ya ke aika su Tasleem kiranta. Yau ta kama ranar talata, misalin daya Munira ta fice domin daukosu. Tana zaune tana karanta sakonnin Raihana wanda ya kasance naci ne ta ke mata tana rok'on ta rik'e alk'awarinta. Banda tsaki babu abinda ta ke ja duk da cewar zuwa yanzun Raihana ta dan burgeta bisa taimakon da ta yi mata akan Masoyinta. Tsayuwar motar da ta ji ne yasa ta saurin mik'ewa, jikinta ya gama bata Deen ne ya dawo cin abincin rana don Munira sau da yawa sai wajejan uku ta ke shigowa gidan. Tana lek'awa kuwa ta hangeshi, da sauri ta saki labule. Ta k'ara gyara zaman rigarta k'arama wacce ta tabbatar ta fiddo komai na jikinta. Babu laifi Dija na da kyau daidai gwargwado, bata da k'iba sosai, ba kuma ta kasance cikin masu rama ba, bak'a ce, dogon hancinta da fararen idanunta ne suka taimaka matuka wajen k'awata fuskarta. Tana da dirin jiki daidai. Da kanta ta isa ta bud'e mishi k'ofa. Idanunsu suka tsarku cikin juna, ya ji wani abu ya dakeshi. Kwanaki biyu kenan yana fama da tunaninta da kuma wani shauki na soyayyarta wanda ya ke jin zai iya mutuwa idan har bai sameta ba. Ta kasheshi da murmushi wanda ya kara rud'ar da shi. Ya bi jikinta da kallo sannan ya sauke ajiyar zuciya. "Sannu da zuwa Deen." Ya amsa da sauri yana kallonta. Ta ba shi hanya ya wuce, ta rufe kofar ta koma ta zauna a falon. Babu jimawa da shigarsa daki ya fito. "Sannu Dija, kin ci abincin ne?" Ta yi dariya a ranta, shakka babu aiki ya soma ci. A fili ta danyi kasa da kanta. "A'a, bana iya ci ni kadai ina jiran su dawo ne." Ya zaro ido. "Haba Dija, sai ki zauna da yunwa? Wannan bai yi ba, yaushe za ki tsaya jiransu alhalin daga nan zata biya kasuwa? Taso maza ki ci abinci please." Ta girgiza kai tana jin dadi a zuciyarta kamar zai kasheta, yau Deen ne ke rarrashinta haka? Ai ji ta yi wani kaunar Raihana na kwararuwa cikin zuciyarta. Gudun kada ta yi saurin bayar da kai ne yasa ta ce "A'a, zan bar..." "Ki bar me? Lallai nima kinaso na juya da yunwata kenan." Ta zaro ido tana dubansa fuskarta dauke da murmushi. "Ina zan so haka? Muje." Ya bita da murmushi sannan suka dunguma zuwa tebur. Da kansa ya ja mata kujera ta zauna tana jin dadi a ranta tamkar ta mike ta daka tsalle. Ya zauna ya yi (serving) dinta shima ya zauna ya zuba nasa sannan ya dubeta da murmushi har lokacin dauke saman fuskarsa yana kasheta da wani irin kallon da tun da suke bata ta6a ganinsa a tare da shi ba sai idan yana tare da Munira. "Bismillah." Itama ta kasheshi da nata salon kallon sannan ta murmusa ta soma ci, tana ci amma ta lura shi sam hankalinsa baya kan abincin. Ta dubeshi cikin alamun tambaya, ya sauke ajiyar zuciya. "Kinga nakasa cin abincin ko? Naga kinmin kyau ne." Ta yi dariya. "Kai Deen, ba fa wani kwalliya nayi ba." Ya kashemata ido d'aya. "Anya? Kamar kin yi kurkur kin shafa jan baki da kwalli, haka nake ganinki a idona." Suka tuntsire da dariya lokaci guda. Ta shagwa6e fuska. "Abin har da tsokana?" Ya yi dariya gami da lakuce hancinta. "Ba zancen tsokana." Ta yi soror tana dubansa, tamkar fa a mafarki ta ke gani, anya kuwa ba mafarkin bane? Cikin dabara ta kai hannu ta mintsili fatar hannunta. "Wash!" Ta fad'a a fili, a rikice ya dubeta. "Meyafaru?" Ta dan dara. "A'a bakomai, gaskiya ka ci abinci idan ba haka ba nima zan daina ci." Ta karashe gami da ture farantin, ya maida mata filet din gabanta. "Na tuba, zan ci. Don Allah karki fasa ci." Sukayi dariya suka hau cin abinci. A ran Dija murna fal ya cikata, ashe akwai sauk'aki'yar hanya da zata samu zuciyar Deen amma ta tsaya shirme da wahala? Deen ji yakeyi kamar ya rungumeta don tsabar so da kauna, bayan sun kammala ta rigashi mikewa ta koma falon, ya bita da kallo cikin shaukin so. Da biyu ta koma falon tasan dole ya bita da kallon. Wayarta ta janyo ta tarar da missedcalls har goma, kasancewar a (Vibration) ta sanyata ne yasa basu ji k'arar ba. Ta dauka ta duba, duk daga Raihana ne, dogon tsaki ta ja, tabbas Raihana dagaske ta ke. Kafin ta yi yunkurin ajiye wayar kiran ya k'ara shigowa. Saida ta waiga bata hangi Deen ya taho ba sannan ta d'aga. "Ina jinki." Raihana ta marairaice murya ta hau yi mata magiya akan ta sanarmata dalilin da yasa ta k'i d'aga wayarta da wuri. Wani bakinciki ya tokare zuciyar Dija, sa'ar da Raihana ke ci awajenta bai wuce na ita din itace silar taimakonta wajen samun Deen ba. Ta daure ta 6oye 6acin ranta. "Kiyi hakuri, ina tare da Deen ne." Wani bakinciki da kishi ya turnik'e zuciyar Raihana, ta daure ne kawai don tana taya masoyiyarta son abinda take so. Ta daure ta ce. "Allah Sarki, ya ji dadinsa tunda yana samun kulawar da bansamu ba." Dija ta ji kamar ta shak'eta. Motsin da ta ji na Deen ne yasa ta fadin. "Zan kiraki karki k'ara kirana." A hankali yanda bazai ji ba, wannan muryar ta k'ara kashe Raihana da dadi. (Wa'iyazubillah) ji ta yi kamar ta shiga wayar ta rukunkumeta, dole ta yi mata sallama ba don taso hakan ba. Deen ya karaso, ya kammala shirinsa zai koma ofis, ya dubeta lokacin da ta ke k'ok'arin ajiye wayar. Suka yiwa juna murmushi. "Har zaka koma?" Ta tambaya cikin kankan da murya. Ya gyada kai. "Zan koma, ga shi basu dawo ba kamar kada na tafi nayi zaman tayaki hira." Ta kasa jurewa ta dubeshi fuskarta na nuni da tsantsan farin ciki. "Wai don Allah kaine kuwa? Ashe akwai ranar da za ka nuna kulawarka a kaina har haka?" Sai kuma ta yi shiru a tunaninta ta yi azar6a6i, amma sai bai bata kunya ba ya amsa. "Idan ban kula da ke ba ai bazan iya kula da kaina ba kenan Dija, bakisan yanda nake jinki a zuciyata ba wallahi." Ta lumshe ido don jin dadin maganarsa gami da murmusawa. "Nagode Deen, yanzu kayi hakuri ka tafi ofis, ai idan ka dawo ina gidan." Ya nok'e kafad'a kamar wani k'aramin yaro. "Aa." Sukayi dariya. Ya kar6i lambar wayarta don a baya ba shi da, sannan sukayi sallama. Ai yana fita ta hau doka tsallen murna, daga wancan kujerar sai wannan tana yi tana dariya. Ba ita ta nutsu ba saida su Munira suka dawo bayan la'asar alokacin har kiranta saida ya yi suka sha hira. A gefe Raihana na faman jaddadamata cewa ta rik'e amana ta cika alk'awari ta yanar gizo. Banda toh babu abinda ta ke cewa a fili kuwa ta ja tsaki don haushi. *** *** *** ABUJA KB ya ji haushi matuk'a akan abinda Faruk ya yi mishi, kuma ya tabbatar muddin ya ce zaiyi wani yunkurin na daukar fansa, to fa Faruk ba karamin aikinsa bane ya tona mishi asiri. A karshe ma sai ya ga menene abin tayar da jijiyoyin wuya akan wacce yasan ya ketare a komai, saidai ya fahimci tabbas akwai wani abun a zuciyar Faruk akan Ummi. Ya yi murmushi a yayinda ya ke kwance saman kujera da misalin karfe uku na rana. 'Baka san wacce ta dace da wacce bata dace ba Faruk, duk abina bazan ta6a ajiye 'yar aiki a matsayin matata ba. Zubda aji kawai.' Ya ayyana a ransa sannan ya ja tsaki a karshe ya shafi goshinsa wanda ya kumbura ya yi dariyar da shi kadai yasan manufarsa.1 Misalin takwas na dare, gidan babu kowa sai kalilan cikin iyaye da kuma yan aiki, sauran duk an tafi raka Amarya Baraka gidan mijinta. Amina na hanyarta ta komawa sashensu bayan ta yi aikin da Hajiya Babba ta sanyata na watsawa gaba daya jikokin nasu ruwa da sanyamusu kayan bacci, ta gyaresu tsaf ta shafa musu hoda sannan ta barsu anan falon k'asa suna kallon(Cartoon), alokacin Faruk ya sauko da zummar neman mai kira mishi Ummi, cikin sa'a ya had'u da ita, ita kanta Amina saida gabanta ya fad'i. 'Ina Ummi ina wannan babban goron? Tab!' Ta ayyana a ranta, a fili kuwa durkusawa ta yi ta kwashi gaisuwa ya amsa yana mai dubanta. "Lafiya, idan kin shiga ki cewa Ummi ta sameni a inda muka had'u jiya." Ta amsa da to sannan ta bar wajen, tana shiga ta tarar da ita sai faman danne-danne takeyi a wayar ita Aminan, Amina ta kwace tana jan tsaki. "Kefa yanzu sai ki hargitsamin ita, ya kamata ki koyi sarrafa waya sai bala'in son wayar amma babu abinda kika iya ciki." Sukayi dariya, Amina ta bar dariya, fuskarta ya nuna alamun damuwa da kulawa. "Ummi ke din kina da babban matsayi gareni wallahi, ina son don Allah ki kula ki kuma dauki dukkan abinda na gayamaki. Nasan tabbas kina son Faruk shima kuma yana sonki , saidai ki dunga tunanin ke wacece ki kama kanki. Yanzu ki tashi ki je yana kiranki, yace ki sameshi a inda ku ka had'u jiya." Ummi ta yi dumm ta tabbatar dukkan abinda Amina ta fad'i gaskiya ce, hakazalika kauna ce ta sanya ta kwa6arta. Ta jinjina kai tare da yin murmushi. "In sha Allah Anti zan yi aiki da shawararki. Daman nima ina tsoron shiga kowace matsala adalilin Yaya Faruk." Amina ta yi murmushin jin dadin irin wannan matsayin da ta samu wajen Ummi wacce a shekaru bai fi biyu ko daya ta bata ba. "Nagode Kanwata, sai kin dawo." Daga haka Ummi ta zura hijabinta ta fita bayan ta duba babu wanda ya ganta. Kai tsaye wajen (swimming pool) na gidan ta nufa ta murda kofar ta shiga. Zaune ta sameshi yana waya, ya juyo yana dubanta yana cigaba da wayar, alama ya yi mata ds ta rufe kofar, hakan yasa ta juyawa gami da rufewa, itama zata fi son hakan kada wani ya iskesu tare. Tana kokarin durkusawa ya ja hijabinta hakan yasa ta dubansa. Da ido ya yi mata alama da ta zauna gefensa akan daya kujerar. Ta numfasa gabanta na dukan tara-tara ta zauna. Ko kamshin turaren Faruk ta ji, takan ji sauyi a jini da tsokarta, ballantana akai ga jin muryarsa da kuma kallonsa. Tunda ta zauna bata dubeshi ba, shine ma ya karkato yana amsa waya yana karewa fuskarta kallo. Ga dukkan alamu da ogansa awajen aiki ya ke magana, ganin yanda ya ke bawa mutumin girma hakazalika batu ne na kudade da wasu takardu sukeyi. Maganarsa tafi yawa da harshen turanci. A jikinta ta ji yana kallonta, ta dan juyo ta saci kallonsa, ya kuwa kafeta da ido kafafunsa saman kujerar ya tankwashesu. Ta kauda kanta ta yi shiru, ji ta ke tamkar ba zata iya rabuwa da Faruk ba, saidai hakan dole ne agareta, ko ta karfi ko kuma ta lumana. Ta karfin kuwa, daga yan uwa da danginsa ne, wadanda a karshe zasu ci zarafinta su korata kauyensu, ta lumanar kuwa shine ta bi shawarar Antinta wanda idan har ta kiyaye to fa baza'a kai ga sauran matakan ba masu ciwo. Saida ya kammala wayar sannan ya ce. "Bari kiga na kashe wayoyinnan, ko waye zai k'ara nemana saidai ya hakura na kammala da iyalina ko?" Kanta ya yi dumm, jin kowanne kalamansa ta ke yi tamkar sun fi gwal da daham tsada a wajenta. Da a bata komai na jin dadin rayuwa ta gwammace a mallakamata Faruk a matsayin mijinta, saidai me? Wutsiyar rak'umi ta yi nesa da k'asa. Tunaninta ya katse sa'ilin da ya dora wayoyinsa a saman cinyarta. Ta dago ta dan dubeshi fuskarsa babu alamun wasa hakan yasa ta maida kanta ga duban wayoyinsa biyu manya wadanda ta tabbatar masu tsada ne saidai hankalinta yafi karkata ga son son jin abinda zai fito daga bakinshi. Ummi, ina muka kwana a zancenmu na jiya? Abin nufi me kika fahimta da yanayin da muke ji game da juna a zukatanmu?" Ta girgiza kai ta daure ta ce. "Babu."+ Ya yi wani murmushi. "Ai nasan zaayi haka." Ba ta ce komai ba, shi kuwa saida ya ja fasali sannan ya cigaba da magana. "Kin sani kamar yanda na sani Ummi, amma mu ajiye wannan a gefe." Shiru ya dan biyo baya kafin ya dora. "Bani tarihin rayuwarki idan da hali." 'Rayuwata?' Ta yi tambayar a ranta. Ganin ta yi shiru ya k'ara magana. "Look Ummi, ki saki jikinki da ni please, ba ma ke ba, ni kaina ban yi sabo da hakan ba, sai kin zauna da Faruk za ki fahimci ko waye shi. Ban fiye sakin jiki da mutane na yi hira har haka ba, da dai cikin brothers na ne ko Hajiyata. So please Ummi ki min alfarmar nan, ki saki jiki da ni, ina so nan gaba ma mufi haka kusanci kinji ko?" Ya k'arashe cikin rad'a gami da yin murmushi mai sauti, baiwar Allah idanunta suka cika da kwalla, ga samu ga rashi. Tana son abinda ba za ta ta6a samunsa ba don a yanzun da ya ke magana ji ta ke yi tamkar ana k'ara rura mata wutar kaunarsa. Bata ba shi amsa ba face ta shiga labartamasa labarinta iyakar wanda ta sani banda wanda batasani ba kuma bata ta6a samun labari ba, wato na zamantakewar mahaifinta da mahaifiyarta. To mai labarta matan ma ba shiga sabgarta ya ke yi, bai dauketa matsayin 'ya ba. Tiryan-tiryan ta ke bashi labari tana yi tana zubda ruwan hawaye har ta kai yanda aka kawota aikatau. Tana kaiwa karshe ta cigaba da kuka mai kona zuciya, ba don komai ba sai tunanin rashin gatanta da kuma na son abinda ba zata ta6a samu ba. Tattausan hannunsa ta ji a saman kumatunta yana share mata fuska, baki ta saki tana kallonsa, ba kwayar idanunta ya ke kallo ba, kyakkyawan farar fatarta ta ke kallo yayinda ya cigaba da magana yana murmushi mai kama da yak'e, fuskarsa dauke da damuwa da tausayi. "Kinzo inda za'a share miki hawaye da taimakon Allah, idan har Faruk na numfashi, in sha Allah zai zame miki haske a rayuwarki. A yanzu ta bakinki nake son ji." Sai lokacin ya dubeta, ita kuwa idanunta a lumshe suke sakamakon yatsunsa da ke akai yana sharemata kwalla. Daidai lokacin kuma ya dauke hannunsa daga kanta. Ummi bugun kirjinta k'aruwa kawai ya ke yi, ita dai bata ta6a jin yanayin nan kan kowa ba sai shi, ta kasa dubansa, anya kuwa zata iya daukar shawarar Antinta Amina? Kai, dole ta dauka don Antinta ba zata cuceta ba. "Kin yarda kin amince mu k'ulla alak'ar da zata kai mu ga AURE? Ta wannan hanyar kadai zan iya taimakon rayuwarki Ummina." Kamar ta tashi ta ruga a guje ta ke jinta, Faruk dama ya muryarsa ta ke wajen sanyi kamar mace ballantana kuma yana cikin yanayi na shaukin so da kauna. Ta dan matsa don rage kusancin da ya yi mata. "Kayi hakuri, ni babu wani abu da nake ji game da kai, ban dauke ka komai ba sai dan uwan Yaya Adnan kuma iyayen gidana, ka yi hakuri, bazan iya jefa zuciyata cikin abinda zan wahala ba." Daga haka ta kwashi wayoyinsa ta mik'a mishi, saidai ba shi da niyyar kar6a, asalima idanu ya zubamata yana murmushi. Ganin haka yasa ta ajiyewa a kujerar da ta mik'e zata tafi. "Ji mana." Ta tsaya cak gami da juyowa. Ya dauke wayoyinsa ya dubeta. "Dawo ki zauna." Ba musu ta dawo ta zauna tana share hawayen saman fuskarta. Ya dawo ta gabanta ya durkusa. "Hey, kalli tsakar idanuna ki ce ba ki amince ba." Ta kauda kanta tana jin tamkar ta fashe da kuka gaba daya ita ta gama tsorata ganin Faruk dagaske ya ke babu wani sassaunci. "Ummi say something please, ki ce wani abu mana." Ya fada cikin shagwa6a66iyar muryar da bai fiye amfani da ita ba sai ko a gaban Hajiyarsa. Ta girgiza kai. "Ni ban amince ba." Ya dubeta na sakanni ya na murmushi. "Dagaske ba ki amince ba?" Ya fad'a yana mai kwaikwayon muryarta, abin ya so bata dariya ta kuwa saki murmushi. "Masha Allah, ko kefe. Naji wannan kuma nagode, amsa tuni na sameshi, hirar ce nakeson muyi don bakisan yanda nakejin dadin ganinki bane." Shiru babu wanda ya k'ara magana, can kuma ya sauke ajiyar zuciya ya kunna wayoyinsa. "Goma har ta kusa." Ya fad'a yana duban wayar, can kuma ya mik'e ya sanya wayoyin a aljihun wandonsa, ya yi amfani da tafukan hannayensa ya dafa gwuiwarsa gami da sunkuyowa yana dubanta. "Saida safe." Ta gyada kai sannan ta gifta ta mike tsaye da sauri don daman tun dazu ta soma jin tsayuwar motoci a harabar gidan ta tabbatar yanzun su Mami sun iso. "Allah Ya tashemu lafiya." Daga haka ta yi gaba da sauri, koda ta isa ga kofar saida ta kasa jurewa ta juyo kanta ta dubeshi, shi ba shi ma da niyyar barin wajen don komawa ya yi ya zauna. Su ka yi ido hud'u da shi, ta dauke kanta da sauri-sauri ta bar wajen tana ji yana fad'in. "Ko na zo ne?" Bata ko juyo ba balle ta tanka mishi. Ya yi murmushi karo na ba adadi sannan ya kwantar da kansa jikin kujera, kai tsaye hotonta ya lalubo wanda ya yi mata a wata rana da ta ke zaune tana wanki a (garden) da kuma na zanen da ya yi mata. "Ke tawa ce in sha Allah." Ita kuwa Ummi tana isa ta tarar tuni Amina ta soma gyangyadi, ganinta ne ya farkar da ita, ta tashi zaune tana kallon Ummin na rufe k'ofa. Binta kawai ta ke yi da kallo jin kamshin turaren da ke tashi a jikinta wanda ta tabbatar na Yaya Faruk ne. Ta cire hijabin ta ajiye saman katifar. "Sai yanzu?" Murmushin yak'e Ummin ta saki. "Eh." Ta zauna ta dan labartamata abinda tasan zata iya. Ta karashe da fadin. "Saidai Anti ban gane manufarsa ba na cewa ya samu amsarsa. Me hakan ke nufi?" Amina ta yi murmushi. "Allah Sarki, na tausayamuku, ai Ummi shi so ba ya 6oyuwa. Ki daure kada ki bari naki ya fito don Allah, bana son ya sanyaki a matsala domin Allah ne shaida bana kaunar ki k'ara dandanar rayuwa irinta baya a hannun matar babanki. Da dai ace shi mahaifinnaki da kansa ya nemeki ne, da babu abinda zai hana ni farin ciki don kuwa shi ne babban gatanki fiye da sauran yan uwa. Kiyita addua akan Allah Ya yi miki za6i kan lamuranki." "Amin Anti." Ta fada jiki a sanyaye sannan suka soma shirin kwanciya. Ta juyawa Amina baya ta lumshe idanunta, tunanin Faruk da kalar soyayyarsa mai saurin kashe zuciyar diya mace ta ke yi, a gefe ta tuno Ihsan ta ji ta tausayamata don bata samu wannan damar da ta samu ba. Ta tsinci kanta da rungumo hijabinta tana mai shak'ar daddad'an kamshin Faruk da ya mamayeshi wani ma sai ya dauka ko rungumarta ya yi. Tana tsananin son Faruk, ita tasan da hakan. Dakyar bacci ya sureta sakamakon tunane-tunanen da ta dunga yi akan Faruk Danzaki har ya kaita da mafarkinsa. Wai har sun yi aure. Abin ma ya bata dariya da ta fark Misalin karfe takwas na safe, yan uwan junan ne kadai a dakin, (wato Hajiya Babba, Hajiya Mama da kuma Mami) suna zaune suna hira, wayar Mami ta soma k'ara, ta d'aga tana mai dubawa. Kiransa kusan na takwas kenan ta k'i d'agawa, wannan karon ma shiru ta yi. Hajiya Mama ta dubeta. "Wai wa ke kiranki haka ne?" Mami ta yamutse fuska. "Abban Adnan ne fa." Mamaki ya kamasu. Hajiya Babba ta ce. "Haba Madina, sai kace wata yarinya k'arama, komai ya yi miki a rayuwa sai kiyi hakuri. Kiyi tunani da kyau, iyakar zaman da ku ka yi da Muhammad, ba ku ta6a samun makamanciyar wannan matsalar ba. Tashi guda ya chanja miki har haka..." Maganar Hajiya Babba ta katse sa'ilin da wayar ta k'ara daukar k'ara. "Ki dauka." Mami wacce jikinta ya soma sanyi da maganganun Hajiya Babba, ta dauki wayar ta kara a kunnenta da sallama. Muryar mijinta radau a dodon kunnenta ya na amsa mata. "Guduna kike yi ko Madina? Shiyasa kika k'i d'aga wayata." Ta numfasa tana duban yayyunta da hankulansu ke kan hira akan ire-iren tuggun makiran kishiyoyi. "Ya zaayi na gujemaka? Bana kusa ne." Ya ji dadin maganar, tun bayan tafiyarta ya soma gano kuskurensa. "Madina kenan, yaushe za ku dawo?" Ta yi mamakin jin yanda ya ke wani sassauta murya ga dukkan alamu dai ya soma saukowa. "Zuwa gobe nake son dawowa." Cike da farin ciki ya amsa. "Yauwa don Allah ki dawo a goben, ina da muhimmiyar maganar da nakeson muyi kuma nayi kewarki fiye da zatonki wallahi." Mami murmushi ta yi, lallai babu abinda ya fi karfin Ubangiji, a yau idan Ya so sai ya chanja lamura yanda ya ke so. "Shikenan, ayi mana adduar dawowa lafiya." Daga nan bayan ya dan ja ta da hira ya tambayi yaransa a karshe ya nemi ta hadashi da su Hajiya Babba su gaisa, Hajiya Babba kadai ta amshi wayar, ita kuwa Hajiya Mama sam ta k'i kar6a don har lokacin ta na jin haushin irin cin kashin da ya yiwa 'yar uwarta. Bayan sun ajiye kan wayar ne nan Hajiya Babba ta yita yi mata nasiha gami da gwadamata akwai wani abun amma ba halin Muhammad Modibbo kenan ba. Mami maganganun sun shigeta hakanan itama ta yi na'am da hakan. "Ki yawaita addu'a Madina, shima ki yi kokarin nusar da shi hakan idan lamuranku sun daidaita. Yanzu ita 'yar aikin ta ki maidata zakiyi?" Mami ta girgiza kai. "Gaskiya inajin dadin ayyukanta, sannan muddin na maidata ma ai burinsu ya cika, abin yi shine zan barta anan gidan Inna har lokacin da zai sauko na maidota." "Wannan shawara ce kam." Cewar Hajiya Mama, Hajiya Babba ta ce. "Ai ni da kin dan barmin ita na kwana biyu kafin na sami madadin Sa'a sai ta dunga yin ayyukanta."+ "Hakan ma ya yi ai Hajiya, sai su taho da Ihsan. Na lalla6a dan nawa naga ko zai bini mu tafi ko aa. Wai me Sa'a ta yi ne ni kuwa?" Fadin Mami. "Shine nima nakeson tambaya ki ka rigani." Cewar Hajiya Mama. Hajiya Babba ta murmusa. "Aikin d'anku ne, shi ta yiwa laifi shine ya koreta." "Wa kenan?" "Faruk." Sukayi dariya. "Lallai laifinta bai girma ne da ba haka ba na tabbatar a tausayi irin na Faruk bazai koreta ba." Suka jinjina kai jin abinda Hajiya Mama ke fad'i. Dakyar hirar ta watse sakamakon Amina da ta shigo ta sanarmusu an kammala shirya abinci. Suka mike suka fita. Washegari kuwa tun safe mutane suka soma tafiya, yan Adamawa kaf dinsu suka fice, Gwaggo surukar Mami bata zo wannan karon ba saidai ta aikowa Mami tsaraba hakanan ta aikowa Hajiya Babba gudunmuwa.

Post a Comment for "DAN ADAM CHAPTER 13"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...