Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

DAN ADAM CHAPTER 10

DAN ADAM CHAPTER 10

- - Post a Comment
DAN ADAM CHAPTER 10
Daren daga Adnan har Ummi babu wanda ya yi bacci isashshe, gaba daya hankalinsu ya tafi ga Mami wacce basusan dalilin damuwarta ba. Hakanan ta yi abinda shi Adnan tun tasowarsa bai ta6a gani ba, wato ta baro sashen Abba aranar (duty) dinta, abu ne da bai ta6a faruwa ba saifa a yau. Itama Ummi abinda ya dauremata kai kenan, domin tunda take agidan tsawon wata daya da kwanaki bata ta6a ganin Mami ta kwana a sashenta ba alhalin Abba na garin kuma itace da aiki. Inaga mai gayya mai aikin, wato Mami, wacce kwana ta yi tana kuka tana kai kukanta ga Mahaliccinta. Ta kasa zaune ta kasa tsaye, idan ta runtse ido babu abinda ke fad'omata a rai sai tsawan da Mijinnata ya dakamata a sadda ya nufeta da niyyar runguma ya rarrasheta ya nunamata dazun da gaske ya ji wari da baisan dalilin wanzuwarsa ba a tattare da ita. Yana jin warin kuwa ya tureta da k'arfi gami da jan tsaki. Ta matso da nufin tambayar ko lafiya, ya yi azamar matsawa gefe gami da dakamata uban tsawa akan kada ta kuskura ta k'araso inda ya ke. Haka ya kyaleta ya fice daga dakin, ta jima anan tana kuka, har ta ji maganarsa inda ya ke bata umarni kan ta fita zai kwanta. Haka ta tashi ta fito nan ma hancinsa a toshe har wani runtse ido. Haka ta k'araci zamanta a falo, ganin babu Sarki sai Allah yasa ta mik'e ta bar masa sashennasa. Mami ta numfasa ta kwanta lamo saman filo, a iyakar rayuwarta da Muhammad, matsala makamancin haka bai ta6a shiga tsakaninsu ba. Kullum cikin yabonta yakeyi musamman a 6angaren kwalliya da tsafta. Ayau ga wani sabon lamari ya 6ullomata. Washegari da safe Ihsan ta yi mamakin ganin Maminta a d'aki, koda ta gayamata, bata 6oyemata cewar ga abinda Abban yace tana yi ba. Ihsan har kuka ta yi ganin yanda Mamin ke hawaye. Ta girgiza kai. "Allah kuwa Mami kawai wani abin ne na daman Abba ya 6ullo da shi, amma babu wani abu da na ji ajikinki, asalima wani bala'in kamshi kikeyi." Murmushi kawai Mamin ta yi, cikin dauriya ta dubi 'yarta. "Nagode, ki tashi ku je kada kuyi latti." Haka dai Ihsan suka fice duk jiki babu kwari. Daidai da yan uwansu sun lura yau yaran dakin Mami basu da walwala. Hassana d'iyar Anti Amarya, wacce basu fiye daukar kishi zazzafa ba akan yan uwansu, ta tambayi Ihsan ko lafiya. Ihsan ta nunamata babu komai hakan yasa dole suka dan saki jiki gudun wata tuhumar. Acan gidan kuwa, Ummi ta kammala komai na gyaranta a sashen yara sannan ta fad'a sashen Mami da sallama. Bata falon, ta hau gyara saida ta gama sannan ta lek'a d'akin. Duk a zatonta Mami na bandaki wannan yasa ta juya da zummar sai ta kammala zata dawo. Ji ta yi an kira sunanta, ta juya da sauri ta dubi gadon tana mai amsawa. Can ta hangeta ta dukunkune cikin bargo tana faman rawar d'ari. Ta karasa ta russuna ta gaisheta. Kai kawai ta gyada. Murya na rawa tace "Kashemin fanka." 'To." Ta amsa gami da mik'ewa da sauri ta aiwatar, ta dawo ta durkusa. "Sannu, a kawomiki kari nan?" Dan yamutsa fuska ta yi ta cire yatsa ta yi mata nuni da dirowar gefen gadon. Cikin rawar muryar dai ta ce. "Duba ki daukomin Paracetamol." Koda batasan (spelling) din ba, tasan maganin, ta bude ta hau bincike cikin sa'a kuwa ta samu ta ciro. Ta taimakawa Mamin kamar yanda ta buk'ata ta mik'e zaune. Saida ta sha maganin sannan ta koma ta kwanta. "Ki yi aikinki." Cewar Mami a sanyaye. Ummi ta mik'e ta hau aikinta, tana yi tana kallon Mami wacce itama tun tana dubanta m, jefi-jefi tana goge kwalla har bacci ya dauketa.1 Kamar wasa, karamar magana ta zama babba. Tun Mami na ganin lamarin a kanta ita d'aya, har ya soma shafar yaranta. Abba ya chanja musu, ko gaisheshi suka je to ba fa kamar da ba, a yanzun ko yana cikin fara'a suka shiga to fa zai tamkemusu fuska, ya zamana Hajiya Madina bata da girki, abin kuma mamakin bai wuce ganin matan sun had'emata kai ba kamar ma sunyi farinciki da hakan. Idan yaran suka tafi makaranta, Mami haka zata zauna da Ramma da Ummi tana nuna damuwarta a fili don tun tana 6oyuwa har zuciyar ta kasa d'auka. BAYAN WATA D'AYA Rayuwa ta yi musu kunci, ayau Ummi suna zaune da Mami a falo suna sauraron rediyo, Adnan ya shigo rai babu dad'i ya zauna d'abas saman kujera yana kunkuni. Mami bata saurareshi ba sai bayan da ta kammala sauraro, ganin an kammala Ummi ta kyalesu su zanta. Ta dubeshi, gaba daya ya bata tausayi ganin yanda ya rame, wannan wasa da dariyar tasa duk ta ragu. "Ya akayi d'an Abba?" Ji ya yi kamar ta watsamasa garwashi a zuciyarsa, a yanzu babu wanda ya ke tsananin jin haushi kamar mahaifinsa, ko hanya ya k'i jinin su had'u. Ya k'ara tamke fuska. "Please Mami ki bari." Mami ta yi murmushi, ita kanta ta rame matuk'a, a baya Mami ba dai ta zauna ta yi hira da su Ummi ba, halin rayuwa yasa duk ta yi sanyi don har Ummi tana bawa ta yi mata sadaka a kofar gida. Hakanan gaba daya sun dage da addu'a, ko ta ji kamar ta sanarwa iyayenta sai wata zuciyar ta hanata, gani takeyi kamar ba jimawa komai zai yanke. "Shikenan, gayamin, meyafaru na ga ranka a 6ace?" Ya numfasa gami da cizan le66ansa na k'asa. Dakyar ya k'ok'arta ya yi magana. "Zan bar gidannan Mami." Gabanta ya fad'i ta zaro ido tana ambaton Innalillahi a ranta. "Kamar ya za ka bar gidannan Adnan? Meya faru kuma?" Ga mamakinta, hawaye kawai ta ga ya soma. Hankalin Mami ya tashi yaronnata akwai hakuri da dakiya, sai ta iya k'irga sau nawa ta ga kukan Adnan tun tasowarsa. Ta yi shiru lokacin da ya katse tunaninta inda ya soma magana. "Wai yau ni Abba ya kira da zargin nayi mishi sata, wai jiya da dare bayan na fito ya yimin fad'an ya fasa turani k'asar waje karatu shine da safe ya laluba bai ga wasu kudadensa da ya bari a falonsa ba, shine yau ya kirani akan wallahi sai na fito mai da kudinsa har Umma na fadin tabbas ta ga sadda na fita wai ina gyaran aljihu. Ni bazan iya rayuwa a gidannan ana tafiya haka ba, na gaji Mami, zan yi nesa da ku." Yana kaiwa nan kawai sai ya cigaba zubar kwalla har yana sheshshek'a. Idan hankalin uwar ya yi dubu to ya tashi, duk a lamarinnan, bata ta6a kuka gabansu ba sai a yanzun. Kuka sosai ta shiga yi, yau Mijinta Modibbo ne ke kiran d'anta da sunan 6arawo, wane irin tashin hankali kenan ya ke faruwa dasu? Jin kukanta ne yasa Ramma da sauri ta fito daga kicin harma da Ummi wacce itama ta ji hankalinta ya yi tsananin tashi. "Hajiya lafiya?" Cewar Ramma. Adnan ma kukan yakeyi babu mai bawa wani hakuri, karshe a fusace ya mik'e ya fita daga falon. Ummi tuni ta soma kukan itama, Ramma da jiki ya gama sanyi ta karasa ga abinda uwardakinta ta russuna. "Haba Hajiya, haba, idan kina haka agaban yarannan sai ki karyamusu zuciya, komai na rayuwa idan ya samu bawa hakanan ya ke hakuri ya dangana. Addu'a kadai ce mafita, duk wannan fa bazai sanya abubuwa su chanja ba sai addu'a." Mami ta jinjina kai idanu a kod'e ta dubi Ramma. "Yanzu har yakai Alhaji da soma zargin d'ansa da sata?" Abinda ta fad'a ya yi mugun kad'a hanjinsu. Ramma ta hau salati, ita kuwa Ummi daskarewa ta yi kukanma ya kasa fitowa. Basu kai ga samun abin fad'a ba suka ga Adnan ya shigo goye da k'atuwar jaka fuskarsa duk ta kumbura. "Zan wuce Mami." Daga haka ya yi gaba, Mami ta mik'e tsaye da azama gami da dakatar da shi ta hanyar kiran sunansa. "Adnan." Ya tsaya gami da juyowa, ta tako har wajensa tana dubansa cike da tsananin tausayi. "Ka yi hakuri, bari naje ga mahaifinnaku." Ya girgiza mata kai da sauri, cikin tsananin fushi da daga murya ya soma magana. "Sai kiyita zuwa yana wulakanta mana ke Mami? For what reason?!! Idan har don ni za ki ki barshi, kudi da yace na dauka, ga wayata can da Laptop zan aiko a kar6a a siyar..." "Kasan abinda ka ke fad'a kuwa? To kada ka soma, na gayamaka ka tsaya bari na je ga Abbannaka." Mami ke maganar a fusace kafin a karshe ta sassauta, daga haka ta giftashi ta zura silifas dinta ta yi gaba, daman da mayafi jikinta, idar da sallar walha kenan ta zauna jin rediyo.... Mami ta isa har k'ofar sashen Abba cike da jin kwarin gwuiwa, hakanan ranta a tsananin 6ace, ayau ta gaji, saidai ayi wacce za'ayi kawai. Ta murd'a k'ofar da sallama ta tura kai ciki. Rabonta da turakar maigidan nata wata daya da satittuka kenan, dariyar Abba da Umma ta katse sa'ilin da sallamar Mami ya ratsa dodon kunnuwansu. Abba nan take ya daure fuska, ita kuwa Umma ta k'ara muskutawa jikinsa kai kace wata yarinya. A hankali ta tako, da sauri ya toshe hanci gami da dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu. "Tsaya anan don Allah!" Ya yi maganar cikin tsananin fusata, ya d'ora da cewa. "Wai Madina meyasa bakya ji ne? Inace na yi miki iyaka da sashena?!" Yana maganar ne kamar zai taso ya daketa ga hancinsa dake a toshe, itama Umman hancinta tosheshin ta yi. "Alhaji agaskiya bazan iya zama ba, ku kammala maganarku tukunna." Umma ta mik'e tana yamutsa fuska kamar gaske, ta shige d'aka, tana shiga ta la6e bayan ta gama kyakyata dariya tana sauraronsu. Mami ta sauke kanta k'asa tana mai fidda gwauron numfashi, DAN ADAM kenan mai saurin manta halacci, tamkar wani abu na kyautatawa a rayuwa bai ta6a wanzuwa tsakaninta da Mijinta ba. Ba tare da ta dubeshi ba ta soma magana, domin kallonsa ma ayanzun kunci ya ke k'ara mata. "Kayi hakuri, na sa6awa umarninka na shigo inda kayimin hani, saidai wannan karon ba zuwan kaina bane, zuwan 'ya'yana ne." Ga mamakinsa sai ya ga ta russuna k'asa. "Domin Allah Abban Adnan, komai da zaka yimin kabar sanya yaranmu ciki, ka cigaba da kyautatamusu kamar yanda kakeyi a baya. Ni..." "Ke sauraramin don Allah!" Ya yi maganar cikin tsawa. Yana zaro ido ya jefamata tambaya. "Wane abu makiran yaran naki suka ce miki nayi musu na wariyar launin fata?" Ta daure ta ciji le66anta, dakyar ta cigaba da magana. "Wani mugun zance naji, wai kana zargin Adnan da yi maka sata. A sanina kafi kowa sanin halayyar danka, bazai ta6a aikata hakan ba." "Toh, kenan kina nufin kice k'arya nayi mishi? Madina ba fa ko isa ki dunga koyawa yarana mugun hali har haka ba. Ki kiyayeni wallahil azim idan ba haka ba zan miki abinda ba ki ta6a zato ba ko a mafarki. Iskancin banza! Don kaza kazansa ni ban isa na hukuntashi ba? Da wannan mugun halin da ya koyo ne ya ke tsammanin zan turashi waje karatu ya lalata yaran mutane? To bazai ta6a yiwuwa ba wallahi, kuma ki amsomin dubu ashirin d'ina idan kuwa ba haka ba, karatun ma kwata-kwata ya jawa kansa bazai yishi ba." Daga haka ya mike yana cigaba da masifa kamar zai ari baki, a haka ya shige daki ya barta durkushe. Mami wacce tun ashar din da ya yi ta girgiza bata iya cewa uffan ba, ta jima anan ta kasa tashi don tsananin tashin hankali, dakyar ta iya mik'ewa ta zura silifas d'inta ta fita. Tana tafe zuwa sashenta tana juya maganganun mijinnata, zuwa yanzun ta k'ara tabbatarwa lallai akwai wani babban lamari. Watakil ko mijin ya soma hauka ne shiyasa abin ya kai har da zagi. A falo ta tarar da Ummi da Ramma sunyi jugum, ta dubesu ta dauke kai tana waige. "Ina Adnan?" Ramma suka dubeta. "Ai kina fita ya wuce, inaga dakinsa ya shiga." Da sauri ta juya zuwa dakinnasa, babu kowa, ta lek'a bandaki nan ba bayanan, akan gadon ta ga takarda ta dauka ta warware ta soma karantawa. "KIYI HAKURI MAMINA, WALLAHI BAZAN IYA ZAMA BA. KADA KI DAMU WAJEN YAYA FARUK NA NUFA WATO ABUJA, MAMI DON ALLAH AYI YANDA NACE, GA WAYOYINA DA LAPTOP A SIYAR A BAWA ABBA KUDINSA KADA KI BADA KWANDALARKI. IDAN NA ISA ZANYI KIRANKI."1 Jin haka yasa ta zauna d'abas saman gadon tana numfarfashi kafin ta soma hawaye. Shikenan farin cikin gidanta ya rushe, ta dauki wannan matsayin jarrabawa daga Allah, ta kuma tabbatar komai yana nan zuwa k'arshe. Hankalinta ya kwanta da jin inda Adnan ya nufa, ko babu komai zai samu kulawa hakanan tasan inda ya ke. Bikin Baraka duka-duka sati d'aya ya rage, itama tana tunanin tattarawa zatayi ta tafi ko zuciyarta ta dan samu nutsuwa idan ta shiga cikin 'yan uwanta. Ta linke takardar ta ajiye gami da kashe komai da ya danganci kayan wuta ta rufe dakin da mukulli ta fito. Ta sanarwa su Ramma cewar Abuja ya wuce su kwantar da hankalinsu. Daga haka ta wucesu zuwa daki. Ramma ta girgiza kai. "Oh, akace zato zunubi amma ina tunanin anya matannan na Alhaji babu sa hannunsu?" Ummi ta yi shiru cike da tunani, kuma mai yiwuwa ne saidai kamar dai yanda Ramman ta fad'a ne, wato zato zunubi ne, hakan yasa ta ja bakinta ta yi shiru batare da ta tofa nata ba. Koda su Ihsan suka dawo sunyi mamakin jin wai Adnan ya wuce Kaduna, saidai Mami ta nunamusu akan abinda ya shafi karatunsa ne. Hakan yasa suka hau murna da tunanin ko Abba ya sakko. A ranar Mami ta saka Ihsan zuwa Atm ta ciro mata dubu ashirin ta kaiwa Abba. Ihsan dai bata da masaniyar ko ta menene, ta ji dai Abba na kiran 6arayin banza da wofi har yana dokamata harara. Sai bayan ta zo da korafin gaban Mami sannan Mami ta rarrasheta gami da nunamata kawai fad'ansa yakeji. *** *** *** Hajiya Binta zaune a falon Hajiya Lubna (Anti Amarya) wacce ita kanta ta dan ji mamakin shigowarta don a yan kwanakin nan ta dauke k'afarta da shigowar, a cewar Anti Amarya ba don komai ta yi hakan ba sai don ganin ta samu kan Alhajin yanamata yanda ta ke so. "Bakya ji dadi ba, na yanda Alhaji ya juyawa 'yar gwal dinsa baya?" Cewar Hajiya Binta kenan tana mai duban Anti Amarya wacce ke danna wayarta. Mace ce gwanin shan kamshi da yanga, shiyasa sau da yawa ta ke k'ular da Hajiya Binta, har a ranta tana yawan fad'in 'Da ace Hajiya Lubna ce ta samu kan Alhajin ba Mami ba, to da gaba daya sun kad'e, domin ta iya daukewa mutum kai ga wulakanci.'+ "Ke kike ganin haka Hajiya Binta, saidai ni ban gano komai ba." Hajiya Binta ta yi mata wani kallo. "Bangane nufinki ba?" Sai lokacin ta ajiye wayar ta dubeta da murmushi saman fuskarta. "Ba nasara a gaba Hajiya Binta, duk abinda za'ayi idan ba na Allah ba, babu inda ya ke zuwa, da dai anyi hakuri an cigaba da yarda da kaddara tunda shi wanda ya ajiyemun yana nunamana kulawa tsantsa da kauna. Amma ina tabbatar miki wannan ba abun murna bane, abu ne na lokaci k'ank'ani."1 Ta danyi shiru ta dora bayan ta gama lura da irin k'uluwar da Hajiya Bintar ta yi da maganganunta. "Ina jiyemana ganin abinda yafi na baya tsakanin Muhammad da Madina anan gaba." A fusace Hajiya Binta ta mik'e. "Ya isheni Malama, na lura ke kin daina damuwa da kayan takaicin da muke kuntsa. Shikenan ai, fatan da kikeyi ba dai ni na ganshi ba, saidai ko ke din. Idan kin k'ara ganina a sashenki ki gasamin wanda yafi wannan." Fuu! Ta fice tamkar akan iska, dariya Anti Amarya ta yi gami da girgiza kai. "Za ki gani ganin idanunki Binta." Ta fad'a a bayyane. Inda Hajiya Lubna ta fi Hajiya Binta kenan, tana da kokarin 6oye sirrinta hakanan bata kauna bin malamai tafi yarda da shaye-shayen magungunan mata, a wannan 6angaren kuwa saidai su tafa da Mami don bazata gwada mata ba. Saidai tasan kaunar dake tsakanin Muhammad da Madina, dad'add'iya ce wacce ko mutum ya yi yunkurin rabasu, to fa a karshe zai ji kunya matuk'a. Ta numfasa, tana da tabbacin uwarmijinsu bata da masaniya akan wannan sauyin lamarin, da tasan yanda d'an nata ya maida 'yar gaban goshinta, da tuni ta yiwa abin tufka. *** *** *** ABUJA Yana tsaye a wajen ajiye motoci a Bankinnasu, lokacin misalin biyar na yamma, dawowarsa kenan daga wani aike da manajansu ya yi mishi, yana kokarin barin wajen wayarsa ta dauki k'ara. Ya yi mamakin ganib lambar dw bai sani ba a kuma layin da mutane d'aid'aiku ya ta6a kira da shi. Jikinsa ya ba shi cewar kowanene wannan, wani na jikinsa ne, hakan yasa ya d'aga da sallama. Daga can Adnan ya amsa, Faruk ya saki fuska. "A'a, k'anina ashe kai ne." Adnan ya gyara zaman jakarsa yana duban cikin tashar gami da yin yak'e. "Ni ne my best, ina Abuja." Faruk ya ji wani dadi har cikin ransa domin yana kaunar yaron, duk kuwa da tazarar dake tsakaninsu na shekaru, yana daukarsa tamkar wani sa'ansa. "A ina kake yanzu?" Ya sanarmishi yana tasha, ya umarceshi da daukar taxi yazo banki ya sameshi. Ya mik'awa mai wayar wayarsa gami da godiya sannan ya kama hanya. Bayan zuwansa saida ya jira Faruk ya kammala sannan suka fito. Faruk ya lura da yanayin Adnan ba mai dad'i bane, ga wata rama da ya yi kamar ba ya cin abinci, har ya kasa hakuri bayan sun hau titi ya tambayeshi ko lafiya. Adnan daman kiris yake jira, kawai sai ya hau kuka, daman tun dazun ya ke cike da tunanin halin da Maminsu ke ciki ga wani dumbin tausayinta. Faruk na ganin haka ya cigaba da tafiya har ya samu wurin fakin ya tsaya. "Ka tayarmin da hankali fa k'anina, meke faruwa ne?" Adnan ya yi shiru, to me kuma ya rage? Dole daman wataran yan uwan su ji abinda ke faruwa muddin Mami ta zo biki ko don yanda gaba daya suka fita hayyacinsu, ya 6oyemasa komai sai abinda Abba ya yi mishi a yau kawai ya sanarmishi. Faruk bai ji dadi ba sam, ya sauke ajiyar zuciya, baiyi zaton Abba zaiyi haka din ba koda a mafarki. Ya dubi Adnan cikin muryarsa sassanya yace "Mami tasan ka taho?" "No, na barmata takarda dai." Faruk ya girgiza kai gami da daukar waya ya dannamata kira. Mami na zaune saman darduma, idar da sallar magriba da gabatar da nafilarta kenan ko mik'ewa batayi ba ta ji wayarta na k'ara. Ta janyo da sauri, Faruk ta gani ta numfasa, daman tun dazun take jiran kira daga wani na Abujan don jin ko Adnan ya isa batason tayarmusu da hankali. Bayan sun gaisa yake sanarmata da isowar Adnan. Farin ciki ya lullu6e zuciyarta. Fuska a sake ta yi hamdala a fili, ta cigaba da magana. "Don Allah Faruk kada ka barshi cikin damuwa, kayi iyakar kokarin ganin ya samu walwala. Nima ina nan zuwa nan da kwana uku da zarar yarannan sunyi hutu." Ya murmusa cikin ransa yana mai tausayinsu, ya gama fahimtar akwai wasu al'amura dake faruwa tare da su duk da suna 6oyewa. "Karki damu Mami, in sha Allah zan yi yanda kikace." Ta yi murna da jin hakan har ta sauke ajiyar zuciyar da hatta Faruk saida ya ji. "Nagode d'ana, Allah Ya k'ara muku albarka." "Amin." Ya mik'awa Adnan. Adnan murya a raunane yace. "Maminaa." Mami ta lumshe ido hawayenta sukq zubo ta bud'e tana murmushin k'arfin hali. "Na'am d'an Maminsa, ka gujemu ko?" Adnan ya yi shiru baice komai ba sai huci yake. "Karka damu, Allah Yana tare da mu. Kayi kokarin 6oyemin sirrin gida, idan ma ka gayamishi wani abu, to don Allah karka k'ara daga abinda ka fad'a. Kayi kokarin sakin jikinka kada tambaya ta yi maka yawa." Adnan ya gyada kai. Haka sukayi sallama bayan tace ya gaishemata da Hajiya Babba. Faruk ya dubeshi da murmushi. "To ya? Domino's Pizza ko kuma Jabi Lake Mall?" Adnan ya dubeshi sukayi dariya, ya kanne mishi ido. "Kaima kasan inda nafi kauri." Faruk ma dariyar ya yi kafin ya tashi motar ya harba titi. Bai zarce ko'ina ba sai da suka samu masallaci sukayi sallah sannan suka karasa ya siyamusu Pizza da ice cream sukayi gida. A hanya Hajiya Babba ta kira Faruk a waya jin ya dad'e, ya tabbatar mata suna tafe da Adnan shima yazo. Ta ji dadi kwarai don Adnan yaro ne dan shafta, yanzun sai ya k'ullar da cikinta, sam baya mata bak'unta. Saida suka isa dakin Faruk, Adnan ya yi wanka shima Faruk ya yi suka chanja kaya daga nan suka nufi cikin gidan. Hajiya na falon tare da Ikram da Baraka suna hira. Ganin Adnan yasa yaran soma ihun murna. Shima a take ya ji ya mance da komai ya washe hakora. Ya karasa ya gaida Hajiya har tana mishi fadan dalilin da bai zarto gidan ba ya soma zuwa ga Faruk. Ya daga ledojin hannunsa yana dariya. "Saboda wannan ne." Sukayi dariya gaba daya. "An kammala karatu kuma sai tafiya ko?" Ya dan yi murmushi bai ce uffan ba. "Ai nima ji nake kamar na bishi wallahi." Cewar Baraka. Ya harareta. "Ki barwa mijinnaki wa?" Ta yi dariya. Nan suka shiga hira, Hajiya ta tambayi dalilin ramarsa ya sanarmata ya danyi rashin lafiya ne. Tare suka ci suka sha kayan makulashen sannan Faruk da Adnan suka shiga wajen Daddy suka gaisheshi ya tambayi yaushe ya iso ya ke sanarmishi daga karshe suka koma sashen Faruk. Faruk kwance saman gado yana danne-dannen waya, yayinda Adnan ke sarrafa Laptop din Faruk yana duba shafin sada zumuntarsa na Facebook, hankalinsa ya kai ga zanen da Faruk ya yi a jikin sketch board. Ya k'urawa hoton ido yana son tuno inda yasan yarinyar. Zaro ido ya yi gami da ajiye Laptop din da sauri ya nufi wajen. Wannan ya ja hankalin Faruk ga dubansa, gabansa ya fad'i. Shaf ya mance bai cire takardar zanen daga jiki ba. Ya kauda kai sa'ilin da Adnan ya dubeshi. "My best, wannan ta yimin kama da Ummi sosai. Ya akayi ka zanata?" Faruk ya daure ya k'ak'alo murmushin yak'e. "Hobby na kenan, kasan zane babu inda baya zuwa, haka kawai na tsinci kaina da zanata." Adnan ya yi shiru, zarginsa yana bashi kamar akwai wani abu game da Ummin a zuciyar Faruk. Ya numfasa, idan ta yi wari watakil shine wanda zai soma ji. A fili kuwa murmusawa ya yi. "Wallahi ta yi kyau, kamar wacce aka dauka a hoto. Gaskiya Allah Ya baka." Faruk ya share maganar ta hanyar jefomishi tambaya. "Wace k'asa ka za6i zuwa ne?" Adnan ya baro wajen zanen ya dawo, ransa ya sosu don ya tuno abin haushi. Ya dan daga kafada. "Bar wannan zancen my best, ni nafasa anan zanyi." Faruk ya lura da wani abu, kawai sai ya share. *** *** *** KADUNA Dija gaba daya ta sauya, daga mai surutu da zafi zuwa marar son hayaniya da kuma sanyi. Komai takeyi muddin Deen zai shigo, to fa zata mance komai ta shagaltu a kallon dukkan wani motsinsa. Tun Deen bai lura ba har dai ya soma tsarguwa da yawan bibiyarsa da takeyi da kallo. A yau juma'a, Munira batanan ta wuce gidan wata aminiyarta da ta haihu, saida ta dauko yaranta daga makaranta suka wuce tare, gidan babu kowa sai Dija wacce ganin Denn a gida yasa fir ta k'i binsu ta fake da ciwon jiki. Misalin karfe uku da mintuna, Deen yana kwance a falonsa yana duban talabijin, ya ji sallamar Dija. Da mamaki ya dubi hanyar falon, yana mai amsawa. Ganin da ya yi mata cikin shigar mutunci marar mishkila sosai yasa ya dan ji nutsuwa a ransa. Ya mike zaune yana murmushin yak'e. "A'a Dija, k'araso mana." Ta dubeshi ta sauke ajiyar zuciya, komai nashi burgeta yakeyi. Ita kuwa ko zata mutu sai ta sace zuciyarsa, shekarunta sun kai munzalin da ya dace ace tana gidan miji ba yawon gidajen yan uwa ba. Itama fa mutum ce ba dutse ba, tana da sha'awa, koda dai takan biyewa k'awarta wacce waya ta hadasu, mai yawan yi mata hudubar banza akan ta amince ta je Kano su had'u don d'ebewa juna kewa, ta k'i yarda amman takan ta6a hirar banza da ita a waya(Wa'iyazubillah). Ta samu wuri ta durkusa gami da gaisheshi. Ya amsa batare da ya kalleta ba yana mai wayancewa da chanja tasha. "Ashe sai kai kad'ai, ga abinci can an jera tun dazu." Ya dan dara. "Eh yanzu zan taso na ci." Ta narkar da fuska. "Haba Deen, don Allah ka zo muje, ni kaina sai yanzu zan ci. Na riga na saba da ci da ku ana yi ana hira, yanzu da basunan bazan ji dadi ba." Ya jefeta da wani irin kallo har saida ta ji gabanta ya fad'i, tsoro ya cikata, sai kuma ya numfasa gami da maida dubansa ga talabijin. "Jeki ina zuwa." Ya bata amsa a gajarce ta mike jiki babu kwari ta fita. Har ta cire ran zai zo sai kuma gashinan, wani sanyi ta ji a ranta ta mike zata zubamishi. Ya dakatar da ita. "No barshi, zan yi da kaina." Ta girgiza kai. "Ban ta6a ganin kunyi haka da Munira ba, nima bazan bari ka zuba da kanka ba kada nayi laifi awajenta." Jin haka ya kauda kai, ta zuba tana murmushi ta tura gabansa sannan ta zauna saitinsa tana cin nata. Idanunta a kansa, da zarar ta ga zai kallota sai ta yi sauri dauke idanun. A ransa ya ji yana mai jin haushinta, da ace yar uwarsa ce da tuni ya korata gidansu, saidai ba yanda ya iya, baya son ran Munira ya 6aci ya lura sosai take kaunar Dija hakanan tana tausayinta wai adalilin har yau bata samu mashinshini ba. Ya rigata mik'ewa ya bar wajen, ta bishi da zazzafan kallo gami da k'ara cin alwashin ba fa zata barshi ba sai ta cika burinta na aurensa. Babu wacce ta fad'omata a rai sai Baba Habiba, ta tabbatar ita daya ce zata iya yi mata kokarin shawo kan Deen ko ta wane hali. Idan ma da hali ya saki Munira ya aureta. (Kun ji butulcin DAN ADAM)1 *** *** *** Bikin Baraka ya iso, komai na shirye-shiryen Mami, ita da kanta ta yi bata saurari Abba ba balle ta tambayi wani abu a aljihunsa har ya samu damar cin zarafinta. Ta yiwa Ihsan anko, hakan ta siyawa Fahad shadda tare da Adnan aka dinka musu. Ummi kuwa ta yi mamaki da Mamin ta bata kudi suka je da Amina bayan isarsu gidan Hajiya Mama ta siyo 'yar kanti da kuma wani abin idan tana so. Ta yi murna matuka duk da tasan ba da ita zasu je ba. Hajiya Mama ta jajantawa yar uwarta kwarai na abinda ke faruwa da ita. Ta kuma yi mata fada sosai akan dalilinta na rashin sanar da ita tun wuri. A karshe tace zata sanya ayi rokon Allah, suma kuma ba kwanciya zasuyi ba, su dage sosai da addua da sadaka har Allah Ya kawo makarin koma menene. Bayan Amina da Ummi sun dawo daga shago suka biya gidan Innar Aminar. Mace mai mutunci kwarai, ta yi murna da ganin Ummin da duk sadda Amina ta zo saitq bata labarinta. Sun jima anan sannan suka lek'a gidan Anti Hauwa yayar Amina daga nan suka kamo hanyar gida. A hanyar ne ma Ummi ke labartawa Amina yanda suka ta6a yi da Hajiya Binta. Amina sosai ta tsorata, hankalinta ya dan kwanta jin Ummi bata bi turbar shaidan ba ta aikata. Ta k'ara fahimtar da ita lallai mai yiwuwa yanzun ma da sa hannunsu cikin lamarin Abba da Mami. A karshe ta kara shawartarta akan ta dage da addu'a akan Allah Ya kareta daga sharrinsu. Ashe kuwa dai sharrin na tafe, domin a daren da suka koma gida daga gidan Hajiya Mama, Abba ya kira Mami ya ke fadamata ta gaggauta korar Ummi daga gidansa don labari ya iso mishi cewar tana biye-biyen maza tana fakewa da zuwa makaranta. Acewarsa, yaransa basu jawomasa abin kunya ba, to babu 'yar wata can da zata janyomasa. Mami ranta ya 6aci, cike da mugun 6acin rai ta dubeshi. "Wannan kuma ba halin Ummi bane, da ace Ummi na yi kasan kafin ka gane ka koreta, da tuni na yi hakan don bana zama da maci amana. To Ummi babu inda zata je, zamanta daram a gidan nan!" Ta yi maganar cikin daga murya har kirjinta na bugu da sauri-sauri saboda tsananin 6acin rai, ba wai don kwatarwa Ummi yanci kadai bane, aa, har ma da gajiyawa da jin zafin yanda ya ke bayar da ita gaban kishiyoyinta, don a wannan karon ma har hadasu ya yi gaba daya a falon yana mata korafi akan Ummin. Abin ya soma isarta. A fusace ya ce. "Sai mu gani idan gidan ke kika ginashi Madina! Amma wallahi kinji rantsuwa ta musulunci babu yar iskar da zata zauna a gidana, saidai ko ki bita." Hankalin Mami ya tashi, su kansu matan sun razana da furucin Abba, Anti Amarya wacce bil hakki ta tausayawa Mamin, ta saka baki. "Haba Alhaji, ya kake..." "Kiyimin shiru Malama, bansaka dake ba, daman na taraku ne don na gargadeku da ku jawa yan aikinku kunne, banaso and iskancin banza da wofi. Ke kuma ki tattara taki ki maida inda kika amso ta, bazan lamunci iskanci ba." Takaici ya sa Mami jan tsaki batare da tasan sadda ya fito ba. "Sai kayi, na gayamaka babu inda Ummi zata je, sa'arka d'aya zan je Abuja da na soma gwadamaka gaskiyar abinda nake fad'a tun yanzun. Naga ai wasu ma nasu cikin suka ta6a yo wa aka zubar aka cigaba da zama da su a gidan." Hajiya Binta ta fahimci da yar aikinta Sa'ade take wacce ta ta6a yo ciki suka zubarmata. Ta fusata ta yi kwafa batace uffan ba. Kafin Abba yace wani abu, Mami ta zura silifas dinta ta fice cikin kunar rai. "Ummi! Ummi!!" Ummi dake daki ta ji Mami na kwalamata kira cikin daga murya. Ta fito a kidime ta russuna. "Naam." Ta tamke fuska. "Ki shirya kayanki, dake zan tafi." Ummi gabanta ya fadi don bata ta6a zato ba, ta mike ta wuce bayan ta amsa da toh kawai. Shigarta da mintuna biyar Fahad yazo ya kara kiranta wai inji Mami. Ta mike ta isa gareta a can daki. Mamin na zaune gefen gado ta yi jugum tana tunani, bayan Ummi ta durkusa ta dubeta fuska daure. "Ki gayamin tsakani da Allah akqn dukkan abinda zan tambayeki Ummi." Ummi a tsorace ta ce. "Toh." Mami ta zubamata ido, ita tasan sharri aka yiwa Ummi, saidai dole ne ta tambayeta don amana ce ita a hannunta.

Post a Comment for "DAN ADAM CHAPTER 10"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...