BA SONTA NAKE BA CHAPTER5 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BA SONTA NAKE BA CHAPTER5

BA SONTA NAKE BA CHAPTER5

- - Post a Comment
BA SONTA NAKE BA CHAPTER 5 

AL-HUSSAIN MANSION Farouq ya faka motar shi zai fito ne Zara tayi saurin riqo hannun shi tace “Ya Farouq don Allah say something” Farouq ya kalle ta yace “idan baki sakar mun hannu ba I will slap you” ajiyar zuciya tayi ta saki hannun shi ta fita daga motar. Da gudu ta wuce cikin gida tana kuka yayinda ya tsaya yana kallon ta. Jikin shi duk yayi sanyi ganin yadda ta shige gida tana kuka. Sashen Mamy ya nufa, bayan sun gaisa ne Mamy tace “Ina Zaran take?” yace “ta wuce dakin ta, ni zan tafi asibiti. I will check on you later” tace “Allah ya tsare mun kai” yayi murmushi yace “ameen” Zara tana kwance a kan gadon ta tana ta kuka ne Mamy ta shigo dakin. Hankalinta a tashe ta qarasa wurinta tace “subhanalillahi, princess me ya faru?” cikin kuka ta rungume Mamy tace “Mamy Ya Farouq yayi fushi da ni, baya mun Magana” cikin mamaki Mamy tace “toh amma ko da ya bar nan ban ga alamun fushi a tare da shi ba, common tashi kiyi wanka ki sauko muyi breakfast don nasan qila baki ci wani abincin kirki ba” haka dai Mamy ta lallashi Zara ta shiga tayi wanka. Ko da ta sauko wurin Mamy ba wani abincin kirki ta ci ba. A dalilin Mamy ta sa mata ido ne ma yasa ta dan ci wani abu. Komawa daki tayi ta kwanta,,wayarta ta janyo ta kunna yayinda saqonni suka dinga shigowa. A cikin saqonnin harda na Mahmood wanda yake tambayar ta inda ta shiga bai gan ta ba. Kiran Hafsat ne ya shigo wayar ta inda ta amsa. Hankalin Hafsat a tashe tace “Babes are you okay? Ina ta kiran wayar ki bana samu” Zara ce ta fashe da kuka. Jin haka ne yasa Hafsat ta kashe wayar yayinda ta qarasa shiga gidan. Hafsat ta shigo dakin zara ta tarar da ita tana ta rusa kuka. Da sauri ta rungume qawarta tana lallashin ta tare da fadin “babes what is it?” cikin kuka Zara ta bata labarin abinda ya faru daga farko har zuwa qarshe. Cikin tausayawa Hafsat tace “babes kar ki damu, thank God na kira Ya Farouq at the right time otherwise it would have been a different case” Cikin mamaki Zara tace “kina nufin ke kika gaya ma Ya farouq?” Hafsat ta girgiza kai yayinda zara ta qara rungume qawarta tace “thank you very much my friend” Hafsat tace “yanzu dai relax ki dan ba Ya Farouq space. Da alama bai fadi ma Mamy abinda ya faru ba, nasan komai zai koma normal insha Allah” haka dai Hafsat ta dinga lallashin qawarta. ************ Wasa wasa dai Zara ta sa ma ran ta damuwa sossai. duk bayan dan lokaci sai ta kira layin Farouq amma baya dauka. Text messages kuwa ta tura mishi sun fi hamsin baiyi replying dinta ba. Ganin cewa Farouq ya share ta ne yasa ta shiga damuwa mai tsanani. Cikin kwana biyu gaba daya Zara ta daina Magana kamar da. Da qyar ma take zuwa makarantar. Mahmood ya ga canji a tare da ita, ya bata haqurin abinda ya faru wanda ta gwada mishi babu komai amma fa dukda haka bai samu kanta ba. STORY CONTINUES BELOW Ganin yanayin da Zara ta shiga ne yasa Hafsat ta sanar da Mukhtar abinda yake faruwa. Mukhtar yayi mamaki domin kuwa abokin shi bai fada mishi komai ba akan abinda ya faru. Yayi alqawarin yi ma Farouq din Magana. CENTRAL HOSPITAL Zaune yake a ofis dinshi yana karanta wani text message din da Zara ta tura mishi. Mukhtar ne ya shigo ofis din cikin sallama yayinda ya zauna yace “abokina what have you done to this garl?” Farouq ya kalle shi yace “I shut her out completely” Mukhtar ya girgiza kai yace “amma dai kasan she is not responding to life kamar kullum ko? Dazu Hafsat take fada mun abinda ya faru” Ya gyara zama ya cigaba da fadin “tunda dai Allah ya taimaka you saved her from them ai bai kamata ka guje ta ba” Ya miqe yace “whatever happens to her is on you, na gaya maka gaskiya” Mukhtar ya fita ya bar shi yana tunanin maganganun shi. Tsaki yayi a ranshi yace “I can’t believe this”. AL-HUSSAIN MANSION A yau tun da safe gidan shiru, motsin masu aiki kawai ake ji a gidan. Mamy ce ta kira wayar Zara don ji ko ta wuce school domin kuwa a kowanne rana irin na yau da wuri take fita a dalilin lecture din safe da take da shi. Mamy ta kira wayar Zara ya fi a qirga amma shiru bata amsa ba. ganin har qarfe tara na safe ne yasa ta ce Larai ta dubo ta. Larai ta qwanqwasa qofar dakin Zara ta ji shiru, cikin sallama ta bude ta shiga. Tsayawa tayi cak yayinda ta ga Zara kwance a qasa. Da alama ma bata numfashi. Ihu ta kwarma yayin da ta nufi wurin Zara tana jijjiga ta. Mamy da take falon qasa ta ji ihun da Larai tayi don haka ne ta hauro saman a guje yayinda ta shigo ta samu Zara a qasa. A rude ta nufi wurin Zara tana fadin “Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un, me ke faruwa haka?” ta kalli Larai tace “maza je ki dauko mun wayata” Larai ta shigo riqe da wayar Mamy ta miqa mata yayinda ta kira layin Farouq ta fada mishi abinda yake faruwa. Cikin minti goma sha biyar Dr Ibrahim ya iso gidan inda yake qoqarin ceto rayuwar Zara. Anyi nasara ta farfado yayinda ya sa mata drip a hannu tare da yi mata wasu allurai a cikin drip din. Zara dai a jigace ta dan bude idanuwan ta don ganin waye a kusa da ita. Ganin Dr Ibrahim da su Mamy ne a dakin yasa ta qara waigawa don neman Farouq amma ta ga wayam. Da sauri ta tashi zaune tace “ina Ya Farouq?” Dr Ibrahim ne yace “yana asibiti, akwai surgery din da zai yi shiyasa ya turo ni” kafin ya rufe baki sai gani suka yi ta zare drip din dake hannun ta sannan tace “ni Ya Farouq nake so” ta koma ta kwanta tare da juya musu baya. Dr Ibrahim dai tsayawa yayi yana kallon ikon Allah yayinda Mamy ta janyo ta tace “Princess kiyi haquri Dr Ibrahim ya duba ki, idan Yayanki ya gama nasan zai zo” Zara ta girgiza kai tace “Mamy bazai zo ba, yayi fushi da ni” daga nan kuwa ta sa kuka. Dr Ibrahim dai sai yanzu yake gane abinda yasa Farouq ya turo shi domin kuwa a zahiri yau baya da wani surgery din da zai yi, lallai akwai abinda yake faruwa a tsakanin su. STORY CONTINUES BELOW Mamy ce ta rungume ta tana fadin “toh me kika yi mishi da har kike tunanin fushi yake yi da ke?” Zara ta runtse idanuwan ta tare da fadin “toh Mamy ki tambaye shi, ni na bashi haquri ya qi. Kin ga na kira shi sau dayawa a waya bai dauka ba sannan text messages dina baya replying” Mamy dai sai yanzu ta fahimci lallai akwai wani abu domin ta lura Farouq ya rage zuwa gidan sannan idan har zai zo sai lokacin da Zara take makaranta. Lallashinta suka yi akan ta bari Dr Ibrahim ya duba ta amma sai ma miqewa tayi ta shige bathroom dinta tayi zamanta yayinda ta cigaba da kuka. Babu shiri Dr Ibrahim ya kwashe kayan aikin shi ya tafi tare da Alqawarin zai sanar da Farouq abinda ya faru. CENTRAL HOSPITAL Zaune yake a ofis dinshi yana bin wani file, Mamy ce ta kira shi a waya. Bayan ya amsa ne Mamy tace “wai me Zara tayi maka ne kake fushi da ita?” Shafa kanshi yayi tare da fadin “babu komai Mamy” Mamy ta girgiza kai tace “tace kana fushi da ita sannan gashi yanzu tace idan ba kai zaka duba ta saidai Dr Ibrahim ya tafi. Yanzu haka ya kwashe kayan aikin shi ya tafi” Farouq cikin bacin rai yace “toh shikenan Mamy, sai zuwa gobe zan zo” Cikin mamaki Mamy tace “ban gane gobe ba, yanzu haka zata yi ta zama da ciwo?” Farouq yace “toh Mamy barin surgery din zanyi? Ai shiyasa na turo mata Dr Ibrahim din”. Mamy tace “don Allah kayi qoqari idan ka samu lokaci ka zo ka duba ta” Farouq yace “Insha Allah Mamy, Allah ya bata lafiya, I gotta go” Yana nan zaune Dr Ibrahim ya shigo ofis din. miqewa yayi yace “what do you think is wrong with her?” Dr Ibrahim yace “gaskiya for now her blood pressure is high wanda idan ba’a samu ya sauka ba ciwon ta yana iya tashi” Farouq ya koma kan kujerar shi tare da sakin ajiyar zuciya ya dafe kai. Anan dai Dr Ibrahim ya bashi labarin yadda ta qi yadda yayi treating dinta sannan ya bashi shawara akan ya je ya duba ta before ciwon nata ya tashi. Yinin ranan dai gaba daya Farouq ya kasa yin komai sannan ya qi zuwa duba zara. Gabadaya hankalin shi yana kanta. Asali ma rufe kanshi yayi a ofis din ya qi fita sai lokacin Sallah ne kawai yake fita. AL-HUSSAIN MANSION Zara dai ganin Farouq bai zo ba yasa damuwar ta ya tsananta. A lokacin Hafsat tana tare da ita. Kwance take cikin bargo, jikin ta yayi mugun zafi yayinda take ta kyarmar sanyi. Mamy ce ta shigo ta tarar da ita a hakan. Wayarta ta dauka ta kira layin Farouq amma bai dauka ba, a lokacin yana can yana zagayen duba patients dinshi yayinda ya bar wayar a ofis. Ganin Zara ta fara zufa ne yasa hankalin Mamy ya tashi domin kuwa babu tantama ciwonta ne ya tashi. Da sauri Mamy da Hafsat suka tarkata ta suka saka ta a mota sai asibiti. Ko kafin a isa ma ta riga ta suma. Dama tun a mota Mamy ta sanar da Abba halin da ake ciki, hankalin shi yayi matuqar tashi. A dole yayi excusing kanshi daga meeting din da suke yi ya dauko securities dinshi sai Central Hospital. CENTRAL HOSPITAL Cikin gaggawa aka shigar da Zara dakin da ya kasance na family inda aka kwantar da ita bisa gado. Farouq ne ya shigo dakin hankalin shi a tashe, Mamy da Hafsat ya gani a kanta inda Hafsat din take ta kuka. Da sauri ya nufi wurin su yace “Mamy let me” da sauri Mamy da Hafsat suka tashi yayinda suka koma waiting room na dakin. Ko da Farouq ya duba Zara ya tabbatar ciwon ta ne ya tashi. Nan da nan aka shigo da na’urori kala kala wadanda ake buqata. Cikin lokaci qanqani aka yi setting din Zara up. Hankalin Farouq a tashe yake yin aikin shi, bai taba tunanin cewa he has anything to do with ciwon Zara ba. tambaya anan shine does he affect her this much????? Farouq ya fito daga dakin Zara ya nufi wurin Mamy wadda take tsaye tana kai da komowa. Janyo ta yayi ya rungume ta yace “relax Mamy she will be fine” a lokacin ne Abba ya shigo asibitin inda ake ta gaishe shi cikin girmamawa. Babu wanda bai san shi ba, sai bin shi ake da kallo ana nuna shi. Waiting room din dakin Zara ya nufa yayinda securities dinshi suka tsaya a waje. Fuskar shi cikin damuwa ya qarasa wurin su yace “tana ina?” Farouq yayi gyaran murya yace “tana ciki Abba, she will be fine Insha Allah, everything is under control” ajiyar zuciya yayi yace “Alhamdulillah” Hafsat ce ta duqa har qasa tace “Ina wuni Abba” cikin fara’a yace “Hafsat kina lafiya? Tace “lafiya lau Abba” yace “madallah”. Su Mamy sun so shiga dakin Zara amma Farouq ya hana. Ta wani gilas ne suka tsaya suna hangen ta. Banda shi da nurse dinshi babu mai shiga ciki. Iyayen Hafsat da na Mukhtar ma sun zo. Mukhtar dai kallon abokin shi yake yi yadda ya shiga tsananin damuwa yana mamakin ace babu wani abu a tsakanin su. Babu yadda Farouq baiyi da su Abba akan su koma gida ba amma suka qi. Wuraren qarfe goma sha daya na dare ne iyayen Hafsat da na Mukhtar suka tafi, Hafsat da Mukhtar dai suna nan tare da su Abba. Haka Abba da Mamy suka tsaya tsaye suna hangen Zara ta gilas yayinda Hafsat da Mukhtar suke zaune a cikin kujerun wurin inda suke addu'ar Allah ya bata lafiya. CENTRAL HOSPITAL Farouq yana zaune a kusa da Zara yana kallon na'urar EKG din da take monitoring bugun zuciyar ta.+ kamar kullum addu'a yake yi Allah yasa ta farfado da wuri domin kuwa shi kadai ya san yadda yake ji a duk lokacin da ta shiga wannan halin. Yana nan zaune yana danasanin qin kula ta da yayi tun abinda ya faru ranar birthday dinta. Bai taba tunanin cewa damuwar da ta shiga yayi tsananin da zai sa ciwon ta ya tashi ba. Yayi ma kanshi alqawarin bazai sake bari ta shiga irin wannan halin ba a dalilin shi. Fuskar ta ya kalla inda ya lura har ta dan rame. Runtse idanuwan shi yayi sannan ya fada a fili "please wake up" Ji yayi ta matse hannun shi wanda yake cikin nata. A razane ya bude idanuwan shi ya kalle ta yayinda ya ga ta fara motsi. Gani yayi bakin ta yana motsi alamar tana magana don haka ne ya dan matsa kusa da ita don jin abinda take fadi. Ji yayi tana fadin "Ya Farouq please I am sorry" ajiyar zuciya yayi ya kai bakin shi saitin kunnen ta yace "sssshhh I am here, relax". Sannan ya koma ya zauna. Abba da Mamy wadanda suke kallon su ta gilas dukda basu ji abinda suke fadi ba sai da suka yi murmushi da suka ga abinda ya faru. Mamy ce take bashi labarin abinda ya faru da har yasa Zara kwanciya. Abba ne yace "dukda bamu san me ya hada su ba I am sure its something serious" Mamy tace "ni kam gani nake lokaci yayi da zamu cika burin mu akan su" Abba yayi murmushi yace "nima ina tunanin hakan, bari ta kammala school dinta kamar yadda ta buqata, daga nan sai ayi komai". Har yanzu zara ta qi sakin hannun farouq, duk yadda ya so ya zare hannun shi daga nata ya kasa. Matsawa yayi kusa da ita ya zauna yace "na san kina ji na, idan baki sakar mun hannu ba I will slap you" Da sauri ta bude idanuwan ta wadanda sukayi ja sannan tace "toh ina zaka tafi ka bar ni?" Yace "zan fadi ma su Mamy ne kin farfado" Ta dan yi murmushi sannan ta saki hannun shi. Su Mamy suna nan tsaye suna kallon ikon Allah. Ko da ya fito kallon shi suke yi cikin murmushi yayinda Abba ya janyo shi ya bugi kafadar shi yace "thank you son" Shima murmushi yayi yace "zaku iya shiga ku gan ta, ta farfado" tun kafin su Mamy su shiga Hafsat ta miqe ta shige a guje. Farouq ya koma ofis dinshi ya tarar wayar shi tana ta ringing, Ruqayya ce take kiran shi. ko da ya amsa wayar ji yayi tace "Honey ina ka shiga ne ina ta kiran ka?" Shafa kanshi yayi yace "sorry I had an emergency ne, how are you?" tace "Fine, na ji ka shiru baka dawo ba" Agogo ya kalla ya ga qarfe biyu na dare yace "bazan samu dawowa ba gaskiya, I am busy" Cikin shagwaba tace "wallahi Honey don dai aikin lada kake yi amma da sai in ce its getting in our married life's way"3 Girgiza kai yayi yace "I will make it up to you insha Allah" bayan sunyi sallama ne ya zauna ya cigaba da duba file din Patient din da zai yi ma surgery da asuba. STORY CONTINUES BELOW ********* Washegari da safe Zara tana kwance akan gadon asibitin tare da Hafsat. Abba da Mamy suna zaune akan kujera Yayinda Mukhtar yake tsaye a gefe. Wata nurse ce ta shigo cikin girmamawa ta duqa har qasa ta gaida Abba da Mamy sannan ta gaida Mukhtar. Ta matsa wurin gadon Zara tace "Anty Zara ya qarfin jiki?" Zara tayi murmushi tace "da sauqi, ina Ya Farouq?" Nurse din tace "he is performing a surgery" turo baki tayi ta mayar da idanuwanta ta rufe. Nurse din ta duba jikin Zara ta tabbatar komai normal don haka ne ta sa mata sabon drip kamar yadda aka umurce ta sannan ta fita. Su Mamy dai sun kula tunda Zara ta ji Farouq bazai zo ba ta bata rai. Qarfe goma na safe ne ya shigo dakin cikin sallama, jin muryar shi ne yasa ta bude idanuwan ta harda guntun murmushin ta. Su Mamy dai har mamaki suke yi. A yanzu kam sun tabbatar Zara tana son Farouq koda kuwa shi baya sonta. Cikin girmamawa Farouq ya gaida iyayen shi yayinda yayi musabaha da abokin shi, Hafsat ta gaishe shi. Gefen gadon Zara ya nufa yana duba na'urorin da suke aiki. Ita kuwa idanuwa ta sa mishi kamar wadda ta shekara bata gan shi ba. kamar ance ya kalli fuskar ta sai gani yayi tana kallon shi. hararar ta yayi yace "what?" Hannun shi ta riqo tace "are you still mad at me?" kafin ya amsa ne Abba yace "wai wane laifi ne haka da har ya ja ma yarinyar nan kwanciya?" da sauri Farouq yace "Abba it has nothing to do with ciwon ta fa" Mamy tayi murmushi tace "toh koma dai meye a yafe mata, horon ya isa haka" Hafsat da Mukhtar dai murmushi kawai suke yi yayinda Farouq ya kalli Zara yace "akwai conditions.." kafin ya rufe baki tace "koma menene Ya Farouq zanyi, I promise" ba tare da ya kalle ta ba yace "lets talk about it later" Farouq ya kalli su Mamy yace "Mamy ga breakfast dinku a waiting room na ga baku ci ba" Abba ne yace "wa ke ta breakfast princess a kwance ba lafiya" murmushi yayi yace "she is out of danger ai Abba, please have your breakfast" Ya kalli Hafsat yace "je ki zuba muku kuma ki tabbatar qawar ki ta ci" da sauri Zara tace "Ya Farouq kai zaka bani da kanka" kallonta yayi yace "Are you mad?" yayinda su Mamy suka fashe da dariya. Abba ne ya miqe yace "mu dai bari mu je gida mu dawo" Farouq yace "kar ku damu Abba, ba sai kun dawo ba zuwa anjima zan sallame ta, I will bring her back home myself" *********** Da rana ne Farouq ya shigo dakin Zara ya tarar da su zaune kan gadon suna ta hira. Ganin shi ne yasa sukayi shiru. Hafsat dai miqewa tayi tace "I will be in the waiting room" ta fita tana murmushi. Tsayawa yayi yana kallonta. Murmushi tayi tace "Ya Farouq come and sit" bai motsa ba daga inda yake balle ya zauna. Ji tayi yace "daga yau kada ki sake fita baki sanar da ni ba" Murmushi tayi tace "yes big brother" sai kuma ta bata rai tace "toh amma fa Ya Farouq idan na kira ka a waya ai baka dauka" yace "send me a text message idan ban dauka ba" tace "toh kana karantawa ne?" Hannun ta ya kamo ya zare allurar drip din da ke hannun har tace "oouch" sannan yace "leave that to me, tashi mu je in kai ki gida. You've been discharged" Murmushi tayi tare da yunqurawa zata miqe tace "Ya Farouq help me" hararar ta yayi ya kira Hafsat don ta taimaka mata. Farouq ya kai Zara gida tare da nuna ma Mamy magungunan ta da yadda zata sha su sannan ya jadada musu akan kada su bari ta je ko ina har nan da kwana uku domin tana buqatar hutu. STORY CONTINUES BELOW FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION Farouq ya dawo gidan shi a gajiye, bacci ne a idanuwan shi don haka ne yana watsa ruwa ya haye gadon shi. Ruqayya tana zaune tare da Aliya a sashen ta suna hira ne Aliya ta shiga instagram dinta inda take ta kallon posts. Zaro idanuwa tayi tace "qawata dama Zara tayi ciwo ne?" Ruqayya tace "anya kuwa? Yaushe?" Aliya ta matso kusa da qawarta tace "kalla ki gani, Father In-law dinki was in Central hospital jiya saboda ciwon Zara ya tashi". Ran Ruqayya a bace tace "oooh, shiyasa ya kwana a asibiti jiya kenan" tsaki tayi tace "wallahi farouq ya raina mun hankali, instead of ya fada mun ya tsaya jinyar 'yar iskar yarinyar nan shine yayi mun qarya" Aliya tace "relax qawata, meye na tada hankalin ki akan wannan? She was ill and i guess its okay for him to stay with her. Yanzu dai gaya mun abinda kike yi don rabuwa da Musty" Ruqayya tayi murmushi tace "ai ki bar maganar rabuwa da Musty, nayi qoqarin fita harkar shi amma na kasa. Kin kuwa san Farouq sai yayi kwana biyu bai biya mun buqata ba?" Aliya tace "toh laifin wa?" Ruqayya tace "hmmm, idan ma ya waiwayo ni yadda kika san an sa shi dole, kwata kwata ma he is not romantic" tayi murmushi ta cigaba da fadin "kin ga Musty kuwa ba qaramin satisfying dina yake yi ba don haka gaskiya na fasa rabuwa da shi" Aliya ta girgiza kai tace "be careful dai, kar reshe ya juye da mujiya" *********** Da daddare Farouq da Ruqayya zaune a kan dinning suna dinner ne tace "ashe Zara tayi ciwo ban sani ba?" ya girgiza kan shi tare da fadin "kwanan ta daya kawai a asibiti ta koma gida, zaki iya zuwa gobe ki duba ta" Ruqayya tace "ashe ita ka tsaya jinya jiya shiyasa baka dawo ba" Murmushi kawai yayi ya cigaba da cin abincin shi wanda yake ci kamar yana cin magani ba don rashin dadin shi ba sai don rashin son irin abincin. Ruqayya dai ta qulu matuqa da Zara, fatan ta Allah ya dawo da Hajjaju lafiya su koma wurin boka cika aiki. AL-HUSSAIN MANSION A yau jikin Zara ya qara warwarewa, 'yan makarantarsu dayawa sun zo sun duba ta har Mamy tana mamakin yawan mutanen da suke ta shige da fice a cikin gidan. Da daddare ne Mahmood ya zo gidan don ganin Zara. Har cikin gidan ya shiga da motar shi, suna zaune a cikin motar shi suna hira ne yace "wai Cutie dama idan ciwon naki ya tashi haka kike shan wahala?" Tayi murmushi tace "wallahi kuwa sweetie, kuma fa kullum laifin Ya Farouq ne" bata rai yayi yace "wai ban tambaye ki ba, shi wannan Ya Farouq din da kike fadi soyayya kuke yi ko me?" Fashewa tayi da dariya tace "ni? Soyayya da Ya Farouq?? Rufa mun asiri" Mahmood yayi ajiyar zuciya sannan yace "idan na tambaye ki zaki bani sincere answer??" tace "ofcourse I will" yace "tsakanin ki da Allah kina son shi ko bakya son shi?" kafin ta amsa ne motar Farouq ta shigo gidan inda ya faka nesa kadan da su. Bai kula da motar Mahmood a cikin gidan ba lokacin da ya fito yana gaisawa da wasu daga cikin ma'aikatan gidan. Da sauri Zara ta fita daga motar ta nufi wurinshi. ganin ta fito daga motar Mahmood ne yasa ya tsaya cak cikin mamaki. Ko da ta qaraso wurin shi tana murmushi tace "Ya Farouq ina wuni" har lokacin kuwa Farouq kallon motar Mahmood yake yi wanda ya ga Mahmood din ya bude qofar ya fito yana shirin qarasowa wurin shi don su gaisa. Ganin hakan ne ran shi a bace ya juya ya shiga gida. A ranshi yana fadin "this must be the so called My luv da yake kiran ta a waya lokacin da muke Dubai" tsaki yayi. Zara dai dawowa tayi ta samu Mahmood a tsaye tace "hmmm, yanzu haka ya shigo da bacin rai kenan, ko gaisuwa ta fa bai amsa ba" Mahmood yace "ko kuma ni ne na bata mishi rai ba" Zara ta fashe da dariya yayinda suka koma cikin mota tace "Ya Farouq fa babu ruwanshi, zanyi introducing dinku soon ai" haka dai suka cigaba da hirar soyayyar su. Farouq ya shiga sashen Mamy ranshi a bace. Mamy ce tace "my prince wa ya taba mun kai ne na ga kamar ka shigo ran ka a bace" zama yayi kusa da ita yace "babu komai Mamy, kaina ne yake dan ciwo" Ta dafa kanshi tare da fadin subhanalillah, bari in kira Larai ta kawo magani" yace "Mamy bar shi kawai" murmushi tayi tace "har yanzu dai kana nan da halinka na rashin son shan magani ko? Toh yanzu ya za'a yi kan ya sauka?" Kwanciya yayi a kan doguwar kujera yace "let me take a nap, nasan zai sauka". Mamy dai ji tayi yace "Mamy wai waye ne a waje tare da waccan yarinyar?" Cikin mamaki Mamy ta kalle shi, a ranta tace "ko dai dalilin bacin ran shi kenan?" Murmushi tayi tace "wani dan makarantar su ne yazo duba ta, yau tun safe suke ta zuwa gaishe ta. Zara akwai jama'a" Cikin bacin rai yace "dubiyan ne harda Maza Mamy?" kasa boye murmushinta tayi tace "toh banda abinka Farouq idan Zara bata kula samari ba wa zai aure ta?" Zuciyar shi ce ta buga inda yace "Mamy she is just a child fa" Mamy ta katse shi tace "yanzu ba bikin qawarta za'a yi da abokinka ba? Tunda har Hafsat zatayi zaman aure Zara ma zata iya. Afterall why do you even care?" daga nan kuwa bai qara Magana ba. Bacci ya dan kwashe Farouq a kan kujerar Mamy ne Zara ta shigo. Ganin yana bacci ne yasa ta kalli Mamy tace "Mamy ya naga Ya Farouq yana bacci, what is wrong with him?" Mamy tace "kan shi ne yake ciwo shine ya dan kwanta" hankalin Zara a tashe ta tsaya tana ta kallon shi. Kallon Mamy tayi tace "bai sha magani ba ko Mamy?" Mamy tace "kin san halin shi ai" juyawa tayi tace "ina zuwa" Mamy ta bi ta da kallo tana murmushi. Zara ta dawo falon tare da Larai wadda ta riqo mata tray yayinda take riqe da Magani a hannun ta. Bayan Larai ta ajiye a side table kusa da Farouq ne Zara ta kalli Mamy tayi murmushi tace "wish me luck Mamy" mamy tayi dariya tace "Allah ya bada sa'a" Zama tayi gefen shi ta sa hannu ta dan taba hannun shi kadan, ganin bai motsa ba ne yasa ta dafa goshin shi. Idanuwan shi ya bude ya ganta zaune daf da shi tana murmushi. Kafin yayi Magana ne tace "Ya Farouq ya ciwon kan naka? Na ji jikinka ma yayi zafi" Tashi yayi zaune ran shi a bace yace "wa yace ki tada ni ina bacci?" tsugunnawa tayi har qasa tace "yi haquri please, magani zaka sha" kafin yayi Magana har ta janyo tray din gaban shi. Kallon tray din yayi ya ga tuwo da miya, da sauri ya kalle ta yace "are you mad? Yunwa nace miki ina ji?" Mamy dai bata san lokacin da ta fashe da dariya ba yayinda Zara tace "wait and see Ya farouq" tuwon ta debo ta sa magani a ciki sannan ta rufe sai ta sa a miyan sannan ta miqo mishi tace "just open your mouth" Dafe kai yayi tare da fadin "Oh My God" Mamy tace "try it mana Farouq, bazaka san ma ka hadiye magani ba" Hararar Zara yayi yace "ajiye zan ci da kaina" murmushi tayi tace "haba Ya Farouq, sai ka bata hannun ka?" can kuma tace "wai ashe da cokali kake ci" sai ta ajiye tace "oya toh" Haka dai Farouq ya hadiye magani a cikin tuwo yayinda Zara ta dinga murna tana fadin "you see, i told you" hararar ta yayi yayinda ta kashe mishi ido. Mamy dai a ranta tace "maganinka kenan, ita ce daidai kai". ************* BAYAN WATA BIYU Tun ana saura sati biyu bikin Hafsat ne Zara ta tattara ta koma gidan su.+ Shirye shirye ake yi sossai. tuni an jera ma Hafsat kaya na gani na fada a gidan ta da yake nan cikin Maitama. Gidan su Hafsat kuwa ya cika da ‘yan uwa da abokanen arziki. Dayake tun saura wata daya aka fara yi ma Hafsat din gyaran jiki duk wani hidima na bikin Zara ce kan gaba wurin shiryawa domin kuwa Hafsat din ta daina fita. Ranar Qunshi Henna Temple aka gayyato, tare da team dinta tazo don haka ne aka dinga zirara qunshi babu ji babu gani. Qunshin Amarya Hafsat yayi kyau sossai, kowa sai yabawa yakeyi. Sai da aka gama ma kowa sannan Zara ta zauna aka yi mata nata a hannu daya, simple one ta zaba domin kuwa ita bata son Lalle dayawa, kwata kwata ma bai dame ta ba. Duk da haka kuwa wanda aka yi mata yayi kyau sossai. Bayan an kammala ana zaune a dakin Hafsat ana hira ne Zara tayi snapping qunshinta. Hafsat ce ta matsa kusa da ita tace “Mahmood za’a tura ma ko Ya Farouq??” Murmushi tayi tace “Sweetie na dai zan aika ma, shi Ya Farouq ko na aika mishi da hoto baya acknowledging, he doesn’t care about me” Hafsat tace “idan nace miki zaiyi acknowledging wannan me zaki bani??” Zara ta fashe da dariya tace “duk abinda kike so zan miki bestie, dukda dai nasan bazai yi ba” Aikuwa haka Hafsat ta zigata ta tura ma Farouq hoton Qunshinta. Bata dade da turawa ba kuwa Mahmood ya kira ta a waya yana ta yaba ma qunshin. Bayan sunyi sallama ne ta kalli Hafsat tace “kin ga wanda ya damu da ni” Hafsat tace “Yaya na ma zaiyi acknowledging” Zara ta tabe fuska ta miqe tana fadin “Hajiya tashi mu fara shiri, Lokacin Bridal Shower ya kusa” FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION Mukhtar da Farouq zaune a Game room din gidan Farouq wanda Mukhtar yake kira da Villa. Mukhtar ya kalli abokin shi yace “amma dai abokina Ruqayya tayi ma kanta da tace bata son wannan gidan” Farouq yayi murmushi yace “da na nuna mata hoton gidan lokacin da muke Germany ko kallo ma bata yi ba, a qarshe ma wai sai cewa tayi ta san its going to be too small for her” Mukhtar yayi dariya yace “Ruqayya kenan, aikuwa nata is too big, wannan shine perfect” Farouq yayi murmushi. Mukhtar ya gyara zama yace “toh yanzu haka zaka bar wannan gidan babu kowa a ciki?” Farouq yace “toh ya zanyi abokina?” Wayar shi ce tayi qara, alaman an aiko text message. Zara ce ta aiko Hoton Qunshin ta, shiru yayi yana qare ma hoton kallo. STORY CONTINUES BELOW A rayuwar Farouq Qunshi yana bala’in birge shi, wannan da Zara ta aiko mishi yayi masifar yi mishi kyau. Mukhtar ne ya ga hankalin abokin nashi ya karkata a kallon wayar shi wanda yayi saurin matsawa don ganin abinda yake kallo. Murmushi yayi yace “gaskiya wannan yayi kyau dukda dai na amarya ta ya fi shi kyau” Da sauri Farouq ya daga kai ya kalle shi yace “bad manners aboki na” Mukhtar yace “yi haquri, ina ta Magana ne ka share ni shiyasa. Zara ita ta dace da kai my friend, just sign her and bring her here” Farouq yayi tsaki tare da jefar da wayar shi yace “mu cigaba da game din ne ko ka haqura na ci ka?” Mukhtar yayi murmushi yace “mu cigaba abokina, kasan daga yau kuma na zama ango, no time to dull anymore” girgiza kai kawai Farouq yayi yana mamakin halin abokin shi. Ko da suka gama buga Game din Farouq ya dade yana tunanin yayi ma Zara Reply ne ko kar yayi. Tunda yake bai taba kiran ta a waya ba haka bai taba replying message dinta ba. Shi kanshi bai san meyasa yake so yayi replying dinta ba a karo na farko. Wayar shi ya janyo ya riqe a hannu. KHALIL MANSION Tuni ‘yan mata an fara shirin Bridal shower, dayake itama Hafsat ba wasu qawaye dayawa gareta ba yawanci ‘yan ajinsu ne a makaranta sai ‘yan uwanta. Zara tana Bathroom din Hafsat tana wanka ne wayarta tayi qara alamun an turo mata message. Hafsat ce ta dago wayar sai ta ga message from Ya Farouq. Zaro idanuwa tayi ta miqe da sauri ta nufi qofar bathroom din tace “babes guess what? Ya Farouq just replied your message” Daga cikin Bathroom din ne suka ji ihun Zara tana fadin “what??” Gaba daya wadanda suke dakin hankalin su ya koma kan qofar Bathroom din yayinda suka ga Zara ta bude qofar daure da towel jikinta duk kumfa. Gaba dayan su fashewa da dariya suka yi yayinda ta qwace wayar a hannun Hafsat ta koma. Hafsat ma tana dariya ta kai bakinta gab da qofar tace “wata da shige cloud 9” Zara zaune a cikin Jacuzzi din Hafsat tana ta fargabar bude message din Farouq. Ajiyar zuciya tayi ta bude text message din, Zaro idanuwa tayi tare da karanta abinda ya rubuta kamar haka: “Beautiful” Ihu tayi cikin murna tayi typing message kamar haka “Ya Farouq dagaske yayi kyau? Kana so?” Riqe take da wayar tana ta addu’ar Allah yasa yayi replying, wayar tana yin qara kuwa ta bude sai ta ga ya rubuta: “yes” Su Hafsat dai da ke daki sai ihun Zara suka ji daga bathroom din yayinda suka cigaba da yi mata dariya. Ko da ta fito rungume Hafsat tayi tace “he said he likes it Babes, I am so happy” Kafin Hafsat tayi Magana ne tace “you know what, a kira mun Henna temple ta dawo tayi mun dayan hannun da qafafuwa” STORY CONTINUES BELOW Hafsat tana dariya tace “wallahi baki isa ba, saidai idan mun dawo daga Bridal shower” Zara ta kalli agogo tace “okay babes amma dai kar a manta a kira ta din” Hafsat ce ta Harare ta tace “alqawarin mu” Zara tayi ajiyar zuciya tace “anything for you babes” Hafsat tace “you are coming to my Dinner with Ya Farouq as a couple” Kafin ta rufe baki ne Zara tace “what? No babes, kin manta yana da mata ne? kuma fa munyi da Sweetie zamu je tare” Hafsat tace “well, kin dai yi alqawari, find a way to make it happen, babu ruwana da wani Mahmood” Murmushi Zara tayi tace “its not going to be possible domin kuwa ko giyar wake na sha nasan Ya Farouq bazai taba zuwa da ni ba” Fati Mamza ce ta shigo tare da Team dinta wadda dama ita ake jira don yi ma Amarya kwalliya. Zara dai mutuminta ta kira wato Jide of Stola, Jide shi yake yi ma Zara kwalliya har Hafsat na fadin ranar bikinta dai mijinta bazai taba bari wani gardi yayi mata kwalliya ba. Zara tana ta dariya. **************** Bridal shower din Hafsat yayi kyau sossai, an ci an sha sannan anyi wasanni kamar dai yadda ake yi. Shahararren mai daukar hoton nan BigH ya dauke su hotuna. Zara kuwa tunda Farouq yayi replying message dinta komai ma dadi yake yi mata. Hafsat har mamakin qawarta take domin kuwa farin cikin da take ciki kamar ma ita ce amaryar. Ko da Hafsat tayi waya da Mukhtar sun ba junan su labarin Farouq da Zara inda suka dinga dariya. Sunyi alqawarin sai sun taka rawar gani a wurin hada aminan nasu har ta kai su ga aure. *************** Washegari ranar Kamu tun da safe ake ta shirye shirye. Da rana ne Safa da Marwa suka iso daga France inda driver din Mamy ya dauko su. Tare da wata qanwar Anty suka zo mai suna Saima. Basu dade da sauka ba suka wuce gidan bikin. Zara tayi murnar ganin qanen ta sossai, haka kuwa aka cigaba da hidima tare da su. A the Glam Hall event centre aka yi kamun Hafsat. Mutane sun cika sossai yayinda amarya ta ci kwalliyarta gwanin ban sha’awa. Su Zara anko suka yi na atamfa, sunyi kyau sossai. ko da dangin Mukhtar suka fesa ma Hafsat turare aka yi ciniki da qawayen amarya si aka yi sanarwar shigowar ango da abokanen shi. Aikuwa tunda aka yi wannan sanarwar Zara ta kafa ma hanyar shigowa ido don ganin Yayan ta. Ko da suka fara shigowa tayi ta zuba ido bata hango shi ba. har komawa tayi kusa da su don neman shi amma bata gan shi ba. Hankalinta a tashe yayinda ranta yake a bace ta fara dialling lambar wayar shi, har ta gama ringing bai dauka ba, ta kira ya fi sau biyar shiru. STORY CONTINUES BELOW Ta juya don zuwa wurin Mamy ta tambaye ta kenan wata qawar su Zaliha ta taba ta tace “Hafsat tana neman ki” Ba don Zara ta so ba sai ta bi Zaliha suka koma wurin Hafsat. An kira amarya da qawayen ta su fito suyi rawa yayinda ake ta wasa amarya da babbar qawarta Zara. Zara dai gaba daya hankalinta baya wurin, tunani kawai take yi akan dalilin da yasa Farouq bai zo bikin abokin shi ba. Juyawa tayi ta kalli fuskar Mukhtar ta ga yana ta fara’a tare da gasiawa da mutane. Da sauri ta zame ta nufi wurin Mamy ta duqo saitin kunnen ta tace “wai Mamy ina Ya Farouq ban gan shi ba?” Mamy tace “bakuyi waya da shi bane? Ruqayya ce ba lafiya amma da sauqi, sai da na je na dubo ta sannan na zo nan” Zara tace “ooooh, Allah ya bata lafiya” daga nan ne ta koma wurin su Hafsat. Har dai aka kammala Kamun babu Farouq babu dalilin shi. haka aka koma gida Zara tana ta jin haushi. Gaba daya har aka kwanta bacci Hafsat bata gane kan Zara ba. ko Mahmood din nata da ya kira ta ya gano lallai akwai abinda ke damunta wanda yayi ta fada mishi amma ta gwada babu komai. Dayake ma Mahmood din nata akwai flows na soyayya ya dan yi nasarar shawo kanta har tana dariya. ********** Washegari aka daura auren Mukhtar Abubakar da Hafsat Khalil akan sadaki naira dubu dari. Aikuwa ana daura auren aka dinga guda cikin gidan yayinda aka dinga tsokanar amarya. A nan gidan su Hafsat aka yi yinin biki, shagali sossai aka yi. da yamma ne aka dauki amarya sai gidanta bayan iyaye sunyi mata nasiha akan zaman aure. Hafsat tayi kuka sossai yayinda Zara ta dinga yi mata dariya har tana fadin sai ta gaya ma Ya Muky cewa amaryar shi tana kuka don za’a kawo ta gidan shi. ************ Da daddare ne aka fara shirin Dinner. Fati Mamza da team dinta suka dawo don yi ma amarya kwalliya yayinda Zara ta kwashi kayanta don zuwa studio din Jide of stola tunda dai bazata iya gayyatar shi zuwa gidan Hafsat ba. Direban Mamy ne ya kaita yayinda yace mata zai je ya hadu da sauran direbobin don kwaso baqi ya kai su event hall idan ta gama sai ta kira shi. Zara tana nan gaban Jide yana ta yi mata kwalliya ne ta dinga kiran wayar Mahmood wanda suka yi zasu hadu a dinner din amma baya dauka. Da ta gaji ne ta tura mishi text message. Tsaye take a gaban madubin Jide yayinda team din shi suke ta yaba kyan da Zara tayi. Sanye take cikin wani royal blue material wanda shine ankon bikin yayinda ta daura head royal blue. Simple accessories ta sa, tayi kyau sossai. Nan da nan tayi mishi transfer din kudin shi yana ta washe baki domin kuwa Zara ba qananan kudade take biyan Jide ba. Direban Mamy ta kira a waya amma not reachable, haka ta dinga trying wayar shi amma bata samu. Jide ya nemi da driver dinshi ya kai ta amma ta qi musamman da ta tuno warning din da Farouq yayi mata kwanaki. Farouq ta tuno ta kira wayar shi bai amsa ba, ta kira ya kai sau uku sai tayi ringing har ta tsinke amma bai amsa ba. Text message ta tura mishi kamar haka: “Ya Farouq please idan zaka je bikin Ya Muky ka biyo ka dauke ni, I am stuck a wani make up studio” Bayan ta aika da message din ne ta riqe wayar tana jira. Kiran Hafsat ne ya shigo wayarta inda tace “hajiya kina ina ne gashi har zamu shiga hall?” Zara tace “yi haquri babes, driver nake jira ya dawo. Gani nan zuwa” Bayan sun gama waya ne saqo ya shigo wayarta daga Farouq kamar haka: “address?” Ajiyar zuciya tayi tare da yin murmushi ta tura mishi da address din tare da yi mishi godiya. A lokacin da Zara ta aika ma Farouq text message ya riga ya iso event centre din. babu shiri ya juya ya koma don dauko ta. Farouq ya shigo harabar studio din Jide of Stola inda ya samu wuri ya faka. A lokacin kuwa Zara ta fito tana tsaye a harabar wurin yayinda take qoqarin kiran shi don ji ko ya iso. Hango ta yayi tsaye yayinda ta bashi baya. Shiru yayi yana qare mata kallo tas, ta bala’in yin kyau. Horn yayi tare da haska ta da wutar motar shi wanda yasa ta juyo da sauri harda kare fuskarta da hannun ta. Farouq dai cigaba da kallonta yake yi kamar yau ya fara ganin Zara, tayi mishi kyau ba kadan ba. Gani yayi tayi murmushi sannan ta latsa wayarta ta kai kunnenta. Ji yayi wayar shi tana ringing yayinda ya ga sunan ta. Cikin mamaki yace “whats wrong with this girl?” girgiza kai yayi ya amsa cikin fada yace “ina wasa da ke ne? zan tafi in bar ki fa” Gani yayi tayi murmushi sannan tace “Ya Farouq be a gentleman and bring the car here or come and carry me” Zaro idanuwa yayi yace “what????!!!! Are you mad?” fashewa tayi da dariya sannan tace “thank you Big brother” ta kashe wayar tana kallon shi. *************

Post a Comment for "BA SONTA NAKE BA CHAPTER5"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...