BA SONTA NAKE BA CHAPTER3 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BA SONTA NAKE BA CHAPTER3

BA SONTA NAKE BA CHAPTER3

- - Post a Comment
BA SONTA NAKE BA CHAPTER 3 R
uqayya dai samun kujera tayi ta zauna ta fashe da kuka yayinda ta dafe kai tana tunanin qaryar da zata yi ma Farouq domin kuwa rabuwa da shi is not an option for her.+ Bata taba sanin cewa Farouq ya gane ba, sannan abinda ya fi bata mamaki shine yadda bai fada mata ba sai yanzu. Jikinta har kyarma yake yayinda take ta kuka. Bata Ankara ba sai ganin shi tayi ya fito daga wanka inda ya cigaba da shirin shi hanakali a kwance. Bayan ya kammala ne ya haye gadon shi ya kwanta. Ruqayya ta miqe cikin hanzari ta nufi wurin shi tana share hawaye ta zauna a gefen shi tace “Honey let me explain what happened please listen to me” Farouq wanda ya qagara ya ji bayanin ta yace “I am listening”. Ajiyar zuciya tayi yayinda ta fara bashi labari kamar haka: “A lokacin da mahaifi na ya rasu, ni da Hajjaju mun kasance mu kadai a gidan mu, sai mai gadi a waje. Bayan ya rasu da wata biyar ne watarana da daddare ‘yan fashi suka kawo mana hari har cikin gida. Sun kashe maigadin mu inda suka samu damar shiga har cikin gidan mu. A lokacin ne..” daga nan Ruqayya ta fashe da wani sabon kukan. Farouq ne ya miqe da sauri cikin tausayawa ya janyo ta ya rungume yana fadin “its okay, you don’t need to go further” Ajiyar zuciya Ruqayya tayi yayinda ta ji dadin kalaman shi. A duniya zata iya yin komai don ta kasance matar Farouq, she cant afford to lose him. cikin sanyin murya ne tace “Honey, Zara..” yana shafa kanta yace “Zara what? Zara qanwa ta ce, she is my baby sister so relax, babu abinda yake tsakanin mu” qara rungume shi tayi cikin farin ciki marar misaltuwa. Soyayyar lafiyayya ta gudana tsakanin Farouq da Ruqayya a wannan daren domin kuwa Farouq ya cire duk wani zargi a ran shi ya rungumi Ruqayya a yadda take. Ruqayya kuwa kamar ta zuba ruwa a qasa ta sha don farin ciki. ************ Bayan su Farouq sun wuce Germany da sati daya ne Sadiq ma ya koma makaranta. Kamar kullum gidan ya koma daga mamy sai Zara domin kuwa Abba kullum yana tafiye tafiye. Idan har yana Nigeria ma ba’a ganin shi sossai domin dai yanayin aikin nashi baya bashi lokacin kan shi balle na iyalin shi. lokutta kadan ne zaka gan shi a gida cikin iyalin shi. Zara dai har yanzu tana nan tana aika ma Farouq hotunan ta kamar kullum tare da bashi labarin abubuwan da take yi. A bangaren Farouq kuwa ko ya gani baya yi mata reply sannan ita kuma bata damuwa da hakan. *************** BAYAN WATA SHIDDA AL-HUSSAIN MANSION Kwance take a kan gadon ta tana ta baccin ta cikin kwanciyar hankali. Qarar wayar ta ce ta tashe ta daga baccin da take yi. Tsaki tayi sannan ta janyo pillow ta toshe kunnen ta da shi. Haka wayar tayi ta ringing tana tsinkewa bata daga ba. Wuraren qarfe goma sha daya Mamy ta qwanqwaso qofar dakin ta shigo. Murmushi tayi ta nufi gadon ta zauna tare da zare pillow din da Zara ta rufe fuskarta da shi. Motsi tayi ba tare da ta bude idanuwan ta ba tace “Mamy please” Mamy tayi dariya sannan tace “I thought kin ce zaki je gidan su Hafsat yau” STORY CONTINUES BELOW Da sauri Zara ta bude idanuwanta ta miqe tana fadin “oh my God, whats the time? Yau Hafsy zata ci qaniya na” Mamy tana murmushi tace “its just past 11, maza je kiyi wanka ki sauko kiyi breakfast” Zara ta sauka daga kan gadonta sannan ta duqo tayi ma Mamy kiss a kumatu tace “okay Mamy” ta nufi dressing room dinta don shirin wanka yayinda Mamy tayi murmushi ta miqe ta fita. Zaune take a cikin qaton Jacuzzi din kewayen ta, qamshi kawai ke tashi kamar anyi barin turarruka, wasa take da ruwan kamar kullum. Idanuwan ta a lumshe suke yayin da take jin dadin ruwan da take ciki. Tayi kusan minti talatin a cikin Jacuzzi din sannan ta dauraye jikinta ta fito. Tana zaune a gaban madubin dakinta tana ta shafe shafen mai da turaruka. Wayar ta ce tayi ringing, ta miqe ta nufi bed side drawer inda wayar take ta dauka. Ganin sunan Hafsat ne yasa tayi murmushi ta amsa tare da fadin “Babes how far” a dayan bangaren Hafsat tace “wallahi if it were possible for me to change a friend I would have done so tuntuni Zara” Zara tayi dariya tare da daga kafadarta tace “toh ko zaki gwada ne?” Hafsat tayi tsaki tace “is that some sort of threat?” Zara ta fashe da dariya tare da hawa kan gadonta tace “sorry bestie, I love you” Hafsat tayi murmushi tace “and I hate you, where have you been ina ta kiran ki tun dazu? Hala kina ta baccin nan naki na mamaki?” Zara tayi murmushi tace “sorry babes gani har nayi wanka ma, as soon as I eat my breakfast zan qaraso”. Bayan sunyi sallama ne ta nufi closet dinta don daukan rigar da zata sa. Tsayawa tayi tana bin kayan ta kamar kullum, wata farar long top ta hango can qasan jerin kayan ta. Murmushi tayi tace “its definitely you baby”. Dakinta ta koma ta latsa intercom, a dayan bangaren Larai ce ta amsa cikin girmamawa. Zara tace “please come” cikin mintuna biyu kacal Larai ta turo qofar dakin Zara cikin ladabi ta duqa har qasa tace “ina kwana Anty” Zara tace “lafiya Larai ba sai kin duqa ba kafin ki gaishe ni, zo ki cire mun wannan kayan” Larai ta miqe ta bi Zara har closet dinta sannan ta nuna mata kayan da zata ciro mata ta juya ta koma dakin. Zara ta sani sarai idan da kanta zata zaro kayan gaba daya sai ta birkita closet din shiyasa ta sa Larai ta dauko mata. Zara tana nan zaune Larai ta fitar mata da kayanta sannan ta fita. Bayan ta shirya ne ta dauki wayar ta tare da makullin motarta ta fita. Ko da ta sauko straight dinning ta wuce ta zauna, kayan abinci ne aka jera kala kala kamar kullum. Murmushi tayi ta sa hannu zata bude warmer din da ke gaban ta sai ga asabe ta shigo da sauri tace “Anty bari in zuba miki” cikin ladabi ta duqa har qasa tace “ina kwana” Zara tace “tashi asabe, lafiya lau” plantain ta nuna ma Asabe tace “I will take this only” nan da nan Asabe tayi serving dinta sannan ta koma kicin. Bayan ta cinye plantain din ne ta miqe ta wuce sashen Mamy. Mamy tana zaune a kan daya daga cikin Royal chairs din falonta inda take waya cikin nishadi. Zara ce ta nufi wurinta ta kwanta akan cinyar ta tana sauraren ta. Mamy ta shafa fuskar Zara tare da fadin “yanzu next week din Ruqayya zata dawo? Toh kai kuma sai yaushe?” ta dan yi shiru tana sauraren shi sannan tace “okay toh Allah ya dawo mun da kai lafiya my prince” Bayan sunyi sallama ne ta kalli Zara tace “my princess har kin fito?” tace “yes Mamy, Ya Farouq ya kusan dawowa ne?” Mamy tace “eh, next month yace amma dai Ruqayya tana nan dawowa next week” Zara ta miqe tace “uhm, Mamy wallahi ni dai bana son Anty Ruqy, batada fara’a. Shima dai ya Farouq duk matan duniyan nan ya rasa wadda zai dauko sai ita” Mamy ta fashe dariya tace “Zara hoo” STORY CONTINUES BELOW Zara tace “Mamy bari in je, I will be back much later” Mamy tace “okay princess, be careful and have fun” haka Zara ta fita Mamy tana mamakin yadda bata son matar Farouq. Tunda ta fito harabar gidan securities din gidan ke ta gaishe ta, kamar kullum sai da ta amsa su cikin fara’a sannan ta nufi motar ta qirar Mercedes Benz ta shiga ta tada ta fita daga gidan. ************** Tana kan hanyar zuwa gidan su Hafsy kawai ta tsinci kanta cikin farin ciki marar misaltuwa. Bata san lokacin da ta fashe da dariya ba tace “Finally he is coming back” kamar ta tuno wani abu kuma sai gani nayi ta faka motar ta gefen titi ta dauki wayarta ta bude camera tayi snapping selfie sannan ta yi dan gajeren rubutu ta tura. KHALIL MANSION Zaune suke a falon gidan su yayinda suke ta hira da Mom dinta, Zara ce tayi sallama. Cikin murna Hafsat ta miqe suka rungume juna. Zara ta tsugunna har qasa ta gaida Mom, Mom tace “ya su Mamy?” Zara tace “they are fine Mom” Hafsat ta ja hannun Zara suka nufi dakin ta. Zara tana kwance a kan gadon Hafsat yayinda Hafsat take nuna ma Zara wasu kayan da ta siyo a India last week da ta raka Mom. Zara ta qura ma wayar ta ido yayinda ta bar Hafsat tana ta surutu. Ganin cewa Zara tayi banza da ita ne yasa ta kalle ta tace “babes ina ta magana kin share ni” kafin Zara ta amsa ta ne ta qwace wayarta tana fadin “what is it you are looking at that is more important than what I am saying?” Da sauri Zara ta miqe ta biyo Hafsat cikin fushi tana fadin “give me my fone” aikuwa nan da nan suka fara zagaye dakin yayinda Hafsat take ta dariya. Da Zara ta gaji ne ta koma ta zauna yayinda Hafsat ta duqe tana mayar da numfashi ta kalli wayar Zara tana murmushi tace “dama na san bazai wuci hoton nan kike kallo ba” Zara ta Harare ta yayinda Hafsat ta cigaba da fadin “wai ke Zara I don’t understand you, ya akayi kika bari yayi aure bayan kin san kina son shi??” Dariya Zara tayi tace “who told you cewa son shi nake? He is my brother for crying out loud, sau nawa zan fadi miki hakan” Hafsat tayi murmushi tace “and you love him” Zara ta bata rai tace “this is something I cant explain, the reality dai yanzu shine I am head over heels for Mahmood Tafida” Tsaki Hafsat tayi tace “no babes, you are obsessed dai. Ni wallahi na rasa meye naki da maqale ma wannan yaron. Sai shegen girman kai” Zara ta koma bisa gado ta kwanta tare da fadin “oho dai”. Haka dai suka cigaba da rubuta list din abubuwan da zasu siyo na bikin Hafsat din wanda ya rage wata uku. BAYAN SATI DAYA Al-HUSSAIN MANSION Zaune suke a bisa dinning inda suke breakfast suna hira. Mamy ce tace “yace Mukhtar ne zai je ya dauko ta daga airport” Abba yace “toh madallah, yakamata dai ya dawo gida haka nan. Mu da dan mu amma wasu su fi mu more mishi” Mamy tayi dariya. Zara ce ta shigo dinning din cikin fara’a tace “morning Sir” ta nufi wurin Mamy tace “morning Mamy” tare da yi mata kiss a kumatu. Abba cikin fara’a yace “princess how are you, kin tashi lafiya?” tace “fine Abba” yayinda ta ja kujera a kusa da shi ta zauna. Mamy ce tace “yau kin tashi da wuri, akwai lecture kenan” Zara tayi murmushi tace “wallahi Mamy wani lecture ne muke da, idan mutum yayi latti bazai shiga ba. lecturer din is very strict” Mamy tace “aikuwa gara ki shiga da wuri because bana so kina missing lectures dinki” Apple ta janyo ta fara ci yayinda suka dan taba hira sannan tayi musu sallama ta tafi. Abba ya kalli Mamy yace “I really wanted her for him” Mamy tayi murmushi tace “ban fitar da ran hakan zai faru ba Abba, Allah ya zaba mafi alkhairi” yace “Ameen” NILE UNIVERSITY Hafsat da Zara zaune a cafeteria inda suke hira. Zara ce tace “yau wannan matar mai baqin hali zata dawo” Hafsat tayi dariya tace “wacce mata kuma?” Zara ta tabe baki tace “anty Ruqy mana, ai gara ma da ya koro ta yayi zaman shi can abinshi” Cikin mamaki Hafsat tace “yau na ga ikon Allah, mutum da matar shi. toh wai ma tsaya me ya ruwan ki da ita ne?” Zara tace “toh ba yaya na take aure ba, ni kawai bana sonta” Dariya Hafsat tayi tace “babes you have a serious problem” Zara tace “I swear idan ta dawo ta nemi ta shiga tsakani na da Ya Farouq sai na taka mata birki don na lura bata da kirki” Hafsat tana dariya tace “toh sau nawa kuka hadu da har kika san batada kirki?” Zara ta harari Hafsat tace “haduwar da muka yi da ita baki ga kallon banzar da take yi mun ba?” Hafsat cikin dariya tace “ina na gani tunda bana wurin a lokacin” Haka dai Zara ta cigaba da masifa yayinda Hafsat ta cigaba da kwasar dariya. Suna nan zaune wata Ferrari ta danno kai a harabar wurin. Tuni idanuwa suka koma kan motar. Zara da ke sanye da gilas a idanuwan ta tayi saurin cirewa tare da fadin “oh my God, today is my lucky day” Hafsat ce ta Harare ta tace “lucky day my foot” A dayan bangaren wani kyakyawan saurayi ne ya fito daga motar sanye cikin jeans baqi da wata T-shirt fara, qafar shi sneakers ne sannan yana riqe da wayar shi a hannun shi. Mahmood Tafida kenan, babban yaro a Nile University, da a wurin Senator Isah Tafida. Friends dinshi ne suka qaraso wurin shi inda suke gaisawa. Daya daga cikin abokanen nashi mai suna Nura ne yace “guy ga fa mutumiyar ka can a Caf” juyowa yayi ya hango Zara tare da Hafsat zaune. Murmushi yayi yace “let me go check on her” Munnir ne yace “abokina kana bani mamaki, ka dai san wannan yarinyar ba irin tamu bace ko?” Mahmood yayi murmushi tare da buga kafadar Munnir yace “idan na samu Zara na tuba” suka fashe da dariya. Ganin Mahmood ya doso wurinsu ne yasa Hafsat ta miqe tace “ni kin ga tafiya ta, bana son harkar jan aji na banza” Zara tana dariya Hafsat ta wuce wanda ko kallon shi bata yi ba. Cikin sallama ya qarasa wurin Zara inda yace “how is my Cutie doing?” Zara tayi murmushi tace “she is fine and you?” yace “I just got better after seeing my Cutie” murmushin jin dadi tayi. Mahmood yace “wai me nayi ma bestie dinki ne na ga kamar bata sona tare da ke? Ko dai wani take yi ma campaign ne?” Zara tayi dariya tace “don’t mind her, kasan bikinta ya matso so she is a bit nervous about everything” murmushi yayi yace “Allah ya nuna mun ranar namu bikin” tace “Ameen”. ************ WANENE MAHMOOD TAFIDA?? Mahmood Tafida ya kasance yaro a gidan Senator Isah Tafida, Mahood ya taso cikin gata na iyaye domin kuwa babu abinda ya nema da ya rasa.+ Mahaifin shi ko a bangaren siyasa ba’a son shi domin kuwa duk wata kafa ta cin hanci da rashawa a bayan Isah Tafida take. Asalin Mahmood ya faro karatun shi a qasar America inda har ya kai mataki na uku amma saboda rashin mayar da hankali da iskanci na shaye shaye da neman mata da ya sa a gaba ne aka kore shi daga makarantar. Da wannan ne Mahaifin shi ya dawo da shi Nigeria inda ya saka shi a Nile University. Mahmood dai ko da ya dawo Nile bai canza hali ba. Abokanen shi Munir da Nura suma ‘ya’yan manya ne a garin Abuja wadanda halayen su ya kasance iri daya. A kullum zaka gan su a club da ‘yan mata inda suke sharholiyar su har asuba. Duka wata uku kenan da Mahmood ya shigo Nile University inda yayi tozali da Fatima Zara Al-Hassan wadda ta kwanta mishi a rai. Wani ikon Allah Mahmood bai taba son wata mace ba kamar yadda yake son Zara. A tunanin shi zai iya barin halin shi idan har ya samu Zara. A dalilin iya tsara ‘yan mata ne yasa ya siye zuciyar Zara. Hafsat dai bata son Mahmood ko kadan domin kuwa bata yadda da halin shi ba, a kullum tana kan ba qawar ta shawara akan ta rabu da shi amma sam Zara ta qi. Abu kamar wasa dai Zara da Mahmood sun qulla soyayya mai qarfi a tsakanin su. CIGABAN LABARI NNAMDI AZIKWE INTERNATIONAL AIRPORT Da yamma ne Mukhtar ya je airport domin dauko Ruqayya. Yana nan zaune yana jiran isowar jirgin su ne wayar shi ta fara ringing. Ko da ya duba sunan abokin shi ya gani. Cikin fara’a yace “abokina how far, gani a airport ina jiran wifey dinka fa” a dayan bangaren sai da Farouq ya dan yi shiru sannan yace “okay my friend, kar ka manta gidan nan da na maka bayani zaka kai ta, that’s her new house” Mukhtar yayi dariya yace “ai bazan yi kuskuren kai ta Villa ba” murmushi kawai yayi domin kuwa ya san halin Mukhtar da tsokana. Sun dan taba hira kadan sannan ya ji ana bada sanarwar isowar jirgin. Bayan sunyi sallama ne ya miqe don tarbar Hajiya Ruqayya. Tafe take cikin qasaita da isa, tafiya take kamar bata so ta taka qasa. Sanye take cikin wata doguwar jallabiya baqa mai shegen kyau. Idanuwan ta sanye da glasses ta riqe hand bag dinta yayinda wani ma’aikacin airport din yake biye da ita da akwatunan trolley dinta. Ganin Mukhtar da tayi ne yasa ta dan yi murmushi sannan ta qarasa wurin shi. cikin fara’a yace “Hajiyar mu barka da isowa” cikin isa tace “yaya na, mun same ku lafiya?” yace “Alhamdulillah” daga nan ne yayi musu jagora zuwa parking lot inda ya faka motar shi. ************ Bayan sun hau kan hanya ne Mukhtar yace “ya kika baro oga?” tace “he is fine, cant wait for him to join me” murmushi kawai Mukhtar yayi. Wayar ta ce tayi qara ta amsa cikin fara’a tace “qawata how are you, gani na shigo gari ina kan hanyar zuwa gida” a dayan bangaren Aliya tace “wow, I am happy girl friend, insha Allah ina nan zuwa gobe” tace “toh shikenan qawa, ki gaida su Ummi. Bye” FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION Gaban get din gidan Mukhtar ya tsaya inda yake ta horn. Cikin sauri aka bude get din gidan yayinda ya shiga ya faka a gab da porch din gidan. STORY CONTINUES BELOW Fitowa tayi tana qare ma gidan kallo tana murmushi, dream house dinta, komai na gidan kamar yadda ta sa ayi mata. Securities din gidan ne suka dinga zuwa suna kawo mata gaisuwa wanda gaba dayan su babu wanda ta kalla balle ta amsa su. Da suka ishe ta da gaisuwa ne yasa ta daga hannunta alamun su tafi su bata wuri. Haka suka koma jikin su a sanyaye. Tuni daya daga cikin ma'aikatan ya bude boot din motar yana ta saukar da akwatinan ta yayinda ta kalli Mukhtar wanda yake shirin komawa cikin motar shi tace “yaya na bazaka shigo ba?” yayi murmushi yace “nope, akwai abubuwan da zan qarasa a ofis, next time” Bayan sunyi sallama ne ta wuce cikin gidan yayinda Mukhtar ya ja motar shi a ranshi yana fadin “oh my friend, why her?”. ************ Tun da Ruqayya ta dawo Zara bata je gidan ta ba, har gida Ruqayya ta zo amma Zara ta qi fitowa su gaisa, da Mamy ta matsa mata ma sai cewa tayi bata da lafiya idan ta warke zata je har gida ta gaishe ta. Mamy dai tana mamakin yadda Zara take nuna tsana akan Ruqayya. *************** A kwana a tashi babu wuya yau asabar, yau ne Umar Farouq zai dawo daga Germany. Tunda Zara ta tashi daga bacci take cikin farin ciki marar misaltuwa. Gaba daya gidan hatta masu aiki sun san Zara tana cikin farin ciki. Da rana ne ta kira Mukhtar a waya don jin qarfe nawa zai je dauko Farouq domin kuwa tana so ta raka shi. A lokacin kuwa Mukhtar yana ofis yana wani aiki mai muhimmanci. Ganin kiran Zara ne yasa ya amsa cikin fara’a yace “Small madam ya kike ne? kwana biyu kin share ni” tayi dariya tace “haba Yaya Muky ai ban isa ba, wallahi school ne, kasan aski ya kawo gaban goshi I need to do my family proud” murmushi yayi yace “we are proud of you” Dariya tayi tace “thank you Ya Muky, qarfe nawa ne zaka je dauko shi, I wanna tag along” agogon shi ya duba yace “sai qarfe hudu na yamma, do me a favour ma ki je on my behalf kawai, wallahi I have work piled up a ofis dina” Da sauri Zara tace “anya kuwa Ya Muky? Kasan halin ya farouq fa, kar yayi mun fada” murmushi yayi yace “common Zara babu fadan da zai yi trust me” jikin ta a sanyaye tace “okay toh, bye”. Miqewa Zara tayi tana tunanin ko dai ta tura mishi direba ne kawai domin kuwa ta san halin Farouq sossai. Hafsat ta kira a waya ta gaya mata yadda suka yi da Mukhtar tace "please babes ki zo mu je tare". Hafsat tace “wallahi Mom ta aike ni Gwarinpa kuma I might not return early, toh meye? Ki je kawai mana me zai yi miki?” Zara tace “kin fa san halin shi” Hafsat ta katse ta tace “ki je ki dauko shi ki kai shi gida ki ba Hajiya Ruqayya haushi don na san da tasan ke zaki je dauko mijin ta bazata lamunta ba” Zara tayi tsalle tace “yesss, I love you bestie” ta kashe wayar sannan ta nufi wurin Mamy don gaya mata yadda tayi da Mukhtar. NNAMDI AZIKWE INTERNATIONAL AIRPORT Tsaye take a harabar arrivals na Airport din, sanye take cikin pencil jeans da top sannan ta dora rigar kimono sai dan qaramin gyalen da ta yafa a kanta, takalmin da yake qafar ta sneakers ne na mata. Tayi kyau sossai. Riqe take da wayar ta inda take ta faman daukar selfie. Mutanen da suke kai da komowa sai kallon ta suke yayinda ta birge wasu sannan wasu suna mamakin yadda bata damu da ana kallon ta ba. Zara kenan, the girl with the non chalant attitude. Matafiyan da suka sauko daga jirgn saman da ya sauka minti talatin da suka wuce ne suka fara shigowa harabar wurin yayinda kowanne yake ta qarasawa wurin dan uwan shi. STORY CONTINUES BELOW Zara ce tayi ta zuba ido tana neman inda zata gan shi. Sai da kusan kowa ya gama shigowa sannan ta hango shi sanye cikin sweatpant baqi da wata Navy blue shirt. Ya qara kyau sossai. Yana janye da wani qaramin akwatin trolley na matafiya yayin da ya rataya wata jaka ta laptop a bayan shi. wayar shi ce a hannun shi yana neman kiran abokin shi Mukhtar don jin inda yake kamar yadda suka yi da shi akan shine zai zo tarbar shi. “Ya Farouq!!” muryar ta ya ji ta qwala mishi kira. Da sauri cikin mamaki ya daga kan shi don tabbatar da muryar wadda ya ji. A guje ta qaraso wurin shi tare da rungume shi wanda hakan ya faru ne a cikin qanqanin lokaci. Tsigar jikin shi ne ya tashi yayinda zuciyar shi ta buga, ji yayi tana fadin “Ya Farouq welcome back, I missed you soooo much” Ture ta yayi baya har sai da ta kusa faduwa yace “what’s wrong with you? are you mad?” Zara ta tabe baki tace “toh wai me nayi maka?” ba tare da ya amsa ta ba yace “me kike yi a nan? Ina Mukhtar?” Murmushi tayi ta kai hannunta ta janye trolley din da ke hannun shi sannan tace “aiki ne yayi mishi yawa shine nace ya bari in zo in dauko ka” girgiza kai yayi a ranshi yana fadin “I will deal with him”. Haka suka jera suka nufi parking lot yayinda take ta zuba mishi surutu wanda ko jin ta baya yi. ************** Suna tafe kan hanya wanda shi yake jan motar yayinda Zara take zaune a gefen shi tace “Ya farouq kana ganin messages din da nake aika maka?” Girgiza kai yayi alamun eh. Cikin shagwaba tace “shine baka taba acknowledging ba?” kallon ta yayi cikin mamaki sannan ya mayar da idanuwan shi akan hanya. Turo baki tayi tace “I mean, kace nayi kyau ko ban yi ba, anyways nasan ma nayi kyau ai tunda dai ni din kyakyawa ce” Tsaki yayi ba tare da ya kalle ta ba yayinda ta cigaba da zabga mishi surutun ta da ta saba. FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION Ko da suka iso gidan Farouq gaba daya securities da ma’aikata suka rufe motar suna yi ma oga barka da dawowa. Haka Zara ma ta sha gaisuwa wanda gaba dayan su sai da ta amsa su cikin fara’a sabanin matar gidan. Haka suka koma suna ta yaba ma Zara. Zara dai kallon gidan take yi tana mamakin kyan tsarin shi, yau ne rana na farko da ta fara zuwa gidan dukda kuwa dama bata taba zuwa wancan gidan da suka bari ba. A ranta ne tace “lallai ma anty Ruqayya, wannan gidan ai yayi mata girma dayawa” A lokacin da suka iso Hajiya Ruqayya tana can sama tana hira da qawarta Aliya a waya. Zara tana riqe da jakar laptop din shi suka shiga gidan. Cikin mamaki Zara ta cigaba da kallon tsarin gidan wanda yayi kama da aljannar duniya. Gani tayi ya nufi wani sashe na gidan wanda ta bi bayan shi, sashen shi ne wanda yayi masifar kyau. Zara dai bata san lokacin da tace “woooow” ba. Qofar dakin shi ya bude ya shiga wanda ba tare da tunanin komai ba Zara ta bi bayan shi. Bai Ankara ba ya ji ta fada kan gadon shi tana fadin “wow Ya farouq, this is beautiful” Daure fuska yayi yace “what the hell…” kafin ya qarasa maganar shi ne Ruqayya ta turo qofar dakin ta shigo, da gudun ta cikin kissa ta qarasa wurin shi ta rungume shi tare da yi mishi kiss a baki tace “welcome home honey, ya hanya?” yace “lafiya, how are you?” Zara tayi gyaran murya yayinda ta tsura musu ido tana murmushi. A razane Ruqayya ta juyo ta ga Zara bisa kan gadonshi cikin wani irin mugun bacin rai tace “Honey what is she doing here?” Zara wadda take zaune a tsakiyar gadon Farouq tace “Anty Ruqy, ina wuni. Tare da Ya farouq muka shigo” Kamar wadda aka yi ma shocking sai ta sauka daga kan gadon da sauri tace “ooops, sorry na hau muku gadon ku” Farouq ya kalli Zara cikin mamaki sannan ya juya ya nufi dressing room din shi ya bar su anan yayinda Zara take ta yi ma Ruqayya bayanin yadda aka yi ta shigo wanda tayi hakan ne don ta bata ma Ruqayya rai. Bayan ya shige bathroom ne ya ji kamar sun fita. Zara dai ko zama bata yi ba ta tafi gida abinta yayinda ta bar Ruqayya tana cika tana batsewa tare da daukan alqawarin sai ta taka ma Zara birki akan rashin kunyar da take yi. Dakinta ta wuce ta ci gayu na qananan kaya wanda suka yi mata masifar kyau domin kuwa dai Ruqy akwai kyau. A lokacin da ta koma dakin shi har ya shirya yana sanye da wandon three quarter da wata t-shirt yayinda yake gaban madubi yana brushing gashin kan shi. Tsaye take a bakin qofar shi tana ta kallon shi tana murmushi. A ranta ne take fadin “Allah ya bar mun kai Farouq” Motsin ta da ya ji a bakin qofar shi ne yasa ya waigo ya dan yi murmushi yace “why are you standing there?” ta nufo wurin shi ta rungume shi suka fada kan gado tace “I missed you a lot honey” tuni ta fara tumurmushe shi yayinda take ta aika mishi da saqonnin kisses kala kala. Ajiyar zuciya yayi yace “I do too dear, I am hungry” turo baki tayi tace “I am here baby” farouq dai ya gane me take nufi domin kuwa a wannan fannin Ruqayya jarababbiya ce ta qarshe don haka ne yace “I mean I wanna eat food, rabo na da abinci tun safe and I am exhausted” Ran ta a bace ta miqe tace “toh mu je dinning ka ci abincin” haka suka fito yana biye da ita. Suna hawa kan dinning din ne masu aiki suka fito don zuba musu abinci. Sun fara ci ne Ruqayya tayi gyaran murya tace “amma Honey yakamata a dinga tsawata ma Zara abubuwan da take yi” cikin rashin fahimta ne Farouq yace “me tayi?” Kallon shi tayi cikin mamaki domin kuwa tayi tunanin zai fahimci abinda take nufi tace “what was she doing in your room dazu? Wai ma ya akayi kuka hadu? Ba Mukhtar ne yakamata ya dauko ka daga airport ba?” Girgiza kai kawai yayi ya cigaba da cin abincin shi ba tare da ya ce komai ba. Wayar shi ce tayi ringing ya duba ya ga Mamy. Cikin fara’a yace “and how is the most beautiful garl in the world doing?” Ruqayya ce ta kalle shi cikin mamaki yayinda ta ji yace “lafiya qalau Mamy, insha Allah zan zo gobe da safe in gan ki kafin in je asibiti” dariya yayi sannan kuma yace “Zara ta dawo?” murmushi yayi yace “take care, I love you”. Daga nan ya miqe yayi gaba abinshi yayinda ta sa ma plate dinshi ido a ranta tace “yace yunwa yake ji amma babu abinda ya ci”. ************* AL-HUSSAIN MANSION Washegari Da safe Mamy tana zaune a kan dinning tana breakfast ne Farouq ya shigo. Cikin sanda ya zagayo ta bayan ta ya rufe mata ido yana murmushi.+ Hannuwan shi ta taba tana murmushi tace “My Prince” ya zare hannuwan shi tare da duqowa yayi mata kiss a kumatu yace “oh my Mamy I really missed you” ya ja kujerar gefen ta ya zauna yayinda tace mishi “ya gajiyan hanya? Hope dai ka huta sossai?” yace “yes Ma” tace “madallah, ya Ruqayya?” ya janyo plate zai zuba abinci yace “she is fine” tambayar Mamy yayi “Abba bai dawo ba?” tace “I think sai zuwa jibi insha Allah”. Haka dai suka cigaba da cin abinci suna hira. Zara ce ta sauko sanye cikin wani crazy pencil jeans da wata sleeveless top, cikin fara’a tace “Mamy ina kwana” Mamy tace “lafiya lau princess”. Kallo daya Farouq yayi mata sannan ya kauda kan shi, kai tsaye kujerar da ke gefen shi ta ja, kafin ta zauna ne tasa hannu ta birkita gashin kanshi tace “Ya farouq good morning” bata jira ya amsa ba ta dauki fork ta sa a plate dinshi ta dauko plantain ta kai bakin ta. Mamy tana kallon su tana murmushi, addu’a take a ranta Allah ya cika musu burin su akan Farouq da Zara. Ran Farouq a bace ya kalle ta yace “meye haka? Baki da manners ko?” cikin shagwaba tace “Ya Farouq me nayi kuma?” tsaki yayi ya ture plate din ya kalli Mamy yace “Mamy I am off”. Mamy ta kalle shi tace “har ka qoshi?” yace “eh Mamy, I will check on you later” ya isa wurinta yayi mata kiss a kumatu yace “I love you”. Mamy dai ta gane cewa saboda Zara ne Farouq ya tashi. Zara tayi shiru yayinda ta bi shi da ido har ya fita. Hawaye ne suke zuba a fuskar ta yayinda ta sa hannu tana sharewa. Da sauri Mamy ta taso ta rungumo ta tana fadin “My zara meye abin kuka kuma? Kin san halin shi ba tun yau ba, me zai sa ki damu kan ki? Qyale shi ki ci abincin ki, bana so kina sa ma ran ki damuwa saboda ciwon ki” Zara tayi ajiyar zuciya tace “Mamy meyasa Ya Farouq baya sona? Am I not his sister? I care about him but he doesn’t, why?” Mamy tace “My Zara ba haka bane, on the contrary Farouq cares about you a lot, kawai bai iya expressing feelings din shi ba ne” Zara ta dago ta kalli Mamy tace “toh amma..” Mamy tace “qyale shi ki ci abincin ki, yaushe ne tafiyar ku Dubai?” Zara tayi murmushi tace “jibi ne insha Allah Mamy” tace “toh Allah ya kaimu” Farouq dai ya fita yana ta mamakin halin Zara, yarinyar gaba daya ta zame mishi matsala a rayuwa. A bangare daya yana so ya nuna damuwar shi akanta sannan a wani bangare kuma baya so ta raina shi. *************** Yana kan hanyar zuwa asibiti ne wayar shi tayi ringing, Tunda ya dawo jiya Mukhtar din yake ta kiran shi a waya amma ya qi amsawa saboda haushin shi da ya ji akan qin zuwa daukar shi da yayi daga airport kamar yadda suka shirya. A yanzu ma babu yadda ya iya ne shiyasa ya amsa wayar domin kuwa Mukhtar ya wuce aboki a wurin Farouq, aminan juna ne sossai, babu secrets din junan su da basu sani ba. Farouq din ne yace “Muky kayi mun laifi, you should have informed me cewa bazaka zo ba da na shiga cab ai” Mukhtar cikin mamaki yace “Haba dan uwa, me yayi zafi? Duk yawan motocin da ke gida a rasa wadda za’a dauko ka da ita sai ka shigo cab? Please kayi haquri” STORY CONTINUES BELOW Cikin tsokana ya cigaba da fadin “Na dai san fushin nan ba don komai ake yin shi ba sai don personal trouble dinka da ta tarbe ka” Farouq ya girgiza kai sannan yace “da gangan ka qi zuwa kenan” dariya Mukhtar yayi yace “ko kadan abokina, wallahi aiki ne yayi mun yawa” Farouq yace “yeah I know abokina, its not easy being an executive” Mukhtar yace “haka dai kace Doc” Farouq yayi dariya yace “I am on my way to the hospital yanzu, insha Allah anjima I will check on you” haka suka yi sallama inda Farouq ya qarasa asibitin shi. CENTRAL HOSPITAL Ofis din Farouq qaton executive ofis ne wanda idan kana ciki dole ka manta da cewa asibiti ne domin kuwa ba qaramin haduwa yayi ba. Bayan sun zauna ne Dr Ibrahim yake yi mishi bayanin wasu patients wadanda suke buqatar surgery yayinda ya nuna mishi files dinsu da yake bisa tebir dinshi. Ko da ya gama duddubawa sai yace “zan shiga in duba su sai ayi surgery din as early as possible insha Allah”. Farouq ya zagaye asibitin gaba daya inda yayi inspecting din komai, babu laifi abubuwa suna tafiya normal. Don haka ne bayan ya ga patients dinshi da zai yi ma surgery ya tattara ya tafi. MUKHTAR ABUBAKAR MANSION Zaune suke a falon Mukhtar suna buga game kamar kullum. Mukhtar ne yace “abokina ka gaya mun gaskiya are you really happy da Ruqayya?” Farouq ya Harare shi yace “me ka gani?” Mukhtar yayi murmushi yace “I can tell idan you are excited about something, akan Ruqayya na kula you are always cold” Farouq yayi ajiyar zuciya sannan ya ajiye control pad din dake hannun shi ya kalli abokin shi yace “the honest truth abokina shine ban san me nake ji game da Ruqayya ba, ina ta qoqarin in so ta kamar yadda yakamata amma I cant. I have realised cewa BA SONTA NAKE BA” Mukhtar yayi murmushi yace “ita din dai kake so kenan” cikin rashin fahimta Farouq yace “wa kenan?” yace “I mean Zara” Runtse idanuwan shi yayi tare da daure fuska yayi tsaki yace “what the hell abokina, sau nawa zamuyi maganan nan” Mukhtar ya katse shi tare da fadin “yeah yeah, ka damu da ita amma baka so ta raina ka blah blah blah, abokina na san ka tun muna yara, ba sai ka gaya mun abinda na riga na sani ba. anyways, whenever you need a listening ear I will always be there” Kafin yayi Magana ne wayar shi tayi qara alamun an aiko mishi message. Ko da ya duba hoton Zara ne ta aiko mishi kamar kullum. Murmushi yayi wanda bai ma san yayi ba yayinda Mukhtar ya kalle shi yace “its her isn’t it?” hararar shi yayi yace “bari in tafi gida tunda yau takura mun zaka yi” Mukhtar yace “yi haquri abokina, na bar maganar” anan ne kuma suka cigaba da hirar su. CALEDONIAN SUITES MAITAMA ABUJA Kwance take a daya daga cikin dakunan Hotel din yayinda take kallon shi. fitowar shi daga wanka kenan. Ko da ya gama shiri dawowa yayi ya zauna a gefen ta yace “I really missed you my Darling” Ruqayya tace “gaskiya Musty this will be the last time da zamuyi hakan, ka fa san cewa I am married. Idan Farouq ya gano abinda nake yi he is going to send me away and I don’t wanna leave him” Ran Musty a bace yace “kina nufin yanzu baki sona ko me?” Ruqayya tace “gaskiya ni ina son mijina..” dakatar da ita yayi yace “amma kuma ba hakan kika nuna mun ba a while ago, infact a yadda kika birkice ya nuna cewa kin dade baki kasance tare da shi ba” Tashi tayi zaune yayinda ta riqe bargon da ya rufe mata qirjinta tace “ni dai na gaya maka, this will be the last time” Miqewa tayi zata shiga kewaye Musty ya sa hannu ya fizgo ta ya tura ta jikin bango yace “I am not done with you Ruqayya, duk lokacin da na buqace ki zaki zo. Kin fahimta??” STORY CONTINUES BELOW Ta bude baki zata yi Magana ne ya tura bakin shi cikin nata inda ya dinga aika mata da saqon passionate kiss. Tuni Ruqayya ta biye mishi domin kuwa tana son yadda Musty yake zama rough akanta a wannan fannin. Fadawa suka yi bisa gado inda suka sake shiga wata duniyar. Bayan komai ya lafa ne Musty yace “I love you so much Ruqs, please don’t leave me” Ruqayya dai ajiyar zuciya tayi tare da tunanin wannan hali da ta jefa kanta. FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION Ruqayya zaune da qawarta Aliya suna hira inda Ruqayyar take bata labarin abinda ya faru tsakanin ta da Musty jiya. Aliya ce tace “amma dai qawa ta yakamata ki natsu ki san me kike yi, kin dai ga Farouq ya amince da ke akan qaryar da kika yi mishi. Bai kamata ki dinga biye ma Musty ba a yanzu. Ki san yadda zaki yi kiyi ending relationship dinnan before it costs you your marriage” Ruqayya tayi ajiyar zuciya tace “its not going to be easy qawata, Musty ya riga ya zame mun addiction. He makes me feel on top of the world” Lumshe idanuwa tayi sannan tace “I love Farouq very much amma ni ina gani kamar ba sona yake yi ba, he doesn’t even care about me” Aliya tace “toh ai duk laifin ki ne, kin manta aikin da boka yayi miki ne?” da sauri Ruqayya tace “sssshhh babes, the walls have ears” Aliya tace “sorry qawa, amma dai na gaya miki gaskiya. Find a way to make him love you sannan ki rabu da Musty” ta gyara zama tace “ban tambaye ki ba ma wai ya labarin Zara?” Ruqayya ta bata rai tace “shegiyar yarinya, rabona da ita tun ranar da ta dauko shi daga airport. Wallahi qawata yarinyar nan idan bata kiyayi kanta ba sai na halaka ta” Aliya tace “forget about her, the most important thing is shi Farouq din bai damu da ita ba” Ruqayya tace “ni fa gani nake kamar yana son yarinyar, kin san fa shi dama wani irin murdaden mutum ne. you never know what is going through his mind” Aliya tace “for now dai qawa, deal with Musty domin kuwa shine babban matsalar ki”. CENTRAL HOSPITAL Zaune yake a ofis dinshi inda yake duba wasu files na marar lafiyan da yayi ma surgery dazu da safe. Banda ruwa da fruits babu abinda ya ci. Tunda ya fito daga surgery din ya shiga ofis dinshi baya fitowa sai lokacin sallah. Yanzu haka dawowar shi kenan daga sallan la’asar inda yake qoqarin qarasa duba takardun da suke gaban shi domin kuwa gobe da safe zai koma domin yi ma patient din surgery na biyu. Kafin ya shiga ofis din sai da ya ba secretary dinshi strict warning akan kar ta bar kowa ya matsa mishi idan ba emergency bane. Kamar kullum bude qofar shi tayi ta shigo ba tare da ta qwanqwasa ba, Farouq ya daga kan shi ya kalle ta sannan ya maida kan shi bisa takardun. Secretary dinshi ce ta biyo Zara inda ta kalli Farouq cikin fargaba tace “sorry Sir, bata tsaya ta saurare ni ba ta shigo” Farouq ya kalli secretary din yace “its okay” ta juya ta fita yayinda Zara tayi murmushi tace “toh wai Ya Farouq dokar harda ‘yan gida?” Farouq bai kalli Zara ba balle ya amsa ta. Kwalin cake din da yake hannun ta ne ta ajiye a kan tebir dinshi sannan ta zauna tace “Ya Farouq how is work? Ka ci abinci?” Dagowa yayi ya harareta wanda yasa ta miqe da sauri tace “subhanalillah, Ya Farouq you look tired. Are you sure bazaka je gida ka huta ba?” Cikin fada yace “hope you know I am extremely busy ko? Ki wuce ki tafi gida kafin raina ya baci” Zagayowa tayi ta gefen shi ta sa hannu ta janye file din sannan ta turo mishi kwalin cake din tace “zan tafi Ya Farouq amma sai ka ci wani abu” ta bude sannan tace “your Favorite carrot cake with little sugar just as you like it” Farouq dai kallon cake din yayi wanda yayi mishi kyau yayinda qamshin duk ya cika ofis din, ya kwana biyu rabon da ya ci carrot cake. Daga kai yayi ya ganta tana kallon shi yace “thank you, zaki iya tafiya” ta tabe fuska tare da komawa kujerarta ta zauna tace “Ya Farouq dama na zo in fada maka cewa gobe zamu je Dubai ni da Hafsy, akwai abubuwa dayawa da zamu siya na bikin ta. From Dubai zamu wuce France akwai saqon da zan kai ma Anty plus na kwana biyu ban je ba” Ji tayi yace “and school?” tace “mun fara mid semester break ai” yace “Allah ya kiyaye hanya, you can go” Zara ta miqe tace “how mean Ya Farouq, I thought zaka ce you are going to miss me” cikin mamaki ya dago ya kalle ta yace “on the contrary No” Girgiza kai tayi ta dauki wayar ta da makulluin motar ta tace “guess what, nima I wont miss you a single bit” ta Harare shi ta fita. Hakan bai yi ma Farouq dadi ba domin kuwa ya ga bacin rai a tattare da Zara wanda shima maganar da tayi mishi ya bata mishi rai. Dafa kanshi yayi yace “oh Farouq what is wrong with you?” Cake din da ta kawo mishi ne ya kalla yace “how I missed this”. Washegari tun da safe su Zara suka hau jirgi sai Dubai. *************

Post a Comment for "BA SONTA NAKE BA CHAPTER3"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...