BA SONTA NAKE BA CHAPTER 9 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BA SONTA NAKE BA CHAPTER 9

BA SONTA NAKE BA CHAPTER 9

- - Post a Comment
BA SONTA NAKE BA

CHAPTER 9


CENTRAL HOSPITAL
Yau kwana uku kenan da faruwar wannan al’amari. Gaba daya dangin Marigayi Alhaji Umar Jimeta sun hallara a Central Hospital, hatta Granny ta zo.
Gaba daya asibitin Farouq babu wanda bai san suna cikin babban tashin hankali ba.

Tunda aka kawo Zara asibitin likitoci suke kanta.
Dr Kevin wanda yake heading unit din Neurosurgery na asibitin tare da team dinshi suna iya qoqarin su wurin ganin Zara ta farfado amma inaa, abin ya nemi ya faskara.
Anyi sa’a anyi stopping brain haemorrhage din amma kuma tuni ta shiga Coma.

Farouq dai hauka ne kawai bai yi ba domin kuwa Dr Kevin da team dinshi sun sha fada da masifa.
A koda yaushe yana nan tsaye tare da su yayinda suke aikin su wanda kusan sun kasa yin komai don ceton rayuwar Zara.
Har threatening dinsu yayi akan idan Ya rasa Zara sai ya hukunta su.
Dr Kevin dai har fargaban ba ma Farouq update yake yi domin kuwa kwata kwata baya so ya ji wani negative report.
Abba da Daddy ne suke ta bashi haquri domin kuwa sun kula ma wasu abubuwan ba a cikin hayyacin shi yake yin su ba.

Su Mamy dai babu abinda suke yi banda kuka. Babu wanda ke iya lallashin wani.
Ruqayya ma ta zo don ganin halin da Zara take ciki, ganin cewa she has little chance of surviving ne yasa hankalinta ya dan kwanta wanda har kukan qarya ta dinga yi.

A kullum Farouq yana dakin Zara zaune a gabanta, dukda likitoci sun hana a shiga amma inaa, ko sauraron su baya yi. Haka yake zama yayi ta lallashin ta akan ta tashi amma a banza.

Ranar da Zara ta cika kwana biyar ne ganin babu wani progress Farouq ya hada appointment da wani best neurosurgeon da yake qasar Germany.
Dr Gerd dai wani shahararren likitan qwalwa ne wanda ganin shi kawai aiki ne balle charges dinshi. Amma fa he is extremely good.
Dayake Farouq likita ne wanda ake ji da shi a qasar Germany, booking appointment da Dr Gerd baiyi mishi wahala ba, kuma dama harka ce ta kudi tuni yayi settling komai.

A private Jet din Abba ne aka tafi da Zara Germany yayinda gaba daya dangin kowa ya bi su amma fa banda Ruqayya.

Ko da Dr Gerd ya ga Zara yayi mamaki qwarai yadda tayi surviving din serious blow din.
Nan da nan kuwa ya shiga aikin shi.

Dare da rana su Dr Gerd suna kan Zara wanda cikin kwana biyu suka samu ta zama stable amma fa bata fito daga Coma ba.

Dr Gerd din ya basu assurance cewa she will get better amma fa babu rana.

Wasa wasa dai Zara tana Coma tsawon kwanaki, satuttuka kai har tayi watanni bata farka ba.
STORY CONTINUES BELOW
A cikin wannan watannin Hankulan dangi kaf a tashe yake don har wasu sun fara fidda rai.
Farouq kuwa saboda tashin hankali ya rame domin kuwa kwata kwata baya cin abinci, kai har kwanciya yayi a asibiti saboda damuwa.

Mamy ce takan zaunar da shi tana yi mishi nasiha akan muhimmancin tawakkali a rayuwar musulmi wanda irin nasihohin ne suke sanyaya mishi zuciya har yana samun sauqi.

Dayake su Daddy sun ce kowa ya koma gida, an bar Mamy da Granny tare da Zara.
Sadiq dai lokaci lokaci yake zuwa daga London saboda karatun shi.
Ita ma Hafsat haka, duk bayan sati biyu suna zuwa tare da Mukhtar don duba ta.
Su Anty ma bayan sati biyu suke zuwa daga France. Daddy da Abba kuwa a dalilin aikin su sai sun samu space ne suke zuwa.

Ruqayya dai ta zo sau daya shima ba wai zuwa na tsakani da Allah bane, ta je ne don ta ga halin da Zarar take ciki wanda hakan yayi mata dadi domin kuwa ta kyautata zaton lallai Zara mutuwa zata yi.

***********

A yau Zara ta kusa wata uku kwance, gaba daya ta bi ta rame. Don ma tana samun kula sossai.
Kamar kullum Farouq ne zaune a gefen gadonta inda yake riqe da hannun ta yayinda su Mamy suke zaune a gefe.
Idanuwa ya sa mata wanda bai san lokacin da hawaye suka fara gangarowa daga idanuwan shi ba.

Hannunta ya matse cikin nashi yace “don Allah ki tashi, I cant take this anymore, I can give up everything to take your place Zara. Don Allah ki tashi please I beg you”
Ajiyar zuciya yayi ya cigaba da fadin “you are very important to me, if I lose you I will die”1
Daga nan sai gani nayi ya saki hannun ta ya kifa kan shi a kan gadon yayinda zuciyar shi ta dinga zafi.

Su Mamy dai suna ta sauraron shi kamar kullum yayinda suke tausaya mishi halin da ya shiga a dalilin Zara, fatan su Allah ya ba Zara lafiya.

Kamar daga sama sai ji yayi an shafa kanshi. Da sauri ya dago ya ga Idanuwan Zara a kan shi. yayinda take qoqarin yin Magana amma ta kasa.

Da hanzari cikin murna ya matsa daf da ita yace “Alhamdulillah, thank God you are awake sis”
Nan da nan su Mamy suka miqe cikin murna yayinda suka zagaye gadon Zara suna gode ma Allah.

Murmushi tayi mishi tare da miqa mishi hannunta ya riqe gam. Ta juya ta kalli su Mamy da Granny tana murmushi.

Likitocin da suke monitoring dinta daga Unit dinsu ne suka shigo cikin hanzari suna qoqarin duba jikin Zara yayinda suka ce ma su Mamy su dan basu wuri su duba ta.
Su Mamy dai sun fita yayinda Farouq yake riqe da hannun Zara wanda ma da alama bai ji abinda likitocin suka ce ba.

Dr Gerd ne yace a qyale shi tunda itama Zarar ta qi sakin hannun nashi.

Ko da suka duba Zara komai lafiya lau don haka ne Dr Gerd ya kalle ta yace "what is your name?" Murmushi tayi tace "Fatima Zara Al-Hassan"

STORY CONTINUES BELOW
Yayi murmushi ya nuna Farouq yace "who is this?"

Farouq wanda ya sa mata idanuwa yana addu'ar Allah yasa memory dinta yana nan ne ya ji tace "he is my favorite brother Umar Farouq Al-Hussain"

Ajiyar zuciya Farouq yayi tare da gode ma Allah.

Dr Gerd ya kalli Farouq yace "i think she hasn't lost her memory but i will have to run a final test on her tomorrow to confirm she is fully ok"

Farouq wanda yake kallon fuskar Zara yace "thank you Doctor"

Bayan likitan ya fita ne Farouq wanda yake riqe da hannun Zara yace "hey i missed you alot" murmushi tayi tace "ka rame Ya Farouq"

Yace "duk laifin ki ne ai" murmushi tayi tace "i am sorry"

Anan ne su Mamy suka shigo cikin murna.

**************
Washegari tuni dangi da abokanen arziki sun iso. Kowa Allah Allah yake ya ga Zara.
Ita kuwa Zara ta ji dadin ganin kowa. Hafsat maqale kusa da ita suna ta hira.

Da rana ne Dr Gerd ya shigo dakin Zara tare da nurse dinshi. A lokacin kuwa gaba daya iyalin Marigayi Alhaji Umar jimeta suna cikin dakin.

Kwance take a kan gadonta amma fa riqe da hannun Farouq.

Dr Gerd ne ya matsa kusa da su yana murmushi yace "i see that you two get along well" murmushi kawai suka yi yayinda su Mamy suka yi dariya.

Dr Gerd ya sallami kowa daga dakin Zara amma kamar kullum Farouq ya qi fita.

Wani machine ya sa a kan Zara inda yayi scanning brain dinta.

Bayan ya gama ne ya karbi file din Zara daga hannun Nurse dinshi sannan yayi wasu rubuce rubuce.

Zama yayi a kan kujera ya kalli Zara yace "tell me what happened the day you met with the accident"

(Ghen ghen ghen🙄)

Farouq wanda yake kallon Zara ne ya ga ta dan daure fuska, can kuma sai tayi murmushi ta nuna Farouq tace "he was the last person i saw before going to bed that day and afterwards..." sai ta dan yi shiru sannan tace "i can't remember"

Dr Gerd ya kalli Farouq yace "i think she must have lost that very memory but its okay, she will remember someday"

A bangaren Farouq dai ya gode ma Allah da yasa ta farka sannan memory dinta yana nan. Abinda ya faru wanda ya janyo accident din ne kawai bata tuna ba wanda kuwa bai dame shi ba a halin da ake ciki yanzu.1

(Ni dai ya dame ni.. na so asirin Ruqs ya tonu😡)1

****************
Ruqayya wadda labarin farfadowar Zara ya isa gareta ne yasa naquda ta tashi mata tun kafin cikin ya shiga wata tara.
Aikuwa babu shiri aka yi asibiti da ita. Farouq dai sai ji yayi matar shi ta haihu wanda C-Section akayi mata aka ciro yaron.

A asibitin kuwa kula na musmman Farouq yake ba Zara. Su Abba har mamaki suke yi. A kullum yana kusa da ita suna hira, abinci ma shi yake bata. Zara tana jin dadin yadda yayan nata yake kula da ita sossai.

STORY CONTINUES BELOW
*************
Bayan sati daya da farfadowar Zara ne aka sallame ta.
A lokacin kuwa Jaririn Farouq wanda ya ci suna Bashir (sunan mahaifin Ruqayya) amma ana kiran shi da Junior yayi sati daya shima wanda tunda aka haife shi bai gan shi ba saidai a hoto.
Ruqayya tayi qorafi har ta gaji.

Hankalinta ya kwanta sossai da ta ji ance Zara bata tuna abinda ya faru ranar da tayi accident din ba don haka ne ma bata wani damu ba.
Abba ya shirya ma Zara da Mamy zuwa Umra da Dubai don saboda Zaran ta samu isashen hutu.

Su Farouq kuwa komawa sukayi Nigeria wanda Zara ta so ace tare zasu je da shi amma a dalilin zai je ganin Ruqayya da Junior shiyasa bai bi su ba.

*************

AL-HUSSAIN SUITE BURJ AL ARAB DUBAI
Kwance take a kan cinyar Mamy yayinda ta kira wayar shi. har ta gama ringing bai amsa ba.
Tsaki tayi tace “wallahi Mamy Ya Farouq baya son amsa waya, kullum sai ayi ta kiran shi baya dauka”

Mamy tayi murmushi tace “kin manta yayan naki likita ne? maybe yana theatre”
Zara tayi murmushi tace “nayi missing dinshi Mamy, kin ga fa yace idan ya samu time zai zo kafin mu koma. How I wish zai zo da mun fita yawo”
Mamy tayi dariya tace “sarkin son yawo”
Kafin Zara tayi Magana ne wayar ta tayi ringing. Tana dubawa ta ga sunan shi kuma da alama Video call ne.
Tashi tayi zaune ta kalli Mamy tace “am I okay?” cikin rashin fahimta Mamy tace “ofcourse Princess” sai kawai tayi answering.
“Hello beautiful” abinda ta ji yace kenan. Murmushi tayi tace “Hi Handsome” Mamy da take gefenta ta miqe tare da girgiza kai tana murmushi.
Farouq ne ya dan kalle ta sossai yace “yanzu kika tashi daga bacci hala?” dariya tayi tace “me ka gani Ya Farouq?”
Yace “your hair is a mess as always” ya cigaba da kallon ta sannan yace “you are still in your nightwear” ya zaro idanuwa yace “me nake gani a fuskar ki kamar pimple?”
Cikin ihu Zara ta miqe tace “inna lillahi wa’inna ilaihir’raji’un” wanda yasa Mamy ta fito tana fadin "lafiya?".
Zara ta jefar da wayar hannun ta ba tare da ta kashe ba tace “Mamy na shiga uku, Ya Farouq ya gan ni da pimple” ta ruga zata tafi daki ne Mamy ta kamo ta tace “come here, wasa yake yi miki. your face is absolutely fine”
Farouq wanda yake jin su a wayar ne ya dinga kwasar dariya.

Zara dai sai da Mamy ta ja ta zuwa madubi ta nuna mata fuskarta ne sannan ta amince babu pimple a fuskar ta.

Cikin masifa ta koma ta dauki wayar, ta kula cewa ya ajiye wayar a gefe yayinda ya cigaba da aikin shi.
Turo baki tayi tace “wallahi Ya Farouq ka cuce ni kuma sai na rama, ka dai san that was an expensive joke ko?”
Murmushi yayi yace “Haba Princess din Mamy, I was only kidding fa. Besides ni ban taba ganin ki da pimple ba, please idan ya fito kiyi snapping ki aiko mun”
Runtse idanuwa tayi tace “aaarggghhh”
Ya kashe mata ido daya kamar yadda take yi mishi.
Cikin fushi tace “I hate you” sannan ta kashe wayar.

Text message ya turo mata kamar haka:

“you are beautiful with or without pimple sis, Have a nice day”

Ko da ta ga message din dariya tayi sossai sannan ta tura mishi reply kamar haka:

“thanks big brother, you are the best"

*************

AL- HUSSAIN MANSION
A yau kwanan su zara Uku da dawowa daga Dubai.
Jiya ne Daddy yazo Nigeria wanda har Zara tana mamakin zuwan shi domin kuwa idan har yazo toh lallai akwai wani muhimmin abu da ya kawo shi.

Daddare Daddy da Abba tare da Mamy suna Zaune a falon Abba ne Farouq yayi sallama ya shiga.
Dama shi suke jira domin kuwa tun da rana Abba ya kira shi akan lallai duk abinda yake yi yayi qoqari ya zo bayan sallan Isha’i.
Ganin yadda su duka suka zama serious ne abin ya dan so ya bashi tsoro amma kuma ya matse.

Zara ce ta shigo falon cikin sallama wadda Mamy ta kira a waya. Ko da ta ga Farouq ta dan yi mamaki.
Gefen shi ta zauna cikin rada tace “hey, munyi musu laifi ne?” yana murmushi yace “ni dai banyi ba, saidai qila ke”
Kafin tayi Magana ne suka ji daddy yayi gyaran murya ya kalli Farouq yace “Farouq” yace “na’am Daddy sannan ya kalli Zara yace “Zara” tace “na’am Daddy”
Yace “dalilin da yasa muka kira ku a yau shine muna so mu cika wani buri namu wanda ya dade a zuciyoyin mu, kun sani cewa a matsayin mu na iyayen ku bazamu taba yanke hukuncin da zai cutar da ku ba”
Cikin rashin fahimta suka kalli juna sannan suka mayar da hankalin su kan Daddy.
Daddy ya cigaba da fadin “tun kuna yara muke da burin hada ku aure..” Bai qarasa Maganar shi bane Zara ta miqe dafe da qirji tace “Daddy!!”

Cikin mamaki su duka suka dago kai suna kallonta musamman Farouq wanda ya zama confused.

Abba ne yace “what is it Zara” gani suka yi ta fashe da kuka tace “ni fa bazan auri Ya Farouq ba” gaba daya suka ce “what????”

*************
ai tace “Daddy wallahi ni ba Ya Farouq nake so in aura ba”
Wannan zancen na Zara ya razana su musamman Farouq wanda kalaman Zara suka soki zuciyar shi.

Muryar Abba suka ji yace “waye kike so ki aura toh?”
Cikin bacin rai Daddy ya bude baki zaiyi Magana yayinda Abba ya dakatar da shi.

Tana kuka tace “Abba sunan shi Mahmood Isa Tafida”
Gaba dayan su suka ce “what?” yayinda Daddy yayi tsaki yace “maganar banza”
Mamy ce tace “dan gidan senator?” Abba yace “toh waye Isa Tafida kuwa banda shi”
Muryar Zara suka ji tace “shine Abba”
Cikin fada Daddy yace “shut up, kin kuwa san waye Isa Tafida a Nigeria? Toh wallahi idan kin ga baki auri Farouq ba mutuwa ce ta shiga tsakani idan kuwa musu zakiyi da mu iyayen ki toh ki nemi wani gidan, ba dai nan ba”
Yana qarasa zancen shi yace “tashi ki bani wuri”
Haka Zara ta miqe ta ruga daki tana kuka.

Abba yace “yau na ga ikon Allah, ana zaton wuta a maqera sai aka ganta a masaqa”
(Ai lallai kam🤣)

Mamy tayi dariya tace “lets give her time to digest everything”

Farouq wanda gaba daya hankalin shi yayi nisa wurin tunanin abinda ya faru yanzun nan wanda yayi kamar a mafarki ne ya ji Daddy yace “toh kai me zaka ce? Ko kaima baka so?”
Abba ne yace “ya ma isa? Ai ko suna so ko basu so sai anyi, in ya so su je su kashe kansu”
Mamy dai dariya ta dinga yi.

(Nima da nake labe a falon dariyar nake yi🤣🤣)3

Farouq dai jiki a sanyaye yace “sai da safe” daga nan ya miqe ya fita yayinda suka bi shi da kallo.

Bayan ya fita ne Mamy tace “sai na ga kamar jikin shi yayi sanyi”
Daddy yace “ba dole ba, yarinyar nan tana nema ta wulaqanta shi. banda iskanci irin nata waye ya fi cancanta ta aura ba yayanta ba”
STORY CONTINUES BELOW
Haka dai ya dinga fada yayinda su Abba suka dinga bashi haquri.

A qarshe dai hira suka cigaba yayinda suka tsayar da biki nan da wata biyu wanda sun yi hakan ne saboda lokaci ne da zai kasance hutu wanda kowa yana nan.
(Hehehehe.. ina jin wannan zancen na miqe na dinga taka rawa💃💃)1

**********

Zara kwance a kan gadonta tana ta rusa kuka.
Ji take yi kamar zata mutu. Wani ikon Allah kwata kwata bata so maganar aurenta da Farouq ba, abinda ta sani shine tana bala'in son Farouq amma fa a matsayin yayanta.
Bata taba tunanin cewa su Abba zasu yi tunanin hada su aure ba.
A rayuwarta babu wanda take so ta aura sai Mahmood.
Mamy ce ta qwanqwaso qofar ta shigo.
Ganin Zara tana ta kuka ne yasa ta girgiza kai sannan ta qarasa wurinta ta rungume ta.
Cikin kuka Zara tace “Mamy dagaske ni bana son auren Ya Farouq”
Mamy dai wannan abu ba qaramin mamaki yake bata ba.
Qara matse ta tayi a jikinta yayinda take shafa kanta tace “meyasa bakya son auren shi?”
Zara tace “toh Mamy shima fa ba so yake yi ba, yana da matar shi. ni bana so in auri mai mata kuma ma ni gaskiya Mahmood nake so”
Mamy tace “sssshhh, kar ki sake kiran sunan yaron nan a gidan nan, mahaifin shi ba mutumin arziki bane. Babu wani wanda zai so ya hada zuri’a da senator Isah Tafida”
Zara ta cigaba da kuka yayinda Mamy tace “kiyi haquri ki cire damuwa a ranki, Farouq is going to be a good husband to you. You have transformed him so much that I can see it in his eyes cewa ya damu da ke fiye da yadda kike tunani”
Zara dai shiru tayi bata qara ce ma Mamy komai ba domin kuwa ta kula cewa babu wanda zai fahimce ta.

(Ni kaina ban fahimce ki ba Zara🙄)

Bayan Mamy tayi iyakar qoqarinta wurin lallashin Zara ne ta miqe ta fita.
Zara kuwa kuka ta cigaba da yi kamar wadda aka aiko ma saqon mutuwa.
Gani nayi ta tashi zaune ta janyo wayar ta ta kira Farouq amma har ta gama ringing bai amsa ba, ta kira shi ya fi sau goma amma shiru.
Daga qarshe ne ta tura mishi text message sannan ta koma ta kwanta tana ta tunanin yadda tana ji tana gani za’a raba ta da mai sonta.

*************

A bangaren Farouq kuwa tunda ya fita daga gidan iyayen shi ya shiga mota, zaune yayi yayinda ya kasa tada motar.
Kifa kanshi yayi a steering yayinda qwalwar shi take qara maimaito mishi kalaman Zara.
Jikin shi har rawa yake yi saboda maganganun nata sun daki qwalwar shi fiye da tunanin duk wani dan Adam.

Kusan minti talatin yayi zaune a cikin motar yana ta tunane tunanen da shi kanshi bai gane kansu ba.
Daya daga cikin securities din gidan Abba ne ya matso kusa da motar ya qwanqwasa gilas din shi wanda yasa Farouq ya zabura.
STORY CONTINUES BELOW
Ajiyar zuciya yayi ya sauke gilas din yayinda ya kalli security din.

Idanuwan shi sunyi Ja yayinda fuskar shi ta nuna yana cikin mugun tashin hankali.

Security din cikin tsoro da fargaba yace “oga daman na ga ka shiga mota ka dade ne baka tada ba shine na zo in bincika ko…”
Farouq wanda bai qarasa jin bayanin security din ba ya ja gilas dinshi ya tada motar ya bar gidan.

Faruq dai a halin da yake ciki ba zai iya zuwa gida ba domin kuwa kwata kwata baya son hayaniyar Ruqayya don haka ne ya wuce dayan gidan shi wanda Mukhtar yake kira da Villa.

FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION (VILLA)
Farouq kwance a kan kujerar Falon shi yayinda kan shi yake azabar ciwo.
Tambayoyi kala kala yake yi ma kanshi:
“me yasa ka damu saboda yarinyar tace bata so ta aure ka?

Me yasa zuciyar ka take tafasa a dalilin tace wani take so ta aura ba kai ba?

Toh kai kana so ka aureta ne da ka damu?

Why do you even care Farouq?”
Ringing din da wayar shi take ta yi ne yasa ya fiddo daga aljihun shi ya duba. Sunan Zara ya gani, haka ya cigaba da kallon wayar har ta tsinke.
A kan idanuwan shi tayi ta kira amma ya kasa amsawa.

Text message din da ta aiko mishi ya karanta kamar haka:

“Ya Farouq please don’t let them do this to us, na san cewa kamar yadda bana so kaima haka baka so. Ka taimaka mun su aura mun Mahmood. I know you will help me, thank you big brother”

Farouq ya karanta wannan message din ya fi sau ashirin.
A yanzu ma qwalwar shi ta kasa tunani.
Ajiyar zuciya kawai yake yi.

**************
A daren yau dai bacci barawo shine ya sace Zara da Farouq.
Ruqayya wadda ta kira wayar shi har ta gaji ta haqura domin kuwa tayi tunanin qila surgery yake da shi tunda dai ya saba kwana a asibiti.

************

AL-HUSSAIN MANSION
Washegari tun da safe Zara tayi wanka ta shirya ta fito don zuwa gidan Hafsat.
Da ganin ta kuwa kasan a rude take.
Zaune ta gan su a dinning suna breakfast.
Cikin girmamawa ta gaishe su kamar kullum.
Abba da Mamy sun amsa cikin fara’a yayinda Daddy ya cigaba da cin abincin shi ba tare da ya kalle ta ba.
Hankalin ta a tashe ta matsa kusa da shi ta sake gaishe shi.
Ganin bai amsa bane yasa Abba yace “haba dan uwa, ayi mata afuwa” ba tare da Daddy ya kalle ta ba ya amsa.
STORY CONTINUES BELOW
Kallon Mamy tayi tace “Mamy zan je gidan Hafsat”
Mamy ta kalli agogo tace “haba Princess, da sassafen nan, ki duba fa ki gani qarfe takwas da rabi na safe. Kiyi haquri mana ko zuwa qarfe goma”

Abba ne ya ja kujerar gefen shi yace “zo ki zauna kusa da ni kiyi breakfast, you shouldn’t go out on an empty stomach”
Zara dai babu shiri ta zauna kusa da Abba.
MUKHTAR ABUBAKAR MANSION
Zara ce ta shigo gidan Hafsat hankali a tashe.
Tana ganin qawarta ta fashe da kuka tare da rungume ta.
Hafsat cikin mamaki tace “babes me ya faru kuma? Ya Farouq ne hala”
Cikin kuka tace “ni wallahi bana so in aure shi”
Cikin mamaki Hafsat tace “ban gane ba, what are you saying bestie? Talk to me”
Anan ne Zara ta ba Hafsat labarin abinda ya faru.

Wani irin ihu Hafsat tayi tace "Yess.. Alhamdulillah. I am sooo happy... this is a dream come true, Finally”

Gani nayi tana waige waige tana neman wayar ta cikin murna da farin ciki tace “bari in kira sweetlove in bashi breaking news because…”
Zara wadda ta cika da mamakin qawarta ta riqe hannunta tace “Bestie, like baki saurari labarin da kyau ba, bana son in auri Ya Farouq”
Hafsat wadda bata damu da zancen Zara ba tace “we both know you are lying, yaushe aka sa bikin? Allah yasa ba zai dauki lokaci ba”
(Da kyau Hafsat🤣)

Zara dai ganin qawar ta bata saurare ta bane ta miqe cikin fushi tace “I hate you babes”
Hafsat tace “yeah I know matar Ya Farouq, kishiyar hajiya Ruqayya”

Zara dai ta wuce ta bar gidan yayinda Hafsat ta kira Mukhtar a waya ta bashi labarin wanda yayi matuqar farin ciki.

Mukhtar yayi mamaki qwarai da abokin nashi bai fada mishi ba.
Kiran wayar Farouq yayi don ya tsokane shi.

FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION (VILLA)
Kwance yake a bisa kujerar falon shi. tunda yayi sallar asuba ya koma ya kwanta.
Kiran Mukhtar ne ya shigo wayar shi wanda ya duba, da farko ya so ya qi amsawa amma daga baya sai yayi tunanin he needs him now more than ever, yana buqatar yayi Magana da wani ko zai ji sanyi a zuciyar shi don haka ne ya amsa.+
Mukhtar din ne yace “Haba angon Fatima Zara, shine bazaka gaya mun abin alkhairin da…”
Farouq ne ya katse shi inda yace “abokina where are you, please come I am at my other house”
Yanayin yadda Mukhtar ya ji muryar Farouq ya san akwai wani abu don haka ne yace “I am on my way”

***********

Farouq yana nan kwance a kan kujera ne Mukhtar ya shiga gidan.

Yayi nisa a tunani wanda har abokin nashi ya shigo bai sani ba.
Dafa shi yayi sannan yace “Hey”

Farouq ne ya tashi zaune tare da sakin ajiyar zuciya.
Mukhtar ya zauna gefen shi yace “I am listening bro, what happened?”

Farouq ya dafe kanshi sannan ya ba abokin nashi labarin abinda ya faru.

Ajiyar zuciya yayi yace “wallahi abokina ban taba tunanin zan ji abinda na ji ba a lokacin da tace bata son ta aure ni. I just… I cant believe this”
Mukhtar wanda yake qoqarin matse dariya ne yace “Toh abokina as far as I can remember ka sha fadin cewa ba sonta kake ba, why are you bothered about this”
Runtse idanuwa yayi yace “because I LOVE HER DAMN IT!!!!!”2

(Ni kuwa nace whaaaaat???🙄🙄)

************
Mukhtar wanda yayi mamakin abinda ya ji daga bakin abokin shi ne ya dan yi pinching hannun shi don tabbatar da cewa ba mafarki yake ba.+

Ji yayi Farouq ya cigaba da fadin “I really love her abokina, I don’t know how it happened”
Ajiyar zuciya yayi sannan yace “she deceived me, she tricked my heart into falling for her”
Ya shafa kanshi sannan yace “na sani cewa nayi denying dinta at first, ban san cewa na kamu da sonta ba sai lokacin da ta fadi cewa bata so ta aure ni. I felt like dying at that moment”
Mukhtar wanda ya cika fam da murna ya dafa abokin shi yace “Hey relax abokina, I am so happy da kayi admitting cewa kana son Zara, ka manta da abinda ta fada tunda dai we both know cewa she is lying, she might just be confused for now but I am sure she will come around”
Farouq ne ya ja numfashi yayinda ya dauko wayar shi ya bude text message din da ta turo mishi ya miqa ma abokin shi wayar.
Ko da Mukhtar ya karanta saqon yayi mamaki matuqa domin kuwa kalaman da tayi sun nuna dagaske take.

Ji yayi Farouq yace “She is trying to blackmail me emotionally abokina, ya zanyi?”
Mukhtar yayi murmushi yace “haba abokina manta da wannan, yanzu dai Idan ma dagaske ba son ka take yi ba kamar yadda ta fada I think its time you make her fall for you. Abu ne mai sauqi, kamar yadda kace tayi tricking dinka kaima trick her, trust me ko nisa baza’a yi ba zaka ga ta dawo hanya”
Farouq ya kalli abokin shi yace “toh abokina yanzu ta ina zan fara?”
Mukhtar yana dariya yace “ai farkon abinda yakamata kayi shine ka sauke girman kan nan naka tunda dai yanzu Zara ta zama sarauniya sai yadda tayi da kai”
(Hahahaha... Muky ma ya dana🤣)

Haka dai Mukhtar ya cigaba da ba abokin shi shawarwari tare da qarfafa mishi qwarin gwiwa akan Zara wanda babu laifi hankalin shi ya kwanta sossai.

Mukhtar kuwa yayi ma kanshi alqawarin bazai fada ma Hafsat wannan zancen ba domin kuwa ya sani sarai idan ya fada mata sai ta fada ma qawarta. Burin shi shine Farouq ya fada ma Zara yana sonta da kanshi.
***********

A yau kwana biyu kenan da aka yi zancen auren Zara da Farouq.
Tun ranar da aka yi maganar Farouq bai sake zuwa gidan ba, haka kuma bai sake ganin Zara ba.
Kullum sai ta kira shi a waya don ta ji matakin da zai dauka akan al’amarin amma baya amsawa.
Ta so ta je asibiti ta same shi amma wani ikon Allah ta kasa saboda kunyan ganin shi ma take yi.

(Lol🤣)

A bangaren Farouq kuwa rashin ganin Zara kwana biyu yana bala’in damun shi.
Bai taba sanin cewa akwai lokacin da zaiyi missing dinta kamar haka ba.
STORY CONTINUES BELOW
A yanzu hotunan ta da take aiko mishi su ne abin kallon shi a koda yaushe.
Tabbas ba qaramin kamu Zara tayi ma zuciyar shi ba.

(Da kyau Zara😃)

Hatta Ruqayya ta fahimci cewa Farouq yana cikin wani hali, yadda yake yawan wasa da Junior ma ya rage sannan ta kula yana yawan zama lost a cikin tunani.
Ko da ta tambaye shi sai ya gwada mata babu komai.

Tunanin shi a koda yaushe shine: Shin idan ya bayyana mata abinda ke zuciyar shi sannan tayi turning dinshi down ya zai yi??? gashi baya son raini.

(Hehehehe... su Farouq kenan🤣)

AL-HUSSAIN MANSION
A yau tun da safe Zara ta shirya akwatin ta don tafiya Adamawa wurin Granny dinta.
Tayi haka ne don ta samu space tayi clearing din qwalwar ta.

Su Mamy dai basu ce mata komai ba domin kuwa ranar aure ne an riga an sa, duk inda zata je dole dai zata dawo idan lokaci yayi.

Bayan Zara ta tafi ne Farouq ya shigo gidan. A yau kam ya kasa jure rashin ganin ta shiyasa ya zo.
Mamy ya tarar a sashen ta tana kallon tashar Zee Tv.
Ko da yayi sallama ya shiga Mamy tayi mamakin ganin yanayin shi looking so dull.
Cikin mamaki tace “kayi ciwo ne ban sani ba shine kullum muna waya baka fada mun ba?”
Girgiza kai yayi yace “I am fine Mamy”
Mamy tayi murmushi tace “ya shirye shirye? Na ga dukan ku kun yi shiru kuma ga lokaci yana ta matsowa”

Farouq ya dan sosa kai yace “Tana ina?”
Mamy tace “bata fada maka zata je Adamawa bane? Ai yau da safe ta tafi”
Cikin rudani yace “what?”
Mamaki Mamy tayi ganin yadda hankalin shi ya tashi.
Wayancewa yayi tare da fadin “Uhm... yaushe zata dawo Mamy?”
Mamy tace “wallahi bata fadi mun ba” daga nan bai qara yin Magana ba. Mamy a ranta tace “Allah sarki yarona ya fada tarkon so”.

(Aikuwa kam😃)

LATE ALH UMAR JIMETA MANSION ADAMAWA STATE
Granny zaune a falon ta inda daya daga cikin masu aikinta take yi mata tausa a qafa.
Zara ta fito daga dakinta ta zauna gefen ta tace “gaskiya granny kina jin dadin ki, har wani tausa ake yi miki”
Granny ta harare ta tace “toh sarkin sa ido” Zara ta turo baki tare da daukar remote tana canza channel.

Granny ce tace “toh wai ke ya aka yi kika taho mun nan kika baro mijin namu a can?”
Zara ta bata rai tace “ni wallahi na bar miki shi, bana so”
Granny tayi dariya tace “tafi can maqaryaciya, kina so kina kaiwa kasuwa. Na sani sarai idan ya auro mana ke mun shiga uku ni da Ruqayya”
STORY CONTINUES BELOW
Zara ta fashe da dariya tace “toh tunda kema baki so ki sa baki su Daddy su manta da zancen”
Granny tayi dariya tace “wa ya gaya miki bana so, ai na fi kowa murnar wannan abu”
Zara ta miqe tana turo baki tace “bari ma in fita in bar miki gidan ki”

Granny tana dariya tace “kin kira mijin naki kin fada mishi zaki fita ko?”
Zara dai bata tanka ta ba ta wuce abinta. Ta riga ta kula kowa ma ya mayar da abin kamar wasa.

*************

Da yamma Granny tana kicin dinta tana qoqarin hada miyan kuka ne ta ji an rufe mata ido.
Hannuwan shi ta taba sannan ta dan yi murmushi.
Cikin masifa tace “na ga alama dai wannan mijin nawa kaine zaka yi silar bari na duniyan nan”
Farouq wanda ya fashe da dariya yace “haba Mi Lady, bala’in sonki nake”
Granny ta ture shi tare da fadin “ni zaka yi ma dadin baki? Yaushe rabon ka da zuwa Adamawa? Wato yau saboda..”
Hugging dinta yayi yace “I am sorry Mi lady, kin san dai ke ce Number 1 dina”
Murmushi tayi tace “ya hanya, ya ka baro su Mamy? How is junior?”
Yace “duk suna nan lafiya lau Mi Lady”

Yayi mata kiss a kumatu yace “Har yanzu da kanki kike dafa abinci? Chefs dinki fa? Bana so kina stressing kanki, your wellbeing is very important”
Granny tayi murmushi tace “kasan na fi gane kan irin nawa kalolin abincin, ba kamar ku ba da kuka biye ma yahudawa”
Zama yayi kan daya daga cikin kujerun kicin island din dake kicin din yace “Wallahi Mi Lady nima na fi son irin naki”

Granny ce tace “ai ka kyauta ma kanka” shafa kanshi yayi yace “Mi Lady ina Zara ne ban gan ta ba?”
Murmushi tayi tace “dama dai na san ita ka biyo, wannan ba zuwana bane. Ta tafi gidan Anties dinta tun dazu”
Ji tayi yace “Allah yasa dai ba kwana zata yi ba”
Granny tace “tab, da alama dai ni da Ruqayya mun shiga uku”
Fashewa yayi da dariya ya miqe yace “bari in je masallaci an kusa kiran sallah”
Zara bata dawo gidan ba sai gab da Magrib, A lokacin Farouq ya tafi masallaci.
Ko da ta shiga Granny bata fada mata cewa ya zo ba.
Dakinta ta wuce tayi wanka sannan tayi sallah. Zama tayi kan sallayar ta har aka kira sallan isha’I sannan ta yi.
Ko da Granny ta aiko a kirata ta sauko dinner sai cewa tayi ta qoshi.

Kwance take bisa gadon ta cikin bargo. Wayar ta ce tayi Ringing, Ganin sunan Mahmood ne yasa tayi murmushi ta amsa inda suka taba hira.
A yanzu kuwa qara ji take yi da mahmood din saboda bala’in so da yake nuna mata.

Bayan tayi sallama da shi ne ta kira qawarta Hafsat wadda kwana biyu har fargaban yin Magana take yi da ita a dalilin tsokanar ta da take yi akan Farouq.

STORY CONTINUES BELOW
Aikuwa Hafsat tana amsa wayar tace “haba amarya, meye duniya kin share ni. Ya Adamawar?”
Zara tayi murmushi tace “duk ke kika ja bestie” Hafsat tace me nayi miki toh? Ba ni na ci zomon ba”
Kafin ta yi Magana ne ta ji an qwanqwaso qofar ta. kallon qofar tayi don ganin waye.

Farouq ne ya shigo dakin wanda har sai da ta zabura. Da sauri ta tura kanta cikin bargon cikin mamaki tace “Ya farouq!!”
Hafsat cikin rashin fahimta tace “kina missing dinshi ne?” Zara dai kashe wayar tayi tare da runtse idanuwan ta.
Zara dai tayi missing din Farouq sossai amma kuma kunya ta hana ta kallon shi, a ranta tace “mutum kamar aljani, yaushe ya zo? Meyasa granny bata fada mun ba?”

Gani nayi ya yaye bargon da ta rufa da shi wanda kuma na ga yayi saurin mayarwa ya rufe ta amma banda fuskar ta.
Yanayin kayan da yake jikinta ne yasa yayi hakan domin kuwa Zara sanye take da wata rigar bacci mai hannun shimi wadda ko gwiwarta bata kai ba, sa’a daya ma rigar ba transparent bace.

Har yanzu idanuwan ta rufe suke yayinda ya samu damar qare ma fuskar ta kallo. A ranshi ne yace “how I missed seeing her”

Ji yayi tace “Ya Farouq yaushe ka zo?”
Girgiza kai yayi yace “can we talk?”
Jin ya fadi haka ne yasa ta tashi zaune tace “ina ta kiran ka a waya baka dauka, you don’t reply my messages”
Ya ja stool din dressing mirror din dakin ya zauna tare da fadin “that’s why I am here”
Da sauri ta sauko daga kan gadon ta tsugunna a gaban shi tace “don Allah Ya Farouq kace ma su Daddy baka so”
Cikin mamaki yace “ni nace miki bana so?”
(Hahahaha🤣)

A firgice ta kalle shi tace “Ya Farouq kana so ne?”
Shi kam yanayin kayan jikin Zara ne baya so.

Ajiyar zuciya yayi yace “cover up please”
Kallon jikinta tayi sannan ta kalle shi tace “toh wai Ya Farouq meye…”
Kallon da yayi mata ne yasa ta miqe don dauko hijab dinta.
Farouq ya qura mata ido tare da dafa kanshi a ran shi yace “Ya salaam, I have to find a way, i just cant let her go”

Zara ta dawo ta zauna kan gadon sanye cikin hijabin ta.
Farouq ne yace “with regards to your message gaskiya babu abinda zan iya yi”
Hankalin Zara a tashe tace “toh ya zamuyi Ya Farouq? Ka ga ni fa nasan baka so ka aure ni kuma nima fa dama bana so in auri mai mata..”
Ji tayi yace “are you the jealous type?”
Turo baki tayi tace “ni fa bana son sharing..” da sauri ta sa hannu ta rufe bakinta sannan kuma tace “uhm.. ina nufin ai dama Anty Ruqy ma bata so na”.
Murmushi yayi yace “well do you have a plan in mind?”
Tace “I was hoping you do Ya Farouq, don Allah ka taimaka mun”
Farouq dai shiru yayi yana kallonta sannan yace “Ina da plan, it might sound crazy but..”
Cikin qaguwa da son jin plan din tace “Alhamdulillah, please tell me”.
(Nima kuwa nan da nan na sa kunne don in ji plan din🤣)

Yace “for now zamu bari ayi auren” gani nayi Zara ta bata rai.

Ya cigaba da fadin “bayan wani dan lokaci zan sake ki sai ki auri…"
Ya dan bata rai yace “ya ma sunan yaron nan?”
Murmushi tayi tace “Mahmood” yace “well okay”
Ji yayi tace “toh Ya Farouq for how long zamu zauna kafin mu rabu?”

Yace “just one month or even less” cikin mamaki tace “wata daya Ya Farouq?” girgiza mata kai yayi alamar eh.
Gani nayi tayi tsalle sannan tace “yessss, amma na ji dadi Ya Farouq, you are the best”
Ya girgiza kai yace “yeah yeah I know”

Shiru tayi kamar tana tunani sai kuma ta matsa kusa da shi tace “toh wane reason zaka basu akan rabuwar?”
Yace “leave that to me, is it a Deal?”
Murmushi tayi tace “it’s the only possible way outta this Ya Farouq”
Yace “one thing though” tace “what?” yace “this will remain our top secret, idan na ji a bakin wani you will remain stuck with me all your life”

(Riqe wuta Farouq🤣)

Zaro idanuwa tayi tace “insha Allah Ya Farouq babu wanda zan fada ma plan din mu”
Dariya ma ta bashi har a ranshi yana fadin “unbelievable”

*************

Farouq dai ko da ya bar dakin mamakin Zara kawai yake yi.
Ya tabbatar lallai ba sonshi take ba kamar yadda dai ta fada.
Yayi alqawarin sai ya sa ta so shi cikin wata daya da yin auren su domin kuwa ko da wasa ba zai taba bari ta bar gidan shi ba bayan ya aure ta.

***************
Lallai Zara ta shigo hannu...🤣🤣

Post a Comment for "BA SONTA NAKE BA CHAPTER 9"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...