BA SONTA NAKE BA CHAPTER 7 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BA SONTA NAKE BA CHAPTER 7

BA SONTA NAKE BA CHAPTER 7

- - Post a Comment
BA SONTA NAKE BA CHAPTER 7 G


GIDAN BOKA CIKA AIKI Zaune suke gaban boka cika aiki inda yake ta dube duben shi tare da kiran sunayen aljanun shi don nema ma Ruqayya mafita.+ Su Ruqayya dai basu ankara ba sai ganin shi suka yi ya girgiza sossai sannan a tsorace yace “toh shikenan” Hajjaju ce tace “ya aka yi boka cika aiki” a firgice ya kalle su yace “a gaskiya gurmusuru dakanshi yace wannan aikin ya fi qarfin mu don haka bazai..” Kafin ya qarasa Ruqayya tana kuka tace “ka taimaka mun, wallahi yarinyar matsala ce a rayuwa ta” Boka cika aiki yace “kiyi haquri bazai yiwu ba domin kuwa ita wannan yarinyar da kike Magana akwai tsaro akanta, idan muka sa qarfi a al’amarin ta gaba dayan mu bazamu rayu ba” Cikin fushi Ruqayya ta miqe tace “Hajjaju zo mu je, kawai mun bata lokacin mu a banza” Hajjaju ta miqe tace “toh boka cika aiki mun gode” ************** A kan hanyar su ta komawa gida Ruqayya sai kuka take yi yayinda Hajjaju tace “kiyi haquri kawai ki koma kiyi ta addu’ar Allah ya dauki ranta ki huta” Ruqayya cikin kuka tace “ai ba sai nayi addu’a ba Mamy, da kaina ma zan kashe shegiya in huta” Mamy ce ta zaro idanuwa tace “kul, kar ki manta Farouq likita ne ba kuma qaramin likita ba sannan idan kika kashe ta a gidan ki all fingers will point at you, so take it easy” Ruqayya dai ji take yi kamar zata mutu don baqin ciki. Bayan sun shigo gari ne ta sauke Hajjaju a gida ta wuce gidansu qawarta Aliya. Aliya dai ko da Ruqayya ta bata labarin abinda boka cika aiki yace tayi mamaki matuqa. Haquri ta ba qawarta tare da bata shawarar ta bi komai ahankali sannan ta zura ido ta ga iya gudun ruwan su sannan ta san abinyi. AL-HUSSAIN MANSION Zara tana kwance a kan gadon dakinta yayinda Asabe da Larai suke hada mata kayan ta. Tun jiya da su Abba suka yi zancen tafiyar su jikinta gaba daya yayi sanyi. Wayarta ta janyo ta kira shi amma bai amsa ba, A kira na uku ne ya amsa. Jin tayi shiru ne yace “what is it?” ajiyar zuciya tayi tace “Ya Farouq ka tabbata Anty Ruqy zata amince da zuwana gidanta?” Farouq dai ya gane cewa Zara a firgice take, bai san lokacin da ya fashe da dariya ba yace “gidan waye zaki zo?” tace “gidan ka” yayi murmushi yace “I got your back, relax” Murmushi ta yi sannan tace “okay big brother” Yace “dazu Abba ya kira ni wai around 5 o'clock jirgin su zai tashi so zanzo mu raka su airport, ko bazaki je ba?” tace “zan je Ya Farouq” yace “toh I gotta go bye” sannan ya kashe wayar shi. CENTRAL HOSPITAL Yana gama waya da Zara ne ya dago kai ya ga abokin shi a tsaye bakin qofa yana kallon shi yana murmushi. Cikin mamaki Farouq yace “what the hell Muky, ya zaka shigo ofis dina babu sallama?” STORY CONTINUES BELOW Mukhtar ya qaraso yayinda yace “haba abokina, yanzu duk sallamar da nayi baka ji ba? Don’t tell me har kun fara soyayya ne? ka ga da ka sani ma da aura maka ita kawai aka yi sai ka ajiye ta a Villa instead of..” Daga mishi hannu yayi yace “be careful, na kusa disowning dinka” Mukhtar ya zauna yana murmushi yace “afuwan, so tell me, ya ake ciki ne?” Farouq ya shafa kanshi sannan yace “she is scared abokina, gani take yi Ruqayya bata sonta, I just don’t know why” Mukhtar yayi murmushi yace “you are the obvious reason why abokina, ni dai fata na Allah ya baku zaman lafiya” AIRPORT Securities ne suka ta zuba akwatunan su Abba a cikin Private jet dinshi yayinda suke tsaye tare da su Farouq. Zara ce maqale a jikin Mamy tana ta kuka yayinda Mamy take ta lallashin ta. Bayan an gama zuba kayan su ne suka yi sallama da yaran nasu. Ganin Zara ta qi sakin Mamy ne yasa Farouq ya matsa ya janye ta. haka ta dinga qoqarin qwacewa yayinda su Mamy suka shiga jirgi suna daga ma yaran nasu hannu. Suna nan tsaye jirgin su Mamy ya tashi. A lokacin kuwa mutane ne suke ta kallon Zara wadda Farouq yake ta qoqarin kwantar ma da hankali. Magana yake yi mata amma gaba daya ko sauraron shi bata yi, janyo ta yayi ya bata side hug yayinda yake shafa bayanta kamar dai yada ake lallashin yara. Ahankali Zara ta fara dawowa hayyacin ta inda ta koma ajiyar zuciya. Ganin ta natsu ne yasa ya sake ta sannan ya harare ta yace “ke fa drama queen ce, meye haka kin sa ana ta kallon mu?” Fuskar shi take kallo yayinda take ta ajiyar zuciya tace “Ya farouq I am going to miss them especially Mamy” Tsaki yayi yace “duka ba wata daya zasu yi ba?, common wuce mu tafi before I slap you” Haka ta wuce suka tafi gida. FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION Tunda suka shigo gidan hankalin Zara ya qara tashi. A yanzu kuwa jikinta har rawa yake yi saboda tsoro. A lokacin da suka iso gidan Ruqayya bata dawo ba don haka ne ko da suka shiga Farouq ya kai Zara dakinta wanda anan ta kwana wancan karon da ta je gidan. Dakin Zara babban daki ne wanda babu abinda babu a ciki. Kallon ta yayi yace “dakin yayi miki ko in canza miki wani?” Waigawa tayi ta kalli ko ina sannan tace “Yayi Ya Farouq, thank you” Wucewa yayi ya fita daga dakin yayinda masu aiki suka dinga shigowa da kayan ta. tuni sun jera mata su a closet din dakin. Zara dai tunda ta samu gado ta kwanta sai bacci domin kuwa har wani ciwon kai ya taso mata. Bata tashi daga bacci ba sai gab da magrib, ko da ta farka kanta ne yayi mugun nauyi a dalilin azabar ciwo da yake yi mata. A daddafe tayi shirin wanka ta shiga bathroom. Ko da ta fito jiki a sanyaye ta shirya cikin wandon sweatpant na mata da wata qaramar T-shirt sannan ta sanya hijabinta dogo tayi sallan Magrib. Ko da ta idar anan bisa sallayar ta kwanta. Bayan sallan Isha’I Farouq ya dawo daga masallaci ya nufi dakin Ruqayya, a lokacin ta idar da sallah kenan tana zaune a kan gadonta yayinda take duba wayar ta. Ko da ya shigo dakin sai tayi kamar bata ji shigowar shi ba. wurinta ya nufa ya zauna gefen ta tare da shafa cikin ta yace “how is my baby and its mom doing?”1 STORY CONTINUES BELOW Ruqayya ta kalli fuskar shi sai kawai ta fashe da kuka. Cikin damuwa ya janyo ta ya rungume ta yana shafa bayanta yace “what is wrong? Baki da lafiya ne?” Cikin kuka tace “Honey I am just scared of losing you” cikin mamaki yace “ssshhhh, you are not going to lose me. Dont you ever say that again. Oya tashi mu je muyi dinner” Ya shafa cikin ta yace “kin san bana so kina starving little Ruqy” murmushi tayi tace “its going to be Little Ruku” yayi dariya yace "ooohh, okay" tare da miqar da ita suka fita don zuwa dinning. Sun zauna bisa dinning din ne suna cin abinci Farouq ya dauki wayar shi yayi typing message ya tura ma Zara. Shiru bai ga reply ba, haka ya sake tura mata wani nan ma shiru. Ruqayya wadda ta kula yana ta duba wayar shi ne ta kalle shi tace “Honey wai ba Zara tana gidan nan ba? ya na ji ta shiru, ko bata cin abinci dadaddare ne?” Kamar dama jira yake sai yace “oho, lets finish up and check on her” Ruqayya a ranta tace “shegiya munafuka kawai”. Bayan sun kammala cin abinci ne suka tashi don dubo Zara. Ruqayya tana maqale a jikin shi ya qwanqwasa qofar dakin amma shiru, da suka shiga ne suka hango ta kwance a kan daddumar sallan ta, ta ninke jikinta a cikin hijabin. Hankalin Farouq a tashe ya qarasa wurin ta ya tsugunna a gaban ta yayinda Ruqayya ta saki baki tana kallon ikon Allah. Goshin ta ya dafa ya ji zafi rau. Da sauri ya girgiza ta yana fadin “Hey, wake up” a galabaice ta bude idanuwan ta tana kallon shi. Tambayar ta yayi “baki da lafiya meyasa baki fada mun ba?” tashi tayi zaune a gajiye tace “Ya Farouq kaina ne yake ciwo, ban ma san nayi bacci anan ba” Ajiyar zuciya yayi tare da shafa kanshi yace “tashi ki koma bisa gado bari in samo miki magani ki sha” Zara tana yunqurin tashi ne jiri ya dan debe ta sai kawai ta fadi a jikin Farouq. Hakan kuwa ba qaramin qona ma Ruqayya rai yayi ba. Riqe ta yayi ya kaita wurin gadon ta sannan ta kwanta ya juya ya fita. Zara wadda take dafe da kanta bata ma san Ruqayya tana dakin ba sai jin muryar ta tayi tana fadin “toh munafuka, dama attention kike nema ko?, toh kuwa zanyi maganin ki a cikin gidan nan idan baki kiyaye ni ba” Zara dai jikinta yana rawa ta juya ma Ruqayya baya ba tare da tace mata komai ba. Farouq ne ya shigo riqe da magani hade da robar Yoghurt ya zauna gefen gadon yace “tashi ki sha magani” Girgiza kai tayi alamar a’a. juyawa yayi ya kalli Ruqayya wadda itama shi take kallo cikin qunar rai sannan yace “idan baki tashi ba sai na mare ki” da sauri ta tashi zaune tana ta ajiyar zuciya. Ruqayya dai saboda bacin rai ma juyawa tayi ta fice daga dakin domin kuwa ta tabbatar idan bata fita ba sai zuciyarta ta buga saboda baqin ciki da takaici. Yoghurt din ya bude ya miqa mata ta karba ta fara sha sannan ya bata magani ta sha. Bayan ta shanye ne ya miqe tare da fadin “ki ajiye wayar ki kusa da ke, if you need anything just call me” ya juya ya fita. Zara ta koma ta kwanta tana tunanin irin zaman da zata yi da Ruqayya, wata zuciya ce tace “ki tashi tsaye ki ci mata mutunci kamar yadda kema take nema tayi miki” yayinda dayar zuciyar tace “toh idan kuma garin yin hakan Ya Farouq ya ji haushin ki fa? Can you bear that??” tsaki tayi ta juya ta cigaba da tunani kala kala. STORY CONTINUES BELOW Wani ikon Allah cikin awa daya kan nata ya warware har waya tayi da Mahmood wanda suka dade suna hira sannan suka yi sallama. Ta kira wayar hafsat ma amma bai shiga ba. Bayan tayi sallan Isha’I ne ta haye gadonta don yin bacci. Wayar ta ce tayi qara alamar an turo mata text message, ko da ta duba sunan Farouq ta gani. Tana murmushi ta bude saqon kamar haka: “hey i am worried, hope ciwon kan yayi subsiding?” Gani nayi tayi murmushi ta aika mishi reply kamar haka: “ya daina ciwo big brother, thank you so much. You are the best”. Shima murmushi yayi Ya turo mata: “say something I don’t know😜” (tare da fuskar gwalo). Ko da ta gani fashewa tayi da dariya. ************* Wuraren qarfe takwas na safe ne Zara ta fito sanye da wani material wanda ya bi jikinta daga qugunta kuma ya bude har qasa. Tayi kyau sossai. Tana riqe da gyalen ta da jakar ta a hannu ta nufi dinning, Apple ta dauka tana ci yayinda daya daga cikin masu aikin gidan ta fito ta duqa har qasa tace “Ina kwana Anty” Zara tace “lafiya lau, tashi don Allah, ba sai kin duqa ba, Ya Farouq ya fita ne?” tace “A’a bai fita ba, yana Gym” Zara tace “kai ni Gym din” Mai aikin ta shiga gaba yayinda Zara take biye da ita. Bayan sun iso ne ta nuna mata sannan ta koma. Ahankali Zara ta tura qofar ta shiga. Tsayawa tayi cak yayinda take qare ma Gym din Farouq kallo, banda don na’urorin motsa jiki da ke wurin zaka rantse ba gym bane. Girgiza kai tayi a ranta tace “Ya Farouq kenan, komai nashi has a wow factor” Hango shi tayi riqe da wani qarfe yana working out. Sweatpant ne kadai a jikinshi. Zara dai idanuwan ta ne suka kai kan abs dinshi yayinda ta qura ma six packs dinshi ido. A duniya six pack abs yana bala'in birge ta. Bata taba sanin cewa Farouq yana da shi ba. Bata san yawan lokacin da ta bata a wurin tana kallon shi ba sai jin muryar shi tayi a kusa da ita yana fadin “if you are done staring at me come in” Da sauri Zara ta dawo da hankalinta wurin shi yayinda ta gan shi tsaye yana shan ruwa, sanye yake da wata polo T-shirt wanda bata san lokacin da ya sa ba. A sanyaye ta qarasa shiga Gym din tace “Ya Farouq I wasn’t staring at you, kawai ina kallon Gym din ne” Murmushi yayi yace “okay, me kike yi anan?” Tana biye da shi tace “kai nake nema, zan je school ne kuma kasan banzo da mota ba” Ya ajiye goran ruwan da ke hannun shi ya dauki tawul yana goge fuskar shi yace “mu je in baki key”. Sun kusa fita daga Gym din ne ya juyo ya kalle ta yace “ki tabbatar kin sa gyalen nan a kanki don na san halinki” murmushi tayi tace “zan sa Ya Farouq” Tare suka fito daga gym din inda Yace "Mamy ta kira ni dazu, she said i should extend her regards to you" Zara tayi murmushi tace "Allah sarki Mamy na, I miss her soo much". Wata drawer ya bude yace “oya dauki daya ki tafi” murmushi tayi ta fara dubawa tana fadin “yauwa Ya Farouq dama ina so in hau sabuwar BMW dinnan taka” makullin ya dauka ya miqa mata yace “sai kin dawo” Zara ta karba cikin murna yayinda ya juya ya shiga dakin shi. Zara tana tafe bata ankara ba sai ta ji tayi karo da mutum. Da sauri ta dago fuskarta ta ga Ruqayya wadda take tsaye tana kallonta cikin bacin rai. A rude Zara tace “yi haquri Anty Ruqy, ban gan ki ba. ina kwana, bye” Da gudu ta wuce ta bar wurin domin kuwa bata son tashin hankali. Ruqayya dai rai a bace ta shiga dakin shi ta tarar har ya shiga wanka. Zama tayi bisa gado tana tunanin yadda zata yi da Zara. ************ NILE UNIVERSITY Zara da Hafsat zaune a garden din department dinsu yayinda suke jiran lokacin next lecture dinsu.+ Hafsat ce tace “hajiya baki bani labarin sabon wuri ba, ya kishiyarki?” Zara ta fashe da dariya tace “ke fa kika san kishiya, na sha warning jiya” Anan Zara ta bata labarin abinda ya faru jiya daga farko har qarshe. Hafsat tayi tsaki tace “wallahi ki daina tsoron ta, duk empty threats ne babu abinda zata iya yi miki” Zara tayi dariya yayinda Hafsat ta cigaba da fadin “ke ni fa gani nake kamar Ya Farouq ba wani sonta yake ba” Zara tace “inji wa ya gaya miki? Da baya sonta ai bazai aure ta ba” ta gyara zama tare da matsawa daf da Hafsat tace “babes baki san wani abu ba, ashe Ya Farouq yana da six pack abs ban sani ba?” Hafsat ta fashe da dariya tare da fadin “haba babes, toh ya aka yi kika gani?” Zara ta bata labari tace “wallahi na ji kunya da ya kama ni ina kallon shi, how I wish..” sai kuma tayi shiru tana murmushi. Hafsat tace “how you wish what? Lallai ma yarinyar nan, wallahi ki cire idanuwan ki daga kan mijin wata, babu ruwana idan Ruqayya ta karta miki rashin M” Dariya Zara tayi tace “toh ba yaya na bane” Hafsat tayi mata gwalo tace “ita kuma mijin ta ne, kuma ta fi ki right din ganin six packs dinshi” Zara ta turo baki tace “not fair babes” Suna cikin hira ne Mahmood ya nufo wurin su. Hafsat dai tana ganin shi ta kai bakinta saitin kunnen zara tace “shi Mahmood hala eight packs gareshi” Zaro idanuwa tayi da sauri ta kalli Hafsat tace “Allah ya isa bestie” Hafsat ta fashe da dariya yayinda Mahmood ya qaraso ya zauna gefen Zara yace “my Cutie ya kike?” tayi murmushi tace “lafiya lau sweetie, har kun fito daga lectures din?” yace “eh, I am done for today ma, kin san tunda za’a fara examz next week gabadaya lecturers din sun ce bazasu sake zuwa ba” Ya kalli Hafsat yace “amarya how far” hafsat tayi dan murmushi tace “lafiya lau Mahmood” Daga nan Hafsat ta miqe tace “babes bari in shiga class, sai kin shigo” bayan Hafsat ta tafi ne Mahmood yace “hope dai ba’a takura miki a gidan yayan naki?” murmushi tayi tace “ko kadan, Ya farouq is the best” Mahmood yace “arrghhhh” ta fashe da dariya tace “yaushe zaka zo, yakamata inyi introducing dinku” yace “bari mu gani zuwa weekend” haka dai suka cigaba da hira har lokacin lecture dinta yayi suka yi sallama. FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION Da daddare Farouq da Ruqayya suna zaune kan dinning ne Zara ta fito sanye cikin wani three quarter da T-shirt, gashin kanta a tsefe yake don haka ne ta kama shi da ribbon a tsakiyar kanta. Sai zabga qamshi take kamar kullum. Cikin sallama ta shiga dinning din inda ta ja kujerar da take kallon Ruqayya ta zauna. STORY CONTINUES BELOW Ta kalli Farouq tana murmushi tace “Ya Farouq how was your day?” yace “good, yours?” Tace “Alhamdulillah” ta kalli Ruqayya wadda take ta hararar ta tace “Anty Ruqy sannu da gida” Ruqayya bata amsa ta ba yayinda ta janyo plate ta ajiye a gaban ta sannan ta kalli plate din Farouq dauke da cous-cous dan kadan. Girgiza kai tayi ta miqe tana bubude warmers din da ke bisa tebir din, gaba daya ta gama budewa amma bata ga abinda take so ba don haka ne ta rufe ta koma ta zauna. Kallon Farouq tayi tace “Ya Farouq dan wannan abincin zaka ci?” Cikin bacin rai Ruqayya tace “sannu Maman Farouq, me ya ruwanki” Farouq dai dariya yaso ya qwace mishi amma ya matse. Zara ce ta kalli Ruqayya tace “Anty toh baki san irin abincin da Ya Farouq yake so bane? Ai…” Farouq ne ya dakatar da ita yace “shut up, dan kadan nayi niyyan ci yau” Zara wadda tasan ba haka bane ta miqe tare da fadin “sorry Ya Farouq” “Dawo ki zauna ki ci abinci, so kike idan su Mamy suka dawo su ce bana baki abinci ko?” abinda ya fada kenan. Murmushi tayi tace “Ya Farouq ni bazan ci wannan abincin ba, zan je in dafa nawa ne” Ruqayya ce ta miqe tace “what? Ai kuwa baki isa ba, abincin da aka dafa a gidan nan shi zaki ci, idan ba haka ba sai dai ki kwana da yunwa” Zara ta bata rai tace “toh wai Anty ni fa bana son wannan abincin, shima fa Ya Farouq kawai ci yake yi don baya da option” Muryar Farouq ta ji yana fadin “dawo ki zauna” Zara ta koma ta zauna tana turo baki. Ya dauki plate ya zuba mata abinci sannan ya tura a gabanta yace “eat” Zara ta harari Ruqayya tace “ni gaskiya bana son wannan” kallon da yayi mata ne yasa ta dauki cokali yayinda Ruqayya take yi mata murmushin mugunta. Bayan sun gama dinner ne zara ta koma Falo ta canza channel zuwa Zee Tv tana kallon Dance India Dance, a yau ake season finale. Kwance take akan doguwar kujera inda tayi nisa a kallon. Kamar daga sama ta ga Ruqayya ta shigo falon ta dauki remote ta mayar Mnet Movies. Zara ta kalle ta tace “don Allah Anty Ruqy ki bari in gama kallon wannan, an kusa gamawa fa” Ruqayya dai ko kallon Zara bata yi ba balle ta amsa ta. ganin haka ne Zara ta miqe ta nufi sashen Farouq a guje. A lokacin da ta shiga falon shi yana kallon tashar CNN ne inda ake hira da wani babban likita. Gaba daya hankalin shi yana kan TV bai kula da ta shigo ba. Ganin ta yayi a gaban shi tayi kneel down tace “Ya Farouq don Allah kace ma Anty Ruqy ta barni in gama kallon DID, yau season finale ne kuma an kusa gamawa.” Remote ya miqa mata yayinda ya tashi ya nufi dakinshi. Zara ta koma bisa kujera ta canza sannan ta cigaba da kallonta. Ruqayya dai jin Zara shiru bata sauko bane yasa ta nufi sashen Farouq. Tana shiga kuwa ta hango Zara kwance tana ta kallon ta har tana dariya. ran Ruqayya a bace tace “toh mayya, wato nan kika dawo kenan. For your kind information ba’a zama nan falon domin kuwa falon maigida ne” Zara dai bata kalli Ruqayya ba balle ta tanka ta. ganin haka ne yasa Ruqayya ta qaraso wurinta tace “ba da ke nake Magana ba?” Gani tayi Zara ta miqe tana ihu tace “yess, na ji dadi da Karan ya ci wallahi, wooow” sannan ta ajiye remote din ta wuce ta gefen Ruqayya ta fita abinta. STORY CONTINUES BELOW Ruqayya tana nan tsaye cikin bacin ran wulaqancin da Zara tayi mata ne kawai ta fashe da kuka. Farouq yana zaune a dakinshi yana kallon hirar da ake yi da likita a tashar CNN ne Ruqayya ta shigo tana kuka. Cikin mamaki yace “wifey what is it? Cikin ne?” Da sauri ta nufo shi ta haye shi cikin kuka tace “Honey yarinyar nan ta raina ni” cikin rashin fahimta yace “me tayi miki?” tace “rashin kunya tayi mun, don nayi mata Magana shine zata wulaqanta ni?” Girgiza kai yayi yace “yi haquri, kin dai san kin girmi Zara nesa ba kusa ba, ki daina kula ta please. I really don’t want problems” haka dai ya dinga lallashin ta har ta haqura. *********** A yau tun da safe Farouq ya wayi gari baya jin dadin jikin shi, yau kwana biyu kenan yake jin wani iri amma saboda rashin son kwanciya sai ya dage yana ta al’amuran shi kamar kullum. Tun da safe ya kira waya asibiti ya fada musu bazai samu zuwa ba dayake baya da surgery ko daya dama. Zara dai ko da ta fito bata gan shi ba sai tayi tunanin ya tafi asibiti ne don haka itama tana gama breakfast ta wuce school. Ruqayya kuwa ko da ta tambaye shi sai ce mata yayi ya gaji ne zai huta for today. Dayake ana shirye shiryen bikin autar su Hajjaju sai tayi tafiyar ta. Yinin ranar kuwa Farouq yana nan gida. Bayan yayi sallar La’asar ne ya koma falon shi a dalilin gajiya da yayi da zama daki. Yana kwance akan kujera ne Zara ta turo mishi text message kamar haka: “yau ban gan ka ba, where are you? I want to see you” Farouq dai ya rasa ya akayi Zara ta shiga ran shi a 'yan kwanakin nan, shi kanshi yana son ganinta domin kuwa duk yau bai ganta ba. Murmushi yayi ya tura mata reply kamar haka: “I am at home” Ganin message dinta yayi kamar haka: “why?” ya tura mata reply kamar haka: “I am not doing well” Daga nan sai ganin kiran wayar ta yayi. Bayan ya amsa ne tace “subhanalillah, Ya Farouq me ya same ka?” Yace “nothing” cikin damuwa tace “please Ya Farouq tell me” Yace “hey its nothing serious, kawai gajiya ce” ba tare da tace komai ba ta kashe wayar. Farouq dai yana nan kwance a kan kujera har bacci ya kwashe shi. ********** A rude ta shiga gidan ta tarar babu kowa a nan qasan don haka ta wuce kicin ta ga masu aiki suna ta faman aikace aikacen su. Gaba dayan su suka duqa suna gaishe ta, ba tare da ta amsa gaisuwar su ba tace “Anty Ruqy fa?” Daya daga cikin su ce tace “ta fita tun da safe” Daga nan ta juya ta haura sashen Farouq inda take ta zagin Ruqayya akan rashin kula da shi sannan anjima ta dinga ikirarin ta fi kowa son shi. Kwance ta gan shi a kan kujera yana bacci. Qarasawa tayi ta zauna daf da shi akan kujerar yayinda ta qura mishi ido. Gani tayi ya gyara kwanciya wanda yasa tayi saurin dafa goshin shi ta ji zafi sossai. Hankalinta a tashe tace “Ya farouq wake up please, me ke damunka?” Bude idanuwan shi yayi wadanda suka yi ja yace “wa yace ki baro lectures bayan kun kusa fara examz?” Cikin damuwa tace “ai mun gama lectures, tutorials ne kuma ma dama na iya. What can I do to help?” Girgiza kai yayi yace “nothing, just stay with me” Haka kuwa Zara ta zauna tana ta kallon shi. Idanuwan shi a rufe suke yayinda ta sa mishi ido. A ranta ne take fadin “how could he be this handsome? Ya Salaam” Bata ankara ba sai ta ji muryar shi yana fadin “ta ya zanyi bacci kin sa ni a gaba kina ta kallo, aren’t you tired of staring at me??” Zaro idanuwa tayi cikin mamaki tare da jin kunya tace “haba Ya Farouq, I am only watching over you ne fa” Yace “okay, thanks for the complement” Zaro idanuwa tayi tare da fadin “laaa, a fili na fada?” Yace “how could he be this handsome? Ya salaam” Runtse idanuwa tayi cikin kunya ta miqe zata gudu yayi saurin riqe hannun ta yace “zanyi pretending kamar ban ji ba, we are good” Daga nan kuwa bacci ya kwashe shi. Lokaci kadan bacci ya fizge shi lokaci kadan ya farka. Motsi kadan sai Zara ta taba goshin shi ta ji ko ya rage zafi amma ga mamakinta zafin qaruwa yake yi. Bayan kusan minti talatin ne ta miqe ta nufi kicin inda ta tambayi masu aiki ko akwai garin tuwo amma abin mamaki sai suka ce babu garin tuwo a gidan, asali ma basu taba tuqa tuwo ba. Ran Zara a bace ta wuce dakinta ta dauko robar ruwa da towel sannan ta koma wurinshi. Towel din ta matse sannan ta dora mishi a goshi, haka ta dinga yi mishi tsawon minti goma sha biyar, ahankali zafin kan shi ya fara sauka. Idanuwan shi ya bude tare da riqe hannun ta yace “thank you my little doctor” Murmushi tayi tare da jin dadin sunan da ya kira ta da shi. Daga nan ne bacci mai nauyi ya kwashe shi. Zara tana nan zaune a gefen Farouq yana ta bacci yayinda take ta kallon shi ne Ruqayya ta shigo falon. Ganin Zara zaune daf da Farouq ne yasa ta zaro idanuwa cikin mamaki tace “what is going on here?” Da sauri Zara ta miqe ta nufi wurinta tace “Anty Ruqy please come with me, kada mu tada shi daga bacci, baya da lafiya” Zara ta wuce ta yayinda Ruqayya ta bi ta da ido. Ganin Farouq bacci yake yi dagaske ne yasa ta bi bayan Zara cikin bacin rai tace “wai ke wacce irin 'yar iskar yarinya ce? Meyasa kika maqale ma Farouq? What is the close marking all about? Me kike so??” Zara wadda maganganun Ruqayya suka soki zuciyarta ne tace “Anty Ruqy kada ki qara zagi na” Ruqayya cikin mamaki tace “idan na zage ki me zaki yi, karuwar yarinya kawai” Zara ta runtse idanuwan ta tace “I really don’t want to disrespect you but I don’t have a choice yanzu, zakiyi regretting kira na karuwa I promise you” Haka Ruqayya ta tsaya tana kallonta cike da mamaki. Zara wadda ta nufi dakinta a guje ta haye gadonta tana ta kuka. Ba’a taba ci mata mutunci irin na yau ba duk tsawon rayuwarta. Zara tayi alqawarin sai ta rama cin mutuncin da Ruqayya tayi mata. *********** Zara ta idar da sallan Magrib ta nufi kicin din gidan.+ A lokacin dai Masu aiki suna ta faman shirya Dinner. Bayan sun gaishe ta ne ta amsa tace “kuna da poundo or anything da zan iya transforming into swallow?” Daya daga cikin su ne tace “wallahi Anty Zara babu, Madam bata son irin wadannan abincin” Zara dai a ranta tace “mahaukaciya bata san irin abincin da mijin nata ya fi so bane” girgiza kai tayi tace “okay amma dai akwai doya ko?” suka ce “eh” tace “akwai turmi?” nan ma suka ce “eh” Zara ta samu wuri tace su miqo mata doya. (Ni kuwa nace "wait what????🙄 Me zata yi??") Wadda ta miqo mata doyar ce tace “Anty ki bari kawai inyi miki” Zara tayi murmushi tace “No ki bar shi kawai, I have to make it myself” Anan fa Zara ta fere doyar wadda da qyar Allah ya taimaka ta qarasa bata yanke hannu ba. Su kansu masu aikin yadda suka ga tana ferewa sun tabbatar bata saba ba. A gaban masu aikin Zara ta hada miyan ganye tare da farfesu wanda nan da nan qamshi ya dinga tashi har suna mamaki. Sun cika da mamaki sossai domin fa tana yi tana ta qonewa amma dukda hakan ta hada komai perfect. Zara tana zaune a bisa wani kujera ne tace su miqo mata turmin. Su dai aikinsu suke yi suna kallon ikon Allah. Gani suka yi Zara ta zuba doya a ciki ta fara daka. Da sauri daya daga cikin su tace “Anty Zara please ki bari in daka miki” Zara tace “barshi kawai ai babu yawa” Haka dai Zara ta cigaba da daka wanda fa da gani kasan bata taba yi ba. Asali a gidan Mamy masu aiki suke yi amma a dalilin tana yawan kallon yadda suke yi ne yasa ta iya. A gajiye ta qarasa dakan wanda kuwa hannuwan ta sunyi ja sossai, har sun kumbura. Sai da ta gama hada komai ne sannan ta kalli masu aikin tace “kuyi serving wannan a dinner, na Ya Farouq ne” cikin mamaki masu aikin suka kalli juna yayinda ta fita daga kicin din hannun ta yana ciwo. (Whoa🙄🙄) ************ Zaune yake a kan dinning din dafe da kanshi inda yake jiran Ruqayya. A lokacin daya daga cikin masu aikin ne ta fito ta jejjera warmers din kamar kullum. Idanuwan shi ne suka sauka akan warmer din sakwarar da Zara tayi wanda marfin shi transparent ne. Ya nuna warmer din yace "hey open this" mai aikin ta bude da sauri. STORY CONTINUES BELOW Cikin mamaki yace “who made it?” cikin ladabi tace “Anty Zara ce” miqewa yayi da sauri ya nufi dakin Zara domin kuwa ya sani sarai babu yadda za’a yi ace ta gama lafiya ba tare da injury ba. A lokacin da Ya shiga dakin tana kwance a kan gado tana kallon hannuwan ta wadanda suka yi ja sannan suna mata zafi. Ganin shi ne yasa ta tashi zaune tace “Ya Farouq ya jikin ka?” Zama yayi gefen ta yace “mu ga hannuwan ki” boyewa tayi tace “me zaka gani?” Kallon da yayi mata ne yasa tayi saurin nuna mishi inda ya zaro idanuwa yace “what the hell, wa ya sa ki?” Murmushi tayi tace “ba kowa Ya Farouq, dama nayi maka ne saboda ka sha magani kuma ma ai nasan its one of your favourite” Farouq dai shiru yayi yana kallon Zara. For the first time ya fara tunanin wai me ma ya hana shi auran Zara ne domin kuwa ita ce wadda ta san komai da yake so wanda ba sai ya tambaya ba.1 A ran shi yace "toh sonta kake da zaka aure ta??" Can kuma yace "ita Ruqayyar sonta kake da ka aureta?" (Ni kuwa da na jiyo wannan zancen sai na fara tunanin anya Farouq bai zurma tarkon Zara ba??)1 Ganin ya qura mata idanuwa ne yasa tace “Ya Farouq kayi haquri, na ga kamar ranka a bace” Ajiyar zuciya yayi tare da girgiza kai yace “raina a bace ne saboda kin ji ciwo a dalili na, don’t do this next time” Cikin mamaki da jin dadin kalaman shi ne tace “I will do anything for you big brother, So yes I will do it again for you” Hararar ta yayi, ya miqe zai shiga bathroom dinta. Gani nayi ta miqe da sauri tare da fadin “Ya Farouq ina zaka je?” Cikin mamaki ya juyo ya nuna bathroom din da hannun shi yace “first aid kit” a rude tace “ehm, da ka bar shi kawai” Hararar ta yayi ya shiga yayinda ta koma bisa gado ta runtse idanuwan ta tana fadin “Oh My God” Farouq dai yana shiga bathroom din ya ci karo da su panties da bra din Zara dayawa a gefen washing machine wadanda da alama wanki zata zuba su cikin machine din amma ya gagara. Girgiza kai yayi tare da yin tsaki ya nufi inda first aid kit din yake ya dauko ya fito. Tunda ya fito ta kawar da kanta daga inda yake yayinda ta kasa kallon shi. Ya gane sarai dalilin da yasa tayi hakan. Ji tayi yace “I hate laziness..” da sauri tace “wallahi Ya Farouq I was about to…” Yace “shut up dirty girl, I know you well” turo baki tayi yayinda ya zauna gefen ta yace “bude hannuwan ki” da sauri ta bude mishi. Ya fara shafa mata magani ne ta sa ihu wanda ya kalle ta yace "shut up, idan kin ji zafi gobe kya qara" murmushi tayi tace "Ya Farouq I will surely do it again and again and again for you" murmushi yayi yace "then you must be crazy" fashewa tayi da dariya. Bayan ya gama ne yace “oya tashi mu je dinning, you need to eat” Ruqayya tana nan zaune a dinning tana ta jiran shigowar Farouq sai gani tayi ya shigo tare da Zara suna dariya, da alama hira suke yi. STORY CONTINUES BELOW Wani wawan harara Ruqayya ta sakar ma Zara wadda a ranta tace “yanzu zaki ga karuwanci” Ruqayya dai bata ankara ba sai ji tayi Zara cikin shagwaba tace “Ya Farouq toh bazan iya jan kujera ba” Ruqayya dai gani tayi ya sa hannu ya janyo mata kujerar gefen shi wadda take saitin ta sannan suka zauna. Ruqayya kuwa sakin baki tayi tana kallon Zara da Farouq yayinda Zara ta kashe mata ido daya cikin tsokana. Mai aikin ce ta fara zuba musu abinci kamar kullum. Sakwarar da Zara tayi ne mai aikin ta bude yayinda hankalin Ruqayya ya kai wurin. Cikin mamaki tace “waye yayi wannan abincin?” Zara tana murmushi tace “ni ce Anty Ruqy, ba naki bane ai, na Ya Farouq ne” Da sauri ta kalli Farouq tace “Honey yaushe ka fara cin irin wannan?” Kafin ya amsa ne Zara tace “toh wai baki san favorite din Honey din naki bane?” Farouq ne yayi ma Zara wani irin kallo wanda ya sa ta yi shiru yayinda ya kalli Ruqayya yace “zan sha magani da shi ne” Ya miqe ya tafi dauko magani yayinda Zara ta kalli Ruqayya tana murmushin mugunta. Ruqayya dai ta cika fam da bacin rai. A lokacin da Farouq ya dawo tuni mai aikin ta zuba ma Ruqayya fried rice. Ta tambayi Zara “Anty Zara wanne zan sa miki?” Zara ta daga hannuwan ta cikin fuskar tausayi tace “I would have loved the poundo but bazan ci ba, thank you” Farouq ne ya kalle ta cikin tausayawa sannan yayi dismissing din mai aikin. Ji suka yi yace “open your mouth” da sauri suka dago kai suna kallon shi yayinda Ruqayya ta ga ya kai cokali saitin bakin Zara. Ita kanta Zara ta razana domin kuwa kasa bude baki tayi tana kallon Ruqayya wadda take kallon Farouq cikin qunar rai. Abinda zara ta dade tana so, Farouq ya bata abinci a baki. Zara dai ganin dama ta samu sai kawai tayi murmushi cikin shagwaba tace “No Ya Farouq ka bar shi” Kallon da yayi mata ne yasa ta bude baki ya sa mata. Aikuwa Ruqayya ta miqe a fusace tace “wane irin wulaqanci ne wannan Honey?” Cikin rashin fahimta ya juyo ya kalle ta yace “ban gane ba, cant you see cewa she is helpless?” Cikin masifa Ruqayya tace “toh shine sai kai ne zaka bata abincin??” Yace “toh in bari ki bata ne?” (Ni kuwa na fashe da dariya... kun ji Farouq da neman hada rigima🤣) Bata ce komai ba ta ruga ta nufi dakinta tana kuka. Ko da Ruqayya ta tafi Zara ta kalli Farouq tace “Ya Farouq Anty Ruqy ta ji haushi fa” Ya harare ta yace “its all thanks to you ai” STORY CONTINUES BELOW Tayi murmushi yayinda ya cigaba da bata tana ci. Gani yayi ta sa mishi ido tana murmushi. Cikin mamaki yace “what?” tace “I am enjoying the fact that you are feeding me, how I wish it will always be like this” Murmushi na ga yayi yace “I have an idea” tace “what” Yace “ki dinga jin ciwo a hannun ki kullum sai in dinga baki abinci da kaina” Fashewa tayi da dariya tace “Yesss” yayinda ya Harare ta yace “if you try that nonsense I will deal with you” tana dariya tace “sorry sir”. Bayan ya gama bata ne yace “ta ya kika boye maganin last time? show me” Zara tana yi mishi dariya ta dinga nuna mishi yadda zaiyi. Tana nan zaune ya cinye abincin shi sannan ya miqe ya dauki plate din Ruqayya yace “let me go and console my wifey, good night” Zara ta turo baki a ranta tace "na dai yi maganinta yau, saura na gobe kuma" (Toh fa🙄) Zaune take a bisa gadon ta tana ta rusa kuka, ta masifar jin zafin wulaqancin da Farouq yayi mata. Cikin sallama ya shiga dakin ya tarar da ita tana kuka. Ajiye plate din yayi sannan ya zauna daf da ita ya janyo ta jikin shi yana fadin “listen wifey..” Cikin masifa tace “ni ka qyale ni, ka koma can wurinta tunda ta fi ni matsayi a wurinka” Qara matse ta yayi jikin shi yace “you are my wife and my top priority" Ya dan yi shiru sannan yace "okay, i am sorry please" Ruqayya dai ta sani sarai idan ma bata haqura ba fita harkar ta zaiyi, ta sani cewa ba qaramin abu bane Farouq ya zauna lallashin mace. Ajiyar zuciya tayi sannan ta rungume shi. Fuskar ta ya shafa yace “meyasa kika zabi kiyi starving little Ruku?” Cikin shagwaba tace “toh ba Ruku senior bane ya…” Katse ta yayi tare da fadin”ssshhhh” ya janyo plate din yace “oya eat your food” Murmushi tayi tace "Honey, I love you” shima murmushi yayi sannan ya fara bata abinci a baki wanda daurewa take tana ci domin kuwa idan ta tuno lokacin da yake ba Zara ranta ba qaramin quna yake yi ba. Ko da ya gama bata nan ya jira ta shirya cikin kayan baccin ta kafin suka wuce sashen shi. *********** Zara dai ko da ta koma daki ta sha dariya sossai. Ear piece ta zura a wayarta ta kira qawar ta Hafsat ta bata labari. A lokacin kuwa Mukhtar yana kusa da Hafsat suna ta kwasar dariya. Ji tayi Mukhtar yace “wallahi small madam kada ki kashe ma yayan ki aure” cikin mamaki tace “laaa, Ya Muky dama kana ji?” dariya yayi yace “speaker phone kike hajiya” Itama dariya tayi yayinda yace “I am glad you are enjoying yourself a gidan abokina amma be careful, no more trouble i beg you” Zara tana dariya tace “I will Ya Muky, thank you. But if she finds trouble i will give it to her, that too on a silver platter”. Mukhtar yana dariya yace "Ruqayya ta shiga uku kuwa" haka dai suka cigaba da hira suna dariya har suka yi sallama. *************

Post a Comment for "BA SONTA NAKE BA CHAPTER 7"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...