BA SONTA NAKE BA CHAPTER 2 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BA SONTA NAKE BA CHAPTER 2

BA SONTA NAKE BA CHAPTER 2

- - Post a Comment
BA SONTA NAKE BA CHAPTER 2
WANENE FAROUQ??+ Umar Farouq ya taso cikin gata na iyaye, fari ne sannan dogo, kyakyawa ajin farko. Kamarnin Mamy ya dauko domin hatta gashin kan shi irin nata ne. Umar farouq tun yana qarami ya kasance murdadden mutum, baka taba sanin abinda yake damun shi, ga rashin son Magana sannan baya son surutu. Farouq baya son raini shiyasa ko Sadiq da yake dan uwan shi uwa daya uba daya baya sakar mishi fuska balle Zara. Farouq yana son tsabta a rayuwar shi wannan ne yasa duk yadda masu aiki suka gyara mishi abu toh fa sai ya sake gayarawa shiyasa ma bai damu da sai an gyara mishi ba. Farouq yana da son motsa jiki, shiyasa a kullum sai yayi exercise a gym. Kalolin abincin da yake so kuwa hatta Mamy bata gama gane su ba, banda Zara ba wanda ya gama gane halin Farouq. Zara ita ta kasance matsalar shi tun yana qarami domin kuwa halin su ya banbanta ta kowanne sabga. Lokutta da dama a dalilin ciwon ta ne yake raga mata amma da lafiyar ta qalau da ta sha wahala a hannun shi saboda baya son takurar da take yi mishi. Tunda Farouq ya tafi Germany gaba daya daily activities din Zara babu wanda bai sani ba domin kuwa a kullum tana kan tura mishi hotunan ta tare da bashi labarin abubuwan da tayi. Duk qasashen da Zara take zuwa Farouq ya sani. Ko sau daya bai taba replying mata saqonnin ta ba amma dukda haka kuwa bata fasa tura mishi ba. Akwai wani lokacin da ya gaji da saqonnin yayi blocking dinta, hankalin Zara yayi mugun tashi a lokacin. Qarshe ma har ciwon ta sai da ya tashi saboda damuwa da ta sa a ranta, da su Abba suka gano dalili ne yasa suka gargadi farouq din akan kada ya sake yin abinda zai yi sanadiyyar tashin hankalin ta. A wannan lokacin kuwa fushin da iyayen shi suka yi da shi ya bashi tsoro domin kuwa basu taba yin irin shi ba. Da wannan ne yayi unblocking dinta. Farouq yakan zo hutu kowanne qarshen shekara, wannan ne yasa duk qarshen shekara Zara take cikin farin ciki marar misaltuwa. A duk lokacin da yake zuwa kuwa boye makullin motar ta take tace ya bace sannan ta takura ma Mamy akan ta sa Farouq din ya dinga kai ta makaranta sannan ya dauko ta. Babu yadda farouq baiyi da Mamy ba akan daya daga cikin direbobin gidan sun dinga kai ta amma Mamy ta qi. Haka nan ba da son ran shi ba yake kai ta. A kullum kuwa sai sunyi fada akan yanayin kayan da take sakawa domin kuwa Farouq baya qaunar English wears din da Zara take sakawa. Ganin haka ne yasa kimono da after dress suke cin uban su a wurin ta a qarshen kowane shekara A rayuwar Farouq ya tsani mage, A lokacin da suke qanana Zara tana da wata mage wadda a dalilin ta ma ko fitowa baya yi, kullum yana daki. Zara kuwa tana bala’in son magen. Akwai ranar da tsautsayi ya gifta inda Sadiq da Zara suke wasa da magen sai kawai Zara ta jefo ma Sadiq magen ashe Farouq ya zo wucewa sai kawai magen ta fado a jikin shi. saboda tashin hankalin da ya shiga har suma yayi. Tun daga wannan lokacin kuwa akan dole Zara ta rabu da mage a rayuwarta domin kuwa duk abinda Farouq baya so to itama bata so. Mukhtar Abubakar ya kasance abokin Farouq tun suna qanana, tare suka yi primary da secondary a qasar ingila yayin da shi farouq ya wuce Germany don cigaba da karatu, shi Mukhtar din ya cigaba a nan Ingilan inda ya karanci Business Administration wanda daga baya shima iyayen shi suka dawo Nigeria. STORY CONTINUES BELOW Idan akwai wanda ya san halin farouq banda Zara toh kuwa abokin shi ne Mukhtar. Lokutta da dama idan Mukhtar yana kallon abubuwan da suke faruwa tsakanin Zara da Farouq yakan tambaye shi ko akwai soyayya. Wannan tamabayar ba qaramin bata ma Farouq rai take yi ba domin kuwa ya sha gaya ma abokin nashi bazai iya auren qaramar yarinya ya ajiye a gidan shi ba saboda baya son raini da shiririta. Burin Farouq bai wuce ya auro mata wadda ta san abinda take yi domin kuwa a cewar shi bayada lokacin raino da lallashi. Umar Farouq yana matuqar son addinin shi, yana da son taimakon bayin Allah sannan yana da tausayi matuqa. A tunanin mutane, dalilin son taimakon mutane ne yasa shi karantar Medecine. Asali Farouq bangaren surgery ya karanta, a taqaice dai surgeon ne wanda ya san abinda yake yi domin kuwa ana matuqar alfahari da shi ba a Nigeria kadai ba hatta qasashen turai da dama. Allah ya daukaka shi fiye da yadda ba’a tunani. Su Abba ne suka tilasta mishi karantar Cardiology A dalilin ciwon Zara wanda tun daga nan case dinta ya koma hannun shi. Dalilin da yasa ya dade a Germany kenan wanda har aiki ya fara yi a can din A lokacin da ya dawo shekarun shi talatin a duniya, likita bokan turai. Ga kudi ga aji domin kuwa tun suna qanana Abba yake zuba musu kudade a account shi da Sadiq. A yannzu kuwa ba qananan kudade gare su ba a accounts dinsu musamman Farouq wanda kudaden da yake samu a bangaren aikin shi ma kawai sun fara neman fin qarfin shi dukda abin alkhairin da yake yi ma talakawa da mabuqata. Farouq dai har zuwa lokacin da ya dawo Nigeria baya da budurwa ko daya, Allah yayi yawa da ‘yan matan da ke son shi har a qasar Germany amma sam babu wadda ya kalla, aikin shi kawai ya sa a gaba. Tun yana Germany kuwa ‘yan mata a nan Nigeria suke targeting dinshi domin kuwa babu wanda bai san labarin Farouq Al-Hussain ba, yaro a gidan CBN governor. A yanzu haka Farouq shine mamallakin wannan fitaccen asibitin wanda yake Maitama wato Central Hospital. Wannan asibitin yana dauke da likitoci wadanda suka qware a fanni daban daban, a cikin su kuwa harda turawa sannan asibiti ne mai kayan aiki na zamani na gani na fada. Akwai bangarorin Asibitin da idan ka shiga zaka manta cewar a asibiti kake domin kuwa an qawata asibitin fiye da tunanin dan adam. WACECE RUQAYYA?? Ruqayya Bashir wadda aka fi sani da Ruqy asalin ‘yar Maiduguri ce, mahaifin ta Alhaji Bashir ya rasu tun tana shekaru goma. Mahaifiyar ta wadda ake kira Hajjaju ta sake yin aure a garin Abuja inda ta auri tsohon ministan garin Abuja wato Alhaji Abubakar Bulama. Hajjaju mahaifiyar Ruqayya ta haifi yara biyu a gidan Alhaji Abubakar, Yazeed da Zain. Hajjaju ta kasance mai son abun duniya, dukda kudin da mijin ta yake da shi bata fasa neman kudi ba. business take yi sossai a cikin garin Abuja na sayar da kaya, boutique dinta kuwa kala kala a cikin garin Abuja. Ruqayya ta taso cikin gata, a cikin garin Abuja tana cikin manyan yara wadanda suke ji da kan su. Ruqayya kyakyawa ce ajin farko sannan fara sol mai dogon gashi har gadon baya. Qirar ta tafi kama da a kira ta da Model. Tana da masifar jan aji gata bata qaunar talaka ko alama, burin ta bai wuce ta auri mai kudi ba domin kuwa halin mahaifiyar ta Hajjaju ta dauko. Qawar Ruqayya wadda ta amince da ita a garin Abuja itace Aliya, Aliya ta kasance halin su daya da Ruqayya shiyasa tasu ta zo daya. Babu party din da basu zuwa a cikin garin Abuja wannan ne yasa suka san manya manyan samarin Abuja. Ruqayya dai ta sha kwana a waje ba tare da mahaifiyarta ta damu ba, a cewar ta wayewa ce. A haka wata rana tana zaune da qawarta Aliya a Frozenscoops ta ga farouq tare da Zara da Sadiq sun zo siyan ice cream. Wannan fitar dai akan tilastawar Mamy aka yi ta domin kuwa a lokacin Farouq cewa yayi bazai je ba. STORY CONTINUES BELOW Tunda ta dora idanuwan ta akan shi tayi alqawarin sai ta mallake shi domin kuwa ya kai matsayin da take nema a mijin auren ta. Tuni tayi bincike akan shi. A takun farko kuwa ta fahimci lallai bazata samu fuska ba don haka ne ta neme shawara a wurin Hajjaju. Hajjaju dai ganin cewa Farouq din mai kudi ne sossai sannan yaron CBN governor shiyasa ba tare da bata lokaci ba ta sa ‘yarta a gaba suka nufi wurin Boka cika aiki a can bayan wani dutse hanyar Bida Niger State. Ko da boka cika aiki ya duba al’amarin ya dan firgita domin kuwa ya gano hargitsi a gaba wanda har ya basu shawara akan su haqura da Farouq domin kuwa ba alkhairi bane a gare su. Ruqayya tayi fafur ta qi, a cewar ta ita dai ko ma meye zai faru tana son ta auri Farouq. Boka cika aiki ya sanar da su cewa ko da ta auri Farouq bazai taba son ta ba sannan gaba daya farin cikin shi da rayuwar shi tana hannun wata wadda bai samu ganin ko wacece ba. Boka cika aiki ya basu shawara akan lallai a bar wannan aikin domin kuwa abinda ya hango ya fi qarfin shi. Hajjaju ta so Ruqayya ta manta da zancen Farouq a lokacin domin kuwa duk aikin da Boka cika aiki yake shakkar aiwatarwa ba qaramin abu bane amma ita Ruqayya ta kafe akan lallai ta amince zata auri Farouq a hakan. Da wannan ne ya bata wani kwalli ta sa a idanuwan ta sannan ta je su yi ido hudu da Farouq, ba da dadewa ba kuwa za’a daura auren su. Aikuwa dai Ruqayya ranar da ta shirya musamman ta nufi asibitin Farouq. Kai tsaye ta nemi ganin shi wanda sai da ta sha wuya sannan domin kuwa yana ganin mutane ne based on appointment ba haka kawai ba. Aikuwa ko da ta shiga ofis din suka yi ido hudu sai ya ji duk duniya babu macen da zai so ya aura idan ba ita ba. Wasa wasa dai Farouq bai san ya akayi ba Ruqayya ta shiga ranshi dukda kuwa ta fi damuwa da shi fiye da yadda ya damu da ita. Dayake ta san yadda al’amuran suke duk wulaqancin da yake yi mata bata damuwa, Farouq ba zai taba kiran Ruqayya a waya ba idan ba ita ta kira shi ba. sannan ko laifi yayi mata sai dai ita ta nemi su shirya idan ba haka ba shi bazai taba neman sulhu ba. Ruqayya dai ta tsani Zara fiye da tunanin dan Adam dukda kuwa haduwar su bai wuce sau uku ba, ta lura da cewa Zara tana shige ma Farouq sossai. A dalilin ganin cewa Farouq din bai damu da Zaran ba ne yasa ta kwantar da hankalin ta. Hajjaju ta so ta rabu da Farouq musamman idan ta tuno kalaman Boka cika aiki amma ita Ruqayya ta qi. Ruqayya Bashir tana da wani saurayi mai suna Mustapha wanda aka fi sani da Musty. Ya kasance saurayinta tun kafin ta hadu da Farouq. Ruqayya tana son Musty sossai amma matsalar baya da irin dukiyar da take buqata. Musty shahararren dan duniya ne domin kuwa shi ya fara lalata ma Ruqayya rayuwa. Sai ya kama Hotel su yi kwana uku suna sharholiyar su. Ruqayya dai tana jin dadin harka da Musty domin kuwa duk wani salo na soyayya ya iya shi. A zahiri Ruqayya tana nuna ma Farouq cewa ita Ustaziya ce mai son Addini, shiyasa a kodayaushe tana cikin shiga ta alfarma. Wannan ne yasa ya ji ta shiga ranshi matuqa domin kuwa dai Farouq yana bala’in son mace kamila. A lokacin da Farouq ya gabatar da Ruqayya a matsayin matar da yake son aure wurin su Abba sunyi matuqar mamaki domin kuwa burin su bai wuce su hada Zara da Farouq aure ba. Duk da su Abba basu ji dadin hakan ba sun ji dadin cewa zai yi aure kuma sun qudurta a ran su burin su zai cika wata rana insha Allah. Dayake Alhaji Abubakar Bulama mutumin arziki ne wanda kowa ya shaida hakan nan da nan aka gabatar da maganar aure. don haka tuni aka fara shirye shiryen auren Farouq da Ruqayya. Har asibiti ya kai Ruqayya inda aka gwada jinin su don tabbatar da lafiyar su sannan aka tabbatar da genotype dinta domin kuwa baya son matsala. A lokacin da Zara ta ji labarin bikin hankalin ta yayi matuqar tashi. Gaba daya gidan sai da aka fahimci lallai wani abu yana damunta amma ta gwada babu komai. Lokacin bikin yana matsowa yayinda Zuciyar Zara ta cigaba da zafi. Duk walwala irin na Zara kallo daya zaka yi mata ka san akwai matsala. A lokacin har fargaban shiga social media take domin duk inda ka shiga labarin auren Farouq Al-Hussain da Ruqayya Bashir ake yi. Ana saura sati daya bikin ne Zara ta kasa jurewa don haka ne ta hada kayan ta tace zasu je Excursion Dubai wanda idan mutum bai je ba sai ya samu carry over. Jin haka ne yasa su Mamy basu kawo komai a ran su ba har ma fadi akeyi zata yi missing din bikin Farouq. Wannan kenan! ******************* CIGABAN LABARI+ MUKHTAR ABUBAKAR MANSION Farouq zaune a falon Mukhtar suna buga game kamar kullum. Idan ka gan su a gaban TV toh fa labaru suke kallo ko kuma game suke bugawa. Mukhtar ne yace “wai yanzu abokina idan ka tafi Germany dinnan har wata shidda zaka yi?” Farouq yace “wallahi kuwa abokina, I really have to be part of the course, I am going to miss you guys” Mukhtar yayi murmushi yace “and she will miss you the most” Farouq yace “toh ai da ita zan tafi, after all bazan tafi Germany inyi wata shidda in bar ta anan ba” Mukhtar ya girgiza kai yace “I am talking about Zara abokina” Farouq yayi tsaki wanda daga nan bai sake yin Magana ba. AL-HUSSAIN MANSION Zaune take a qaramin falon Mamy inda ake fama da ita wurin kitso. Mai kitson duk ta bi ta jigata a dalilin rashin natsuwar Zara. kamar kullum idan aka yi kadan sai tace a tsaya ta huta. A lokacin ne Farouq ya shigo gidan, dawowar shi kenan daga asibiti inda ya zo duba jikin Abba wanda ya dan yi rashin lafiya. A gajiye ya shiga gidan domin kuwa surgery yake ta yi tun safe. Ya tarar da Mamy a babban falonta inda take kallon labaru. Bayan sun gaisa ne yace “Mamy Abba fa? Ya jikin nashi?" tace “yana daki yana bacci, da sauqi babu laifi” farouq yace “Allah sarki Abba, harda stress yasa shi kwanciya”. Mamy tace “He has been busy fa tun kafin bikin ka. ko tafiye tafiyen nan da yake yi tsakanin qasashe ai dole ya gaji” Farouq yayi murmushi yace “ban taba ganin hardworking mutum ba kamar Abba, I am so proud of him” kafin Mamy tayi Magana ne suka ji anyi ihu da qarfin tsiya wanda har sai da Farouq ya dafe kanshi. Cikin mamaki ya kalli Mamy yace “meye haka mamy??” Mamy tayi murmushi tace “Zara ce ake yi ma kitso, kasan haka ake fama. Yinin yau haka zata qarasa shi a gaban mai kitso” tsaki yayi yace “wallahi Mamy yarinyar nan ta raina mutane, da girman ta zaki qyale ta tana wannan shirmen?” Mamy tace “haba Farouq idan tace yana mata zafi ai dagaske yana mata zafin ne” girgiza kai yayi yace “toh a aske kan mana kowa ya huta” Mamy ta fashe da dariya tace “a aske kan ta zama kamar namiji? Haba Farouq” wani ihun Zara ta sake yi wanda yasa Farouq ya miqe yayinda Mamy take fadin “kada dai ka bata mata rai don na san halinka” Kwance ya tarar da ita kan kujera yayinda mai kitson tana zaune tana jiranta ta huta kamar kullum. Ga kitso dai an yi rabi yayinda rabin kan yake a tsefe. Muryar Farouq ta ji yana fadin “what is happening here?” da sauri Zara ta miqe tana kallon shi. mai kitson ce tace “ina jiran ta ne ta huta sannan mu cigaba” kallon Zara yayi cikin yanayin da ke bata tsoro yace “je ki zauna a cigaba ko in sa almakashi in yanke gashin ki gaba daya” cikin fuskar tausayi tace “don Allah Ya Farouq kayi haquri, wallahi akwai zafi ne shiyasa nake dan hutawa” kafin ta rufe baki yace “idan kika bari na qara maimaita abinda nace you wont like the outcome” jikinta a sanyaye ta koma ta zauna tana kuka. Cikin fadan da ya fi na farko yace “idan kika bari na sake jin ihun ki daga falon Mamy I will deal with you” ya juya ya fita yayinda mai kitso ta cigaba da kitson har a ranta tana fadin “Allah yayi maka albarka yau ka taqaita mun wahala”. STORY CONTINUES BELOW Hatta Sadiq da ya dawo sai da yayi mamakin yau ana yi ma Zara kitso babu tashin hankali. Mamy ce ta bashi labarin yadda akayi suka dinga dariya. NILE UNIVERSITY Zaune suke a cafeteria inda take ba qawarta labarin abinda Farouq yayi mata jiya. Hafsat tayi dariya har ta gaji yayinda tace “Allah ya qara miki, wallahi Ya Farouq shine daidai da ke” Zara ta Harareta tace “ke muguwa ce dagaske, I think ma zan dauki shawarar da ya kawo na aske kan nawa ma, kin ga da haka zan huta” Hafsat ta fashe da dariya tace “you are not serious” Suna cikin hira ne cikin Zara ya fara ciwo. Yamutse fuska tayi tace “babes na shiga uku, cikina ya fara ciwo” Hafsat cikin damuwa tace “Subhanalillahi, har lokaci yayi kenan?” Zara ta kifa kanta a tebir tace “I think zan tafi gida kawai don nasan any moment zai zo” cikin tausayawa Hafsat ta dafa ta tace “ko in zo in kai ki gida ne?” Zara ta miqe tace “No bestie bari in lallaba in tafi, kin san akwai lecture in ten minutes time gara ki shiga ki ji mana” Hafsat ta raka Zara har motar ta sannan suka yi ma juna sallama. AL-HUSSAIN MANSION Tana isa gida dakinta ta wuce ta jefar da jakar ta sannan ta haye bisa gado. Idan cikin nata ya fara ciwo sai tayi ta juyi idan kuma ya lafa sai ta natsu, a haka har bacci ya sace ta. Zara bata farka ba sai qarfe biyar na yamma, ko da ta farka miqewa tayi a daddafe ta shiga kewaye tayi wanka. Bayan ta sa Pad ne ta sanya wandon three quarter da wata sleeveless top. Yau dai ko mai bata shafa ba balle turare amma fa dukda hakan qamshi takeyi domin kuwa qamshi ya riga ya kama jikin ta. Komawa tayi bisa gadonta ta kwanta. Zara kwance cikin bargo tana sallama da qawarta a waya wadda ta kira ta don jin yanayin jikinta. Mamy ce ta qwanqwaso qofar ta shigo. Ganinta a kwance cikin bargo ne yasa ta nufi wurinta ta zauna a gefen ta cikin damuwa tace “Princess what is wrong? Kin dawo daga school baki zo kika duba Mamyn ki ba. Are you alright?” girgiza kai tayi alamar a’a tace “Mamy I am not okay, my menstrual pain again” cikin damuwa Mamy tace “toh ko in kira Farouq ne idan akwai..” da sauri Zara ta dakatar da ita tace “No Mamy please No, I will be fine zuwa anjima. Ai na saba kullum haka nake yi” Murmushi Mamy tayi tace “bari in sa Larai ta hado miki tea dinki toh, it will help you get better” tayi mata kiss a goshi sannan ta miqe ta fita. Dadaddare Abba zaune a falonshi tare da Mamy suna kallon labaru a TV suna hira. Farouq ne yayi sallama ya shiga. Kamar kullum sai da suka yi musabaha da Abban nashi sannan yace “Abba ya jikin ka?”. Cikin fara’a Abba yace “Alhamdulillah da sauqi, na ji dadin magungunan da ka bani” Farouq yace “masha Allah” ya nufi wurin Mamy ya mata kiss a kumatu tare da fadin “and how is the most beautiful garl on planet doing?” Abba ne ya Harare shi yace “a gaba na?? take time” Farouq yace “Sorry boss” gaba daya suka fashe dariya yayinda Farouq ya zauna gefen Mamy inda ta kamo hannun shi tace “hala daga asibiti ka fito?” yace “eh mamy, anjima ma zan koma saboda akwai surgery din da zanyi cikin dare” Abba ne yace “yaushe ne tafiyar ku Germany din?” farouq yace “jibi ne insha Allah, Ruqayya zata zo gobe tayi muku sallama” Abba yace “toh da kyau, Allah ya taimaka” suka amsa da “ameen”. Abba ne ya kalli Mamy yace “wai ina Princess ne ban gan ta ba? kullum tana qorafin bana zama a gida muyi hira gashi yau throughout ina gida amma ban ganta ba” Mamy ta dan yi murmushi tace “tana dakinta, bata jin dadi ne sossai shiyasa ta kwanta da wuri” Hankalin Farouq ya tashi jin hakan amma bai nuna ba sannan bai tambayi abinda yake damun ta ba. Cikin damuwa Abba yace “Subhanalillahi, me yake damun ta? Ba dai ciwon ta ba?” kafin Mamy ta amsa ya kalli Farouq yace “Farouq je ka duba ta..” Mamy ce ta dakatar da shi tare da fadin “ba wani serious bane, idan ta samu bacci komai zaiyi normal” cikin rashin amincewa Abba yace “dukda haka dai Farouq ya dubo ta ya tabbatar” Farouq dai dama kamar jira yake, ba tare da bata lokaci ba ya miqe yace “bari in dubo ta” Mamy dai dayake ta san abinda ke faruwa bata so Farouq din ya je ba domin kuwa ta lura Zaran bata so. Qwanqwasa qofar dakinta yayi ya shiga. Kwance take a kan tiles din dakin ta. Da alama ma bacci take yi. Cikin mamaki ya qarasa wurinta ya tsugunna a gaban ta yana kallon ta. “What could be wrong with her?” tambayar da yayi ma kan shi kenan. Gani yayi ta motsa tare da dafe cikinta yayinda tayi squeezing fuskar ta kamar zata yi kuka. Ajiyar zuciya yayi yace “hey wake up? Me kike yi kwance a qasa?” a razane ta bude idanuwan ta tana kallon shi. hararar ta yayi yace “tashi ki koma kan gado” girgiza kai tayi tace “Ya Farouq na fi son nan” kallon da ya mata ne yasa ta miqe babu shiri ta koma kan gado ta shige bargon ta.1 Dawowa yayi kusa da ita yace “me ke damun ki?” idanuwan ta a rufe tace “ba komai Ya Farouq” yace “qarya kike” cikin shgwaba tace “don Allah kayi haquri” Ran shi a bace yace “idan baki fada mun ba sai nayi miki Allurai guda goma yanzun nan, kin dai san I am not bluffing” A razane ta bude idanuwan ta tace “its my Menstrual pain” kafin ta rufe bakinta yayi tsaki ya juya zai fita, tace “Ya Farouq na gaya maka kuma baka..” kafin ta qarasa maganarta har ya fita abinshi. Ko da ya koma wurin su Abba ce musu yayi tayi bacci amma da alama its nothing serious. Farouq ya miqe yayi musu sai da safe sannan ya tafi. Bai dade da barin gidan bane Larai ta qwanqwaso qofar dakin Zara ta miqa mata saqo daga Farouq. Magani ne hade da prescription. Wayar ta tayi qara ta duba. Text message ne daga Farouq kamar haka: “idan kin ga dama kada ki sha” murmushi tayi ta tura mishi reply. FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION A lokacin da farouq ya iso gida ya tarar da Ruqayya kwance a falonta tana waya, bata ji motsin shigowarshi ba. ji yayi tana fadin “but dai ka san I Love you ko, dagaske I missed you a lot”. Hankalin Farouq ya tashi matuqa yayinda ya kasa motsi, a yanzu dai ya fara tunanin lallai zargin da yake yi ya tabbata gaskiya. Ji yayi ta dan yi shiru kadan sannan tayi dariya tace “insha Allah”. Qamshin turaren shi da ta ji ne ya bata tabbacin lallai Farouq yana cikin falon, aikuwa nan da nan cikin siyasa tayi gyaran murya tace “idan ka dawo Ya Musty yakamata ka zo ka hadu da Honey, okay sai dai mun dawo daga Germany kenan” A can bangaren dai Musty ya zama confused da farko amma dayake dan duniya ne ya fahimci cewa mijinta yana kusa ne don haka ne ya dinga dariyar mugunta. Bayan ta kashe wayar ne ta juyo tace “laaa, Honey ashe ma ka shigo, yanzu Ya Musty yake tambayar ka” Ajiyar zuciya yayi ya matsa kusa da ita yace “sorry i ddnt want to interrupt ne” anan ta rungume shi tana fadin “ya aiki? Hope dai yau bazaka koma ba?” yace “ina da surgery anjima, I am just going to freshen up sai in koma” bata rai tayi tace “gaskiya bazan bari ka tafi ba sai ka sallame ni, jiya ma fa haka ka gudu ka bar ni” Farouq dai mamakin jarabar Ruqayya yake yi. A haka dai cikin siyasa ta janye shi suka wuce daki. Lokacin da ya shirya komawa asibiti tuni Ruqayya tayi bacci. Wayoyin shi ya dauka da makullin motar shi ya fice abin shi. A lokacin da ya shiga motar shi ne ya duba wayar shi inda ya ga reply din Zara kamar haka: “thankyou very much Big brother, I love you” tsaki yayi ya jefar da wayar ya tada motar ya tafi. ************** AL-HUSSAIN MANSION A yau dai ciwon cikin Zara da sauqi sossai domin kuwa tunda ta sha maganin da farouq ya aiko mata ta samu sauqi. Dukda hakan dai qin zuwa makaranta tayi. Tana kwance a daya daga cikin kujerun falonta tana kallon wani series a TV ne Larai tayi sallama ta shigo. Har qasa ta duqa ta gaishe ta sannan tace “Anty Zara wai Mamy tace ki zo ku gaisa da Anty Ruqy” zuciyar ta ce ta buga domin kuwa kwata kwata sau uku ta taba haduwa da Ruqayya shima tun kafin bikin su. Ran ta a bace ta miqe tace “ki ce ma Mamy bacci nake yi” Larai ta zaro ido tace “Anty Zara!!!!” Zara ta Harare ta tace “what? Just do as I say” ta wuce dakin ta yayinda larai take mamakin dalilin da yasa ta ce hakan. Zara dai ko da ta koma dakinta kasa zama tayi, sai zage zage take yi wanda bata san dalili ba, ita ta rasa dalilin da yasa bata son ganin Ruqayya. Daga qarshe ma komawa tayi ta haye gadonta ta qirqiro baccin dole. Har Ruqayya ta bar gidan kuwa Zara bata fito ba. Dadaddare Zara tana kwance a kan cinyar Mamy suna kallon tashar Zee TV. Farouq ya shigo falon. Wurin Mamyn shi ya nufa ya duqa yayi mata kiss a goshi yace “Hello Beautiful” kafin Mamy ta amsa ne Zara ta dago kanta tace “Ya Farouq, ni fa?” ko kallonta bai yi ba ya koma kujera nesa da su ya zauna yayinda Mamy take dariya tace “Zara hoo, daga yau dai sai nan da wata shidda kuma” cikin rashin fahimta Zara ta tashi zaune tace “ban gane ba Mamy” Mamy tayi dariya tace “Farouq din bai fada miki ba?” Da sauri ta kalli Farouq wanda hankalin shi yake kan wayar shi tace “Mamy tell me” Mamy tace “gobe zasu tafi Germany shi da Ruqayya, they will be there for 6 months”. Da qarfi tace “what??!!” har sai da Farouq ya dago cikin mamaki yana kallon ta. A yanzu itama shi take kallo, Ji tayi kawai idanuwan ta sun cika da hawaye har suna nema su gangaro. Da sauri ta miqe zata tafi dakinta Mamy cikin mamaki ta riqo hannun ta tace “Zara what is it?” Farouq dai kallon su yake yi ba tare da ya san abinda yake faruwa ba. Juyowa tayi ta kalli Mamy tace “Nothing Mamy, good night” ta wuce dakinta. Farouq ya kalli Mamy yace “what’s wrong with her? Ciwon cikin ne?” Mamy tayi murmushi tace “dama baka fada mata zaka tafi Germany ba?” Cikin mamaki yace “does that have to do with what just happened?” Mamy tayi murmushi tace “Farouq stop pretending kamar baka san halin Zara ba, ka fi kowa sanin yadda ta damu da kai. Knowing cewa daga gobe bazata qara ganin ka har tsawon wata shidda ba is not going to be easy for her” Farouq ya girgiza kai yace “toh Mamy wai fasa tafiyar zanyi saboda Zara ko me?”murmushi tayi tace “ba haka nake nufi ba amma please ina roqon ka for once ka je kuyi sallama, if possible make her feel you care about her, ina so ta samu memory mai kyau akan ka for the next six months” Farouq ya kalli agogon hannun shi yace “I guess it was a mistake coming after all” murmushi Mamy tayi tace “its not my Prince, just do me this favour, just for today please” miqewa yayi yace “toh Mamy, as you wish”. Bayan Farouq ya tafi dakin Zara ne Mamy tayi murmushi. STORY CONTINUES BELOW Kwance take a kan gadonta ruf da ciki tana kuka. Idan zaka shaqe Zara bazata iya gaya maka ainihin dalilin da yasa take kuka ba. Na daya dai ba yau Farouq ya saba tafiya ya dade ba balle, lokacin da yake makaranta ai qarshen shekara yake zuwa hutu kuma idan zai koma hankalin ta bai taba tashi ba kamar na yau, toh meyasa?? Qwanqwaso qofar ta yayi kamar kullum sannan ya shiga, matsawa yayi ya zauna bisa stool din dressing mirror dinta yayinda ya cigaba da latsa wayar shi. Zara da take a kwance ta ji shigowar shi, tun tana sa ran zata ji yayi Magana har dai ta gaji ta dago fuskar ta wadda tayi ja. Dago kai yayi ya kalle ta wanda har yayi mamaki amma bai nuna ba ya murtuke fuska yace “go and wash your face ki zo mu yi Magana” da sauri ta sauka daga kan gadon ta wuce bathroom dinta yayinda ya bi ta da kallo. Bayan ta fito ne ta koma kan gadonta ta zauna tana kallon shi. Shima kallonta yake yi yace “are you crying saboda ban fada miki cewa zanyi tafiya ba?” da sauri ta sauko ta koma kusa da shi tayi kneel down tace “don Allah Ya Farouq kada ka tafi” yace “why?” ba tare da tunanin komai ba tace “because I am going to miss you”. Farouq dai shiru yayi yana kallon ta, a ran shi ne yake fadin “does she care about me this much?” Miqewa yayi yace “shirya mu je, I will be waiting for you in the car” cikin mamaki Zara ta miqe tace “Ya Farouq, ina zamu je?” a lokacin har ya kai qofa yace “idan baza ki je ba yi zaman ki” murmushi tayi tace “sorry big brother” yayinda ta ruga ta nufi closet dinta. Zaune yake a cikin motar shi inda yayi shiru yana tunanin Zara. Meyasa duk yadda ya so ya daina kula ta he ends up stuck with her?? Zara ce ta fito daga cikin gida sanye cikin pencil jeans da wata farar long top sai wani gyale dan qarami da ta yafa a kanta. Tafe take fuskar ta dauke da fara’a kamar ba ita bace ta ci kuka dazu. Tana shiga motar ta kalle shi tana murmushi tace “sorry Ya Farouq na tsaya canza kaya ne, na yi kyau?” ko kallonta bai yi ba ya tada motar yayinda ta turo baki. **************** Suna tafe a cikin motar ne tace “toh wai Ya Farouq tare da Anty Ruqy zaka je?” ya girgiza mata kai alamar eh. Bata rai tayi tace “toh ita me zata je yi a can? Ba aiki zaka je yi ba?” cikin mamaki ya dan kalli fuskar Zara har a ranshi yana fadin “what is wrong with this girl?” kafin ya ba kanshi amsa tace “God knows that I will miss you” daga nan kuma sai tayi shiru. Frozenscoops ta ga ya shiga ya faka. Ihu tayi cikin murna tace “thank you very much Ya Farouq” kafin yayi Magana har ta bude qofarta ta fito. Bayan ya fito ne suka shiga wurin. Security din wurin ne yana ganin Zara ya fara murmushi yace “Hajiya welcome” tana murmushi tace “thank you” ya kalli Farouq wanda yake biye da ita yace “oga welcome” Farouq ya daga mishi hannu. Bayan sun shiga ne suka nufi wurin da ake siyar da ice cream, wanda ke wurin ne ya kalli Zara da Farouq yana murmushi yace “Madam Good evening, you came with your husband today” Zara ta zaro ido tare da kallon Farouq wanda ya murtuke fuska sannan ta matsa kusa da Farouq ta riqo hannun shi tace “Yes Steve, meet my baby…” kafin ta rufe bakinta Farouq fizge hannun shi yace “are you…” da sauri ta qara matsawa kusa da shi sossai, ahankali tace “sorry Ya Farouq, ai dai ka san wasa nake” STORY CONTINUES BELOW  Mutumin dai Kallon Farouq yayi yace “you both make a beautiful couple” Zara tana dariya tace “wow, thank you soo much steve” yayin da Farouq ya Harare ta. Bayan Steve ya hada ma Zara abubuwan da take so ne Farouq ya biya sannan suka fito. A cikin mota ne Zara ta bude ice cream tana sha, kallon shi tayi tace “Ya Farouq are you going to miss me?” kai tsaye yace “No” Cikin damuwa tace “wai Ya Farouq meyasa baka damu da ni bane? Is it that you don’t like me?” Farouq dai ya fara gajiya da tambayoyin Zara domin kuwa ta fara neman kure shi. Wayar shi ce tayi ringing ya amsa. daga asibiti ne inda ake buqatar shi cikin gaggawa. Ita dai Zara gani tayi ya dauki hanyar zuwa asibitin shi. CENTRAL HOSPITAL Ko da suka isa tare suka shiga inda Zara ta tsaya gaisawa da wasu Nurses yayinda yayi gaba abinshi. Nurses din asibitin Farouq suna son Zara domin kuwa tana da son mutane. Daga nan kai tsaye ofis din Farouq ta nufa. Ko da ta shiga baya nan amma wayoyin shi suna nan akan tebir din shi. bata Ankara ba ta ji daya daga cikin wayoyin na ringing. Da sauri ta qarasa wurin wayar sai ta ga “wifey”, tsaki tayi tace “fitinaniya, kina ta damun shi da waya bayan tare da ke zai tafi Germany din”. Haka Ruqayya tayi ta kiran wayar babu amsa. Da Zara ta ga kiran yayi yawa ne yasa tace “bari ma in amsa in ji wannan nacin kiran na meye” aikuwa tana amsawa Ruqayya tace “hello Honey, kana ina ne gani nan ina ta jiran ka?” Zara tace “Hello Wifey din Big Brother, how are you? Dazu kin zo gida ina bacci” Cikin mamaki Ruqayya ta bi wayar ta da ido sannan ta mayar a kunnenta tace “Zara???!” Zara tayi murmushin mugunta tace “Na’am Anty Ruqy” cikin qunar rai Ruqayya tace “ina Farouq yake?” Zara tace “Honey? Yana duba patients dinshi idan ya dawo zan fada mishi kin kira” Zara dai bata tsaya jin abinda Ruqayya zata fadi ba ta kashe. Zama tayi dafe da qirjinta tana sauke numfashi tare da fadin “mayya kawai” can kuma tace “why do you care Zara?” tsaki tayi sannan ta dauki daya daga cikin wayoyin shi tana dubawa. Farouq ya shigo ofis din shi ya tarar da Zara zaune bisa kujerar shi tana ta latsa wayar shi. cikin fada ne yace “me kike yi da waya ta?” murmushi tayi tace “ba komai Ya Farouq, kawai na dauka ne” ta miqe tace “ka gama ne mu tafi gida?” ba tare da ya amsa ta ba ya kwashe wayoyin shi da makullin mota ya fita yayinda ta bi shi. AL-HUSSAIN MANSION Ko da ya dawo da Zara gida tare suka shiga har sashen Abba inda suka tarar da su a falon Abban suna ta hira harda Sadiq. Abba ne yace “My Princess kin je yawo da yayan ki ne?” murmushi tayi ta koma kusa da Abba ta zauna tace “Yes Abba, Ya Farouq ya kaini favourite ice cream spot dina” Sadiq ne yace “amma dai an cuce ni, shine ko ki fada mun in biyo ku nima” Zara tayi mishi gwalo yayinda Mamy ta kalli Farouq wanda yake zaune kusa da ita tace “thankyou my Prince”, murmushi yayi. Farouq yayi ma iyayen shi sallama yayinda suka dinga yi mishi fatan alkhairi. Har mota Zara da Sadiq suka raka shi inda Zara ta dinga share hawaye. Farouq ya kula da hakan amma sai ya nuna kamar bai gani ba, wannan ne ya sa bai bata lokaci ba ya tada motar shi yayi tafiyar shi. Har lokacin da maigadi ya rufe gate Zara tana nan tsaye tana kuka, Sadiq ne ya janyo ta yace “hey Princess, why are you even crying? Ya Farouq ne fa. Bari in gani idan zan koma school zakiyi kuka haka ko kuwa” Zara tana kuka tace “bazaka gane bane Ya Sadiq” Sadiq yace “make me understand” juyawa tayi ta nufi cikin gida yayinda ya bi ta yana lallashin ta. FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION Farouq ya shiga gida ya tarar da Ruqayya zaune a daya daga cikin falukan shi tana jiran shi. fuskar ta a murtuke take yayinda take ta jijiga qafar ta. Ruqayya tana ganin shi ta miqe cikin tsiwa da fada tace “ina ka baro karuwar yarinyar?” cikin mamaki Farouq yace “what?!” Tayi murmushin takaici tace “na kira wayar ka Zara ta dauka, me hakan yake nufi?” Yace “it means she was with me lokacin da kika kira” cikin mamakin amsar da ya bata tace “kuma kana tunanin hakan ba wani abu bane?” Dakin shi ya shige yayinda ta bi shi a baya tana fadin “idan har son yarinyar nan kake meyasa baka aure ta ba? wannan ai wulaqanci ne”. Da surutun ta yayi mishi yawa a kunne ne ya daga mata hannu yace “lower your tone Ruqayya” cikin tsiwa tace “and if I don’t?” Yana cire agogon hannun shi yace “before I explain myself zaki iya gaya mun who you slept with kafin in aure ki????” Cikin razana Ruqayya ta kalle shi yayinda ya wuce ya shiga dressing room dinshi.1 ************

Post a Comment for "BA SONTA NAKE BA CHAPTER 2"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...