Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BA SONTA NAKE BA CHAPTER 14

BA SONTA NAKE BA CHAPTER 14

- - Post a Comment
BA SONTA NAKE BA CHAPTER 14
Washegari wuraren qarfe bakwai na safe ne Farouq ya shigo dakin Zara dayake bayan ya dawo daga masallaci da asuba dakin shi ya wuce.+ Har yanzu dai Zara bacci take yi. Zama yayi gefen ta a kan gadon yayinda ya zuba mata idanuwa yana murmushi. Gani nayi ya matsa tare da hura mata iska a fuskar ta yace “hey sleeping beauty wake up” Zara ta dan motsa tare da bude idanuwanta. Aikuwa tana hada ido da Farouq sai na ga tayi saurin shigewa cikin bargonta. Dariya ma ta bashi sossai yayinda ya qara matsawa daf da ita yace “haba Baby angel, meye haka kuma? Kunya na kike ji?” Zara dai tana nan a cikin bargo yayinda ta kasa Magana. Ita dai kunyar Farouq take ji musamman da ta tuna abinda suka yi jiya. Ji tayi yace “tashi mu je in taimaka miki kiyi wanka, kin ga baki yi sallah ba ma” A rude tace “please No ya Farouq i beg you..” cikin rashin fahimta yace “why?” can kuma sai na ga yayi murmushi yace “wai dagaske kunya kike ji? Toh wai ba na ga komai ba?” Cikin shagwaba Zara tace “na shiga uku, ni ka bari zan yi da kaina please” Hannu ya sa ya janye bargon da ta rufe fuskar ta da shi yace “okay my Baby angel” idanuwan Zara dai a rufe suke yayinda ya duqo yayi mata kiss a baki sannan ya miqe ya fita daga dakin yana yi mata dariya. Farouq yana fita ne Zara ta tashi zaune. Da qyar ta lallaba ta shiga bathroom dinta. Ruwan zafin ma kasa shiga tayi, sama sama dai ta dan gasa jikinta sannan tayi wanka kamar yadda addinin mu ya tanada. Zara dai ko da ta fito bata wani zauna gaban madubi ba, spray kawai ta fesa a jikinta. Wata doguwar sleeveless gown marar nauyi ta sanya sannan ta fesa turaruka, nan da nan ta dauki qamshi. Bayan ta idar da sallah ne ta dauki wayarta ta fita. Tura qofar dakin shi tayi kamar kullum ba tare da tayi sallama ba. Ko da ta shiga ganin shi tayi kwance a kan gadonshi, idanuwan shi a rufe wanda ya tabbatar mata da bacci yake yi. Ahankali ta qaraso wurin shi ta zauna daf da shi tana kallon shi. Gani nayi tayi murmushi tare da duqowa tayi mishi kiss a goshi, ta qara yi mishi wani a kumatu sannan tayi mishi a baki. Ji tayi yace “thank you baby angel, I love you” Zaro idanuwa tayi ta miqe zata gudu, da sauri ya bude idanuwan shi ya riqo hannunta tare da janyota ta fado jikin shi yace “ina zaki je?” Idanuwanta a rufe tace “dama ba bacci kake yi ba?” murmushi yayi yace “ta ya zanyi bacci bayan kin haukata ni” Bude idanuwan ta tayi cikin rashin fahimta tace “ban gane ba ya Farouq, me nayi maka kuma?” Murmushi yayi yace “I just can’t forget the beautiful moment we shared together yesterday” Itama tana murmushi tace “Me too Ya Farouq” yace “toh ko mu cigaba daga inda muka tsaya ne?” Gani nayi ta zaro idanuwa tare da ture shi tace “don Allah kayi haquri, har yanzu fa ina jin zafi..” kafin ta qarasa yace “subhanalillah, let me see..” Da sauri ta matsa muryar ta na rawa tace “me zaka gani? Don Allah Ya Farouq kayi haquri” girgiza kai yayi yana murmushi yace “toh wai meye ne kike boyewa wanda ban gani ba?” STORY CONTINUES BELOW Daga nan kuwa sai na ga yana qoqarin dubawa yayinda ita kuma Zara take ta kaucewa tana ture shi. Dayake dai qarfin su ba daya ba tuni Zara ta gaji ta haqura yayinda ta janyo pillow ta rufe fuskar ta. Bayan kuwa ya duba ne na ga ya sauka daga kan gadon ya wuce bathroom din shi. Can kuma sai na ga ya fito ya hau kan gadon ya zare pillow din da ta rufe fuskarta da shi ya dauke ta tare da fadin “you surely need this don haka ki natsu” Zara dai tana ji tana gani Farouq ya mayar da ita cikin ruwan zafi wanda ta dinga zabga mishi ihu. Dukda kuwa ta bashi tausayi bai nuna hakan ba domin kuwa ya sani sarai idan ya nuna tausayawa qin zama zata yi. Farouq dai bai fiddo Zara ba sai da ya tabbatar ta zama normal. Bayan yayi wrapping dinta da towel dinshi bai ajiye ta ko’ina ba sai kan gadon shi. Zama yayi gefenta yace “I am sorry my baby angel” murmushi tayi tace “thank you Ya Farouq, I am feeling much better” Miqewa yayi ya shiga dressing room dinshi ya dauko wata shirt dinshi ya fito ya dawo ya zauna a kan gadon yace “wear this kafin ki koma dakin ki” shi ya saka mata da kanshi sannan ya gyara mata pillow yace “kwanta ki huta let me go get you something to eat” Zara ta zaro idanuwa cikin mamaki tace “what?” Ya Harare ta tare da fadin “shut up, just wait for me” Zara ta fashe da dariya ta kwanta akan pillow tace “sorry, I love you” murmushi yayi ya fita. Zara dai tana nan kwance Farouq ya shigo riqe da tray a hannun shi. Simple toast ne wanda yayi garnishing da straw berry sai fresh milk. Tana ganin shi ta tashi zaune tana murmushi yayinda ya ajiye tray din a gaban ta sannan ya zauna. Kallonta yayi yace “manage this Baby angel, its all I can produce” tana murmushi tace “come here” ya matsa kusa da ita tayi hugging dinshi tare da yi mishi kiss tace “having you prepare breakfast for me alone gives me joy Ya Farouq. Please feed me, I am starving” Murmushi yayi sannan ya fara bata a baki. Zara tana kallon shi cikin shagwaba tace “please stay with me for the rest of today, will you?” Kafin yayi magana ne kuwa wayar shi ta fara Ringing. Ko da ya amsa daga asibiti ne inda aka yi mishi tuni akan surgery din da zai yi a yau din. A lokacin da yake wayar kuwa kallonta yake yi yayinda itama ta sa mishi ido ranta a bace domin kuwa ta sani sarai daga asibiti ne. Bayan ya gama wayar ne yace “I am sorry my Baby angel, I have to go amma I promise to return as soon as I am done” gani nayi ta turo baki tace “toh wai kai kadai ne surgeon a asibitin? Sauran fa?” Matsawa yayi ya rungume ta yace “yi haquri baby angel, kin san cewa saving lives is my priority as a doctor, I wouldn’t want to risk people’s lives” Cikin shagwaba tace “toh ni dai kana gamawa ka dawo” yace “Yes Ma” yayinda yayi mata kiss a kumatu. Zara dai tana kallon shi ya shirya ya tafi ya barta. Bayan ya fita ne na ga ta sauka daga kan gadon ta nufi wurin window ta tsaya tana kallon shi a harabar gidan yayinda take murmushi. Zara dai a rayuwarta tun asali Farouq yana bala'in birge ta balle kuma yanzu da ya zama mijinta wanda take mutuwar so. A yadda ta ga yana Magana da daya daga cikin masu aikin gidan mai suna Habibu ne ta tabbatar fada yake yi. Da sauri ta dawo ta dauki wayarta wadda ta ajiye a kan side drawer ta koma wurin window din ta kira shi. STORY CONTINUES BELOW Gani nayi ya fiddo wayar ya duba yayinda yayi ma Habibu alama da ya koma bakin aikin shi, murmushi yayi sannan ya amsa tare da fadin “Baby angel ya akayi ne? are you missing me already?” Murmushi tayi tace “I started missing you the moment you stepped out of this room” Murmushi na ga yayi yayinda ta cigaba da fadin “Me Habibu yayi maka ne na ga kana ta yi mishi fada?” Gani nayi Farouq ya dago kan shi da sauri ya hangota ta window din dakin shi sannan ya girgiza kai tare da yin murmushi yace “he didn’t wash my black Mercedes benz kuma da ita nake so in fita” Zara tace “kayi mishi haquri, take the white Audi that’s beside it, ina son motar” Murmushi yayi yace “an gama my baby angel, I feel like coming back inyi ta kissing dinki all day long” dariya tayi tace “toh hurry up and save a life, I will be waiting for you” A haka dai Farouq ya bar gidan yana ta hira da Zara a waya. Sai da ya shiga asibitin ne suka yi sallama. ************ Wasa wasa kuwa surgery din ya zo ma su Farouq da gardama. Kusan ma an fidda rai akan patient din wanda dai a qarshe da taimakon Allah aikin ya zama success. Gaba daya kuwa daga Farouq har team din shi a gajiye suka fito daga surgery din, wannan yana daga cikin complicated Surgery din da ya taba yi a rayuwar shi. Ko da ya dawo daga sallan Isha'i wayoyin shi kawai ya dauka da makullin motar shi ya fita. Da ya duba wayar shi kuwa missed calls din Zara da ya gani sun fi hamsin banda text messages wadanda suka nuna alamar tayi fushi da shi. Ajiyar zuciya yayi tare da fadin “I am in trouble” FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION (GIDAN ZARA) Farouq dai ko da ya shigo gida kai tsaye sashen shi ya nufa yayi wanka sannan ya nufi sashen Zara. Qwanqwasa qofar dakinta yayi ya shiga, ganin ta yayi kwance a cikin bargo. Girgiza kai yayi ya qarasa wurinta ya shige bargon tare da rungumeta, yana shirin yi mata kiss ne ya ga hawaye na bin fuskarta. Da sauri ya juyo ta saitin shi yace “subhanalillah, Baby angel are you crying?” Fashewa tayi da kuka yayinda ya rungume ta yana fadin “I am sorry, an samu complication ne infact I almost lost the patient” Zara dai har yanzu bata ce mishi komai ba. Ji nayi yace “hey please forgive me, I love you unconditionally” Ji nayi tace “Ni fa bazan iya zama for long without seeing or hearing from you ba, I called you so many times you didn’t pick, you didn't reply my...” qara matse ta yayi jikin shi yace “I am sorry it wont happen again, kiyi haquri kin ji?” Da qyar dai ya lallabata ta haqura. A yanzu kuwa Farouq ya tabbatar zasu samu matsala a duk lokacin da zai koma gidan Ruqayya. Tana nan maqale a jikinshi ne tace “ka ci abinci?” ya girgiza mata kai alamar a’a. Tashi tayi zaune tace “Na shiga uku, Gashi ban dafa komai ba" ta harare shi tace "Duk laifinka ne, I couldn’t do anything throughout today” Shi dai Farouq kallonta kawai yake yi yana murmushi. Duk abinda Zara tayi birge shi take yi, hatta surutun ta ma yanzu so yake yi. Hannun shi ta riqo tace “Mu je ka raka ni in dafa wani abu sharp sharp, nima yunwa nake ji” Tare suka shiga kicin din yayinda ya zauna yana ta kallon ta. Zara ta dade tana ta hidimar abincin ne ta Ji yace “what can I do to help?” Juyowa tayi cikin mamaki ta nuna shi tare da fadin "you??" Ya harare ta yace "ofcourse, what??" Tana murmushi ta girgiza kai tace “do you really want to help?” ya miqe tare da fadin “yes Baby angel, bana so kina wahala” tace “okay, If you insist” Gani nayi ta miqo mishi albasa da wuqa tare da chopping board tace “bissimillah” aikuwa ba tare da tunanin komai ba Farouq ya dauki wuqa. Zara dai bata ankara ba sai ta ga hawaye yana ta gangarowa daga idanuwan shi wanda kuwa tun yana daurewa har ya jefar da wuqan yace “oouch, my eyes” Zara kuwa me zata yi banda dariya. Qarasawa tayi wurinshi ta sa hannu tana ta goge mishi tare da fadin “sorry Ya Farouq” ji tayi yace “ai da gangan kika bani, please help me kar in makance” Zara ta sake fashewa da dariya ta janyo shi ya zauna akan daya daga cikin kujerun Kitchen Island sannan tace “I am coming” Gani nayi ta bude wani drawer ta dauko wani sabon hand towel sannan ta debo ruwa mai sanyi ta dawo gaban shi yayinda take dariya tana fadin “sorry Ya Farouq, you said you wanted to help” ya bata rai tare da fadin “not like this” ta dinga yi mishi dariya. Daga nan ta fara goge mishi idanuwan shi da damped towel din wanda Gradually kuwa ya fara samun sauqi. Zara bata ankara ba ta ga ya karbi towel din daga hannunta ya jefar a gefe tare da janyo ta bisa cinyar shi yayi mata kiss sannan yace “thank you my little doctor, I love you like crazy” murmushi tayi tare da jan gemun shi tace “I love you too” daga nan kuma sai suka fada wata duniyar. Basu ankara ba sai suka ji qauri alaman lallai abinci ya qone. A razane Zara ta miqe ta nufi wurin abincin tana fadin “na shiga uku Ya Farouq ka sa abinci na ya qone, ban taba qona abinci ba a rayuwa ta” Farouq kuwa yana zaune yana ta yi mata dariya. Zara ta cigaba da fadin “duk laifin ka ne” yana dariya ne yace “laifin ki dai My Baby Angel, manta komai nake yi idan kina kusa da ni” Gani nayi Zara ta tsaya tana kallon abincin yayinda Farouq ya taso ya zagayo ta bayan ta yana leqen tukunyar. Girgiza kai yayi yace “this is bad” rungume ta yayi ta baya yace “hey I am sorry” yayi mata kiss yace “lets get something else” A taqaice dai Rice krispies suka sha wanda ita Zara ta so ta sake dafa wani abincin amma kuma Farouq ya hana ta a dalilin baya so ta wahala gashi kuma dare yayi sossai. ************* Hmmm.. lallai akwai matsala! Ni dai ban ga ana haka a gidan Madam Ruqs ba🤔 13 Anya adalcin nan zai yiwu kuwa???2 Toh wai tana ma ina ne??? Ina fans din Madam Ruqs??? Muna cigiya abeg🤣2 *********** FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION (GIDAN ZARA) Da safe Farouq yana cikin Power Rack machine a Gym dinshi inda yake working out. Zara ce ta shigo riqe da Mug na moringa Tea tana sha. Zama tayi a kan leg curl machine yayinda ta sa mishi ido. Tunda ta zauna kuwa six pack abs din shi take kallo tana murmushi. Tsawon lokaci Zara tana nan zaune tana ta kallon shi. Gani nayi ya fito daga Rack din ya nufo wurinta ya zauna a gefenta yace “hey, what are you staring at” tana murmushi tace “nothing” Mug din da yake hannun ta ya karba ya kai bakin shi ya sha sannan yace “do you have a crush on my abs?” tana murmushi tace “Ya Farouq I love it” dariya yayi yace “Na dade da sanin hakan my baby angel, its all yours” Zara tayi mishi kiss a kumatu yayinda tace “Ya Farouq in tambaye ka?” Ya shafa fuskarta yace “Go ahead my Baby angel” tana kallon shi tace “tsakanin ni da Anty Ruqy wa ka fi so?” Cikin mamaki Farouq yake kallonta, bai yi zaton zata yi mishi irin wannan tambayar ba. Shiru ya dan yi sannan yace “I love you both My Angel” gani nayi ta kwantar da kanta a kan kafadarshi yayinda ta bata rai tace “toh Ya Farouq ka fada mun abinda zanyi maka da zai sa ka fi so na” Wannan karon dai dariya yayi sannan ya janyo ta ya zaunar da ita a kan cinyar shi yace “hey Baby angel, you don’t have to do anything, I love you unconditionally” ya ja mata hanci yace “I see perfection in you my dearest” Turo baki tayi tace “ni na fi so ka so ni fiye da ita Ya Farouq” yana murmushi yace “I love it when you get all jealous, tashi mu je ki raka ni inyi wanka, I have worked out enough for today” Tare suka fita daga Gym din suka wuce sashen shi. Sanin cewa a yau Farouq zai bar gidanta ne yasa duk ta birkice, gaba daya Zara bata jin dadi dukda kuwa a yau Farouq bai je asibiti ba throughout, asali ma close marking ta dinga bashi domin kuwa duk inda ya shiga sai ta bi shi. Farouq dai ya riga ya hango rikici ganin yadda Zara ta bashi close marking. Yinin yau kuwa maqale suke da juna suna ta buga soyayya kala kala. Ko da ya tashi tafiya lallashin ta yayi akan zai je asibiti wanda sai ya dawo ne sannan zai tafi gidan Ruqayya. A hakan ta haqura ta bar shi ya tafi. Aikuwa ko da ya tafi bai dawo ba. Zara dai haka ta zauna tana ta jiran Farouq, tana sa ran zai dawo Kamar yadda yayi mata alqawarin dawowa. *********** Kwance take a kan gadon dakin shi tana ta jiran shi. A haka kuwa tun tana gyangyadi har bacci ya kwashe ta. Wuraren qarfe daya na dare ta farka don gani ko ya dawo amma bata gan shi ba. Gani nayi ta tashi zaune cikin damuwa ta dauko wayarta ta kira shi. Zara dai haka ta dinga kiran shi a waya amma shiru Farouq bai amsa ba. Haka ta kwana tana kewar shi yayinda baqin kishi yake ta ratsa ta sanin cewa yana can tare da Ruqayya. *********** A lokacin kuwa yana can tare da Ruqayya wadda take kwance a jikin shi tana bacci. Farouq dai ko da ya farka ya ji wayar shi tana ringing, janyo ta yayi ya duba ya ga sunan Zara. STORY CONTINUES BELOW Girgiza kai yayi ya mayar da wayar silent sannan ya ajiye. A ranshi ne yake fadin “I really miss you too my Baby angel” CENTRAL HOSPITAL Washegari da safe zaune yake a ofis din Dr. Ibrahim inda yake duba wasu files na wata patient da zai yi ma surgery a yau din. Sanin cewar lallai Zara zata iya zuwa asibitin neman shi ne yasa ya boye a ofis din Dr. Ibrahim din. Zara ce ta shigo harabar asibitin inda ta faka motar ta. Kamar kullum kuwa tana tafe yayinda take amsa gaisuwar ma’aikatan asibitin dukda kuwa fuskarta ta nuna cewa tana cikin tsananin damuwa. Tunda Zara ta shiga asibitn Farouq ya gan ta a dalilin na’urar CCTV da take maqale a ko wanne lungu na asibitin. File din da yake hannun shi ya ajiye yayinda ya sa mata ido. Hijabi ne dogo a jikinta amma fa tayi masifar kyau dukda kuwa fuskarta a yamutse take. Girgiza kai yayi yana murmushi yace “she is trouble I swear” Secretary din Farouq ce ta gaishe ta wanda bata bi ta kanta ba ta wuce qofar shi kai tsaye. Jin qofar a rufe ne yasa ta dawo wurin secretary din tace “where is he?” Secretary din tace “uhm, bari in duba” gani nayi tana duba system din da yake gaban ta don neman inda Farouq yake. Ji suka yi wayar intercom na Secretary din tana ringing, Ko da ta amsa wayar Farouq ne yace “don’t mention my name, tell her cewa na fita” Secretary din tace “okay” Bayan ta ajiye wayar ne ta dan duba system din sannan ta dago tace “ban gan shi ba fa Anty Zara, I think ya fita kenan” gani nayi Zara ta runtse idanuwan ta tare da fadin “yau na shiga uku, Ya Farouq where are you?” Dr. Ibrahim wanda ya fito daga wani ofis zai nufi ofis dinshi ne ya hango Zara a tsaye, qarasawa yayi wurinta cikin fara’a yace “madam sannu da zuwa, ya na gan ki a tsaye?” Zara ce tace “don Allah ina Ya Farouq yake?” Dr. Ibrahim wanda ya sani sarai Farouq din ya boye a ofis dinshi ne don kar Zara ta gan shi yace “Uhm ya tafi wani emergency case a wani asibiti, gashi kuma ban san sunan asibitin ba domin kuwa kiran gaggawa aka yi mishi....” Ran Zara a bace tace “shikenan Dr. Ibrahim, na gode” haka dai Zara ta juya ta fita daga asibitin yayinda zuciyarta take tafasa. Farouq wanda yake zaune yana kallon ta duk ya bi ya damu. Ji yayi kamar ya fita ya same ta amma sanin cewar zai samu matsala da ita ne ya haqura. Haka kuwa Zara ta dinga kiran shi a waya yinin ranar amma bai amsa ba, text messages kuwa har ya gaji da karantawa. FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION (GIDAN RUQAYYA) Zaune suke a kan dinning suna dinner. Wayar Farouq ce ta fara ringing, ko da ya duba dai sunan Zara ya gani. Ba tare da ya bi ta kan wayar ba ya cigaba da cin abincin shi. Ruqayya ce tace “Honey bazaka amsa wayar bane?” murmushi yayi yace “yeah its not important” Gani nayi ya ajiye cokalin da yake hannun shi sannan ya kalle ta yace “wai cousin dinki bai dawo bane har yanzu?” Ruqayya wadda cokali ya kufce mata a dalilin razana da tayi ne tayi gyaran murya tace “ehm.. bai dawo ba Honey, ai idan ya dawo zai zo ku gaisa” Yace “toh Allah ya dawo da shi lafiya” Bayan sun gama dinner ne Farouq ya wuce sashen shi yayinda Ruqayya ta nufi wurin Nanny din Junior don duba shi. *********** Wuraren qarfe tara da rabi ne na ga an bude gate din gidan Farouq. Ko da na leqa motar Zara na gani tana shigowa gidan.1 STORY CONTINUES BELOW Bayan driver yayi parking ne na ga Zara ta fito daga motar. Sanye take cikin doguwar jallabiya yayinda ta yafa gyalen a kanta. Fuskar ta kuwa cikin tsananin damuwa. A lokacin da ta shiga gidan babu kowa a babban falon gidan don haka kai tsaye sashen shi ta nufa. Ba tare da ta qwanqwasa qofar dakin shi ba ta shiga. Farouq yana bathroom dinshi a lokacin da ta shiga. Jin alamun motsin shi a cikin bathroom din ne yasa ta zauna kan gadon shi tana jiran shi. Tsawon minti goma Zara tana zaune tana jiran Farouq ne ta ji motsin fitowar shi. Daure yake da towel yayinda yake riqe da wani dan qaramin towel a hannun shi yana goge gashin kan shi. Farouq dai tunda ya fito yake jin qamshin Zara har a ranshi yana fadin “am I missing her this much da har nake jin qamshin ta?” Bai ankara ba sai ya ji an rungume shi ta baya. Da sauri ya juyo ya ganta a tsaye wanda kafin yayi Magana ta shige jikin shi tace “Ya Farouq meyasa ka gudu ka bar ni, bazan iya zama for long without seeing you ba” Daga nan kuma sai ta fashe da kuka yayinda ta cigaba da fadin “you were not picking my calls, na je asibiti ban gan ka ba. I couldn’t do anything, why did you choose to punish me this way?” Farouq wanda jikin shi yayi sanyi ya ma kasa Magana domin kuwa ya sani sarai idan Ruqayya ta shigo ta samu Zara a nan ba qaramin rigima za’a yi ba. Ganin Zara tana kuka ne ya rungume ta yana fadin “I am sorry my baby angel, ba da son raina bane. kin san cewa yakamata in kamanta adalci a tsakanin ku…” Zara ce ta katse shi tare da fadin “ni gaskiya ya Farouq ka zo mu tafi gidana, ka ga fa ita Anty Ruqy tuntuni kuna tare, ni kuwa..” “Me zan gani??!!” muryar Ruqayya suka ji. Gaba dayan su suka juyo suna kallon ta. Zara wadda take maqale a jikin Farouq ne tace “kiyi haquri please..” Ruqayya ce ta qaraso cikin dakin ta dago hannu zata wanka ma Zara mari wanda Farouq yayi saurin riqe hannunta. Farouq yana kallon Ruqayya yace “don’t you ever do that”2 Ruqayya cikin qunar rai ta fizge hannunta sannan tace “can you explain to me me wannan karuwar yarinyar take yi anan?” Da sauri Zara tace “I needed to see him ne Anty...” Ruqayya ce tace “shut up you stupid brat, kwanan ki ne yau da zaki gan shi?” Zara ce ta kalli Farouq tace “Ya Farouq don Allah kayi haquri wallahi bazan iya bacci ba idan ban gan ka ba, i tried amma na kasa..” Farouq ne yace “ssshhhh, relax” Kallon Ruqayya yayi wadda take cike da takaici yace “Wifey please kiyi haquri, kin ga she is far younger than you, she still doesn’t understand some things” Ruqayya tana kallon Farouq cike da mamaki tace “ban gane ba, kana nufin Zara yarinya ce? Hmmm, ai kuwa ta san abinda take yi sarai tunda har ta san dadin miji ta biyo shi cikin dare” Daga nan kuma sai ta fashe da kuka tace "ni wallahi an cuce ni da aka hada ni da wannan 'yar iskar yarinyar a matsayin kishiya, Allah ya isa tsakani na da ke" ta juya ta fita daga dakin da gudu. (Ni kuwa me zanyi banda dariya🤣🤣)+ Bayan ta fita ne Farouq ya kalli Zara wadda jikinta har rawa yake yi saboda tashin hankali. Ajiyar zuciya yayi a ranshi yana fadin “wai dama haka masu mata suke fama? Shi kenan mai guda biyu, toh masu hudu ya suke yi?” (🤣🤣🤣) Hannun Zara ya kamo ya nufi gadon shi da ita yace “sit here, let me dress up and take you home” Zara dai qin zama tayi, bin shi tayi har dressing room din nashi ya shirya sannan suka fito. Farouq bai bi ta kan Ruqayya ba ya ja Zara suka fita daga gidan. Bayan ya sallami driver din da ya kawo Zara ne ya ja ta zuwa motar shi. FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION (GIDAN ZARA) Tana riqe da hannun shi suka shiga gidan. Zama yayi bisa kujerar babban falon gidan yayinda ta haye kan cinyar shi ta kwanta a jikin shi tayi shiru. Ji nayi yace “My Baby Angel” tace “na’am Ya Farouq” yace “what you did was wrong, hope you know?” Fashewa tayi da kuka tace “Ya Farouq don Allah kayi haquri, I didnt know what to do ne, I can’t even sleep neither can I do anything without seeing you, I love you Ya Farouq and I want to be with you each and every single moment” Ajiyar zuciya yayi tare da shafa kanta yace “I love you too my Baby angel, amma kin san I wont be with you every single moment tunda akwai Ruqayya” Ya dan yi shiru sannan yace “Manzon Allah (SAW) yace duk wanda yake da mata biyu kuma yayi favouring daya akan dayar, ranar tashin al-qiyama zai tashi da barin jikin shi a shanye” Ita dai Zara shiru tayi tana tunanin maganar da yayi. Tambayar ta yayi “kina so nima in tashi a hakan?” da sauri ta qara maqalewa a jikin shi tace “a’a Ya Farouq” yace “toh please kiyi haquri kin ji? You will get use to this” Yana murmushi yace “qila ma wata rana gajiya zakiyi da ni ki ce kin bar ma Ruqayya” turo baki tayi tace “wallahi bazan bar mata ba Ya Farouq, I love you so much” Dariya yayi yace “I love you too, yanzu tashi mu je kiyi bacci” Zara dai qin tashi tayi tace “kai zaka dauke ni, kuma a dakin ka zan kwana” murmushi yayi sannan ya dauke ta suka nufi dakin shi. Ko da ya kwantar da ita zama yayi a gefen ta yace “oya sleep” dariya tayi tace “don’t worry Ya Farouq just go, I love you” murmushi yayi ya duqo yayi mata kiss sannan yace “good night my baby angel, I will be with you tomorrow Insha Allah kin ji?” Ta daga mishi kai alamar toh. Tana kallon shi ya tafi amma kuma bata nuna damuwa ba domin kuwa kalaman Farouq sunyi tasiri a zuciyarta.3 (Ni kuwa nace barka🤣) FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION (GIDAN RUQAYYA) A lokacin da Farouq ya shiga gidan Ruqayya tana zaune a kan kujerar dakinta tana ta kuka. Qarasawa yayi kusa da ita ya zauna. Gani nayi ta tashi zata bar mishi dakin wanda yayi saurin riqo hannun ta yace “I am sorry wifey, it wont happen again I promise” Cikin kuka Ruqayya tace “ni ka qyale ni kawai cuta na zaka yi, dama na sani sarai ka fi son wannan yarinyar. Idan ba rashin mutunci ba ya za’a yi ta zo har gida na…” Ji tayi ya rungume ta wanda hakan ya sa ta yin shiru yayinda ta cigaba da kuka. Farouq wanda yake rungume da Ruqayya yace “na sani cewa abinda tayi is wrong kuma bazata qara ba kin ji, I love you” Bakinshi ya kai saitin kunnen ta yace “oya zo mu je dakina in nuna miki wani abu" a haka kuwa ya lallabata har ta haqura ta bi shi. *********** Haka dai zaman nasu ya kasance, Farouq yana iyakar qoqarin shi wurin tabbatar da adalci a tsakanin matan nashi dukda kuwa ya fi jin dadi idan yana gidan Zara domin kuwa ta bala’in shiga ran shi. ************ BAYAN WATA BIYU AL-HUSSAIN MANSION A yau ne su Zara suka zo gidan don duba Mamy wadda ta dan kwanta rashin lafiya.+ Ko da suka yi parking a guje Zara ta shige gidan don ganin Mamy yayinda ta bar Farouq a waje yana Magana da daya daga cikin ma’aikatan gidan. Ta shigo dakin Mamy cikin sallama ta tarar da ita kwance kan gadon ta. Da sauri ta qarasa wurin ta tare da rungume ta tace “Allah sarki Mamy na, how are you feeling?” Mamy tayi murmushi tace “da sauqi Princess, hope you doing good?” tace “I am fine Mamy” Mamy tace “baku gaisa da Ruqayya ba” cikin mamaki Zara ta juya ta ga Ruqayya zaune a kan kujera wadda ta hada rai kamar zata mutu. Zara ta dan Harare ta sannan tace “ina kwana Anty Ruqy” Ruqayya wadda ta mayar mata da harara cike da bacin rai tace “lafiya” Ruqayya dai mamaki take ta yi yadda ta ga Zara duk ta bi ta canza ta qara kyau kamar ba ita ba. Mamy ce tace “ina mayafin ki Princess? Ba dai haka Farouq din ya bar ki kika fito ba?” Gani nayi tana waige waige tare da fadin “wallahi Mamy na fito da gyale, qila ya fadi ne” kafin Mamy tayi Magana ne Farouq da Sadiq suka shigo dakin cikin sallama. Sadiq wanda yake riqe da gyalen Zara ne yace “Hajiya ga gyalen ki nan, I picked it up a bakin qofar falon Mamy” Zara tana murmushi tace “ban ma san ya fadi ba Ya sadiq, thank you” Farouq wanda ya ga Ruqayya zaune ne yace “wifey how are you? Yaushe kika zo?” Ruqayya tayi murmushi tace “tun dazu na zo” Zara kuwa bata rai tayi har a ranta tana fadin "yau ban fito da sa'a ba" (🤣🤣) Farouq ya matsa kusa da Mamy tare da dafa goshin ta yace “Mamy ya jikin?” tace “da sauqi My prince, tun da na sha magungunan da ka bani na samu sauqi” Larai ce tayi sallama ta shigo riqe da Junior, bayan ta gaishe su ne ta nufi wurin Ruqayya zata miqa mata Junior din. Zara ce tace “Larai bani shi, na kwana biyu ban gan shi ba” Larai ta miqa ma Zara sannan ta fita. Zara tana riqe da Junior tana yi mishi wasa ne ta kalli Farouq tace “Ya Farouq Junior da wa yake kama? Na ga baya kama da kai” sai kuma ta kalli Ruqayya tace “sannan baya kama da Anty Ruqy ma, toh wa ya biyo??” (Babbar magana🙄) Jin haka ne yasa hankalin Ruqayya ya tashi wanda yasa tayi saurin dago kai ta kalle su. STORY CONTINUES BELOW Sadiq ne yace “kuma fa haka ne, ban taba kula ba sai yau” Farouq wanda shima ya kula da hakan shiru ya dan yi sannan yace “qila cikin dangin su Wifey ya dauko kamarnin shi” (Hahaha.. ni kuwa nace kalan dangi kenan ko me??🤣) Ruqayya dai zuciyar ta ce take ta bugawa yayinda take ta tsine ma Zara a ranta. Ji suka yi Zara tace “Ya Farouq ni triplets nake so in haifo, duka maza masu kama da kai” Gaba dayan su suka fashe da dariya yayinda Sadiq yace “triplets maza?? Are you okay? Ya zakiyi da su? Ke da idan an biye miki komai ma sai anyi miki” Mamy tace “ai Zara akwai son yara, nasan zata iya kula da su” Farouq yana dariya yace “Allah ya kawo su my Baby angel” gaba daya aka amsa da ameen. Ruqayya ce tayi wani murmushin mugunta a ranta tace “ba sai ta haifo mu gani ba??”3 (Da kyau malamin cotonou🤣)3 *********** Da rana suna zaune a kan dinning harda Abba, Dayake yau Sunday kuma yana gida. Mamy ma ta sauko domin kuwa jikin nata ya warware sossai. Zara wadda take zaune a gefen Farouq tayi murmushi tace “how I missed this moment, yau ga mu harda Abba muna lunch” Abba yayi dariya yace “Nima nayi missing moment dinnan my princess” Sadiq ne ya kalli Zara yace "toh ko zaki dawo ne??" Da sauri Zara ta girgiza kai tare da fadin "Noooo, Ya Sadiq" gaba daya aka yi dariya amma fa banda Ruqayya. Mamy ce tace "wato kin fi son gidan Farouq fiye da nan ko?" Zara tayi murmushi tace "ba haka bane Mamy, i am equally fine a gidan Ya Farouq so there is no need in dawo nan din" Mamy tace "mu zakiyi ma siyasa ko?" Haka suka dinga dariya, Ruqayya kuwa sai hararar Zara take yi. Ko da masu aiki suka yi serving dinsu kowa ya fara cin abincin shi amma banda Zara. Mamy ce ta kalle ta tace “Princess why aren’t you eating? Ko ba kya son abincin ne?” Zara ta kalli Farouq tace “jira nake yi Ya Farouq ya gama cin nashi sannan ya bani da kan shi” maganar Zara ta sa su Abba dariya yayinda Ruqayya ta cika da mamaki. Sadiq ne yace "lallai Ya Farouq ka samu aiki" Farouq yayi murmushi yace "su Mamy ne suka ja mun" yayinda aka cigaba da dariya. Ko da ya fara bata abincin a baki Ruqayya dai sakin baki tayi tana kallon ikon Allah har Sadiq yana fadin “wai a haka ne take fadin zata haifi triplets, ki kula da su ta ya?” Zara ta kalli Sadiq tace “wallahi ya Sadiq zan iya kula da su” su Abba dai sun sha dariya. Dama dai idan ana zaune tare da Zara toh fa haka ake kwasar shirme kala kala. Ganin Ruqayya ta ajiye cokalin ta ne yasa Mamy tace “ya akayi Ruqayya? Ko dai kema jira kike ya baki ne?” Gaba daya suka juyo suna kallon Ruqayya wadda ta qirqiro murmushin dole tace “ko kadan Mamy, ai ni na ci girma” Sadiq ne yace "kin huta Anty Ruqy" STORY CONTINUES BELOW Haka dai aka tashi daga dinning din yayinda matan Farouq suke ta yi ma juna kallon banza. ************* Farouq da Sadiq zaune a babban falon gidan suna hira bayan sun dawo daga sallan magrib. Farouq ne yace “yanzu dai kayi deciding bazaka yi aiki a world bank din ba kenan?” Sadiq yayi murmushi yace “wallahi Ya Farouq na gaji da zaman London din ne, kawai zanyi accepting offer din central bank. Ka ga that way, I will be close to all of you” Farouq yace “eh toh kayi tunani mai kyau, Allah ya taimaka” Sadiq yace "ameen bros" Zara ce ta shigo falon ta qarasa wurin Farouq ta zauna a kan cinyar shi tare da kwanciya a jikin shi kamar mage. Sadiq ne ya Harare ta yace “yanzu duk yawan kujerun da suke falon nan babu inda zaki zauna ne??” Farouq wanda ya rungume Zara ne ya harare shi yace “me ya ruwanka toh? sarkin sa ido” Zara tayi ma Sadiq gwalo yayinda ya girgiza kai yana dariya yace "afuwan Romeo" Zara ce ta hango Ruqayya wadda take shigowa falon. Gani nayi ta fara aika ma Farouq kisses kala kala tana fadin “Ya Farouq I am going to miss you, har bana so shift dina ya qare wallahi” Sadiq wanda ya hango Ruqayya tsaye ne yayi murmushi tare da girgiza kai. Ruqayya kuwa tana nan tsaye yayinda zuciyarta take ta tafasa, ji take yi kamar ta hada rai ta mutu. Ita dai a rayuwarta bata da maqiyar da ta wuce Zara, ji take yi kamar ta shaqeta ta mutu ta huta. Ganin ta juya zata koma ne Zara tace “Anty Ruqy” Gaba dayan su suka mayar da kallonsu gareta yayinda Ruqayya ta juyo tana kallon su. Farouq ne yace “wifey shigo mana” A sanyaye Ruqayya ta shigo yayinda zuciyarta take ta zafi ta zauna a gefen Sadiq tare da qirqiro murmushin dole. Zara ce tace “Ya Farouq tunda yau zaka koma gidan Anty Ruqy ka bar ni in kwana a nan please” Farouq yace “akan wane dalili?” Cikin shagwaba tace “toh ko na koma gida baka nan, kuma ka ga tunda Mamy batada lafiya I want to stay with her for a while” ta birkita gashin kanshi tace “please don’t say no” Murmushi yayi yace “shikenan but gobe zaki koma gida” Sadiq ne yace “zan mayar maka da ita ma Ya Farouq” Ruqayya wadda zuciyarta ta kusa fashewa ta dan yi gyaran murya tace “uhm honey yaushe zamu tafi gida?” Farouq ya kalli agogo yace “bari muyi isha’I sannan” Zara wadda ta dan saci kallonta ne ta Harare ta yayinda itama ta mayar mata da harara. Sadiq kuwa yana ta kallon ikon Allah har yana mamakin yadda Zara ta koyi kishi haka. ************ Bayan sallan isha’I ne su Farouq suka yi ma Mamy sallama. Sadiq da Zara ne suka rako su har wurin mota. Ruqayya wadda take riqe da Junior ta zagaya yayinda Sadiq ya bude mata ta shiga. Farouq ya bude qofar shi kenan Zara ta riqo hannun shi tare da fadin “hey come here, is this how you say good night?” Murmushi yayi sannan ya juyo yayi hugging dinta tare da kai bakin shi saitin kunnen ta yace "i am going to miss you alot" Tana murmushi tace "me too, i love you" yayi mata kiss a kumatu yace "i love you so much more my baby angel" Wannan al'amari dai duk a kan idanuwan Ruqayya ake yi. Zara ta dan leqo Ruqayya tace “Anty Ruqy take care of him for me please”1 (Hahahaha... Zara da tonon rigima🤣) Ruqayya dai yi tayi kamar bata ji Zara ba domin kuwa ta riga ta cika fam da baqin ciki. Shi kuwa Sadiq babu abinda yake yi banda dariya. Murmushi Zara tayi a ranta tace “kadan kika gani” Bayan su Farouq sun bar gidan ne Sadiq ya kalli Zara yace “can you tell me what the show was all about?” Zara ta kalle shi cikin mamaki tace “what show?” Yayi murmushi yace “you think i didn't notice?? kina ta using Ya Farouq kina attacking Anty Ruqy, why?” Zara ta fashe da dariya tace “sannu sa idawa, wato dai baka taba missing abu ko Ya Sadiq??” Sadiq ya fashe da dariya. Zara ta matsa kusa da shi tace “its called strategy Ya sadiq, wallahi bana son Anty Ruqy ko alama, muguwa ce dagaske” Tayi ajiyar zuciya tace “how I wish its just me and Ya Farouq” Sadiq ya girgiza kai yace “toh ai yanzu ma zan iya cewa daga ke sai shi ai” Zara tana dariya tace “tukunna dai ya sadiq” Sadiq yana dariya yace "hmmm, toh me ya rage?? Babes i fear your strategy, you are indeed dangerous" Zara kuwa dariya ta dinga yi. FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION (GIDAN RUQAYYA) Da safe Ruqayya zaune a falonta tana kallon wani series a TV. Wayar ta tayi ringing, ko da ta duba Musty ne yake kiranta. Bayan ta amsa ne Musty yace “hey love, I miss you alot” murmushi tayi tace “wallahi Musty ka zama mun addiction, no matter how hard I try to leave you I just cant” Dariya yayi yace “that’s Musty for you my love, toh ya muke ciki ne? I want to see you” Ruqayya tace “ba dai yau ba gaskiya don Farouq gidana yake plus I don’t want to take chances don zai iya dawowa at any time” Musty ya dan yi ajiyar zuciya yace “well dama I wanted to tell you cewa Mama ta matsa mun akan inyi aure, maganar da muke yi yanzu ma ta samo mun mata kuma har an sa rana..” Ruqayya tace “what??” tsaki Musty yayi yace “toh ba kin qi rabuwa da Farouq din naki ki dawo gare ni ba? why are you even surprised?” Ruqayya ta dan yi shiru sannan tace “hope it won't be the end of us?” Musty yace “not at all my dear, ai ni da ke mutu ka raba”1 ****************

Post a Comment for "BA SONTA NAKE BA CHAPTER 14"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...