Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BA SONTA NAKE BA CHAPTER 13

BA SONTA NAKE BA CHAPTER 13

- - Post a Comment
BA SONTA NAKE BA CHAPTER 13
FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION (GIDAN ZARA) Wuraren qarfe goma na safe Zara ta fito harabar swimming pool din gidan. Tafe take tana ta tunanin shi kamar kullum. A yanzu kuwa ta fara tunanin bazata iya barin gidan Farouq ba saboda ta saba da shi sossai sannan tana bala’in jin dadin zama da shi. Farouq wanda yake working out a Gym dinshi ne ya hango Zara ta Glass wall na Gym din. Dayake ana hango swimming pool area din daga Gym din a dalilin Glass wall da yake bangare daya na Gym din. Wanda yake cikin Gym din yana iya ganin swimming pool area din clearly amma kuwa wanda yake waje baya hangen komai a cikin Gym din sai reflection. Cikin mamaki Farouq ya matsa yana kallonta domin kuwa ya sani sarai Zara bata zuwa swimming pool area don bata iya swimming ba. Zara kuwa tana tafe bata ankara ba sai tayi tuntube da resting chair din da ke gefen swimming pool din yayinda tayi missing steps dinta. Ni dai gani nayi ta fada cikin swimming pool din yayinda ta kwarma wani irin ihu. Cikin tashin hankali Farouq ya bude qofar Glass din da zata sada shi da swimming pool area din a guje ya qarasa wurin. A lokacin kuwa Zara ta riga ta nitse a qasan pool din. Farouq ya fada cikin Pool din don ceton ta. Cikin hanzari ya fiddo ta sannan ya kwantar da ita a nan qasa yayinda ya juyar da kanta ta gefe saboda ruwa ya fita daga hancinta da bakinta daga nan ya maido kanta daidai. Ajiyar zuciya ya dan yi sannan ya fara bata Mouth-to mouth resuscitation tare da matse hancin ta, kunnuwan shi ya kai saitin bakinta tare da qura ma qirjinta idanuwa don ganin breathing movement dinta. Haka ya dinga yi mata har kusan tsawon minti biyar sannan na ga ta yunquro yayinda ruwa ya dinga fitowa daga bakinta. Idanuwan Zara a rufe yayinda take kakarin amayar da ruwan da ta hadiye. Farouq wanda yake riqe da ita ne yake ta jijjiga ta tare da shafa bayanta yana fadin “sorry my Baby angel, I am here” Gani nayi ya rungume ta tare da daukar ta cak ya nufi cikin gida da ita. Dakinta ya kai ta ya kwantar da ita yayinda hankalin shi yake a tashe domin kuwa ya kula ma kamar suma tayi. Wannan ne ya sa yayi hanzarin fita don dauko kayan aikin shi. *********** Awa biyu kenan da Zara ta fada cikin Pool. Kwance take a kan gadonta cikin bargo yayinda Farouq yake zaune a gefen ta yana kallonta. Tunani yake yi kala kala akan dalilin da ya sa hankalin Zara yayi nisa har ta fada cikin Pool din. STORY CONTINUES BELOW Tambaya yayi ma kanshi "me take yi a wurin when she perfectly knows cewa she shouldn't be there tunda dai bata iya ba??" Zara ce ta motsa tare da bude idanuwan ta wadanda suka yi ja, muryar ta qasa qasa tace “Ya Farouq” Da sauri ya matsa kusa da ita tare da dafa goshin ta yace “hey, how are you feeling?” cikin sanyin murya tace “bad Ya Farouq” Ajiyar zuciya yayi tare da fadin “What were you doing by the pool bayan kin san baki iya swimming ba?” Lumshe idanuwa tayi tace “I am sorry” kafin yayi Magana ne ta dan ja bargon da ta rufa da shi. Gani nayi ta dan bude bargon sannan ta kalle shi da sauri tare da zaro idanuwa tace “Ya Farouq??!” Cikin mamaki yace “what?” Tace “ina kaya na suke?” murmushi yayi ya nuna qasan dakin yace “gasu can” Ji nayi Zara tace “innalillahi wa'inna ilaihir raji’un, Ya Farouq me kayi mun?” Wannan karon kuwa fashewa yayi da dariya yana kallon ta. Cikin muryar kuka tace “Ya Farouq I am practically naked fa” bata rai yayi yace “toh meye? I had to save your life, kayan sun jiqe kuma idan na barki da su zasu sa ki mura da zazzabi” Ji nayi tace “me da me ka gani Ya Farouq?” Farouq ya dan yi murmushi sannan yace “na ga komai my Baby angel” Zara ta zaro idanuwa tace “yau na shiga uku, wallahi Ya Farouq ka cuce ni” Gani nayi ya miqe ya kwaso kayan nata yace “toh tashi in mayar miki da kayan ki”. Ya zauna gefenta yana qoqarin janye bargon da ta rufa da shi. Gani nayi Zara ta tashi zaune dafe da bargon a qirjinta yayinda take qoqarin hana shi janye bargon tana fadin “don Allah kayi haquri” shi kuma yana fadin “ai baki isa ba sai na sa miki kayan ki tunda dai kin ce na cuce ki” Haka fa suka dinga kiciniya wanda da qyar Zara tayi nasara dukda kuwa shima Farouq din da wasa yayi mata hakan. Cikin haushin Farouq ne Zara ta sauka daga kan gadon don zuwa dressing room dinta ta sa kaya. Tana taka qafarta na ji tayi ihu tare da fadowa a jikin shi. Gaba daya jikinta rawa yake yi yayinda take ta sakin ajiyar zuciya. Gani tayi Farouq ya sa mata idanuwa yayinda fuskokin su suke fuskantar juna. Cikin shagwaba Zara tace “Ya Farouq stop staring at me like that” Shi kuwa Farouq wanda yake ta qare mata kallo gani nayi ya tura bakinshi cikin nata ya fara kissing dinta. Zara wadda abin ya zo mata babu notice gani nayi ta zaro idanuwa yayinda zuciyarta take ta bugawa da qarfi. Tuni jikinta yayi sanyi a dalilin wani sabon yanayi da ta shiga. Zara dai tun tana nema ta qi bada hadin kai har ta zage tare da biye mishi. Gani nayi ta sagala hannuwanta a wuyan shi yayinda suka cigaba da kissing juna passionately. STORY CONTINUES BELOW Tsawon mintuna suna abu daya, gaba dayan su ji suka yi kamar sun shiga wata duniyar ta daban. Wayar Farouq ce da ta fara ringing ta ankarar da su. Da sauri ya zare bakin shi daga nata tare da sakin numfashi. Gani nayi Zara ta janyo bargon ta da sauri ta koma kan gadon ta kwanta tare da rufe idanuwan ta. Farouq wanda ya ankara da abinda yayi ne ya shafa kanshi tare da janyo wayar wadda har ta tsinke bai amsa ba. Ganin daga asibiti ne yasa ya kira don jin ko meye. Zara tana jin shi yana bayani a waya yayinda zuciyarta take ta harbwa, abinda ya faru yanzun nan ne yake dawo mata. Bata taba sanin haka first kiss yake da dadi ba sai yau, gaba daya ji tayi kamar kar moment din ya qare. A ranta ne tace “the stupid phone had to cut the beautiful moment short” (Ni kuwa da na jiyo ta na dinga kwasar dariya.. su Zara manyan gari🤣) Bata ankara ba sai ji tayi Farouq yana shafa mata balm a wurin da ta bige a qafarta. Qara runtse idanuwan ta tayi saboda zafi amma a dalilin kunyar hada ido da shi ne yasa ta matse. Bayan ya gama ne ya miqe ya nufi closet dinta ya dauko mata kayanta sannan ya dawo ya ajiye mata a gefenta. Ganin har yanzu idanuwan ta a rufe ne yasa ya matsa kusa da ita tare da kai bakin shi saitin kunnen ta yace “Thanks for the kiss, it’s the best one ever” Zara dai qarasa shigewa tayi cikin bargon yayinda Farouq ya juya ya fita daga dakin yana murmushi. *********** Yinin ranar dai Zara babu abinda take tunowa sai kiss din da suka yi. Motsi kadan sai in ga ta shafa lips dinta tana murmushi. Gaba daya Farouq ya qarasa dagula mata lissafi. (Ni dai ina daga gefe ina ta dariya🤣) ************ Da yamma Zara tana kwance a kan daya daga cikin kujerun falonta tana kallon Zee Tv a zahiri amma fa a badini tunanin Farouq kawai take yi. Gaba daya Farouq ya mamaye zuciyarta. Wayarta ce take ta ringing yayinda tayi nisa a tunani. A ringing na uku ne ta ankara, ajiyar zuciya tayi sannan ta duba wayar, Sunan Mahmood ta gani. Turo baki ta dan yi sannan ta amsa. Mahmood din ne yace “haba cutie, kin share ni. I have missed seeing you a lot” Zara dai shiru tayi yayinda ta kasa fadin komai. Ita dai a yanzu ta ma rasa me take ji a game da Mahmood domin kuwa gaba daya zuciyarta Farouq ne a ciki. Jin tayi shiru ne yace “Hello, cutie are you on the line?” Gani nayi ta qara turo baki sannan tace “yes, how are you?” Mahmood yayi ajiyar zuciya sannan yace “i am not doing good cutie, please can I come and see you? Ko da minti biyar ne please” (Ni kuwa nace whaattt??🙄) Zara ta dan yi shiru sannan tace “gaskiya bazan…” katse ta yayi tare da fadin “please cutie, just five minutes, after isha’I prayer zan zo, send me the address please” Zara dai ce mishi tayi “toh” sannan suka yi sallama. STORY CONTINUES BELOW Tana nan zaune tana tunanin ta tura ma Mahmood address ne ko kuwa ta qyale shi. (Ni dai addu'a na dinga yi kar ta tura amma kash🤔) Gani nayi tana typing a wayar ta yayinda tace “just five minutes yace” ********* Bayan Sallan Isha’i ne Farouq ya shigo gidan. Ganin Zara bata main palour din gidan ne yasa ya wuce sashen shi. Wayar shi ce take ta ringing yayinda yake shiga dakin shi. Ko da ya duba Dr Schurle ne daga Germany yake kiran shi. Bayan ya amsa ne Dr schurle yace “hey Colleague, how you doing? Have you decided yet?” Farouq wanda ya shafa kan shi yace “uhm, not really, when is it going to be?” Dr Schurle yace “next week, but we are going to need you here the soonest so we can review the case, please try and make it” Farouq ya girgiza kai yace “alright, I will get back to you tomorrow” Bayan sunyi sallama ne ya jefar da wayar a kan gadon shi sannan ya wuce dressing room dinshi don shirin yin wanka. Farouq ya fito daga dakin shi sanye cikin Sweatpant da T-shirt inda ya nufi sashen Zara. Yana gab da shiga dakinta ne suka yi karo da juna wanda har ta kusa faduwa yayinda Farouq ya riqo ta yana fadin “careful”. Ganinta yayi tayi shirin fita yayinda ya cika da mamaki. Yana kallonta ne yace “hey, ina zaki je?” ba tare da tunanin komai ba tace “Ya Farouq dama Mahmood ne yazo shine…”3 Kafin ta qarasa yace “what??” yayinda ranshi ya baci sossai. Zara ta turo baki tace “kawai fa Five minutes zanyi” gani nayi Farouq ya dunqule hannun shi tare da runtse idanuwan shi ya bude. Cikin bacin rai ya tura Zara jikin bango da qarfi sannan yace “you are very stupid, ina wasa da ke?” Nuna ta yayi da yatsa sannan ya cigaba da fadin “idan na kuskura na sake jin sunan yaron nan a gidan nan I will deal with you” Zara dai tuni ta fashe da kuka domin kuwa bata taba ganin Farouq cikin bacin rai irin wannan ba. Cikin kuka tace “Ya Farouq please” cikin fada yace “shut up, wuce ki bani wuri before i slap you” aikuwa da gudu Zara ta koma dakinta yayinda Farouq ya juya ya fita cikin qunar rai. Mahmood wanda yake tsaye a jikin motar shi ne ya hango Farouq ya fito daga gidan yayinda ran shi yake a bace. Ko da Mahmood ya ga yanayin Farouq ya tsorata. Farouq yana qarasowa ne Mahmood yace “ina wuni” Farouq wanda bai amsa gaisuwar Mahmood ba yace “this will be the first and the last time da zan yi warning dinka, kar ka kuskura ka qara zuwa gidan nan. Zara is married to me kuma she will remain with me till forever” Ya nuna hanyar gate yace “you should get going kafin in sa securities su nuna maka hanya” Bai tsaya jin abinda Mahmood zai ce ba ya juya yayinda Mahmood din ya lallaba ya shiga motar shi cikin tashin hankali ya bar gidan. Farouq kuwa ko da ya shiga gidan sashen shi ya wuce straight. Zaune yake a kan gadon shi yayinda zuciyar shi take ta tafasa. Dafe kan shi yayi yana tunanin abinda ya faru. Ji nayi yace “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un, what have I done to deserve this? Yanzu ya zanyi da yarinyar nan?”2 ********** Hmmmm... 🤔🤔🤔 Kwance take a kan gadonta tana ta kuka a dalilin fadan da Farouq yayi mata. Zara dai tun asali bata so Farouq yayi fushi da ita domin kuwa ba qaramin tashin hankali take shiga ba.+ A yanzu kuwa tayi nadamar abinda tayi domin kuwa ta gane cewa babban kuskure tayi. A matsayinta na matar aure ta fita ganin wani ba tare da amincewar mijinta ba. Ta ma rasa ya akayi tunaninta ya gushe da har tayi wannan wautar. Tana nan kwance ne cikinta ya fara yi mata azabar ciwo yayinda ta dafe shi tana ta juyi. Haka Zara ta dinga fama har wuraren qarfe goma sha daya na dare. Zara dai ta sani sarai al’adarta ce ta zo, da qyar ta lallaba ta shiga bathroom tayi wanka sannan ta kimtsa kanta. Drawers din dakinta ta dinga budewa tana neman maganinta amma babu. Daga baya ne ta tuno cewa ya qare don haka ne ta koma ta kwanta a qasa. Zara dai haka ta cigaba da juyi a qasa, wani ikon Allah bata taba jin azaba irin na yau ba. (ni kuwa nace abubuwa ne suka hadu mata har biyu🤣) Wuraren qarfe daya na dare ne da ta kasa jurewa ta miqe da qyar ta fita don zuwa neman taimako a wurin Farouq. A daddafe ta qaraso dakin shi ta bude qofar sannan ta shiga. Kwance yake a kan gadon shi, idanuwan shi a rufe amma ba bacci yake yi ba. Ya sani sarai cewa Zara ta shigo dakin amma bai motsa ba balle ya bude idanuwan shi. Ita kuwa Zara ganin cewa yana bacci ne yasa ta kasa tada shi. kwanciya tayi a nan qasa dafe da cikinta yayinda ta cigaba da juyi. Farouq kuwa saboda bacin rai da yake ciki yana jinta amma yayi watsi da ita. So yake ya nuna mata kuskurenta tare da tuna mata cewa ana iya tsawata mata a duk lokacin da tayi ba daidai ba. Zara dai da ta kasa jurewa ne na ga ta tashi ta matsa gefen gadon, muryar ta qasa qasa tace “Ya Farouq” Farouq yana jin ta yayi shiru. Fashewa tayi da kuka ta taba shi tare da fadin “Ya Farouq please help me, cikina” Jin tana kuka ne yasa ya dan bude idanuwan shi yace “meye?” Cikin kuka tace “cikina ke ciwo kuma na duba magani na ya qare, please help me” Shiru ya dan yi sannan yace “come here” Cikin rashin fahimta Zara tace “na’am” daga nan kuwa shiru yayi bai sake yi mata Magana ba. Gani nayi Zara ta miqe jikinta yana rawa ta hau gadon. Hannuwan shi yasa ya janyo ta jikin shi yayinda ta saki ajiyar zuciya. Gani nayi ta juya mishi baya tare da dan matsawa nesa da shi yayinda jikinta yake ta rawa. Farouq dai janyo ta ya qara yi jikin shi yace “idan bazaki tsaya ba tashi ki bani wuri” STORY CONTINUES BELOW Zara wadda hawaye yake ta gangarowa daga idanuwan ta ne ta natsu tana sauraron ikon Allah. Bata ankara ba ta ji hannuwan shi a ta cikin rigarta inda ya fara massaging cikinta zuwa lower abdomen dinta. Ji nayi Zara ta saki numfashi yayinda ta lumshe idanuwan ta. Wani ikon Allah ko minti goma sha biyar Zara bata yi ba bacci ya kwashe ta domin kuwa ta samu relief sossai. Shima kuwa Farouq bai san lokacin da baccin ya kwashe shi ba. Cikin dare ne Zara ta farka inda ta juyo tana fuskantar Farouq wanda yake bacci. Gani nayi tana ta kallon shi yayinda tayi murmushi. Kiss tayi mishi a kumatu tare da fadin “thank you big brother” sannan ta rufe idanuwanta. *********** Da asuba ana Kiran Sallah ne Farouq ya bude idanuwan shi. Zara ce maqale a jikin shi kamar mage yayinda take ta baccin ta. Girgiza kai yayi sannan ya zare jikin shi daga nata a hankali ya sauka daga kan gadon ya gyara mata bargon da suka rufa da shi sannan ya wuce bathroom dinshi. Alwala yayi ya fito sannan ya wuce masallaci. Ko da Farouq ya dawo daga masallaci Gym dinshi ya wuce ya dan yi working out har zuwa qarfe bakwai na safe sannan ya koma dakinshi don yin wanka. Har wannan lokacin kuwa Zara bacci take yi sossai dayake dai dama bata samu baccin kirki ba. Bayan Farouq ya fito ya gama shirin shi ne ya fita abinshi domin kuwa dama akwai surgery din da zai yi da safen nan. Zara dai bata farka ba sai wuraren qarfe goma na safe. Juyawa tayi ta ga babu Farouq, da sauri ta tashi zaune tare da murza idanuwanta. Agogo ta kalla ta ga qarfe goma da minti goma. Gani nayi ta zaro idanuwa tace "what??!!" Da sauri ta sauka daga kan gadon tare da yaye bargon tana kallon inda ta tashi. Ji nayi tace “huh... thank God I didn't stain his sheet” Jikinta babu qwari ta wuce ta fita don zuwa dakinta tayi wanka. CALEDONIAN SUITES MAITAMA ABUJA Kwance suke a bisa gadon daya daga cikin dakunan Hotel din kamar kullum inda suke holewar su. Musty ne yace “wai ina Farouq dinki ne, yaushe yakamata in je mu gaisa kamar yadda ya buqata?” Ruqaya ce ta tashi zaune cikin bacin rai tace “what? Ai wallahi bazaka je ba, ka kuwa san zai iya gano wani abu a duk lokacin da kuka hadu? He is very smart fa” Musty ya fashe da dariya yace “toh ma in banda abinshi yanzu da ya qara aure ai ya kamata ya baki space kema” Ruqayya ta harari Musty tace “ni na fada maka ina son space?” Musty yayi dariya yace “gashi nan kuwa kin samu har kin waiwaye ni” Ruqayya ta girgiza kai ba tare da tace komai ba. STORY CONTINUES BELOW Janyo ta yayi yace “I really love you Ruqy, wani lokacin ma ji nake yi kamar in kauda Farouq din naki don in same ki all to myself” Ruqayya ta ture shi tace “don’t try anything with Farouq, I am warning you” Musty ya fashe da dariya yace “sorry love, I won’t as long as zamu cigaba da haduwa” daga nan ne ya canza hirar inda yace “wai dagaske kike yi Junior ba yaro na bane?” Ruqayya dai tashi tayi zata shiga bathroom tace “ai kuma sai kayi” ta shige kewaye yayinda Musty yake ta dariya. FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION (GIDAN ZARA) Zara kwance a kan gadon dakinta cikin bargo yayinda take tunanin Yadda zata ba Farouq haquri. A yanzu dai zuciyar Zara gaba daya ta karkata ga son yayan nata. Gaba daya Farouq ya mamaye mata zuciya, babu abinda takeyi sai zagin kanta da har tace bata son shi a lokacin da za’a yi auren su. A yanzu ta gano lallai shi take qauna kuma a yanzu haka ma ta fasa rabuwa da shi kamar yadda suka tsara.3 (Yesss... Good girl Zara😘) Wayar ta ce tayi ringing, ganin sunan Hafsat ne yasa ta amsa tare da fadin “bestie dama yanzu nake shirin kiran ki, I really need to talk to someone” Hafsat cikin farin ciki marar misaltuwa tace “aikuwa nima wani labari nake so in baki da dumi dumi but it can wait, how far” Ajiyar zuciya Zara tayi tace “I have fallen deeply in love with him bestie” Cikin rashin fahimta Hafsat tace “ban gane ba babes, who are you talking about??” Zara tace “Ya Farouq, I just realised I can’t live without him” Hafsat tayi tsaki sannan tace “say something I don’t know babes, ai ba wanda bai san wannan ba..” Zara ce ta katse ta tare da fadin “you don’t understand bestie, akwai abinda ban fada miki ba” Hafsat tace “tell me” Anan fa Zara ta bata labarin plan din da suka yi na rabuwa da juna bayan wata daya da yin auren su. Hafsat kuwa me zata yi banda dariya. Cikin dariya ne Hafsat tace “toh wai ke dama a tunanin ki Ya Farouq dagaske yake zai rabu da ke?” Zara tayi ajiyar zuciya tace “its not funny bestie, Ya Farouq fa ba sona yake ba…” Hafsat ta katse ta tare da fadin “Hajiya, Ya Farouq loves you a lot, dama kin natsu kin bude mishi zuciyarki, kin dai san kina da competition ko?” (Ni kuwa nace ah toh.. remind her dai Hafsat) Zara tayi ajiyar zuciya tace “toh ai babes yanzu haka fushi yake yi da ni saboda nayi mishi laifi jiya” Hafsat cikin mamaki tace "huh bestie, wallahi ba kya jin magana. Me kika yi mishi this time??” anan Zara ta bata labarin zuwan Mahmood jiya da yadda Farouq ya dinga yi mata fada har yayi fushi. Hafsat tace “gaskiya babes kinyi mistake, you need to grow up and please try to always think before you act I beg of you" STORY CONTINUES BELOW Zara tace "Insha Allah babes" Hafsat tace "Well dama a dalilin Mahmood din ma na kira ki, ki shiga Instagram ki ga labarin da yake ta yawo regarding him. Just get back to me idan kin gama kallo” Zara kuwa bata tsaya amsa Hafsat ba ta kashe wayar tare da tashi zaune ta shiga Instagram. Gani nayi Zara ta zaro idanuwa tare da fadin “Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un, na shiga uku. Dama haka Mahmood yake?? Allah ya isa tsakani na da shi” Ni kuwa da na leqa wayar sai na hango Hoton Mahmood tare da wasu karuwan ‘yan mata a hotel yayinda ake sanarwar daya ta mutu saboda mugayen qwayoyi da suka yi mata yawa wanda a yanzu haka an kama mahmood tare da sauran ‘yan matan ana tuhumar su. Da sauri Zara ta kira Hafsat a waya tace “bestie wallahi na gani, dama haka Mahmood yake ban sani ba?” Hafsat tana dariya tace “Jiya da daddare aka kama su, ai dama na fada miki tun farko bana son Mahmood, wallahi tun ranar da na fara ganin shi ban yarda da shi ba” A lokacin da suke wayar ne Farouq ya shigo gidan. Kai tsaye dakin Zara ya nufa don duba ta domin kuwa dukda bata mishi rai da tayi baya iya fushi da ita na tsawon lokaci saboda bala’in son da yake yi mata. Zara ta riga tayi mishi mugun kamun da yake tunanin ko wanne irin laifi tayi mishi zai iya yafe mata. Yana gab da shiga ne ya ji Zara tana fadin “wallahi bestie kwata kwata ko ganin shi bana son yi, a yanzu haka na tsani kaina wallahi. Bana son shi ko alama, I hate him with every fibre of my being....”2 (Oh my... oh my... Not again) Gani nayi Farouq ya dafe qirjin shi tare da runtse idanuwan shi, komawa yayi da baya cikin tashin hankali yayinda kalaman Zara suke ta amsa kowa a qwalwar shi. Da qyar Farouq ya qarasa falon shi ya zauna a kan kujera dafe da kanshi. A zuciyar shi ne yake fadin “does she hate me this much? Subhanalillah, me nayi ma yarinyar nan haka ne da zata fadi irin wadannan kalaman?” Idanuwan Farouq sunyi jajawur yayinda zuciyar shi take ta radadi. Farouq dai bai san yawan lokacin da ya bata a wurin ba domin kuwa yayi nisa a tunani. Har wani zazzabi ya rufe shi. Gani nayi ya ja numfashi sannan ya ciro wayar shi daga aljihun shi yayi dialling lambar Dr. Schurle. Ji nayi yace “Hello colleaque, I have decided to join the team, I will be in Germany the soonest Insha Allah” Farouq yana gama waya da Dr. Schurle ne ya miqe ya nufi dakinshi ya hada akwatin shi sannan ya fita daga gidan. ********** Zara dai ta dade tana waya da qawarta inda suke ta zagin Mahmood. Daga nan kuwa Hafsat din ta bata shawara akan lallai ta ba Farouq haquri. Bayan sunyi sallama ta sauka daga kan gadon ta shiga bathroom don yin wanka. Bayan ta fito ta kimtsa kanta ne ta ji wayarta tayi qara alamar an turo mata text message. Ko da ta duba sunnan Farouq ta gani, tana murmushi ta bude saqon kamar haka: "I am on my way to Germany right now, I have an emergency case to attend to. Take care." Zaro idanuwa Zara tayi ta saki wayar, ta dafe kai tare da fadin “yau na shiga uku, ya tafi ya barni” Gani nayi ta zame qasa ta fashe da kuka. Gani nayi ta janyo wayar ta kira layin shi amma switched off, haka ta dinga kira bata samu. Jefar da wayar tayi ta cigaba da kuka. Ji nayi tana fadin "Ya Farouq why would you leave me now?? Na shiga uku ya zanyi??" (Ni kuwa ina daga gefe nayi tagumi..🤔) ********** Zara dai daren yau baccin kirki bata yi ba. Ta sani sarai Farouq ya tafi yana jin haushin ta, a duniya babu abinda yake tada mata hankali irin fushin Farouq. Damuwa sossai ta sa a ranta. Kafin safe kuwa ta fita hayyacinta. Ko da gari ya waye da qyar ta ja jikinta ta wuce bathroom don yin wanka. Tana zaune a kan kujerar dressing mirror dinta ne na ga ta miqe yayinda jikinta yake ta rawa. Da qyar ta lallaba ta haye gado ta shige bargo, tuni zazzabi ya rufe ta yayinda take ta kyarma. ********** MUKHTAR ABUBAKAR MANSION Dayake yau saturday Mukhtar yana zaune a falonshi da safe yana buga game ne wayar shi tayi ringing.+ Yayi mamakin ganin layin Farouq na qasar Germany. Ko da ya amsa cikin mamaki yace “abokina ya na ga ka kira ni da wannan layin? Where are you?” Farouq yace “ina Germany abokina, ban dade da sauka ba. na kira ka lokacin da zan tafi amma wayar ka bata shiga ba” Mukhtar yayi murmushi yace “tare da Zara ka tafi kenan?” Farouq yayi ajiyar zuciya sannan yace “abokina Zara tana gida kuma I have made up my mind on letting her go, idan na dawo insha Allah I will free her” A lokacin ne Hafsat ta shigo falon riqe da tray na Coffee domin kuwa shi dama Mukhtar da Coffee yake farawa duk safiya. Gani tayi Mukhtar ya zaro idanuwa cike da mamaki tare da fadin “whoa, wait abokina ban gane you are letting her go ba, please tell me. Wani abu ya faru ne? me Zara tayi maka?” Hafsat ta sa ma Mukhtar ido yayinda hankalin ta yake a tashe tana sauraron shi. Farouq ne ya bashi labarin abinda ya faru sannan yace “I cant force her to be with me, I want her to be happy ko da kuwa hakan zai qona zuciya ta” Mukhtar yayi ajiyar zuciya sannan yace “hey relax please take it easy, lets sort this out idan ka dawo. By the way me kake yi a Germany? Don’t tell me saboda Zara ta bata maka rai shiyasa ka gudu?” Girgiza kai Farouq yayi yace “nope, matar president ce zata yi undergoing series of surgery so they need me on board” Mukhtar yace “okay, all the best, but please relax kaji abokina?” Farouq ya dan yi murmushi yace “thanks my friend” bayan sunyi sallama ne Mukhtar ya kashe wayar shi tare da kallon Hafsat wadda itama kallon shi take yi. Hafsat ta matsa kusa da shi tace “sweetlove, me Bestie tayi ma Ya Farouq? Please tell me” Anan dai Mukhtar ya ba Hafsat labari wanda Hafsat din ta zaro idanuwa tace “what? Wai dama shima yana sonta dagaske?” Mukhtar cikin rashin fahimta yace “toh ita din son shi take?” Hafsat tayi murmushi sannan ta bashi labarin abinda ta sani itama. Mukhtar ya fashe da dariya yace “ikon Allah, su kuma haka tasu salon soyayyar take kenan” Hafsat tana ta dariya. Mukhtar yace “Thank Goodness they are both on the same page, I guess there is nothing to sort out after all” FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION (GIDAN ZARA) Kwance take a cikin bargon ta tana ta kyarma. Bacci ne yake fizgar ta, cikin dan qanqanin lokaci kuma ta farka. jikinta yayi zafi sossai sannan ga kanta da yake azabar ciwo. STORY CONTINUES BELOW Hafsat ce ta shigo dakin. Ta kira wayar Zara ya fi a qirga amma bata amsa ba wannan ne yasa ta zo gidan domin ganin halin da take ciki don kuwa its unsual a kira wayar Zara bata amsa ba. Hafsat dai ganin qawarta a cikin bargo tana ta kyarma ne yasa ta zaro idanuwa ta nufi wurinta tare da fadin “subhanalillah, bestie what is wrong with you?” Da sauri ta yaye bargon da Zara ta rufa da shi tare da janyota ta rungume ta. Zara wadda take ta kyarma ta fashe da kuka tana fadin “bestie ya tafi ya bar ni, wallahi bazan iya jure fushin Ya Farouq ba, I really love him. I will die idan bai…” Da sauri Hafsat ta sa hannu ta rufe mata baki sannan tace “relax babes, Na zo miki da proof cewa Ya Farouq Loves you a lot. Yanzu sweetlove ya gama bani labari” Zara ta dan dago cikin mamaki tana kallon Hafsat tace “dagaske bestie??” anan kuwa Hafsat ta ba Zara labari tun daga lokacin da Farouq ya bayyana ma Mukhtar yana son ta har zuwa wayar da suka yi da safen nan. Gani nayi Zara ta rungume qawarta cikin murna marar misaltuwa tana fadin “Alhamdulillah, I am glad he loves me too, wallahi bestie I love him so very much” tuni ta share hawayen fuskar ta. Hafsat ce tace “ba a baki ba hajiya, prove to him cewa you do” Zara wadda ta gyara zama tace “toh ai baya nan bestie, ya tafi ya barni” Hafsat tace “make him come back mana” can kuma tace “ko dayake fa na ji aiki ya kai shi, kuma its kinda important” Gani nayi Zara tayi shiru kamar tana tunani sannan na ga tayi murmushi tace “I have a plan bestie and I think I can wait for him to return, knowing cewa he loves me alone gives me joy” Hafsat tayi dariya tace “that’s like a good girl” Zara tace “I forgot to ask you, Ya cikin ki? komai normal?” Hafsat ta shafa cikinta tace “fine bestie, kawai dai wani lokaci yana dan yi mun ciwo. Can’t wait to see you become pregnant kema” Zara tayi murmushi tace “ni triplets ma nake so bestie, dukkansu maza masu kama da Ya Farouq” Hafsat dai fashewa tayi da dariya tace “what?? You are crazy bestie” Zara tayi dariya tace “crazily in love with Ya Farouq” Haka dai suka cigaba da hira wanda tuni Zara ta warke domin kuwa Hafsat dai ta kawo mata maganin ciwon da yake damun ta. ********** Tun daga lokacin da Zara ta ji labarin cewa Farouq yana sonta ne ta kwantar da hankalin ta. Bata neme shi a waya ba sannan shima bai kira ta ba. Tana zuwa gidan Mamy ta yini duk bayan kwana biyu sannan Watarana kuma gidan qawarta take zuwa. Wasa wasa Farouq sai da ya kusa sati uku a Germany. Sun yi nassarar ceto rayuwar matar President wanda gaba daya surgery din da aka yi mata ya zama successful. Gaba daya likitocin sun ba Farouq credit domin kuwa yayi qoqari matuqa, shi yayi heading team din gaba daya. STORY CONTINUES BELOW President din Germany ya nuna farin cikin shi matuqa tare da jinjina ma Farouq akan qoqarin da yayi wurin ceto rayuwar matar shi. Har wani special dinner yayi organinzing don qara nuna godiyar shi ta musamman. Abubuwan alkhairin da yayi ma Farouq kuwa ba’a Magana domin kuwa qadarori masu yawa aka bashi kyauta a nan Germany din, a ciki kuwa harda wani danqareren gida a Berlin. Sunan Farouq kuwa ya qara yaduwa a qasashen duniya, babu wanda bai san da shi ba. Su Abba ma sun ji dadin yadda dan nasu yayi progressing ya zama successful. Zara ma tayi murna sossai, duk inda ta shiga a social media sai ta ga labarin Farouq. Ta tura mishi text message na taya shi murna amma kamar yadda tayi zato bai yi replying dinta ba. Hakan bai dame ta ba, fatan ta Allah ya dawo mata da shi lafiya ta samu damar nuna mishi matsayin shi a zuciyarta. (Hmmm...😏) Ranar da Farouq ya dawo gidan Ruqayya ya sauka. Tunda ya dawo kuwa abokin shi Mukhtar yake ta lallabar shi akan yayi haquri kar ya rabu da Zara dukda kuwa bai fadi mishi abinda ya sani ba. FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION (GIDAN ZARA) A yau ne Farouq zai dawo gidan Zara. Wani ikon Allah a bakin Hafsat ne Zara take ji cewa ya dawo daga Germany kwana biyu da suka wuce. Tun da safe da ta tashi daga bacci take tunanin yadda zata aiwatar da plan dinta domin kuwa ta sani sarai har yanzu fushi yake da ita. Yau sati uku kenan basu ga juna ba sannan basu ji muryar juna ba, A zahiri Zara tayi bala’in missing dinshi musamman yanzu da take bala’in son shi. Da Yamma ne na ga daya daga cikin masu aikin Zara ta shigo falonta riqe da wata qatuwar mage a hannunta. Zara dai tana ganin ta tayi murmushi tare da fadin “yauwa, this is perfect” Gani nayi ta karbi magen sannan ta fara wasa da ita (kun san Zara da son mage) Ta dade tana wasa da magen domin kuwa har hotuna ta dauka da ita. ******** Wuraren qarfe tara saura Farouq ya shigo gidan. Ko da ya shiga babu kowa a main section din gidan. Sashen Zara ya kalla a ranshi yace “how I missed her” tsaki yayi sannan ya wuce sashen shi. Farouq ya shiga dakin shi ya jefar da wayar shi kan gado sannan ya wuce dressing room dinshi don shirin shiga wanka. Bayan ya fito ya shirya cikin black sweatpant da Navy blue T-shirt. Yana gaban madubi ne ya ji kamar kukan mage a dakin. A firgice ya waigo tare da zagaya ko wanne lungu na dakin ahankali amma bai ga komai ba. Ajiyar zuciya yayi sannan ya koma ya cigaba da brushing kanshi. Bayan ya gama ne ya nufi gadon shi ya hau ya kwanta. Aikuwa yana janyo bargon shi yayi ido hudu da qatuwar mage a gefen shi wadda ta sa mishi ido. STORY CONTINUES BELOW A tsorace na ji Farouq yace “subhanalillahi” Hankalin shi a tashe ya matsa da sauri wanda har ya fado daga kan gadon. Zuciyar shi ce take bugawa da sauri yayinda jikinshi yake rawa. Gani nayi Magen tayi approaching dinshi yayinda take kuka, Farouq dai kasa tashi yayi domin kuwa da rarrafe ya fita daga dakin da saurin gaske. (Ni kuwa me zanyi banda dariya🤣) Zara wadda take zaune a gaban dressing mirror dinta tana fesa spray sai ganin Farouq tayi ya shigo dakin a gigice yayinda ta miqe da sauri. Ba tare da tunanin wani abu ba ya rungume ta yayinda jikin shi yake ta rawa. Zara wadda ta rungume shi itama tace “Ya Farouq lafiya, yaushe ka shigo?” Farouq dai kasa Magana yayi. Bugun zuciyar shi kadai Zara ke ji. Gani nayi tayi murmushi sannan tace “hey tell me please, I am scared” Muryar shi qasa qasa yace “please hug me tight” Zara kuwa qara matse shi tayi ba tare da tace mishi komai ba. Sun kusan minti goma a haka domin kuwa ba qaramin tashin hankali Farouq ya shiga ba. Zara kuwa a zuciyarta har ta fara regretting abinda tayi mishi. Jin ya samu natsuwa ne yasa Zara tace “i have never seen you this scared before Ya Farouq, please tell me” Cikin rada yace “I saw a cat in my room” Zara ta zaro idanuwa tace “what? Shine ka tsorata haka Ya Farouq?” can kuma sai tace “toh ya aka yi mage ta shiga dakinka?” Janyo shi tayi zuwa bakin gadon ta tace “come and sit, let me go and check” Dayake towel ne kawai a jikinta sai ta dauko dogon hijabi ta sa har tana fadin “I can’t believe cewa someone let a cat into this house when Ya Farouq na tsoron ta” Shi dai Farouq yana nan dafe da kan shi yayinda yake tuno encounter dinshi da magen har ta fita. (🤣🤣🤣... ka ji maza) Zara kuwa tana fita daga dakin na ji ta fashe da dariya a ranta tace “weldone Zara” sannan ta nufi dakin Farouq ta dauki magen ta rungumeta ta fito. Gani nayi tana shafa kan magen tace “thank you very much cutie, you just saved my marriage” Bayan Zara ta fitar da magen ne ta dawo dakinta. Ko da ta shiga ganin shi tayi zaune a kan gadon ta dafe da kanshi har yanzu. Matsowa tayi kusa da shi tace “Ya Farouq ban ga komai ba fa, maybe you didn’t see well, ka tabbata lafiyarka kuwa?” ta dafa goshin shi sannan tace “your temperature seems to be normal though” Gani nayi yayi ajiyar zuciya yayinda ta rungume kanshi tana shafa gashin shi tace “relax, I am here for you” Bayan dan lokaci ne ta sake shi tare da fadin “ina zuwa” ta juya zata nufi dressing room dinta ne ta ji ya riqo hannunta. STORY CONTINUES BELOW Da sauri ta juyo tana kallon shi yayinda ya miqe tsaye yace “ina zaki je?” muryar ta qasa qasa tace “I want to dress up ne Ya Far..”2 Gani nayi ya sa hannu ya cire hijabin da yake jikin ta yayinda ya tura ta jikin bango ya kai fuskar shi kan wuyan ta yana ta shaqar qamshinta. Zara dai tuni jikinta ya fara rawa. Ji tayi yana ta aika mata da kisses a wuyan ta da kafadarta yayinda hannuwan shi ke ta yawo a jikinta yana fadin “I Missed you, I missed your smell my Baby angel” Zara dai idanuwan ta a rufe yayinda take ta sakin numfashi tare da amsar saqonnin da Farouq yake aika mata, gaba daya tayi surrender. Ji nayi tace “Ya Farouq” Farouq dai hankalin shi yayi nisa da bai ma ji tana Magana ba. ji nayi ta qara fadin “Ya Farouq please stop, you are heating me up” murmushi yayi ya kai bakin shi saitin kunnen ta yace “that’s the idea my Baby Angel” Ya dawo da Fuskar shi saitin fuskar ta yace “Baby angel look at me” Zara wadda idanuwanta suke a rufe ta girgiza mishi kai alamar a’a. Murmushi yayi sannan yace “I love you very much, please don’t leave me” Gani nayi Zara ta bude idanuwanta da sauri tana murmushi tace “I love you too Ya Farouq, I simply can’t live without you” daga nan dai sai gani nayi ya tura bakin shi cikin nata suka fara kissing juna. Daukar ta yayi ya dora ta bisa gadonta yayinda suka cigaba da kissing juna. Tawul din zara dai tuni ya kwance. Hakan kuwa ya ba Farouq damar sarrafa ta yadda ya ga dama. Zara dai gaba daya tayi nisa domin kuwa yanayinta ya nuna lallai ta shiga wata duniyar. Ina nan maqale na ga Farouq ya fara rage kayan jikin shi yayinda ya dalla mun wata muguwar harara wadda ta sa nayi saurin boyewa bayan labule. Ina nan maqale na ji Zara tana fadin “ouch please Ya Farouq ka bari” da alama kuwa Farouq bai bi ta kanta ba domin kuwa daga baya ma ji nayi tana ihu, ni kuwa ban gane ko ihun dadi bane ko na wahala. Ina nan a maqale dai tsawon lokaci har na fara gyangyadi. (Ah toh🤔) Da na ji shiru ne na dan leqo don ganin abinda yake faruwa. Ganin Zara nayi cikin bargo tana share hawaye yayinda Farouq yake kwance a gefenta yana kallonta. Ji nayi yace “hey I am sorry” Matsawa tayi ta rungume shi tace “don’t be, I love you very much” Ajiyar zuciya yayi yace “huh.. thank God she still loves me after everything that just happened” Murmushi Zara tayi tare da jan gemun shi tace “bad boy” yayi murmushi tare da fadin “only for you my baby angel, I love you too” Zara tana kwance a qirjin shi yayinda yake shafa gashin kanta yace “you know what?” ta girgiza kai alamar a’a. Yace “you are so sweet, so soft, so... infact I have never felt this good in my life, you just completed me” Zara dai cikin farin ciki ta dago tayi mishi kiss tace “I am soo happy, please don’t stop loving me” Murmushi yayi tare da ja mata hanci yace “son da nake miki na daban ne my Baby angel. I know you are exhausted for now, get some sleep” Yayi mata kiss yace “good night” tayi murmushi tare da fadin “good night” A haka dai yana shafa kanta har tayi bacci. Shi kuwa Farouq ya dade bai yi bacci ba. abubuwa dayawa suke yawo a qwalwar shi. Bai taba sanin cewa haka abun yake ba, Ya amince lallai Zara daban ce. A yanzu kuwa addu’a yake yi akan Allah ya bashi ikon yin adalci a tsakanin matan nashi. (Ni kuwa nace ameeeeen🤣... amma fa da kamar wuya) ************

Post a Comment for "BA SONTA NAKE BA CHAPTER 13"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...