BA SONTA NAKE BA CHAPTER 10 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BA SONTA NAKE BA CHAPTER 10

BA SONTA NAKE BA CHAPTER 10

- - Post a Comment
BA SONTA NAKE BA CHAPTER 10
Wani ikon Allah tun daga lokacin da Farouq da Zara suka hada plan din ne Zara ta kwantar da hankalin ta.+ A yanzu ma ta qagara lokacin bikin ya zo ayi a gama har su rabu ta koma ma Mahmood dinta.2 (She is not serious🤣)2 LATE ALH UMAR JIMETA MANSION Zaune yake rungume da ita kamar kullum idan suna tare. Hira suke yi sossai. Granny ce tace “ina gimbiyar taka, na ji ta shiru bata fito ba? ko bata tashi daga baccin bane?” Kafin yayi Magana ne Zara ta fito cikin rigar material doguwa har qasa. Gashinta buzu buzu wanda yake a tsefe, da gani kasan ma ya kwana biyu bata taba shi ba. Kallon Farouq tayi sannan ta kalli granny tace “ina kwanan ku” Granny ce ta amsa yayinda Farouq ya bi ta da kallo. Zama tayi akan kujerar da take nesa da su sannan ta dauki remote ta canza channel zuwa Zee Tv. Granny ce tace “yau na ga ikon Allah, ni nace miki ina son kallon India?” Zara ta turo baki tace “toh wai ba fa kallon kike yi ba, hira fa kuke yi” Granny ta kalli farouq tace “wannan matar taka bata jin Magana” Murmushi yayi yace “yi haquri Mi Lady” agogon hannun shi ya kalla yace “ina ganin fa anjima zan koma Abuja” Da sauri Zara ta dago ta kalle shi yayinda ta ji Granny tace “haba dai anjima, ai baka isa ba sai ka qara kwana biyu don kuwa na san idan har ka tsallake ka tafi bazaka qara waiwayo ni ba musamman idan ka auro wannan gimbiyar” Farouq ya kalli fuskar Zara wadda ta turo baki sannan yayi ma Granny kiss a kumatu yace “haba dai Mi Lady, ai na kusan dawowa nan gidan da zama, ke ce number 1 remember? I love you soo very much” Granny wadda take kallon Zara wadda ta dago tana kallon su ne tace “lafiya kike kallo na? ko kishin ne ya motsa?” Farouq yayi murmushi yayinda Zara tace “Allah ya sawaqe inyi kishi da ke, idan dai Ya Farouq ne nace miki na bar miki” (Iyeeh.. kun ji Zara🤣)3 Granny tace “qaryar banza, mun dai san lokacin da ciwon ki ya tashi har kika suma saboda yayi aure” (Da kyau tsohuwa😄) Zara ta zaro idanuwa tare da bata rai tace “haba Granny, ni na fada miki hakan?” Granny ta kalli Farouq tace “Zaka yi fama da wannan yarinyar domin kuwa kishi gareta na bala’i, ba tun yau nasan ta ba” Ta kalli Zara tace “sai ki daura damara domin kuwa mata biyu zaki tarar” Kafin ta qarasa zancen ta ne Zara ta miqe cikin fushi ta wuce dakinta yayinda ta bar Farouq da Granny suna ta dariya. STORY CONTINUES BELOW Farouq dai akan dole Granny ta hana shi tafiya don haka ne ya fasa tafiya Abuja. Gaba daya yinin ranar kuwa Zara a daki tayi shi. haushin granny da Farouq take ji. ************ Da daddare ne Mahmood ya kira Zara a waya. Bayan sun gaisa ne yace “cutie yi mun kwatancen gidan Granny gani a gari” Cikin mamaki Zara tace “what, dagaske kake?” yace “yes” Cikin murna Zara tace “I am soo happy zan gan ka” murmushi yayi yace “me too” Aikuwa nan da nan tayi mishi kwatance. Zara dai wanka ta shiga ta fito ta shirya cikin wata doguwar rigar jallabiya wadda tayi mata kyau sossai. Turaruka ta fesa wanda nan da nan ta fara zabga qamshi. Tana qarasa shiri ne Mahmood ya kira ta a waya ya sanar da ita isowar shi. A lokacin da Zara ta fito ta tarar da Farouq da Granny zaune suna hirar su da bata qarewa. Zara tana mamakin yadda Granny take ji da Farouq fiye da kowa a cikin jikokin ta. Ganin ta fito cikin shirin fita ne yasa Farouq yace “ina zaki je?” murmushi tayi tace “Mahmood ne ya zo Ya Farouq” Wannan maganar da Zara tayi sai da ta soki zuciyar Farouq, ran shi ya bala’in baci amma sai ya matse tare da kauda kan shi. Bayan Zara ta fita ne Granny ta kalle shi tace “me nake gani?” yace “a ina Mi Lady?” tace “yanzu barin ta kayi ta fita wurin wani bayan an sa ranar bikin ku?” Farouq dai murmushin takaici yayi yace “toh ya zanyi Mi Lady?” Granny ta girgiza kai tace “anya son da kake mata zai bari ka dinga tsawata mata kuwa? Kada fa ka biye mata tana abinda ta ga dama..” Farouq yace “I will try to keep her under control Mi lady” Granny dai cikin mamaki tace “yau na ga ikon Allah” Wani ikon Allah dai tunda Zara ta fita hankalin Farouq ya qi kwanciya. Granny ta kula cewa jikan nata ya shiga damuwa amma sai ta nuna kamar bata gani ba. Gani tayi ya miqe yace “Granny bari in je daki, kaina yana ciwo” Granny tace “subhanalillah, ko a kawo magani?” yace “No, idan na kwanta zai tafi” ya duqo tare da yi mata kiss a goshi yace “good night” sannan ya tafi. Farouq zaune a kan kujera dafe da kanshi yana tunanin yadda Zara take qoqarin ta haukatar da shi. Ni dai ji nayi yana fadin “why Farouq, why did you let her take control over your heart like this?” tsaki yayi sannan ya kwanta kan kujerar.2 (Ayyah...☹) Farouq dai baccin kirki bai samu ba, har wani zazzabi ya taso mishi cikin dare saboda tsabar damuwa da ya sa a ran shi. STORY CONTINUES BELOW Da asuba ma kasa zuwa masallaci yayi, a nan dakin shi yayi sallan asuba. Wuraren qarfe takwas na safe Granny da Zara suna kan dinning yayinda suke breakfast. Ganin Farouq bai fito bane yasa Granny tace “wai maigidan namu bazai zo cin abincin bane yau?” Zara ta turo baki tace “qila baya jin yunwa ne” granny tace “ko kuma ciwon kan nashi ya matsa mishi ba” Gani nayi Zara ta miqe a rude tace “what? Ya Farouq ba lafiya? Shine baki fada mun ba?” Kafin Granny tayi Magana sai gani nayi Zara ta ruga a guje ta nufi dakin shi yayinda ta bar Granny sake da baki. Girgiza kai tayi tace “kuma a haka ki ce ba son shi kike ba? kai wannan yarinyar halinta sai ita” Ba tare da ta qwanqwasa mishi qofar ba ta shiga a rude. Tsaye ta gan shi gaban madubi yana brushing kanshi sannan ga jakar shi a gefe, da alama tafiya zai yi. Tana sauke numfashi a dalilin gudun da tayi ne tace “Ya Farouq” Kallonta yayi cikin mamaki ba tare da yayi mata Magana ba sannan ya juya ya dauki cufflinks dinshi yana sakawa. Ta dan matsa kusa da shi tace “Ya Farouq ya kan naka, ya daina ciwo?” yace “eh” tace “tafiya zaka yi?” ya kalle ta yace “yes” Ba tare da tunanin wani abu ba tace “why” yace “I am a doctor remember?” Ya dauki jakar shi sannan yace “take care” ya fita. Zara wadda ta kasa motsi ta rasa dalilin da yasa bata so ya tafi ba. Gani nayi ta matsa ta zauna bisa kujerar dakin ta kifa kai ta fara kuka. Granny tana zaune a kan dinning Farouq ya fito riqe da jakar shi, cikin mamaki tace “ya na gan ka da jaka?” Yayi murmushi yace “ina da emergency ne Mi Lady, I have to reach Abuja today” Ganin Granny tana kallon shi cikin rashin yarda ne yace “okay not really, amma dai ina da abubuwan da zanyi please don’t stop me” Murmushi tayi tace “I wont, bazaka yi breakfast ba?” Zagayowa yayi har wurin da take ya dauki apple ya nuna mata sannan yayi hugging dinta yace “I am going to miss you Mi Lady” tace “me too, Allah ya kiyaye hanya. Take care” Granny dai ko da Farouq ya tafi ta dade zaune a dinning din bata ga Zara ba don haka ne ta miqe ta nufi wurinta. Tsaye take a bakin qofar dakin yayinda take kallonta tana kuka. Girgiza kai tayi tace “au, kuka kike yi saboda ya tafi? Toh me ya hana ki bin shi?” Zara ta dago kanta tace “ni fa ba don ya tafi nake kuka ba” Granny ta Harare ta tare da qarasawa ta zauna kusa da ita. Cikin tsokana tace "toh ko in ce ya dawo ne?" STORY CONTINUES BELOW Zara ta kwanta a jikin Granny ta cigaba da kuka wanda ko shaqe ta zaka yi bazata iya fada maka dalilin kukan nata ba. ********** Zara dai tunda Farouq ya tafi ta ji duk babu dadi, gaba daya ma bata wani sakin jiki tayi hira da Granny dinta kamar da. Ita kanta Granny ta kula da hakan amma ta zuba mata idanuwa. Bayan kwana biyu da tafiyar Farouq ne Zara ta hada kayan ta tayi ma Granny sallama akan zata tafi. Granny dai bata yi mamakin hakan ba domin kuwa ta kula da yanayin Zara wanda ta canza gaba daya tun ranar da Farouq ya tafi. Bayan sunyi sallama ne aka zuba kayan ta cikin boot sai Airport. AL-HUSSAIN MANSION A yau kwanan Zara daya da dawowa daga Adamawa. Kwance take a kan cinyar Mamy yayinda suke kallon tashar Zee Tv, Mamy dai a dalilin zara take kallon tashar domin kuwa duk lokacin da Zara zata zauna kallo toh fa Zee Tv ne. Mamy ce ta shafa kanta tace “wai ya maganar shirye shirye ne? na ga kin yi shiru haka shima yayi shiru” Zara ta turo baki tace “Mamy ni fa har yanzu ban yarda cewa Ya Farouq zan aura ba” Mamy tayi dariya sannan ta dauki wayarta ta kira layin Farouq. Bayan sun gaisa ne tace “hope you are not busy?” Yace “not at all Mamy” tace “ya maganan kayan lefen Zara?” Shafa kanshi yayi yace “Mamy kin dai san ko na Ruqayya ba ni nayi ba, ya za’ayi?” Mamy tayi murmushi tace “kamar yadda Ruqayyar ta hada nata ai itama sai ta hada nata ko kuwa?” Yace “ba matsala Mamy” Bayan sunyi sallama ne Mamy ta kalli Zara wadda hankalinta yake kan TV tace “sai ki shirya ku je ku hado kayan ke da Hafsat idan Mukhtar ya amince ko?” Zara tace “toh Mamy” ************ Da daddare bayan Farouq ya fito daga asibiti ne ya biyo gidan. Ya tarar da Mamy tana kallon labaru yayinda Zara take zaune akan kujera inda Larai take yi mata Oiling din gashin ta. Bayan sun gaisa da Mamy ne Zara ta dan dago kai tana murmushi tace “ina wuni Ya Farouq” Shima murmushi yayi yace “lafiya lau Princess din Mamy” Zara tana kallon shi tace "Princess din Mamy kadai?" Mamy tayi dariya yayinda Farouq yace "sorry Princess din Farouq" Dariya tayi tare da fadin "yesss" yayinda Mamy tace "Zara hoo" Suna cikin hira da Mamy ne suka ji zara tace “ouch” da qarfi. Cikin masifa tace “haba Larai ki bi ahankali mana, akwai zafi fa” Mamy ce tayi murmushi tace “na dai kusa hutawa da wannan halin naki, babu dama a taba kan ki sai ki ce zafi” Farouq ya kalli kan Zara yace “gashin nata yayi yawa ne ai Mamy” Mamy tayi dariya tace “tabarkallah, Zara akwai gashi ga tsawo ga cika, haka zaka je kayi ta fama da raki duk ranar da za’a yi kitso” Farouq yace “sai in sa a aske kan kowa ya huta” da sauri Zara tace “what??” Mamy da Larai suka fashe da dariya. Farouq ya miqe yace “Mamy ni zan tafi gida, I am a bit tired today” Ya ciro visa card dinshi ya miqa ma Zara yace “use this, zan aiko miki da Pin din” Bayan Zara ta karba ne yayi musu sallama ya tafi. Bai dade da tafiya ba wayar zara tayi qara alamun an aiko mata da message. Ta duba ta ga sunan Farouq. Ko da ta bude pin din ta gani sai saqo a qasa kamar haka: “its my savings account, idan kin ga dama ki kwashe duka ki zo kuma ki sha wahala a gida na”4 Zara dai fashewa da dariya tayi a ranta tace “aikuwa sai na kwashe su tas in ga yadda za’a yi” Reply ta tura mishi kamar haka: “wahalar na wata daya ne Ya Farouq, I can endure” Ko da ya gani yayi dariya sossai sannan ya tura mata saqo kamar haka: “you are crazy”2 Tana dariya ta tura mishi reply kamar haka: “and you are the best” Haka dai suka cigaba da chatting yayinda na koma gefe abuna..3 ************* MUKHTAR ABUBAKAR MANSION Zaune yake a falon abokin shi Mukhtar wanda bai dade da shigowa gidan ba.+ Suna buga game ne kamar kullum yayinda suke hira. Mukhtar ne yace "abokina wai kuwa Ruqayya ta san cewa zaka auri Zara?" Murmushi yayi tare da shafa kan shi yace "wallahi bata sani ba, I am going to tell her soon" Mukhtar ya girgiza kai yace "na san dai zata yi hauka" Kafin Farouq yayi Magana ne wayar shi tayi qara alamar an aiko mishi text message. Yau dai tun da safe yake ganin debit alert wanda hakan ya tabbatar mishi da cewa Zara ta fara operation. (Toh fa🤣) Ko da ya duba debit alert din ne dai, murmushi yayi sannan yace "toh ya zata yi abokina? Ai dole tayi haquri..." Wani message din ya sake shigowa ya duba. Wannan karon zaro idanuwa yayi yayinda Mukhtar yace "abokina lafiya?" Farouq yace "I am so in trouble, she is gonna wipe out my whole savings"2 (Habawa...🤣) Mukhtar ya fashe da dariya yace "ai gara ta taya ka kashe su tunda dama sunyi maka yawa" Kafin Farouq yayi magana wani message din ya shigo, girgiza kai yayi yace "I swear she is crazy but I still love her" (Hmmm🙄) Mukhtar yana dariya yace "Allah dai ya baka ikon yin adalci a tsakanin su" Farouq yayi murmushi yace "dole in qoqarta abokina, bazan so in ci wutar Allah ba" Mukhtar ya fashe da dariya yayinda yace "zan dai taya ka da addu'a abokina" (Nima dai zan taya ka da addu'a Farouq🤣)2 Haka dai debit alert ya dinga shigowa wayar Farouq wanda Mukhtar din ya dinga yi mishi dariya. AL-HUSSAIN SUITE BURJ AL ARAB DUBAI Zara ce kwance a kan kujerar falon suite din inda take ta hira da Mahmood a waya yayinda qawarta take mamaki. Bayan ta gama wayar ne Hafsat tace "wai babes baki gaya ma Mahmood aure zakiyi ba? kin fa san an sa ranar bikin ki yakamata ki rabu da shi hakanan" Zara tayi murmushi tace "wallahi bestie ban fada mishi ba, ni na ma kasa fada mishi ne gaskiya. Amma idan mun koma i will try and tell him. Kin ga fa shima Ya farouq baya damuwa tunda ko da muke Adamawa a gaban shi Mahmood ya zo na fita kuma bai ce komai ba" Hafsat tayi tsaki tace "amma dai kin sani sarai that was wrong ko?" Zara ta turo baki tace "toh hajiya tashi mu shirya mu je wurin Galiafahad, kin san appointment dinmu is gonna be in an hour's time". ************ Da yamma ne suka je wurin Galiafahad wanda shine zai dinka ma Zara kayan bikin ta. Kayan da ta zaba kuwa masu tsada ne na bala'i har Hafsat tana fadin "ke hajiya, kudin nan fa ba a banza ake samun su ba, ki tausaya ma bawan Allah mana" STORY CONTINUES BELOW Zara tace "toh ni me ya ruwana, ba shi ya bani ba?" Aikuwa Galiafahad ya kwashi miliyoyin kudade masu yawa. Hafsat dai ta tausaya ma Farouq yadda ta ga kudaden shi suna ta bacewa. (Hahahaha) Haka Zara ta dinga kashe kudade wanda duk na kayan da zata sanya ne na bikin. Ko kayan lefen ma basu fara hadawa ba amma miliyoyin kudi sun riga sun bace. Wasu kayayyakin ma babu abinda zata yi da su amma a dalilin tana so ta qure account din Farouq take siyan su. Har London da France sun je wai duk ana siyan kayan biki. Da dai Zara ta ga alama account din nashi infinity ne sai ta haqura suka dawo gida. (Habawa.. ai da gangan kika yi hakan Zara🤔) CENTRAL HOSPITAL Yau kwana biyu kenan da dawowar su. Zara ce ta shigo ofis dinshi kamar kullum babu sallama. Ta tarar da shi yana waya da gynaecologist dinshi wadda take yi mishi bayanin wani complicated C-section da suka yi cikin dare. Kamar kullum zuwa tayi ta tsaya mishi a kai yayinda ya dago ya kalle ta cikin mamaki sannan ya cigaba da wayar shi. Ji tayi yana fadin "you did great honestly, weldone. Infact you deserve a treat from me, perhaps Dinner??" Can kuma sai yayi dariya yace "okay thanks dear, I will see you later". Bayan ya gama wayar ne yace "lafiya kika tsaya mun kamar bodyguard?" (Ah toh.. nima dai haka na gani🤣) Ran ta a bace tace "wacece ka gama waya da ita?" Zaro idanuwa yayi cikin mamaki yace "whoa, ashe dai da gaskiyar Mi Lady da tace kina da kishi..." Bata bari ya qarasa maganar shi ba tace "ni fa ba kishi nake yi ba, kawai dai ina so in sani ne" Murmushi yayi yana kallonta wanda yasa tace "manta kawai bana ma so in sani" Wayar shi ya miqa mata yace "call her and confirm" Gani nayi Zara ta karba tayi dialling last call din da yayi sannan ta kai kunnen ta. (🙄🙄🙄... ni kuwa nace kai!!!) Farouq dai kallonta yake yi cikin mamaki yayinda ran ta yake a bace. Har wata girgiza na ga tana yi. (🤣🤣🤣) Cikin Sallama Gyneacologist din ta amsa tare da fadin "Sir, you forgot to tell me something?" Zara tace "yeah, go to hell" ta kashe wayar. (Me zanyi banda dariya🤣🤣) Cikin mamaki Farouq ya zaro idanuwa yace "what??? Me tayi miki??" Gani nayi ta jefar mishi da wayar ta juya zata tafi. Da sauri ya riqo hannun ta yace "hey, ina zaki je?" Tace "ka qyale ni in tafi" Yace "why? Are you jealous? Like seriously?" Cikin masifa tace "no I am not, I just... I just..." Visa card dinshi ta fiddo ta jefa mishi a kan tebir dinshi tace "dama ga abinda na dawo maka da shi nan" sannan ta juya zata tafi. Jin muryar shi tayi yana fadin "idan kika fita daga ofis dinnan ba tare da nayi miki izini ba I will deal with you" STORY CONTINUES BELOW Tsayawa tayi cak ba tare da ta juyo ba. Wayar shi ya dauka ya kira gynaecologist din yace ta zo ofis dinshi yanzu nan. A rude ta shigo ofis din inda ta tarar da Zara a tsaye tana kuka. Farouq ne ya kalli gynaecologist din wadda hankalinta yake a tashe tace "sir, what have I done wrong?" Farouq yayi murmushi yace "nothing Dr Nila, its my sister who wants to meet you" Zara ce ta Harare shi yayinda Dr Nila ta miqa mata hannu tace "please to meet you Madam" Zara ta miqa mata hannu ba tare da tace komai ba. Farouq ya kalli Zara yace "she is one of my gynaecologists from Turkey, baki san ta ba because she is new here" Ya kalli Dr Nila yace "that will be all Doctor" Bayan Dr Nila ta tafi Farouq ya zagayo ta bayan Zara yace "I am sorry, I will be careful not to arouse your jealousy next time" Zara dai a guje ta bar ofis din cikin bacin rai hade da kunya. A bangaren Farouq kuwa tana fita yace "weldone Farouq, you don't have much to do at this point in time" (Hahaha... nima dai ina maqale a gefe nace ka riqe wuta Farouq🤣) ********** Wasa wasa dai lokacin biki yana ta matsowa. Tun daga ranar da Zara ta ji haushin Farouq bata qara ganin shi ba. Asali ma idan ya zo gidan har ya qarashi zaman shi ya tafi bata fitowa. Duk lokacin da ya zo gidan makulli take sakawa ta rufe qofar dakinta. Idan ya kira ta a waya bata dauka, haka text messages din shi ma bata replying dukda dama yawanci na tsokana ne. A bangaren shi dai ya gano cewa lallai Zara ta damu da shi fiye da yadda yayi zato, don haka ne bai damu da shariyar da tayi mishi ba. Zara dai kasa fada ma Mahmood tayi cewar zata yi aure. Har yanzu kuwa kamar kullum suna hira da juna a waya sossai amma fa ta qi barin shi ya zo gida saboda tsaro. (Hahahaha... Mahmood dai ya sha qasa💃) ************* Tuni an fara shirye shiryen bikin Zara da Farouq. Hidima sossai Mamy take yi. Tun ana saura wata daya ne su Anty da 'yan biyu suka zo Nigeria dayake 'yan biyu suna hutun makaranta. Musamman Mamy ta gayyato wata shaharariyar mai gyaran jiki daga qasar Egypt mai suna Layla Hayat don tayi ma Zara gyaran jiki. Zara dai bata son wannan abubuwan amma akan dole Mamy ta tilasta mata, dare da rana Layla Hayat aikin ta take yi akan Zara. Cikin lokaci qanqani Zara ta koma kamar tsada, gaba daya Zara glowing take yi. Jikinta yayi kyau yayi laushi, gashinta wanda take fama da shi tuni Layla ta gyare mata shi da mayyuka kala kala yayi laushin gaske har ana mamaki. A duk inda Zara ta zauna babu abinda kake ji sai qamshi. ************ Su Safa ne suke zaune a kan gadon dakin Zara suna hira daddare yayinda Zara take bathroom dinta tana wanka wanda Layla ta hada mata wasu turaruka a cikin ruwan wankan. Kamar kullum kuwa sai da tayi kusan awa daya tana wanka. Zara ta fito daure da tawul a jikinta ne Saima ta kalle ta tace "kai Zara, kin ga yadda kike ta glowing duk kin bi kin canza kuwa? anya Ya Farouq zai iya adalci a tsakanin ki da Anty Ruqy kuwa?" Su Safa suka fashe da dariya yayinda Zara ta harare su tace "an gaya muku sona yake da har adalci zaiyi mishi wahala?" Marwa tace "hmmm, ni fa gani nake yi kamar Ya Farouq yana son ki" Safa tace "kuma ke ma mun san son shi kike Anty Zara" Zara ta zauna gaban dressing mirror dinta tace "Ya Farouq is my brother and he will forever be" Suka fashe da dariya yayinda Saima tace "hmmm, mun ji ki gimbiya" Marwa ce tace "wai Anty baku yi pre-wedding pictures bane?" Safa ce ta matsa kusa da Zara tace "aikuwa yakamata kuyi, I know very well cewa burinki ne idan zakiyi aure" Zara dai sai yanzu take tunanin lallai fa bata yi pre-wedding picture ba kuma kamar yadda Safa ta fada, its her dream idan zata yi aure. Daga nan kuma sai ta fara tunanin yadda zata sa Farouq yin Pre-wedding picture. A ranta tace "I have to find a way to make him" (Hahahaha... babban magana🤣) Zara wadda ta kalli kanta a madubi har tsoron kyan da tayi take, bata taba sanin tana da kyau haka ba sai da ta sha gyara a wurin Layla. Gani nayi tayi murmushi sannan ta cigaba da shafe shafen mayyuka a cikin wadanda Layla ta bata ta dinga shafawa. FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION A yau saura sati biyu bikin Zara da Farouq. Ruqayya ce kwance a kan gadon ta yayinda take chatting da Musty. Har yanzu dai rigima take yi da shi akan Junior, Musty ya dage akan lallai Junior yaron shi ne yayinda ta kafe akan na Farouq ne. (Habawa madam Ruqs🤔) Farouq ne ya shigo dakin riqe da Junior a hannun shi wanda ya dauko shi daga wurin nanny dinshi. Dago kai tayi ta kalle shi yayinda tace "Honey har ka dawo? Yi haquri ban ji shigowar ka ba" Murmushi yayi yace "its okay" Qarasowa wurinta yayi ya zauna gefenta tare da ajiye Junior a kan gadon yace "how was your day" Ruqayya ta matsa kusa da shi tayi mishi kiss a kumatu tace "it was good Honey" Yace "bari in je in watsa ruwa in zo, akwai maganar da nake so muyi" tayi murmushi tace "its okay" *********** Kwance take a kan cinyar shi a Falon shi inda ta natsu tana sauraron abinda Farouq yake so ya fada mata. Gyaran murya yayi yace "wifey you know I care about you right?" Shiru ta dan yi tace "yes I know Honey, please tell me, me ke faruwa?" (Ghen ghen ghen🙄) Kai tsaye yace "I am getting married" Miqewa tayi tsaye a firgice tace "what???" tare da dafe qirji. Hannunta ya riqo yace "please sit" Ruqayya dai tana nan a tsaye tana kallon shi yayinda hawaye ke bin fuskar ta. Shafa kanshi yayi yace "uhm, I am getting married to Zara in two..." Kafin ya qarasa maganar shi ne ta kurma wani irin ihu tace "Noooo, wallahi baku isa ba"2 Ni kuwa da ihun Ruqayya ya firgita ni ban san lokacin da na ruga na fita daga falon a guje ba... 🤣 ********** Farouq ne rungume da Ruqayya yana fadin “please listen to me, su Abba ne suka hada auren…”2 Cikin masifa Ruqayya tace “dama can kuna son juna, babu wani munafircin da za’a yi mun” Fizgewa tayi daga jikin shi tace “ni bazan taba zama tare da karuwar yarinyar nan ba a matsayin kishiya” Cikin bacin rai na ji yace “what?” Nuna ta yayi da yatsa yace “kar ki kuskura ki sake kiran Zara karuwa, she is my sister and my wife to be, she deserves some respect” Ya miqe yace “just accept the fact and move on, zan tura miki kudi a account idan basu ishe ki ba let me know”. Ya wuce ya nufi dakin shi. Ruqayya kuwa zamewa tayi qasa ta dinga rusa kuka, da qyar ta laluba ta nufi dakinta. Haka Ruqayya ta raba dare tana kuka. Kafin safe kuwa ta fita hayyacin ta. Ruqayya dai ta sani sarai idan Farouq ya auri Zara toh fa kashinta ya bushe a gidan don kuwa abinda boka cika aiki ya fada shine yake nema ya tabbata. Washegari tun da safe ta tattara kayanta ta dauki Junior ta bar gidan. A bakin masu aiki Farouq yake jin cewa Ruqayya ta tafi. Ran shi ya baci da jin hakan amma ya matse. A cewar shi idan ta gaji zata dawo da kanta. (Da kyau Ruku🤣) ALH ABUBAKAR BULAMA MANSION Ruqayya tana kwance a kan cinyar Hajjaju tana ta rusa kuka yayinda Hajjajun take ta mamakin abinda ya faru wanda ma ba abin mamaki bane tunda dai boka cika aiki ya fada musu hakan zata faru. Cikin kuka Ruqayya tace “wallahi Hajjaju bazan iya zama da Zara ba, ‘yar iskar yarinya ce. Dan zaman da tayi a gidana lokacin da su Mamy suka yi tafiya hawan jini ne kawai bata sa mun ba” Hajjaju tace “toh yanzu ya kike so mu yi?” Ruqayya tace “kawai mu nemo wani bokan ko nawa ne zan biya, dama jiya ya aiko mun da millions of naira a account dina, I have enough money to pay ko ma nawa ne as long as za’a kauda mun Zara daga rayuwata” Hajjaju ta dan yi shiru sannan tace “bari zanyi ma Hajiya Baraka Magana idan ta dawo daga India, kamar akwai wani malaminta a Cotonou, qila ya taimaka” Ruqayya tace “thank you Hajjaju” Hajjaju tace “amma yanzu haka zaki zauna bazaki koma gidan ba, ai gara ko daular ki ci ki more” (Hajjaju fa kudi kawai suka dame ta a rayuwa🤣🤣🤣)2 Ruqayya tace “ni bazan koma ba, sai yazo da kan shi” Hajjaju tace “toh shikenan” STORY CONTINUES BELOW CENTRAL HOSPITAL Zaune yake a ofis dinshi tare da Dr Ibrahim inda suke discussing issue din wani patient. Wayar shi ce tayi qara alamar an turo mishi text message. Sunan Zara ya gani da saqo kamar haka: “zamu je daukar Pre-wedding pictures” Dr Ibrahim dai gani yayi Farouq ya fashe da dariya. Cikin mamaki yace “Sir, lafiya kuwa?” Farouq yana typing message ne yace “nothing Dr Ibrahim” Ya tura mata reply kamar haka: “toh sai kun dawo” Daga nan kuwa bata sake yi mishi Magana ba. ************* Yana nan zaune tare da Dr Ibrahim suna ta reviewing case din patient din ne ta shigo ofis din kamar kullum babu sallama. Farouq dai ganin Zara tsayawa yayi yana qare mata kallo, ta masifar yin kyau sannan ta canza gaba daya sai qyalli take. Sanye take da jallabiya baqa mai masifar kyau wadda ta dace da jikinta. Nan da nan wani kishi ya rufe shi a dalilin gani da yayi tana gaisawa da Dr Ibrahim wanda har washe mishi baki tayi suna hira. Ji suka yi yace “ehm, Dr Ibrahim please can we finish up later?” Dr Ibrahim ya miqe yace "okay Sir, Excuse me please" sannan ya fita. Rabon da su hadu da juna tun ranar da tayi fushi a ofis dinshi. Dukkanin su sunyi missing din ganin juna sossai. Gani nayi sun qura ma juna ido babu ko qyaftawa. Wayar shi ce da tayi ringing ta sa suka ankara. Gani nayi ya amsa wayar yana kallonta yayinda itama take kallon shi yace “okay, I will call you later” bayan ya kashe wayar shi ne ya nuna mata wayar tare da fadin “sorry that was my secretary” Gani nayi tayi Ajiyar zuciya ta zauna tare da fadin “ina wuni Ya Farouq”9 Yana kallonta yace “lafiya my beautiful Amarya” da sauri ta kalle shi cike da mamaki yayinda yace “what? Atleast for a month” gani nayi tayi murmushi.2 Farouq dai kasa cire idanuwan shi yayi daga kan Zara. Ji yayi tace “ehm dama maganar Pre-wedding picture..” kafin ta qarasa yace “ba mun gama maganar ba?” Tace “toh ai tare da kai zamu je” Ya zaro idanuwa yace “what?? Ko aure na da Ruqayya bamu yi wadannan abubuwan ba balle ke da auren wata daya ne” Sai kuma na ga yayi murmushi yace “except if you are planning to spend the rest of your life with me”6 Da sauri ta kalle shi sannan ta duqar da kanta. Zara dai gani take yi kamar Farouq yana sonta idan yana fadin wasu abubuwa. Wata zuciya ce tace “babu wani sonki da yake, don dai baya da choice ne shiyasa”5 STORY CONTINUES BELOW Muryar shi ta ji yana fadin “kawai ki je kiyi hoton ki ke kadai” Gani nayi ta miqe ta zagaya ta wurin shi tayi Kneel down yayinda hawaye suka fara bin fuskarta tace “please Ya Farouq” Cikin mamaki yace “whoa, meye haka? Please stand up” Ya shafa kanshi yace “yanzu saboda nace bazan je ba shine har da kuka? Is it that important to you?” Cikin shagwaba tace “it is very important to me ya Farouq please” Gani nayi yayi shiru yana tunani, can kuma sai yace “gaskiya ni takura mun kawai zakiyi, I am only going because its you” Miqewa tayi cikin murna zata rungume shi kamar kullum sai kuma na ga ta ja baya da sauri wanda yasa Farouq yayi murmushi yace “iyyeh, Princess din Farouq ta girma”3 Turo baki tayi ta koma ta dauki wayarta da makullin motarta. Yana kallonta yace “let me know when you are ready” tace “okay, thank you big brother” sannan ta wuce zata fita. Har ta kai qofa ne yace “hey I forgot something” ta juyo da sauri tace “what Ya farouq?” yace “you look beautiful” tare da kashe mata ido kamar dai yadda take yi mishi.2 Bata san lokacin da tayi murmushi ba ta fita. Haka dai Zara ta fita ta bar qamshinta wanda ya mamaye ofis din yayinda ya lumshe idanuwan shi yace “how I love this girl”6 *********** Washegari direban Mamy ne ya kai Zara studio din Jide wanda daga can ne Farouq zai dauke ta su tafi daukar hoton. Tare da su Saima ta je wadanda suka nace mata akan lallai suna so su ga irin hotunan da za’a dauka. Bayan Jide ya gama yi ma Zara kwalliya ne ta sanar da Farouq kamar dai yadda suka tsara. Zara kuwa tayi masifar kyau, masha Allah. Studio din BigH suka je wanda ya riga yayi decoration mai masifar kyau kamar yadda Zara tayi requesting. Farouq dai har mamaki yayi yadda ya ga anyi setting komai. Ya amince lallai hoton is very important to her. BigH dai ya kwashi kudade domin kuwa aikin shi yayi kyau. ************ A kan hanyar su na dawowa gida cikin motar Farouq, Zara tana zaune a gaba yayinda su Safa suna baya. Saima ce tace “Ya Farouq gaskiya mu ka kai mu shopping” Zara ce ta waigo ta Harare ta tace “meye zaku siya wanda baku da shi?” Farouq yayi dariya yayinda Saima tace “toh gimbiya, ke dai kawai ki ce ba kya so mu ci kudin Mijin naki ne” Zara cikin bacin rai tace “aikuwa bazaku ci ba” Marwa ce tace “yi haquri Anty Zara, ba dayawa zamu ci ba” Zara tace “ba fa zamu je ba” Farouq yana dariya yace “tunda Princess tace baza’a je ba then so be it” Da sauri Saima ta matso ta bayan Zara tace “please Zara, kiyi haquri toh” STORY CONTINUES BELOW Zara ta turo baki tace “Na haqura” ba tare da ta kalle shi ba tace “mu je” Yayi murmushi yace “your wish is my command princess” Da sauri ta dago kai ta kalle shi yayinda tayi murmushi a dalilin jin dadin maganar da yayi. Ji suka yi Saima tace “hmmm, power of love, Ya Farouq haka dama kake son Zara? Who would've thought so” murmushi yayi yace “amma ita bata sona ba”2 Da sauri Zara ta qara kallon fuskar shi wadda ta nuna alamun dagaske yake akan maganar da yayi. Tambayar kanta tayi a ranta “da ace Farouq yana sonta dagaske, shin itama zata so shi??” Gani nayi ta girgiza kai tare da yin murmushi. SHOPRITE ABUJA Tafe suke yayinda suke ta daukan abubuwan da suke so a Mall din. Safa da marwa ne suka tsaya a bangaren Chocolates yayinda Saima ta janyo ra’ayin Farouq suka nufi wurin plates na Games. Zara wadda take tsaye nesa da su kallon su take yi yayinda suke ta hirar wani sabon FIFA da yake hannun Saima, ran ta yayi mugun baci ganin har dariya yake yi. Juyawa tayi ta cigaba da tafiya abinta, tsayawa tayi a gaban wani counter yayinda zuciyarta take tafasa. Ita ta rasa dalilin da yasa idan ta ga mace a kusa da Farouq take jin haushi. Zara dai tayi nisa a tunani ne ta ji muryar shi a daidai saitin kunnen ta inda yace “shi kike so in ciro miki?” A firgice Zara ta dago kai ta kalli hannun ta da yake kan wani shegen sexy Lingerie wanda yasa ta zaro idanuwa tare da cire hannun ta da sauri.3 A rude ta dan kalle shi cikin jin kunya tace “Ya Farouq ba fa…” Matsawa yayi daf da ita yace “okay na gane. Mu je toh, I think sun gama” Zara dai duk ta bi ta rude, ta zo wucewa ta gaban shi ne ta ji ya riqo hannunta. Jikin counter din ya jingina ta ya sa hannuwan shi a jikin counter din ya tare ta don kar ta gudu sannan ya duqo saitin fuskar ta yace “I am sorry again”. Cikin mamaki tace “for what?” murmushi yayi yace “for the raeson you had to come here” tare da nuna Lingerie din. Mutanen da suke ta wucewa a shagon ne suke ta kallonsu yayinda ake ta nuna su ana yi musu dariya. Zara dai kasa Magana tayi tana murmushi. Ganin ana ta kallon su ne yasa ta tura shi baya tace “ana kallon mu fa” Ajiyar zuciya yayi yace “who cares right?” Girgiza kai tayi ta fashe da dariya yayinda ta ji yace “Good job Farouq, atleast your apology has been accepted” *********** Ko da suke hanyar dawowa su Saima ne suke ta yi ma Farouq tsiya akan abinda yayi a Mall din yayinda Zara tayi shiru tana ta sauraren su. Ita kanta mamaki yake bata yanzu. A da tayi tunanin yayan nata baya sakin fuska har ayi wasa da shi amma kuma a yanzu sai ta ga sabanin hakan. STORY CONTINUES BELOW ************* AL-HUSSAIN MANSION Washegari da safe wuraren qarfe goma Hafsat ta zo gidan su Zara inda suka cigaba da tsare tsaren su na biki. Larai ce tayi sallama ta shigo da wani qaton package tace “Anty Zara wani delivery man ya kawo saqo wai a baki” Zara cikin mamaki tace “daga ina?” Larai tace “wallahi bai fada ba” Zara tace “toh nagode, you may go” Bayan Larai ta fita ne Hafsat tace “waye wannan kuma? Bestie bude mu gani, na qagara in gani because the packaging looks classy” Zara tana murmushi ta sauka ta bude. Zaro idanuwa tayi tace “na shiga uku bestie” Hafsat ta sauka daga kan gado ta nufi wurin Zara don ganin abinda yake ciki. Gani nayi itama ta zaro idanuwa. Wayarta ce tayi qara alamun text message wanda tana dubawa ta ga sunnan Farouq. Message ne ya turo kamar haka: “They are thirty for thirty days equivalent to one month, hope you will like my wedding gift, have a nice day”2 Zara dai sakin wayar tayi tare da zaro idanuwa, bakin ta a bude cikin tsananin mamaki yayinda Hafsat tace “bestie waye ya aiko miki da Lingeries dayawa haka? Wallahi idan Ya Farouq ya kama ko ma waye…”3 Zara ce ta katse ta tare da fadin “shi ya aiko” Hafsat ta kalli Zara cikin mamaki tace “what??” daga nan kuma sai ta fashe da dariya. Zara dai har yanzu ta kasa Magana. Hafsat tana dariya tace “bestie akwai kwasar soyayya kenan a gidan Ya Farouq” Zara ta turo baki tace “wallahi Ya Farouq bai kyauta mun ba” Hafsat tace “meye abun rashin kyautawa a nan? Go jor” Haka dai Zara ta dinga masifa yayinda Hafsat take ta kwasar dariya. ************ Tuni dai Pre-wedding pictures din su Zara ya zagaya duniya. Ko ina labarin auren su ake yi. Social media ko wanne page sai ka ga hoton su Zara. Complements din da Zara ta dinga receiving kuwa har sun ishe ta saboda yawa. Ko da Mahmood ya gani yayi mamaki matuqa. Hankalin shi ya tashi domin kuwa ya sa ran zai samu Zara ko da kuwa auren ta ne zaiyi dukda ba hakan ya so ba. Ya kira ta a waya ya fi a qirga amma ta kasa dagawa. Babu abinda zata iya fada mishi, kunyar shi take ji sossai. Text messages ma idan ya aiko mata sai dai ta karanta ta fashe da kuka, ta kasa replying mishi ko daya. (Ni kuwa nace uhmmm🤔) ALHAJI ABUBAKAR BULAMA MANSION Ruqayya tana kwance a dakin ta tana ta faman saqe saqen yadda zata yi da auren Farouq ne Aliya ta shigo. Aliya ta Harare ta tace “wai ke kullum baki da aiki sai zama daki” Ruqayya tace “toh me kike so inyi qawata banda wannan?, gaba daya komai yayi mun zafi” Aliya ta gyara zama tace “aikuwa babu abinda zaki iya yi domin kuwa Farouq da Zara sun gama zagaya duniya” Ruqayya wadda take kwance ta tashi zaune tace “ban gane ba qawata” Aliya ta miqa mata wayarta tace “kalli ki gani”2 Hankalin Ruqayya a tashe ganin hotunan Pre-wedding pictures din su Farouq da yadda suka yi bala’in kyau. Babu qarya ko maqiyan su suka yi tozali da hotunan sai dai su kauda kai domin kuwa sun masifar yin kyau, Perfect match. Bata qarasa kallo ba na ga tayi wurgi da wayar Aliya ta fashe da kuka. Aliya ta dauki wayarta tace “ni dai na ga fa ba lokacin kuka bane yanzu, tashi zakiyi ki san abin yi” Ruqayya cikin kuka tace “na shiga uku, me zanyi Aliya? Farouq ya cuce ni da ya hada ni da 'yar iskar yarinyar nan” Aliya tace “kin tabbata ba gara ki koma gidan Farouq ba kuwa? Ko kin haqura kin bar mata ne?” Cikin kuka Ruqayya tace “wallahi bazan koma ba sai ya zo da kanshi” (Ni kuwa nace anya Ruqayya??? Farouq zai waiwayo ki kuwa???🙄)2 ************* Uhmmm... Wai yaushe asirin Ruqs zai tonu ne mu rabu da ita mu huta???😡

Post a Comment for "BA SONTA NAKE BA CHAPTER 10"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...