BA SONTA NAKE BA CHAPTER 1 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BA SONTA NAKE BA CHAPTER 1

BA SONTA NAKE BA CHAPTER 1

- - Post a Comment
BA SONTA NAKE BA CHAPTER 1
THUMBAY HOSPITAL DUBAI Kwance take a kan gadon asibitin, babu abinda ke motsi a jikin ta sai qirjinta wanda yake hawa da sauka a hankali. An jona mata na’urar EKG wadda take recording din motsin da zuciyar ta take yi a kowane daqiqa. Hannun ta na dama dauke da robar drip. Ahankali ya bude qofar dakin inda suka shigo tare da likita yayinda wata nos take biye da su a baya. Idanuwan shi suka sauka a kanta, da ganin fuskar shi kasan hankalin shi a tashe yake. Ajiyar zuciya yayi tare da kallon likitan yace “So Dr. Zayyad when can she leave?” Dr Zayyad ya kalli Zara wadda take kwance yace “it all depends on when she wakes up, it might take days or even weeks”. Shafa gashin kanshi yayi cikin wani irin boyayyen tashin hankali yace “can I stay with her for a while?” Dr Zayyad yayi murmushi yace “why not? I will be in my office incase you need me even though I am certain that she is safe with you” ya dan yi murmushi yace “how so?” doctor din yace “you are her doctor, remember?” ya girgiza kai yace “but you are in charge here” likitan yayi dariya tare da bugun kafadar shi sannan suka fita tare da Nos din suka bar shi a tsaye yana kallon ta. A hankali ya tako ya nufo gadonta ya zauna a gefe sannan ya qura mata ido. Bai taba tunanin cewa a rana irin ta yau zai zo Dubai ba, sai gashi Zara tayi sanadin zuwan shi babu shiri. A duk lokacin da ciwon Zara ya tashi wani irin mugun tashin hankali yake shiga wanda shi kan shi bai san dalili ba. Yanzu haka ko da ya qura mata ido addu’a kawai yake yi akan Allah ya bata ikon farfadowa da wuri domin kuwa shi kadai ya san yadda yake ji a duk lokacin da ta shiga irin wannan halin a yayinda ake jiran farfadowar ta. Yayi kusan minti goma sha biyar yana monitoring din EKG machine din, Ajiyar zuciya yayi sannan ya kai hannun shi ya dan taba hannun ta na hagu. Kamar wadda aka yi ma shocking ya ji ta riqe hannun shi gam. idanuwan ta a rufe tace “Ya Farouq.. Ya farouq… ya…” kallon fuskar ta yayi cikin mamaki sannan yace “ssshhhh”. A gajiye ta bude idanuwan ta tana kallon shi yayinda shima yake kallon ta. Murmushi tayi mishi wanda ya mayar mata da harara yace “how are you feeling?” Zaro idanuwa tayi yayinda ta bi dakin da kallo sannan ta kalli hannun ta da yake dauke da drip tace “me ya faru da ni? Ya akayi na zo asibiti?” fuskar shi a murtuke yace “they found you lying on the floor unconscious” ajiyar zuciya tayi tare da tuno halin da ta shiga a lokacin da ta zame ta fadi. Wata na’ura ya danna wanda cikin mintoci kadan Dr Zayyad tare da Nurse dinshi suka shigo. Ganin Zara a farke ya ba likitan mamaki matuqa domin kuwa bai sa ran zata farka nan da kwanaki uku ba ma domin yanayin yadda jikin nata ya nuna. Ko da ya qaraso murmushi yayi yace “welcome back Mrs Farouq” cikin mamaki Farouq ya dago ya kalle shi yayin da Zara tayi murmushi. Farouq yace “hey Doc, she is not..” doctor zayyad ya dakatar da shi yace “its evident that she will be even if she is not because this just proves that your hearts are connected”. Farouq dai saboda bacin rai miqewa ma yayi ya koma nesa da su ya zauna yana duba wayar shi. Bayan Dr Zayyad ya gama dudduba Zara ne yayi disconnecting din EKG din sannan ya dawo wurin Farouq yace mishi “I think I will discharge her later, she has gotten what she wants and basically she doesn’t need my services anymore” Farouq dai ya gane sarai abinda likitan yake nufi don haka ne ma ko kallon shi bai yi ba har ya fita yana dariya.2 STORY CONTINUES BELOW Muryar shi ta ji yace “are you okay?” cikin shagwaba tace “Ya Farouq ya akayi ka zo? Are you not supposed to be…” zaro idanuwa tayi tace “inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un, Ya Farouq yau ranar bikin ka” cikin rudani ta taso daga kwanciyar tace “Ya Farouq please Forgive me, toh wai ma wa yace su kira ka?” shi dai Farouq tunda ta fara Magana bai qara kallon ta ba domin kuwa ba son surutun Zara yake yi ba. wayar shi ya cigaba da latsawa abinshi. Jin tayi shiru ne yasa ya miqe yana fadin “do you need anything” turo baki tayi ta koma ta kwanta cikin shagwaba tace “ice cream” juyawa yayi ya fita yayinda ta bi shi da kallo tana mamakin yadda ya baro bikin shi ya zo wurin ta. Ta sani sarai sai ya hukunta ta akan hakan wanda ita da kanta tasan bata kyauta ba, toh amma kuma ai ba laifin ta bane. Tana nan kwance farouq ya shigo riqe da favourite flavour na ice cream dinta wato Vanilla. Cikin murna ta tashi zaune ta karba tare da fadin “thank you Ya farouq” ganin yanayin ta a yanzu sai ka rantse qarya take lafiyar ta qalau. Haka Zara take, baka taba gane bata da lafiya koda kuwa tana bisa gadon asibiti domin kuwa she is a vibrant person and so full of life. Ganin ya juya ne yasa tace “Ya Farouq ka dan bude mun please” ya juyo zai fara mata masifa ne ta dago hannun ta wanda yake dauke da drip tare da kashe mishi ido daya. Karba yayi ya bude mata sannan ya miqa mata, qin karba tayi tana kallon shi yayinda shima yake kallon ta fuska a murtuke. Cikin shagwaba tace “Ya Farouq drip din hannu na yana mun ciwo kuma ma a hannun dama ne, ka bani da kanka” cikin bacin rai ya dalla mata wata muguwar harara sannan ya juya ya danna na’ura wanda cikin daqiqoqin da basu wuce uku ba wata Nos ta shigo. Farouq ya miqa mata robar Ice cream din yace “help her please” Nos din ta karba yayinda Zara ta bi shi da kallo cikin jin haushi har ya koma kan kujera nesa da su ya zauna. Zara tana zaune tana shan Ice cream din tana kallon shi, wayar shi ce tayi qara ya fiddo daga aljihun shi ya duba. Gani tayi yayi murmushi ya amsa tare da kai wayar kunnen shi yace “hello Mamy” a can bangaren Mamy tace “Farouq how is she?” ya shafa kanshi sannan yace “she is fine Mamy, its not serious. I think any moment ma zasu sallame ta. Tell me hows the tension over there?”+ Mamy tace “well, gashinan dai mun dawo gida amma yakamata ka kira Ruqayya domin da alama ran ta ya baci matuqa, nobody could calm her down har aka bar dinner dinnan. You should have called her ai ka gaya mata abinda ya faru” ajiyar zuciya yayi yace “wallahi Mamy I wasn’t thinking straight ne but zan kira ta yanzu” mamy tace “ka gaida mun Zara, I will call to hear her voice anjima”. Bayan yayi sallama da Mamy ne ya kira layin Ruqayya kusan sau hudu amma bata amsa ba. tsaki yayi yace a ranshi “idan kin sauko zaki neme ni da kanki”. Zara dai tana kallon shi har ta shanye ice cream din tayi ma Nos din godiya. FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION MAITAMA ABUJA Kwance take a bisa tangamemen gadon ta a sabon dakin ta wanda ya kasance dakin auren ta. Kuka take yi sossai yayinda qawar ta Aliya take kusa da ita tana bata haquri. Tun daren jiya da aka kawo ta gidan take kuka wanda idan tayi ta gaji sai ta koma ajiyar zuciya idan kuma ta tuno da wulaqancin da yayi mata sai ta rushe da kuka. Haka dai suka kwana basu runtsa ba daga ita har Aliya. Idanuwan ta duk sun kumbura sunyi ja. Muryar mahaifiyarta ta ji cikin fushi tana masifa. Shigowar ta kenan tana fadin “ai ga irinta nan ya tsallake ya tafi ya bar ki a ranar bikin ku, yana can yana holewa da karuwar yarinyar nan. Ai dama sai da na gaya miki kada ki aure shi kika nace sai shi, dama kin tashi kin daura damarar yaqi domin kuwa wannan yarinyar dukda ba auran ta yayi ba wallahi kishiya ce a gare ki” tayi tsaki tace “ai da ba’a riga an daura auren nan ba wallahi sai dai a fasa shi”. Ruqayya ta dago fuskarta ta kalli mahaifiyar ta tace “kishiya Hajjaju? Wallahi bata isa ba, ni kadai ce matar Farouq babu wata har abada” kalaman Hajjaju suka sa ta bude wani babi na kuka yayinda Aliya ta janyota ta cigaba da bata haquri. 1 AL-HUSSAIN SUITE (BURJ AL ARAB- DUBAI) Kwance take a falon suite din da ya kasance na Al-Hussain Umar Jimeta wanda a nan iyalin gidanshi suke sauka a duk lokacin da suka zo Dubai. Magana take a waya da Mamy wadda take tambayar ta yanayin jikin nata yayinda take ta buga mata shagwaba kamar kullum. Farouq ne ya shigo falon cikin sallama. Da sauri ta tashi zaune ta amsa sallamar shi tare da ce ma Mamy “I will call you back, I love you bye”. Zama yayi a kujera nesa da ita yayinda ta miqe da sauri ta koma kujerar kusa da shi tace “Ya Farouq Good morning”. Sanye take cikin wandon sweatpant da wata qatuwar sweater sai hula da ta dora a kanta. Bai amsa gaisuwarta ba yace “ki shirya anjima da yamma zamu koma Nigeria” a razane ta kalle shi tace “Ya farouq ni fa ba yanzu zan koma ba, kuma ma ai excursion muka zo, ya za’ayi in tafi ba’a gama ba” kallon ta yayi fuska a murtuke yace “I wont repeat myself, just get ready” Jiki a sanyaye ta miqe sannan ta nufi hanyar dakin ta. Bata dade da shiga daki ba kuma sai ganin ta yayi ta dawo da sauri tace “ya farouq kayi break fast?” a ranshi yace “kamar idan na ce ban yi ba zata bani” ya girgiza kai alamar eh sannan yace “I had my breakfast a Hotel din da na sauka” cikin mamaki tace “ba a suite dinnan ka kwana ba?” ko kallon ta bai yi ba balle ya amsa ta. Tace “bari in je inyi wanka sai in kira masu aiki su hada mun kaya na” can kuma sai tace “wai.. zan hada da kaina” ta juya ta tafi yayinda ta bar shi yana kallon ta yana mamakin yadda Zara take da surutu, tambayar kan shi yayi “wai bakin ta baya mata ciwo ne?”. Wayar Zara da ta bari a kusa da shi ne ta fara ringing, ko da ya juya ya kalli fuskar wayar sai ya ga “My luv”. Ji yayi gaba daya ran shi ya baci wanda bai san dalili ba, da sauri ya miqe ya fita daga Hotel din gaba daya yayinda zuciyar shi take daci. ******************* ASALIN LABARI Alhaji Umar Jimeta da Hajiya Fatima sun kasance fulanin asali na Yola. Asalin su ‘yan qaramar hukumar Jimeta ne. Yaran su ‘yan biyu kacal, Al-Hassan da Al-Hussain. Alhaji Umar Jimeta ya kasance babban dan kasuwa, yana da dukiya mai tarin yawa. Wannan ne yasa yaran shi suka taso cikin gata, sunyi karatu mai zurfi na boko da na addini. Lokacin da Al-Hassan da Al-Hussain suka kammala karatun su na sakandire Mahaifin su ya tura su qasar ingila don cigaba da karatun su, hatta masters din su a can suka yi. Al-Hassan da Al-Hussain sun taso cikin qaunar junan su, a koda yaushe suna tare. Abinda kadai ya raba su shine karatun su domin kuwa shi Al-Hussain Banking and finance ya karanta a wannan lokacin yayinda shi kuma Al-Hassan ya karanta International studies. Zaman Al-Hussain Ingila ne ya hadu da Labiba wadda take karatun ta a can itama, Labiba asalin ‘yar Egypt ce, mahaifin ta mutumin Egypt ne yayinda mahaifiyar ta ta kasance ‘yar Nigeria. Labiba kyakyawar mace ce son kowa, sun qulla soyayya mai qarfi tsakanin ta da Al-Hussain. Bayan da su Al-Hussain suka kammala makaranta ne ya nemi son auren Labiba. Dayake Al-Hassan yana da tashi budurwar mai suna Zainab, Zainab diya ce a wurin gwamnan jahar Adamawa a wannan lokacin, nan aka hada akayi bikin su a rana daya. Al-Hussain ya samu aiki a world bank na Ingila a wannan lokacin, dayake lokaci ne da duniya take kwance. Bankin duniya wato World bank musamman suke bi makarantu don neman dalibai masu hazaqa wadanda da zarar sun kammala karatun su zasu samu gurbi a bankin. Haka ne ya kasance a bangaren Al-Hussain domin kuwa gaba daya turawan nan a lokacin ya bige su a fannin ilimi. Dayake dama Labiba bata kammala da karatun ta ba a can Ingilan sai faduwa ta zo daidai da zama inda suka tattara suka koma can da zama. Al-Hassan kuwa ya fara aiki a embassy na nan Nigeria da shekara daya ne aka tura shi france inda yake matsayin ambassador mai wakiltan Nigeria a qasar. Haka rayuwar su ta kasance gwanin ban sha’awa. Cikin shekara biyu da auren su ne Labiba ta haifi yaron ta namiji wanda ya ci sunan kakan shi Umar farouq. Zainab dai har zuwa wannan lokacin shiru, ta sa damuwa sossai a ranta domin kuwa a rayuwarta tana son yara. An tabbatar musu da cewa lafiyar su qalau a asibiti, lokaci ne dai baiyi ba. yau da gobe tun tana tausasa zuciyar ta har ciwon hawan jini ya kamata. Kullum ana hanyar asibiti. A lokacin da Farouq ya kai shekaru takwas ne Zainab ta kamu da ciwon zuciya. Hankalin dangi yayi matuqar tashi, da taimakon Allah da kuma likitoci da suke tsaye akan ta tayi qarko a wannan lokacin. Labiba ta qara haifo yara mata ‘yan biyu amma Allah ya dauki ran su gaba daya, daga baya ne ta haifo yaron ta namiji ya ci suna Abubakar Sadiq wanda Farouq ya ba shekaru takwas. Cikin ikon Allah zainab ta samu ciki bayan shekaru goma sha biyu da auren su. Murna a wurin dangi ba’a Magana. A dalilin ciwo da ya riga ya mamaye jikin Zainab ne tun cikin ta yana wata takwas aka yi mata C-section aka ciro ‘yar jaririyar ta kyakyawa wadda ta ci sunan kakar ta Fatima Zara. Zara bata yi arba’in ba mahaifiyarta ta rasu.+ STORY CONTINUES BELOW A wannan lokacin kuwa Zara ta zama abin tausayi, Al-Hussain ne ya ba dan uwan shi shawara akan ya bar mishi Zara a hannun shi saboda Labiba ta kula da ita kafin yayi wani auren. Iyayen su ma sunyi na’am da wannan shawarar. Zara ta cigaba da shan madara har ta girma. Ko da Al-Hussain ya sake yin aure Zara bata koma gidan su ba domin kuwa ta shaqu da Mamyn farouq sossai. Anty kamar yadda Zara take kiran matar Daddynta ta haifi yaran ta ‘yan biyu mata Safa da Marwa wadanda Zara ta ba tazarar shekaru hudu a duniya. Lokacin da Farouq ya tafi Germany karatun likita ne Su Abba suka koma Nigeria inda ya samu Political appointment na muqamin CBN governor. A lokacin da suka bar Ingila kuwa Zara ta gama secondary school dinta zata shiga jami’a, suna komawa Nigeria ne ta shiga Nile University inda take karantar computer Science. Shi kuwa Sadiq dayake ya fara karatun shi a nan Ingilan sai suka tafi suka bar shi a can inda yake karanta Banking and finance kamar mahaifin shi. Alhaji Umar Jimeta ya rasu a lokacin Zara tana shekaru goma, A yanzu haka Hajiya Fatima kakar su Zara wadda suka fi kira da Granny tana nan zaune a garin Adamawa cikin danqararren gidan ta wanda babu yadda su Abba basu yi da ita ta dawo Abuja ko France ba kusa da su amma ta qi. Suna yawan ziyartar ta bayan lokutta musamman Zara sarkin son yawo. Har wurin dangin mahaifiyarta tana zuwa. WACECE ZARA? Fatima Zara Al-Hassan, ‘yar kakaura doguwa, fara ce amma ba tas ba, kyakyawa ce ajin farko. Shekarun Zara goma sha tara a duniya amma idan ka gan ta zaka rantse ta wuce haka domin kuwa tabarkallah tana da girman jiki. Zara akwai qira mai kyau, figure 8 ce wadda tayi gadon su na Fulani. Gashin ta dogo ne amma fa a cike yake ga tauri. Duk yadda ka taba gashin sai tace akwai zafi. Dukda sai anyi stretching ake yi mata kitso amma fa tana kuka ana yi. Sai a yini ana yi ma Zara kitso domin kuwa da an yi guda biyu sai tace ta gaji a qyaleta ta huta, haka ake drama da ita har a gama. A lokacin da Zara take shekaru biyar ne aka gano tana da ciwon Cardiovascular disease, lokutta da dama idan ciwon ya tashi numfashin ta har daukewa yake yi sannan tayi ta zufa. Tun daga wannan lokacin ne aka dora ta bisa medication tare da kiyaye duk wani abu da zai janyo mata matsala, musamman bacin rai da tashin hankali. Sanin cewa mahaifiyarta ta rasu tana da ciwon zuciya ne yasa ba’a yi mamaki ba domin kuwa ciwo ne da yake trailing back to family history of heart problems. A rayuwar Zara tun da ta taso take bala’in qaunar Mamy da Farouq. Dukda ta lura Farouq din ba sakar mata fuska yake yi ba amma a hakan kullum maganar ta daya biyu na Farouq ne. Duk wulaqancin da yake yi mata bata fushi. A gidan gaba daya komai yi mata ake yi saboda kiyaye dokokin likita amma wani ikon Allah duk wani abu na Farouq da kanta take yi mishi. Mamy ta sha hana ta yin wasu abubuwan musamman wadanda zasu sa ta gajiya amma Zara bazata taba bari ba, duk wannan tana yi ne ba don komai ba sai don tana so ta kyautata ma dan uwan ta a dalilin damuwa da tayi da shi. Wasu abubuwan ma da take yi mishi idan ya dawo ya tarar bai yi mishi ba sai ya hau ta da fada akan ta bata mishi. Zara kuwa a duk lokacin da Farouq ya sa ta a gaba yana mata fada toh fa ta dinga kuka kenan tana bashi haquri wanda idan har bai haqura ba toh tashin hankali ya same ta kenan. Hakan yana janyowa har ciwon ta ya tashi, ganin irin haka ne ya sa su Abba suka ja mishi kunne akan ya daina sanya ta a cikin damuwa sannan ya dinga haquri da ita tunda dai yarinya ce. A rayuwar Zara tana son duk wani abinda zai kawo kwanciyar hankali, tana so kowa ya kasance cikin kwanciyar hankali. Bata qaunar tashin hankali ko alama. ta taso cikin gata na iyaye, dukda ta san mahaifiyarta ta rasu tana qaunar matar Daddyn ta wadda take kira da Anty. Yaran Anty ‘yan biyu Safa da Marwa ma suna son yayar su Zara. Anty ta so Zara ta dawo wurin ta da zama a France amma Zara ta qi domin kuwa ta shaqu da Mamy sossai, ita da France sai dai hutu. Zara yarinya ce mai fara’a sossai da son mutane amma fa akwai ta da surutu. Surutun ta yana cikin abinda yasa Farouq baya son zama inda take domin kuwa har ciwon kai surutun nata yake sa shi. Zara dai rayuwa take yi kamar sarauniya domin kuwa idan ta ga dama hatta wanka idan da hali sai dai ayi mata. Mamy bata barin ta tayi komai, wannan ne yasa take qara son Mamyn. Ita kuwa Mamy dalilin ta shine don kar ciwon zaran ya tashi tunda dai stress na cikin abubuwan da ke yin barazana ga rayuwar mai dauke da shi. Farouq yana matuqar jin haushin yadda Mamy ta shagwabar da Zara, a cewar shi idan bata yin wasu abubuwa da kanta ya zata yi zaman rayuwa a gaba musamman rayuwar aure. Ganin cewa farouq baya son hakan ne yasa Zara ta fara yin wasu abubuwa da kanta musamman idan tana ganin idanuwan shi. Duk wani abun da Zara zata yi da kanta kuwa sai ta samu minor injury, babu ranar da zata shiga kicin bata fito da yanka ba ko quna. Kai hatta gyaran gadonta kullum sai ta fito tana kuka wai ta bige qafa. Mamy dai bata son hakan amma ita kuwa Zara a dalilin Farouq take qoqarin yin abubuwa da kanta. Zara a rayuwar ta tana son kula da jikin ta, tana son turaruka. Shiyasa duk inda ta gifta toh fa zaka ji qamshi. Saboda kula da take yi ma fatar jikin ta ko pimple daya bazaka gani a fuskar ta ba. a duk lokacin da pimple ya fito mata a fuska kuwa sai kowa ya san akwai matsala domin kuwa ko fitowa ma bata yi. Yini take yi a daki wai fuskarta ta lalace bata so kowa ya ganta. Tun wannan abu yana ba Mamy mamaki har ta zo ta saba. Fashion yana daga cikin abubuwan da take qauna shiyasa duk bayan lokaci zaka ji ta tafi turai ba don yin komai ba sai shopping. Wasu kayan ma haka take siyo su ta zuba a closet dinta amma bata taba sakawa ba. Zara tana qaunar hoto a rayuwarta, ko daga bacci ta tashi sai ta dauki hoto. Sannan tana son social media musamman instagram, hotunan ta da tayi posting a instagram Allah yayi yawa da su. Followers dinta kuwa sun fi miliyan. Qawar Zara a duniyar nan wadda ta aminta da ita qwaya daya ce tak, Hafsat Khalil. Makarantar su daya sannan ajin su daya inda suke karantar Computer Science. A koda yaushe zaka gan su tare. Hafsat dai ta kasance Budurwar Mukhtar abokin Farouq wanda suka taso tare. Mukhtar dai ya hadu da ita a gidan su Farouq wata rana da ya je gidan. Tun daga wannan lokacin ne suka qulla soyayya a tsakanin su. Babu yadda Farouq bai yi da shi akan ya qyale ta ba domin kuwa a ganin shi tayi mishi qanqanta amma sai ya gwada shi dama irin su yake so ba wadda zata nemi fin qarfin shi ba. ******************* Jirgin sama wanda ya taho daga qasar UAE ne ya sauko inda matafiya suka dinga fitowa.+ Farouq ne tare da Zara wadda take riqe da wayar ta a hannu yayinda wani ma’aikacin wurin yake turo akwatunan ta. Sanye take cikin pencil jeans da ‘yar qaramar top yayinda ta dora wata kimono mai kyau a sama, ta bala’in yin kyau domin kuwa Zara dai kyakyawa ce sannan kuma ta iya gayu. Duk inda ta wuce sai an kalle ta. Shi kuwa gogan ko kallon arziki ma bata samu a wurin shi ba balle ya ga kyan da ta yi. Riqe yake da wata qaramar jakar shi ta matafiya yayinda yake tafe tana biye da shi. Ko da suka nufi car park direbobin farouq guda biyu suna nan suna jiran su. An saka akwatunan Zara a cikin mota daya yayinda Farouq ya wuce zai shiga dayar motar. Cikin hanzari Zara ta riqo hannun shi tace “ya Farouq ni kai zan bi” da sauri ya kalli hannun ta wanda ta riqe shi ya fizge sannan ya kalle ta yace “ke ba kya jin Magana ko? Sau nawa zan ce ki daina riqe ni?” da sauri tace “yi haquri, mantawa nake yi” yace “oya wuce ki bi Sani” cikin qunar rai ta juya ta nufi motar. Yana kallonta tana goge fuskar ta da hannun ta wanda ya tabbatar mishi da lallai kuka take yi. Sanin halinta na sanya damuwa akan abubuwa musamman idan shi ya sanya ta damuwar ne yasa ya bi bayan ta ya bude qofar motar ya duqo yace “are you crying?” girgiza kai tayi tace “no” yace “ki gaida Mamy, zan zo gobe insha Allah” tayi murmushi sannan tace “toh yaya, kar ka manta ka ci abinci don na ga baka ci komai ba tun breakfast din safe” ba tare da ya amsa ta ba ya rufe qofar motar sannan ya juya ya nufi tashi motar. A cikin mota ne Zara ta fiddo wayarta ta kira qawarta Hafsat. Cikin murna Hafsat ta amsa wayar tare da fadin “ke bestie How far, dazu Sweetlove yake bani labarin abinda ya faru da ke. Ina ta trying wayar ki ma ban samu ba”1 Zara tayi murmushi tace “Hmmm, ke dai bari bestie. Wanda na gudu a dalilinshi kuma ya biyo ni” Hafsat ta fashe da dariya tace “babes I don’t understand you honestly, yanzu dai gashi da bakin ki kina gaya mun a dalilin shi kika gudu anjima kuma idan nace miki son shi kike sai kice ba haka ba” Zara ta fashe da dariya tace “manta da wannan zancen bestie, its kinda complicated. Yaushe kika dawo? I missed you a lot” Hafsat tace “dazu muka dawo, network din wurin is terrible shiyasa ma kika ji ni shiru, yanzu kina ina? Don sai na zo har gida na ji labari. Haka kawai kin sa Ya Farouq ya bar amaryar shi ya bi ki wata qasa, Anty Ruqayya zata ji haushi ba kadan ba” Zara tayi murmushi tace “toh ta fashe mana, ni dama ba sonta nake ba” Hafsat tace “ai dole ki tsane ta tunda ta auri masoyin ki” Zara ta turo baki tace “point of correction babes, he is my big brother whom I so much care about” Hafsat tayi dariya tace “keep deceiving yourself” Zara tace “whatever, I am on my way zuwa gida, yanzu muka dawo. Idan kin ga dama ki zo” Hafsat tayi dariya tace “ai dole in zo babes” haka dai suka yi sallama inda Zara ta cigaba da tunanin maganganun Hafsat. Ta rasa dalilin da yasa Hafsat take gani kamar tana son Ya Farouq. STORY CONTINUES BELOW Ajiyar zuciya tayi tare da tuno dalilin da yasa ta suma a Dubai, hawaye ya fara gangarowa a fuskar ta wanda nan da nan ta sa hannu ta goge. FAROUQ AL- HUSSAIN MANSION Farouq ya iso gidan shi inda ma’aikata suka dinga kawo mishi gaisuwa yana amsawa cikin fara’a kamar kullum. Bayan ya shiga gidan kai tsaye sashen shi ya wuce. Da ya shiga dakin shi ne yayi shirin wanka ya shiga. Bayan ya fito ya shirya cikin qananan kaya sannan yayi sallah. Komawa yayi bisa gadon shi ya kwanta don ya huta. A lokacin da Farouq ya dawo Ruqayya tana tare da Aliya a falon sashen ta. Daya daga cikin masu aikin ta ne ta sanar da ita isowar shi. A tunanin Ruqayya zai shigo sashen ta ya neme ta tunda dai shi yayi mata laifi amma tun tana sa ran zata gan shi har ta haqura. Cikin bacin rai ta kalli qawar ta Aliya tace “kin gani ko? Yanzu fa kusan awa daya kenan da dawowar shi amma bai zo ya neme ni ba, wai ma yana so na kuwa?” Aliya ta matso kusa da ita tace “qawata relax, qila yana shirya miki ne. kin dai san yau ne zai zama daren farkon ku don haka go and get ready to welcome him. Ni bari ma in tafi gida” Ruqayya tayi dan murmushin qarfin hali tace “thank you very much qawata, ban san ya zanyi ba without you” Aliya tayi murmushi ta miqe tare da fadin “behave yourself”. Har wurin motar ta Ruqayya ta rakata sannan ta dawo ta wuce sashen ta. Tayi alqawarin idan bai zo ya neme ta ba ita bazata je ba. AL- HUSSAIN MANSION Zara dai ko da ta iso gida sai da Mamy ta cika mata cikinta da abinci sannan ta wuce sashen ta. Tuni masu aikin ta sun shirya mata abubuwan da take buqata na wanka, bayan ta fito ne tana zaune a gaban dressing mirror dinta ne Hafsat tayi sallama ta shigo. Cikin murna ta miqe suka rungume juna inda Hafsat din ta ture ta tare da fadin “matsa jor, duk kin jiqa ni” Zara tana dariya tace “yi haquri, fitowa na kenan daga wanka” ta koma ta zauna gaban dressing mirror dinta yayinda Hafsat ta koma kan gadon Zara ta kwanta suka shiga hira. Suna hirar yayinda Zara ta gama shirin ta tsab cikin wani wandon three quater da t-shirt qarama ta koma bisa gadon wurin Hafsat. Hafsat ce tace “hmmm, su Zara sarkin son qamshi. Duk kin cika dakin nan da qamshi” Zara harare ta tace “a gaban ki fa na shirya, me kika ga na sa banda spray?” Hafsat tace “zaki fadi gaskiya dai, ni dai ba wannan ba wai meyasa kika suma ne a Dubai? Ko in ce ya akayi ciwon ki ya tashi?” Zara tayi ajiyar zuciya tace “wallahi babes ni dai all I could remember was na shiga instagram sai na ga hotunan Ya Farouq bayan an daura auren shi inda ake ta congratulating din shi, for once I just wished I was able to stop this marriage” cikin mamaki Hafsat tace “why?” Zara tace “wallahi babu wadda zata iya kula da Ya Farouq kamar ni, ni kadai nasan abubuwan da Ya farouq yake so da wadanda baya so” Hafsat ta fashe da dariya tace “kuma kin ce ba son shi kike ba?” Zara ta jefe ta da pillow tace “ke baki ganewa wallahi, an gaya miki sai na auri Ya Farouq ne zan iya kula da shi? da bai aure ta ba ni zan iya kula da shi, muyi zaman mu a nan gida hankalin kowa a kwance” Cikin dariya Hafsat tace “ai yanzu ma Hankalin kowa a kwance yake saidai idan naki hankalin ne yake a tashe. Banda abinki haka zai zauna bazai yi aure ba? common stop this game and accept the fact that you feel something for him” kafin Zara tayi Magana ne aka qwanqwaso qofar dakin. Sadiq ne ya shigo yana fadin “where is my Princess?” cikin murna ne Zara ta miqe ta ruga a guje zata yi hugging dinshi sai ya matsa da sauri yace “Haram” STORY CONTINUES BELOW hararar shi tayi tace “ai kuwa baka isa ba” daga nan kuwa ta biyo shi suka dinga zagaye dakin Hafsat tana ta yi musu dariya. Daga qarshe dai janyo ta yayi ya bata side hug sannan yace “and how is my princess doing?” cikin shagwaba tace “I am doing much better, I missed you My Luv” Hafsat ta fashe da dariya yayinda Sadiq yace “don Allah ki daina kira na My Luv kada Ameera ta ji tace ta fasa” Gaba dayan su suka fashe da dariya sannan Zara tace “ai itama dai don batasan waye kai ba shiyasa ta maqale, idan na bata labarin ka guduwa zata yi” cikin fuskar tausayi yace "yi haquri princess" suka dinga yi mishi dariya. Haka dai suka cigaba da hira har aka kusa kiran sallan Magrib. FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION Gab da magrib ne Farouq ya farka daga baccin da ya kwashe shi. yayi addu’ar tashi daga bacci sannan ya fada kewaye. Wani wankan ya sake yi sannan yayi alwala ya fita domin zuwa masallaci. Bai dawo gidan ba sai bayan Isha’I. ko da ya shiga gidan ko’ina shiru. Har ya wuce zai nufi sashen shi sai kuma ya dawo ya nufi sashen ta. Bai gan ta ba a falukan ta don haka ne ya wuce main bedroom dinta. Cikin sallama ya shiga wanda tana jin shi ta qi amsawa. Tsayawa yayi bakin qofar yana kallonta yayinda take zaune a gefen gadonta tana kallon wayar ta. A duniya abinda Farouq bai iya ba wanda kuma ya tsana shine lallashi, lallashin ma wai mace. Gyaran murya yayi ya taka zuwa wurin ta ya zauna gefen ta yace “how are you?” bata ko kalle shi ba balle ta amsa shi. Dafe kai yayi sannan yace “look, I didn’t mean to… kin san she is my patient..” ganin bata juyo ta kalle shi ba ne yasa ya miqe zai tafi abinshi. Ji yayi ta riqo hannun shi wanda ta san idan bata yi haka ba tayi ma kanta don ba dawowa zaiyi ba, ta san halin shi sarai. Miqewa tayi ta dawo ta gaban shi ta rungume shi tana kuka tace “honey why? Meyasa ka tafi ka bar ni a ranar Dinner din bikin mu? I was hurt and I am still hurt” Farouq ya tausaya ma Ruqayya domin kuwa shi kan shi ya san bai kyauta ba toh amma ya zaiyi. Ba tare da yace komai ba ya rungume ta yayinda ya cigaba da wasu tunanin da bai san kansu ba. Da ya ji alamun ta natsu ne ya kai bakin shi saitin kunnen ta yace “what’s for dinner? I am hungry” murmushi tayi sannan tace “mu je mu duba mu gani ko anyi serving dinner". Suna zaune bisa dinning yayinda masu aiki suke ta bubude kalolin abincin, gaba daya Farouq kallo yake yi amma babu irin abincin da yake so. Da qyar dai ya nuna wata fried rice inda ya sa suka yi serving dinshi kadan. Ya fara ci kenan wayar shi tayi ringing ya amsa. Daga asibiti ne ake yi mishi bayanin wani patient, tun Ruqayya tana sa ran zai gama wayar har dai ta gaji da jira. Ganin haka ne yasa ya miqe tare da fadin “excuse me please”. Tunda Farouq ya shiga dakinshi bai sake fitowa ba. Ruqayya dai da ta gaji da jiran shi ne ta nufi dakinta ta shirya cikin wata gajerar sexy gown tare da tsayawa gaban madubi ta kalli kanta. Murmushi tayi sannan tace “I will make you mine today Farouq. I love you so much that I can do anything to be with you” can kuma sai ta dan bata rai tace “Allah yasa kar ya gane”. Turaruka ta sake fesawa sannan ta wuce ta fita. Zaune yake a bisa gadon shi yana duba reports din patient din a laptop dinshi. Qwanqwaso qofar shi tayi ta shigo. Dago kai yayi ya kalle ta sannan yayi murmushi. Cikin yauqi ta tako har inda yake ta sa hannu ta janye laptop din shi sannan ta haye gadon. Fadawa tayi bisa shi ta shiga kissing dinshi kamar zata cinye shi. A yadda Ruqayya take sarrafa Farouq zaka rantse itace namijin domin kuwa da qwarewa take harkar. Gaba daya dakin yayi shiru banda nishin Ruqayya babu abinda kake ji. Tuni sun fada wata duniyar inda Farouq ya sa ran zai tarar da farin ciki amma kuma sai ya tarar da sabanin hakan. A yadda ya samu Ruqayya ya tabbatar ba shi ne mutum na farko da ya fara sanin ta a matsayin ‘ya mace ba. dukda kuwa bai taba yi ba amma kuma ai ya san yanayin da yakamata ya tarar. Duk gyaran da Ruqayya ta sha bai hana Farouq ganewa ba domin dai Farouq din nata ai ko bakomai likita ne. Gaba daya hankalin shi a tashe yake yayinda tunani suka dinga zuwa mishi daban daban. Ruqayya dai ta dan lura da cewa jikin shi yayi sanyi. Cikin shauqi na soyayya tace “Honey what’s wrong?” da qyar Farouq ya saita murya yace “I am tired ne” ta bata rai tace “Ni fa bai ishe ni ba, please one more round sai ka huta”. Farouq yace "not today" komawa yayi ya kwanta ya rufe idanuwan shi yayinda qwalwar shi take ta lissafin abubuwa da dama. Dukda sanyin AC din da yake ratsawa a dakin bai hana Farouq zufa ba. Ita kanta jikinta ya dan yi sanyi. Komawa tayi ta kwanta bisa qirjinshi tana ta tumurmushe shi yayinda take fadin "sorry honey nasan ka gaji" Gaba daya Farouq yayi nisa a tunani da bai ma san lokacin da tayi bacci ba. Miqewa yayi ya shige kewaye yayi wanka, gaba daya hankalin shi baya tare da shi, tunani yakeyi kala kala akan yanayin da ya samu Ruqayya. Ko da ya shirya fita yayi daga dakin ya bar ta nan kwance tana ta bacci. Falon shi ya koma ya kwanta bisa doguwar kujera yayinda ya cigaba da tunanin matakin da yakamata ya dauka akan wannan sabon al’amari. Wata zuciya tana raya mishi Ruqayya ba nutsatsa bace kamar yadda ta nuna mishi yayinda wata take fadin qila matsala ta samu na fyade da makamancin hakan. Shin ya tunkare ta ya tambaye ta ya akayi ne ko kuwa ya haqura ya bar komai a hakan??? Shin zai iya cigaba da zama da ita ko kuwa????2 ***************

Post a Comment for "BA SONTA NAKE BA CHAPTER 1"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...