BA SONTA BAKE BA CHAPTER 4 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BA SONTA BAKE BA CHAPTER 4

BA SONTA BAKE BA CHAPTER 4

- - Post a Comment
BA SONTA NAKE BA CHAPTER 4
 AL HUSSAIN SUITE BURJ AL ARAB DUBAI Kwance take a kan gado yayinda ta riqe wayar ta kamar wadda take jiran wani important call. Hafsat ce ta shigo dakin riqe da kwalin Pizza wanda tayi order. Kusan awowin su biyu kenan da isowa. Hafsat ta ajiye kwalin Pizza din a kan gadon tare da komawa ta fita. Ta dawo riqe da drinks ta haye gadon ta miqa ma Zara daya. Ganin Hankalin Zara yana kan wayar ta ne yasa Hafsat tace "babes lafiya? Are you expecting a call?" Zara ta kalle ta tace "he hasn't called me har yanzu" cikin mamaki Hafsat tace "Ba dazu na ji kina waya da shi ba, are you expecting his call again?" Zara ta miqe zaune tace "ba Mahmood ba, ina nufin Ya Farouq" Hafsat tayi tsaki tace "not again babes, wanda ya fi muhimmanci a rayuwar ki ya kira ki, why do you care idan Ya Farouq bai kira ki ba?" Zara tace "ya nuna damuwar shi akaina is all I want babes" Hafsat tace "toh wai tsaya ma, ni fa ban taba gani Ya Farouq ya kira ki a waya ba, what makes you think zai kira ki. Abeg juyo mu ci Pizza dinnan mu huta mu fara preparation. Kin dai san we have a lot to do" Haka Zara ta juyo ta fara cin Pizza din yayinda qawar ta take mamakin halin da take shiga a game da Farouq domin kuwa wannan al'amarin ya wuce yadda Zaran take ikirari. FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION Farouq zaune a falon shi tare da abokin shi Mukhtar, labari suke yi akan bikin Mukhtar din wanda yake matsowa. Mukhtar ne yace "wallahi abokina I cant wait to have Hafsat a gida na" Farouq ya Harare shi yace "zaka sha raino dai" Mukhtar ya fashe da dariya yace "you are too serious abokina, a little fun bazai sa a raina ka ba don nasan abinda kake tunani kenan. How I wish zaka gwada you will understand what I mean" Farouq ya girgiza kai yayinda Mukhtar ya cigaba da fadin "ka kuwa san cewa irin su sun fi dadin sha'ani? Duk abinda kake so shi za'a yi maka.." bai gama Magana bane wayar shi tayi ringing. Murmushi yayi ya yanke kiran sannan ya kira. Hafsat cikin shgwaba tace "sweetlove how are you, I have missed you alot?" Mukhtar yace "sorry love I have been busy ne, ya kike. Hope dai Zara bata baki wahala don nasan ta da son yawo" Dariya tayi tace "ko kadan, its like ma wannan karon the tables have turned because she is not being herself tunda muka zo" cikin mamaki yace "what?? Me ke damun ta??" Jin haka ne yasa hankalin Farouq ya tashi yayinda ya sa ma Mukhtar ido yana sauraren shi. Hafsat tace "its like tunda muka zo Ya Farouq bai kira ta ba ya ji ko ta iso lafiya shiyasa ran ta ya baci, kasuwar ma da muka shiga ni ta bari ina ta zaben abubuwa when she was supoosed to assist me" Murmushi Mukhtar yayi yace "tana ina? Bata wayar" Hafsat ta miqe ta nufi dakin Zara ta miqa mata waya tace "sweetlove" A lokacin da Zara ta karbi wayar Mukhtar ya miqa ma Farouq wayar shi yace "your sister" Farouq ya karbi wayar daga hannun Mukhtar ya kai kunnen shi yace "hello" a razane ta miqe zaune tace "Ya Farouq" yace "how are you?" ajiyar zuciya tayi tace "ya Farouq please forgive me" dakatar da ita yayi yace "for what?" Tace "I didn't mean all that I said the other day a asibiti" daga idanuwan shi yayi ya kalli Mukhtar wanda yake kallon shi sannan yace "shikenan, ki tabbatar kin kawo mun tsaraba idan ba haka ba zanyi miki allurai guda goma" STORY CONTINUES BELOW Ji yayi ta fashe da dariya tace "insha Allah Ya Farouq" miqa ma Mukhtar wayar yayi yayinda yayi shiru yana mamakin yadda yarinyar ta zagaye rayuwar shi kaf. Bayan Mukhtar yayi sallama da Hafsat ne ya kalli Farouq yace "kasan me? Tunda suka sauka she wasn't herself simply because baka kira ta a waya ba" Farouq yayi tsaki yace "wallahi abokina kai wani iri ne, don ban kira ta bane ya zama wani abu? Da can na taba kiran ta a waya ne??" Kafin Mukhtar yayi Magana ne Ruqayya ta shigo cikin sallama ta nufi wurin Farouq tana fadin "Honey how are you?" ta zauna bisa cinyar shi yayinda yace "kin dawo?" tace "eh, Hajjaju tace in gaishe ka" ta juya ta kalli Mukhtar tace "Ango ango, ya garin?" Mukhtar yayi murmushi yace "lafiya lau gimbiya" tace "rabon da in ganka har na manta, ka guje mu" murmushi yayi yace "ba haka bane, aikin ne namu sai godiyar Allah" A haka dai suka taba hira har Mukhtar yayi musu sallama ya tafi gida. ************* Zara dai tun lokacin da tayi waya da Farouq hankalin ta ya kwanta sossai. tuni sun shiga sayayya iri iri. A kullum idan sun fita sai ta siyo ma Farouq abubuwa, Hafsat dai kallonta kawai take yi. Satin su daya a Dubai ne suka hau jirgi zuwa France. Su Anty sun ji dadin ganin Zara. Safa da Marwa maqale da ita a koda yaushe suna mata hira kala kala yayinda itama take musu nata hiran. Tare suka dinga shiga shaguna suna siyayya. Akwai wata rana da sun shiga wani shagon sayar da turaruka. Zara ce ta bi layin turarukan maza tana ta zabe, Marwa ce ta matsa kusa da ita tace "big sis wai wa kike siyo ma turaruka haka? Gani nayi fa duk na maza ne" Zara tayi murmushi tace "na Ya Farouq ne" Hafsat ce ta matso tace "au, na zata na Mahmood ne" da sauri Zara ta kalli qawarta yayinda suka dinga yi mata dariya. Safa ce tace "wai ni kam yaushe ma kuka fara shiri da Ya Farouq ne?" Zara ta Harare su tace "toh wai me ya ruwanku da ni ne?" haka dai suka dinga yi mata dariya. Ana gobe zasu koma Nigeria ne dadadare Daddy ya kira Zara falon shi. A lokacin daga shi sai Anty zaune a falon. Cikin sallama ta shiga ta zauna a kusa da Anty tace "Daddy you sent for me" Daddy yayi murmushi yace "yes Princess, yaushe zaki gama school?" Zara tace "sai next year insha Allah Daddy" yace "in few months time kenan, hope kin san kina gamawa you will be getting married ko?" Gaban ta ne ya dan fadi inda tace "but Daddy na dauka sai na gama masters, I am just nineteen fa" yace "you will be twenty in less than a month kuma masters ba matsala bane, idan kinyi aure I am sure mijin ki zai bari kiyi don nasan he is not strict" cikin mamaki ne Zara ta kalli Daddy tace "Daddy kasan shi ne?" Murmushi yayi yace "ke zaki fada mun sunan shi" dariya tayi tace "zan fada maka sunan shi Daddy, I know you will like him" Daddy yace "I surely do". Anty ta shafa kan Zara tace "I am going to miss you Princess" Zara ta rungume Anty tace "idan an yi hutu zan zo insha Allah Anty". ************* Washegarin ranar da su Zara suka dawo daga France ne Zara ta nuna ma Mamy tsarabar da ta siyo ma Farouq. Mamy dai mamaki tayi sossai. bayan ta gama gani ne tace "toh ni me aka siyo mun?" Zara ta zaro idanuwa tace "laaa, wallahi Mamy na manta" Mamy ta fashe da dariya tace "wato mu duk ba mutane bane ko Princess??" Zara ta rungume Mamy tace "sorry Mamy, next time Insha Allah" haka dai Zara ta kira masu aiki suka zuba mata kayan a mota yayinda Mamy take mamaki. FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION Zara tayi Horn gidan Farouq inda aka bude mata ta shiga. Masu aikin gidan dukda sau daya suka taba ganin ta sun tuna ta domin kuwa Zara akwai fara'a. Nan da nan suka dinga gaishe ta cikin girmamawa. Bayan ta gama gaisawa da su ne ta sa aka fitar da kayan da ta zo da su sannan ta wuce ta nufi qofar shiga gidan. Mai aiki ce ta bude mata qofa, ko da ta shiga babu kowa a babban falon don haka ne ta sa mai aikin ta biyo ta da kayan sama. Zaune yake a falon shi yana buga game, kofin moringa tea ne a gaban shi yayinda hankalin shi yayi nisa wurin buga game din. Zara ta dade a tsaye tana kallon shi, murmushi tayi a ranta tace "ya Farouq and game, addiction" qarasowa tayi wurin shi ta bayan shi ta sa hannu ta birkita gashin shi kamar kullum sannan tace "hello big brother" kamar daga sama ya ji muryarta inda ya dago da sauri ya kalle ta ran shi a bace yace "what is wrong with you?" murmushi tayi ta zagayo ta zauna gefen shi tace "sorry Ya Farouq". Tsaki yayi yayinda ta dauki kofin tea din shi ta fara sha. Wani irin kallo yayi mata wanda yasa ta kusan qwarewa ta nuna mishi kofin tea din tace "yi haquri, I kinda missed it" Ya cigaba da buga game dinshi ne ta sa mishi ido tana murmushi. Ji yayi tace "oh how I missed you Ya Farouq" ta miqe ta janyo akwatunan tsarabar shi ta ajiye a gaban shi tare da budewa tace "look what I bought for you" control pad din hannun shi ne ya ajiye bayan ya sa pause ya kalli kayan cikin mamaki yace "all these?? For me??" tace "Yes". Kwalin Wata agogo ta fiddo daga cikin kayan tace "Ya farouq see, wannan shine favourite dina. Yayi kyau?" kallon ta yayi yace "wa ya sa ki siyan kaya dayawa haka?" cikin shagwaba tace "baka so ne? basu yi kyau ba?" kafin ya amsa ne Ruqayya ta shigo falon tana Fadin "Honey wannan game din ya isa haka" Ganin Zara zaune kusa da shi ne yasa ta tsaya cak tana kallon ikon Allah. Zara ta kalle ta tace "Anty Ruqy ina kwana, yanzu nake shirin tambayar Ya Farouq ke" cikin bacin rai Ruqayya ta qaraso tace "yau kin ga daman zuwa gidan namu kenan" Zara tayi murmushi tace "tsarabar Ya farouq na kawo" Ruqayya tace "aikuwa kun yi saurin dawowa, na zata zakuyi wata daya a can" Zara tayi dariya tace "haba Anty Ruqayya kin manta da school ne?" Farouq dai tuni ya cigaba da buga game dinshi wanda kwata kwata baya sauraron su domin dai kamar kullum idan Zara tana surutu a kusa da shi dauke hankalin shi yake daga wurin. Zara ce ta miqe tace "Ya Farouq ni zan tafi, I hope you will like each and every one of these" ta kalli Ruqayya tace "Anty Ruqayya kiyi haquri na manta ban siyo miki komai ba, next time insha Allah" Ruqayya tayi murmushi mai kama da yaqe tace "ba komai, ki gaida gida". Bayan Zara ta tafi ne Ruqayya ta matso kusa da shi ta fara dudduba kayan tace "wai Honey wa ya aike ta siyo wadannan kayan ne haka? Duk ma sai dai ka bayar da su don na ga kamar.." bai bari ta qarasa ba yace "no one knows what I like better than her" Ruqayya ta tabe fuska tace "she is your sister after all" yayinda zuciyar ta take quna. *************** Ah toh... nima dai nace 'hanta da jini... ba'a raba su' KHALIL MANSION Zaune suke a dakin Hafsat inda Hafsat din take waya da Galiafahad akan kayan bikin ta da zai dinka mata. Galiafahad dai wani shahararren fashion designer ne wanda ake ji da shi a Dubai. Bayan ta qarasa wayar ne ta juyo ta kalli Zara wadda take latse latse a wayar ta tana murmushi. Hafsat ce tace "Babes wai ban tambaye ki ba, me kike shirya mana ne na Birthday? Kin dai san ba haka nan zaki bar mu ba ko?" Zara tayi murmushi tace "labarin da muke yi kenan da Sweetie, yace zaiyi organizing party, I don't know whether to agree or not" Hafsat ta bata rai tace "idan dai Mahmood zai hada party toh bazan je ba" Zara ta ajiye wayarta ta kalli Hafsat tace "haba bestie, wai meyasa ba kya son Sweetie ne? rannan ma fa sai da ya tambaye ni" Hafsat tace "babes ni fa ba wai shine bana so ba, I don't like him with you ne. baku dace ba gaskiya" Zara ta fashe da dariya tace "ke ai kin dace da Ya Muky" Hafsat tace "yi haquri qawa ta". Haka dai suka cigaba da plans din bikin Hafsat din wanda kusan ma sun gama tsara komai. Zara bata bar gidan su Hafsat ba sai qarfe takwas na dare. Bayan sunyi sallama ne ta shiga motar ta tayi gida. ************ A kan hanyar ta ne ta biya Frozenscoop don siyan Ice cream. Ko da ta shiga ta siya ta fito tana shirin yin reverse ne wani mai mota ya shigo wurin da gudu, dayake waya yake bai lura da motar Zara ba sai ya gabza mata da qarfin tsiya. Kan Zara ne ya bugu da steering yayinda qafarta ta taka birki. Tuni mutane sun zagaye su yayinda ake ta yi ma mutumin fada tare da bashi rashin gaskiya. Zara dai ko fitowa daga motar bata yi ba. kanta ne yake matuqar ciwo yayinda hawaye ke ta bin fuskar ta. Mutumin ne ya zagayo ta gefen Zara ya qwanqwasa mata gilas don bata haquri domin kuwa barnar da yayi mata yasan bazai iya biya ba don kuwa motar Zara Mercedes Benz ce mai tsada wadda sai kayi dagaske zaka ga mai irin ta a cikin garin Abuja. Zara ta sauke gilas yayinda take riqe da wayarta tana kuka. Mutumin ne ya dan duqa tare da fadin "don Allah kiyi haquri" Zara ta daga mishi hannu akan ya tafi kawai yayinda ta kai wayar a kunnenta cikin kuka tace "Ya Farouq don Allah ka zo" A lokacin ya baro asibiti kenan zai je gida. Cikin fada yace "are you mad? In zo ina?" tace "yi haquri, I had an accident yanzun nan, ina frozenscoops" Hankalin shi a tashe yace "subhanalillah, are you okay?" tace "not really, please ka zo" kashe wayar tayi yayinda ta kifa kanta a steering wanda yake bala'in yi mata ciwo yayinda mutane suke ta jajanta abinda ya faru. Bayan motar Zara ya hango wadda ta bugu sossai domin kuwa hatta Bumper din motar ta fadi. Gefen motar ta ya faka ya fito, qwanqwasawa yayi ta dago tare da saurin bude motar ta fito. Bata jira komai ba ta rungume shi tana kuka. Bai san lokacin da ya riqe ta ba yana fadin "its okay, I am here" wannan shine rana na farko da Farouq bai ture Zara ba don tayi hugging dinshi. Mutanen wurin ne suka dinga yi mishi bayanin abinda ya faru tare da jajantawa yayinda yayi musu godiya. Har yanzu Zara kuka take yi, janyo ta yayi ya sa ta a motar shi sannan ya koma motar ta ya fiddo jakar ta da ledar ice cream din tare da wayar ta sannan ya rufe motar. STORY CONTINUES BELOW Bayan yayi ma security bayanin zai turo a dauki motar Zara gobe ne ya dawo motar shi ya tada suka tafi. Kukan da Zara take yi ne yake damun shi, gashi ya kasa ce mata komai tunda dai bai iya lallashi ba. haka ya qyale ta har suka kai gida. AL-HUSSAIN MANSION Mamy zaune a falon ta sai ganin su tayi Zara na tafe tana kuka yayinda yake biye da ita riqe da kayan ta. Cikin tashin hankali ta miqe tace "Princess ya na gan ki haka?" Zara ta nufi wurin Mamy ta rungume ta yayinda Mamy ta kalli Farouq tace "lafiya?" yace "tayi accident ne, amma dai da sauqi" Mamy ta dafa goshin Zara wanda yayi zafi sossai tace "subhanalillah, ga kanta ta yayi zafi sossai" ta kalli Zara tace "kin bige ne? ina yake yi miki ciwo?" Zara ta dafa kan ta tace "Mamy kai na" Farouq ne ya runtse idanuwa tare da fadi a ranshi "oh my God I didnt even ask her". Mamy ta kalle shi tace "meyasa baka kai ta asibiti ba? You have to do something" yace "yi haquri Mamy, mu kai ta daki first". Kwance take a kan gadon ta tana bacci. Mamy ce zaune a gefen ta yayinda Farouq yake tsaye yana kallon ta. Mamy ta kalle shi tace "hope dai she will be fine?" yace "Insha Allah Mamy, maganin da ta sha will do the magic" stool ya janyo ya zauna sannan yace "daga yau kada Zara ta sake fita da mota da daddare" Mamy tace "abinda na gama tunani kenan, don't worry about that, I will take care of it" Washegari da safe Zara tana kwance a kan gadonta ne Hafsat ta shigo. Da sauri ta nufi wurinta tace "bestie how are you feeling" Zara tayi murmushi tace "I am feeling much better, baki je school bane yau?" Hafsat tace "wane school bayan bestie dina ba lafiya, Allah dai ya tsare gaba" Kafin Zara tayi Magana ne aka qwanqwaso qofar. Farouq ne ya shigo. Hafsat tace "Ya Farouq ina kwana" yace "lafiya" ya kalli Zara yace "how are you?" Zara ta tashi zaune tace "better amma dai I am weak" ya matso ya zauna a gefen gadon tare da dafa goshin ta domin jin yanayin temperature dinta. Zara dai idanuwa ta sa mishi har a ranta tana fadin "he is so cute" Tunanin ta yayi nisa ne ta ji Hafsat ta girgiza ta tace "babes ya haka?" da sauri ta juya tana kallon Hafsat yayinda bata ga Farouq ba. Cikin mamaki tace "Bestie ina yake?" Hafsat ta fashe da dariya tace "he just left" ajiyar zuciya tayi ta koma ta kwanta. Hafsat tace "yanzu dai na tabbatar there is more to this, you couldn't even control yourself. Qila ma kallon da kike yi mishi ne yasa ya tafi" Zara ta Harare ta yayinda take yi mata dariya. Wayar Zara ce tayi ringing, Hafsat ta dauko wayar inda ta ga sunan Mahmood, tayi tsaki tace "sarkin jan aji" sannan ta miqa mata. Zara tana murmushi ta amsa wayar. Bayan ya tambaye ta jikinta ne suka shiga hira, hira sossai suka yi har yana fada mata cewa ya gama preparation na birthday party dinta yayinda take ta murna. Sunyi akan zai kira ta anjima sannan suka yi sallama. Zara ce ta kalli Hafsat tace "babes wai dagaske bazaki je partyn ba?" Hafsat tace "bazan je ba babes, kin san fa tunda bikina ya matso Mom ma ta hana ni fita idan ba wurinki ba toh sai school" Zara ta tabe fuska tace "but I will miss you a partyn" Hafsat tace "anya? Ni da ko kallo na bazaki yi ba idan kina tare da Mahmood dinki" Zara tayi dariya. STORY CONTINUES BELOW ************* ************* Zara zaune a dakinta tana duba saqonnin mutane wadanda suke taya ta murnar zagayowar shekaran haihuwar ta. Text messages, instagram, facebook, twitter sannan wasu suna ta kiran ta a waya. Daddy, Anty da 'yan biyu duk sun kira ta sunyi mata happy birthday. Sadiq ya kira ta har yana fadin idan ya dawo sai ta bashi cake dinshi. Kai hatta Granny da dangin mahaifiyarta sun kira ta. Bayan ta gama duba saqonnin ne ta jefar da wayar ta miqe tana fadin "kowa ya aiko mun best wishes banda shi, yanzu kam na tabbatar baya sona" Haka ta shiga bathroom tayi wanka ta fito. Tana zaune bisa stool din dressing mirror dinta tana shafa mai ne Mamy ta shigo dakin tace "Birthday girl kin tashi?" Zara tayi murmushi tace "Na tashi Mamy, ina kwana" Mamy tace "lafiya lau, Happy birthday, yau shekarun ki ashirin cif cif. My princess ta girma, sai aure" Zara ta bata rai tace "Mamy ba yanzu ba, sai na gama masters dina" Mamy tayi murmushi tace "toh shikenan princess" Tana fesa spray ne tace "Mamy kin ga kowa yayi wishing dina amma banda Ya Farouq, ban san meyasa Ya Farouq baya so.." Kafin ta qarasa ne Mamy ta miqa mata wani dan qaramin kwali wanda bai wuce girman kwalin agogo ba, anyi packaging dinshi simple. Zara ta karba tana kallon Mamy wadda tace "dazu yayan ki ya aiko driver dinshi ya kawo miki" cikin murna ta rungume kwalin tana fadin "I cant believe this" Mamy tana dariya tace "wannan irin murna kamar kin bude kin ga abinda yake ciki?" Zara tace "ai Mamy ko ma me ke ciki I am glad Ya farouq ya tuna da ranar Birthday na" Mamy dai mamaki take yi yadda Zara take girmama Al'amuran Farouq. Bude kwalin tayi ta ga makullin mota, miqewa tayi tana ihu ta ruga da gudu zata fita daga dakin yayinda Mamy ta riqo ta tace "da towel zaki fita?" kallon jikin ta tayi tace "oops" ta koma a guje ta dauko hijabin sallan ta dogo har qasa ta fice. Mamy tana dariya ta bi bayan ta. Zara tana fita tayi tozali da wata danqararrar BMW baqa wuluk sai qyalli take. Ihu tayi yayinda gaba daya masu aikin gidan suka taso suna kallon ta suna ta yi mata dariya. Zara kam zagaye motar ta dinga yi tana kallo sannan daga qarshe ta bude ta shiga. Mamy tana tsaye a kan porch din gidan tana kallonta. Bayan ta gama kalle kallen ta ne ta fito yayinda Ma'aikatan gidan suke ta fadin Allah ya sanya Alkhairi, ita kuma tana ta yi musu godiya. Da gudu ta dawo wurin Mamy ta rungume ta sannan tace "Mamy you know what? Wannan dream car dina ne, ya aka yi Ya Farouq ya sani? I am soo happy" Mamy tace "yanzu dai kin tabbatar he cares about you ko?" Zara tace "in his own way Mamy, he is kinda weird but I still love him. Bari in shirya in je inyi mishi godiya" kafin Mamy tayi Magana har ta shige cikin gida. CENTRAL HOSPITAL Cikin sabuwar motarta ta shigo asibitin yayinda aka dinga kallon motar, wasu ma har nuna motar suke ana yaba kyan tsarinta. Bayan ta faka ne ta fito cikin fara'a kamar kullum masu aikin asibitin suka dinga gaishe ta har ta shiga ciki. Bayan ta gaisa da Nurses din asibitin ne ta nufi ofis dinshi. Secretary dinshi ne ta gaishe ta, bayan ta amsa ne ta shige ofis din ba tare da jiran ayi mata izinin shiga ba. ko da ta shiga baya nan don haka ne ta zauna a daya daga cikin kujerun ofis din. STORY CONTINUES BELOW Tayi kusan awa daya da rabi tana jiran shi ne ya bude qofar ya shigo. Bai kula da Zara wadda take zaune ba amma kuma ya ji qamshin ta wanda ya tabbatar mishi da lallai ta shigo ofis din. Bai Ankara ba sai ji yayi an rungume shi ta baya. Da sauri ya juya don ganin waye. Kafin yayi Magana ne tace "Ya Farouq thank you very much for the gift" a daidai lokacin Dr. Ibrahim ya shigo ofis din. Ganin Zara a jikin Farouq ne yasa yace "oh sorry" ya koma yayinda Farouq ya tura Zara baya cikin bacin rai yace "wai ke me ke damun ki ne? me yasa ba kya jin Magana ne?" Zara ta kalle shi cikin bacin rai tace "Ya Farouq is it a crime don nayi hugging dinka?" cikin mamaki yake kallon ta yace "kina nufin baki san hakan ba? you are not a child anymore don haka start behaving like a grown up" Matsawa tayi kusa da shi ta riqo hannun shi tace "sorry big brother, dama na zo inyi maka godiya ne akan birthday gift din da ka bani" Farouq dai mamaki Zara take bashi, ita bata san cewa baya so tana zuwa kusa da shi ba domin kuwa a duk lokacin da ta zo kusa da shi yana shiga wani yanayi wanda bai gane ba. Hannun shi ya fizge yace "na ji, go and enjoy your day". Ya zagaya ya zauna bisa kujeran shi yayinda ya fara duba laptop dinshi. Zara a tsaye tana kallon shi tana tunanin abinda zata yi mishi da zai bata mishi rai kamar yadda ya bata mata. Murmushi tayi ta zagaya ta wurinshi ta duqa tayi mishi kiss a kumatu tace "I love you big brother bye". Farouq dai kamar anyi mishi shocking ya dago da sauri ya kalle ta wanda tayi mishi gwalo ta ruga ta fice. Daskarewa yayi a zaune yayinda halin Zara ya fara bashi tsoro, ya lura ma gaba daya bata jin tsoron shi kamar da. Kuma wani ikon Allah shima baya iya hukunta ta akan wasu abubuwan da take yi mishi. Why??? ************ Zara dai tuni tayi posting din hoton sabuwar motar ta a instagram yayinda mutane suke ta yi mata congrats. Mahmood ma cewa yayi he is jealous domin kuwa ya gano cewar akwai aure a tsakanin ta da Farouq wanda yake qorafi akan kada ayi mishi juyin mulki. Hakan kuwa ya ba Zara dariya sossai yayinda ta jaddada mishi babu komai a tsakanin ta da Farouq. ALHAJI ABUBAKAR BULAMA MANSION Ruqayya tana zaune a falon Hajjaju tana duba wayar ta ne ta ga hoton motar da Farouq ya ba Zara. Cikin tashin hankali tace "what? Honey ya ba Zara kyautar wannan motar? Ni fa?" Hajjaju da take zaune tana lissafin wasu kudaden ta ne ta kalli Ruqayya tace "zauna nan dai, arzikin ma kin kasa ci. Haka dai kika ce bai damu da ita ba, ga zahiri kin gani. Mu ga hoton motar" Ruqayya hawaye na bin fuskarta ta miqa ma Hajjaju wayar. Hajjaju tace "danqari, ai wannan ko shi baya da irin ta. Lallai ma yarinyar nan, ko sarauniya sai haka" Ruqayya tace "wallahi bai isa ba, ni zai wulaqanta haka?" Hajjaju ta miqa mata wayar ta tace "ai kam sai dai kiyi haquri" Ruqayya tace "Hajjaju yakamata mu koma wurin bokan nan, ya nemi yadda zai yi kawai ya batar mun da Zara, she is trouble in my life" Hajjaju tace "kin manta abinda yace ne?" Ruqayya tace "ai dole ne ya samo wata hanyar" Hajjaju tace "toh ki bari idan na dawo daga Dubai sai mu je". *********** AL-HUSSAIN MANSION Zaune take a dakinta inda take ta shirin zuwa Birthday partyn ta da Mahmood ya shirya mata. Kiran Hafsat tayi a waya tace "babes gani nan ina shiri, in biyo mu je?" Hafsat tace "Allah ya tsare qawata" Zara tayi dariya tace "ba komai qawata, I will keep you updated". Stephanbeauty ce take ta faman yi ma Zara kwalliya a dalilin Jide yayi tafiya zuwa america. Jide shine ya kasance mai yi ma Zara kwalliya amma a dalilin baya gari ne yasa ta kira stephanbeauty. Wani stylish burgundy jumpsuit ta sa. Sannan ta daura wani multi-color gyale turban style. Ta masifar yin kyau. Sashen Mamy ta je inda tayi mata sallama yayinda Mamy ta ja mata kunne a kan kada tayi dare. Daya daga cikin direbobin gidan ne ya kai Zara wurin Party din inda Mamy ta bashi strict warning akan ya tsaya ya jira Zaran sannan su dawo tare. SAPPHIRE HALL Wurin cike yake da manyan yaran Nile University yayinda ake ta shagalin taya Zara murna wanda Mahmood ya shirya mata. Sanarwa aka yi akan isowar Zara wanda yasa aka kashe wutacen hall din tare da yin shiru. Tana shiga cikin hall din aka kunna wutar tare da yin ihun waqar Happy birthday. Tsayawa tayi cak tana ta murmushi yayinda Mahmood ya qaraso wurin ta yace "welcome Cutie, you look gorgeous" tayi murmushi tace "you don't look bad yourself sweetheart" Tare suka qarasa shiga hall din yayinda aka dinga daukar hotuna. Tun da Zara ta shiga hall din wasu maza su biyu suke ta kallon ta. daya daga cikin su ne yace "guys, wannan ne perfect time da yakamata mu samu yarinyar" dayan ne yace "kana tunanin Tafida zai bari mu je kusa da ita?" gayen yayi dariya yace "I have a plan" Taro yayi taro, Zara ta yanka cake dinta sannan mutane suka dinga bata gifts kala kala. Mahmood ne tare da abokanen shi Nura da Munnir suka dan kebe inda aka kawo musu drinks suna sha. Munnir ne ya hango wata babe wadda ta kafa ma Mahmood ido, ya kalli Mahmood yace "guy how far, naga waccan babe din tana ta kallon ka fa" Mahmood yayi murmushi yace "if not because Zara tana nan da na dana wallahi, don na kwana biyu ban yi aiki ba har bana ji na normal" Nura yace "kar ka samu damuwa, zan yi maka cover daga nan, just go" Mahmood ya lallaba ya shige wani part tare da yi ma yarinyar signal da ido ta bi shi. Gayun da suke targeting din Zara ne suka tafa tare da fadin "yes". Daya daga cikin su yace "ka ga dan iskan ya ga mace ya tafi ko?" dayan yace "oya its time for plan B, lets move" Zara tana hira da wasu 'yan ajin su ne wata ta zo wurinta cikin sallama tace "Mahmood yace ki same shi a waje wai he has something for you" ba tare da tunanin wani abu ba Zara ta miqe tare da ce ma 'yan ajin su "excuse me please, I will just be back" Zara tana tafe ne zata fita daga hall din wayar ta tayi ringing. Ganin sunan Hafsat ne yasa tayi murmushi ta amsa tare da fadin "babes gaskiya kinyi missing, I so love everything here" Hafsat tayi murmushi tace "ai gashi nan ina ganin posts a instagram.." kafin ta qarasa ne ta ji Zara tayi ihu. Cikin tashin hankali Hafsat tace "bestie what is wrong??" amma sai ta ji an kashe wayar. FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION Zaune suke a Falon shi inda take ta fada akan ya siyo ma Zara mota mai tsada amma ita bai siyo mata ba. STORY CONTINUES BELOW Farouq wanda hayaniyar Ruqayya ya ishe shi ne yace "duk yawan motocin ki basu ishe ki ba?" tace "toh itama ai motocin ta suna da yawa, ko da tayi accident da daya ai tana da wasu" Farouq ya girgiza kai yace "gaya mun sunan motar da kike so sai in sa a kawo miki, shikenan?" cikin murna ta rungume shi tare da yi mishi kiss kala kala. Wayar shi ce tayi ringing, ko da ya duba ya dan yi mamakin ganin sunan Hafsat amma ya amsa cikin sallama. Hafsat dai ba tare da amsa sallamar shi bane tace"Ya Farouq please go and help her, I think she is in trouble" miqewa yayi ya dauki maqullin motar shi a kan centre table yace "who? Me ya faru?" Hafsat ta shiga yi mishi bayani yayinda Ruqayya ta miqe tana fadin "Honey ina zaka je haka?" ko sauraron ta baiyi ba ya fice abinshi. SAPPHIRE HALL Janyo Zara suka yi inda suke nema su kai ta can wani gefe na event centre din yayinda take ihu tana qoqarin qwacewa. Jefa ta suka yi ta fadi a cikin filawowi yayinda suke ta dariya. Daya daga cikin su ne ya fara shirin cire belt dinshi yayinda dayan yake riqe da wayar Zara yana leqe don tabbatar da tsaro. Zara dai tuni fuskarta ta kumbura saboda kuka, banda sunan Allah sai na Mamy da Farouq kawai take kira. Ganin dai dagaske yake yi ne wani qarfi ya zo mata inda ta dauko wani dutse ta jefe shi a kai. Ihu yayi tare da dafe goshin shi wanda yake jini, tuni dayan ya juyo don ganin abinda yake faruwa. Da sauri Zara ta miqe tana shirin gudu. Dayan ya sa hannu ya cafko ta, wurin qoqarin qwacewa ne ya yaga mata riga. Da qyar ta qwace tare da fizge wayar ta a hannun shi ta ruga a guje, gudu take yi yayinda take ta kuka tana kallon bayan ta don gani ko sun biyo ta. Bata Ankara ba ta ji ta bugi wani abu wanda yasa tayi baya da sauri don ganin ko meye. Farouq ta gani tsaye a gaban ta. Tsayawa yayi a wurin ya kasa motsi, kallonta yake yi sama da qasa yayinda hankalin shi yake a tashe ganin yadda rigar jikin ta take a yage, what does it mean?? Runtse idanuwan shi yayi a ranshi yace "I pray nothing really happened" Zara dai ganin baya da alaman motswa ne yasa ta rungume shi cikin kuka tace "Ya Farouq gasu nan zuwa, don Allah ka fitar da ni daga nan" Farouq ya dade tsaye a wurin yana wasu irin tunanin da bai san kansu ba. Janyo ta yayi suka nufi motar shi. Har a wannan lokacin kuka take yi yayinda ya kira direban Mamy a waya yace mishi ya tafi gida shi zai dawo da Zara. Zara ta kula tunda ta hadu da Farouq bai ce mata komai ba. Cikin kuka ne tace "Ya Farouq I am sorry" gani tayi ya faka wani boutique ya fita yayinda ta bi shi da kallo. Bai dade ba ta hango shi ya fito riqe da wata leda. Bude qofar motar yayi ba tare da ya shiga ba ya jefa mata sannan ya rufe. Cikin mamaki Zara ta bude ledar ta ga wata Jallabiya doguwa baqa. Da sauri ta kalli jikinta ta ga rigar ta da ta yage, hatta saman qirjinta a bude yake. Runtse idanuwan ta tayi ta fashe da kuka yayinda take dana sanin zuwa party din. Bayan ta sanya jallabiyar ne ta fito tare da kallon shi tace "Ya Farouq na gama" bai ce mata komai ba shiga ya tada suka tafi. A tunanin Zara gida zai kai ta amma sai ta ga ya dauki hanyar gidan shi. Zara bata ce komai ba domin kuwa ta kula ran Farouq ya baci matuqa. STORY CONTINUES BELOW FAROUQ AL HUSSAIN MANSION Ko da ya faka motar fitowa yayi ya wuce zai shiga gida yayinda Zara ta biyo shi ta riqe hannun shi tace "Ya Farouq please say something mana" juyowa yayi ya kalli hannun da ta riqe shi wanda yasa tayi saurin sakin shi tace "yi haquri" Ko da suka shiga gidan babu kowa a main parlor. Yana tafe yayinda take bin shi. Wani daki ya bude a nan qasan sannan ya matsa mata ta shiga. Ko da ta shiga juyowa tayi ta kalle shi yayinda ya rufo qofar yayi tafiyar shi. Zamewa tayi qasa ta fashe da kuka. Wayar Farouq ce ta fara ringing inda ya duba ya ga Mamy ce ke kiran shi. ya amsa wayar suka gaisa sannan Mamy tace "driver yace Zara na tare da kai?" yace "eh Mamy, sai gobe zata dawo, I had to rush back to the hospital so na sauke ta a gida na" Mamy tayi murmushi tace "toh shikenan, Allah ya tashe mu lafiya" Zara tana zaune a qasa tana kuka ne Farouq ya dawo riqe da magani da ruwa a hannun shi. ba tare da yayi mata Magana bane ya ajiye sannan ya juya zai fita. Da sauri ta miqe ta shige gaban shi ta hada hannuwan ta biyu tana fadin "don Allah Ya Farouq kayi haquri, wallahi bazan qara ba" runtse idanuwan shi yayi sannan ya bude yace "out of my way" da sauri ta matsa yayinda ta cigaba da kuka tana kallon shi ya fita daga dakin. Farouq zuciyar shi tana zafi ya nufi dakin shi. ganin Ruqayya yayi tana zaune tana jiran shi. cikin kissa ta miqe tace "Honey ya na ga ka fita cikin gaggawa ne? me ya faru?" girgiza kai yayi yace "nothing" rungume shi tayi ta fara aika mishi da kisses kala kala. Cikin siyasa ya zame jikin shi daga gareta yace "let me freshen up and come" Ruqayya ta koma kan gadon tana jiran shi yayinda ya nufi dressing room dinshi don yin shirin wanka. Farouq yayi kusan minti talatin zaune cikin Jacuzzi dinshi inda yake tunanin halin da Zara zata iya shiga idan da Hafsat bata kira shi ba. Runtse idanuwa yayi ya tuno lokacin da ya gan ta, rabin qirjinta a bude. Da bai isa wurin akan lokaci ba da shikenan.. da sauri ya bude idanuwan shi a ranshi yace "Subhanalillah" Bayan ya fito daga wanka ne ya tarar Ruqayya har tayi bacci. Da alama ta jira shi ta ji shiru. Ko da ya shirya komawa yayi ya hau gado ya kwanta. Zara dai ganin cewa kukan da take yi bazai tsinana mata komai bane yasa ta shiga kewaye tayi wanka ta fito. Bayan tayi sallah ne ta janyo maganin da Farouq ya ajiye mata ta sha. Ba da dadewa ba kuwa tayi bacci. Abinda bata sani ba shine maganin da ta sha na bacci ne domin kuwa ya sani sarai idan ba shi ta sha ba bazata yi bacci ba Washegari Farouq da Ruqayya suna zaune a kan dinning suna breakfast ne ya kira daya daga cikin masu aiki yace ta shiga dakin da Zara take tace mata ta fito tayi breakfast ya mayar da ita gida. Cikin mamaki Ruqayya ta kalle shi tace "What? Zara?? A cikin gidan nan? Ya aka yi ban sani ba" ko kallon ta bai yi ba balle ya amsa ta. Zara ce ta fito cikin sanyin jiki ta nufi dinning din. Kallon fuskar shi tayi wadda take a murtuke tace "ina kwana Ya Farouq" ba tare da ya kalle ta ba yace "lafiya" ta kalli Ruqayya wadda take ta faman hararar ta tace "ina kwana Anty Ruqy" a daqile tace "lafiya" kujerar da ke kusa da Ruqayya ta ja ta zauna yayinda ta tsaya tana kallon tebir din. Ruqayya dai ta fahimci akwai wani abu don haka ne ta gyara murya tace "Zara ya aka yi kika kwana a gidan nan ban sani ba?" Zara ta bude baki zata yi Magana ne ta ji Farouq yace "na kai ta asibiti anyi running wasu tests ne akanta so I couldn't take her back home" Da sauri Zara ta dago kai ta kalle shi a ranta tace "why did he lie about this?" Muryar Ruqayya ta ji tana fadin "ki ci abinci mana" Zara ta miqe tace "bana jin yunwa" ta wuce falo ta zauna. Tayi kusan minti talatin zaune a falo ne Farouq ya fito ba tare da ya kalle ta ba yace "mu je in mayar da ke gida" Zara ta miqe kenan Ruqayya ta biyo bayan shi tana fadin "Honey my kiss" ta rugo ta rungume shi yayinda yayi mata kiss a kumatu. Zara dai ji tayi kamar ta mutu don baqin ciki, ta rasa dalilin da yasa bata qaunar ganin Ruqayya tare da Farouq. Da sauri ta kauda kanta ta fice daga falon yayinda Ruqayya tayi murmushi. *********

Post a Comment for "BA SONTA BAKE BA CHAPTER 4"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...