AMAREN BANA CHAPTER 5 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

AMAREN BANA CHAPTER 5

AMAREN BANA CHAPTER 5

- - Post a Comment
AMAREN BANA CHAPTER 5

  Bude littafin hannunsa ya yi ya ci-gaba da karantawa, alamar ya sallameta, idan ta gama surutunta. Haushi ya kara kamata, ta fita a dakin tana tunanin abin da za tai masa ta huce. Haka suka shafe sati a gidan. Fawzaan ya ma manta anyi ruwan wata abu wai Rumaysah a gidan sa, ya samu ya shawo kan Meenarsa, yanzu sun dasa a inda suka tsaya, wataran har a falo za ka ji suna hirarsu. Rumaysah kuwa ko a kwalar rigarta. Jira take yi ta samu damarta, ta gwada masa ko zai yi yaya ne, ba za ta gaji ta rabu da shi ba, ta aure shi ne, don ta zauna kuma sai dai mutu ka raba.2 Ranar alhamis ne ta same shi ta-ce. "Yaya Fawzaan ina son ka kai ni gida." "Me za ki je yi a gida kuma, wane abu ne ya faru?" ya fada ba tare da ya dube ta ba. "Kawai ni dai na gaji ne, ina so na ga 'Yan-uwana." Murmushi yayi yace "Ke da ki ke tare da babban Yayanki, me za ki yi da wasu dangi kuma? Na dauka ai na dauke miki komai."2 "'Yan-uwana mutane na ke nufi jinina, ba bare ba irinka. Idan motarka ce matsalar ka, ni sai na tafi a tawa." "Oh, to me ya sa da farko za ki fada min, tunda zaman kanki ki ke yi? "Don Allah Yaya Fawzaan ka daina min wulakanci." "Na ji, je ki shirya." Cikin doki ta haura sama ta shirya. Ta sa a ranta ma za ta kwaso sauran kayanta idan ta je. Lafiya kalau suka isa, sai da ta tashi sauka ne daga motar ya-ce. "Idan kin tashi ki nemi mai maida ke. Ga makulli." Ya wulla mata makullan gidan, ranta a bace ta cafke. Ta shiga ciki, da gudu ta haye dakin Radiyya, ta-ci sa'a dawowarta daga aiki kenan. Nan suka hau tsalle a dakin. "Sis, kin shareni, shi ne tun dawowarku ba ki zo mini ba ko?" Murmushi ta yi ta-ce. "Kuma don ni ce yayar kwabo, daga yin aure, sai na je na fara maku sintiri? So yaya amarci?" Ta fada hade da daga mata gira. Harararta Rumaysah ta yi ta-ce. "Ke ni raba ni da wannan maganar, ina Momi ta dawo kuwa?" "Tana wurin aiki, amma ta kusa isowa gida." "Sis, ta ki ta dauki wayata, tun bari na Gusau na ke nemanta, amma ba ta dauka, shi ya sa na fi so na zo mu yi magana." Radiyya ta rasa yadda za ta fada mata cewa Momi ta-ce, duk wanda ya taka gidan Rumaysah ba ta yafe masa ba. "Sis, kin yi shiru ba ki ce komai ba, kodai har yanzu ba ta sauko din bane, kin ce za ki min waya mu yi magana, amma har yau ba ki kira ba, shi ya sa fa na saukar da kai na roki Yaya Fawzaan ya kawo ni." "Kar ki damu. Muna mata magana dai kullum, yanzu ma don Abba ya tafi Lagos jiya ne, amma ya-ce da zarar ya dawo, zai daukemu da kansa ya kai mu, tunda mu ne ba ta yarda mu je ba, ai shi yana iko da ita ko." STORY CONTINUES BELOW "Yaya Radiyya, Momin ce ta-ce ba ta yafe maku ba, don kun zo inda na ke?" Radiyya ta sa hannunta a cikin tafin hannun Rumaysah, hawaye kawai ta ji sun fara zubo mata, ita da ta san wannan bakin-cikin za ta samu a dalilin auren Yaya Fawzaan, ina ma da ta hakura da auren. Yanzu wai mahaifiyarta ce take fadin a gujeta. Nan take ta ji da kyar idan za ta iya hada idanu da ita. Yaya Ra'id ta nema, amma baya gida, don haka ta kira wayarsa suka gaisa, sai da ta yi maghriba, sannan ta fito da niyyar tafiya gida. A babban falo suka ci karo da Momi, jikinta a sanyaye ta gaisheta. Ba tare da ta-ce komai ba. Momi ta juya zuwa kofa, ta kwala kira. "Audu". Ta-ce "Zo ka fitar min da wannan da Allah".4 Idanunta suka cika da hawaye ta-ce, "Momi, ki yi hakuri, mu yi magana ta fahimta. Wallahi na tuba, ina neman afuwarki." "Audu ba ka ji me nace maka bane? Ku yi min waje da wannan yarinyar, kar ku kara bari ta tako min inda na ke, idan kuma na ga akasin haka, to ku tabbata dukkanku da ku ke rike da dawainiyar harabar gidan nan, za ku rasa aikin ku, kuma sai na tabbata kun wulakanta ma tukuna." Da sauri Rumaysah ta durkusa, ta kama kafafun Momi, tana rokonta Allah, Annabi. wani irin ball ta yi da ita, sai da ta kusa isa bakin kofa. Bayanta kuwa ya samu mummunar buguwa a jikin bango.7 Haka ta mike tana kuka, ta fita a gidan ubanta. Abba ne ya yi nisa, ta san da ba ta ga wannan wulakancin ba. Tana kuka har ta iso gate, nan ta tuna ba yadda za ayi ta koma gida. "Yanzu yaya zan yi Yaya Raa'id baya gida? Idan nace Yaya Radiyya ta maida ni kuma na jawo mata matsala." Haka ta zauna a gate ta buga uban tagumi. Audu ya kade mata benci ta zauna, can dabara ta fado mata, ta kira Ra'id. "Yaya daman don Allah lambar Yaya Fawzaan na ke so ka turo min, na yi mantuwa ne." "Kin ji kunya kuwa, ace ba ki da lambar mijinki, haka ku ke zaman?" "A'a fa Yaya Ra'id kawai dai na yi Missing Number din ne." Bai ce komai ba, don ya san tana rufe masa ne, cikin minti daya sai ga lambar ta shigo, sai dai tun kafin ta buga wayar, ta ga an bude gate din gidan, motar Yaya Fawzaan ta gani, wata irin ajiyar zuciya ta yi. Bai ce mata komai ba, da kanta ta bude kofar ta shiga, a daddafe ta zauna saboda bayanta da aka hada da bango, tana goge hawaye. Tissue ya mika mata, ta karba a sanyaye, shi kuwa ya juya motar, suka fita daga gidan. Momi tana kallonsu ta windon dakinta, ta tausaya mata da ta koreta, amma kuma dole ta nuna mata kuskurenta, ba za ta bata sarari ba, har sai ta ce ta gaji da auren za ta dawo gida. Musamman da ta ga Fawzaan ya zo ta bi-shi, sai wani bakin-ciki ya kara turnike ta ****** "Me ya sa ka zo daukata, bayan ka ce na nemi mai kai ni, ai da ka sha zamanka, an fada maka ban san yadda zan kula da kaina bane." Ta fada cikin shesshekar kuka. "Ai ga shi na ga kin yi handling matsalarki, dube ki." Ya fada hade da jan tsaki. Ta juyo da sauri ta dube shi. "Wace irin matsala?" Juya idanunsa ya yi ya-ce. "Haba Rumaysah, tsammaninki dama Momi za ta tare ki da farin-cikin zuwanki ne, ko kuwa girke-girke za ta sa ayi miki na tarba?" "Oh, farin-ciki ma ka ke yi, don mahaifiyata na fushi da ni, wanda by the way, saboda kai take wannan fushin." "Ki fadi koma meye, don ki rarrashi kanki, amma da ni da ke mun san menene gaskiyar. Ke ki ka zabi komai, don haka sai ki gashe ke kadai." Tun daga nan ba ta sake ce masa komai ba. Suna isa gida, ta killace kanta a dakinta, a hankali ta dan daga rigarta tana duba bayan nata a madubi, ga shi har jini ya kwanta wurin ya yi baki, sai dai ba ta gani da kyau. STORY CONTINUES BELOW Don da zarar ta motsa da niyyar juyawa, wani azaba take ji har cikin kwakwalwarta. Tana cikin wannan halin, ta ji motsin bude kofa. Da sauri ta saki rigarta, ta juyo tana kallonsa. Kai tsaye ya nufeta ba tare da ya-ce mata komai ba ya matso daf da ita ya sa hannu a rigarta zai daga. Da sauri ta matsa da baya, tana masa kallon tsoro, tamkar zai cinyeta danya. Ga shi ta ga fuskarsa nan tamau! Babu alamun wasa, wannan ya sa ta tsorata sosai game da abin da yake shirin yi mata. Ba abin da take tunowa, sai irin yadda ya maida zancen fushin da Momi take yi da ita, da ma ita kanta abin dariya, idan banda haka ba, ashe bai ci ya tausaya mata ba, sai ma cewa da ya yi, ita ta jawo wa kanta. "Ka sake min rigata." Fawzaan ya san me take tunani sarai, don haka ya nuna mata daya hannunsa Pack din kankara ne irin na asibitin nan ya samo. "An ce maka ina bukatar taimakon ka ne? Zan iya daukar komai ni kadai, zan iya jinyar kaina, don haka ba na bukatar taimakon ka, ko tausayinka, ko wata kankararka. Tun kafin ka zo, ka na cewa ni ce mai..." Bai jira ta gama surutunta ba, ya daga rigar a fizge, sannan ya kawo kankarar ya manna a wurin, ba shiri ta yi tsit! Yana manna mata kankarar akan ciwon ta-ce. "Ishhh" Ganin haka ya sa yana kallon cikin idanunta.6 Ya lalubo hannunta guda ya sa a kan kankarar, da ya tabbatar ta rike abin ta, ya juya ya fice daga dakin. Ita kuwa ta bi bayan sa da kallo, tana mamakin al'amarin Yaya Fawzaan. Kwarai ta dan ji dadin jikin nata, sai dai ba ta da aikin da ya wuci kwanciya, har dai ta samu dan sauki. Sai dai tun da ya manna mata kankarar bai ko kara tambayarta labarin jikinta ba. Don haka ita kidimata yake yi, sai ta ga kamar shi mai tausayi ne, mai kulawa, sai ta ga ashe ba wanda ya kai shi rashin tausayi da mugunta. Bayan kwana biyu. Da safe aka danna Bell din gidan. Rumaysah ta tashi ta leka ko waye a kofa, wata mata ta gani, amma ba ta gane ko wace ce ba. Don haka ta bude a hankali, har sai da matar ta shigo falo, sannan suka gaisa. "Na san ba ki gane ko wace ce ni ba ko?" "Gaskiya ban dauki fuskar ba." "Ni makwabciyarki ce, sunana Safiyya, shekaranjiya Mai-gidana yake fada min an kawo amarya a gefen mu, shi ne nace bari dai na fara shigowa mu gaisa." "Ayya, ki yi hakuri nai miki kallon rashin sani. Sannu da zuwa. Ni sunana Rumaysah." "Da fatan dai ba ki da wata matsala da unguwar ta mu?" Rumaysah ta yi dariya ta-ce. "A'a, Alhamdulillah, har na fara sabawa." Nan ta mike ta kawo mata drinks da abubuwan tabawa. Ta kula Safiyya ta fita shekaru, don za ta yi kusan sa'ar Yaya Khadija, don haka Anty Safiyya take ce mata. Ba ta dade sosai ba ta-ce. Za ta tafi tare da fadawa Rumaysah (Flat Number) din su. Kwarai Rumaysah ta ji dadin yadda Anty Safiyya ba ta duba ta fi ta ba, har ta shigo suka gaisa. 'Yan Gombe ne, da ita da mijinta aiki ne ya kawo mijin Abuja, matar akwai ta da karamci ,irin dai na Gombawa, diban fari. Birni mai kamar Kano daga nesa.8 *********** Khansa'u na zaune a daki, ranta duk a bace wunin yau, saboda gaba daya ta rasa gane kan Sa'ad haka kawai kuskure ba yai masa kadan, zai hau zazzaga mata masifa, zuwanta Gusau ta so ta fadawa Momi matsalarta. Amma ta tadda wanda ake ciki ta fi tata. Abubuwan da suke damunta sun yi mata yawa, ga aiki a gidan kamar sun samu mai aiki, ba wani yawa suke da shi a gidan ba, amma idan aka fara kirkire kirkire, don kawai Sa'ad ne babba idan kannensa suka rinka tuttudowa gidan kamar dama jira suke yi ya kara mata, ga shi Bilkisu kamar ko a jikinta, koda yake ita kam aiki take kamar jaka. STORY CONTINUES BELOW Yanzu yau din da safe tana shiga falonsa, bayan sun gaisa ne yake ce mata. "Wai me ya sa ke duk al'amuran da suka jiban ceni ba ki maida hankalinki a kai kwata-kwata? Kin ce ba ki iya girki ba, koda yake gani na yi da kaina na nema maku mai girki, amma ki tsaya ki kula da yadda za ayin ma aiki ne a gare ki? Na rasa wace irin rayuwa ki ke so ki yi. Gaskiya ni ba zan lamunci wannan abin ba, ni mutum ne mai jama'a kuma ina son a kula min da komai na su da nawa. Sannan daga yau ba na son a kara sawa yaran nan Indomie, domin tafiya makaranta." Tana jiransa har ya gama sai ta-ce. "Ni gaskiya ban maka karya ba tun farko, ni ban saba da wahala ba, kuma hakan ka ganni, ka yarda ka na so-na, sai kawai ka kama ka yi ta fadace-fadace? Indomie kuma ina yi ne, saboda shi ya fi sauri, kar yara su yi latti". "Ke ba ki koyi dabara bane a gida? Ashe ba rage aiki ake yi ba da dare, da safe sai a kammala shi? Koda yake meye amfanin fada miki ma." Fita ya yi ya bar mata falon. Tun lokacin kuma bai dawo ya-ci abincin rana ba, duk da Hasiya ce ke yi, ita nata ta tsaya ta ga rabiya, don ita ba wai iyawa ta yi ba. Shigowarsa dakinta ma ba ta sani ba, saboda ta yi nisa a tunani, sai hawaye take yi. A hankali ya zauna a gefenta ya-ce. "Khans, meye ne ya sameki?" Dauke kanta ta yi cikin fushi. "Yaya za ka tambayeni me ya sameni, bayan kai ka fi sani." "Wai na tambayeki mana, kin san muhimmancin aure a rayuwar Dan-Adam kuwa?"3 Shiru ta yi tana kallonsa. "Aure ibada ne Khans, kuma hakuri ake yi, kin ji ko? Yanzu meye problem dinki?" "Ni gaskiya ba na son fadan da ka ke min, sannan aiki yai min yawa a gidan nan, tun safe fa ba ni da hutu." "To na ji. Insha-Allahu zan rage miki, fada kuma zan maki cikin kulawa, amma kuma ga shawara, me zai hana ki shiga Islamiyyar nan da Bilkisu ke zuwa, kin ga asabar da lahadi ne kuma tare da yara duka za ku na tafiyar. Idan ya so a cikin ranakun sati kuma ki shiga makarantar koyon girki?"3 Da sauri ta kalle shi, sai kuma ta ji kunya da ya-ce da makarantar koyon girki. "Kin ga ba na son a kawo min miyar kukar da ta fi kama da kunu, ko me ki ka ce?"13 "Sa'ad ka na tsokanata ko? To ni na taba kada kuka ne, za ka ce min shi ka ke so, bayan ka san ba kai kadai za ka zo gida cin abinci ba?" "Mun surka da ruwan zafi, kar ki damu." Duka ta kai masa cikin shagwaba.2 "Na amince zan shiga, yaushe zan fara?" "Kar ki damu, zan sa ma miki Forms din, idan na fita da safe Insha-Allahu, zuwa lokacin, don Allah idan Hasiya na girki, ki tsaya a kanta ki ga me take yi, saboda gaskiya idan ba dole ba, ni ba na son cin abincin 'yan aiki. Ki tabbatar cikin tsafta ake hada min abinci na."3 "To shi kenan. Insha-Allahu zan kula." "Yawwa, my Khans ko ke fa, yanzu dan yi murmushi mu gani?" Nan ta sakar masa da murmushi, lokacin ne wayarta ta shiga kara. Sa'ad ya yamutsa fuska, "Waye kuma wannan zai damemu?" Dariya ta yi, sannan ta daga ganin lambar Radiyya ya sa ta dauka. "Hello, Radiyya?" "Hello Yaya Khans, yaya gida, yaya su Ummi da Uncle Sa'ad?" "Lafiyarsu kalau, me ya faru na ji kamar ki na kuka?" "Yaya Khans, ba mu san yaya za mu yi ba, jiya fa Momi ball ta rinka yi da Rumaysah wai ta fita daga gidan, kar ta sake zuwa inda take." "Momin ta fadi haka? Me ya sa ba za ta hakura bane, ni ban san meye dalilin wanan tada hankalin ba, bayan an riga an daura aure, ai sai dai ta dau hakuri. Watakila ma sun daidaita kansu warhaka." STORY CONTINUES BELOW "Meye abin yi?" "Kar ki yi komai, ki jira sai Abba ya dawo, sai ki fada masa." Suna gama wayar, ta fadawa Sa'ad abin da ake ciki. "Kai wannan abin, to kun taba tambayar Momin ko me ya sa ta tsani Maman haka?" "Koma menene, yanzu kam tunda an riga anyi masu aure, ai sai ta hakura, amma sai fushi take yi da Rumaysah." **** Ranar laraba da yamma Umar ya ajiye Firdausi a gidan Rumaysah, dadi ya cika su fal! Saboda murnar ganin juna. "Na ji halinki, shi ne har da ce min tun wancan satin za ki zo, ki ka shanyani." "Wai, ina ni ina zuwa gidan amarya tun a satin biki, shi ya sa na matse, ki ka ji ni shiru. To yaya angon naki?" Ta fada hade da zungure ta da kafada. "Uhmm oho, ni wataran ina mantawa ma mu biyu muke rayuwa a cikin gidan nan, sabgarsa yake yi, ina tawa. Tsaya tukun Firdausi, wai me ki ke nufi ne? Na ga kin wani canza min. Kar dai ki ce min ciki ki ke da shi, yau kin shiga uku." Firdausi ta yi murmushi ta-ce. "Ehem, meye abin shiga uku, me zan jira? Ni da karatu na ya zo karshe, ko yau na fara karatu, ba abinda zai hanani haihuwa, sai dai idan Allah bai kawo ba. Bare ba wanda na ke so irin Umar, to me zan ba shi da ya wuce wannan?"2 Rumaysah ta tabe baki, sanann ta-ce. "Ayya ke kam kin ji dadi, ni kam har abada ba zan haifi yara ba, ga shi ina son yara." Firdausi ta yi dariya ta-ce. "Me ya sa za ki ce haka? Komai lokaci ne. Kar dai ..." Rumaysah ta-ce "Meye, ni ki rabu da ni, ba ki san matsalan da na ke ciki ba, ranar fa Momi korata ta yi da duka, wai don na auri Yaya Fawzaan, ba ta san shi ma gara ni yake yi ba. Ni kamar ma na koma gida na yi zamana, ya fi min komai." Firdausi ta-ce. "Ki na hauka ne? Yaushe muka kawo ki, za ki wane ce za ki kashe aure? Ai ke da Yaya Fawzaan tip da taya, ba mai raba ku sai Allah". "Ke ni bar maganarsa yana sani yunkurin amai, kar na kwaro miki ki kala min sharri."2 Suka sa dariya, suka tafa dai-dai lokacin Fawzaan ya shigo, ya dawo daga ofis. Tsabar murnar zuwan Firdausi ya sa Rumaysah ba ta isar da ita sama ba, wanda shi ne falon da take amfani da shi, nan falonshi suka baje. "Yaya Fawzaan, sannu da dawowa." "A'ah sannu da zuwa." Ya dubi Rumaysah ya dubeta sannan ya-ce. "Firdausi right?" Mamaki ya kama su dukansu biyu, saboda Rumaysah ba ta taba nuna masa Firdausi ba, haka bai taba ganinsu tare ba. "Sannu da zuwa, lallai Rumaysah muna da manyan baki, shi ne ba ki fada min ba, haka ake yi ne, ko ruwa ba ki kawo mata ba?" Nan ne Rumaysa ta tuna tsabar hira na cinsu ba ta ko tuna kawo abin sha ba. Sama ya haye. Ta make Firdausi. "Wash! Za ki karyani". "Meye na wani washe masa baki har da wani sannu da zuwa, tukuna ma a ina ki ka san shi?" "Ke easy, meye kuma don mijinki ya ganni ya gane ni, watakila ke ki ka taba nuna masa hotona." "Ni ban taba hira da shi ba." "To can maku, kya tambaye shi, za ki kawo mun ruwan ne, ko sai na shiga na daukoda kaina." "Ba ki da kyau, ki shigo ki karba ta nan, kya ga kicin din nawa." Wanka ya yi kawai ya fito, domin tafiya masallaci, kicin ya bar su, sun bi sun cika gidan da kamshin girki. Idan sun fara hira a Chats dinsu har ba a cewa komai, bare sun hadu kam, ai sai ta Allah. Ya tuna mamakin da ya gani a fuskokinsu, da ya kira sunan Firdausi, sai ya yi dariya. Yana fita, suka haye sama, ta nunawa Firdausi gidan, dakin Fawzaan ne kawai ba ta kai ta ba. Firdausi kuwa an bar ta da santin gida, domin kuwa komai dan ajin gaba aka zuba a gidan. Rumaysah ba ta san aikin waye ba. Ita dai ba abinda ya fi ba ta haushi sai tsabar cin fuska ma, ko ya kwashe kayan da ya saya, don Meenar da yake so, ko nufinsa haka zai bari, sai ya aurota, oho? Sai da aka yi Issha, sannan Umar ya dawo daukar Firdausi. "Daughter karfi da yaji dai an yada gwamnatin mu." "A'a Baba na kar mu yi haka da kai, ku da kanku ku ka yasar." Dariya ya yi sanan ya-ce. "Tunda kin ce haka na yi shiru, kin san ance matar mutum kabarinsa. Allah ya sa ke ba rabon aboki na bane. Allah ya ba ku zaman lafiya." Sam ba ta so Umar yana dauko mata batun Saleem, shi ya sa ma ba ta cika zumudin zuwa gidan Firdausi ba, don sai dai idan ba su hadu ba, maganr kenan. "Mun gode kwarai da zumunci." Har bakin kofa ta raka su, sai da suka tafi, sannan ta koma cikin gida. "Bakin naki sun tafi ne?" Ya tambaya. "Dama ka na ciki, shi ne ko ka zo ku gaisa da Umar din?" Hada rai ya yi, sannan ya-ce. "Ba lalle bane a yi abota da abokanki ba, bayan kuma na san Firdausi ita-ce abokiyar gulmarki." Zaro idanu ta yi, ya-ce. "Oh, da sai ki yi tunanin ki na ta Chatting ban san me ki ke yi bane?" "Bincika min waya ka ke yi? Wannan ai bai dace ba leken asiri ne. Kai na taba leka maka abinka, ko kuwa na shiga gonar ka?" Juyawa ya yi, bai ba ta amsar tambayarta ba, sai cewa ya yi. "Yawwa, don Allah a bar shiga min daki na, na fi son ganinsa yadda na ke tsara komai na. Idan ba ki kula ba, ki na da dakinki a gidan ke ma." "Me zai sa ka iyakance min wuri, dakin da na ga dama nan zan kwanta, idan ka na da matsala da hakan kuma, za ka iya sake gida, idan ka ga dama ka wuce ta can, kar ka sake dawowa." Ta juya ta haye sama abin ta, tabbas ya rainawa yarinyar nan, amma ya fara ganin alama idan ba ya yi da gaske bane, idanunta a bude suke za ta ba shi mamaki. Ranar kwatsam! Sai ga Abba ya zo duba su, bai fada masu ba, wannan karon Rumaysah kuwa yayi mata daidai, domin kuwa ta ga alama rabata da mutane yake son yi, bayan shi ma kuma bayi da dadi.+ Haba murna wurin Rumaysah har ba a magana, tana ganinsa kawai, ta saka masa kuka. Fawzaan ya shiga damuwa kar wannan tai masa shirme mana, yanzu idan ta fadawa Abba abin da yai mata wancan zuwan Abban ai ta kwafsa masa. "Baby, lafiya ki ke kuka? Me yake faruwa?" Fawzaan ya yi yake ya-ce. "Abba ina ga dadin ganinka ne ya sa ta kuka." Ai kuwa ya canka daidai, domin kuwa nan ta sa dariya a tsakanin kukan nata. Ajiyar zuciya ya sake. Abba ya-ce. "Da fatan dai ku na zaune lafiya, babu wata matsala?" A sanyaye Rumaysah ta-ce. "Lafiya kalau Abba, yaya Momi?" Domin duk yadda ta tsani auren Yaya Fawzaan, ta fi tsanar rabuwanta da shi, saboda tana gani idan ta rabu da shi kamar ta ba shi wani 'yancinsa ne, wanda zai mata duk abinda yake so. "Lafiyansu kalau, an kusa komawa makaranta ko?" "Eh saura sati daya Insha-Allahu." "To ya yi kyau. Allah ya taimaka. Fawzaan ina fata dai Baby ba ta saka ciwon kai? Da zaran fa ka ga tana wani kuskure, to ba wanda ya fi cancanta ya yi mata gyara, sai kai. Ka na ji na ko? Ba sai ka bari wani ya shiga maka al'amarin gida ba, ka tsaya ka yi da kanka." "Insha-Allahu Abba, bare ma ba wata matsala, tana kwatanta komai daidai gwargwado. Akwai ta da kokari gaskiya." Ta gefen ido ta saci kallon Yaya Fawzaan, wane dalili zai sa ya yi ta koda ta a gaban Abba? Maimakon shi da bai ba ta daraja ba, yai mata cin mutuncin da ya so, amma sai kareta yake yi yanzu. "To shi kenan, dama nace bari na zo ne na duba ku, tunda komai lafiya. Alhamdulillah! "Abba yaushe su Yaya Radiyya za su zo? Dukan su fa har yau ba wanda ya zo min." "Har yanzu babu wanda ya zo? Lallai ba su kyauta ba, ina komawa, zan turo su ko gobe ne, sai ki shirya ganinsu kin ji ko?" Cikin murna ta-ce. "Na ji Abba, mun gode. Allah ya kara girma." "Ameen." Har mota suka raka shi, ita ta fara shigowa ta bar shi da Fawzaan, suna kara tattaunawa. Yana shigowa ta-ce. "Na dauka yanzun ma a gabansa za ka tasa keyata ka kora ni ciki ne, tunda abin neman magana baya maka kadan."2 "Kin san bai yi nisa ba, sai na kira shi nace masa kuka ki ke min kullum ba kya son zama a gidan nan, wai sai dai na sake ki."2 "Na fada maka ai, aure kam ka auru, kuma ko za ka yi yaya, ba ka isa ka rabu da ni ba, sai dai mu ci-gaba da zama a haka". Bai tanka mata ba, don haushinta yake ji, wucewa kawai ya yi abinsa, ya bar ta tsaye a falon.6 STORY CONTINUES BELOW Abba yana komawa gida, kai tsaye dakin Momi ya shiga, da yake tana gida, ya sameta a ciki. "Atika ashe dama hana yaran nan zuwa gidan bebin ki ka yi da gaske? To akan wane dalili za ki raba masu zumunci? Idan ke kin gaji da ita, kin yafe kyautar da Allah yai miki, ai ban ga dalilin da zai sa ki raba ta da 'Yan-uwanta ba. Sannan kuma daga yau ba na son na sake jin makamarcin haka ya sake faruwa. Duk ma furucin da ki ka san kin yi, ki janye, saboda ranki zai baci idan na sake samun labarin har nan da kwana biyu, ba wanda ya je ya dubota. Wane irin shirme ne wannan?" Tayi shiru ba ta ce masa komai ba, sai da ya gama sannan ta-ce. "Ba sai su yi ta zuwa ba, ni dai kar ta zo inda na ke, tunda ba ta ba ni darajar mahaifiya ba." "Ashe da kin dauketa a matsayin 'ya ne, kin ja ta a jiki, da sai ki fadi hakan?" "Daman ai ba ta laifi a wurinka tunda ta shiga zuri'ar Sogiji da su da ita duk ba za su yi maka laifi ba, ni ce dai Atika Sarkin laifi. Yaranka ne, kai ma sai ka fada masu su je." Ran Abba a bace ya bar dakin nata. Nan ya bada umarni wa Ra'id da Radiyya su shirya su je su ga Rumaysah. Tana shirya 'yan kayanta a wardrobe din dakin da ta dauka wa kanta, tana goge hawaye saboda tuna irin yadda Momi ta yi mata. Fawzaan ya shigo dakin ya-ce. "Me ya sa ba kya amfani da can dakin, ai ya fi girma?" "Ina ruwanka? Baya ga haka ma ta ina zan yi amfani da daki, ba ka kwashe kayan matarka a ciki ba." Fawzaan ya dubeta kai a daure. "Kayan matata?" "Eh mana, don ma ka wulaqantani, shi ne har da jera mata kayanta a dakin, tun ma kan ta zo kenan, idan ka aure ta kuma ina ga gidan za ku fidda ni, dama Momi ta daina so-na saboda kai, yanzu kam ban san inda zan shiga ba kenan, idan hakan ta kasance." Sai yanzu ya gane kayayyakin da take fada, su ne wadanda Muneerah ta zo ta shirya mata su ana gobe zai tafi Gusau daurin aurensu. "Ki dauka na ba ki."4 Wani kallo tai masa tukun sannan ta-ce. "Lallai ma, ai ban ce maka banda kaya ba, don dai kawai ranar na bar su a gida ne, kuma tunda su Radiyya za su zo, zan ce mata ta kawo min su. Ka rike kayanka, ka jira dai ta zo, sai ka bawa mai su." Murmushi ya yi sannan ya-ce. "To ni na ba ki su, tunda ita ba ta ma gansu ba, kin ga kenan ikon bayarwa duk wanda na so yana hannuna, kuma ke na bawa, shi kenan, idan ta zo sai na saya mata sabbi irin na yayi, kin san wannan kalolin, sai irinku ai..." Ya fada a kyamace. Ran Rumaysah ya soma baci. Don haka ta bar abinda take yi, ta juyo ta dube shi. "Ni ban ga meye amfanin ma soyayyar taku ba, tunda har yau dai kun kasa aure. Idan don ta ni ce, da ka auro ta randa ka aureni, da ya fi min kwanciyar hankali." "Ba ruwanki da wannan, duk lokacin da na yi niyyar kawota, ai za ki gani, ki yi sabgar gabanki, ko kuwa abin da ya fi, ki more rayuwar kuncinki kafin nan." Ya fada zai fice daga dakin ne. Rumaysah ta-ce. "Me ya sa ka ke kareni wurin Abba? Tunda ka san ba son zama da ni ka ke yi ba?". "Saboda zama dake ya zama dole, domin shi ne maganin matsalolinmu, duk kuwa lokacin da matsalar ta warware to (You are free to go). Za ki iya tafiya". Da sauri Rumaysah ta sha gabansa ta-ce. "Mene ne manufarka da wannan furucin, na tafi gidan mu kenan?" "Ban ce na sallame ki ba, amma duk randa ki ka ga kin cimma burinki na aurena, zabi ya rage naki, ko ki tafi, ko ki zauna." Yana fadan haka, ya fice a dakin. Nan kan Carpet ta zauna, ta ci-gaba da kukanta abin ta, wanda yanzu kam har ya fara yiwa jikinta illa, saboda yanzun ma ciwon kai take yi. Daurewa ta yi ta sauka, ta hada abincin ta mai dadi.2 STORY CONTINUES BELOW Tana gamawa, ta diba a (Food Flask), sannan ta debi wani daban, ta shirya ta fita zuwa gidan Anty Safiyya da shi. Sun saba kwarai da matar, haduwansu sau uku kawai, amma tana ji kamar sun dade da sanin juna, yaran Anty Safiyya biyu, duka mata gwanin ban sha'awa. Fawzaan kuwa duk maganganun Rumaysah sun dame shi, shi ma kwarai yake son ya ga ya mallaki Meena, amma tun aurensa da Rumaysah kullum idan ya sake dagowa Meena maganar, sai ta kasance kamar da wata a kasa, don ta ita baya samun matsala, saboda ya san tana son sa, amma ya qudurta a ransa, zai bincika ya ji menene. A satin da Rumaysah za ta koma makaranta ne. Fawzaan ya je gaida Mama, take ce masa "Ya kamata fa ku je ku gaida su Yaya Shatu, ban yi tsammanin ko waya ma kun yi ba ko?" "Wallahi Mama abubuwan ne sai a hankali, amma Insha-Allahu ko ran asabar ne, sai mu je, in ya so mu wuce Kano ma mu kwana. Mu dubo miki Sajeedar ki." Mama ta yi dan murmushi. "Ai ta-ce kowa ya shareta. Yaya Uwa kawai take gani." "Kar ki damu, za mu je Insha-Allahu, zan gani, idan ina da sarari a ofis asabar din da safe sai mu tafi." "Yawwa, to Allah ya kai mu. Yaya Rumaysah ba kwa dai samun matsala ko?" Kansa a kasa ya-ce. "A'a babu." "To, na fi son jin hakan. Don Allah ka rike ta tsakaninka da Allah, kar ka kuskura na ji komai ya taso daga wurinka, ko daga wurinta ne, na san kai ne ka tayar, saboda na san ba ta da fitina". Fawzaan kuwa a ransa ya-ce Hmm! Ba ki dai sani ba kam Mama. "Ka kula da ita kamar yadda ka yiwa Baffanka alkawari, yana jin dadi kullum, idan ya duba ya ga yadda ka hakura da son ranka, ka dubi zabinsa. Yaya labarin Ameenan ne?" Haba an kirawa Fawzaan abin da ya fi so, nan ya shiga washe baki. "Lafiya kalau take."2 "Kun sake magana ne da ita? Don kamar wancan satin na ji Baffa ya-ce za su yi magana da Babanta, to ya dai ce zai waiwaiyi Baffan, ban san yaya suka yi ba." Fawzan ya yi shiru, domin Meena ba ta fada masa komai game da hakan ba. "To na gode Mama." "Ba komai, ya kamata ka koma ka bar Rumaysa'u ita kadai a gida, ga dare ya soma yi." Har ya mike ne, ta-ce masa. "Ga wannan, dambun kaji ne, sai ka kai mata." Fawzaan ya yi godiya, sannan ya sa aka sa masa a mota ya wuce gida. Yau kuma yana shigowa falon, ya tsaya cak! Saboda Madam din tana kan kujera, sai sana'a take yi, wato danne-dannen waya. (Bumper Shorts) ne a jikinta da wata 'yar riga da ba ta kai Vest ba, amma ta wuce Bra. Gashinta a ware ya zubo kan kafadunta. Kau da kansa ya yi, tamkar ya ga wata dodo. Kai tsaye ya ajiye mata sakon Mama bisa (Dining Table), daga can ya-ce. "Ga sakon ki Mama ta bayar a kawo miki."8 Tashi ta yi ta isa, don ta ga sakon, tana ganin dambun nama, ta hau murna. "Wai Mama gaskiya ta burgeni, mun gode; Allah ya biyata." Nan ta debi kadan ta sa a bakinta, tana lumshe idanu cikin santi. Fawzaan ya kau da kansa daga fuskarta, daidai lokacin ta-ce. "Ka na so na zuba maka?" "A'a ki bar shi, sai da safe zan ci." "To Allah ya kai mu." Dauka ta yi ta wuce da shi kicin, ba abinda yake damunsa, illa bugun zuciyarsa. Ya yi niyyar kallon labaru, amma ba shiri ya shige kwanciya. Koda ta kammala, ta kashe komai abin ta, ta yi shirin barci.2 Yana dakinsa yana tunanin, kamar ya sauka, sai can wata zuciyar ta-ce masa me zai yi da yarinyar da ba ta da kamun kai, ta gama yawonta da samari? Sam ba daidai shi bace ita, dole ya hakura su yi aurensu da Meena ita kadai yake so. STORY CONTINUES BELOW Da safe ya zo fita, ya ga abinci kan Table, yau ma kamar kullum, kin bi ta kai ya yi, don tunda ya sa tayi masa abinci, ta ki, ya daina cin abincin gidan, sai dai ya saya. **** "Ki shirya kayanki gobe za mu tafi Kaduna, daga nan za mu karasa Kano, saboda haka may be mu kwana daya, idan Allah ya kai mu." Da ido kawai ta bi-shi, ya juyo ya san sarai taji abinda ya-ce, amsawa ce kawai ba ta ga damar yi ba. Ta shirya kayanta komai fes! A akwatin ta dan karami, randa za su tafi kuwa, wani lace ta sa mai laushi (Olive Green) mai haske, an masa ado da zare kalar makuba da kuma ruwan goro, ta sha daurinta da kwalliyarta ta yi fes!5 Sannan ta sa mayafin da ya shiga da kayan nata. Yana saukowa, ya samu ta shirya. Ya kare mata kallo ya-ce. "Je ki canza mayafi." Ta karewa jikinta kallo ta-ce. "Meye matsalar wannan?" "Wai ke ba kya taba yin abu ne, sai kin yi wa mutum gardama? Ki je ki canza mayafi nace, kuma kar ki fesa turare a jikin wanda za ki sa din." "Yau na ga ikon Allah, turaren nawa wari yake maka?"2 "Wa ya fada miki mace na bulbula turare idan za ta fita? Sannan wannan yana wani irin hamami-hamami". Ya fada yana yamutsa fuska. Haka ta hakura ta je ta canzo mayafi ba don ta so ba, ranta duk a bace. Kulle gidan suka yi suka tafi. Sai da suka bi gidan Baffa da Abba su kai masu sallama.4 Rumaysah kamar ta yi tsuntsuwa ta je ta ga Momi haka take ji, amma ta san ko sun hadu, ba za ta ba ta fuska ba. Duk da haka ta hakura, sannan ta yi shahada, ba ta daki, a falo ta sameta. "Ina kwana Momi?" A hankali ta dago ta dubeta, da gani hankalin yarinyar a kwance, wato ita kam ma ba ta damu da abinda ke faruwa ba, ta je ta natsu abin ta ita ta samu gidan miji. "Ba na ce miki kar ki sake nuna min fuskarki ba?" "Momi, tafiya za mu yi, shi ya sa na zo mu yi sallama, don Allah Momi ki yafe min, ki daina fushi da ni." Wani irin tsawa mai gigitarwa ta sauke mata, ba shiri ta bar falon. Ta sauko suna shiga mota, ta fashewa Fawzaan da kuka. "Lafiyanki, meye haka kuma? Ko kin fasa tafiyar ne, na maida ke?" "Ba haka bane, mu tafi kawai". Fawzaan ya fara jin haushin yadda Momi take yiwa Rumaysah, sai ka ce ba ita ta haifeta ba, haba ai gabar ta yi yawa. "Hmm! I guess muna nan tare kenan, tunda har yau Plan dinki bai soma aiki ba, bare ki cimma manufarki, ki rabu da ni ko?" "Sai dai ka mutu, ba inda zan tafi na barka, auren mu, auren dindindin ne, mutu ka raba, takalmin kaza, idan ana auren kaca, to namu auren kaca ne, kuma yanzu na fara komai wuya komai dadi.12 Ko Momi ta sauko sun shirya da Mama, ba inda zan je, gwamma ka san da wannan, idan ma ka fadawa budurwarka ne, za ka rabu da ni, to ka je ka ce ka fasa." Shi Mamakinta ma yake yi yadda ya ga ta wani dage sai masifa take yi. "Yadda ki ka so, koma yaya ne." Yanzu kam ta fara tantamar anya ba da gan gan yaya Fawzaan yake jan birkin nan ba? Don har ruwan cikinta ya fara tsalle, haka kawai mota sai fincikarsu take yi?2 Ba ta ce masa komai ba, suka ci-gaba da tafiya motar ta ware, sai can kuma ta ci-gaba da yin hakan. Kai daga karshe kam ma tsaya masu ta yi sai da Fawzaan ya gangara gefen hanya. Buga tayar motar ya yi cikin jin haushi, yanzu me ya san zai fara yi? Wayarsa ya fitar domin, ya gwada neman lambar bakanikensa. Ya daga kai ya kalli Madam din ta wani harde a gaban mota, sai wani ciccin magani take yi. Ina ruwan gimbiya 'yar Sarki. STORY CONTINUES BELOW Ya buga ya yi sau shida, baya samu, sai da ya kalli wayar ta sa da kyau ne ya fahimci cewar babu Service ne a wurin. "Ya Allah!" Ya furta a hankali, nan da nan kansa ya shiga caji, yana tunanin abin yi. Cire hularsa ya yi ya bude Bonnet din motar ya yi iya dabarar da ya ke tunanin zai taimaka motar ta tashi, amma duk lokacin da ya koma kan sitiyarin, sai ta sako wannan kukan. Daga karshe ya bugi sitiyarin, ya dubi Rumaysah tana zaune a gefe, ko a jikinta. Wai an tsikari kakkausa. Tabbas yanzu kam ya san ba daga nan matsalar take ba, bai wuci man da ya sha jiya bane, ya jawo masa wannan kwabar. "Wai ke ba ki da aikin yi ne, sai danna waya?" Kallonsa ta yi tsab! Sannan ta-ce. "Ka tanadar min da wani abin yi, kafin ka san na yi da mu?" Ba tare da ya ba ta amsa ba, ya wangale kofofin motar ya ci-gaba da neman Muftahu Bakanikensa. "Ni fa gaskiya na fara jin zafi, ka kunna mana AC." "Ki shiga karkashin bishiya ki sha iskar Damina" Kallon sa ta yi, ta ga ko a jikinsa, baida niyyar yin wani abu. "Don Allah ka fita ka gyara mana mu tafi, ka ga wannan hadarin, idan ruwa ya sauko, yaya za mu yi?" Wafce! Wayarta ya yi, za ta yi magana, bayan ta ga yana buga wasu lambobi. Ya rasa me take yi da wayar, tunda ita ma ba ta da Service. Kan cinyarta ya wulla mata kayanta. "Ka san dai akwai kalmar na gode da don Allah ko? Yanzu yaya zan yi da ka fasa min wayata?" ""Ke! kin cika min kunne da surutu, ki min shiru." Amma ina, kamar wanda ya-ce ta kara bude baki. "Allah, duk randa ka fasa min waya, sai ka biyani, kuma ni na fara jin yunwa ka sama min abinci."4 Fita ya yi a motar ya tsaya a bakin titi, yana kokarin tare mota. Fitowa ta yi ta biyo shi bakin titin. "Yaya Fawzaan, ba ka ji ni bane? Babu wani kauye ne a kusa, ni fa idan ban ci abinci ba, hankalina yana gushewa, suma zan yi."2 Ya kusa ya mangare ta, ko za ta fi suman da wuri, don ya fara gajiya da surutunta. 9 "Yanzu yaya za mu yi, ka kawo mu jeji ka ajiye mu, ko wace mota idan ta zo ta wuce. Ni dai gaskiya, ka maida ni gida kawai, haka kurum!" Juyowa ya yi ransa a bace, ya zaro mata idanunsa. "Koma mota ki zauna, idan ba haka ba, ki na ji ki na gani zan tari mota, kuma na tafi na bar ki anan, ke ki gyara motar, tunda kin fi kowa iya surutu, sai ki aikata wani abin zai taimakeki." "Ina ji ka na taka birki da gangan, za ka ce wani wai mota ta lalace."4 Juyawa ya yi ya nufi kanta da sauri, ba shiri ta koma da baya, hannunsa ya saka ya ritsata a cikin marfin mota. "Kin dauka ina jin dadin zama da ke a jeji ne? Ko kuwa kin dauka fuskanki abin burgewa ne, ko kuwa kyawunki ya kai ya sa na tsaya a kungurmin jeji, na sa ki a gaba na yi ta kallo, don na rasa aikin yi? Bari na fada miki, mota ta farko da zan fara gani, shiga zan yi na tafi na bar ki a jejin nan, saboda ba na son ganin koda inuwarki, bare jin surutunki marar yankewa. Da na san shan mai na a wannan gidan man zai sa na kara zaman fiye da awa biyu dake a mota guda, da na taho da kwatan tanki na yi shahada. Duk Mama ce ta janyo min, idan banda haka, na yi niyyar na tafi gaishe-gaishe na ni kadai, ba tare da ke ba, matar kaddara."6 Maganganunsa sun yi mata dirar mikiya, wani irin bakin-ciki ne ya taso ya turniketa, ta ji kamar ta yayyaga masa fuskarsa, ga shi ba hali, don ba ta tsammanin yadda ya mata nan, za ta yi kwakkwarar motsi ba tare da ta gogi jikinsa ba, da ta goge shi kuwa gwamma ta yayyanke fatar jikinta. STORY CONTINUES BELOW "To ni na sa ka shan mai marar kyau, za ka zo ka sa ni a cikin wuya? Ni dai ko ka sa ma min mota ko kuwa duk motar da ta zo wucewa na sa maka ihu, nace ka sato ni ne."3 Ba shiri, ya matsa daga kusa da ita, ya ja tsaki, sannan ya koma aikinsa na tare mota, bai kara minti biyar ba kuwa, ya-ci sa'a sai ga wata motar kasuwa ta tsaya. Matsawa ya yi kusa da direban, suka yi magana. Rumaysah kuwa sai aikin kwado masa harara take yi daga inda take tsaye, a jikin motarsa. Tana jira ta ga motar ta wuce, kamar wacce ta tsaya dazu ta wuce, sai ta ga mutumin ya gyara Parking. Boot ta ga ya bude, ya fidda jakunkunan su, ya sa a motar can. Hannunta ta sauke daga goyon da ta masu kirjinta, don ita tunanin ta daya, a ina zai sa ta a wancan motar? Domin kuwa wata shirgegiyar mata ta gani a gaban motar, sai wata 'yar-uwarta a baya da kuma 'yar tsaka tsaki a gefenta. Mai motar ne ya bawa matar hakuri, akan su zauna a baya, don za su kara fasinja. "Yaya Fawzaan, yanzu a ina za mu zauna? Dubesu fa, ai su kadai ma sun lotsa motar, ina za su kara daukar wasu kuma? Ni gaskiya ba zan shiga ba, ina tsoro, don ban taba shiga irin wannan motar ba." "Sai ki yi min gadin motata, dama aikin ki kenan". Ya fada yana mata murmushinsa na gefe. Bayan Fawzaan ya kulle motarsa ne, ta ga alamar baida niyyar mata tayin shiga motar, da gaske sai ya bar ta a jeji, ga kuma hadari da yake ta kururuwa alamar zai fashe ruwa ya sauko. Don haka ta yi shahada ta duru a bayan motar ita ma, inda mata biyun nan suka yi mata matsin tunkuza, rabin cinyarta kuwa yana kan daya 'yar madaidaiciyar matar. Domin kuwa direban ya-ce su zauna su biyu a gaba budan bakin Fawzaan ya-ce. "Malam, da ka hakura ta zauna a can, ka ga bai dace na zauna da wacce ba muharramata ba".6 "Oh, ai Yallabai, ca na ke ita matarka ce ai? Juyowa ya yi ya kalleta. "A'a tafiya ce ta hadamu kawai, mun kuma kusa rabuwa ma."4 Jin haka direba ya bawa sauran mutanen motar hakuri, sannan suka dauki hanya. Ga direban da dan karan surutu kamar Waziri Aku. Sai yi ya ke yi shi kadai, duk da Fawzaan ba kula shi yake ba, shi dai bai yi shiru ba sai zuba yake kamar ruwan sama. Mugu, dube shi ya bararraje a gaba har da hakimcewa ya bar mu a baya sai cin wuya muke yi, ga wani zafin tsiya da motar ta dauka. Tsaki ta yi a ranta, daidai lokacin Lukuta A. Ta juyo ta kalleta, ba shiri Rumaysah tai mata yake. Ba a dau lokaci ba Lukuta B ta zunguri kwankwasonta da Lukutayen cinyoyinta.8 Kuka ne kawai ba ta sa ba a motar. Tafiya kadan suka yi suka iso Kaduna, amma sai da Rumaysah ta ji tamkar wuni suka yi a motar. Suna isa wurin Service. Fawzaan ya yi waya ya fadi inda motarsu za ta tsaya, don haka sun samu dan Yaya Shatu. Yaya Isyaka yana jiransu a wurin. Da kyar Rumaysah ta sauka a motar, tsabagen ciwon jiki. Su Lukata A da B kuwa har da yi mata murmushi da daga mata hannu, su a dole sun yi kawa, ba su san kalar haushinsu da take ji ba, koda yake ga can ogan 'yan dura bakin-ciki can yana faman shirya wata muguntar. "Ke, bebin Abba, zo ki tafi gidan Goggo Shatu da Yaya Isyaka, ni zan bi direban nan mu koma na dauko mota." Wani dadi ta ji za ta rabu da rakai, murmushi ta yi ta karasa kusa da Yaya Isyaka, suka gaisa. Ko ta kalle shi, balle ya samu Allah ya kiyaye. Allah-Allah take yi ta wuce gida ko ta samu ruwan dumi, ta watsa ko za ta rabu da wannan ciwon jiki. Shi ma bai ko waigeta ba. Direba ya nemi Bakanike suka koma garin da motar ta tsaya. Kai tsaye Rumaysah da Yaya Isyaka, Unguwar Sarki suka wuce inda gidan Alhaji Aliyu, wato mijin Yaya Shatu, yake. Suna isa gidan Goggo Shatu, ta same su cikin farin-ciki da murnar isowarta, ga 'ya'yansu sa'anninta su Hajara suna nan. STORY CONTINUES BELOW Haba gida sai murna, nan suka shiga tambayarta Yaya Fawzaan, ce masu ta yi ya je dauko motarsa a bayan gari. Ai daki ta isar da jakarta kawai ta yi wanka, ta yi sallar azahar, sannan suka jero mata kayan abinci. Sai da ta yi dan barci ta fito falon, dai-dai lokacin shigowar Yaya Fawzaan kenan, wajen la'asar da alama shi ma sai da ya tsaya ya yi wankan a Side din su Yaya Isyaka, sannan ya shigo cikin gidan, don yanzu ba jamfar bace a jikinsa, ya sauya da kananan kaya. Wani kallo suka sakarwa juna, mai dan karen zafi tukun, suna zaune a falon Yaya Shatu da ya sha kyau kamar ba falon tsohuwa ba, 'yan kannenta sun gyara mata shi fes! Shigowarta ne ya dakatar da su, da Allah kadai ya san wacce fadar za a kwakulo. "A'a sannun ku da zuwa, yaya ku ka baro iyayen naku?" "Lafiya kalau Goggo, mun same ku kalau?" "Lafiyan mu. Alhamdulillah. Da fatan dai ku na lafiya, ba wata damuwa ko?" Fawzaan ne ya yi saurin amsawa da lafiya. Rumaysah kuwa ta dago da sauri ta dubi yadda yake sharta karya, bai ko jin kunya. Don yau ya sharta guda nawa, sai Allah. Hmm! Su Ustaaz manya. "Haba, Goggo kullum na fada miki ki rage shan raba da sanyin A.C, shi yake kashe maki kasusuwa, amma ke son dadi ya miki yawa." Goggo ta rike haba, tana ganin ikon Allah. "Fawzaan, ka yi wa matarka fada, wai ni an ce mata ni kakarta ce?" "Goggo jikokinki da suka girmeni guda nawa?" Rumaysah ta fada tana dariya. "Ungo naki, tashi ki bace min da gani. Haka ka ke fama da ita ne?" "Hmm! Ai Goggo ki bari dai ba a cewa komai, sai hamdala."4 "Wato ki na sa mijinki ciwon kai ko?" "Goggo shi ki tambaye shi ciwon meye baya sani, Goggo fa har yau ya kwashe kayan matarsa da yake so a gidan ya ki, ya zuba su a daki guda, sai dai na gani raina ya baci." Yaya Shatu ta dubi Fawzaan yana hararar Rumaysah. "Meye ka ke mata wani kallo, wato kar ta fada kenan ko? Me na ke ji wai kayan matarka, yaushe ka yi wani auren ba mu da labari?" "Goggo fa bai ma aureta ba, auren ta zai yi, wai don ita yake so, shi kenan har yai mata sayayya ya ajiye, da na yi magana, sai cewa ya yi wai ya ba ni kyauta." Yaya Shatu ta-ce. "Shi ne za ku ce min ku na zaune lafiya, haka ku ke zaman? Ka kwace daki guda ka ajiyewa budurwarka? To zan shiga hancinka da kudundune, tun wuri dama ka kwashe, idan ka ga dama ka kai mata gidan su, amma ai wannan cin fuska ne." Yana jinsu har suka gama sannan ya-ce. "Goggo Shatu, idan ki na biyewa Rumaysah ba tare da ita kanta ta san abu ba, wataran za ku yi gurguwar shari'a. Kayanta ne fa a dakin. Mama ce ta turo Muneera ta shirya mata su kafin tafiyata Gusau, don sai da ta rufe gidan ma, ta ba ni key, sannan washegari na tafi Gusau din." "Yo, ke kuma haka aka yi, shi ne ba za ki tsaya ki ji komai ba, kin sako kishi a gaba haka? Kai kuma ai ya dace ka yi mata bayanin komai". Rumaysah ta turo baki, tana jin Goggo Shatu, ji dai Goggo Shatu wani kishi kuma za ta yi akan Fawzaan? Idan ya ga dama gidan ma gaba daya ya dauka ya bawa budurwarsa, ita meye damuwarta. Ba su dade sosai ba a gidan, saboda gudun kar su yi dare, suka wuce gidan babban danta dake Malali. Can ma suka gaisa, sai wajen karfe biyar da rabi suka bar Kaduna, suka wuce Kano. Sai a mota ne ta-ce. "Daman ka san kayana ne, shi ne ka na ji na, ka yi shiru har da wani cewa ka ba ni kyauta." "Ke ba sarkin tsiwa da surutu ba, har da wani bude baki ki na kai karana. Ai na fada miki idan dai kin zabi zama a gidana, to sai ki dau hakuri, don haka kuwa ba kai kara. Idan na kuskura na ji kin kara fadar wani abu a wani wurin, sai na yi maganinki." Murguda bakinta ta yi, sannan ta kau da kai gefe. "Da zama a wannan gidan, gwamma zaman jeji, ba ci, ba sha, mutum ya koma kamar akuyar mayya."4 Yi ya yi kamar bai ji me ta-ce ba. Suna isa gidan Yaya Uwa suka fara isa, nan ya bar ta ya fita, domin yin sallah har sai bayan Issha ya dawo. Aka gaisa sosai, suka ci abinci, sai wajen karfe tara ya-ce wa yaya Uwa. "Mu za mu wuce. Insha-Allahu, da safe za mu tafi idan ba dai akwai wani abin ba, ina ga mun wuce kenan." "To ya yi kyau, mun kuma gode sosai, amma da na zaci za ka bar mana ita mu kwana a nan." "Wai, ai tun dazu Sajeeda, sai waya take min, ta kagara ta je, ina ga sai dai wani lokacin yau Sajeeda ta riga ku." "To, ina ruwan Sajeeda." Nan Yaya Uwa ta hada masu sha tara ta arziki, ta bawa yara suka kai masu mota, har kofar gida ta raka su. Suna tafiya, kasancewar Rumaysah ba ta taba zuwa gidan Sajeeda ba, ba ta san unguwar ba, sai dai inda suka yi Parking tabbas ba gida bane Hotel ne, don haka ta fahimci ba gidan Sajeeda suka zo ba. "Ba za ka bari sai ka ajiyeni ba, sannan ka dawo masauki, koda ma ba ka yi booking bane?" Wani kallo ya buga mata tukun. "Na ajiyeki a ina? Ai mun iso masaukin mu, ki fito kar ki manta jakarki a booth." "Ban gane mun iso ba? Yanzu ka cewa Goggo Uwa gidan Yaya Sajeeda za ka saukeni, wato karya kayi mata kenan. Meye manufarka na kawoni nan?"4 "Koma menene, ki shigo za ki gani ai."

Post a Comment for "AMAREN BANA CHAPTER 5"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...