Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YAR MAKIYAYA CHAPTER 8

YAR MAKIYAYA CHAPTER 8

- - Post a Comment
YAR MAKIYAYA

CHAPTER 8


Wait!! Na san tambayar dake zukatan ku readers! Kuma nasan kuna jiran jin amsa daga *Y'AR MAKIYAYA* Well! Lets hope it's a yay! Yanzu de Bari mu bi Suraj muji yadda zasu yi da dreamy girl d'in shi. +

****** ******* *******

Safiya ce mai d'auke da ni'ima,k'amshin sassanyar iska dake busawa kad'ai ya isa ya tabbatar da hakan. Bayan Suraj ya yi parking motar sa ya jingina jikin ta ,hannayen sa cikin aljihu ya d'aga kai yana kallon sararin samaniya, sink'in tunaninnika ne a ransa na yadda zai yi ya fara magana da Laila game da wannan al'amari ba but he has to try.
Mak'e kafad'a yayi sannan ya Fara tafiya a daidai wannan lokacin ya san babu inda zai same ta in ba bakin ruwa ba don haka ya garzaya don duba ta a chan.

Zaune ya hango ta a bakin ruwan tana kallon yadda yake gudana babu sautin komai wajen se na tsuntsaye da kuma gudanar ruwa , da Sallamar sa ya zauna gefen sa yayinda ta amsa tana masa murmushi, sun kai minti biyar suna zaune sun k'ura wa ruwan ido babu wanda ya ce komai a cikin su. Suraj ya nisa ya juyo yana kallon ta ita ma hakan tayi ta k'ura masa ido.

"Bakin ka da magana! Ka fad'a mana, yau naga kamar kana cikin damuwa."

Zaro ido Suraj yayi yace "wa ya fad'a miki cewa ina da matsala?" Murmushi Laila tayi tace "ai naji kad'o sun ce wai labarin zuciya a tambayi fuska." Murmushi Suraj yayi gami da jinjina kai yace "hakane".

"Laila yanzu ki K'addara ace ni ne bani da lafiya ,kuma ke kad'ai ce zaki iya samo min maganin ciwo na ,shin zaki nema min magani ko kuwa.?"

Daidai lokacin Habeeb da Junaid suka k'araso ba tare da sun yi magana ba suka tsaya don suji amsar tambayar Suraj

Murmushi Laila tayi tace "Tabbas Zan samo maka magani duk rintsi in dai zaka samu lafiya"
Kai Suraj ya girgiza yace

"Laila! Ko da hakan yana nufin zaki tafi waje mail nisa? Zaki yi kamar wata da watanni kiyi nesa da Baba da komai na gida? Zaki iya yin wannan don ki sama min lafiya?"

Shiru Laila tayi na y'an dak'ik'ai kafin ta dube shit tace "tabbas kazo min da wata iriyar zolaya, in Allah ya yadda ma hakan bazata faru ba dan Allah ka daina d'aura wa kanka cuta irin haka"

Mik'e wa Suraj yayi ya cusa hannun sa cikin aljihu ya kalli Laila yace "ba zolaya bane Laila kinji kinji abunda muka yi da Dad (nan ya labarta Mata duk abundaya faru tsakanin sa da iyayen sa )

Ja da baya Laila tayi tace "Kayi hak'uri Suraj, da na d'auka zolaya ce kawai,amma yanzu da na riga na gano cewa da task kake ina so ka sani Suraj
Belel shi ne komai nawa nan na taso kuma ban tab'a yin nesa ba. Suraj zan iya yin komai domin naga soyayyar mu ta taka rawar gani amma in har magana ta zo da cewa se na bar Baba , da komai a baya Toh Lallai da kamar wuya, in baka manta ba na tab'a fad'a maka cewa bayan na rasa Inna zuciya ta duk ta tarwatse, amma saboda Baba kad'ai na tarkata wanda ya rage don in bashi dukkanin kulawa ta , bashi da kowa se ni dan haka Suraj Zan baka hak'uri bazan iya yin wannan shawarar taka ba Wannan mafitar ba mai bille wa bace ,Suraj ina fatan zaka fahimce ni kuma ka sani ina matuk'ar k'aunar ka Suraj".

  Kafin ta kammala maganar ta tuni fuskar Suraj babu masakar tsinke saboda zufa da hawaye duk sun mamaye ta ,Kai ya jinjina ya dubi Laila dake kuka wurjanjan  yace 
"Na fahimta! I understand, kiyi hak'uri na kasance mai son zuciya ta, kafin na iske ki da Wannan maganar ya kamata nayi tunanin halin da zan jefa ki ciki in har kika yi nesa da Baba, kiyi hak'uri na manta cewa mahaifin ki ya kasance mutum Mafi soyuwa a tare da ke unlike mine,da badan nawa uban ba da kuma dabi'ar shit na k'in talaka da kuma halin ko in kula da duk haka baza ta faru ba, amma ina so kar abunda ya faru yasa Ki d'auke ni a matsayin makaryaci nayi k'arya ne don in samu mafita saboda bana son na auri wata ba ke ba. Nagode da kika fad'a min abin da ke cikin zuciyar ki Laila."

Yana kai wa nan a jawabin sa  Suraj ya juya zai tafi karaf idanuwan sa suka sauk'a kan Habeeb da Junaid wanda a halin yanzu duk jikin su ya gama sanyi , Suraj bai ce k'ala ba illah wuce wa da yayi ya bar su a tsaye Laila ta bi shi da kallo har ya b'ace sannan ta maida duban ta ga su Habeeb da Junaid dake tsaye har lokacin. 

K'arasa wa Habeeb yayi kusa da ita yace "Ina so duk abunda zai je ya zo ,bisani cewa kafin kiyi tunanin makomar da Baba zai shiga in bakya nan Suraj ya riga ki yin ta, dan Allah kada ki d'auke shi a matsayin mai son Kai ,Suraj yana k'aunar ki, kuma zai kasance mai k'aunar ki na har abada.
Juyawa Habeeb yayi ya bar  wajen zuwa inda ya bar motar sa duk gwiwar sa a sake babu kuzari tare da shit.

Ba Shiri Laila ta zube k'asa kan gwiwa tana kuka mai tsananin ban tausayi hannuwan ta tasa a k'asa se fiffisge ciyawi take ,tsabar kuka kuwa har sautin su yana fita ,Junaid ya kasa ko da matsa wa, yana so ya lallab'e ta amma a wannan yanayin bazai iya hana ta kuka ba, dan haka ya zauna inda yake shima zuciyar shi fal k'una.

Duk abunda ya faru ashe a kan idon baba ya faru, kamar yadda Laila take kuka haka shima kukan yake yi wurjanjan kamar k'aramin yaro , da kyar ya juya ya bar gurin saboda ya kasa bawa kansa ma hakurin kuka bare ya lallashi y'ar sa Laila...........Ya dad'e zaune cikin mota ya kwantar da kai a sitiyarin motar yana hawaye wayar sa ta d'au ruri , Kusan Sau biyar ana k'iran sa bai kula wayar ba se a Karo na shida tukunna ya d'aga ya kara a kunne bai ce komai ba Kusan minti uku sai lokacin yace "yes, thank you sire " sannan ya ajiye wayar. Tsabar kukan da yayi idanuwan shi da kyar suke bud'e wa ga ciwon Kai kuma bai fasa driving ba duk da motar tana kwace masa da kyar ya isa gida, Habeeb yana ganin yadda motar Suraj tayi ta walagigi a hanya duk tsoro ya mamaye shi amma da yaga har ya shiga gida yayi parking hakan yasa hankalin shi ya kwanta shima ya kai motar wajen parking ya ajiye ta sannan ya nufi falo. +

Suraj kuwa da ya shigo falon bai kula kowa dake wajen ba ya mik'e zuwa sashen su, Mom dake zaune taga tashin hankali k'arara a fuskar Suraj don haka ta mik'e tsaye sai kuma taga Habeeb ya shigo da sauri

"Habeeb what exactly happened? Laila bata amince bane?" Kai Habeeb ya gyada sannan yace "yes Mom, and .......... Mom Laila did not agree" nan Habeeb ya kwashe labarin komai ya fad'a mata ,mom ta d'an share guntun hawayen ta tace

"Suraj was right, we shouldn't be selfish, da munyi tunanin hakan da baza mu kawo solution din
d'in ba, mahaifin ta shine komai nata a rayuwa rabuwa da shi zai zame mata wani abu ne mai matuk'ar wuya....

K'ofar falon su ya tura zai shigo, d'aga kai da zai yi ya hango mutum zaune wutar falon ya kunna full sannan ya juya da kyar ya bud'e idanuwan sa don yaga wane ne.

"Ameer!!?* what the hell are you doing here!!?",Cewar Suraj wanda yayi mamakin ganin Ameer d'in a falon All alone, ya kuma san ruwa baya tsami banza, ganin Ameer kad'ai ma ya sake chusa wa Suraj wani sabon bakin cikin.

"Relax Bro ! Am not here to fight you am here to........"
Bai k'arasa ba Suraj ya Fara magana in his stylish serious tone yace

"Look man, I don't bloody care what ever you here for, I just need you to get out of here ASAP!" Mik'e wa Ameer yayi ya zira hannayen shi a aljihu gami da Mak'e kafad'a yace "sorry man! Zan fita but like I said earlier I came in peace na kawo maka birthday invitation ne as a brother ya kamata ka zo" Ameer ya mik'a wa Suraj k'aramin card amma Suraj ko kallon wajen bai yi ba dan haka ya chusa masa card d'in a aljihun rigar shi abunda ya k'ara hassala Suraj kenan ba shiri ya dunkule hannu ya kai ma Ameer naushi wanda yasa Ameer kwanciya sannan ya fitar da card d'in ya keta shi gida biyu ya watsa wa Ameer a fuska.

Ameer ya mik'e rai a b'ace yana huci Amma Suraj bai bashi chance na magana ba illa hankad'e shit da yayi cikin tsawa wanda har muryar shi na sark'e wa yace

"Ameer am tired of your creepy attitude! Just get out of my house and my life as well! And you know what? To hell with your bloody birthday!!! Wai ma yaushe na zama mutum da har zaka tuna ni ka yi inviting d'ina I know you Ameer komai kana yi ne da wata manufa Wannan Karon you won't get me "
Hankad'a shi yayi hanyar k'ofa yace "zai fi maka ka fita tun da sauran hankali a jiki na don in na Saki demon d'in dake jiki na bazaka fita daga d'akin nan da k'afar ka ba".

Ameer ya d'ago kai da muguwar Murmushi idanuwan sa duk sun yi jajir yace "haha! Try that sai na sauya maka kamanni Suraj ko da yake ma me ya rage maka? You have no one who trust you except that bloody woman you called your Mother !,kasan me? I hate her as much as I hate you kuma tunda kayi min wannan nasha alwashi se na zame maka karfen k'afa Suraj just watch me!.

Cikin zafin nama Suraj ya zari size stool ya wurga wa Ameer ya same shi a k'afa sannan ya fara kai wa Ameer d'in duka har suka fita daga d'akin through the hallway Suraj bai fasa dukan Ameer ba Ameer kuwa bai fasa zagin Mom ba don yaga hakan ne yake k'ara ingiza wutar k'iyayyar dake zuciyar Suraj.

Mom da Habeeb basu ankara ba suka ga an Hankad'a mutum daga staircase ,ganin Ameer ne sannan Suraj ya k'ara dumfaro inda take hakan yasa Habeeb yayi saurin rik'e Suraj wanda ke k'ok'arin kufce wa daga rik'on da Habeeb yayi masa Mom ta rik'e Ameer sannan tayi magana da wata hadima kan ta kawo first aid kit amma kafin ta kawo Suraj ya kwace daga hannun Habeeb ya chafko Wuyan rigar Ameer ya ja shi har k'ofar fita ya Hankad'a shi.

Cikin tashin hankali mom ta sharara wa Suraj mari har biyu wanda ya sa saida Suraj ya daina ji na minti biyu

"Baka da hankali ne? What if you kill him! Ba fa shi ya janyo ka rasa Laila ba ka dawo Hankalin ka mana!."

Suraj ya Fara ja da baya even more crazier than before yace "Yau a Karo na farko nayi loosing, tun ina k'aramin yaro nayi alk'awari cewa bazan tab'a b'ata miki rai da har zai jawo ki d'aga hannu ki mare ni ba,gashi a dalilin wannan Mara mutuncin wanda tun daga sashe na babu kyakkyawan kalma guda d'aya da ya fad'a a kanki, ni kuma baki haifen dan kawai in tsaya sauraron wani jaki yana zagin ki ba batare da na d'auki mataki ba yayi kad'an"!!!.

Yana kai nan ya juya ya koma d'aki direct bayi ya shiga ko kayan jikin sa bai cire ba ya sakar wa kan sa shower ya kifa kai jikin glass d'in.

Ta dad'e tsaye tana k'are wa hannun ta kallo yayin da Habeeb ke zaune kan kujera ya kife fuskar sa cikin tafukan hannun sa. Kamar daga sama suka jiyo muryar Dad d'aga k'ofar shiga falon

"You did the right thing!, Mari kad'ai ma bai isa ba you should have beaten the hell out of him! ". daga bayan Dad suka hango Ameer kina kina dan munafurci har wani nishin k'arya yake ,Dad ya nuna Ameer da hannu yace "dubi abunda d'an ki ya aikata! Tunda nake iya rayuwa ta ban tab'a cin Karo da mara imani ba se yau and you know what? Your son must pay for what he did"

Fuska tag da hawaye Mom tace "I knew it! Ko da yaushe maganar bakin ka kwaya d'aya ce tak and! D'ana d'ana d'ana! Kuma waye uban shi ? Kar tsanar da kayi masa yasa kayi talking kan ka out of this issue, the Suraj i knew back then won't even harm a lizard wannan Suraj d'in wanda ka had'a ne , you made this,Suraj kuma Kai kayi unleashing demon d'in dake cikin sa , duk abunda yayi ba daidai bane a wajen ka ,bai tab'a burge ka ba sannan you hate him! Amma ka sani the biggest monster is you! Yes Abdul-malik for once baka tab'a yabon shi ba , kaje kayi tunani tsakanin Kai da shi waye take kan gaskiya? Shi da yace duk wani mai kud'i ko mulki must make sure that talakawa are his number one priority ko kuma kai da kace tsakanin ka da talaka babu komai se kyara da kyama? I am more than proud of him! Ina matuk'ar alfahari da shit coz ya tabbatar min da cewa shit d'an halal ne domin babu d'an da zai tsaya ana zagin Uwar sa mahaifiya bai d'auki mataki ba,gashi a rashin fahimta yau na farko na d'aga hannu na Marie Suraj bayan shekaru d'ai d'ai har ashirin da uku!" 
Mom tana kai nan ta juya ta nufi staircase zuwa sashen ta.....Mom ta nufi gidan su Laila, Suraj kuwa bamu da masaniya akan inda ya shiga , Laila ta amince zata je garin KD dan haka Bari mu Fara daga kan Mom muji dalilin ta na zuwa gidan su Laila
*******       ******    **,***** +

   A k'ofar gidan Habeeb ya ajiye mota sannan yayi sallama, baba ya fito ganin harda Mace suka zo yasa Baba ya musu iso cikin karramawar gaske. Bayan y'an gaishe gaishe Mom ta gabatar da kanta a matsayin mahaifiyar Suraj kafin taci gaba da cewa

"Na sani cewa bai kamata ace nice a nan a wannan lokacin ba Amma babu yadda Zan yi ne, na zo in tabbatar maka cewa kamar yanda Laila take y'a a wajen ka nima haka nake uwa a gareta, alk'awari na d'auka cewa iya rayuwa ta Zan bata kariya ,so da kuma k'auna da tarbiyya tamkar y'a bugu da Kari bi iznillahi bazan bar wani ko wata su cutar da ita ba kuma tafiyar nan ba ita kad'ai Zan d'auka ba saboda in har da wani na kusa da ita hakan zai rage zargi domin nayi tunani bai kamata ba mu d'auki yarinya budurwa muyi nesa da ita daga gida , in wasu sun fahimta wasu bazasu fahimta ba , saboda haka ne Nazo domin ina so kayi magana da Junaidu in ba matsala ya taho da mu"

  Murmushi Baba yayi kafin yace " kafin yanzu ban tab'a ganin mutum mai arzik'i wanda ya damu ya killace mutuncin d'an talaka ba sai ke, ba kamar sauran samarin da suka fito daga wancan gidan Sarautar ba, d'an ki Suraj na daban ne, yanda yayi zamantakewa da mu da kuma karamcin sa da rashin kyamar mu talakawa sune abubuwa na farko da suka sa shi  ya kwanta a raina, kuma na yarda da shi wannan yasa ban nuna damuwa ba ganin shi tare da Laila ,Suraj na daban ne, kuma Junaidu da kike magana a kansa ni d'an uwan mahaifin sa ne babu abunda Zan sa shi ya tsallake , duk lokacin da kuka shirya tafiya Junaidu zai zama a shirye nidai fata na ku rik'e amana , Laila Marainiya ce " Murmushi Mom tayi tace " Ni kaina nasan ciwon maraici don na dandana shi tun bansan me duniya ke ciki ba saboda haka ka kwantar da hankalin ka in dai wannan ne, ni yanzu Zan koma se Mun shirya tafiya zamu zo d'aukar su Mun gode da karramawar ka Kwarai kuma Allah ya bar zumunci and. Shima Baba godiya yayi musu ya nad'e tabarmar bayan sun fita. Kai tsaye gidan su Junaid ya nufa aka yi sa'a ya iske mahaifin Junaidu a gida, bayan sun gaisa ya kwashe labarin komai ya labarta masa , shiru baban Junaidu yayi na wasu lokuta kafin ya d'ago ya dubi Baba yace

"Har yanzu na rasa gane dalilin da yasa ka kwallafa rai kan wannan yarinyar *MARA ASALI* kar ka yi k'ok'arin saka d'a na Junaidu a wannan Al'amarin se me in wani abu ya cutar da ita ? *jinin ka ce da zaka damu har se wani ya tafi tare da ita su je su kashe ta ma in sunga dama* mik'e wa Baba yayi rai a b'ace yace

"Duk duniya banda Kai kad'ai se Innar Laila marigayiya suka san Laila ba y'ar mu bace amma wannan bai zama dalilin da zai sa ka yi burus da al'amarin ta ba domin tun tana *y'ar jaririya* muke tare da ita har na mutt Laila a matsayin y'a take waje na ,kuma ban yafe ba duk wanda ya sake d'ago wannan maganar. Kawai ka ce Junaidu babu inda zashi amma ba ka fake da guzuma ba sannan ka harbi karsana." Baba yana Kai nan ya fice rai a b'ace.

  Duk abunda ya faru a kunnen Junaidu don yana bayan d'aki , sosai ya dinga kuka don ya girgiza da jin cewa Laila ba jinin sa bace kuma a wani b'angare bai ji dad'in abunda baban shi yayi ba dan haka ya fito ya samu baban cikin ladabi ya dinga Rok'on sa yana bashi hak'uri da kyar ya amince Junaidu ya tafi.

Washegari

    "Razia I know it's all my fault amma Suraj bazai tafi babu dalili ba watak'il aiki ne ya taso cikin gaggawa" Murmushi Mom tayi tace " Oh! Aiki mai gaggawa, no wonder Abdul-malik shiyasa ko sallama ma bai yi ba ko? Ya kuma kashe wayoyin sa ba tare da kowa yasan inda zashi ba, come on grow up! Abdul-malik! Ni yanzu Zan je Kaduna domin shirye shiryen bikin Sapna (K'anwar Habeeb) kuma I believe kana sane da tafiyar tawa" kai Dad ya jinjina yace "eh ina sane amma nayi zaton se next week ne zaki tafi" Kai ta girgiza tace

"Eh haka ne Toh se aka samu sauyin al'amura shiyasa Zan tafi yau d'in nan besides tafiyar da nisa" Murmushi Dad yayi ya kurb'i ruwa kafin ya ce "Shikenan Allah ya kaiku lafiya ,nima Zan tafi Egypt next week in shaa Allah. Kai mom ta jinjina tace Allah ya kaika lafiya" tana kai nan ta mik'e ta zari handbag d'in ta sannan ta nufi k'ofa

  "Razia! Wai har yanzu kina fishi ne? I taught Mun gama magana sannan nayi apologizing amma kamar baki huce ba."
Chak Mom ta tsaya ta d'an juyo ta kafad'a tace

"No not at all sweetheart ina sauri ne kawai zan shiga nayi sallama da matan gidan " da kasaitaccen murmushi ta fad'i hakan amma ai ance Labarin zuciya a tambayi fuska Dad yana same Razia da sauran b'acin ran shi a zuciyar ta sedai kawai tana iya k'ok'arin ta don ganin ta danne zuciyar ta. .Murmushi shima yayi ita kuwa ta fice zuwa cikin gida.

Cikin awa biyu Mom ta kammala duk wasu shirye shiryen ta suka kama hanya motocin escort d'aya gaba d'aya a baya , sun bi gidan su Laila suka d'auke ta da Junaid sannan suka d'auki hanya, "and that was the beginning of the journey!"

Post a Comment for "YAR MAKIYAYA CHAPTER 8"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...