Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YAR MAKIYAYA CHAPTER 4

YAR MAKIYAYA CHAPTER 4

- - Post a Comment
YAR MAKIYAYA
CHAPTER 4


K'arisa wa tayi har inda suke ta nemi waje ta zauna kafin ta dubi Suraj tace
"Kullum nakan yi mamakin dalilin da yasa kai bana ganin ka cikin y'an uwan ka , amma bayan abun da naga sun aikata maka d'azu ina tsaye daga sashen da nake se naji ba abun mamaki bane don ni kaina ban san halin wa Saeed da Ameer suka yo ba a bak'in hali, ina so kayi hak'uri My son kada ka biye musu zan yi magana da mahaifin su amma please kar na sake jin batun wai zaka koma Cairo, a lokacin da mahaifiyar ka ke fuskantar takura da tsanani bata gudu ba wa matsalolin ta ,zama tayi ta fuskance su like a lioness I want you to do the same, rise above all odds in kana son abu go for it ,in baka so babu dole yi watsi da shi like a man bana son in k'ara jin kalma irin ta karaya daga bakin d'an Auta na, live your life the way you think is right after all rayuwar ka ce hmm?". +

Ta kasance uwa mai dad'ad'an kalamai wanda tuni sukayi tasiri a zuciyar Suraj , nan take yaji a ranshi cewa koma me zai je ya zo, zai yi rayuwar shi yadda ya tsara kuma bazai sake barin wani obstacle ya tare mishi hanya ba komai wuya. Dan haka yayi Murmushi ya dubi Mom yana shafa ciki. Ko ba komai ta san me yake nufi dan haka ta umarci Hadimai da su shirya masa abinci wanda yin hakan bai wani d'au lokaci ba, Razia da Aunty Maryama sun dad'e suna hira Suraj kuwa tun da ya idar sallar isha ya kwanta.

***** ***** *****

Tun shida na safe Laila ta kad'a kan dabbobin ta zuwa saman tsauni inda suka saba kiwo gudun kada Yariman Belel ya zo ya iske ta ,a takaice de tabi shawarar Zubaina.

8:30am.
Kamar an tsikare shi ya mik'e daga kan gado duk da idanuwan shi da nauyi haka ya k'ok'arta ya fad'a bayi ya watsa ruwa, fitowar sa ke da wuya ya hangi mug of hot tea ajiye, Murmushi yayi kawai ya zauna bakin gado, cike da kula ya sha Shayin sannan ya mik'e ya kammala shirin sa.
D'akin Mom ya nufa yayi sallama ta amsa ,bayan sun gaisa ya sanar da ita zai fita "Zaka je ka Faso d'ayan b'arin goshin ko?
Suraj da dariya ta kufce masa yace "no way Mom sai na dawo". Ya fice yana dariya.

Bak'ar mota ta hango tsaye yana fuskantar ta , a zaton ta Suraj ne tace "wato Wannan saida ya gano inda nake ko?" Gadan gadan ta nufo motar a fusace har da rik'e k'ugun ta , saida ta iso daf da motar se tayi turus jikin ta yayi sanyi ta juya zata koma amma ta kasa ko da d'aga k'afa dalilin chafko ta da akayi, ba shiri ta sa ihu aka rufe bakin ta , bata sake yunk'urin motsa wa ba sai da suka yi ido da wanda ya chafke ta , tsananin tsoro ta tsorita da ganin shi. Cikin muryar maye ya ce

"Kkkeee!! Rufa man baki *Y'AR MAKIYAYA*! Ba kowa a nan se in yi yadda naga dama da ke don haka ki nutsu! Kawai de kin min baby! In kina son zama lafiya Toh kkkkiii!! So ni kawai baby!

Cike da firgici ta Hankad'a shi gefe guda ta ranci na kare yayinda yake tsaye yana kyalkyala dariya.

Tun daga nesa Suraj ya hango ta da gudu tana dumfaro hanyar da yake, duk da bai san dalilin gudun ba ya ga firgici tare da ita , tana iso wajen da yake yayi k'ok'arin tsai da ita amma suna yin ido hud'u ta sake sauya hanya da gudu , ganin haka Suraj yabi bayan ta da gudu Hegiya Laila kamar ana k'ara mata mai dan gudu

"Oooooh! Come on!! I am not going to hurt you Miss Runner , ki tsaya dan Allah" Cewar Suraj dake ta faman zabga gudu. Ganin ta tsere masa ya kasa cimmata hakan yasa ya zube a k'asa yana ta haki har Wuyan shi ya bushe . dariyar Junaidu ce tasa ya bar kallon yadda taci gaba da gudu ya juyo yana kallon Junaid dake k'ok'arin zama kusa da shi yace

"Wow! That was amazing. wannan gudun da K'anwar ka tayi ya tabbatar min cewa ita babba ce a harkar guduwa, yo ai ko shirwa mai tashi sama bata nuna wa wannan Lailar iya gudu ba, amma zan baka shawara akwai gasar tsere na Marathon ina kyautata zaton in Laila ta shiga tabbas zata zamo zakara ta duniya baki d'aya".

Junaid ya tab'e baki yace "miye kuma Maratos?" Wage baki Suraj yayi na y'an dak'ik'ai kafin ya d'aga gira d'aya yace " Kasan me? Kawai ka mance Maratos or what ever just forget it nidai ka fad'a min ya akayi ta iya falfala gudu haka ita ba sak'ago ba?"
Junaid ya kwashe da dariya yace "Baiwa! Kyautar Ubangiji!!" Kad'a kai Suraj yayi yace "tabbas! Se fa hakan! Yanzu Idan tana gudu na ta Yaya zan samu na fuskance ta muyi magana? Ni ka fad'a min inda zan same ta yau bazan koma ba har sai na bayyana mata sirrin dake raina".

Junaidu yace "da Wannan gudun nata ai da alama kad'an ya rage ta bar Belel," Suraj ya bugi kafad'ar shi yace "kai dallah bana son tsiya nidai ka fad'a min inda zan gan ta." Junaid ya kama hannun Suraj suka nufi inda tayi.

Chan a gida kuwa Dad ya shirya tsaf zai fita ko kallon Mom bai yi ba ya ja hannun Ameer suka fice

"Ina so ka sa min ido wa duk wani motsin Suraj , let me know what exactly he's up to". Ameer yayi Murmushi ya girgiza kai as if Mutumin kirki ne ,suka yi sallama da Dad driver ya ja motar suka tafi.

  Murza hannayen sa biyu Ameer yayi yace "Perfect! Sounds like an bawa kura ajiyar nama" yana kai nan ya koma cikin gida yana Murmushi.

   Suna tafe suna hira mai ban dariya Suraj na Jan Junaid wai su yi sauri kamar daga an jefo shi ya hangi Dad tsaye jikin mota yana kallon shi ,wannan karon Suraj kawar da kanshi yayi ya cigaba da tafiya abunsa kamar ma bai ganshi ba at that point Dad bazai iya bayyana takaicin da yake ji ba haka ya koma mota driver ya cigaba da tuk'i..

Ta dad'e zaune jikin wata bishiya ido a lumshe tana maida nufarfashi, mayafin kanta ma yana gefe guda duk tayi gumi. A hankali Suraj ya k'arasa daf da ita sannan ya kurma ihu ,hakan ya mugun razana ta ,mik'e wa tayi zata ranci na k'are Suraj ya chafke rigar ta hakan yasa ta tsaya chak don tasan in tayi k'ok'arin guduwa tsumman rigar yagewa zata yi dan daman ta sha ruwa.

"Har tsawon wane lokaci ne zaki cigaba da gudu Lady runner?" Ya tambaya in a serious tone.
Baki na rawa tace "Nidai ka sake ni bazan gudu ba wlhy kayi hak'uri ".
D'aga gira Suraj yayi  yace 
"Wato kin d'auka bayan kin buga min sanda kenan kin bugi banza ko?
Zaro idanuwa tayi waje ta fara hawaye "kayi hak'uri kada ka buge ni kaga ni kad'ai nake wa baba abinci, babu mai taya shi kiwo kuma , in ka buge ni da wannan k'arfin naka kawai mutuwa zan yi"

  Junaid yana gefe banda dariya ba abunda yake yi ita kuwa tsakani da Allah take bashi hak'uri ganin ta wahala sosai Suraj ya sake rigar ta ya yi mata nuni da k'asa yace "zauna!".
Ba shiri ta zauna ta takure waje guda tana kallon shi , durk'usa wa yayi yana kallon ta fuska duk hawaye yace " miye kuma na kukan yanzu? Ai nace ba bugun ki zan ba". Kai ta d'ago ta ce 
"Toh me zaka min?" 
Ya mik'a mata handkerchief yace " ungo ki share hawayen ki tukunna. A tsorace ta karb'a ta goge fuskar ta sannan ta d'ago ta kalle shi tana jira yayi mata magana.

   "Zab'i biyu zan baki ,na farko sakayyar bugu na da kikayi a goshi ina son ki bani wani abu in ba haka ba sai mu koma zab'i na biyu wanda shine in rama dukan da kikayi min"

  Daga zaunen da take tace "Ka fad'i me zan baka kwan zabi, saniya ,tunkiya ko rago babu wanda bazan baka ba amma Nide dan Allah kar ka buge ni nafi son zab'in farko"

Murmushi yayi gami da matsowa daf da fuskar ta yace "bana buk'atar k'ananan kadarar ki Laila, guda d'aya tak nake so kuma kullum yana tare da ke"

Tab'e baki tayi tace "nidai kam ban gane ba,sedai ka fad'a".

Murmushi yayi yace *Zuciyar ki nake buk'ata Laila, ki mallaka min ita ina matuk'ar k'aunar ki, babu amfanin in tsaya bayyana miki son da nake miki zai fi kyau ki ganshi a aikace so nake iya rayuwa ta mu kasance tare da......"
  Bai k'arisa maganar ba Laila ta sa gudu saida tayi nisa ta juyo tana kyalkyala dariya ,shi kanshi dariyar yake yi don bai san ya akayi ya furta kalaman ba , bai san ta inda suka fito ba. Junaid ya nufo shi yana Murmushi yace 
"Amma de wannan shine karo na farko da wani ya furta kalaman so? " kafad'ar shi Suraj ya buge yace "dallah yi min shiru bana son tsiya"

     Nan suka kama hanyar komawa gida....Junaid  ya kasance bai tab'a yin aboki kuma Aminin gaske kamar Suraj ba, da kyar yake bari su rabu domin Suraj ya kasance mai arziki na farko da yake bai tab'a nuna kyamar su ba sam baya fargaba soyayyar su da Laila sedai hankalin shi bai kwanta ba Kasantuwar daga irin ahalin da ya fito , b'angaren Suraj kuwa ji yake he's unstoppable! Koma me zai je ya komo babu fargaba a tare da shi indai a kan Laila ne he's ready to do the unimaginable. +

   Daga b'angaren Ameer kuwa ya koma tamkar paparazzi yayinda Suraj ya zama celebrity don duk inda Suraj yaje ko motsin da yayi duk a kan idon Ameer ne kuma ba Wannan kad'ai ba Ameer ya kware wajen aika sak'onni na photuna through multimedia messages ga Dad wanda hakan yake k'ara ingiza wutar k'iyayyar da ke balbala a zuciyar Dad ji yake kamar ya dawo komai ma zai faru kawai ya faru.
A yayinda Ameer ke jin dad'in buga wasan shi da Suraj akwai wani daban wanda yake neman gata Laila tamkar kwallon hockey.

      Yau sati guda da Dad ya bar gida a b'angaren Suraj is like Paradise Dad kuwa ji yake ya d'auki shekaru bai dawo ba.

Tun da ya idar da sallar Asubah bai  runtsa ba, downstairs ya sauk'a bai zame ko ina ba sai kitchen, banana fritters ya soya gami da had'a mug na peppermint tea ya d'aura kan tray yayi setting sannan ya hanzarta ya koma d'aki, wanka ya shiga direct yana fito wa bayan ya gama shafa ya d'auko plane white v-neck shirt ya zira had'e da blue jeans ya d'aura dark blue jacket by Armani ya zira ya feshe jikin shi da turare mai dad'in k'amshi  . wayar sa kawai ya d'auka ya sauk'a downstairs, ya d'auki tray d'in ya nufi sashen Mom, duk inda ya gifta se gaisuwa daga ma'aikatan gidan wanda sabon abu ne a wajen su yarima guda a kitchen.

  Kwance ya iske ta tana barci bata ma san me duniya ke ciki ba , Murmushi yayi ya ajiye tray d'in ya k'arisa bakin gadon ya zauna. Jin motsi yasa Mom ta bud'e ido, suna had'a ido ta yi Murmushi sannan ta jingina bayan ta da gado tace

"Hmm! Seems like yau wani special occasion ake yi , looking handsome and smart my Prince" kai ya yi bowing yace "thank you your Majesty! na had'a miki favourite naki ni zan fita ki cinye duk fa!"

K'urban tea d'in Mom tayi sannan tayi Murmushi tace "thank you it's yummy! In ka je ka gaida ta".

Suraj's POV

    Like seriously? Mom har ta gano cewa am going to meet a girl?
Ko da yake ban yi mamaki ba saboda Mom ne, tafi kowa sanin take take na da halaye na dan haka na dawo na zauna kusa da ita nace

"Mom, Yaya akayi kika san yarinya zan gani?" Amsar ta guda da na saba ji shi ta bani 
"Mother knows best"
Murmushi kawai nayi sannan na mata sallama na fice ban zame ko ina ba se sashen mai martaba..
Bayan sun gaisa da Sarki Suraj yana tsaye daga saman balcony duk wani shige da fice yana iya gani daga wajen. Ameer na zaune daga k'asa kan kujera yana kallon Suraj. Sun dad'e suna kallon juna kafin Suraj ya juya ya fice daga sashen Sarki. Motar sa ya shiga cike da zafin nama ya fice. Inda ya saba ajiye ta a nan yayi parking, ya kutsa cikin ciyawi masu kyaun gani zuwa hanyar da ya saba bi.

    Sanyin da ake yi yasa mutum baya ganin abun dake gaban sa tsananin hazo da ya rufe ko ina,  tafiya take saboda Idan da sabo ta saba. Sunkuya wa tayi zata gyara takalmin k'afar ta bata ankara ba taji an chafke gashin kanta wanda hakan yasa ta saki k'ara har sai da wajen duk ya d'auki muryar ta Sanyin da ake yi yasa mutum baya iya ganin abun da ke gaban sa sosai saboda tsananin hazo da ya rufe ko ina. Tafiya take saboda in da sabo ta saba fita kiwon ta indai ba ruwa ake ba. Sunkuya wa tayi zata gyara takalmin k'afar ta ,bata ankara ba taji an chafko gashin kanta wanda hakan yasata saki k'ara har saida wajen duk ya d'auki muryar ta +

  "Don Allah ka rabu da ni kada ka cutar da ni, sam ni ba irin matan da kake nema bana ka bar ni na tafi kiwo na" kokawa sosai suka dinga yi Laila na ihu basu ankara ba taji an fisge ta da k'arfin tsiya ta fad'i gefe guda tana kuka. Mayafin ta Suraj ya mik'a mata ba shiri ta amsa tana share hawaye.

   "Waye kai? In son ta kake ka fito kamar namiji ba rago ba, banza fasik'i" Cewar Suraj wanda ya riga ya cire jacket d'in jikin sa ya jefar k'asa, da sauri Laila ta d'aga jacket d'in tana karkade masa. Har lokacin Mutumin bai juyo ba dan haka Suraj ya kai hannu kafad'ar shi sa zummar juyo da shi amma sai Mutumin ya kawo wa Suraj duka amma saboda babu wani k'arfi a tattare da shi sai ya zame..

  "SAEED? daman kai ne , so it's been you trying to molest this lone girl a wannan dajin? Kasan kuwa abun da kake son aikata wa daidai yake da tarnishing image d'in Wannan Masarautar? Meye ya shige ka haka? Shaye Shaye daman kake yi?  
I should have known! Tun farko daman bakai kama da Mutumin kirki ba"
Saeed na jin kalaman da Suraj ke furta wa a kan shi dan haka ya kama shi da fad'a yayi ta kai wa Suraj naushi ,ganin bashi da niyyar daina wa Suraj ya fara maida martani har saida ya fitar masa jini da mijina, Ameer dake lab'e yana kallon abun da ke wakana ya taho da gudu dan tsoron kada suyi wa kansu illa musamman Saeed da ba k'arfin kirki a jikin shi duk giya ta kashe masa jiki.

  Laila ma ganin yadda suke fad'an yasa ta ruga ta k'ira Junaid sannan ta lab'e daga chan baya tana kallon yadda Ameer ke fisgar Saeed sannan Junaid ke janye Suraj. Da kyar Ameer ya ja Saeed zuwa mota har ya shiga ya fito cikin muryar maye yace 
"She belongs to me! She's all mine"
Suraj ya gyara rigar sa gami da goge jinin da ke bakin shi kafin yayi Murmushi yace "We shall see!".

  Ameer ne ya ja motar rai a b'ace da gudun tsiya ya harari Saeed yace " yanzu dan Allah dubi abunda ka jawo wancan mahaukacin ya aikata maka! Ina kai ina tunkarar shi in this state?" Murmushi  Saeed yayi idanuwan shi da suka kad'a ya d'ago yace 
*"Y'ar MAKIYAYA*tawa ce ni kad'ai, I want her all for myself"!!
Ameer ya ce 
"Dakata Bro! Tell me something, waye Wannan *y'ar MAKIYAYA* or what so ever ni na fa kasa gane maka! Yanzu harkokin naka kuma ya bar wayayyu ka dawo kula filthy talakawan nan? Ina nufin ina classic Bebe's d'in naka ? Me zakayi da herdsman daughter? Kazamai"

Cije leb'e Saeed yayi gami da lumshe ido yace "God damn she's so hot, har yanzu ban gama gane kyaun ta ba , I know nothing of her name but I want her badly! Ita ta banbanta da sauran Bebe's nawa, Bro zo kaga figure kamar wanda aka sassaqa, I longed to hug her  kai ita ta musamman ne".
Ameer ya kwashe da dariya harda buga stirring mota yace. "Kai! kai! Ina ma zan ga wannan mak'uran kyau d'in da ta birkita tunanin wani har yake. shan giya you should se yourself, yanzu de ba wannan ba barin yi sauri muje gida ko za'a samu a dunduma maka wannan ciwon tun kafin ya fara tsami dan wallahy ka sha naushi dubi yadda fuskar ka take shek'i kai ba da yarinya ba kai da shan na jaki wlhy kar ka yarda don in ka kyale shi kenan ma ya doki banza daga nan kuwa zai fara fankama yana burga cewa ya tab'a d'aura hannu a kan ka.

Tuni fuskar Saeed ya sauya ya harari Ameer yace "cigaba da irritating d'ina ka gani in ban fara ramawa ta kanka ba.

*Suraj*

    Jikin sa har rawa yake tsabar zuciya , da kyar Junaid ya iya bashi hak'uri ita dai tana tsaye rik'e da jacket nashi tana kuka cike take da tsoro ganin yadda fuskar shi tayi purple ga baki a fashe. K'arisa wa yayi daf da ita suna kallon juna ido cikin ido yace
  "Da kyau! Wai har yanzu kukan kike yi? Yawancin yammata in suna kuka muni suke yi amma a ke sai naki ya banbanta da su don kyau kika k'ara! Oh! Barin zauna don ban gaji da kallon kukan nan ba"
Tuni Laila ta tsinci kanta da sakar Murmushi sannan ta jefa mishi jacket d'in a fuskar shi. Dariya yayi ya janye jacket d'in ya dubi Junaid yace  
"Dan Allah kada ka sake barin ta ita kad'ai don in wani abu ya faru da ita bazan yafe wa kaina ba,  ina kaunar ta kuma bana so ta shiga wani hali" Junaid Murmushi yayi sannan ya koma bakin aikin sa Laila kuwa ita da Suraj suka kad'a dabbobin zuwa saman tsauni....

Post a Comment for "YAR MAKIYAYA CHAPTER 4"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...