Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YAR MAKIYAYA CHAPTER 3

YAR MAKIYAYA CHAPTER 3

- - Post a Comment
YAR MAKIYAYA




CHAPTER 3






Suraj da Junaid sun zamto tamkar da ma chan sun san juna, Suraj had his little fun adventure! Amma daga dawowar sa gida ya tarar da b'acin rai tun daga k'ofa. Bari muji yanda zata kaya tsakanin Suraj da Mahaifin shi Abdul-malik.... +

******* ********* ********

"Where have you been"? Dad ya tambaya cikin murya ta nuna isa, gaban Suraj ba k'aramin fad'uwa yayi ba da jin tambayar da yayi mishi amma yasan dole akwai aikin wancan bak'in munafukin Ameer.

"Tambayar ka nake kayi min shiru, ina ka shiga all this while? Ameer yace ko minti biyar baka yi tare da su ba kasa k'afa ka fita, haka naji wai kun yi akan zaka fita da Abubakar nan ma kayi wasting time d'in shi a banza ka fice ka tafi cikin wad'annan k'ask'antattu talakawan kana cudanya da su you are not even ashamed of your self!
Kai a k'asa Suraj yace "Dad I know this people are poor financially but so rich by heart! Ba dole bane se in suna da kud'i ko mulki za'a yi cudanya da su, mesa Dad?"

Wani Murmushi Dad ya sakar kafin ya zare medicated glass dake idon shi yace "Kamar yadda ya kamata ka fahimci cewa ba dukkanin su bane zasu yi appreciating duk abunda zaka musu na alkhairi, you have to figure out Who's worth your kindness and who's just taking advantage of it"!.
Su talakawa ne, da zarar ka sake musu tabbas zasu kunyatar da kai kuma daga baya kayi dana sani, ai kamar mahaukaci ne duk yadda ka saba bashi wataran ka gaza sai ka sha kashi a wajen shi."

Dad yana kai nan ya mik'e ya nufi k'ofar da zata sada shi da flat nashi, har ya bud'e k'ofa Suraj ya mik'e yace

" *Dad! Duniyar nan cike take da mutane na gari, in baka samu ko d'aya ba at least ka zamto guda zaka gane abinda nake nufi "*

Wani tsawa Dad yayi wanda hakan yasa falon ya d'auki echo shi kuwa Suraj bai jira me zai biyo baya ba ya haura upstairs ya bar Dad se tafasa yake yana huci ,har saida Suraj ya kusa k'ure staircase kawai ya lek'a k'asa abinda ya sake bashi mamaki da takaici ya hango.
Ameer ne tsaye hannun sa dafe a kafad'un Dad yana nuna kamar ya damu playing it cool amma idanuwan sa kan Suraj har wannan shu'umin Murmushin yana nan kwance a fuskar shi, Suraj ya cika da haushi ya daka masa harara sannan ya shige zuwa flat nashi.

Takalman kaf'an sa ya zare kusa da shoe rack sannan ya zare kayan jikinsa short kawai ya bari ya fad'a bayi, bai tashi jin zafin ciwon da yaji a hannun sa ba saida ruwa ya zuba a kai cikin sauri ya janye hannun yana kallon yadda knuckles nashi suka yi jajir haka ya ida wankan ya fito sanye da bathrobe yana goge fuska da k'aramin towel , da kyar ya yi shirin bacci tsabar takaici da k'uncin da Ameer ke chusa mishi. Bayan ya kwanta kan gadon ne ya d'auko wayar sa ya kunna, messages Kusan biyar duk na Oummin shi ne kafin ya gama karanta guda se ga k'iran ta ya shigo, time ya duba yaga 9:30 pm yace

"Oummi! You are still awake?" Am sorry ban d'auki wayar ki ba ban samu space bane ina tare da mutane."
Murmushin Razia ne yayi fading ta ce "Me yake damun ka? Your voice, it sounds as if akwai wani abu bothering you, tell me is it your Dad?

Tuni idanuwan Suraj suka kad'a murya na rawa yace "He's so annoying, sam baya fahimtar komai nawa, he has not changed a little k'iyayyar shi ga talakawa everything, bazai bar ni in yi rayuwar da naga shi ya dace ba miye aibun talaka, Oummi am not a kid ,yau na shigo garin nan amma gaba d'ayan su iri d'aya ne, they have no human feelings, I need you here Oummi pls ki taho"

A karo na farko kenan taji Suraj yana kuka, tun yana k'arami rabon da taji yayi kuka Amma for him to cry at 23 years tasan tura ta kai bango tana gudun kar wani ya cutar mata d'a dan haka ta yanke shawarar zata kamo hanya first thing in the morning, ba tare da ta sanar da Suraj zata zo ba ta yi k'ok'arin kwantar masa da hankali, sannan sukayi sallama , Suraj ya samu bacci amma banda Razia tuni ta fara had'a kayayyakin ta tayi shiri tsaf, gashi dama y'ar Uwar tata ta samu lafiya.

*Washegari*

Cikin bacci yaji k'aran bugun k'ofa , da kyar yayi k'ok'arin mik'e wa daga  kan sallayar da yake kwance da alama tun sallar Asubah yake kwance a wajen,  cikin magagi ya nufi k'ofar yana mutsitsika ido ya bud'e. 
   Abubakar ne tsaye tare da wata chocolate color mace kyakkyawa ta rik'o hannun Mimi yarinyar jiya duk suna Murmushi, Ajiyar zuci yayi kafin ya bud'e musu k'ofar suka k'arisa cikin d'akin.

  "Jiya nayi ta jiran ka baka dawo ba bamu samu zama ba sam, Wannan mata ta ce Fad'eematu mahaifiyar Meemy , tun jiya itama ta jira dawowan ka sedai ka dawo late shiyasa yau ta matsa se Mun zo don ta gayyace ka personally for breakfast" 
Murmushi Suraj yayi ya d'auki Meemy yace "Babbar Yaya guda ta girka abinci don ni ai ya zama dole in je, I'll just freshen up and come." Cikin jin dad'i Fad'eematu ta mik'e tace "zamu jira ka be fast". Kai kawai ya jinjina Abubakar ya masa Murmushi gami da dafa kafad'ar sa kafin ya fice Meemy kuwa tak'i bin su wai da Unclee zata zo hakan yasa Ya kunna mata cartoon a  tab nashi ya fad'a bathroom don watsa ruwa, bai wani dad'e ba ya fito cikin sauri ya kimtsa wata blue long sleeve shirt ya saka kan farin vest sannan ya sa blue jean flat shoe ya saka sannan ya rufe laptop nashi ya saka a side bag sannan ya d'auki wayar sa ya chusa a aljihu Hannun Meemy ya kama suka fice ko lek'a Dad bai yi ba ya ja motar shi ya bar harabar gidan. A daidai gate ya had'u da Ameer yana waya,saida suka yi kallon kallo iya son ransu kafin suka yi clear kowa yayi nasa waje, ko ba'a tambaya ba Suraj yasan Ameer wajen Dad zai je. Dan haka ya ja motar shi ya nufi b'angaren Abubakar.

   Bayan sun kammala breakfast Suraj ya taya Aunty Fad'eematu cleaning table suka dawo falo Suraj ya shiga wasa da Meemy, Abubakar ya k'ira sunan shi hakan yasa ya tattara duk hankalin shi ya maida gun Abubakar

"Ammm....... Suraj! Nasan jiya ranka ya b'aci ainun Saeed da Ameer haka suke kawai kayi hak'uri akwai ranar da zata zo su gane kuskuren su just don't take it to heart" Murmushi kawai Suraj yayi ,ya bud'e baki zai yi magana sai ga su sun shigo kowa ya nemi wajen zama hakan yasa yayi saurin gimtse maganar da zai yi ya mik'e yana duba agogon hannun shi kafin yace " Ni zan fita Yaya Matar Yaya  thanks for the breakfast it was great dining with you."

"Ena kuma zaka je haka daga shigowar mu?" Ameer ya tambaya wannan shu'umin kallon d'auke a fuskar shi
Hannu Suraj ya saka a aljihu gami da Mak'e kafad'a yace "kai kafi kowa sanin inda zan je Ameer but in case ka manta lemme remind you " A place full of love chan zan je I guess you have no problem with that?"

Kwashe wa Ameer yayi da dariya sannan ya d'aga hannayen shi biyu in surrender mode yace "No not at all me yasa zan damu? A dawo lafiya" Tab'e baki Suraj yayi ya fice yayinda Ameer ya bishi da kallo yana wata muguwar dariya.........Uwa mai dad'i! Sautin muryar d'an ta kad'ai ya isa gamsar da ita irin damuwa da kad'aici da yake ciki same applies to dear Suraj, ku biyo ni don jin yadda za'a kaya tsakanin Suraj, Dad, Mom da kuma bak'in maciji wato Ameer
#hearts to all moms out there! +

******          ******            ******

     "Junaid!" Suraj ya kwala masa k'ira wanda yasa Junaid mik'e wa daga tsugunno da yayi ya dube shi . "Aboki ka makara! Kai da nake ta jiran ka tun sassafe gashi har rana ta take?"

Yamutsa fuska Suraj yayi ba tare da ya amsa ba ya k'arisa inda Junaidu ke tsaye, wata k'atuwar saniya ce a tsaye k'afafun ta a d'aure gaba da baya ga madara mak'il Junaidu ya tatsa hakan ya burge Suraj sosai don haka ya matsa wa Junaidu da se ya koya masa yadda ake yi nan ya shiga gwada masa tun yana baya baya har ya kware, amma kam an sha dariya don daga saniya ta motsa Suraj se ya dungura gefe da kyar ya iya. Iya madaran da aka samu Junaidu ya nufi gida da shi Suraj na tsaye yana jiran shi.

    Da y'ar wak'ar ta ta iso tana wainar da sandan hannun ta, jin murya yasa Suraj ya d'ago bai ankara ba yaji gau! Sandar ta b'alle daga hannun ta zuwa goshin Suraj haka yayi sanadiyyar fashewan goshin sa yayinda Laila ta rufe fuskar ta da duk tafukan hannun ta gami da durk'ushe wa cike da fargaba.
Shiru ne ya dabaibaye wajen na y'an dak'ik'ai, Laila ji tayi kamar komai ya daskare ,daga tsakanin yatsun ta take lek'a shi yayinda ya rik'e goshin sa jini yana zuba d'ayan hannun kuwa ya rik'e sandar yana dumfaro ta, tuni gumi ya keto mata ba shiri ta fara ja da baya gani take zai rama ne ganin ja da baya bazai kai ta ko ina ba hakan yasa ta ranci na kare shima Suraj ya rufa mata yana fad'in "Ki tsaya ba abunda zan miki kawai sandar zaki karb'a" ko waigo wa bata yi ba tun abun yana iya gudun har kanshi ya fara Sara mishi sai lokacin ya tuna  da ciwon da yaji k'afafun sa suka yi nauyi ya kasa Jan su tuni komai ya koma dishi dishi Juyawan da Laila zata yi taga ya zube k'asa gashi wajen ba kowa se bishiyoyi , dawowa tayi gami da durk'usa wa kusa da shi tana k'ok'arin goge jinin dake goshin shi daga bisani ta ruga cikin tarin ganyayyaki da suka yi tsiro a wajen ta tsunko wani matse shi tayi a goshin sannan ta murza ganyen ya rufa a wajen da ya fashe, ganin ko motsi baya yi ne yasa ta ruga ta bar wajen, bata jima ba se gashi ta dawo tare da Baba wanda sai da yayi wasu dabarun Suraj ya farfad'o sannan ya taya shi mik'e wa da kyar don hajijiya da yake ji , 
"Yaro kana buk'atar Hutu muje gida sai ka huta" Cewar Baba, shi kuwa Suraj hankalin shi na ga Laila wanda ke b'oye a bayan wata bishiya tana lek'o shi. Murmushi yayi kawai ya lumshe idanuwa.

    A hankali take bin bayan su bata ankara ba taji an rik'o hannun ta gami da fisgo ta , da masifa ta juya  har zata yi magana suka yi ido hud'u da Junaidu, jiki na b'ari ta sunkuyar da kai k'asa kamar zata yi kuka tace

"Yaya Junaidu ba da gangan nayi masa ba ban sani ba ne dan Allah ka rufa mini Asiri kar ka fad'a wa Baba ni naji masa ciwo" cikin hasala Junaid ya ce " Ke rufe min baki! Yarima Belel ne shi in aka ga Wannan tabon ko wani abu ya same shi ai zaman mu da duk dangin my a nan garin ya k'are gashi abun da kika ja mana yanzu de kawai muyi addua kar wani abu mummuna ya same shi in".

*Wait a second! Did Laila just called Junaid as YAYA? In haka ne menene dangantakar da ke tsakanin su?*

   ****************

     Motoci uku ne suka shigo bakake haka ma gilashin  baka iya ganin komai na ciki, direct part d'in su Suraj suka nufa. Ba tare da ta jira an bud'e mata k'ofa ba ta fito, tana da k'iba kam amma ba na tashin hankali ba ,doguwar riga ce jikinta ta rufa mayafin a kanta ba tare da barin ko da ziri d'aya a waje ba, sannan fara ce sosai mai kama da Suraj ta wani wajen kamar idanuwa da kuma dogon hanci bugu da kari tsawo. cikin sauri ta shige k'ofar da zata sada ta da main house.

  Zaune ta iske shi yana kan laptop nashi duk hankalin shi ya tattara waje guda, bata tsaya b'ata lokaci ba wajen masa magana kawai ta ajiye handbag nata kan centre table sannan ta haura stairs. Cike da mamakin ganin ta da yayi Dad ya mik'e ya bi bayan ta zuwa flat nata   
   
A fusace ta juyo tana duban shi yayinda ya shigo d'akin gamida rufe k'ofar "Razia am not aware you are coming hope komai lafiya?".
Cikin hausar da bata isheta ba Razia ta dubeshi tace 
"Nazo ne saboda ga dukkanin Alamu kana nema ka salwantar min da rayuwar yaro, why can't you let him be who he is? Wannan rayuwar ta luxury ba sune a gaban sa ba sannan he's all grown up a shekarun shi bai kamata ba ka ce dole se ya zama kamar kai, ba duk aka taru aka zama d'aya ba Abdul-malik ina tsoro ranar da Suraj zai bijire yafi sauk'i ka fara appreciating respect da yake maka as a father before its too late".

Ajiyar zuci Dad yayi kafin yayi wata y'ar dariya yace "I knew it! In ba dan Suraj ba da bazaki zo ba, ko da na ganki ma nasan sai haka, now listen attentively! In har kina so mu shirya you better stay out of this! Babu rangwame tsakani na da talaka kuma in Suraj bai shiga hankalin shi ba I will disown him as a child!" Yana kai nan ya juya zai fice Razia ta katse sa da magana

  "Nasan bazaka aikata hakan ba! He's your only son! Kuma kar ka manta ni ma talaka ce ka auro ni, ko in tuna maka? Gidan bredi babana ya mallaka daga shi se k'aramin gida, nasan kimar talaka tunda nima ita ce, kuma you still can't change that, same applies to Suraj."

   Ko juyo wa Dad bai yi ba ya fice daga d'akin ita kuwa Mom ta wuce cikin gidan dan su gaisa da mutan gida.

*SURAJ*

   Yana bud'e ido Junaid ya fara gani cikin sauri ya d'ago a take yaji kan sa ya Sara ba shiri ya rik'e kan , gani yayi duk waje yayi dim yana d'aga agogon shi yaga biyar da rabi. Tsaye take bakin k'ofa tana kallon shi duk hankalin ta ya tashi a tunanin ta ya margaya ne.

  Murmushi ya sakar mata hakan yasa ta daina lab'en da take ta gudu shi kuwa ruwa ya buk'ata don bai yi sallolin shi ba ,yana idar wa bayan yayi addua ya ce zai tafi Junaid duk a rikice yake

"Yanzu in aka ga Wannan ciwon fa? Don Allah kada kasa ayi wa Laila wani abu, y'ar Kawu na ce ,nasan bata jin magana amma na tabbatar ba da gangan tayi ba"
Murmushi Suraj yayi,saida ya shiga mota yace "kar ka damu ba abunda zai sameta amma ka sanar da ita gobe in shaa Allah zan bata zab'i biyu! In kuma tak'i shine zata gane kuren ta domin zan nuna mata yadda ake yiwa wanda ya tab'a Yariman Belel!" Cikin Junaidu ya d'ura ruwa a tunanin shi Suraj zai yi wani hukunci mai tsauri ne gobe a kan Laila dan haka duk ya rasa sukuni shi kuwa Suraj tuni ya ja motar sa ya dad'e da barin gurin.........In bamu manta ba a episode na baya Laila cikin rashin sani ta yi wa Suraj rauni wanda hakan shi yayi sanadiyyar muka gano wata gaskiya guda ma'ana Laila K'anwar Junaid ne mahaifin ta k'anin mahaifin Junaid ne, a wani b'angaren kuma Mun ji yadda karon Dad da Mom Razia ya fara , shin wanne zab'i Suraj zai bawa Laila, sannan menene reaction d'in Dad Idan yaga wannan tabon dake goshin Suraj? Wanne hali Laila zata shiga Idan Suraj ya bata wad'annan zab'i biyu? Wanne makircin Ameer zai cigaba da kitsa wa? Don jin amsoshin tambayoyin nan sai mu garzaya shafi na Tara....
  
*****           ********          *******

     Tun a bakin k'ofa wani daddad'an k'amshi na Arabian turare ya bugi hancin sa wanda hakan yasa ya lumshe idanuwa gami da sake shak'ar Iskan karo na biyu. Tana hango shi ta mik'e cike da damuwa ta nufo inda yake, Suraj ko da wasa bai bari sun had'a ido ba kan shi a k'asa yace "Mom! am glad you are here!". Ba tare da ta ce komai ba ta d'ago fuskar sa "Who did this? Kayi fad'a ne? Speak to me!"

"Ammm.... No mom ban yi fad'a da kowa ba zame wa nayi na fad'i se kai na ya bugu shine wasu bayin Allah suka taimaka min that's all".

Murmushi mom tayi gami da girgiza kai tace 
"Suraj yau na farko kai min k'arya". Zaro idanuwa yayi lab'b'an sa suna rawa yana neman kalaman fad'a ya rasa , katse masa tunani tayi ta ce "Mu je in maka treating ciwon daga nan se ka yi wanka I have already cooked your favourite dish, later in ka huta se muyi magana." Ba musu ya k'arisa falon ya zauna yana kallo ta d'auko first aid kit ta fara treating ciwon Kasantuwar  tsagewa ce y'ar kad'an bazai d'auki lokaci ba wajen warke wa bayan ta kammala ta umarci hadima ta tattare wurin Suraj ya mik'e zai haura stairs suka ji  an bud'e k'ofa .

   Dad ne rik'e da kafad'ar Ameer sai kyalkyala dariya yake "that's good! Am so proud of you son!" Kalaman da Suraj ya dad'e yana begen ji daga lab'b'an Dad yau su Dad yake fad'a wa Ameer,  Mom ta ga reaction d'in dake fuskar Suraj bayan yaji wad'annan kalaman da Dad yayi na yabo ga Ameer dan haka ta dafa kafad'ar Suraj tayi masa nuni da ya shige ciki ya watsa ruwa , ba tare da ya yi magana ba ya kalli Ameer wanda daman tun shigowar shi abin da yake buk'ata kenan dan haka ya saki Wannan murmushin makircin , Suraj ya dunkule hannu kamar zai yi naushi sannan ya juya yaci gaba da tafiya bai ankara ba yaji an ajiye hannu a kafad'ar shi, rik'o irin na maza aka masa a tunanin sa Dad ne amma akasin hakan sai yaga Ameer ne, saida sukayi kallon kallo cike da b'acin rai Suraj ya buge hannun Ameer daga kafad'ar shi amma kafin Dad ya gani Ameer ya sauya fuskar sa zuwa na damuwa har da rik'e baki

  "Oh my God Bro! Suraj dubi goshin ka! Kar kace min wad'annan talakawan ne suka aikata maka wannan aika aika? Daman na sani they can never be trusted,
Look at you!  Dad ka dubi abun da suka aikata mishi. Ko ma waye yayi wannan dole ya karb'i hukunci mai tsauri because ya tab'o Royal blood."
Shi dai Suraj kallon sa yake cike da mamakin yadda Ameer ya juya salo ya nuna kamar ya damu kawai don Dad ya ga ciwon dake goshin sa kuma hak'ar sa ta cimma ruwa domin Dad tun kafin Ameer ya k'ark'are maganar har ya iso yana k'ok'arin duba raunin, Suraj na tsaye kamar gunki yana kallon yadda Ameer ya ja da baya ya bar filin wa Dad da Suraj suna tsaye yayinda Dad ke aika wa Suraj sak'onni ta ido shi kuwa Suraj kawar da kan shi yayi yana kallon gefe ganin haka Dad ya fusata ya waigo yana kallon Mom yace 
  "Yanzu kuma me zaki ce? How can I accept a son who doesn't even respect my presence? Wannan duk laifin ki ne , Suraj k'arami ne, give him more time ! Now look what has come of him! Rashin kunya tsantsa, yanzu dubi yadda kaje suka Faso maka goshi now tell me who did this?"

  Suraj idanuwan sa na bakin k'ofa yana kallon mai martaba Sarki da kansa tsaye, bakin k'ofa tun farko yaji abunda ya faru.

   Mom ta lura Suraj akwai abunda yake kallo tana juyawa taga mai martaba a tsaye yana kallon Suraj har zata yi magana ya hana ta  ya d'aga mata hannu sannan ya k'ariso inda suke. Ameer na ganin haka ya sulale ya bar wajen.

   "Suraj wuce ka jirani a chamber na yanzu ina zuwa" abunda Mai martaba ya furta kenan kuma ba tare da b'ata lokaci ba Suraj ya fice ya nufi chamber d'in kakan shi mai martaba.

Zama yayi bisa d'aya diga cikin kujerun living room d'in Razia ta duk'a ta gaida shi ya amsa cike da sakin fuska  "y'a ta naji duk abubuwan da suke wakana, kai bai kamata ba a matsayin ka na uba ace kana furta irin kalaman nan ga matar ka a gaban d'an ka, abu na biyu takura da kake nuna wa Suraj shi yake k'ok'ari ya b'ata duk tarbiyyar da kayi masa a baya. Speaking of talakawa ina so ka sani ni mahaifin ka ma asalin tushe na kenan, a talauci muka taso Allah yayi ikon sa ya bamu wadata dan haka bana so ka dinga chusa masa wannan banzar ak'idar, ni ba ma Wannan ne ya kawo ni ba, Akwai inda zan tura ka da wasu muhimman takardu zuwa England zai d'auki lokaci at least a month kafin a kammala komai kafin nan zaka tsaya sai takardun sun had'u" Mai martaba yana zuwa nan a jawabin sa ya mik'e ya fice at once.

    Tun shigar sa chamber d'in Mai martaba ya zube a   kan kujera yana  ta sharar bacci......
 

Sassanyar iska ce ke busawa yayinda Laila ke zaune kai a sama tana kallon sansanin taurari dake sararin samaniya, duk yadda tayi k'ok'ari don taga ta cire tunanin abun da ta aikata wa Suraj daga kundin kwakwalwar ta abun ya ci tura dan a tsorace take akan zab'i biyu da zai bayar ta kasa ko da runtsa wa. Zubaina dake hira da Junaid ta lura k'awar ta na cikin damuwa dan haka ta dawo kusa da ita tace

"Ina da shawara!" Da sauri Laila ta juyo a firgice tace "fad'a min Zubaina miye mafita?".
"Mafita d'aya ne kawai kar ki yarda ku had'u, diga kin ganshi ki gudu. Tab'e baki tana tunani ba tare da ta sake magana ba.

******************

     Sai daidai Maghreb Suraj ya farka inda ya hango d'an tsohon kakan shi na shirin fita masallaci, da sauri ya fad'a bathroom ya d'auro alwala suka fita tare da mai martaba
A hanyar sa ta dawowa yana waya da abokin sa  mistakenly ya ci karo da su Saeed ,sauk'e wayar yayi ya d'ago kai yana k'ok'arin basu hak'uri amma se Ameer ya hankad'e shi ta hanyar dukan k'irjin shi , duk da haka bai gaza ba ya kai hannu zai tab'a Saeed shi ma Saeed ya masge hannun sa.

   "Kai dallah get lost half cast kawai! Baka da gurbi a nan me zai hana ka koma wajen masu jajayen fata? Ina ga a chan zaka fi samun wajen shiga a nan kam babu abunda ka isa ka tab'uka. We rule here." Cewar Ameer in his husky voice.

  "Kuma kada ka sake yunk'urin tab'a jikina, don duk wanda ke mu'amula da wad'annan talakawan kafin ya kai hannu ya tab'a ni sai ya yi wankan tsarki" Cewar Saeed. shi kam Suraj ya dad'e da daskare wa a wajen a tare suka banke shi suka wuce ya juya ya bi su da kallo har suka b'ace.
Juyawan da Zai yi idanuwan sa suka yi arba da na Mom  . daga hawayen dake zuba a fuskar ta ya fahimci Cewar ta ji duk abun da ya wakana dan haka ya wuce cikin gida ba tare da furta komai gareta ba ita ma ta bi shi da ido kawai ta kasa ko d'aga k'afa.

  A living room ya zube yana kallon yadda masu aiki ke kai kawo kowa da nashi hurumin babu mai shiga hurumin wani daidai lokacin Mom ta shigo , zama tayi gefen shi tana kallon how desperate he looks. Suraj yana feeling idanuwan ta a kan shi dan haka ya kwantar da kan shi a cinyar ta yace
"If only zasu yi minding business nasu, su fita harkar abun da bai shafe su ba, mom na gaji already! Am going back to Cairo Wannan wajen babu soyayya, babu komai se takura,hantara da tsananin rashin tausayi..."

Bai gama rufe baki ba suka jiyo murya diga k'ofa
"Kada ka kuskura! Kar na ji ka sake maganar komawa Cairo ,wannan gari shi ne tushen ka sannan ko ita mahaifiyar ka yanzu bata da wajen da yafi Wannan! Kai gwara kai domin ko rabin tsangwamar da Razia ta sha kai baka sha ba"

A tare Suraj da Mom suka d'ago kai Mom ta saki Murmushi Suraj kuwa duk'a wa yayi ya gaida ta. 
Matar Uncle Ahmadu ne Mahaifiyar su Ameer wato Maryam.........

Post a Comment for "YAR MAKIYAYA CHAPTER 3"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...