Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YAR MAKIYAYA CHAPTER 12

YAR MAKIYAYA CHAPTER 12

- - Post a Comment
YAR MAKIYAYA
CHAPTER 12Kwalbar giya Brandy ita ce a hannun sa ,fuskar nan a dak'ile ga d'akin duk duhu ya mamaye se d'an hasken rana da ya hasko ta windon wanda bai kai ya haska d'akin ba , surutai yake ta yi shi kad'ai yana b'ab'atu +

"Saeed Bro! Kai dai bazaka tab'a sauya halin ka na shan giya ba," Cewar Ameer da ya shigo she toshe hanci yake.

Wata gajiyayyan dariya Saeed yayi kafin da kyar ya ja jikin ya gyara zaman sa yace

"Kamaaar yyadda bazzzakka t..taab'a daina gulma da shishigi ba ko? Tell me shin kkaaa samo yarinyar ko Yaya? Kasan yyadda nake son ta kuwa? I will spend the whole night with her! "

Shu'umin dariya Ameer yayi gami da shafa fuska yace "Na ga yarinyar ma, Amma bazan iya kawo maka ita ba because kawai zaka lalata mata rayuwa ne ka jefar da ita, bazan iya bari kayi haka ba, dan Allah baka da wani aikin ne se Shaye Shaye da neman mata ? Mutum kamar d'an bunsuru?

Kwalbar giyan Saeed UA fasa har saida Ameer ya tsorata ya mik'e kafin yace

"Look Ameer! Ni da kai kar ta san kar ne , I know you more than yourself kai ma crook d'in kanka ne, banbancin shine kai baka antaya Kwalaben "

Dariya Ameer ya sake yi saida Ya isa k'ofa ya juyo yace "sannan I am not a womanizer like you Saeed!" Yana kai nan ya fice yana dariya

Yayinda gida ke k'ara cika da bak'in y'an uwa da abokan arzik'i daga nesa , Angwaye da Amare kowa yana fama da nashi shirin Ameer shima yana nashi shirin, so babu wani wanda ya shiga harkar d'an uwansa haka zalika ko Dede da matsala d'aya ba'a samu ba.

*The day*💃🏽

Zaune take gaban madubi k'afa d'aya kan d'aya yayinda Famous makeup artist Feedoh y'ar ficika da wasu masu taimaka mata su biyu ke ta faman chanchad'a mata kwalliya, Sapna da Zubaina na kan gado suna hira

"Finally! Nan da mintina basu fi talatin ba wata zata tashi daga Laila ta koma Mrs Suraj" Cewar Sapna , duk su Feedoh suka sa dariya.

Bayan Sallar juma'a a masallacin Sarki aka d'aura auren Laila da Suraj, bikin da ya samu halartar wasu jinin sarautar , da masu fad'a aji a siyasa, domin mai martaba ya kasance na kowa ne shi, immediately ana d'aura Aure aka wuce reception.

Bak'in riga ya saka Pakistani sannan ya toshe fuska da bak'ak'en shades ya shigo wajen reception, straight wajen Dad ya wuce ya d'an Sunkuya daidai kunnen sa ya fad'i wata magana, Dad ya d'ago a nutse ya kalle shi kafin ya yi excusing kanshi ya fice ya bi yayan Ameer suka fita.

Wani makeken falo ne wanda yaci sunan sa falo suka shiga, zama Dad yayi sannan yayi wa Ameer nuni da ya zauna babu b'ata ko da second d'aya Ameer ya nemi waje ya zauna sannan ya zare shades d'in idon shi

"Ahan! Ameer fad'a min, menene matsalar ? Kaga ina tare da mutane amma jin kace its urgent shiyasa na taho"

A cikin ranshi Ameer yace "Hah! Bayan kaji abunda nake son fad'a maka inaga baza ma ka samu kwarin gwiwar komawa wajen mutanen ba".

"Ameer tunanin me kake yi haka? Ka taso ni kuma kayi shiru baka ce komai ba har yanzu!"

Cikin salon nuna rashin jin dad'i Ameer ya fara

"Na d'auka matsayin ka a wajen Suraj yafi komai, Ashe kawai tunani na ne! Dad ban san ya zan fara fad'a maka ba domin maganar tana da matuk'ar nauyi da girma, da ace kai ne mahaifi na I would do anything in my power to make you the happiest and proudest father in the whole world, unfortunately se gashi baka yi sa'ar d'a ba Dad, how can I even start telling you this?"

Ya goge hawayen munafurci . "Ameer ka fa saka ni a duhu just go straight to the point! Me Suraj ya aikata?" Dad ya tambaya a rikice

"Suraj ya zalunce ka Dad! Its all a lie, Laila ba wata y'ar kawu Rasheed bane y'ar nan Belel ce kuma *Y'AR MAKIYAYA* Su duka sun yi maka karya yarinyar da bata da asali! It's all Suraj and his plans".

Mik'e wa yayi a take yaji kamar an raba jikin shi da jini idanuwan Dad suka kad'a ya kalli Ameer yace

"Suraj bazai tab'a aikata haka ba! Maybe akwai abunda baka fahimta ba d'ana Ameer.".

Kuka Ameer ya sa sannan yace "dubi yadda ka yarda da shi, dubi yadda soyayyar sa ta fito k'arara a fuskar ka amma shi kuma sai yayi taking advantage d'in wannan soyayyar da kake masa ya zab'i ya saka maka da rashin biyayya da cin amana".

Tsugunno wa yayi a gaban Dad yaci gaba da cewa
"Ban tab'a maka k'arya ba, kuma bazan tab'a ba saboda nasan value d'in uba da kuma muhimmancin sa ga d'a, wannan file d'in yana k'unshe da gaskiyar lamarin sannan ga cameran Suraj nan wanda ina kyautata zaton ka san shi ka duba, in har abubuwan da na fad'a maka sun sha Banban da abunda zaka ci karo dashi a cameran duk hukuncin da k'anin na d'auka".

Dad da yanzu kam gumi ya keto masa ya d'auki cameran ya kunna yana scrolling duk hotunan Laila da dabbobin ta da na Junaid ne har ma da video clips, haka ma files d'in yana k'unshe da pics na makeover da akayi wa Laila da papers na agreement da duk wani kud'i da aka kashe don ganin ta dawo Laila Rasheed.

A lokacin da Dad ya gama ganin komai ,jikin shi ne ya d'au rawa ya ma kasa mik'e waduk da ana yunk'urin yin hakan.
Kafad'ar Dad Ameer ya dafa ya mayar dashi cikin kujerar kafin ya nufi fridge ya zubo ruwa mai sanyi a glass ya bashi yana wannan murmushin irin na samun nasara.

@reception.

   Suraj na tare da abokan sa kowa yana fad'in Albarkacin bakin sa ana ta hira da raha Habeeb ya shigo

"Suraj I thin akwai matsala, Dad ya k'ira waya na yace yanzun nan kaje. Kuma kafin nan d'azu naga ya fita tare da Ameer ,gaskiya hankali na bai kwanta ba.

Suraj da ke ta murmushi na yak'e gudun kar agano matsala ya mik'e ya ja hannun Habeeb suka nufi sashen da Dad d'in yake........Tsaye tayi bakin k'erarrun French window da ke sada ta da gaba d'aya filin gidan tana kallon yadda  mutane ke kai kawo , masu bada tsaro na yi yayinda sautin wajen duk ya sauya daga k'aran kukan tsuntsaye masu dad'i zuwa busan kakaki da algaita
  Sabon al'amari ne a wajen ta , dawowa tayi gaban madubi tana k'are ma kanta kallo diga sama har k'asa
Bak'in atamfa mai pink floral prints ne a jikin ta riga da skirt tayi mata cif cif ,kuma ta karb'i farar fatar ta sosai gaskiya Feedoh y'ar ficika ba baya ba wajen iya tsara kwalliya ,yadda kasan y'ar tsana haka Mrs Suraj ta koma, sedai gaba d'aya bata da wani sukuni don duk fargaba ya cika ta ba tare da dalili ba gashi duk su Sapna sun fita wai a hakan sun bari ne ta huta, kan gado ta koma ta zauna ta k'ura wa k'ofa ido.

***    ******** *****

  Da sallama ya tura k'ofar ya shigo, Dad ya hango tsaye ya juya baya hannuwan sa ya nad'e su a bayan sa , kamar an ce kalli gefe ,Suraj ya hango Ameer tsaye yana masa wannan kallon na munafukai ,yayinda ya jingina da wani tsohon book shelf ya nad'e hannuwan sa a k'irji.

Suraj bai k'ara masa kallo na biyu ba ya k'arasa gun Dad ya tsaya "Dad ka aika a kira n....."

Suraj bai k'arasa ba dad yayi wani irin tsawa tare da sharara wa Suraj mari lafiyayye a kunci
"DON'T YOU DARE ADDRESS ME AS YOUR DAD!!"

Sam Suraj bai yi mamaki ba tunda har yaga Ameer a wajen. D'ago wa yayi ya kalli Dad da har huci yake yi sannan ya sake bud'e baki zai yi magana

Hannu Dad ya d'aga masa sannan yace
"You betrayed me! Kun yaudare ni, kun maida ni mahaukaci Bravo alaika ya Suraj bravo!  I regret having you as a son! 
   Kayi abunda kake so ka auri kaskantacciya y'ar k'ask'antattu ,marasa ilimi, ka huta! Yes!

   Suraj bai ce komai ba se hawaye d'aya na bin d'aya diga idon shi, yayinda Ameer ke gefe yana jiran lokacin da ya dace ya shigo maganar.

  Habeeb ne ya shigo falon da sauri har yana cin karo da Zainab 
"Kai dallah me haka baka da ido ne?" 
Cikin rud'ani yace

"Look Zainab don Allah ki taimaka ki nemo min Ummi akwai matsala ,dan Allah ba don ni ba ".
Sosai Zainab taga rud'ani a tare da shi dan haka ta haura upstairs neman Ummi shi kuma ya hango mom tare da wasu mata yayi sauri ya kutsa cikin yana k'iran ta

"Ganin fuskar shi kad'ai ya isa ya fahimtar da ita tashin hankalin da yake ciki ,hannun ta yaja suka fita Sapna dake zaune a gefe taga fitan su jikinta ya bata akwai matsala dan haka tabi bayan su ,haka ma Ummi suka fito da Zainab

"Habeeb lafiya na ganka haka? Me haka kamar baka da lafiya".
Kai Habeeb ya girgiza yace 
"Mom gwara rashin lafiya ta so dubu akan abunda yake neman faruwa yau d'in nan! , Ameer ya sanar da Dad komai game da Laila yanzu haka Suraj yana chan anything can happen Mom"

  Kasa Tsayawa Mom tayi kan k'afafun ta ,da sauri Sapna ta rik'e ta ,Ummi tace "Sapna ki kaita d'aki ta huta ni barin je, kai kuma Habeeb iya saurin da kake da shi kayi amfani da shi wajen nemo  Abban ka tunda nasan yanzu mutane sun tafi reception ya k'are .

Habeeb ya juya da sauri ya tafi Ummi ta nufi sashen da Dad yake Mom ta tattara duk k'arfin da take da shi ta k'ok'arta ta mik'e tace "Sapna bari kawai na je  koma me zai faru ya faru, bazan bari a tauye wa d'ana farin ciki ba kawai don son duniya, babu aibu don ya auri y'ar talaka, what ever happens bazan yarda in rasa d'ana ba" 
Tana maganar tana hawaye ta wuce ta nufi hanyar sashen dad.

"Suraj me nayi da zanyi deserving Wannan cin amana? "Dad ya tambaya duk hannuwan sa biyu ya shak'e wuyan rigar Suraj,yayinda Suraj ke tsaye jiki a sake ya kasa cewa uffan.
Hankad'a shi Dad yayi bai ankara ba yaji ya fad'o kan dank'areren centre table dake falon inda ya dare ya tarwatse,  Dad ya sake d'ago shi yana kallon fuskar sa yace "d'ago ka kalle ni ! Look me in the eyes and tell me duk abubuwan da ke file da cameran nan k'arya ne!"

Suraj ko d'aga kai bai ba se Ummi dake tsaye bakin k'ofa ne ta tanka masa .

    "Babu k'arya ko d'aya daga cikin abunda ka gani ,everything is just the damn truth! "

Mari Dad ya sharara wa Suraj wanda yanzu kam farin rigar jikin sa ta sha fentin jini ga yakan da glass yayi  masa. "Kai ba d'ana bane! You are nothing compared to irin y'ay'an da na ke burin samu,but zan baka zab'i biyu! Just two choices! Ka rabu da y'ar
Makiyayan nan yau yau d'in nan ka auri khadija yanzun nan, ko kuma daga yau hanyar da nabi kar ka bi balle mu sake had'uwa."

   A galabaice Suraj yace "Am sorry Dad, kayi hak'uri nasan na maka laifi amma ba laifi na bane, ni banga aibun talaka ba, yanzu in na auri khadija cutar ta kawai zan yi don bazata tab'a samun soyayya daga gare ni ba,akwai hakkin ta da zan tauye masu yawa ,sannan wata gaskiyar itace *ina matuk'ar k'aunar Laila ,ka zo min da zab'i mai wuya ,bazan iya rabuwa da kai ba sannan bazan iya yin saki ga Laila ba I can't divorce her Dad ka bani wani zab'in dan Allah ka min sassauci Dad.".

   Duk maganganun nan a gaban Abban Affan, uncle Rasheed da baban Ameer uncle Ahmad Suraj yayi shi.

A hankali Uncle Ahmad ya k'araso ya janye Suraj daga Hannu Dad ya nuna mishi waje kan cewa ya zauna. Ba musu Suraj ya zauna da kyar yana maida numfashi ,Sapna kam ta manne da bango tana kuka Habeeb baya ma kallon cikin falon ya fuskanci Ameer suna kallon kallo.

  "Suraj tashi muje ciki dubi yadda kake bleeding , muje in treating maka ciwon." Cewar Ummi " da kyar ya mik'e suka bar falon ta wani k'ofa daban inda babu mutane saboda gudun magana.

Uncle Ahmad ya dubi Dad ya ce "am very disappointed in you Abdul-malik! How can you be so mean? D'an ka na cikin ka zaka yi wa illa haka? Me ya sha kanka?  Ka sha wani abu ne?"

Shiru yayi da ya juya idanuwan sa suka sauk'a kan na Ameer ya daka masa tsawa yace

"Uban mi kake yi a nan? Kaga sa'annin ka ne ? Will you get the hell out of here stupid ! Manya suna magana ka saka su a gaba , nasan ko wannan matsalar da ta faru bazai rasa nasaba da kai ba! Ina da yak'inin cewa you were involved".

  Kafad'a a d'age Ameer ya fice yana Murmushi Se lokacin Uncle Ahmadu ya maida duban sa zuwa ga su Mom yace "maganar nan ba na tsaye bane ku zauna ina buk'atar explanation Razia tell me miye ya janyo duk wannan?.....Duk wad'annan abubuwa sun faru while ina cikin gidan nan but no body dares to tell me? Razia ta Yaya zaki biye wa tsoron fushin Abdul-malik har zaki yi k'arya? Ita Laila ba mutum bace? Ko kuma kai Abdul-malik wayon ka ne ya baka arzik'i ko kuma duk duniya kaga  wani mahalukin da ya aka zana masa a goshi cewa shi mai kud'i ne ko kuma talaka? Ko kuma ka tab'a ji ance wa mai kud'i sai mai kud'i? Ya kamata ace by now ka san abunda ya dace .
Mik'e wa uncle Ahmadu yayi ya ce 
"Kai in tak'aita maka ban son k'ara jin an d'aga wannan maganar da babu ma'ana , Laila ta shigo gidan nan a matsayin matar d'an mu ,dole mu d'auke ta a matsayin y'a kuma mu rik'e ta Amana kada ka kuskura maganar nan ta je kunnen mai Martaba". Yana kai nan ya fice Dad ya bi shi da kallo har ya b'ace. Ba tare da kowa yayi magana ba kowanne ya kama gabansa. +

****         ****     ****

    Gajiya tayi da zaman shiru dan haka ta bud'e k'ofa ta fito, wajen shiru yake duk hayaniyar na downstairs.
Daga corner dake hallway d'in ta jiyo taku juyawan da zatayi ta hangi Ummi tare da Suraj a wani irin yanayi wanda yasa ta firgici ainun.

    "Sapna ki kula da Laila, Suraj kana buk'atar Hutu muje ka kwanta"

  Kai Suraj ya girgiza kafin yace "Ina son na ga Laila na wani d'an lokaci, hankalin ta bazai kwanta be she's shocked ,kar ki damu da ni ,nasan Mom zata fi buk'atar ki yanzu."
Murmushi Ummi tayi ta dafa kafad'ar shi sannan ta juya ta barshi tsaye a wajen.

    "Ki kwantar da hankalin ki Laila Yaya Lafiyan shi kalau kawai de d'an hatsari ne " kasa zama Laila tayi gaba d'aya she's restless sai yarfe hannu take.
A tsanake ya turo k'ofar ya k'ura musu ido su biyun yayinda su ma suka maida duban su gareshi.
Ficewa Sapna tayi ta bar su tsaye, Jinin Daya b'ata jikin Suraj shi ya k'ara birkita Laila ta hau rawar jiki, Idan yayi taku d'aya kusa da ita se ita kuma ta ja baya ta rufe ido, se lokacin ya lura Cewar sosai glass ya yanke shi ga jiri da yake ji. Bai bi ta kanta ba ya wuce  bathroom ya fisge rigar jikin shi ya jefar sannan ya saki shower a kan sa, shi kanshi yanda ruwan ke wanke jinin ya razana shi, ya tabbata in yayi wasa zai yi kwanan asibiti. Towel ya d'aura ya fito rik'e da cikin sa ya jingina da k'ofar yana kallon ta , zaune take k'asa ta had'e kai da gwiwa bazai iya tantance kuka take ko kuma akasin hakan ba.

"Laila". 
Ya k'ira sunan ta ,dago wa tayi a hankali ba tare da ta kalle inda yake ba, da kyar ya ja jiki ya dawo inda take ya d'ago ta ,ta hanyar rik'e kafad'ar ta duk da haka bata kalle shi ba tana kuka.

"Tsoro na kike ji? Nine fa Suraj, dan Allah ki kalle ni ko zan samu nutsuwa."
Idanuwan ta ta d'ago tana mai aza su kan fuskar Suraj zuwa faffad'an k'irjin shi sannan cikin shi da ya rik'e wanda bai bar fitar da jini ba, tuni ta fara rawar jiki ta kasa fad'in ko da kalma guda.

    "Stop it Laila! Dan Allah ya isa haka! Babu abunda zai same ni ki nutsu don Allah , ga ruwa Ki sha yanzu zan dawo ina zuwa"
Yana mik'a mata ruwan ya fice ya barta cikin tsoro.

"Razia take it easy, komai zai dawo daidai kuma Suraj ba k'aramin yaro bane, zai kula da kanshi nasan Abdul-malik kawai yayi zuciya ne saboda k'aryar da muka yi tarayya muka masa kum..."

Bata k'arasa ba Suraj ya shigo gami da maida k'ofar ya rufe cikin b'acin rai da hasala yace

"No! Sam wannan ba haka bane! Bai yi zuciya don k'aryar da muka masa ba ,bai yi zuciya don yana tunanin duk Mun raina masa hankali ba, sedai don na auri *y'ar makiyaya* da bakin shi ya fad'i hakan cewa *in rasa wanda zan aura se y'ar makiyaya?* in one word He hates me kuma ba tun yau ba nasan cewa ya tsane ni, bay tab'a yin alfahari da ni ba ko Dede da rana d'aya tak!

Ummi ni fa wani sa'in sai in dinga kokwanto anya Dad mahaifi na ne kuwa?"

Kuka Mom ta saka yayinda Suraj ya juya zai bar d'akin

"Dakata!" Ummi ta tsayar shi, tsaya wa yayi chak yayinda yake jiran k'araso wan ta

"Kar na sake jin wad'annan munanan kalaman daga bakin ka, in ba mahaifin ka bane Toh na waye?
Abunda ya kamata ka fahimta game da Dad d'in ka shine yana so yaga d'an sa yana irin lifestyle d'in shi, Suraj mahaifin ka ne shi kar ka sake fad'in kalma mara ma'ana gare shi.

"Oh my god Suraj!
You are bleeding"!! Se lokacin Mom ta d'ago a firgice ta taso ta rik'e hannun shi tana kallon yankan da glass d'in yai mar.

"Mom please kar ki damu , lemme get dressed first, zan kula da ciwon."

Murmushi yayi ya fice Mom ta dafe goshin ta ,Ummi ta bud'e baki zatayi magana suka jiyo k'aran fad'uwar abu . mom bata b'ata lokaci wajen k'iran sunan Suraj ba cikin tashin hankali suka yi waje.

Kwakkwaran motsi baya yi kawai yana kwance a k'asa kamar babu rai a tare da shi , daidai lokacin Habeeb ya iso wajen ,bai yi wata wata ba yayi k'ok'arin d'aga Suraj da taimakon Ummi suka saka shi a d'aki kafin ya k'ira likita a waya.

   Zubewa tayi k'asa tana hawaye ,Ummi ta dad'e tana kallon ta kafin ta nemi waje ta zauna gefen ta

"Razia wai mesa kike haka ne? Kukan da kike ba chanja komai zai yi ba, ga doctor yana duba shi am sure jinin da ya zubar ne, yasa shi fad'uwa in Allah ya yarda komai zai dawo dedai"

Likita ne ya fito yana kallon su se Habeeb ne yayi ma Ummi magana

"Ummi Suraj yana buk'atar Hutu ne kawai, depression da frustration ne duk suka had'u suka masa yawa gashi kuma ya zubar da jini ,duk abunda ya dace doctor yayi amma yana buk'atar Hutu ,duk wani abu da zai d'aga hankalin shi ba'a so."

Ummi ta mik'e tace "well! In that case se kuzo mu bar nan mu bar shi ya huta.
Mom tace "Amma ai bai kamata mu barshi shi kad'ai ba."
Murmushi Ummi tayi tace

"I know ! Nasan wanda yafi dacewa ya zauna kusa da Suraj yanzu, ki je sashen ki kawai ki huta don nasan a gajiye kike ni zan kula da komai.

    Habeeb yayi sallama da doctor sannan ya nufi inda suka sauk'e bak'in su , domin kar suga shiru gashi yamma tayi wasu sun dad'e da tafiya se close relatives......

Post a Comment for "YAR MAKIYAYA CHAPTER 12"