Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YAR MAKIYAYA CHAPTER 11

YAR MAKIYAYA CHAPTER 11

- - Post a Comment
YAR MAKIYAYA
CHAPTER 11

Tun had'uwar Suraj da Ameer basu sake had'uwa ba babu wanda ya shiga harkar wani se yau da suka tattara zasu koma Belel , Dad ya Matsa wai se an taho da Laila amma Ummi tayi y'an dabarun ta tace "ai zata koma Istanbul saboda karatun ta, Dad ya juya yace "ina Suraj d'in? " +

Daidai lokacin Suraj ya fito yana jan jakar sa ,sallama yayi wa su Ummi da Laila ya kuma tabbatar mata zai dawo kwana kusa " Junaid ma suka yi sallama da Suraj Su Dad suna mota suna jira Suraj ya shigo suka ga ya nufi inda motar sa take ya jefa jakar sa ciki
Wata shu'umin murmushi Ameer ya yi kafin ya ce "Aha ah? Daman ba tare zamu tafi da Suraj ba?"

Se lokacin Dad ya lura da inda Suraj yake amma kafin ya ankare Suraj ya ja motar sa yayi gaba abunsa ,Murmushi Mom tayi yayinda driver ya ja mota suka wuce Airport direct, shi kuwa Suraj ya tafi by road abunsa hankali kwance .....

*three months later*

Watanni uku ba wasa ba Laila ta yi clean da ita har wani d'an k'iba tayi ,duk inda Ummi zata tare suke zuwa harta Egypt da London Laila ta je sedai har lokacin Uncle Rasheed bai samu had'uwa da Laila ba , harta bikin Sapna ma a gurguje ya yi ya koma.

B'angaren Suraj kuwa tun komawar sa gida Ameer ya fita harkar sa abun har mamaki yake bashi, gashi Dad har wani jan shi yake a jiki, Mom dad'in hakan take ji amma Suraj sam hankalin sa bai kwanta ba don Dad bai saba jan shi a jiki haka ba. Cikin watanni uku komai daidai yake tafiya wa Suraj ,da Laila yanzu haka suna shirin komo wa Belel ,Junaid da Habeeb kam sun fi sati a Belel.

Ummi na shigowa Belel bata fara sauk'a ko ina ba se gidan su Laila, da taimakon Laila , tun kafin ta shiga take k'iran baba, shima tun diga d'aki ya jiyo muryar ta ya fito ,rungume shi tayi cike da murna harda d'an kukan ta, Baba kuwa mamakin yadda ta sauya yake kamar dama chan a birnin take , bayan Ummi sun gaisa da Baba ,Laila ta kawo kayan da ta kawo masa ta bashi yayi ta godiya da sa Albarka sannan suka masa sallama suka nufi gida.

Su Mom suna zaune a falo ana ta hira harda su Uncle Ahmad se ga su Ummi ,sun sha tarba kam musamman Laila kowa se jan ta yake a jiki , Mom ce ta k'ira Fati d'aya daga cikin hadiman ta ,tace

"Ki kai surukar tawa d'akin ta, ina fatan ko ina a gyare kuma ki tabbatar bata yi lacking komai ba" Laila ta mik'e suka nufi upstairs. Ba shakka d'aki ne mai kyaun gaske amma sam Laila ba dad'in zaman take ji ba don ita in da son ranta ne tunda yau ta dawo a barta ta sha hira da Baba don tayi kewar shi da kuma dabbobin ta dan haka ta dubi Fati tace

"Ammm.... Ina Suraj yake? Don Allah ina son magana da shi."

Murmushi Fati tayi tace "Da sauri haka ranki shi dad'e? Da dai kin yi wanka ki huta zan kawo miki abinci ,me kike buk'ata?"

Kai ta girgiza tace "ni duk abunda kika bani zan ci amma nidai kafin nan ki min magana da Suraj maganar tana da muhimmanci.

Rusuna wa Fati tayi sannan tace "kamar yadda kika ce ranki shi dad'e". Tana kai nan ta fice.

Tsaye yake bakin k'ofa ya rik'e handle din yana waya tayi knocking, at once ya bud'e yana kallon ta ido cikin ido kafin ta sauk'e kai k'asa ta gaida shi , cike da kula ya amsa gaisuwar sannan ya katse wayar tasa ya ce

"Yes? Me kike yi a nan?". Cikin rusuna wa tace

"Ranka shi dad'e yarima daman......" Bata k'arisa ba ya dakatar da ita da cewa

"Ke! Ni Sunana Suraj! Faqat, tell me me ya kawo ki ?

"Gimbiya Laila tace tana son ganin ka yanzun nan tace wai maganar na da muhimmanci ".

Murmushi Suraj yayi ya tura k'ofar ya rufe yace "muje". Nan Fati ta wuce gaba yana bin ta har d'akin Laila We are back in Belel ! Shin creepy Ameer me yake shirya wa nan gaba? Ko da yake at least yanzu Dad da Suraj suna jituwa damuwa ta ragu but beware "A snake will always be a snake🖊 +

Yana shigowa idanuwan su sukayi arba da na juna gaba d'aya aka rasa me kawar da idon sa , zama yayi gefen gado yayinda take zaune kan stool a gaban mirror
, d'ago wa yayi ya dube ta kafin yace

"Madame! Gani na zo! Fati tace kina son gani na"

Duk courage d'in ta na magana sai ta rasa saboda yadda ya kafe ta da ido yana kallon ta

"Ina so na kwana a gida ,nai kewar Baba sosai shine .....kum...kumaa....

Dariya ce ta kufce wa Suraj ya mik'e yace "d'auko mayafin ki in kai ki gun Baban Y'ar Baba"
D'ago kai tayi ta kalle shi da mamaki tace "kayi hak'uri Suraj....." Dakatar da ita yayi ta hanyar d'aura yatsan shi a kan leb'en sa yace

"Shush! Na sani cewa abu ne mai wuya ka sadaukar da farin cikin ka domin wani ya samu, Laila ba k'aramin namijin k'ok'ari kika yi ba ,saboda nine kika yi nesa da gida da duk abubuwan da kika saba rayuwa cikin su, baki iya irin rayuwar da nake ciki ba amma kika koya duk don farin ciki na ,kin sadaukar da abubuwa da dama Mai so na, Idan har yau na kasa cika miki d'an k'aramin burin ki ban yi miki adalci ba, yau a gidan baba zaki kwana nai miki alk'awari dan haka d'auko mayafin ki"
Ba b'ata lokaci ta zari mayafin ta suka fita ,bai dire ta ko ina ba se gida, shima Babban ya hana shi tafiya saida suka sha hirar su.

Wajen yaban isha Suraj ya kamo hanyar dawowa gida ,daga gefen hanya ya hango mota an yi parking ga full light , Ameer ne tsaye tare da wani mutum wanda ko shakka babu Baban Junaid ne yayan Mahaifin Laila ,Suraj yana ganin su saida gaban shi yayi wata irin fad'uwar da bai san dalili ba , Ameer me yake nema? Suraj ya tsorita sosai don yasan in Ameer ya gano Laila y'ar Makiyaya ce akwai matsala.

Tuk'i ya cigaba da yi ya k'arasa gida ,babu kowa a falo dan haka ya nufi d'akin sa,.
Wanka yayi ya fito sanye da bathrobe yana goge fuska ya sauk'o downstairs ya nufi dining,

"Yallabai me za'a kawo maka?"
"Anything eatable" ya amsa a takaice.

Tuwon semo ne da miyar alayyaho ga manyan parts din catfish a ciki ,Suraj ya sa Tuwon a gaba shi bai ci ba shi bai tashi ba , Kusan mintina goma ya k'ura wa abincin ido.

Hannun shi a aljihu yana tsaye a tsakiyar falon yana kallon Suraj da wad'annan idanuwan nashi masu kama da na maciji kafin ya saki Murmushi ya k'araso ya ja kujera ya zauna yana facing Suraj.

"Ina mamakin wasu mutane, ban san meyasa ba mutum irin ka gaka prince ga kuma yarinya y'ar masu kud'i daga kaduna kuma ma gata daga Istanbul ta yi karatu ba wata *y'ar makiyaya*ba zai damu kansa ya dukufa yana tagumi."

Rai a bace Suraj ya d'ago yana kallon sa kafin ya cigaba da cewa

"Ai tagumi yanzu ka fara shi brother! Sai na fallasa ka ,I promise you this , *y'ar makiyayan* da ka d'auka ka kai birni ka wanko ta sai ta koma gidan jiya , wannan kusanci da ka samu wajen Dad se na tarwatsa shi,ko ka d'auka zaka raina min hankali ne? Nasan komai Suraj , you can fool any body but not Ameer".

Tsabar Suraj ya hau dokin zuciya ,jikin sa na karkarwa ya d'auki gaba d'aya plate d'in ya wurga wa Ameer abinci ya zuba gaba d'aya a jikin sa kafin Ameer ya motsa Suraj ya chafko shi ya dinga surfa masa lafiyayyun mari ,gaba d'aya a gaban y'an aikin da hadimai kafin ya ci kwalar Ameer murya na rawa yace

"Stay away from me! Stay away from my life in ba haka ba zan illata ka a gidan nan

"Suraj relax! Duk illar da zaka min fa bazai kai wanda zan maka ba, domin illar da nake shirin yi maka ba, sai na tarwatsa komai naka!"

Suraj da ya cika da mamaki yace "Wai nikam Ameer ka fad'a min iya rayuwar ka me na tab'a yi maka da zan yi deserving irin wannan wulakancin haka? What wrong have I ever done to you? Ni a iya sani na ban tab'a shiga rayuwar ka na takura maka ba amma gaba d'aya kafi son kaga ka kuntata min? Ka rabu dani ko zan samu in sha iska, ka fita harka ta!"

  Dariyar k'eta Ameer ya dinga yi harda kama ciki kafin yace "wow! That's more like it! Nasan za'a zo wajen, Suraj kenan, ka bari tukunna in na cimma buri na a kanka sai in sanar da kai dalilin yin hakan, and oh! Congratulations! Naji wai saura wata d'aya ka zama mijin Laila, yes! Ango, ayi dai mu gani" yana kai nan ya juya zai fita ,a cikin b'acin rai Suraj ya chafko wuyan rigar shi ta baya amma kafin ya yi wani abu Habeeb da Junaid suka rik'e shi

"Come on! Bar shi ya tafi, control your anger! Babu abunda ya isa yayi ka bar shi kawai "

Cire rigar sa Ameer yayi ya fita yana  fafa Suraj kuwa wafce hannun shi yayi daga rik'on da Habeeb yayi masa ya wuce zuwa d'akin sa.Haba Suraj ,meyasa zaka wani tada hankalin ka ? Bayan babu yadda zai yi in har bai samu proof ba? Ka bar shi kawai yayi ta yi! "
Habeeb kenan da yake ta k'ok'arin kwantar da hankalin Suraj. +

Mik'e wa yayi daga kujerar da yake zaune ya dubi Habeeb yace

"wai ma Habeeb what is the use of all this? Abun da muke ma bashi da wani amfani! Ban ga laifi a cikin auren y'ar talaka ba muddin akwai soyayya!  Miye aibun talaka? Shi kanshi mai arzik'i ba shi yayi kansa ba saboda haka yau zan kawo k'arshen wannan al'amarin kowa ya huta, zan je straight to Dad in fad'a mishi gaskiya,Laila y'ar makiyaya ita nake so kuma ita kad'ai zan iya rayuwa, babu ragi ba kari "

Murmushi Habeeb yayi yace "daga nan kuma se me? Iye? In ka fad'i hakan shi kuma se kayi tsammanin zaice 
"Wow! My son am very proud of you ! Go ahead and marry her ko???" Haka kake tunani?

Come on! Ka farfad'o Suraj! Dad ne fa! Don ka fad'a masa gaskiya babu abunda zai sauya sedai ma ya k'aru , kayi tunani, Ameer nema yake ka zama kullum Kaine a k'asa ,you can't let him win! Saboda haka babu inda zaka je stick to the plan kawai mu yi ta addua nasan Allah yana kallon zuciyar mu, ka kwantar da hankalin ka"

  Haka de Habeeb yayi ta shawo kan Suraj har ya hak'ura, suka maida hankulan su kan shirye shiryen bikin. Laila kuwa ba ranar da bazata je ganin Baba ba, su sha hira har ma ta raka shi kiwo , Zubaina kuwa kullum suna tare.

    Yau saura Sati biyu bikin Suraj da Laila amma Suraj yana chan Egypt zai taho da y'an uwan Mom , Sapna ma sun zo da mijin ta, Habeeb shi yake kula da sauran harkokin Suraj na gida kuma komai yana tafiya kan saiti.

    "Rasheed dole ne kazo, kamar yadda na maka bayani Mun fad'a masa kaine mahaifin Laila is like kana auran y'ar ka ne , koma me kake yi kawai ka zo ,tun ba yau ba kasan halin Abdul-malik, ba ma wannan ba ina so ka had'u da Laila akwai wani al'amari mai ban mamaki tattare da yarinyar" Abban Habeeb ne kan waya da k'anin shi Rasheed wanda Suraj yayi k'arya cewa shine mahaifin Laila.

"Ba komai in Allah ya yarda zan zo kuma zan halarci d'aurin auren"

Abban Habeeb yaji dad'i sosai ,yana katse wayar kuwa ya dubi Mom yace

"Alhamdulillah ,tun last three weeks mahaifin Laila ya bada ita amana, sannan gashi Rasheed zai zo yanzu kam bamu da wata damuwa sauran nasan yadda zan yi.

Kai kawai Mom ta jinjina tayi shiru kafin ta d'ago Abban Habeeb ya fice "I don't know if we are doing the right thing, bai kamata a gina relationship a kan k'arya ba I just hope we are doing the right thing."

******   *******    *******
Four days to biki.
10:49pm

    D'akin Suraj ya bud'e a hankali, babu kowa cikin d'akin se k'aran ruwa dake zuba a bathroom , a hankali ya shiga ciki ya d'an tsaya yaka k'are wa d'akin kallo kafin ya nufi k'ofar bathroom d'in ya murd'a Makullin ya rufe k'ofar sannan ya fara bud'e drawers yana bincike, bai samu komai ba ,ya koma wardrobe, har ya gaji da dube Duban sa zai fita yaga an murd'a hannun k'ofa
Shu'umin Murmushi yayi ya cigaba da tafiya, daidai bakin k'ofa akwai wata drawer a gefe ,digital camera ya gani ,Murmushi yayi ya d'auka ya fice ba tare da ya ja k'ofar ba.

   Buga k'ofar Suraj yake iya k'arfin sa amma tak'i bud'e wa, haka ya gaji ya jingina da k'ofar ,ganin ya kai Kusan mintina talatin babu wanda ya shigo yasa yaci gaba da buga k'ofar yanzu kam bugun ya fi na da

"Waye a nan? Open the damn door! "

     Sauk'o wa yake daga staircase yana dariya suka ci karo da Laila 
"Ah ah! Amaryar mu! Me kuma kike yi downstairs har yanzu bakiyi bacci ba? Oh na manta !! Wedding preparations ko? "

Rawa jikin Laila yake don ita Ameer tsoro yake bata ba kad'an ba, da sauri ta rakub'e ta gefen shi ta wuce , saida tayi nisa da shi yace

  "Amaryar mu! Na manta in sanar da ke ,ki duba wajen Angon naki don kamar fa ya shiga matsala naji se buge buge yake"

  Miyau Laila ta had'iye kafin ya k'arasa ma ta yi saurin tafiya don sam irin kallon da yake mata yana razana ta sosai.

  Dariya yayi mai k'ara kafin ya fice daga sashen gaba d'aya.

   Da sauri take tafiya ruwan sanyin da ta d'auko ma fad'uwa yayi bata bi ta kanshi ba ta wuce. Bugun k'ofa ta jiyo daga hallway d'in dake West wing don haka ta tuna maganar Ameer na cewa da yayi Suraj ya dan shiga matsala

A bud'e ta samu k'ofar d'akin dan haka ta kutsa kai ciki ,k'ofar bathroom d'in ta nufa tana k'ok'arin bud'e wa , saboda ta rikice da kyar ta iya murd'a Makullin k'ofar ta bud'e..

"Laila? Suraj ya k'ira sunan ta kafin ya ce "waye ya rufe ni? Ya baki kwanta ba har yanzu akwai wata matsala na?"

  "A'a na je in d'auko ruwa ne se na had'u da Ameer yace wai in duba ka shiga matsala"

Dariyar takaici Suraj yayi kafin ya ce "daman na sani! Muje in raka ki d'aki ki kwanta, kar ki k'ara fita a irin Wannan lokaci domin akwai munafukai iri daban daban, Ameer ba abun yarda bane ,na tabbata akwai dalilin zuwan shi, amma koma miye Allah ya fi shi.

Nan ya wuce gaba Laila tana biye da shi har d'akin ta saida ya tabbata ta kwanta sannan yayi mata sallama ya fice bayan ya ja mata k'ofa.......

Post a Comment for "YAR MAKIYAYA CHAPTER 11"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...