Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WATA FUSKA CHAPTER 6

WATA FUSKA CHAPTER 6

- - Post a Comment
WATA FUSKA CHAPTER 6
Sosai yasha mamakin yarinyar to ita kuwa menene da riqa ninke wannan fuskar ta d'aura *Wata Fuskar* akan kyakyawar fuska irin wannan? Dukda ya kula akwai makeup a kan fuskar amma ya tabbatar da cewar itace tawa makeup d'in kyau bawai makeup d'inne ya mata kyau ba, tana sanye da rantsattsen lace maroon color ta yafa mayafi fari dayake ratsin fari ne ajikin lace din, mayafinta asaman kafad'unta duka biyu ta zagoshi be sauka ba bare ya rufe mata jikinta wannan ya sanya duk a takure take, yakuma kula sosai da hakan murmushi ya sakarwa kanshi ya kula ya shagala sosai da kallon Nancy yana qoqarin kawarda dubanshi gareta ta juya masa baya nan take doguwar sumar kanta da aka linke kusan hudu aka mata daurin zara buhari ya bayyana, kafe idanshi yae akan sumar kanta ko shakka bayayi yanayin Nancy ya masa shi duk wannan qaton qugun nata be dameshi ba sam hankalinsa yatafine akan murmushin ta me qayatarwa daya tabbatar murmushin ne yake sada zuciyar sa da tata wuri d'aya suke tattakin had'ewa su tarwatse masa!!! Gyaran zaman sa ganin dayae ta tinkarosa gaba d'aya, runtse idan sa yae haka halittar tafiyarta take ya gano hakan sanda take nufar sa ko a hijan haka tafiyar ke nunawa qafafuwanta ba tsaye suke ba miqe sundan bole aqasansu irin bow legs din nan sedai ba sosai ba kamarma heeps din dasuke shirin mata yawane suka miyar da qafafuwan haka, miyarda kallonsa yae zuwa ga fuskarta Allah ya mata arziqin goshi kam qatoto ma kuwa bazece yawa fuskar kyauba muniba amma bako shakka be wani yi mata kyau ba sedai yarasa ata ina kyawun ke fitowa to? Lumshe idon sa yae ya furta a sarari "Daga cikin ruhin mamammalakiyar fuskar ne bako shakka" Zuhair ya miqa masa kyakyawan kallo yace "Kaima kana kallon wacce yarinyar ne ko, ban taba ganin bow legs sunyi kyau ba se nata dukda ba sosai suka bole ba amma kam ana gani tangaram, sedai kalli fuskar tsarki ya tabbatarwa ubangijin daya qera wannan halittar" kan Maheer ya lalubo wata kalma harta qaraso da yaron masu rarraba abinci a bayanta dauke da tray tana murmushi ta nuna ma yaron table tace " yaa Maheer ga abinci kui hakuri se yanzu yake isowa ina wuni" yau kawai Maheer yaji kalmomin bakinsa sun masa nauyi ya kasa furta koda qwaqwaran kalma dayace se murmushi yake zuba mata itama haka aka gama jere abincin tace "Yaa Maheer idan kana buqatar wani abun call me plss, islam fa banan na ganku atare ba" kallon wurin datake yae bema san yaushe ta tashi a wurin ba, murmushin sa kawai yake narka mata,kanma yace wani abun islam ta dawo, harara ta wurga mata "Danla ni muje ki tayani nuna wa masu rabon abincin nan baqin mu na musamman Allah a tsauwale nake da mayafin nan, tamkar zan runtuma ihu" Dariya tayi "To ai kuma wlhy kinyi kyau qawata kamar bake ba, babu ma wanda ze yadda kece Nanuwan Baba iro" dariya suka kwashe dashi dukkansu kan su juya a tare yanayin tafiyar Nancy yake kallo ata baya yana murmushi........ Mintsilinta lslam tai tace "ke mazari a hijabi yau banga kina rawar ba" Murmushi tae "A wannan taron zanyi rawa Islam? Kumama babu sutura ajikina fa dan wannan mayafin wlhh gwara na wurgar ma nake gani nikam" "Amma kinsan beyiba kice bazakiwa ummul lik'i ba, koda na 2 mns kiyi, kina sani sarai mutanen nan kallon maqiya suke muku, plss ki nuna musu kin fisu murnar bikin kije kiyi rawa abinki, bafa komai bane ba yanzu an wuce wannan abubuwan dakike Nancy" murmushi ta sake yi a karo na barkatai "Zanyi liqin mana rawar cedai bazan yiba" haka suka wuce suna wannan zancen,tayi likin amma batai rawar ba sam har aka tashi a wurin bikin...... *********** Yayar Maheer sam ta kasa aminta da aurensa da islam yayinda mahaifiyarsu tace sam baza'a takura masa ba, idan bazasu tayashi da addu'a ba tokuwa su bari kawai sabida ita bataga dalilin fasa yin auren ba dan kawai ana taqamar yarinya bataji, a bincikenta kaf bataji inda akace yarinyar ta tab'a barin gidansu zuwa wani wurin domin yin zaman kanta ba, in ko hakane meye nasu na dirza rashin mutunci har suce bazasu bari ya aureta ba, qaddarace ta rayuwa kuma wlhy kowa ze iya afka mata" Badan sunso ba suka hakura tare da sanyawa abun albarka....Anty Nasara itace babba kuma itace fitinanniya acikinsu sam ita bawai dan ance yarinyar tayi yawon tazubar ba kawai batason talakawa, yanda friends dinta ke bata girna ace auren Maheer dataci buri zasuyi da er matsiyata qyaure kofar gidansu yarinyar ance basuda shi se fatar buhu a irin wannan gidan zasukai baqin su ko en rakiyar daukan amarya da en kai lefe? Gaskia da sake wai an baiwa me kaza qafa.....bari yaje amma taga maheer din! STORY CONTINUES BELOW A parlor shi ta sameshi zaune ya d'aura k'afarsa d'aya kan d'aya ta kalleshi da kyau ta murtuqe fuska alamar ba wasa...shi d'inma tashi fuskar ya had'e sosai "Maheer mesa zaka mana haka?" Kallonta ya qarayi "Name fa?" "Kamar yaya name? Ita muna danace kaje ku shirya meta maka dazaka d'akko mata er gidan matsiyata kuma tsohuwar karuwa kace mana ita zaka aura, banda kake mara tunani ma menene alaqarka da er talakawa?" Takaici sosai ya kama sa harya gaza furta mata komai ganin haka taci gaba "Gaskia maheer da sake, ka janye wannan zancen auren idan auren kakeso kaje mana ga muna tun yaushe take dauke sa sanka aranta, yarinyar er masu dashi wannan ma ai ko kayan gida sesu gagara yi" yanzu kam mutumina ya sosu, ko ita da kanta daya d'ago ya kalleta seda taji wani iri cikin takaici yace "Danke zaki zaunamun da matar zaki gayamun wacce ta dace dani? Haba anty Nasara yaya da iliminki da komai zaki gagara gane cewar da arziqi da talauci duk na Allah ne? Da Allah ya had'aki da miji me arziqi mahaifinki ma me arziqi se akace miki wayonkine ko dabararki ya baki? Kokuma aa sabida kawai Allah yafisanki da sune ya barki ajikin daula su kuma akasin haka, ki sani wlhy bazan taba auren muna ba sabida ba zab'ina bace zab'inki ce islam nace inaso kuma inshaa Allahu kodan tsarkakkiyar niyyar danake da ita akan islam Allah ze bani aurenta, magana ta qarshe kuma gaskia karki qara kiranta da sunan karuwa cox ni banga wannan sunan a tattare da ita ba, salihatul Islam shine asalin sunanta incase baki san sunan ba" Harara ta wurga masa "Au tunkan yarinyar tashigo ma harka soma mun rashin kunya Maheer abinda baka tab'a yiba lallai wannan yarinyar ga alama da bokaye ta had'aka" Miqewa yae "Anty nasara zanje kano ne yanzu nikam, akwai bikin friend dina yau ake dinner friday kuma kinga goma ta gota" be jira cewarta ba yabar gidan ita kuwa tashiga neman yanda za'ayi tayi maganin d'an banza..... ************** D'aya daga cikin jallabiyoyin da Maheer ya baiwa Nancy ta saka me ja din, tayi masifar karb'ar ta ta sanya takalminta ja mayafin abayar ma jane, tayi asalin kyau dukda kwalli ne kurin a fuskar nan se powder da red lips stick...... Sha biyun na ranar akai walima sabida suna so suje makeup din dinner da wuri yasan ya suka saka walimar da safe da wannan rigar taci walimar ta, ganin rigar ba wata me matsewa bace ya sanya tafita zuwa karb'o d'inkinta na dinner da ita, A daidaita take nema gashi so take tayi taje ta dawo kar su tafi gun makeup su barta amma shiru babu alamar adaidai tan tamkar anyi ruwa an d'auke ma gaba d'aya........motar data sha gaban tane yasa tadanja baya tana yamutsa fuska har dimple nata seda ya lob'a loda glass yaje qasa setaga islam da Maheer "Banza da kin zata saurayine kimai halin ko, to nice ina zaki?" Murmushi tayi daya sanya Maheer lumshe idanuwan sa ya saukesu a kanta a hankali... "Bauchi road zanje shagon su Munir, kayan dazan saka dinner suna cen kuma 4 zamuje makeup kinsan wannan" Sauke ajiyar zuciya tae " kinsan me dama gidanku Maheer ze saukeni mu tafi makeup d'in a tare, amma nifa wanka nakeso inyi, abinda ze faru bari na sauka na qarasa da qafa tunda ga gidan cen ke kuma sekuje yakaiki ki karb'o ku dawo, kannan kinga nayi wanka semuje makeup d'in atare" Bataso hakan ba amma tasan Islam da wanka tamkar er agwagwa bazata yarda wai ta bisun ba dole ta fito ita kuma ta zauna agaban motar, shidai banda islam datace dashi "Honey bye" ya sake mata murmushi tare da d'aga mata hannunsa bece kanzil ba, seda suka lula kan titi yace "Ina wuni?" Wata iriyar kunya ce ta lullub'e ta taji tamkar ta nutse da qyar tace dashi "Kayi hakuri Yaa Maheer senaga kamar mun gaisa" be kula taba jin yayi shiru ya sanya ta d'ago ta kalleshi sosai ya qura mata ido sekace ba tuqi yakeyiba ita yake kallo....kallon nashi ya nayar kan titin batare dare dayace qala ba itama shiru tae ya mata qwarjini a takure take jinta matuqa STORY CONTINUES BELOW "Rigar nan tamiki kyau fiyeda tunaninki" ta tsinkayi muryar sa yana fad'a.... Murmushi tayi "Nagode yaa Maheer, yaya nane ya siyamun ita dama yasan zatamun kyau" Be zaci tanada barkwanci haka ba amna beyi magana ba se murmushi dayakeyi......har suka isa shagon Babu wanda ya qarayin magana acikinsu,fita tae bayan ya tsaya data nuna mai wurin tace tana zuwa........koda taje telan ya fita yakuma rufe durowarsa dayake ajiye kayan daya karba, abokin aikknsa kuma ya tabbatar mata indai kayan data kawone ta karbi wani ranar alhamis to kuwa be qara d'inka ko d'aya ba aciki, seda taji kanta ya sara mata ga wayansa a kashe, koda taje motar kuka takeyi juyin duniya kuwa Maheer yayi ta gaya masa menene amma se kukan take tamkar wata yarinya qarama.....head ma ta siya kalar lace d'in takalmi haka, har yalolon mayafin dazata yafa dukta siya d'ankunnayenta ma haka gashi uku saura. Shidai ficewa yae daga cikin motar ya nufi shagon bayan daya tambaya suka mai bayanin komai bece komai ba se godiya daya musu ya juya.....Da qarfinsa ya figi motar "Ki dena kukan nan haka, sekace wata jinjira tela seya sanyaki kuka, bari muje da akwai lace danake da a gida na siyane dama in sanya a lefe amma zan baki, nasan inda zasu miki d'inki cikin awanni biyu" "Nibase ka bani ba, ka barni kawai nafasa zuwa bikin, harfa head da takalmi da komai na siya kalar lace din shine zasumin baqin ciki" murmush yae sekace wata jinjira ji yanda take shagwab'a ya fada a ranshi, a fili kuma be kula taba yaje gidan nasa ya shiga ya d'akko, ya dawo ya tuqa motar suka dauki hanyar zabira mall ....Appareal sukaje ya kira babba acikin telolin yace dashi "Dinkin riga da skirt nakeso acikin awanni biyu zan samu?" Kallonsa telan yae "Yallab'ai sedai idan zakayi doubling kud'in" "Nawa kukeyine?" Ya buqaci sani "Dubu shida muke dinka set, kaga 12k zaka bayar amaka express kenan" zaro kud'i yae a aljihunsa ya miqa masa sunkai 15k yace maza ka aunata ga 15k nan, kuma yae kyau d'inkin nanda qarfe biyar da rabi zanzo na karba" murmushi telan yae ya hau godiya kana suka shiga daga ciki macen dake shagon ta aunata, ya karbo guntun lace din ya dawo mota suka tayar "Ki kaini kasuwan da kuke siyan Ashoeken zan siya miki da komai kinji" kallon sa tae "Ka bari wancen sena hadasu a haka kawai d'awainiyan seyae yawa" B'ata fuska yae ganin haka ta nuna mai, laylac purple ne touch up din dake jikin farin lace din haka suka siya komai suka biya MR.BIGS sukai take away, tawa Islam waya take sanar mata komai inda tace su hafu gun makeup sukam sun wuce abinsu..... Se after 6 d'inkin ya kammala, har lokacin suna nan atare, bayan angama taje gidan ta tarar na kowa, yace ta komatsa tazo haka tafito sanye da dinkin daya matuqar karbeta ya kaita wurin makeup daban yace tajira ya shirya yazo d'aukarta ........ ******** Shida kansa data fito be gama shaida ita bace ba, tayi asalin kyau na musamman makeup d'in babu wani hayaniya amma tayi kyau sosai, bud'e motar tae tashigo qamshin turaren daya siya mata d'azu ya daki hancin sa seda ya lumshe ido....beyi magana ba wayanshi ya soma ruri d'agawa yae "Baby" shine abinda ya furta a d'aya b'angaren "Kiyi hakuri gashima na d'akko qanwata zamuzo" shagwab'e fuska tayi "Honey kowa ya gama kallemun kwalliyana baka zoba ga angon ma naji yana tambayarka" "Kiyi hakuri Babyna, ina hanya yanzu zanzo naga kwalliyan zanma bada kudin wankan tunkan nagani na siya naira goma ina zuwa zam baki goman ki lakadan" dariya ta bushe dashi sosai yabata dariya ainun......Lokaci d'aya Nancy taji ba dad'i amma bata nuna ba sabida batasan dalilin jin hakan ba "Kinyi kyau Hafsat" kallonsa tae tana murmushi "Kaima kayi kyau yaa Maheer sosssai kuma banma ganekaba" Kallon ta ya qarayi,ita d'inma shi take kallo dukkansu suna murmushi ya d'age mata girarsa d'aya abinda ya sanya ta kwashe da dariya sosai har wushiryarta ta bayyana, shima qasa qasa yake dariyar yaja suka lula... Tun a qofar shiga wurin daze sadaka da hall d'in suka had'u dame d'aukar hoto nan take ya soma d'aukarsu hoto....tun suna kaucewa har suka tsaya ya musu haka suka doshi hall d'in bamewa wani magana amma murmushi ya kasa d'aukewa a fuskokinsu haka suka tunkari hall d'in aiko suna shiga kallo ya koma sama sabida d'aukacin mutanen dake wurin kallon su suke acikin dakakkiyar farar shadda maheer yake dinkin babbar riga yasha kyau ita kuwa farin lace ne me ratsin laylack purple tasha kyau, se haskawa suke tamkar wasu amarya da nagon me hoton da kanshi ya zata wasu ango da amaryar ne aiko ya soma danna musu pics hatta mutane da wayoyinsu se pics suke musu wasu basumasan dasu ba......islam qirjinta se dokawa yakeyi ganin shigowar su kasa hakuri tae tazo da sauri ta riqe hannun maheer murmushi ya sakar mata yace "Na matsu azo tamu dinner nanda jibi baby, duk naji tamkar ace nidakene, tajiyoshi sosai dukda waqar dake tashi ta saki murmushi "Allah ko?" Ta fada ya dage mata gira suka sanya dariya Hafsat kuwa harta sulale wurin Ummul dataga tana mata aamar tazo da hannunta... Yaune karon farko na had'uwar hannayensu wuri d'aya, zame hannunsa yae ya kalleta yace "Ba kyau kina had'e hannunki da nawa, tukunna dai" hannayenta ta had'e wuri d'aya "Am so sorry honey rud'ewa ne nayi dana ga kyawun dakayi" bece komai ta jagoran ceshi zama wurin da aka keb'e don abokanan ango da qawayen Amarya,kusa dashi ta zauna yayinda Nancy tazo itada khadeeja ita kuma ta zauna kujerar dake fuskantar tasa batare dama ta lura da shi ba, har kad'a kanta take sabida waqar na ratsa ta soosai😍😍😍 shi kuwa gogan ya shagala da kallonta har seda islam ta kula da hakan, deejah ce ta zungureta "Banza da zaran kinji kid'a se rawa, ikon Allah gaki saliha har saliha inda Allah ya rageki d'aya duk inda kikaji kid'a sekin raya" Dariya tayi ta dauki samosa dake gabansu acikin small chops da aka ajiye musu ta kai baki ta gutsura ta soma taunawa a hankali "Karkace kansa yae yana kallon yanda gefen kuncin ta na dama ke lob'awa idan tana chewing ramin is do deep gashi da tsawo shisa koba murmushi take ba sekaga kamar tana murmushin......islam kuwa kasa hakuri tae tace da Maheer " Honey mu koma sit na baya am not confortable anan" kallonta yae ya matso daf da kunnen ta ya rad'a mata "Kishine kawai kinga en mata se kallo na suke, karki damu duk kin fisu kyau kuma babu wacce nakeso seke, ko gani kikai idona ya sauka kan wata ni kece a idona,kuma kece a raina kinji?" Murmushi ya sub'uce mata ta saki murmushin tana wani mammaqale masa... Hafsat kuwa ta kaiwa moctail daya cafka ta soma tsotsa seda ta zuqi yafi rabi sannan ta dire ta miyarda kallonta ga khadeeja "Ina islam ke?" Dariya tae "Banza kinzo kina kwad'ayi ba gata a gaban ki ba" kallon gabantan tayi tana murmushi tace "Kai lallai ma wlhy islam ke er Air ce tunda kikaga yaa Maheer niko oho ko, zaki nutsune idan ma miki fushi" Dariya tai tana qoqarin yiwa Nancy magana aka qara muryan waqa dole tai shiru cox bazata iya ihu ba.... Waqar hausa ke tashi me taken Hasashena ya tabbata...sosai Nancy ke qaunar waqar wannan ya sanya ta kasa hakuri ta zari hannun khadeeja sukai cikin filin rawar a tare, wannan ne ya d'auke hankalin Maheer zuwaga islam bebi takan masu rawar ba sabida an cika.....suna hira aka sauya waqar zuwa waqar Arashi naso aikam se sowa suka jiyo, islam ce ta miqe Honey bari naga meke afkuwa acen wurin yasin dukda kake ganin nancy haka nan ne kawai Allah ya rageta yanda kasan me aljanai inda taji kida tokoda d'an yatsane seta taka rawa" murmushi yae "A sauka lapia to" juyawa kawai tayi taje ta shige cikin sahun gaba dayike duka a zaune ake masu rawar ne kawai a tsaye, to sekuma masu video dake gefe wasu har a wayoyin su......maheer ma juyawa yayi bil haqq Nancy da khadeeja se step dance skeyi duk inda aka sare ko aka karya a waqar ta arashi se sunyi murmushi ya sub'uce masa aranshi yace wannan ustazancin na Nancy yazo da wani salo irin na raini ma, kalli yanda take rawa har tana wani fari da ido wakar ma akanta yake, tsintar kansa yae dasoma yin video step dance da suke acikin wayar sa daga wurin dayake ya juyo gaba daya ya, dama sune a jerin gaba amma sit din dayake yana da nisa shisa islam ta koma gaban sosai ita kanta video take na rawar dasuke seda aka tsayar da waqar tukunna suka sarara wa kansu sukaje suka zauna,yanzu kam bata zauna da Maheer dan ita harga Allah ta manta dashi ma a wurin seshi da duk motsi yana kanta, aka qara kiran ango da amarya da abokanan ango da abaokanan amarya sui rawa haka suka jeru mata layi daya mazan ma haka, akwai wani gasa da ake na dance for the groom and dance for the bride qawayen amarya su mata na ango su masa aga wayafi iyawa,akan bada kyauta wa wanda yaci idan ango abokanan sa sukaci shi za'a baiwa in kuma qawayen amarya sukaci to....anyi anyi islam taqi ta shiga ita dai wai kunyar Maheer takeji ita kuwa Nancy ba ruwanta tunda ta soma rawar setaji ba kamar ranar kamu ba duk tadena jin kunyar beside acewarta ingaka fuskarta zuwa sunday anyi final....... Shida kanshi Maheer Bason yin rawar yake ba amma ya zeyi? Ameen shi ya saka a gaba akan lallai seyayi bashida zab'i mc ke zab'ar wa koea partner dazasuyi gasar anyi yakai mutane bakwai se a na 8 MC ya nuna maheer da kuma Nancy......tafi wurin ya d'auka har suna sowa akan zab'in na mc wasu daga ciki na ihun basu yarda ba a qarshe dai dukkaninsu kasa rawar sukai, shidai Maheer ya kasa rawar ne ganin yanda Islam tae kici kicin ita kuwa kunyar mutanen dake wurin dana Maheer ya hanata rawar, haka aka tashi a gasar maza suka cinye Bikin ba qaramun qayatarwa yayi ba zan iya cewa yafi sauran duka events da akayi.....Maheer da kanshi ya ebi su islam zuwa gida tare da khadeejah da Nancy, juyin duniya da shagawb'a Islam tayi amma Maheer ya kafe akan ita ze fara direwa gida tukunna sabida unguwarsuce cikin gari Nancy kuwa basuda nisa, badan tasoba ta hakura da haka ko sallama batawa Nancy ba ta shige ita kamma vata kulaba ta mance se dannan wayanta take....bayan fitar islam a motar ta dawo gaba ta zauna haka yaja suka tafi jugum jugum dama khadeeja gidansu take kwana wannan ya sanya suka d'auki hanyar gidan kai tsaye ya tsaya Flamingo ya siyan musu kaza da chips daganan suka lula hanyar gida, haka kawai daduka tsaya se khadeejah ta fita Nancy bata ko motsa ba deejah dai ciki ta wuce abinta,kallon ta ta miyar zuwaga Maheer "Yaa Maheer thank u so very much for everything i reallg Appreciate it, Allahu yabar zumunci ya qara bud'i ya kuma jiqan iyaye, Allah ya share maka hawayenka kamar yanda ka share nawa hawayen" Murmushi ya sakar mta dukda babu watacciyar haske yace "Ba komai ai yiwa kaine, yanzu se gobe kenan?" Murmushi itama tame kan tayi magana call yashigo wayarta tana dagawa islam tace "Frienf d'an bami deejah mana na tambayeta wani abin" bata kawo komai a ranta ba tace "Ki kira wayarta ta shiga cikin ni ina waje" qirjin islam ne ya doka tace "Waje kuma, after 11 fa keda wa?" Murmushi tae tamkar tana ganin ta "Nida yaa Maheer ne, na tsayane na masa godiyar d'awainiyar dayamun yau" tsaki Islam taja ta kashe wayarta kallon wayar Nancy tae da mamaki amma batace da Maheer komai ba, sallama ta masa ta fice a motar, taje tayita kiran islam bata dagawa tarasa dalilin wannan iskancin amma ba komai ruwanta. *********** Maherr dayaje gida ya kintsa wuraren sha biyu ta gota seya kira Islam so biyu bata d'aga ba, haka kawai yaji yanason yaji muryar Nancy kai tsaye ya juya akalar ntwrk dinsa zuwaga lambobin wayarta, ringin biyu ta d'auka "Yaa Maheer ka isa gida lapia?, kayi hakuri ban kirakaba na gajine wlhy" murmushi yae "Lapia lau ni gashi nakira ai, ya gajiya yaukin gaji ko?" Murmushi tayi me sauti "Na gaji wlhy duk jikina se tsami yakemun" "Ayya sannu kinji dear Allah ya baki lapia, dama nacene barin tab'oki,yanzu kin yi shirin kwanciya?" Gyaran kwanciyarta tae "Ea na kwanta amma na gagara bacci ko motsinsa banaji".... Hira suka hauyi sosai ita kuwa islam ganin call din Maherr ya sanya ta kira back amma shiru be dagaba se dogon call waiting haka ta juya tana kiran Nancy nanma call waiting, lokaci d'aya ta shaqa sosai wani azababben kishi ya bijiro mata na bazata ta gigice tana neman haukacewa Jin alamar kira nashiga wayar Nancy ya sanya Maheer yace " Hafsat wake miki waya cikin daren nan inajin qarar shigowar waya" tayi mamakin shi amma setace "Islam ce dayime nakirata bata daga ba shine take ta kirana ko zakamun uzuri injita" ya gano bincike take masa amma seya basar "Ba damuwa muyi waya da safe, promise that u'll call me early in d morning 2mrw" da murmushi tace "Allah ya kaimu goben zan kira" koda takira islam bata d'aga ba. A wannan daren islam ta gama shirin yaya zatayi da Nancy bazata bari wannan yarinyar tamata qwacen Maheer ba zata iya yin komai akansa!!!!1 ************** Washe gari asabar akayi wuni dakuma kai Amarya agidanta dake sama road en daukar amarya sun watse en mata sun dawo gidansu amarya amma babu Nancy babu labarin wayarta.....ankira layin har an gaji, kowa seyace rabon daya ganta tunkan isha!!! Wasa farin girki haka aka dinga neman Nancy har safe babu ko labarin inda take!!!. Maheer besan meke faruwa yana zaune a parlor gidansa babu abinda zuciyar sa ke masa se azalzalarsa akan yaje yaga Islam beson fushin ta ko b'acin ranta ko kadan, yayita kiran layinta a kashe gashi gaba d'aya ya damu, Maheer yana qaunar Islam sosai baso na wasa ba......breakfast kurun yake jira ya tafi ya qakara, whatsapp nashi ya shiga yaje gun status kai tsaye.....acen yaga wani friend dinsu ya saka rawan dasu Hafsat sukayi jiya beso hakan ba ze mata fad'a sosai akan rawa, tanada kamun kai koyaya takeson rawa tasan inda ya dace tayi rawar shine yafi,acikin maza bayaso yanzu gashi video din yana yawo hakan aibe kyautuba tsaki yaja a ranshi yace "Nikuma awa?" Wuce status d'in yayi sekuma ya miqe tsaye da sauri kamar wanda aka tsikara ya qara qurawa picture din ido, hoton sane shida ita anja arror akusa da ita wai ana cigiyarta tun jiya da dare daga kai amarya kowa ya mata shedar batada yawo an jajje gidajen en uwa ba'a same taba.......da jallabiyar jikinsa ya fita daga gidan jikinsa har rawa yakeyi b'ata fa, jiya ya ganta wurin kai Amarya to ina tashiga? Shida kanshi ya kula da rashin ganin dabe mata ba sanda ake qoqarin barin gidan amaryar akai en mata gida har layinta ya nema be shiga ba...... Kai tsaye gidansu islam yaje anan yakejin wai tana kwance babu lapia tun shekaranjia.....har ciki ya shiga suka gaisa yake gaya mata aikuwa ta nemi cutar dake damunta ta rasa, se kuka tare sukaje gidan su Nancy islam se kuka take masa amma hankalinsa baya gunta, koda suka je khadeeja ce me musu bayanin "A tare muka fito daga cikin gidan Amaryar fitsarine ya mayar dani da gudu inyi kafin mu dawo, na barta aharabar gidan...mune farkon fita gaba daya amma sena samu matsala danaje fitsarin nashiga toilet setai locking ga d'akin dana shiga babu kowa acikinsa haka nayita kici kicin na bude ga wayana na bata riqo yana jakarta qaramun wayana dake hannuna ba kati haka naita jiran tsammani da qyar na bude qofar koda nazo ba kowa shisa ban nemetaba na hau adaidaita kawai na dawo, neman wayana dana bata riqo ne ya ankarar da mutanen cewar ba'a gantaba a wurin sam!!!! Ta qarashe maganar tana kuka hadr da toshe bakinta da hijabin ta " tundaga lokacin wayanta da nawa aketa kira basa tafiya ko nan da cen, Mamanta sumanta biyu muna zargin kidnerpers dinnan dasukai yawa ne a gari" Shiru Maheer yae yana nazarin kalamanta kanshi yayi zafi yarasa ma mezeje ga islam se qara d'aga masa hankali take tana faman kuka... ************** Nancy se zare iso takeyi tarasa gane inda take bayan ta farka, hankalinta ya matuqar tashi ganin kanta datae acikin qungurmin daji ita kad'i kuma a d'aure jikin icce, takasa gane shin mafarki takeyi ko Gaske ne......innalillahi wa innah ilaihirraji'un itace kalmar dataketa nanatawa a bakin ta, bilhaq dai ta gano tana cikin musiba bazata iya tuna komai ba se ganin wasu maza suna tambayarta ko nane gidan Amaryar Aminu tace e shikenan seta wayi gari ta ganta a wani d'akin tare da wata mace kantae wani yunqurin kuma tarasa ina take se yanzu, waiga wa tae gabas da yamma kudu da arewa bataga alamar ko kadangare a jejin ba, babu alamar gari a gaba bare a baya, wurin yayi tsit se ita kadai runtse idanta tae ta soma rero duk wata addu'a datazo bakinta haka ta wuni har yamma ga jakarta a kusa da ita an ajiye mata amma bataza iya kunce kantaba bare ta dauki jakar ko zataga wayarta!!! Wannan shine tashin hankali wanda ba'a saka masa rana.....wata irin razananniyar qara ta saka sabida ta gaji ga yunwa ga qishiruwa, ta qosa ta ganta a kunce, babban abinda yafi daga mata hankali shine rashin yin salloli idan zata irga da kyau tunjiya da aka d'akkota rabon datae salla yo batamasan inda kanta yakeba bare tace zatayi salla.... Adu'ar taci gaba dayi ganin ihun ba abinda ze fitar da ita bane......duhu ya sauka se wannan lokacin tasoma jin kukan tsuntsaye alamun sun dawo daga inda suka tafi qishiruwa takeji sosai tamkar zata mutu, yawun bakinta ya gama qafewa wani duhu ta gani tsaye agabanta abinda , a hankali ta d'aga kanta sama domin kallon meye anan ta sume bayan ganin abin.... ************* Maheer ya rasa dalilin damuwar sa akan Mancy, ko Ummul bata cikin nutsuwa kullum setayiwa Ameen kuka, ango ya kasa gane kanta, mahaifiyar Nancy tana nan an miyarda yaranta Niger amma tana nan, gashi an koma skul amma Nancy bata nan yanzu tsawon wata d'aya kenan da b'atan Nancy amma bako wanda yaga sanda wani abu ya sameta, Islam kam an gama ramewa an lalacewa akan rashin Nancy indai ka santa to kallo d'aya zaka mata ka gano cewar tana cikin rashin kwanciyar hankali da nutsuwa na rashin Aminiyarta school d'inma tana zuwane kawai sabida babu yanda zatayi, auren ta kuma saura sati uku gaba d'aya ji takeyi batason auren nan kwata kwata, indai Nancy bata nan gani take auren ma gwara babu, da farko ta dauka kidnappers ne har tana shirin kudaden data tara na yawon duniya take shirin siyan kayan daki ta bayar a hada a karbo ta amma segashi shisu basu kiraba...tafi qaunar yau ace gawar Nancy aka gani tasan mutuwace akan hakan..... Maheer kam acikin ranshi yakejin azabar daya kasa bayyana ta sabida babu wata alaqa ta jiji a tsakaninsa da nancy dazata sanya ya kasa mancewa da lamarin ta ya bita da addu'a kawai, wani zubin har abinci yake kasa ci,abu mafi bashi mamaki shine yanda yake mata kuka duk sanda ya tunata seyayi kuka kenan kuka ya zame masa d'abi'a kullum sabida da ita yake kwana yake kuma tashi baya manta ta wanda ya sanshi ma yasani walwalarsa ta ragu sosai... Yauma kamar kullum kwance yake acikin bahon wanka an zuba flowers masu tsananin qamshi acikin ruwan dayake wanka dasu, ya kasa koda mosti bare yae wanka hawaye yakeyi yana tunanin Hafsat metawa mutane? Dawa take fad'a?, police sunyj shiru da binciken inda ta shiga to yaya hakane?..".. Kallon Anty reeda anty nasara tae tace "Wai matar tasa tana nan ne? Kike zancen an bugo IV?" Kallon ta tae "To anty ina zataje tana nan mana?" Biki fa saura sati biyu ko d'inkuna bamui ba, Umma kuma tayi zancen kayan lefe" Zaro wayarta tae jikinta har rawa yakeyi, ta nunawa Reeda wani hoto "Wannan dake tare dashi wacce suke ajikin wannan hoton atare wacece ita to? Nasha itace amaryar ai?" D'an murmushi tae ."Ba wannan nasani ba bari kiga wacce ze aura damukaje gidansu kina dubai" nan take ta nuna mata hoton islam jikin ta kuwa har rawa ya somayi ita anty nasaran ta kalli fareeda cikeda tsoro tace "Nashiga uku sis, wlhy nayi hauka da shirme kuwa?" Qura mata ido tayi tana mamakin kalamanta kantace "Ban fahimcekiba sis?" "Kinsan na sanar dake banason auren nan,nakuma kira Maheer namasa magana akan ya janye yaqi, shine danaga wannan pic a social media nace to lallai itace, senawa er akuri sending lokacin zanje umra daganan na wuce dubai, tofa shine dana tura mata nace a sace yarinyar a tsoratar da ita sosai akan maheer, ni tunda tace ansace yarinyar ban qarawa hajiya maganar ba, jin anyi shiru ya sanya nayi tunanin yarinyar ta janye ne shisa banbi ta kaiba, amma bawai sace yarinyar dawowar danai shekaranjiya hajiya azumi ke gaya mun wai taga fuskarta ta farka musu bisa kuskure shisa ta sanya aka kaita jejin amanawa wannan mugun jejin aka manna mata igiya suka jibge mata kayanta anan, wai idan ta mutu ko oho basu suka kashe taba, to nima banji dadin hakan ba amma senace bani nayiba ko lahira banida laifi" Mamakinta ne ya sanya Reedah miqewa tace1 "Anty Binta yaushe kika canja? Wannan wane irin mugun tane fisabilillah? Koda islam dince yanzu keba ruwanki kenan? Idan da ace Meerah ce zakiji kwanciyar hankali tana wannan jejin? Karfa ki manta ko masu shiga ciki seda tsafe tsafe haba anty Nasara wlhy baki kyauta ba, qyamar dakikewa talaka hartakai kiga kamar idan ya mutu ruwansa shisa kiyashi duk d'ayane a gunki? Lallai ma Anty" shiru ta danyi kantace "Karkimun raini wayau Fareedah kinaji ba" zama tayi ta dauki wayarta tawa kanta sending pic din ta wtsapp sannan batama mata sallama ba ta fita..........

Post a Comment for "WATA FUSKA CHAPTER 6"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...