Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WATA FUSKA CHAPTER 3

WATA FUSKA CHAPTER 3

- - Post a Comment
WATA FUSKA CHAPTER 3
Zaman makarantar haka ya kasance cikeda wata iriyar shaquwa tsananin maheer damuka islam, kullum suna tare kokuma idan basa tare to kuwa suna nan maqale a waya amma Maheer betab'a furtawa Islam kalmar so ba....yayinda Nancy ke matuqar shan wahalar soyayyar datake wa Maheer wacce ta tabbatar koda babu Islam baze so er qauye irin taba, kullum setayi kukan rashin sa da soyayyar sa datake neman illatar da ita, yauma kamar kullum tana zaune yana zuba lecture yana musu sallama akan se sun dawo hutu tunda sun kammala exams dinsu yau, ji tae wani zazzafan zazzab'i ya mata dirar mikiya, koyaya zata iya jure rashin Maheer na watanni uku? Koyaya zataji bayan rabuwar da zasuyi? Ganinsa kawai yakan saukar mata da nutsuwa sosai azuciyarta mesa zuciyarta da gangar jiknta basu mata adalci ba akan soyayyar Maheer? Ina ita ina shi? Ko bayan talauci batada wani gata a duniyar nan se Allah.....haka aka watse kowa ya fashe hannunta Islam taja1 "Muje office d'in sir maheer yace na sameshi office" badan bataso ba amma tasani sabon ciwon zuciya kawai zata samu sabida yanda Islam ke wani karairaya tana zuba shagwab'a kuma Sir Maheer d'in yana biyeta abin sam ba'a magana...... Kallon kallo suka tsayayi na en daqiqu yayinda kan daga bisani Maheer ya sauke ajiyan zuciya yace cikin zolaya "En mata lapiya kinga fine boi kin bini da kallo se ince se an biyani kallo na da akeyi" shagwab'e fuska tae "Allah ni Sir kaine kake kallo na, kuma kasan nafika kyau" murmushi yae yace "Am dena yayin lukutayen mata ne silinda nake so kinji naga alamun so kike ki nanuqemun yanzu kuma meya kawo ki" murmushi tae ta zauna kusa da Nancy datae zaune tae quri da ido tana kallon su, kamo hannunta tae tace1 "Dan Allah Nancy nida Sir wayafi kyau? Kuma ina agabanki yamun waya kafin mushiga exams cewa na sameshi office" murmushi tae aciki niqafin ta tace cikin muryan ta me sanyi "Qawata kin fishi kyau shima yasani ai, kuma mu bamuce munayi dashiba sadakin mu tsadanr dashi baze iyaba" kallonta yae karo na farko kenan dayaji tayi magana da raha kuma me tsayi har haka yace "Aini banasan lukutar mace, aje cen akai kasuwa" dariya suka saka dukkansu se yau yajiyo sautin dariyarta daya kusa kashesa akan yanda yaji yakeson yanayin dariyar ta cikin jan ciki murya can qasa qasa me taushi, kawar da wannan tunanin yae,cen kuma ya tsinkayi muryan ta tana fad'in "Dama Lukutaye seme mota kaiko taya baka dashi, bana baiwa talaka qawata" dariyar suka qara sakawa dukansu ya zauna kana yace yana kallon islam "Issy baby nifa daga nan se kano, shisa nace kizo mui sallama, inshaa Allah yau kano ta dabo zan kwana, tunda aka soma exams banje naga umma na ba zumud'i nake" Ga mamakin Nancy Qwallah tagani a idon Islam harya fara silalo mata ta tsinkayi muryanta tana furta "Haba mana dan Allah, ka bari se gobe kaji" ta qarashe maganar murya na rawa har tana langwab'e kai, a rikice ya d'an kalle ta "Bana san kukannan Islam ki dena naji sengobe shikenan?" Murmushi tai ta soma share hawayenta "Zan bika muje gidan ka tare yau muyi hiran bankwana" murmushi yae yace "Ina godiya Issy baby" miqewa tae tace STORY CONTINUES BELOW "Kanku fito Barinje in karbi saqo gun Asmy bala zan dawo" Islam tasan qarya take amma bata takura taba harta juya Maheer yace "Nancy!!" A rayuwa setaji babu namijkn daya iya kiran sunanta kamar shi kai gabaki daya duniyar ma sunan yafi dacewa da bakinsa, juyowa tae ta kalleshi ido cikin ido ata madubin yake hango idanta masu d'aukar hankali tace6 "Sir" miqewa yae ya janyo envelop a aljihunsa ya matso kusa da ita ya miqa mata "Bana kyauta ace baza'a karb'a ba, karki mun gaddama ungo kawai kije ki siya sabon niqafi da hijabai, itama wannan lukutar zan bata na siyan mayafai" hannunsa ta kalla ta miyarda dubanta a kansa "Amma Sir....." "Shsssssssshhhhh" ya furta,tare da d'aura d'an yatsanta na nuni saman lips nashi "Reserve it plss, ki karb'a kawai kinji" ya qarashe maganar da taushin murya, hannu biyu ta sanya ta karb'a har tana russunawa "Allah ya saka da alkhairi ya qara bud'i" murmushi yae yace ."Banaji zaki samemu anan dan yanzu zamu bar nan so inaga kwa had'u town ko?" Murmushi ta masa dame san tanayi ba tunda ta lullub'e fuska tace3 "Badamuwa ina maka fatan alkhairi, Islam mayi waya ko" haka ta fice zuciyarta tana mata quna ta sona zargin sun fara abinda islam ta iya da Maheer wataqil shima din ta gama dashi a wannan bangaren in shima fasiqi ne gwara tun wuri ta ciresa a ranta amma dukda haka zata tambayi Islam taji!.... Durqushe yake agaban Islam yana faman rarrashi, juyin duniya yayi amma taqi hakura ta dena kukan shiya yasan zeyi da rayuwarsa, cikin dakiya yace "Yanzu abinda za'ayi kiyi hakuri duk bayan sati biyu namiki alqawarin zanzo har sokoto na ganki shikenan ya miki" kallon shi tae ta wani shagwab'e fuska "Bazan iya yin sati bane ban ganka ba ai, ni gaskia yamun nisa" daganan taci gaba da rusa uban kukan ta wiwi tamkar wata jinjira, har cikin ransa bayason kukan yarinyar ya tsani jin kukan ta, ji yake tamkar ya rumgumeta amma sam baze iya ba sabi sanin haramcin aikata hakan dayayi, miyarda dubansa yae zuwaga hannunta yanaso ya riqo hannun nata ya rarrashe amma wani sashin na zuciyarsa ya masa hani dayin hakan, duk zamansa turai be taba yin irin wannan shashan cinba, yasandai yakanje gidansu qawayensa mata suma kuma sukan zo masa amma babu wannan aransa, yana dai ganin ziyarar ba komai bace idan kasan zaka riqe kanka da mutunci kaji tsoron Allah. Note: muba al'adarmu bace kuma sam musulunci be aminta da keb'ewar mace da namiji idan har ba muharramarsa bace,so kar ayi tunanin zuwa gidan saurayi ko dakinsa a kallesa ba'a bakin komai ba. "To kiyi hakuri sati d'aid'aya duk bayan sati d'aya zanzo ranar saturday da safe in koma sunday da azahar ya miki" tana qwalla tana murmushi ta gyad'awa Maheer kai,miqewa yae daga tsugunon da yae ya juya mata baya kanya soma magana "Islam inaga lokaci yayi daya kamata kisan matsayin dakike dashi a zuciyata, ki sani tun farkon ganina dake naji kin kwantamun arai, ina qaunar ko qauna me tsanani zan iya yin koma miye akan in faranta miki rai, dan Allah Islam ki soni ki qaunaceni kamar yanda nake miki karki gujemun" miqewa tae wani farin ciki ya gama mamaye ranta tace cikeda shauqi "Nagode sosai da soyayyar ka agareni Maheer bazan tab'a manta karamcin kaba ka sani nima ina qaunar ka sosai kuwa" dukda yake ya hango tsantsar tsoyayyarsa a wurin Islam beyi tsammanin zata amsa masa kai tsaye haka ba .....sosai ya fad'ad'a fara'arsa ya matso daf da ita yace "Ina qaunarki islam sedai inada tsananin kishi, wannan hutun da zamuje na tsawon watanni uku inaga senayi rama dan Allah ki riqr amanar dazan baki na kanki, ki kularmun da kanki, ba alfahari ba amma dukkanin lalurar dakike da ita zan iya d'auke miki ita, base kin had'amun soyayyata data wani naba kinji Islam" murmushi tae "Kar wannan ya dameka dear Maheer inshaa Allah baka tarar da kowa ba kaima ba wanda ze tarar dakai bare ya ture gwamnatinka koyace zeyi takara dakai, basemunje gayin quri'a ba ka cinye" zama yae yana murmushi.....2 ************ Acikin watanni biyu da akai hana hutu sosai Nancy tae jiki ta kuma freshh sedai damuwar fal a ranta akan Maheer, tayi iyakar yinta ta kasa ciresa aranta duk yayinda taso ta zamesa a ranta abin seya faskara gaba daya har ciwon rashinsa tae tsaitsaye, ji take tamkar ta janyo wata dayan daya rage ya zama gobe kowa ya huta!!! ************* Maheer wannan satin beje sokoto ba kasancewar islam ta sanar masa zasuje jega da mamanta biki, yana matuqar kewarta wannan ya sanya yace bari yaje gidan Ishmal danya ragewa kanshi zaman kad'aici da kewar Islam duk yaje sokoto tare suke wuni yau kam ta sauya zani tunda gashi bata kusa dashi har wani zazzabin rashinta yakeyi *********** A parlor Eshmal se hira sukeyi suna shewa, yace yana kallonshi "Gauro ko kaima ka nemo cook ne motsi nakeji da tashin qamshi agidan" murmushi yae yace "Wane cook wata ce er hannu na samu tazomun daga sokoto, girki takemun ba tun wednesday tazomun yarinyar tayine a rayuwa ai" girgiza kanshi yae1 "Kai har gobe bazaka dena neme nemen matan banza ba wai, nagode Allah daya yini badon mata ba Ina dalili wasu zunubai" tsaki yaja "Kaina zanci an hanani aure a gida, duk wacce nakawo sesun kushe na dena zancen auren Rayuwar bariki ta ishen" tsaki yaja "Ka dena duba gidanku kaji tsoron Allah" kan wani yae magana islam ta shigo d'auke da plates biyu ta zubo taliyar data dafa da kifi se tashin qamshi takeyi, tana sanye da riga iya gwiwa mazaunanta se magana suke, kai tsaye dining ta wuce ta dire su sannan ta kalli inda Eshmal yake !!!!!!!!! Mummunan dokawa qirjinta yae ganin Maheer ta kusa zamewa ta fad'i ta dafa kujerar dining d'in, idanta ta murza taga lallai shine shi d'inma ita yake kallo miqewa yae yace da friend dinshi ..2 "Bari naje Eshmal akwai inda zani" lokaci daya ya zaro wayarshi yana dannan Number ta, wayarta dake kusa da inda ya tashi ta shiga ruri ya juya ya kalli wayar "my Heart" yaga an rubuta, kan yae wani yunquri Eshmal yace da ita "Kizo ga garan daxe aure mana ke nan, dan baqin ciki yana miki waya" da sauri yae waje har anan hada kafa.....koda Eshmal yazo masa rakiya har yayi reverse yana shirin barin gidan hannu kawai ya daga masa ya figi mota zuciyar sa na masa tauna da tuquqi😭😭😭😭 Seda ya fita daga gidan yae parking motarsa ya d'aura kansa saman stiring motar ya soma miyarda numfarfashi a hankali, hannunshi yakai ya lalubi kuncinsa yaji shinwai da gaskene abinda yakeji qwallah yakeyi? Yaushe rabon da yae kuka a rayuwar sa? Ya manta whly akan wata yau gashi yana kuka wannan wace irin jaraba ce? Yafi mintun 30 a wurin batare daya san time ya tafi har hakan ba!!!!!!1 ************ Eshmal dan Allah ka kaini tasha, nahau mota akwai uzurin daya tasomun yanzun nan aka kira ni daga gida, kafita rakiyar friend dinka, namaka alqawarin zan dawo da kaina idan komai ya lafe" da zargi ya kalli fuskarta ta d'auke kanta gefe d'aya tana nazarin yanayin sa "Ka taimaka Eshmal ka kaini kaji, wlhy akwai damuwa fa!!" Mamakin jin da yae muryanta na rawa ya kama shi,yace "Subhanallah kaddai mutuwa aka muku" daganan ta samo qaryan dazata mai "E mama nane batada lapia shine zanje gunta ance sosai ne" "Ayya toki shirya muje ko, Allah ya bata lapia amma to abincin fa, ki danci ko kadanne mana" "Banida appetite ka kaini tashar kurun"...... Haka suka fito cikin qasa da mintuna 30 a bakin hanya ha hango motar Maheer da plate an rubuta Sidi dala range 12 wacce ta baro compound dinsa yanzu, gangarewa yae ya parka ya fito yamai knocking d'agowa yae bayan daya zuge glass din yama manta aduniyar me yake, kuma ya manta yana kuka ma, mamaki ya kama Eshmal uace " Subhanallah friend, menene ya samu haka da sauri sauri kuka fa" se a sannan ya tuna ya share qwallan sa yace "Kasanni da raki ai, bawai kuka nake ba muddin dai ina numfashi wani abu namun ciwo senayi qwallah, ina baro gidanka cikina ya murda shine na paka anan se juyamun yake" kallon sa yae cikin tausayi yace.. "Ayyah toka kawo na qarisa maka da motar acikin gidana sena direka gida kanka samu sauqi driver ma yaje ya miyar maka motar gida" kasa yi masa musu tabbas ze iya fad'uwa ya mace idan yace zeyi tuqin nan.....haka ya fito ya miqa masa key ya nufi motar sa, mamakin ganin Islam yae ta sadda kanta a qasa batasan meke faruwa ba batama san da zuwan saba, kwantacciyar sumar kanta data sakko har wuyanta ya kalla ya tabbatar ita dince dan haka nata zubin yake ya bud'e gidan baya ya shige bata koda d'agoba tana cen tana kuka tana sauke numfarfashi a hankali kukan me sauti takeyi me ban tausayi, leqowa Eshmal yae yace da ita1 "Sweetest barin je na sauke motar friend d'ina acikin gida nazo, cikinsa yana masa ciwo baze iya tuqi ba dan bani minti daya nai parking nazo muje" gyad'a masa kanta kurun tae, bata gano ma Maheer yake nufi ba shi kuwa ya dawo tsakiya ata bayan motar ya qura mata ido ko qiftawa bayayi har Eshaml ya dawo ya miqa masa key karba'a kurun yae ya tura aljihun gaba rigar sa "Yaya cikin? Yana raguwa yanzu?" Gyad'a masa kansa yae ba tare dayayi magana ba, shi kuwa bayan ya saisaita motar kan titin seya d'aura hannunsa daidai ta bayan wuyan Islam yace "Karki damu sweety, inshaa Allah maahmaah zataji sauqi kinji, ki dena kukan nan karkizo kiyi mana ciwon kai a banza" bata d'ago ba, shi kuwa maheer yabi hannun Eshmal da kallo yanaji tamkar ya dauki adda ya datse matsa wutsiyar hannun dake gangancin tab'a masa islam d'insa....katse masa tunani ya yana meci gaba da murza bayanta a hankali yace1 "Maheer ka ganta nan se kuka take tunda ka fito aka mata waya mamanta batada lapiya sosai" Da sauri ta d'ago jinya ambaci Maheer amma seta gagara waigowa ta kalle sa shi kuwa yace da kyar "Allah ya bata lapiya, zata samu sauqine inshaa Allah" batai magana ba dai Eshmal ya qara riqo hannunta, yace "Ki bani acc details naki zan tura miki 200k nasan aikin dakikamun ba dare ba rana yafi qarfin hakan, wannan ba ladan aikinki bane kije asiya maman me sweet magani, ladan aikinki da yamma zan tura miki" kasa d'aukar maganganun kunnuwan Maheer sukai yace cikin qarajin daya baiwa su duka biyu tsoro "Kaiiiiii" parkawa Eshmal yae yace "Maheer lafiya kake kuwa kodai muje asibiti naga alamar ciwon cikin nan naka baze barka ka huta ba" cikkn baqin ciki yace "Dan Allah ka kaini gida, direni gida tukunna kankaje inda zaka kaji" beyi musuba ya karkata akalar motarsa zuwa lameed'o crescent domin diresa gida, yana tsayawa yafita a motar Islam ta bisa da kallo, had'a layi yake kukanta taci gaba dayi harya kaita tashar ya biya mata drop na qaramar mota ya bata 20k tasha ruwa a hanya yakuma yimata alert na 200k kai tsaye, yauga kud'in amma basuda amfani agareta, har suka isa sokoto kuka takeyi...... 4 Tana isa gidan su innar ta dake wanke wanke ta miqe da plate a hannu tace "Ernan bikin nan har an gama, bacewa kikai se litinin ba?, naga duk kin kumbura a fuska wani abin ne ya faru?" Lumshe idanuwanta tae tace "Ba komai innah zazzab'i nakeyi yasa na gudo gida kai tsaye ba'a gama bikin ba yau asabar ake wuni, gibe bud'an kai" jinjina kai innan tayi tabi bayanta har d'akin, bayan sun zauna a bakin gado tace "D'azu lamimi tazo nemanki, wai yaronta baida lapiya babu kud'in dazata kaishi asibiti nace bakya gari amma na bata dubu d'aya" murmushi tae na yaqe tace,tana kwanciya "Akwai kud'i a jakana ki aika mata dubu biyar yau bana jin dadi innah, karki bari su faruk su tasheni idan na shiga d'akina" batace komai ta miqe tana murna yau tasan zasuci kaji tunda Islam taje biki...... 1 *********** Part d'insa ya wuce yaje yayi kuka harda majina, yanawa islam wani irin so dabesan dame ze fassara saba, wannan abu da idansa ya gane masa yau besanya yaji ko gyazau ba game da yanayin dayake ji akan qaunar islam, b'acin ransa d'aya ta karya masa alqawari ta siyar masa da jikinta me tsada arha banza, awurin fasiqan bariki tausayinta yakeji yanda ta lalace, batun yauba ya kula Islam tana yawon banza amma babu abinda yafi dakar mar zuciya kamar wannan mugun abin dayaji yakuma gani, be shigar kallewa islam jiki yanzu ba, be shirya ganinta a yanayin daya ganta ba yau, dama yayi niyyan auren ta koda kuwa karuwan ci take aganinsa yayi jahadi!! Menene ke shirin faruwa da soyayyar sa? Yayi kukan harya gaji bame rarrashin sadole yae shiru!!! Yakoma kukan zuci...3 ************** An kammala gyaran gidansu Ummul, ya dawo acikin jerin gidajen da ake lissafawa na masu kudi acikin unguwar ta lowcost, su ummul sun tare hatta Nancy ta samu an ware mata d'aki d'aya dayasha ado da kayan more life, wannan karon kam har qaramun plasma ne manne a d'akin na Nancy da wardrop gado dai set dan Niger me kyau!! Duk wannan daular duniyar nancy batajin dad'in zaman gidan nasu ko kad'an cikeda tashin hankali take na rashin Maheer, yaudai tayi shirinta tsaf na soma zuwa Catering school na billy galadanchi wanda takeyi a unguwar su na arqilla, acikin gidanta take koyarwar ta gaji da zaman ko oho datake agidan nasu, ada takanyi girki yanzu kuwa en aiki sukeyi an zauna daula, tanajin labarin wannan me koyarda girki ta ruga tae registration domin tana qaunar fannin girki gashi ko alihi bata iyaba banda abincin gargajiya daba laifi Baba Azumi ta koyar dasu!!.....a daidaita ta hau har zuwa gidan domin yaune zasu fara tarigada tayi registration da kud'ad'en da Maheer ya bata kanya bar garin.....tana sauka adaidaita wayanta ya soma bulayin neman dauki...dakatar da komai tae ta d'auki kiran na qawar ta islam1 "Hafsat nashiga uku na" shine abinda ta furta tana kuka, hankalin hafsat ya tashi tace tae hakuri zata zo gidansu idan ta kammala da school aikam ana idarwa ta wuce gidansu nanuwa.....babu abinda ta b'oye mata komai seda ta sanar mata dake faruwa from A to Z abinda ya faru, nanuwa kanta ta girgiza tace "To yanzu dai Islam kiyi hakuri na san zezo miki jibi saturday semu bashi hakuri" kallinta tae "Tun ranar yau kwanaki kusan 5 be qara kirana ba, ni kuma gagara kiransa" shiru Nanuwa tae kan tace "Zezo miki a lokacin dabakiyi tsammani ba ina gaya miki karki damu kinji?" Haka tae ta bata baki har yamma kanta wuce gida akan washe gari juma'a zata dawo... Shirinsa yae tsaf cikin shiga ta alfarma tamkar babu abinda ke damunsa kansa ya qurawa ido a mudubi yana kallon yanayin ramar dayae, ya rasa dalilin dayisa ya kasa jurewa idansa ganin islam!! Mesa zeje gunta? Mezata gaya masa? Me zeje shima yace mata? Ina dalilin wannan soyayyar dayike mata? Yana jin zafinta tamkar ya kashe ta amma soyayyar dayike mata ta wuce tunaninsa besan yana santa ba seda yae wa ennan kwanakin beji muryarta ba!!! Sanye yake da wani irin lallausan farin yadi me asalin kyau rigar guntuwace iya cinyarsa da wandon ta dinki big man amma me kame jiki hannun rigar dogone ya daure da clips yasha hula a kanshi qirar mu had'u a banki kalarta baqa wuluq, agogon hannunsa baqine takalmin kansa baqine kallon saman mirror d'in yae d'auki black shade d'insa ya manna a idon sa ya juya bayan ya zari key na benz d'insa baqa......+ ************* *Sokoto* Cikin awanni hud'u ya isa a sokoton, kai tsaye gidansa ya nufa yaci abinci yae sallan azahar sannan ya miqawa kamala key yace "Gidan da kake miyarda islam kaje ka d'akko ta ka kawomun ita anan, bana samun wayanta dan haka ka aika amaka kiranta daga ciki" durqusawa yae ya karb'i key d'in ya juya bayan daya dire masa yan kakkun fruit's agabansa...... Yauma se kuka Islam kewa Nancy ita kuma se faman rarrashi takeyi "Dama shisa nace miki ki kame kanki daga bin mazajen nan na banza....... Baze amfaneki da komai ba se tarwatsa miki future kuma kije lahirarki skelin zunubin ki ya rinjayi na ayyukan alkhairin ki islam, tunkan aje ko ina kin had'u da musibar rashin me aurenki, batun yauba ya dace islam kisan cewa kanki kikewa mugunta yau ina Ashraf? Halinki nabin maza ya kore miki shi, ina Aminu bawa? Shima yabi ruwa yae tafiyarsa, mazaje nawane sukai ta kansu wane namijinne ze auri karuwa islam, nasha fad'a miki abinda kike international karuwan cine me lisence bazan boye miki ba hadda laifin innah dan Baba nagani ba gayamun akaiba bayaso, har cewa yake na miki magana akan halayenki na banza yanzu wa gari ya waya? Wannan ma basanshi kike ba ai kud'insa ne ya rud'eki dabadan kud'iba nasan bazaki zauna zaman kuka haka ba" wani yawu me d'aci ta had'iya sannan ta kalle ta kallon nutsuwa tace mata "Bawai banason Maheer bane wlhy ina sonsa sedai bawai akan inason sa nake kukan nan ba abu biyu ne suke sakani kuka,na farko koda zamu rabu da Maheer bata wannan hanyar naso mu rabu ba yanayin daya ganni a riqaqqiyar karuwa me zuwa kwanan gida, na biyu kuma na kwad'aitu da dukiyarsa tunda ya furta kalmar so agareni nake hangoni acikin gidansa na alfarma ina wulaqanta naira, Nancy shejarata ashirin da uku acikkn talauci se zuwan Maheer na somawar warewa, ina samun kudi har kyautar miliyan ammun a kwana d'aya amma ni zanbaiwa wani labarin kud'in karuwan ci basa tab'a albarka!! Rasa kike me kikai dasu, amma kudin Maheer ko naira dubu biyar yaban senaga albarka ta" d'an guntun tsaki taja tace "Kinga matsalarki ko Islam, babu Allah a ranki ko kad'an yanzu bakiji tsoron Allah ba dukkanin bayananki selfish interest nakine kawai kike fad'a haba mana islam dan Allah kiji tsoron Allah!! So nake inji kona istigfari akan abubuwan dakika aikata" kallon ta islam tae "Indai ze aureni zan tuba wlhy" haushi ya qara kama Nancy tace " Auu danshi xaki dena badan Allah ba? Ki tuba wa Allah kiyi komai dominsa ze cika miki burinki haba mana islam" nisawa tae "To Nancy namiki alqawarin inshaa Allah na dena, na tuba sabida Allah kuma koda Maheer be dawo gareni ba zan dena zinace zinace har abada daga waccen danai" murmushi Nancy tae "Nagode sosai Islam Allah ya baki ikon yin taibatun nasuha kinji qawata" murmushi tae ta rungume ta "But i still missd him ya zanyi nancy" kan wanu yae magana sejin muryan yaro sukai a tsakar gida " Innan salaha wai inji wani mutum yace sunansa Kamala salaha tazo suje inji Maheer" miqewa innan tae daga hura gawayin datake "Tana ciki jeka zan gaya mata" kan innan ta shigo har islam ta miqe ta soma neman mayafi koda inna tazo sunkai waje, suna ganin kamala suka fad'a mota.... ************** Sunyi zaman fiyeda 30 mns be shigo ba, islam dukta gama rudewa se zufa take duk AC dake parlor nan, se dukan uku uku qirjinta keyi tana zare ido tana jin qarar bude qofa ta miqe tsaye!! Kallon wurin take harya tura kofar ya shigo qirjin ta se dukan uku uku yake, a hankali ya tako ya qaraso daf da ita har suna jiyo bugun zuciyar juna, Kuka takeyi ta kasa tsayarda hawayenta!! Shi kuma idanshi yayi jajir tamkar gaushin wuta!! Dukta qarisa rikicewa wannan daf da ita daya matso, wannan ne karonsa na farko daya matseta har haka!! Kana kallonta zaka hango yanda jikinta ke qyarma dukta rikice kallon shigarta yae yau kad'ai yaga islam da hijabi, idonshi ya sauke akan qafafuwan ta,qafan islam kawai ta cancanci yabawa bare fuskarta da surar jikinta!! Miyarda dubansa yae zuwa gareta yace murya na rawa "Islam Why? What on earth kika nema kima rasa? That u stood so low!!! Mesa aduk sana'o in dake duniya se zina Islam!! Kinsan ko handa na tsani zina dame yinta? Kin tab'a sanin aibun zina? Zinar taki ma bawai da saurayinkiba with any man!! Meaning bakya gudin komai? Azabar Allah, daga qabari har xuwa tashin qiyama har yakaiga murqusaki cikin wutar sa islam? Ashe bakya tsoron cututtukan zamanin nan, ashe bakya tsoron mutunci da martabar iya yenki idan kinsan duk bakya tsoron wa ennan mesa arayuwa zaki shiga rayuwata? Ni dukkanin abubuwan dana lissafa ina tsoron su yaua zakimun haka?" Jin yayi shiru ya bata damar d'aga idanta ta kallesa dan tunda ya fara magana ta dire idanta a qasa!! Zubewa tae saman gwui wanta duka biyu "Maheer dan san manzan Allah ka bani second chance!! Wlhh zan sauya, zan sauya to a good and better person please karka fita arayuwa, kayi wannan jihadin ka fitar dani acikin wannan musibar ka tallafi addinin islama Maheer ka aureni, wlhy na tuba tsakanina da Allah bazan qara ba" ta qarashe maganar tana kuka sosai me sauti!!! Qura mata manyan idanuwanshi yae ya kasa koda motsi shin menene mafita? Ya amsawa Islam tayinta yayiwa addininsa hidima kokuma aa ya barta besan me iya auren karuwa ba?"......

Post a Comment for "WATA FUSKA CHAPTER 3"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...