Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WATA FUSKA CHAPTER 1

WATA FUSKA CHAPTER 1

- - Post a Comment
WATA FUSKA CHAPTER 1
Cikeda nutsuwarta take tafiya dukda yake yanayin ta kad'ai ya isa ya sanar dakai cewar lallai a gajiye take kuma kallon farko dazakawa fuskarta zaka tabbatar cewar lallai tana tattare da yunwa matsananciya.....batada sukuni batada cikakkiyar lapia tamkar wacce qwai ya fashewa aciki.... Iyakar inda aka direta bakin first gate na jami'ar usman d'anfodio d'in batada ko sisi!!! Batasan se yaushe zata isa gidansu ba dake low-cost.....Mataccen agogon dake wutsiyar hannunta daduk fatarshi ta gama tashi ta wurgawa kallo qarfe bakwai ta kusa....magrib kenan fa ta doso kai idan hakane tashiga ukunta da Baba iro...... Cira kafarta tayi taci gaba da tafiya sauri da sauri......se gab da isha ta isa k'ofar gidansu Babur d'in Baba iro ta wurgawa kallo ta tabbatar yau kashinta ya bushe batasan me aka gaya masa ba,batasan qazafin da za'a mata ba....batasan me ze mata ba!!!! Cikin dokawar qirji ta shura qafarta zuwa cikin gidan had'e da wara Bakinta dasunan yin sallam amma jin muryar Baba Azumi ne ya dakatar da ita.... 2
"Ban isa in gayawa Nanuwa tajiba malam, Ban isa na hanata fita yawonta na banza ba, d'ari biyar daka bayar na basu yanda na baiwa Ummul haka itama na bata amma tunda tafice gidannan da safe har yanzu bata shigo ba nime zance?" Kwafa tajiyo shi yayi kanyace "Yau sena wulaqanta rayuwarta kuwa agidannan wlhy, badai burinta ta b'atan suna da sunan gida ba wlhy bata isaba aiba gidan ubanta bane nan d'in" girjinta ne ya doka amma a haka murya na rawa tae sallama, da sauri Baba azumi tazo gunta "Nanuwa lapia kuwa meya tsaidaki se yanzu kika shigo? Gashi kuma Baban ku se fad'a yakeyi,mesa bakyajine wai?" K'wallan datake qoqarin tarewa ne ya silalo mata tace "Baba Azumi a qafa fa na dawo" wara ido tae da mamaki "Kud'in motarki fad'uwa yae ne?" Mamakinta ya sanya Nanuwa kasa magana ta bita da kallo kurun kan wani yae magana har Baba iro ya taso yae kanta ya hauta da duka baji ba gani seda tae lilis ga yunwa sannan Baba Azumi ta qwaceta ta kaita d'akin dayake mallakinsu itada ummul, dariya tae bayan ta wurgar da ita kan matacciyar katifarta tace "Wahalalliya er iska, idan kina numfashi sekin bar gidannan wlhy" batace komai ba tayita kuka tana mayarda numfarfashi sama sama......Ummul ce ta kalleta ta girgiza kai tace
"Mesa baki mun wayaba Nanuwa? Dasena bi ta departments d'nku na d'akkoki ai tare da mahal muka dawo" bata kulataba ita d'inma bawai dad'inta takejiba sedai takan kwatanta mata adalci wasu lokutan. da qyar ta iya miqewa zuwa ban dakin dake cikin dakin nasu tae wanka da ruwan d'imi dayike akwai heater jonawa kurun tae ta watso ta fito tae sallan magrib da isha sannan tafita ta ebo abinci tazo tanaci tana hawaye.... ************** Washe gari tunda safe tana idar da sallan asuba taje gun Baba iro,har qasa ta duqa "Baba ina kwana?" Kallon takaici ya mata "Lapia lau Nanuwa, lapia dai?" "Dama Baba kud'in handout ne da akace mu siya nace barin maka magana" murmushi yae yace "Dad'in abin gadon ubanki kikrta cinyewa, nawane kud'in?" Sadda kanta tae qasa tace "Zekai dubu da d'ari biyu ga kud'in xuwa makaranta kuma" zaro dubu biyu yae ya miqa mata...... "Ni Nanuwa duk karuwancin nan dakikeyi ace wai ko sisi bazaki iya ajiyewa kiyi laluran makarantar ki, Allah ya wadaran naka ya lalace an tsotsi mugun hali a nonon uwa" qwallane ya gangaro mata ta miqe tana me ganin jiri na ebarta, idan bata karb'i kud'i a hannun Baba iro da kanta ba,Baba Azumi bawai batan zatayi ba....idan kuma tazo karb'a a gunsa seya zageta tatas ta uwa ta uba tukunna yake bata kudin.....shirinta tae kaman yanda ta saba acikin doguwar rigar yadin hijabi kalar ja, wacce take had'e da hijabinta da d'ankwalinta tayi kyau daidai nata irin kyawun irinna jan buzu!!! Hartakai qofar Baba Azumi ta kirata,tasan kwanan zancen karb'e kud'in data karb'a zatayi ita kuwa bata had'a komai da karatunta ba, bazata tab'a bari a ruguza mata abinda take ganin shikad'aine abinda zatayi ta taimaki kanta ba,wannan ya sanya tayi biris da kiran ta qarawa kafanta gudu har tana hard'ewa ta ruga da gudu tabar gidan har layinsu ma da gudu tabarshi ta nemai adaidaita ya d'auketa kan naira d'ari da hamsin zuwa dandima (Bus stop)..... STORY CONTINUES BELOW
Kai tsaye hall d'in dazatayi lecture ta wuce,ta tarar da qawarta Islam tana zaune tana bitar handout d'in ta,dafa tae tace "En mata Dr. Tahir d'in ya makara ko yau ko?" Murmushi tae "Bari kawai Nancy ai takaici ya ishen tun safe se'a rena maka wayau ka dako sakko ka fito kuma ka tafi empty ba karatun" zama tae kusa da ita "Kaine a qasa ya zakayi? Bakada zab'in daya wuce ka hakura" tsaki islam taja me tsayi "Idan kuma bakazo ba suka zo su karta rashin mutunci dan isa" murmushin ta qara yi "Kiyi hakuri islam wataran se labari" tab'e bakinta tae tace "Wai jiya se naseer ke gayan sun had'u dake kina tafiya da qafa zuwa gida, gaskia bakyawa kanki adalci Nancy, kina mace cikakkiya ma acikin matan! Ishasshiya meji da kanta da cikar zatin halitta da haiba fara kyakyawa Nancy ga diri son kowa qin maqiyin Allah zaki zauna dari biyu kacal ta gagareki, koni islam da bankaiki kyauba nafi qarfin mallakar miliyan biyu yanzu haka, bareke kyakyawa ki riqa turbud'e fuska a niqab kina cutar kanki, wlhy Nancy kullum ina gaya miki kiyiwa kanki fad'a, ni abu mafi bani takaici ma befi yanda kike cewa wai bazaki kyautar kud'i naba na haram ne, ina zinar bajikinki nake kaiwa ba nawa ne kuma bake kikai ba, amma ace kina qawata kina tafiya da qafa, ko Naseer yace akan babur suke susu uku daya wuce dake" murmushi tae tace "Islam koke fatana Allah ya shiryar dake babu wani kalar matsatsi na rayuwa dazan shiga na aikata zina ba, musamman irin wacce kukeyi, islam kefa intnl karuwa shine sunan ki!!! Kina wofintar da darajarki ta 'ya mace kina wulaqanta suturar da Allah yae miki kina kaiwa mazajen bariki jikinki, suna amfana da ni'imomin jikinki suna halllakar dake, suna amfani da 'dan abinda Allah ya basu na dukiya suna dulmiyar dake suna rud'ar dake....yayinda 'ya'yayensu suna cen suna cikin gidajen a garqame auren daze gagareki anan gaba su na gata suke yiwa 'ya'ya yensu wanda dan gwamna se er gwamna!! Er councilor kuma se d'an kantoman qaramar hukuma d'an shugaban qasa kuma se er minister!!! Yayinda ke kuwa aure ze gagareki koda dame shayin layin kune sabida wanda suke b'atancin dake sune dai zasu koma su zageki, wlhy koda yaron abokanansu sukaji zasu aureki zasuce er bariki ce!!!! Er Bariki shine sunan dazaki samu daga bakunansu amaimakon Islam!!! Kiwa kanki fad'a qawata ki saisaita nustuwarki" tab'e baki Islam tae tace
k "Bari kiji ko annabi dakanshi yace mu nemi tsari da talauci daga wurin mahaliccin bayi!! Kisani wlhy mahaifina dashi babu duk d'aya, mumu goma sha shida ya haifa 4 daga cikin mu sunyi aure duka matane agidan mu, sanin kanki ne yaranmu maza uku suma sune en auta, da qyar da sid'in goshi kake samun na break fast, ni yanzu Allah yamun hanyar kasuwanci bazan cuci kaina ba" girgiza kai Nancy tae kud'i masifane ta furta a sarari ta qara da cewa "Karuwanci shine sana'a Islam?? Dan Allah ki dawo madaidaiciyar hanya kinji qawata, wlhy zina masifa ce, bafa cewa annabi yae karmui zinaba cewa yae damu mu nesanceta ma'ana karmu kusance ta, mezesa ki kira wannan da sana'a? " jingina tae da kujerar ta yatsine fuskarta alamun gajiyawa da qosawa da zancen tace "Nancy, banida wani zab'i daya wuce wannan idan na dena neman kud'i da jikina ke zaki ciyar damu nida mahaifiyata da en uwana? Ki sani wlhy Nancy ina sane sosai da haramcin aikata zina amma wlhy bazamu rayu da yunwa ba" lumshe idonta tae tana me qoqarin hanawa qwallan idanta zubowa "Islam ki barwa haramcin nan dakike aikatawa suna tarihi dan Allah, ki ja jari da kudad'en dakika tara tare da addu'ar albarka ga abun sekiga kinci har kin baiwa maqota" "Nancy mujewa wata sabga mutane sun soma taruwa" shiru tae sabida ba kowa kusa dasu ta sani sarai wlhy gujewa maganar islam keyi kurun sabida tayi nisa batajin kira,wannan ya sanya bata qara cewa komai ba ta tsuke bakinta gum!!! Bayan da suka kammala da morn lecture hostel suka wuce wuce,sabida suna lecture da yamma, acen Suka qara buga sabuwar daba.... "Aa Ameena se kuma ina? an cab'a ado iya ado ana jiran isowar Alhaj Birwa Naira,tomu wai meye namu kason?" Harara ta wurgowa yusrah dake mata maganar "Gardawan dasuke hawan ki idan sun hauki nawa kike bani idan sun biyaki?" Dafe kafada tae tace "Allah sarki maida wuqar ni wasa nake wlhy" darewa tae itama "Wainikam yusrah ya zancen Alhajin mamula ne? Yafa matsanta akan zancen sabon hannu, na gama zaga en level 1 d'in nan ina latsawa duk kanwar jace, yaran a lalacen su sukazo shi kuwa tear leather yakeso wacce ze b'anb'are da kansa ya yaga ledar yaci biredin ya wurgar" dariya suka kwashe dashi dukkansu,yusrah ta ce "Ai baki sani ba, wlhy Alhajin mamula ban yarda dashiba, se kullum seyace se virgin kuma seya baki miliyan biyu kofi ifan kika had'ashi da virgin ita kuwa har miliyan goma seya iya bata, sekace abin tsafi,yo wata budurwar ai har sadakinta da lefe baze wuce dubu dari biyar ba" dariya suka qara bushewa da shi, yayinda Nanuwa ta girgiza kanta cikin qunan rai tana mamakin wannan halin ace aciki Mata goma babu daya ta gari to meye matsalar? Daga kuma ina abun ya samo tushe?" ......********** "Wainikam Islam ina zakijene haka? Goman dare yarigada ya wuce fa? Kuma sanin kankine munada test gobe morning abinma daya sanya nazo hostel kenan sabida in sanmu nutsuwar karatu" tsaki taja ta kunna turaren wuta me dad'in qamshi ta tsuguna aciki bayan ta lullub'e jikinta da barko batare data kulata ba, ita kuwa da abin magana baya isarta se cewa takuma yi 3
"Islam wainikam kinawa kanki adalci kenan kike gani? Kinawa iyayenki adalci kenan islam, bakya jin tsoron Allah kenan islam, bakya gudun mutuwar ki tazo miki kina cikkn wannan halin, bakya tsoron cututtukan zamanin nan, bakya gujewa fad'awa cikin wutar Allah, bakya tsoron 'yq'yayenki su tambayeki game da rayuwar daza'a goranta musu kinyi islam? Dan Allah islam ki rufa mana asiri ki dawo hanyar daya dace" miqewa tae 2 "Ki adana kalamanki Nancy!!! Wata qil zasu miki amfani anan gaba, idan kuma zaki dauken lalurorin dake kaina ne na komai sena fasa sana'ata na zauna kimun su, gaskia wlhy kin soma isana huldar nan fa bawai dole bace kuma ina qabarinki daban nawa daban? To meye na damuwa?" Qwallan ta ta share daya silalo mata bata qara cewa komai ba.....Allah ya gani tanason Islam bata mata fatan fad'awa halaka amma yazatayi iyaye suna suke taka muhimmiyar rawa wani xubin wurin gurb'acewar tarbiyan yaran su.... Babu me kulawa da karatun Islam, babu wanda yake damuwa da suturunta babu wanda ya tab'a cewa islam ina kima samo abu kaza!!! Yaya tarbiya zata ingantu? Yaya yarinya bazatabi ko wacce iriyar hanya ta nemi kud'i ba??..... 4 ******** Tunda ta soma cin hanyar motar ke biye da ita tana yin tata tafiyar tamkar hawainiya.... Ba ai mata magana ba kazalika ba'a dena binta ba, tundaga gate din na jami'a har zuwa gidan man ada!! Ganin ta yanki dogon titin Rima Tv dayake tsit ya sanya ma mallakin motar yaje yae parking a gaba da ita kad'an kana ya bud'e motar tashi qirar range rover 2018 black wuluk ya fita, ji yajingina jikin motar ya hard'e hannayenshi asaman qirjinsa yana nazarin tafiyar nutsuwar da yarinyar keyi, yanda tae tamkar ma bata gan shiba shine abinda yafi bashi mamaki dabita sabida ya saba harka da en matan jami'a wannan slow dayaje badole seya tsayar dasuba su zasu tsaya har sumai tayin number wayar su kuwa, gabanta yasha yace "Kenake bi en makaranta Ina san zanyi magana dake kina mun yanga, dan Allah ki bani time d'inki" ya soma furto maganar tamkar wanda akawa dole" rausayar da kanta tae kantace "Bana saurarar mazaje a bakin titi, bana magana da maza akan hanya, gidanmu babu nisa danan wajen amma idan ka matsu zaka iya ci gaba da bina zuwa qofar gidan mu" kallon mamaki ya bita dashi, tsakani da Allah kuwa tai tafiyarta ya jima yana kallonta kanya tashi motarsa yabita a baya..... Yaso ya basar amma ya kasa,yaso ya wuce abinshi amma yarasa dalilin dayisa zuciyarsa take azalzalarsa akan yarinyar dako fuskarta be tab'a gani ba kasancewar da niqabi sanye a fuskarta ga madubin data sanya baqi wuluk ta rufe idanta dashi......har duka isa qofar gidan yana biye da ita, ita kuwa tae shigewarta ta barshi a waje yana mamakin hali irin nata!!!!! Ganin yafi 20 mns tsaye bata dawo ba ya sanyashi kiran wani yaro yace dashi..
m "Kasan budurwar dake nan gidan yaro?" Kallon sa yaron yae "Susu biyu ne se qaramar su, Akwai Ummul akwai kuma Nanuwa wacce aciki?" Shafa tsajensa yae "En matan guda biyu inaga daya ce daga cikin su a jami'a take kaje kamun kiranta bansan sunan taba, amma dai ba jimawa tashiga gidan kace nace wacce take sanye da niqabi da mudubi acikin kalar kaya koraye" juyawa yaron yae yace STORY CONTINUES BELOW "Na santa barin maka kiranta" Da sallamar sa ya shiga cikin gidan ya had'u da baba azumi "Baba wani ne awaje yana jikin motarsa yace amai sallama da wacce tashigo yanzu da niqafi da madubi inaga kamar nanuwa yake nufi" zabura tae jin an ambaci kalmar mota ta riqe hannun yaron da ake kira da suna ilu ta leqa waje da hannu ta nuna mutumin tace "Wancen na jikin wancen bakar qatuwar motar?" Murmushi ya mata yace "Ea Baba azumi shine wancen" washe haqora tae "Jeka kace tace gatanan zuwa" yaro ya jiya ita kuwa taje ta janyo hannun Ummul "Er qwarai jeki ki ari kayan Nanuwa har niqafin da madubin ido ki saka, wani me qatuwar motane ya biyota ya aiko yaron ko sunanta be sani ba, kinga kuwa zamu samu damar qwace shi wataqil ko gaisawa basui ba yaga ta shigo ne ya aiko kiranta" murmushi ummul tae seda haqwaranta suka bayyana tace "An gama hajiyar ummul barinje" 1 Duk abinnan dasukeyi a kunnen Nanuwa ita dariya ma suka bata ta sani, dirinta kawai dako a hijab seya bayyana ne ya gayyato mata wannan mutumin data kasa yadda da nutsuwarsa da kamalarsa duk basui mata ba! Ita kamma aita huta dasuka rabata da shi salun alun haja ta shige toilet yin wanka yayinda Ummul ta sace kayan tafito dasu....d'akin Baba Azumi taje ta sanya kayan sannan ta fita waje....kai tsaye gun motar da Baba Azumi ta kwatanta mata ta nufa taje ta kalleshi "Sannu da zuwa bawan Allah" haka kawai seyaji muryan kamar ba wancen data mai magana ba d'azu yanayin sautin cikin nutsuwa yasha banban sosai da wannan gyaran tsayuwarsa yae "Kece kuwa?" Kallonshi tae daga cikin madubi wanda ya qara d'aura kokwantan shi akanta domin waccen bata kallon sama ya kula da hakan daga yanayin tafiyarta da kuma sanda take mar magana sam bata kallesaba, maganarta cikeda sanyi take yinsa amma wannan sauyin na miye haka?" "" Wa kace kake nema ne bawan Allah? Ina wacce tashiga gidan ba dad'ewa? Kodai Nanuwa kake magana nama sallama da ita? Koda yake batada lapia yau duk a kwance ta wuni,da wuya idan zata iya fitowa,sedai ko zaka dawo wani lokacin" da sauri ya dakatar da ita "Ko d'aya ked'ince dai, indai wacce ta shiga gidan ce da wannan shigar kuma, muryan ne kawai nake kokwanto,koda yike dazu kincene akan hanya ne bazaki tsaya ba" gyara tsayuwarta tae 1 "Tonikam yaya zan zubar da mutuncina na tsaya yin magana da wani akan titi, nan din dai yafi ko" murmushi ya sake mata shima 1
"Hakane amma to yanzu fuskar fa, zan iya ganin mamallakiyar zuciyar data sacen tawa tunkan nae tozali da fuskar?" Murmushi tae acikkn niqafin ta soma zare gilashkn idanta kanta yane niqafin gaba d'aya ta bayyanar masa da kyakyawar fuskarta me d'auke da qayataccen murmushi, shakka babu ummul kyakyawa ce ta nunawa sa'a ma kuwa,sedai asaran hali da akae, da qyar ya saisaita nutsuwarsa yace "Sunana Al-Ameen amma anfi kirana da sun yaro da kud'i!!! Ina fata na miki danni kinmun kuma bawai da wasa nazoba aurarki nakeso nae idan kin shirya kuma na miki" wani murmushin ta qara saukar masa dashi "Kamun yaro da kud'i!! Kuma nima da gaske nake ko gobe ka shirya kazo a d'aura" dariya ya bushe da ita "Allah en mata" itama tana dariyar tace "Allah kuwan d'an samari" dariya suka qarayi sannan ya miqa mata wayarsa yana me rungume murfin motarsa dayake a bud'e tun zuwansa yana binta da wani kallon shaqiyanci, "A zuramun digit inason naci gaba da jin wannan zazzaqar murya a kowane lokaci" ba musu ta cafe ta zura mai ya karba yae saving tare da kiran layin nata,wayan yae ringin ya kalleta ."Na saka miki sunan wife to be a wayana,ga nawa nan ki bani husband to be ko kuwa?" Murmushi tae wanda tun zuwanta shine a fuskarta 1 "An gama Yaro da kud'i..... Koda baka buqaci jin sunana ba zan fad'a maka, sunana ummul khulsum" hade hannayensa yae...."Afuwan Babyna zumudi ne ya hanani tambaya" taji dadin sunan daya kirata dashi matuqa ta washe masa baki.....ya zaro rafar dubu d'ai d'aya a motar sa har qwaya biyu ya miqa mata ba wani musu ta karb'a yace "Aje a sauya waya, bansanki da wannan qaramar wayan, kuma a mun kwalliya kafin wani satin idan nazo, savida zan shiga jeji zan kwana biyu ban zoba" kalmar jeji ta nanata a zuci kan tace "Me zakajeyi jeji sekace mafarauci?" Dariya yae "Mafaraucinne kuwa, aikin dazanjeyi jejin kenan farauta, amma bata dabbobi ba" a wasa ta dauki maganar sa wannan ya sanya tace "Allah ya baka sa'a husband to be" "Naji dad'in adu'arki babyna....kuma ko yanzu kasuwar ta watse d'an koli yaci riba ai" kallon sa tae da rashin fahimta,ya d'age masa girarsa d'aya "Ea mana babyna, nayi sa'a had'uwata dake ai sa'a ne musamman yin na'am dani dakikai haka da sauri wannan shine babbar nasarar danai a rayuwata" taji dad'in zuzutatan dayae ta masa godiyar jin haka, daga haka sukai sallama ta juya tana sauri taje ta gayawa Baba Azumi yau dai ga dubu dari biyu har cikin gidansu!!! Al-ameen kuwa yau farin cikinsa ya ninka na kullum yau yafi komai yin sa'a ya bada d'ari biyi ya tabbatar seta zama miliyan d'ari biyu!!!!! ........Baba! Baba ina kike kizo ga abun arxiqi ya samemu har gidannan Baba......Allah ze cika mana burin mu zan auri attajiri Baba... Baba Azumi take ban daki tana kashi haka ta kutsire kashin ta fito da gudinta da buta a hannu ganin uwar kud'i a hannun ummul ya sanya ta wurgar da butar tayi kanta 7 "Ummul yaya dai kudin wa kika kawo nan gidan" washe baki tae sosai "Saurayin arziqin da kika samamun ne ya bani waina siya waya kuma namai kwalliya wani satin ze dawo" karb'ar kud'in tai ta shiga jujjuya su da mamaki..... "Kodai wasa kike ummul in banyi kuskure bafa dubu dari biyu chif chif!" Rausayawa tayi tace "Tunda na yaye niqafi yaga fuskana ya mace mun, bako tantama aurena zeyi Baba na hango haka atattare dashi kuma ya nanata harya fara cemun matarsa fa" gud'a ta dire ta soma rawa tana jujjuya kud'in yayinda ummul ke qyalqyala dariya a haka Mahmud ya shigo ya samesu, adane kudaden tae a bayanta tasoma muzurai ta kallesa tace "Mahmuda kaine haka" kallonta yae ya miyar da dubansa zuwa wani wajen kana ya wuce batare dayace mata kanzil ba....tun shigowar yaron da aka aiko yaji komai shi mamaki Baba Azumi ke bashi sam ba Allah a ranta amma Allah ya sanya shiyafi zamarwa hafsat Alkhairi. 1 *********** Kallon mamaki take bin Ameena dashi yanda ta dage taketa shiri da baza turaruka ajikinta da sunan zuwa gun mommynta....ba wani dogon sabo sukai da Ameenan ba amma tana son yarinyar kallonta tae a karo na barkatai tace cikin tattaro kalaman dasuka wa bakinta nauyi da qyar "Aminty bakya tsoron wannan hajiyar wai?" Murmushi ta mata "Nancy kenan hajiyar nan ranar data fara ganina ranar ta bani kyautar dubu d'ari ina cikin wani mugun talauci yanzu kuma kice inji tsoron ta to tsoron me?" 1 "Duk da haka ki duba dai da kyau, haka kawai mace tace mace er uwarta ta mata harda bata kyauta kudad'e haka anya hakan daidai ne kuwa?" Tsaki ta d'anja "Nancy ina baki shawarar ki fita a harkar dabe shafeki ba kinji ko" shiru tae tana nazarin yarinyar kan daga bisani ta miqe da zummar barin d'akin zuwa d'ayan d'akin dake manne da nasu.....numfarfashin data jiyo ne ya sanya ta fad'uwar gaba tare da mayarda dubanta zuwaga gadon dake gefen ta na dama inda takeda yaqinin nanne nunfarfashin ke tashi!!! Su Jameelah ne ta furta abinda bata tab'a sanya tsammanin sunayi ba jameela sani da humaira Ali suna wasanni da sassan jikin juna suna sharing toy daya me hakan ke nufi har hostel din takai cen? Qarfe sha dayan dare ba kowa! Kowa yaje iskancin sa su kuma susu biyu suna wani bala'in fitila a kunne kenan duniyar tazama haka basa jn kunyar kallon qwayar idon juna!!! Basajin kunyar Allah mad'igo da sauri taja da baya ganin yanda jameela ke kallonta cikeda wani shauqi tabbas basa tsoron a gansu wataqil har metron din hostel din nan tasan da zaman wa ennan hatsabiban, baya taja da sauri zuwa d'akin su data baro akan takaicin Ameena ne ya sanya ta baro d'akin.....ba kowa se ita kadai tsoro ya kamata har wani zazzab'i takeji tsoron Allah mahalicci ya qara shiga jikinta tana tsoron yanda Allah zeyi dasu idan ya gaji da wannan bad'alar da ake aikatawa a makarantar tana jin tsoron hakan fiyeda komai arayuwa!! Iyayen 'ya'ya mata suna bata tausayi matuqa!! Ta firgita sosai da yanda duniyar ke sama lubaye da rayuwar wanda ta rud'a!!!! 1
Washe gari tanata saurin zuwa yin test yayinda mutanen dasukaje kwanan gida lokacin suke dawowa hostel din domin daukar kayan su zuwa lecture....aciki kuwa hadda Islam batako kalleta ba ta juya abinta ita d'inma inda sabo tota saba da halin Nancy indai taje yawon ta to idan tashigo bata kulata sam!! Waje tae ta wuce cikin school rayuwarta duk ba dad'i ba karatu kawai yake kawota zaman hostel ba hadda rashin wadatattun kud'in kashewa dana transport irin yau zasui test setai missing intace zatazo da qafa tasani ba lallai Baba azumi ta bata kudin ba koda ta karba gun Baba iro...... STORY CONTINUES BELOW ******* "Baby me ki shirya yau zamuje na siya kayan more rayuwa da yawa, da suturu masu kyau kinji matar al'ameen" gyaran kwanciya ummul tae ta qara maqale wayar a kunnenta "To sweety when zaka shigo inada lecture se 2 zan qare" "Ki shirya by 5 na yamma kinga rana tayi sanyi fitar zatafi dad'i koya kikace?" Murmushinta ta fad'ad'a "To nagode sosai se zuwa lokacin ko?" Sallama sukai ta daka tsalle...... Da yamman kuwa yazo ya d'auketa suka fita sututu da kayan abinci da abubuwan maqulashe kawai ya kashe mata 400k ita harya soma bata tsoro ma haka suka dawo gidan aka kira yara suka dinga jibgar kayan zuwa cikin gidan a wannan lokacin baba iro yana gidan ya dawo sabida har angama isha....kalllon Al-ameen ummul tae tace "Kaje kayi sallah nima sallah zanyi ko magrib bamui ba" kallonta shima yake yace "Dukiyar jeji ta hanani sallah a inda nae tsintarta" kallon mamaki ta bisa dashi bata gane kan zancen saba ko kad'an tace "Dukiyar jeji kuma Al-ameen? kacika yin magana me d'aure kai" dariya yae seda fararen haqwaransa suka bayyana "Se yanzu na d'aure miki kai? Tu kunna dai bazan d'aure miki kaiba semunje jeji" zuwa yanzu kalaman al'ameen sun soma tsorata ummul "Jeji kuma zamuje? Yin me?" Dariyar shi ya qarawa sauti dayake cikeda shaqiyanci yace "Ahaff yin noma mana, aini manomi ne kuma qauyen mu jeji ne kazalika tare da matayenmu muke noma, kinga kuwa duk ranar danakai ki jeji kanki zefi haka d'aure wa" sauke ajiyar zuciya tae tace "Allah? Yanzu seka sakani noma?" Bece komai ba yace "Jejin mu danisa Ummul kuma akwai masu jirana da yawa acen ki huta abinki zanje cen nae sallah" marairaice fuska tae sabida Ummul koba komai akwai son ibada 1 "Bazanso ka qarajan wani lokaci batare dakayi sallah ba koba komai magrib tsuntsuwa ce ta hira abinta" murmushi yae had'e da d'aura tafin hannunsa saman kuncinta yace.. "Masallacin cen na baya zanje nae sallah karki damu kinji baby" juyawa tae bayan ta masa lallausan murmushi a ranshi yace zaki ganene..... ****** Kwance yake acikin bahon wankan dayake cike da ruwa masu tashin qamshi na musamman.... Iya kanshi ne a waje yablumshe idanuwan sa yana me tunani me zurfi wanda nake da tabbacin ya mantar dashi a duniyar dayake yanzu haka ya jima sosai acikin ruwan wankan kan daga bisani ya wanke jikinsa ya fito.....towel blue ya d'aura a qugunsa ya kuma fito da wani qarami shidinma kalar light blue yana tsane sumar kansa datake cike sosai baqa wuluk! Mai ya shafe jikinsa dashi tsadadde ya gyara sumar kansa itama tasha mayuka masu kyau da gyara suma........kayan da aka rigada aka ciro masa ya wurgawa kallo dogon wandon jeans ne blue da shirt fara qal me asalin kyawu an mata zanen Nike ajikk da blue din colour se agogon hannunsa dayake baqi takalimin ma gas ajiye baqaqe ne se zuben azurfa dayike ajiye a saman rigar sosai yae kyau acikin wannan shigar ya feshe jikinshi da turaruka masu asalin qamshi sannan ya shuri takalminsa ya soma tafiya zuwa qasa cikeda qasaita da isa...... Da umman shi ya soma karo a qasa, har qasa ya tsuguna ya gayar da ita ta amsa da fara'ar ta "Maheer shirin tafiyar ne haka?" Murmushi ya sakar mata "Ea Umma tafiyar kenan fa senaga kamar nayi late ma" kallon shi tayi "Naji dad'i matuqa daya kasance kana sha'awar neman na kanka dukda kasancewar mahaifinka me daula sosai, amma Maheer anya zaka iya kuwa? Lecturing abune me matuqar wahala ni shaidace tunda kasan aikina kenan"
"Umma adu'arku nake nema, inshaa Allah kuma zan iya tunda ina son abin" jinjina kanta tae "Allah ya sanya alkhairi da albarka me tarin yawa a rayuwarka,Allah ya tsareka da tsarin sa Allah ya kareka da kariyarsa Allah kuma yae maka jagora a duk abinda ka sanya a gaba" da murmurshi d'auke a fuskarsa ya furta Ameen yaa Allah umma nagode sosai sena kiraki" miqewa yae lokaci d'aya yabar parlor d'in zuwa harabar gidan..... Kamala yana tsaye a waje yaga me gidansa ya fito da saurin sa yazo kusa dashi yana duqawa har qasa,cikin qasaita yace "Gidan dana siya a sokoton baya buqatar komai naku se kayan sakawarku kaida matarka, part ne d'aya na ware muku qarami dake ata gaban gidan, karka wuce yau idan Allah ya kawo ka lapia mudi yazo da benz kaikuma kazomun prado baqa idan munje shise ya dawo a motan haya" Yana gama fadan hakan ya juya..... farar motarsa qirar range rover yaje ya shige had'e da bad'e ta da key kafin ya taka totor ya furta "Bismillahi tawakaltu Alal lah! Wala haula wala quwata illah billah" sau uku sannan ya karanta ayatul kursiyyu da falaq da nass qafa uku uku sannan ya furta a sarari "yaa Allah" ya bar harabar gidan kai tsaye babban titin daze jagoranshi zuwa sokoto ya miqa yayiwa kanan dabo bye bye......... *Wanene Maheer sidi Ali?* D'ane d'aya tilo namiji da Alhaji sisi Ali dala da matarsa Hajiya sakina kabeer sudan suka malla shine na tsakiyan yanada yayyu mata susu biyu se qaninsa mata susu biyu....mahaifinsa Alhaji sidi Ali dala shararren d'an kasuwane wanda kasuwan cinsa bama a Nigeria ya tsaya ba har qasashen qetare yanayin abubuwa da dama kama daga shinkafa, sikari,gishiri,taliya kai da sauran abubuwa masu yawa acikin Nigeria d'aid'aikun mutanene basusan sidi Ali dala ba, kai koma baka sanshi ba zaka san shinkafa me taken Ali dala parboiled rice....kuma agidan kuma baza'a rasa cin taliyar Ali dala ba!! Idan nace arziqi ina nufin d'an asalin arziqi sanannu ne a kano mutanen wudil ne daga uwar har uban sedai mahaifiyar sa er tsallake ce ba mutuniyar Nigeria bace, daga sudan mahaifinsa ya aurota daya had'u da ita tun tana qaramar ta!!! Maheer yarone d'an qwalisa kasan cewar namiji d'aya tilo a wurin iyayensa ya sanya kwata kwata basu so masa zuwa lecturing ba amma ya kafe shi lallai se ya zama lecturer....mahaifinsa har private university yace ze bud'e masa amma yace sam ba yanzu ba shi lallai seya tafi, yanzu haka a jami'ar usmanu dan fodiyo dake jihar sokoto ya samu aikin kuma cen ya nufa. ****** Duk uban saurin da Nanuwa keyi be isa ya hanata daka uban late ba zuwa lecture hall din kasancewar yau da ciwon kai ta tashi ya sanya tae late gashi ance akwai test kuma yau lecturer dake daukar course din ze miqawa sabon dayazo komai...... Koda ta shigo har an fara test din taje ta zauna ta zaro paper da pen amma cash bata samu question paper ba, tsaye tae kamar wani statue da qyar ta gayyato kalmomin "question paper sir" Kallonta Maheer yae "U came late and ur asking for a question paper just like that how dare u?" Qwarjini maheer ya mata amma seta kasa cewa komai haka ya barta tsaye har kowa ya qare aka watse d'aya bayan d'aya yarage susu biyu lecturer's se ita....batae magana ba abin ya mata ciwo haka ta sauka daga steps din a hankali da zummar barin hall d'in...tsohon lecturer dinne yace mata "Hafsat kisameni office yanzu" jiki a mace ta juyo tace "Ok sir" tsaki maheer yaja wanda tasani da ita yake, shi kuwa a ranshi yace wannan me mugun girman kan tsiya kyaji dashi"..... A gafarceni najina shiru, rashin lafiya nai amma na samu sauqi Alhamdulillah.

Post a Comment for "WATA FUSKA CHAPTER 1"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...