Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WATA BAKWAI CHAPTER 4

WATA BAKWAI CHAPTER 4

- - Post a Comment
WATA BAKWAI CHAPTER 4
Yaji shigowarta sarai ya ci gaba da game dinsa. Ya kuma ki abinda tace. Dame take ji da ba zata dauke shi da muhimmanci ba.+ Dan shi bata gabansa bashi zai bata damar jin hakan game dasji ba. Ba ai macen da zata nuna masa iyakarsa ba. Ko da huddy ce kuwa. Dole ta bashi girma ko bata so. In tana son magana dashi ta zagayo ta kalli fuskarsa. Husna kamar zata saka ihu don takaici. "Magana fa nake maka kazo kasa a budemin gate." Ta sake fadi cikin alamar qulewa. System dinsa ya rufe ya miqe yana shirin nufar dakinsa.....tasha gabansa shade din idonta ta cire ta kalle shi cikin fuska sosai. Tunda yake bai taba ganin kiyayya irin wadda yagani a cikin idanuwanta ba. "Don na tambayeka abu zaka nemi wulaqantani?" Da mamaki sosai yake kallonta. A. Lokaci daya kuma yana tambayar kanshi akan me zata aure shi. Ta tsane shi!!! Yagani cikin idanuwanta bata son shi. Ko da zaka auri mutum dan kudin shi da kalar tsanar datai masa kam zata hakura. Sai dai duk wannan bai bata damar yi masa magana yanda take so ba. Kamar wanda magana ke ma wahala yace. "Not that i care. Ki rubuta ko me kike so aje a siyo miki" Hawayen ta take iya bakin kokarinta wajen tarbewa. Da tana da bindiga harbe wannan nataccen zatai. Me yasa baya ganewa ne. Me yasa yake son kara mata kunci har haka. Muryarta na rawa tace. "Kabarni da abinda yake damuna. Just kasa a bude mun gate" Kallon nutsuwar nan ya tsaya yake mata. Kallon da zaka rantse bashida wani muhimmin abun dazai daya wuce ya zuba mata idanuwan shi yana kallonta kamar yana hango har abinda yake bayan fatar jikinta. Tun da ta kalli idon shi tai magana dazun ta sauke kanta kasa. Tana jin yanda idanuwansa ke mata yawo. Saboda duk damuwar da take ciki bai hana kamshin shi damunta ba. Bai kuma hana bangaren zuciyarta dake dokawa duk idan taganshi ci gaba da aikin shi ba. Ganin suna shirin daukar mintina biyar bai ce komai ba. Yasa ta fadin. "Bana son duk wata alfarma da zata fito daga wajenka zan je da kaina kuma zan shiga motar haya" "Motar haya" ya nanata a zuciyar shi. Bawai bai san akwai bayin Allah da suke hawa motar haya bane. Sai dai har ga Allah ya manta da wani abu waishi motar haya. Saida yazo daf da ita wannan karon ma kanta a qasa hannu yasa ya dago mata da fuska ranshi ya baci. Bakuma ya son ana bata mishi rai saboda bako yaushe yake iya controlling abinda yake aikatawa ba cikin bacin rai. "Ba.a fadamin duk abinda ake so....idan kika qure haqurina ba zai maki kyauba. Daga randa kika tako kafafuwanki cikin gidan nan kike cin alfarmar da duk wanda yake karka shin sa yake ci." Ganin yanda jikinta ke kyarma a hankali ta kuma kasa kallon idanuwanshi. Duk da idanuwanta akan fuskar shi suke. Ya jinjina kai kamun yace. "Ko hadiman gidan nan suke bukatar wani abu fita ake a siyo musu." Ko ina na jikinta kyarma yake. Karo na biyu kenan daya kai hannun shi a habarta. Kuma dumin hannun yana shigar mata wajaje da yawa a jikinta. Hannunta tasa ta ture nashi hannun. Karfin gwiwar da take ji ya gama narkewa. Kawai so take ta samu abinda take bukata. Karo na biyu da yai misalin matsayin yan aiki da nata. Ta rasa abinda yasa hakan ya sosa mata rai. Yana kallonta ta bude jakar hannunta ta dauko dan karamun diary da biro. Ta rubuta always da recharge card. Ta rubuta pin din ATM dinta daga kasa taja masa layi. Sannan ta rubuta 10k da take so a ciro mata. Ta dauko ATM din 3k. Always ta 1k. Katin MTN na 2k. Batare data kalle fuskar shi ba ta mika mishi takardar da kudin da ATM din. Wani irin kallo yai mata sannan ya karbi takardar kawai yabar kudin da ATM din suka fadi kasa. Bai jira amsarta ba ya wuce abinsa ya tsani wannan yarinyar da take ji da kanta. Duk a yanzun ya tabbatar ba kwadayine yasa ta aure shi ba tunda yaga tsanarsa a idanuwanta. Sai dai ya rasa dalilin dazaisa ta aure shi idan tana masa wannan tsanar. Waya yai akawo always din guda goma da katin MTN na 5k. Bai koma dakin shi ba saida ya bar umarnin in an kawo kayan akai ma natacciya bangarenta. Yana shiga dakin shi ya sake duba list din yaga ta saka a ciro mata kudi. Yaja tsaki. Baya son harkar karanta ko kadan da zubda mutunci. Drawer din gadon shi ya janyo ya dauko rappers na kudi yan naira dubu dubu. Na 50k ya dauka dan babu ma kudin sosai. Sai ya kira an ciro mishi. Baya jin zai iya sake fita babban falo. Saboda yanda ranshi yake a bace. Waya yai ma Kamala da yake kula da komai na gidan. Yasa a turo masa wata bangare shi. Falon shi ya fito ya tsaya. Sai da tazo ya bayar da kudin a akaima natacciyar yarinyar can. Kan kujerar falon ya zauna. Ya lumshe idanuwan shi yana karanto addu.o.in dazai samu nutsuwa a bisa koyarwar musulunci. Sallama yaji. Ya bude idon shi. A ladabce hadimar da take tsugunne tace. "Allah ya ja da ran yarima" "Lafiya?" ya bukata muryarshi a dake. A tsorace hadimar tace. "Rankai dade. Uwargida tace a dawo maka da sakon nan" "Kije da shi kawai" ya fada yana kirga 1-10 cikin kanshi. So yake ya nutsu ko yaya ne kamun ya fitar da kafarshi daga falon nan. Cikin rawar murya hadimar tace. "Rankai dade ban fahimta ba" Cikin tsawa yace. "ki dauki kudin nace yaren hausa ne bakya ganewa!!!" Da sauri ta mike tana fadin. "Allah ya huci zuciyar yarima" Tana fita ya saka takalmanshi ya nufi sashin husna da tun ranar da aka kawo ta rabon da ko hanyar ya kalla. Husna kam tana zaune gefen gadonta ta rafka tagumi da tunani kala kala a zuciyarta.+ Sanda aka zo aka kawo mata kudi wai inji yarima. Wani abu taji tun daga dan yatsan kafarta har zuwa zuciyarta. Waye shi dahar zaiyi zaton tana bukatar kudin shi? Tana kallon mamakin da yake fuskar hadimar data ce ta mayar masa da kudin shi. Kasa jurewa tai. Batasan lokacin da hawaye suka zubo mata ba tasa hannu ta goge su. Kirjinta na mata wani irin zafi. Turo kofar akai da wani irin karfi da saida karar tasa husna zabura. Da yanayin yanda ya turo kofar haka ya mayar da ita y kulle. Tana kallo yasa mukullin jiki ya na shirin kullewa. Gabanta ya shiga dukan uku uku. Murya na rawa tace. "What are you doing? Ka fitarmun daga daki. Bana........ " Ganin ya cillar da mukullin gefe ya nufo gadon. Yanayin fuskar shi ya sa ta hadiye sauran maganarta. Da sauri ta dinga jan jiki tana matsawa har takai karshen gadon. Ta takure jikinta. Gefen gadon yazauna ya fuskanci idan take. Cikin muryarshi da ta kara budewa saboda bacin rai ya kalleta sosai yace. "Zo nan" Yana bubbuga kan katifar kusa dashi. Girgiza kai ta shiga yi tana kara matsawa jikin gadon kaman zata shige cikinsa. "Bazai miki kyau ba inhar na karaso na jawoki da kaina" Ya fadi a gajiye. Muryarshi da yanayin shi sun tsorata husna. Wasu hawaye suka gangaro mata. Kallonta kawai yakeyi. Gani tai bata da wani zabi. Batason me yake nufi da ita ba. Ko menene bata son yazo inda take ya janyota. Bataso hannun shi ya sake kaiwa jikinta. Bataso sam. A yanayin daya fadi maganar tasan zai aikata. Saboda bata ga wasa a fuskarshi ba. Gata Allah ya zuba mata tsoron tsiya. A hankali taja jikinta ta matsa tsakiyar gadon tana hawaye. Kallonta yake yi. Yanda duk ta firgice ga hawaye wani nabin wani. "I really don't want to repeat myself" Ya fada yana kallonta. A yanda yake jin shi komai zai iya faruwa. Matsowa tai inda ya nuna mata. Jikinta ko ina kyarma yake. Yaja wani uban tsaki a zuciyar shi. Daga shi har ita auren nan da akai musu an shiga rayuwarsu ya kula. Kalli yanda jikinta yake kyarma kamar wanda ta ga wani mugun abu. Ranshi ya kara baci. Bason tabata yake ba. Bata jin magana ya kula. Ya kuma rasa dalilin dayasa take da karfin bata mishi rai har haka. Bayason raini. Inhar yan son rage matsalar zaman su dole ya koya mata guje ma bacin ranshi. Duk tsanar datai masa kuwa. Dan haka ya kamo hannuwanta da baisan mai taje ta tababa sukai sanyi karara haka. Hannu daya ya saki. Yakai shi fuskarta ta janye. "Stay still" Ya fadi da wata irin murya da tasa ta tsayawa. Wasu hawayen suka kara zubo mata. Hannu yasa ya goge su yana fadin. "Bana son ganin hawayen nan. Magana nakeso muyi. Kina jina?" Husna kam a tsorace take. Kai ta daga mishi. Tana kokarin tarbe hawayen ta kasa. Hannu yakai ya dago mata fuska. Ya tsani yanda duk da hawayen fuskarta tayi kyau. Cikin idanu yake kallonta dan yana son ya tabbatar da sakon shi ya kai mata. "Yau ya zama ranar farko da zan aiko miki abu kisa a mayarmun. Matsalolin da nake ciki sun mun yawa bakuma nason kara su da gulmace gulmace tsakanin hadimai na, cewar matata ta raina ni" Yanayin abinda tagani a idon shi sai taji sam abinda tai masa din bata kyauta ba. Sai dai shima yanayin da ya saka ta shiga da wanda ta tabbatar yanzun haka ammar yana cikin fin nata bai musu adalci ba. Bata son yanda jikinta yake bin umarninsa. Hannun shi dayake taba mata fuska take son turewa. Saidai bata son bijirema umarninsa. Bata son mai zai iyayi ba. Ga dakin ya kulle hakanma shi yafi daga mata hankali. Kai ta daga masa alamar. "Eh" A dake yace. "Talk to me da bakinki bana son magana da kai" Sai da ta hadiye wani miyau sannan can kasan makoshi tace. "Eh naji" "Good girl" Ya fadi yana cire duka hannuwanshi daga jikinta. "I am waiting" Ya fadi a kagauce. Saida ta sa hannu ta goge fuskarta sannan tace. "Me zanyi kuma?" "Kinmun laifi and bakisan me ya kamata kiyi ba kenan?" Da wata sabuwar tsanar shi tace. "Kayi hakuri" Jinjina kai yai ya mike daga kan gadon. Inda ya cilla mukullan dakin ya dauko. Yana budewa wata hadima zata kwankwasa. Da sauri ta tsugunna kasa tana fadin. "Allah ya kara maka lafiya" Ko kallonta bai ba ya wuce. Tashi tai ta karasa cikin dakin da sallama. Ta tsugunna ta mikama husna ledar hannunta. Karba tai ta ce mata zata iya tafiya. Dan ta kula inba tace su tafi ba haka zasuyita tsugunno. Zuciyarta yanzun bata natacce take ba. Ture shi da abinda yai mata tayi gefe daya sai zuwa anjima. Ta bude ledar ta zazzago kayan ciki. Katin wayar ta dauka ta kankare su duka. Ta lalubo wayarta tai loading hannunta ma rawa yake. Kaman yanda zuciyarta ke rawa. Numbar ammar da take kamar tambari a zuciyarta saboda zaman datai ta saka ta danna kira. Da duk ringing din da zatai da yawan hawayen da suke zubo mata. Sai da ta yanke bai dauka ba. Ta sake kira bai dauka ba. Saida ta jera kira biyar bai dauka ba. Tanajin zuciyarta kamar zata fashe sabo da fargaba. A karo na shidda ya daga muryarshi can kasa yace. "Hello" Ko a mafarki ko a ido biyu ko a cikin dandazon taron jama.a zata iya gane muryar ammar dinta. Sai yanzun dataji muryarsa tasan kewar sa da zuciyarta tayi. Numfashinta har wani barazanar daukewa yake. Cikin murya mai matuqar rauni tace "Nawan nice." "Husna ta" ya fada tasan shi sosai hakan yasata fahimtar yanayin muryarsa da alamar rashin yarda da cewar ita dince ta kirashi. Shirun da yaji tayi ne yasa shi cewa "husna da gaske kece? Tawan kimin magana dan Allah." Muryarta na rawa tace "nice ammar." "Ya Allah" ya fadi yai shiru. Tasan kuka yake daga yanayin muryarshi. Can kasan makoshi cikin kuka yace. "Husna dan Allah kice mun mafarki nake. Kice abinda suke fadamun ba gaskiya bane." Itama kuma kukan na neman cin qarfinta tasan idan ta kuskura ta fara batasan ranar barinta ba. Dole ta zama mai qwarin gwiwa tai masa magana. "Ka saurareni....wallahi bana son auran nan bana son wanda aka auramin ban taba son kowa ba sai kai ammar ka yarda dani." Tun da take bata taba jin namiji saurayi babba kaman ammar na gunjin kuka haka ba. Kukan shine ya karasa karyar mata da zuciya. Bata san sanda kukan ya kwace mata ba. Sun fi mintina goma sun kasa magana kamun ya samu yace. "me yasa zakimin haka? Ke baki san irin son da nake miki bane? Haba babyna komai da nake nema a rayuwa don na aureki ne." "Nasani nasan haka wlh ta fada" zuciyarta na wani tafasa. Lokaci daya zazzabi ya rufeta ruf. Wani irin kuka take daga zuciyarta yake fitowa dan hawayen ma sun daina zuba. Cikin kuka ammar yace. "To ki kashe auren nan indai kina sona da gaske ba qarya kikemin ba husna" Bata san ya akai ma bata taba kawo ma ranta wannan shawarar ba a tsahon sati biyu datai a wannan qaddararren gidan. Wani sanyi taji a zuciyarta ta wanni fannin. Hannunta tasa ta dafe kirjinta saboda zafin da yake mata. "Ammar zan kashe auren nan na maka alqawari zamuyi rayuwarmu tare." Tanajin yanda ya sauke ajiyar zuciya. Muryarshi harta shige saboda kuka. "Husna ina sonki da yawa nasan ba zaki taba barina ba wallahi tun jiya dana dawo aka fadamin na dauka zuciyata zata fashe ne tunda nazo daki na kwanta jiran mutuwata nake...husna kece numfashina." Murmushi tai duk da halin da suke ciki bai hanata jin son shi har ranta ba wanda ta jima bataji irinsa ba. "Nima kasan ina sonka aiko?" "Da auren wani akanki husna zai wahala zuciyata ta yarda da hakan" Ya fadi a raunane. Da sauri tace. STORY CONTINUES BELOW "Zan kashe auren nan. I promise you nawa" Hira sukai tayi abinsu yace mata bara ya tashi yai sallah yai wanka. Bata bari ya tafi ba saida tasa yai mata alkawari zaici abinci tukunna. Duk da taji muryar ammar da alqawurransa masu sakata natsuwa. Itama ta masa alqawarin da bata san yanda za.ai ta cika shiba. Wani farin ciki take ji ammar bai tsaneta ba yana sonta har yanzun. Wani bangare na zuciyarta yana son nuna mata kuskuren abunda suka aikata. Ita kam koma menene bai dameta ba a yanzun da wutar soyayyar ammar take tsarga mata. Kwanciya tai kan katon gadon maganganun su na mata yawo. Sanyi taji tanaji dakyar ta iya sakkowa daga kan gadon ta kashe AC din dakin ta koma ta kwanta. Ta lullube amman jikinta kyarmar sanyi yake saboda zazzabin da ya lullubeta. A haka asabe ta shigo ta sameta. Da gudu ta sauka kasa ta je ta fada a kira kamala a gaya mishi ya kira prince ishaq uwargida ba lafiya. * Prince ishaq kam tunda ya fita daga dakin husna. Ya sa aka kaishi lambu yai zamansa. Dan sam zaman gidan duk da bangaren su daban dana natacce ya fita daga ranshi. Baya son yanda take bata masa rai tana saka shi yana abu dan dole. Yana kishingide kan daya daga cikin kujerun dake lambun ya lumshe idanuwanshi yana tunanin kalar zaman da zasuyi da natacciyar nan a abuja. Wayarshi ta kama ruri. Yanaji ya share sai da tai har sau uku. A na hudunne ya dauko batare daya duba ba ya amsa ya kara a kunne. Cikin ladabi kamala ya gaishe dashi kamun ya fada mishi cewar husna bata da lafiya. Ya bude idanuwan shi a hankali yanajin tamkar duka nauyin duniya aka dora mishi akai. Ina amfanin wannan auren da babu komai a cikin shi sai matsala da takura. Yayi niyyar ya kira doc din kawai yaje gida ya dubata sai dai baya son karanta. Wannan kuma zai nuna cewar bai damu da matarshi ba wanda gaskiyane. Yadai damu da kare mutunci da martabar gidansu. Dan haka ya kira cikin hadiman wajen yace ai ma driver dinshi magana yazo au tafi. * Yana shiga gida bangaren husna ya nufa. Ya sallami hadiman da suke zagaye da ita. Gefen gadon ya zauna. Yanda yaganta sai ta bashi tausayi. Hannu yakai ya taba goshinta yaji shi kamar wuta. Cikin rawar murya tace. "Karka sake tabani.... Bana so" Bai san sanda murmushi ya kwace masa ba. Cikin taushin murya yace. "Save it saikin warke. I am stuck with you like you are stuck with me. Badon ina so hannuna ke kaiwa jikinki ba" Baya son jin kanta. Saboda shi ya kamata ya daga mata kai. Ba wai ita ba. Duk da yasan abinda ya kamata yai mata. Saidai bazai karya alkawarin daya daukar ma kanshi ba. Doc dinsu ya kira. Tashi yai ya shiga toilet dinta. Ya wani yamutsa fuska ganin pants dinta da bra data wanke. Karamun towel ya dauka ya jiko shi ya matse ya fito. Bargon da take lillibe dashi ya janye. "Banaso" ta fadi dakyar. Ko bi takanta baiyi ba. A goshi ya fara dora mata towel din. Ta zabura saboda sanyin da ta kara ji. Hannuwanta duk biyun tasa tana rike nashi. Dayan hannun shi yasa ya rike nata duka biyun gam. A dake yace. "Bana son gaddama. Ba yanda za.ai muyi tafiya bakida lafiya. I am not rescheduling saboda ke" Bata da karfin yin fadan. Ba kuma tason yana tabata. Musamman yau dataji muryar ammar. Sai ta sake tsanar shi. Wasu hawaye suka gangaro fuskarta. Bata manta abinda yai mata ba dazun. Da kuma wanda yake mata yanzun. "Ka sakeni please. Dan Allah ka sakeni" Ta fada tana kallon fuskarshi. Hannuwanta ya saki yaci gaba da dora mata towel din a goshi. Ta bude baki zata sake magana dan taga bai gane me take nufi ba aka kwankwasa kofar. "Come in" Ya fadi dan yasan yace in doc din yazo ya ce a rakoshi bangaren husna din. Da sallama ta turo kofar. Ta gaishe da prince ishaq da ya amsa cikin mamaki. "Kayi hakuri. Doc amir ya samu flat tire a hanya saiya kirani coz ina kusa daku fiye dashi" Jinjina mata kai yai kawai. Ya nuna mata husna da take kwance. Duddubata tai sosai da aune-aune. Tace ma prince ishaq. Damuwace tai mata yawa. Tana bukatar hutu sosai. Ta bada list na prescription din data rubuta. Kira yai akazo aka karba. Doc din ta zauna saboda za.ayi allurai guda uku dan zazzabin ya sauka. Ba.afi mintina sha biyar ba aka kawo. Ai husna na kyalla ido taga allura ta mike zaune. Idanuwa cike taf da hawaye tace. "Wallahi na warke. Dan Allah karka bari taimun allura" Doc din ta kalli prince ishaq. Matsawa yai kusa da husna ya kamo hannuwanta. A tsorace ta rike shi sosai tana magiya. Tun tana karama harta girma sai an riketa ake mata allura. Bata sonta ko kadan. Ko wani za.ayiwa hankalinta tashi yake balle kuma ace ita. Hannuwan shi ya zame daga na husna ya tallabi fuskarta. Ya saba mu.amala da patients irinta da yawan lokutta a baya. Musamman yara kanana. Cikin idanuwa ya kalleta yace. "Pull yourself together. Babu zafi fa" A rikice husna ke girgiza masa kai tana fadin. "wallahi zan bika abuja karka bari tamun allura" Girgiza kai yai a ranshi yana fadin saikace zuwan shi abuja da ita zabi ne.1 Kamo ta yai. Ya dagota sosai ya rike rungumeta a jikinshi. Kiciniyar da take ta kwacewa ma taso ta bashi dariya. Sake matseta yai sosai a jikinshi hakan yasa ta yin luf. Alama yaima doc din cewar tazo tai mata allurar. Ganin tana kokarin zame skirt din dake jikin husna ya sakashi lumshe idanuwanshi. Yanajin yanda husna ta sake rukunkume shi da shigar allurar. Haka kawai yaji zuciyarshi wani iri. Yanda take rike shi yana saka shi jin wani yanayi da baisani ba kuma bama yason ya fahimta. . "Na gama" Doc din ta fada. Kai kawai prince ishaq ya daga mata. Ya nuna mata kofa. Ta tattara kayanta ta fita. Yana rike da husna har yaji yanayin numfashinta ya canza alamar bacci ya dauketa. A hankalo ya ajiyeta yana bambareta daga jikinshi. Da wani irin yanayi a jikinshi mai wahalar fassarawa ya fita daga dakin yana ja mata kofa.

Post a Comment for "WATA BAKWAI CHAPTER 4"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...