Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 9

SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 9

- - Post a Comment
SILAR GIDAN AIKI
CHAPTER 9


Yasmin da seemah suna tafe, Seemah ta kalleta tace" kawata inbazaki damuba inaso muyi wata magana, Yasmin tace" OK no problem inajinki kawata
Seemah tace" OK but zaifi kyau muje gida cos naga kina driving, murmushi yasmin tayi tace" ai bakomai inajinki

Seemah tace" alright kawata are you sure Mansur nasonki kuwa? Ni kinsan bazan cutar dakeba, amintarmu dole na fada miki gaskiya cos banso ki cutu arayuwa, Yasmin najin haka ta sama waje tayi parking tace amma meyasa kikace haka? Kinga wani alamune?

Seemah ta gyada Kai tace naga alamu, thought bansan dai ko zafin ciwo bane but yanda na fahimta Mansur don't like you at all, ba mum dinshi muka ganiba kafin Mu shiga ba? Yasmin tace" yeah she's d one, Seemah girgizakai tayi tace kawata tun kafin son Mansur ya zaman maki masifa please ki farawa koyawa zuciyarki hakuri dashi cos I don't think yanasonki, in fact Bari kiji Mansur Wallahi besonki!

Yasmin ne ta zare ido tace" na shiga uku wani abun Ne? Seemah tace muna tare dole na fada miki gaskiya, inzaki Iya tinawa sau tari frnds dinmu suna gulma akanki da Mansur wai ke kikesonshi shi bayasonki tun Ana boye maki har kikaji KO?

Yasmin ta sake baki tana kallonta tace eh na tina, seemah tace" good, toh gaskiya dole Mansur bazai so kiba, kalle dressing din da kikeyi, Party wanne ne bakya zuwa, kina ganin namiji kamar.Mansur zai sokine? Wanda tun farkon haduwarki yake miki nasiha akan dressing dinki da irin kawayenki, Yasmin to be frank Kinsan bakyaji KO? Beside ma mahaifiyarshi zata yarda ya aurokine? Dama abun kanki zai tsaya da sauki, to tarbiyyan yara, anan ake gane matar da yakamata miji ya auro

Wannan rayuwar gaba daya duk karyane, Wanda suke zigaki yanzu suna Ina? Basun kyalekiba! Dafa kanta Yasmin tayi tana haweye, Tace tabbas Gaskiyane maganarki inshaa Allah zanyi kokari na gyara rayuwata, Ashe dalilin da yasa kenan Mansur yake guduna! Yanzu bashi kadai ba kenan maza da yawa bazasu aureni ahakaba!

Seemah tace" hmm ba abun tada hankali bane AI, just Mu gyarene gaba daya sai muga dakyau, basai munje muna rawan jikin wajen samariba da kansu zasu kawo kansu cos yanzu kowa Neman mace tagari yakeyi

Yasmin tace hakane in shaa Allah I'll change for good kuma bazan sake cusa kaina wajen Mansur ba, ni dama nasan basona yakeyiba amma zuciyata taqi yarda yanzu da Kika fadamun da kanki inshaa Allah Zan kiyaye
Seemah tace" Amma naji dadi wallahi haka nakeson mutun Mai fahimta, inama yan Mata zasu dinga daukan shawarar da aka basu da kowa ya huta Wallahi

Yasmin tai murmushi tace" nagode Seemah da Kika hankaltar Dani, sannan suka Kama hanya, tundaga ranar Yasmin ta goge number Mansur tana rokan Allah ya hadata da Mai sonta Dan son maso wani koshin wahalane........!

****
Koda Su Yasmin suka fita, Mansur ne yai tsaki, Abdallah kuwa girgiza Kai yayi yace" yarinyar nan naban tausayi sosai cos tana Sonka, Mansur yace ni.kuma bana sonta KO kadan, Abdallah yace" then kindly tell her mana kalle kudin da ta kashe maka! Mansur yace Bari naji sauki Zan sanar da ita, Abdallah yace OK yafi dai

Sundau awa daya suna hira saiga Hajiya da kawayenta sunzo gaishe da mansur, dayar matar tazo da yarta budurwa suna shiga sukai 4eyes da mansur, nan take aranta tace" wow see handsome guy inama ace saurayinane danaji dadi, inajinta nace kwalelenki M.T na Nazeefa ne lol, tana ta kallonshi har suka Fita shi ko gogan naka ya hada rai!

Abdallah Ne yace kaganni dramanku da Yasmin yasa na manta da Zan Shugo na hadu da dad da mum sukace zamui magana nasan be wuce Akan meke damunkane
Mansur ya zare ido yace" abokina to mezakace musu!

Abdallah yai dariya yace" tsoro kakeji ace kana neman aure?

Mansur yace" wani aure Ina Neman aljana dai cos gashinan tinaninta ya kusan illatani

Abdallah Ne ya dafashi yace karka damu, da izinin Allah inaji ajikina zamu hadu da aljanarka

Mansur Ne yakaimai duka yace" zaka sani wallahi, suna wasa suna Dari ya doctor ya Shugo ya gwada BP dinshi saiga hajiyarshi

Yai Mata bayani yanzu B.P din ya sauka please ayi gaggawar bashi abunda yakeso a kwantar Mai da hankali sannan ya fito

Hajiyane tazo kusa dashi tace' Son meke damunka me make so pls murmushi yayi yace ke nake so mama na, shafamai Kai tayi tace" Allah yama Albarka, wayartane yai ringing ta amsa taje taho da kannanta wai basu gane ward dinba

  Tana fita Mansur yace" kasan da mum tace me nakeso saura kadan nace A auramun aljana shine kwanciyar hankalina

Abdallah ne ya kwashe da dariya yace Abokina kaso aure Wallahi, Mansur yace" aure AI abun sone

Abdallah yace hmmm we yanzu nagane wato ciwon soyayya kakeyi kenan KO? A yace saiga Su Hajiya sun Shugo marairaice fuska yayi, Abdallah ya kalle abokinshi yace" Allah ya shiryaka....Kwanan Mansur 3 a hospital aka sallamesu, Jikinshi yayi kyau sedai ramar da yayi kuma yayi baki, shi yanzu tinaninshi daya Ina zaiga other half dinshi sunan da ya chanza Mata kenan from aljanah to other half saboda yanzu yasan she's part of his life bazai iya rayuwaba seda ita +

    Abdallah kuwa Mum da Dad sun tsareshi dole saiya fada musu abunda ke damun Mansur..be musu karyaba ya fada musu komai, Sunyi matukar mamaki suka in Alherine Allah ya tabbatar

Bangeren Su Nazeefa kuwa tunda suka dawo gida bata Kara sakewa kowa fuskaba balle Mubin, Abubuwan da takeyi yanadan ba hajiya tsoro KO abinci Nazeefa zatayi bata tambayar me za'a dafa se abunda tai ra'ayi shi zatayi, Fita kam ba Wanda ma yake mata maganar ina zata ko Ina ta fito Dan ta sauya musu gaba daya

    Mubeen kuwa hankalinshi ba karamin tashii yayiba se yanzu yaji yana mugun kaunar Nazeefa, kullun seya bata hakuri amma tai burus kamar ba ita yakewa magana ba

Bikin Haleema da Mubin yanata matsowa, hankalin Haleema kwance, Mubin kowa dukda ankaishi wajen boka Dan samai son Haleema shi ko har yanzu beji sonta KO dayaba kawai zebi umarnin iyayanshine

WASHE GARI
    Kasancewar weekend as usual, Abdallah ne yazo ya dauke mubin suna zagawa ko zasu ga Nazeefa, Layin su Nazeefa sukazo, zaune suke cikin mota, sun dade Suna tinanin yanxu ta ina zasuganta cos basusan daga inda takeba balle suje, Sun kusan 20mins suna cikin moto Mansur ne yace Abokina kawai muje gida heart Dina na beating sosai, Abdallah Ne ya girgiza Kai yace" OK Abokina Allah ya bayyana mana ita duk na kosa muganta

Nazeefa kuwa tashi tayi da bikin ciki ya isheta ta rasa Ina zatasa kanta, Wanka tayi tazo tana shafamai taji kirjinta na mugun bugawa, Dafa kai tayi tace oh Allah ka kawomun karshen wannan bakin ciki, 1

Ji tayi bazata iya zama gidan ba tace bari naje gidansu Amira, Kaya ta saka ta fito,  tana fitowa taga wasu mutane cikin mota sun tadata sun wuce, Gabantane ya Kara bugu sosai tace" aranta tace wannan motar nada kyau, Allah ya bamu arziki na halal Ameen, Tafiya takeyi saiga Mubin ya biyowata ta baya horn yai mata ta tsaya fitowa yayi yace Nazeefa Dan Allah har yau Ina koranki ki yafemun kinki, ki tunafa Munawa Allah laifi ya yafe mana

   Kallonshi tayi idonta nason zubar da hawaye tace" Mubeen kaje na yafe maka, Shima kwalla yayi a ranshi yace" tabbas kaina na yaudara!

  Share hawayenta tayi ta Fara lafiya, Kara biyota yayi yasha gabanta yace" inazakije kizo inkaiki mana! Wani harara ta bankamai tace" ka matsamun a hanya ko na I maka ihun barawo, wawa gara kawai! Jikinshine ya tsoma rawa a da sauri ya matsa Mata ya koma cikin mota yana zubda kwalla

Tafiya takeyi yana kallonta har seda Tasha kwana, Gidansu Amira ta wuce, Sallama tayi Amira ta fito tace muryan wa nakeji kamar Nazee baby, Nazeefa kirkiro murmushi tayi tace" nice, Amira tana kallonta seda gabanta ya fadi, Allah yasa ba kowa a gidan Amira tace Na shiga uku meye sameki?

Nazeefa fashewa da kuka tayi, Amira ne ta janyo hannunta sukai daki, Take tambayarta meke faruwane duk ta Chan za

   Nazeefa nan ta kwashe labarin komai da komai ta fadawa Amira tace Sirri please, Amira tace ba Wanda zaiji

Amira ita kanta tayi kuka sosai amma ta kwantar ma Nazeefa da hankali akan Allah ma na sonta daya nuna Mata hanyar data dakko bamekyau bane, Kuma ta Kara hankali da samari, Sannan tace ta Kara addu'a sosai da istigfari komai zai dinga zuwa Mata me sauki tace Inshaa Allah

Ranar sun wuni Amira ta bata addu'oi Sosa I sannn suka tattauna akan inshaa Allah zasu fito da miji kowa ya huta

Mubin kuwa tunda Nazeefa ta fita hankalinshi a tashe, Yanaji ina ma Soyayyan gaskiya yake mata, Yana cikin tinanin hakane Haleema tace" tamai text  kamar haka...Angon 2weeks nawa, ya preparation....I love you

Yana ganin text din haushi yaji yamayi switching off na wayarshi, Ita kuwa tanachan da kawayenta tana jiran reply dinshi, saboda tace musu angonta na sonta yana kasheta da texts, kawayenta sukai shewa sukace er lelen mubin

Waya na hannunta taji shuru ba reply...kira tayi ta rage volume ita kadai takeji, kawai taji _the number you're trying to call is kindly switch off_ bata jira Please try again letter ba tai maza ta kashe wayar Nata


Nazeefa kuwa sai 5:00PM Ta dawo gidan, Hajiya sai masifa takeyi wai ba AI musu lunch ba, Bare dinner, Mubin ne yace hajiya zata yine ai

Hajiya sama tahau, Nazeefa tai tsaki tace" Wallahi ba abincin da zanyi a gidan nan tab,

Mubin kuwa Son Nazeefan da yakeyi yasan idan batai abincin nan ba akwai matsala, Dasauri ya hau mota yaje  restaurant ya siyo musu abincin da zai ishesu ya Shugo kitchen yasa a food flask, yazo dining ya jera... Nazeefa kuwa kallonshi takeyi aranta tace wahalalle

Miko mata Nata yayi ta shiga daki ta zauna taci tazo ajiye plate din suka hadu da Hajiya tace" Nazeefa sannu da kokari wai Dan hawana Sama har kin girka abinci? Sannu

Yauwa tace but KO kallon inda take batai ba ta shige daki, flat tayi akan gado tana tinanin abubuwan rayuwa, it's her high time daya kamata tasan Ina ta dosa cos lokaci na tafiya

Kwafa naga tayi kome ke ranta ohoooBayan Sati Daya
    Biki Nata matsowa Hankalin Nazeefa yai mugun tashi, Dan wani kishi da takeji a zuciyarta, Sam bazata iya zama a gidan ba tana ganin mubin tare da matarsa kawai ta yanke shawarar zata bar gidan Dan bataga amfanin zamanta a gidan ba

Su Faeez da faeeza sun dawo saboda an musu hutu, A ranar da Nazeefa zata bar gidan sai kai kawo takeyi a cikin gidan, Faeez Ne ya Lura da ita yace" wai yayane Nazeefa? Ko baki da lafiyane? Girgiza kai tayi tace ba abun dake damuna, Ta kalleshi tace" Faeez Ya kamata ace inada number wayarka, koda wata Rana! Ohh Yace kumafa hakane, dakko biro da Yar memo tayi Wanda ta Rubuta numbers din kawayenta da duk wani Abu daya faru da ita a rayuwa, ya na fada tana rubutawa,Sannan tace tagode ta maida Yar Memo dinta Chan kasan kayanta

    Faeez ne yace sorry karfa kici na cika damunki, Nazeefa kamar kinada damuwa KO naga duk kin chanza, Kirkiro murmushi tamai tace" ba  doleba inason ganin iyayane tun Ina karama fa aka kawoni nan gidan wacce ta kawoni ba ita ba labarinta, Nan take tausayinta ya Kara kamashi yace Hakane amma kiyi hakuri Ki zauna nan kamar gidanku, Kallonshi tayi tace" OK dear, itadai tana ganin hankakin Faeez,

Sunsha hira Sosai sannan yadan fita wajen abokanshi

Ita kuwa faeeza uwar iyayi a matsayinta na mace ko kula Nazeefa batayi, illama tsanar ta datai,

Misalin karfe 1:00PM Nazeefa ne zaune a parlor tana nazarin yanda zatabar gidan! Faeeza tazo ta tsaya Mata akai tace" ke jeki dakkomun ruwa a kitchen, KO sauranta batai ba, ta Kara Mata magana, Nazeefa cikin zafin rai tace" KO yayanki Mubin yayi kadan bare Ke! Karan kada Miya! sake baki tayi tana kallonta

******
   da daddare Nazeefa ta dakko Yar jakarta tana Kallon Kofar Mubin! Aranta tace" Inasonka Mubin amma SILAR KA Zan bar gidan nan! tai ajiyar zuciya ta fito tsakar gidan se rabe rabe takeyi har takai bakin gate

Tana zuwa tace" baba me gadi taji shuru, Alhamdulillah tace baba me gadi bayanan ya tafi sallah, Juyawa tayi ta Kara kallon gidan taji hawaye na shirin kubcemata, Dake zuciyarta tayi ta fita tabar gida, cikin dare gudu takeyi Kar wani yan gidan Su ganta

Gudu sosai tayi taji ta gaji, laluba jakarta tayi taga tanada 510 naira, cire 10 naira din tayi tasai pure water sannan Tasha, lafiya takeyi Sosai saboda ta gaji da gudun ga dare nayi, Hannu tasa tana tare mashin, kowa yaki tsayawa, Chan wani ya Isa yace" baiwar Allah Ina zaki haka? Nidai ba Dan achaba bane Ina zaki?

Tace ka kaini KO Ina Dan Allah tana magana tana haki Dan ta mugun gajiya, daukarta yayi sunyi tafiya kusan 30mins yace to KO sauka niga hanyar da Zan shiga nan tace tagode

tunda ya sauketa ta fara tafiya a kafa, tayi nisa Sosai da unguwar data fito gashi garin dare yayi kuma batasan ko inaba ta sama wani Dan kango ta shimfida zani ta kwanta, saboda gajiyar datai tana kwanciya bacci ya kwasheta

Washe gari Tun asuba ta tashi ba ruwa tai taimama tai sallah

Tashi tayi ta kakka6e kayanta, da tambaye tmbaye tayo tasha (inda ake hawa mota) cos zatabar garin ne gaba daya, tsayawa tayi tana tinanin ta ina zatahau moto cos 500 ne Gare ta

Nazeefa na tsaye tanata waige waige, Chan gefe ne taji Ana Kano, tace ba kano zataba, taji Ance Katsina tace banan zataba, Wasu mutane ta gani suna YOLA YOLA. taji sunan garin ya Mata saboda haka taje ta tsaya a Chan baya,

Gashi bata da kudin moto,

Chan gefen Taga dandazon mutane wasu mutane suna ihu gobara gobara (Wuta )gaba daya hankalin mutanan yai wajen gobarar, ita kuwa bot ta shige ta loda kayan dake bot din akanta, Wanda zasu tafi Yola suka hanzarta suka shige motar cos tsoro sukeji saboda Motocin wajen karsu kama da wuta,

Alhamdulillah tace aranta Su kuma Allah yamaida musu abun dayafi alheri,

Tafiya suke duk ta galabaita ga yunwa ga gajiya ga kishir ruwa, duk ta kosa Su sauka

Chan yamma Suka sauka! Tinaninta daya idan aka ganta a bot din, tsurewa tayi sai zare ido take yi.

An sauka kowa yazo zai dauka kayanshi kawai akaga mutun ya bullo! Sai innalilillahi akeyi, wasu sun tausaya wasu sunji tsoro sosai

Kamata akai akace ta fada gaskiya ita aljanace ko mutum? Tace ita Wallahi mutun Ne, Wani mutun Ne yazo yace" shi gaskiya besantaba amma duk Wanda kukagani Haka kawai Ku kyaleshi, yanzu ita kadai tasan wahalar da Tasha ko ince halin da take ciki

   Mutane da yawa suka amsa da tabbas hakane, Nazeefa kuwa inbanda kuka ba abun da takeyi, Wani yace Ku kalleta dakyau daga gani da gatanta, but duk yanda akwai sedai ahankaline Kawai, kunsan wasu mutanan namu sedai muce Allah ya shirya Amen

nan masu kirkin suka harhada Mata kudi, wasu suka sai Mata abinci, masu bata kayan sawa nayi kowadai duk Wanda Allah ya horemawa ya bata

    Wani Babban Me kudine yace indai ita tasan mutun Ne to zai dauketa yakaita gidanshi, nan take ya kira matarshi tace OK badamuwa cos yaro na kowane AI

a wajen aka tambayeta ita Yar inane! Tace ita tun tana karama aka satota ba tasan kowa ba yanzuma daga gidan yan Kai Kai ta gudu!

Kowa yace Allah Sarki aka tausaya Mata, Wannan Alhajin ya tafi da ita gidanshi

Bangaren Mansur kuwa Bacci yakeyi yana mafarkin Wai ga aljanarshi nan tanashan wahala yazo zai ceceta kenan ya tashi a Bacci yaganshi rik'e da pillow a kirjinshi yana other half other half.....

Daya tashi ya ganshi Rik'e da pillow yaba kanshi Dariya amma daya tino halin da other half dinshi take sai ya shiga tinani Sosai

Post a Comment for "SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 9"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...