Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 7

SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 7

- - Post a Comment
SILAR GIDAN AIKI

CHAPTER 7

Maganar da Nazeefa tayi Yai bala'in batama Haleema rai daurewa tayi tace" kinji kunya dai, Nazeefa tai tafi tace kedai kikaji kunya, me biyo saurayi har cikin gida Ashe bakida class, Haleema maganar tai Mata zafi takai Tafin hannunta kan fuskar Nazeefa ji kake Tass, Itama Nazeefa ta rama Tasss tasss har sau biyu
Haleema tace ni kika Mara? Nazeefa tace yes who are you, an Mara din banma kinci darajar cikin gidane da ace a titin gwamnatine sekin fi haka dakuwa kuwa, Haleema ta janyo Nazeefa, zasu Fara dambe Saiga mubin ya shiga tsakiyarsu, Haleema taji dadi kamar me Dan badan Allah ya kawo mubin ba tasan zata daku ne, cewa yayi meye haka kukeyi, Nazeefa tai tsaki ta wuce Daki
Haleema tace" wallahi sai na gyarawa Yar aikin nan hankali harni Zata Mara! Mubin yace" duk laifinkine, yarinyar nan fa bata shiga harkanki kece kikeso Ki matsa Mata! Uhmmm tace" saina fadawa mummy, Rik'e Hannunta yayi yace please inhar kina So na karki Bari Su Hajiya suji, nandai yai Mata wayau yace" AI ba class dinki bane ma ace kinyi fada da Nazeefa! +

Hakane tace" sannan ya riko hannunta sukai falo, drinks ya kawo Mata da snacks taci sannan sukai hira daga bisani tace tanajin Bacci ta shige dakinshi ta kwanta

Dayaga tayi bacci ya fito falo ahankali kamar barawo, Room din Nazeefa ya shiga ya sameta A tsaye tana ninke kayan wankinta da tayi Rungumota yayi ta baya, afirgice tace Mai meye haka Mubin, banason irin wannan iskancin Gaskiya, ka fitar mun a Daki, yace" maganar da Kika fada dazu da gaske kina sona

Shuru tayi, Yace sai kince kinasona Sannan Zan fita a dakin nan! Rufe ido tayi tace" yes I love you....besan sanda ya rungumeta ba yace" Nazeefa na gode, Rungumeta dayai taji wani iri a jikinta

Rufe ido tayi, tace" mubin please ka fita banason ganinka anan room din

Dariya yayi yace" i can't believe kina sone Nazeefa, Ashe zanga wannan ranar! I love you I want to spend d rest of my life with you sannan ya fita yana wani smiling

Ita kuma bawai sonshi takeyiba kawai dan ta batawa Haleema rai ta fada haka, aranta tace na shiga uku *SILAR GIDAN AIKI* na so ya janyomun wani Abu

Falo ya wuce ya zauna a kujera, ya zaro wayarshi ya Kira friend dinshi
Dr Bashir...yake sanar dashi finally Nazeefa tayi accepting tana sonshi, Tarkon shi ya kamata, Wow Dr Bashir yace'' I'm happy for you sai ka Iya allonka, kasan takunka!

Yai kasa kasa da murya yace" yanzu Zan koya Mata wayau AI, wulakancin da tai mun a baya yanzu zata gane kuranta, Dr Bashir yai dariya yace kaifa kwararren Dan yaudarane abokina, ni dama dakace kanasonta nasan abunda kake mawa, that thing ko? Kwashewa da dariya sukai, Sannan yai cutting din call din

***
Su Hajiya sunje sundawo boka yayi aiki sosai akan Mubin, ya dasamai son Haleema a zuciyarshi, ba fashi ita zai aura, hankalin Hadiza a kwance, sannan suka dawo gida

mubin ne zaune saiga Su Hajiya sun dawo, Hajiya Hadiza ta kalleshi tai wani murnushi tace" Son inlaw, Gaisheta yayi yace" kundawo? Tace" eh Hajiyarshi kuwa se tambaya suke ina Haleema yace tana bacci, sukace OK

Hajiya kuwa tausayin danta ya kamata wani irin son abun duniyane Ya rufe masu ido da har zasukai dansu wajen.malami but idan ta tina zasu karya asirin cikin sirri sai hankalinta ya kwanta

Misalin 12pm Haleema ta tashi a bacci, da sauri ta fito falo taga hajiyarta tazo ta zauna kusa da ita 1 hour kawai suka Kara a gidan tace" zasu wuce Abuja bazasu Kara kwana ba, Da zasu tafi Alhaji ya basu 1Million kyauta sannan yai Mata godiya itama tace tagode

Dazasu tafi Haleema sai wani iyayi takema ma mubin alamu yai mata da ido yace" bamu kadai bane fa, sannan ta hankalta

Nazeefa kuwa na kallonsu ta window tace" akin banza, Mubeen nawane banakiba,

Bayan Kwana biyu, Nazeefa ne Zaune tana nazarin Wani Abu, Mubeen yazo ya sameta yace" kizo ki rakani hospital Zan dakko wani Abu please, Kallonshi tayi tace" I can't salon Hajiya ta ganni kasan Bataso taga muna magana KO?Smiling yayi yace" karki damu ki fita Zan sameki a hanya

Haka KO akai, karya taje ta hadawa Hajiya ta amince, ta fito wajen
Bata dadeba saiga Mubeen ya fito a mota ya sama waje yai parking sannan ta Shugo

 Slow driving yakeyi Wanda kana gani kasan Masoyane a cikin Car din,

Kallonshi tayi tace muyi sauri mana kar Hajiya tace na dade, Parking yayi yace dama magana nakeso muyi Kinga tunda kina sona Soyayyan Mu dole ya zama secret karki  yarda KO masu gadin gidan Su sani
.      shuru tayi na tsawon lokaci daganan ta Fara tinani

      Wajen idonta yazo ya hura ta dawo daga tinanin da takeyi yace why kikai shuru? KO akwai wani abune? Tace ah ah Karka damu xanyi yanda kakeso

    yace good My NAZEE.....wannan kenan Kwanci tashi asarar mai rai, Wani Shakuwa ta shiga tsakanin Nazeefa da mubin, Sonshi ya kamata sosai da kullun suna tare idan bataganshiba batajin dadi, Ko wajen aiki yaje saita damuwa akan ta kosa ya dawo, ita batasan yaudararta yakeyiba Dan Ko alamu bata ganiba.. +

     But Kullun indai Zasu hadu da Mubin setai Mafarkin Aljanin nan Nata yana Mata murmushi yana ce mata kar taje wajen Mubin Idan ta farka bacci sai taji ta tsana Mubin tanason ganin Aljanin mafarkinta, da an dau mintina kadan sai taji tana tsananin son haduwa da mubin, Wata zuciyane take ce Mata karta biyewa mafarkin nan duk shirmene kuma dan tanason Aljanin da tagani yake sata mafarkin

  Bangaren Mansur Turaki kuwa, Kullun seyai mafarkin shima ga waninan yana son kusantar Nazeefa, a firgice yake farkawa ya shiga toilet yai alwala yazo yai addu'a, A yanzu ya gane Budurwan da yake haduwa da ita ba Aljana bace! Mutun ce, da yake Mansur Dan baiwane, Se ya fassara mafarkin a Duk yanda akai yarinyar nan da yake gani tana Neman tai mako, shi kuma ya kudara duk randa Allah yasa ya hadu da ita saiya Mata magana Dan yana jinta sosai a zuciyarshi

Saboda yawan Mafarkin Da Mansur yakeyi ya zama so silent sosai, Mafarkin yana tadamai da hankali sosai but ba yanda ya Iya hakanan Sedai yaita addu'a inhar mutun ce Allah ya bayyanar da ita

    Bangaren Su Mubin kuwa, Son mubin ya Riga ya ringaye Nazeefa, Club Club ba inda bata zuwa, Mubin ya bude Mata ido sosai, yanzu Nazeefa ta zama Yar gayu, balle jikinta da ya amsa mayuka Kala kala yayi kyau yayi kyalli, Kowa se wa Mubin magana yake Ina ya samo wannan fine baby haka, sedai kawai yayi dariya, Ita kuwa Nazeefa Sam bata taba kawo Mubin bazai auretaba, ta sake jiki dashi kamar Wanda yai ma asiri komai ma yi sukeyi.

Hajiya Da Alhaji Sada se su tafi China, Dubai siyan kayan akwatin lefen mubin, Sai subar Nazeefa da Mubin a gida, Mubin KO ya sama a bun da yakeso cikin kankanin lokaci ya chanza Nazeefa, Wani crazy dressings da takeyi baza kuce Yar Aiki bane, KO yaushe suna manne da juna kamar Mata da miji, in fact ya gama bata Nazeefa Dan KO be nemetaba Ita Zata nemashi, Nazeefa yanzu ta waye duk ta manta KO ita wacece, Amma kuma abun dake bata tsoro wani lokacin idan ta tina kalmar MUBIN na cewa Karta yarda wani ma a gidan nan ya gane suna soyayya, Dan inhar ta Bari wani ya sani to daga ranar seta raina kanta

Idan ta tino sedai ta shige daki taita kuka, tana istigfari, ita kanta iskancin da sukeyi ba So takeyiba, dan Abun na damunta balle idan ta tina Asalinta

Haka dai Mubin da Nazeefa sukadau lokaci suna tacewarsu Hankalinta kwance shima haka

Bangaren Mansur turaki kuwa, Yawan mafarkin da yakeyi da Nazeefa ya wuce tinani har ya Dan chanza yayi zuru zuru, Gashi ko ya Kira number abokinshi Baya Shiga

Bayan kwana biyu
     Mansur Turaki yana zaune a garden din gidansu dagashi sai gajeren wando yana shan iska, bodyguard sun zagayeshi yana latsa waya, Maigadine ya zo da sauri ya tsugunna a gabanshi yace" Oga Wani na son ganinka Wai shi Abdallah

Mansur ne ya kelleshi yace" haba Sau nawa zance maka idan har Abdallah ne yazo direct ku barshi ya Shugo

Mai gadi kasa yai dakai yace" kayi hakuri ranka ya dade, Ya tashi Da sauri ya bude gate yanaba Abdallah hakuri

Abdallah yace" karka damu nasan dokan gidan commissioner ne! gateman iso yai mai har inda Mansur yake, nan Bodyguard din suka gaisheshi Abdallah ya amsa

Mansur yace" excuse us kuje Ku huta zamui magana da Shine, sukace sungode!!
  
    Abdallah ne ya karemai kallo yace" Abokina meke damunka? Murmushi karfin hali M.T yayi yace" bakomai fa

Abdallah yace sedai ka fadawa wani badai niba, M.Turaki yace" hakane kasan meye? Abokin nasa yace seka fada!

Since that day damu ka rabu wallahi mafarkai nake tayi akan Aljanar nan, se indinga mafar kai wai gamunan muna soyayya amma se wani yazo yana dauke Mata hankali, this n that that

Abdallah sake baki yayi yana kallonsa yace" abokina na you? Mansur yai murmushi yace" yes nine mana kana mamaki KO?

Abdallah yace AI ni dama nasan Kyan junankune ya rudeku zakace wata Aljanah yanzu dai you mean Kanasonta kawai!!

M.T ne yakaimai duka yace" bakyaji abokina haka nace maka

Yace alamu sun nuna haka mana, Mansur yace" Yes I love her....

Abdallah yace" Kason gidansu KO? M.T yace ina nifa bansaniba Allah dai yasa ba aljana bace,
Abdallah yace" in shaa Allah mutun ne but yanzu meye abunyi?

Mansur yace abunyi kawai shine Mu shiga gari nemanta KO Allah zaisa Mu dace

Abdallah yace hakane, Nima a tsaye nake Dan temakawa maka abokina Dan kA chanchanci hakan

Mansur yace" Allah ya bamu sa'a Ameen Chan Gida kullun Mahaifin Nazeefa cikin mafarkin yarshi yake, haka mahaifiyarta ma da Nazeefa take kwana da Nazeefa take tashi, Yau Safiyar Asabar Mahaifiyar Nazeefa tasa mahaifinta a gaba tana kuka tana rokan gafararshi akan abunda tayi
    Ko kallonta beyiba balle yace Mata wani abun, Kuka sosai takeyi da har seda makota suka Shugo, Kowa yasan be wuce kukan har yanzu ba'asan inda Nazeefa takeba
    Malan Nalado Kuwa ko tausaya Mata beyiba cos duk halin da suke tsince Kansu itace" ace wai mace bazatai hakuri da abunda Allah ya hore mataba se ankai yarinya aikatau Dan samun abun duniya
    Yan makotan gaba daya sun bata rashin gaskiya, kuma suma yan kauyen sun hankalta, sannan suka roka Malan Nalado daya yafe Mata, shidai bece komaiba damuwarshi yawan mafarkin Nazeefan da yake yasan duk inda take tana cikin wani hali, as usual tashi yayi ya barsu a tsakar gidan ya tafi masallaci yai alwala yaita wa yarshi addu'a da sauran yan uwa musulmai +

****
   Bangaren Haleema kuwa zaune take a kan gado ta mik'e kafafu tana kwalliya, phone dintane yai ringing tana dubawa taga ansa "MY MAN" wani murmushi tayi tai picking tace" ganinan zuwa, Wani Hotel ne? Ya fada Mata tace OK soon Zan iso

Fitowa tayi da damammun kaya, Tazo ta zauna kusa da mahaifiyarta tace" mum an going Kinsan yaune bikin kawata KO? Zantafi zanyi kamar 4days sannan indawo! Hajiya Hadiza ne ta kalleta tace" oh har ya matso kenan? Haleema ta murtuke fuska tace" Eh mum Dan taga take taken mahaifiyarta in batayi da gaske ba ba barinta za tai ba kuma bataso tai mata fuck up, Wayantane ya Kara ringing tai maza ta kashe tace" Mum kinga suna jirana ko

     Kallonta tayi aranta tace" haba nima na samu na shakata,  Bude bag dinta tayi ta ciro mata bandir din kudi na 50K tace Mata gashinan, a kula sosai kuma.   
    Rungumeta tayi tai Mata kiss tace thanks Mum nagode, I'll miss you sannan ta Kama hanya ta fita

     LUKMAN ne a hotel se jiran Haleema yakeyi, Batai 20mins ba sai gatanan ta iso Hotel din, kafe da ido yayi KO kiftawa bayayi, murmushi tamai tace" wannan kallon fa sai kace zaka cinyeni? Yace bazaki gane bane nida na kusan rabuwa dake nasan dagayau kafin Mu hadu sai wani ikon Allah

    Kai goshinta tayi wajen nashi tace" look deep into my eyes ance maka KO auren wanchan garan (Mubin) nayi Zan Iya rabuwa dakaine? Rungumeta yayi yace" are you serious?
  
     Tace" yes I'm serious nasha fada maka bazan Iya tarayya da kowani namijine face Kai, you're my everything bana ce maka ni bawai son mubin nakeyiba kawai dan kudinsu nake sonshi sannan kuma bansanshi da wannan matsiyaciyar yar aikin nakeba gwanda na raba Su, Kuma KO aurenshi nayi ai nan zamu dinga haduwa Muna shanawarmu
   Kara hugging dinta yayi Tide nan ya Fara sarrafata yanda yakeso itama haka tana maidamai da martani

Hmmm Ashe Haleema itama A ce Lukman kuwa shine abokin tacewarta, sun Dade da juna suna sheke ayarsu amma ba Wanda ya sani.... Kunji dalilin da yasa Ashe takeson Mubeen....muje zuwa

Haka suketa hutawarsu Har 4 days tayi, A ranar da zasu rabu tayi kuka sosai cos ta Riga ta tasaba da Lukman, da kyar ya lallasheta yace" ta kwantar da hankalinta AI suna tare amma fa bazasu Kara haduwa ba har se bayan bikinta saboda yanzu saura 1 month bikinsu ita Da mubin, take cemai badan Akwai wani cimma burin da sukeso suyiba da ba makawa shi zata aura, ya lallashetadai Dai yace Mata ta tafi gida cos Dare nayi, dakyar dai tabar Hotel din ta koma gida, da zata tafi 50K din da hajiya ta bata ta cire 30K ta bashi Dan idan ta koma gida dasu batasan me Zata siya dasu ba

  Lukman kuwa sai murna yakeyi bayan Tafiyarta yace" ga lada ga la'ada sai yasa nakeson Harka dake haleema akwai Sakin hannu, yana magana yana juya kudin, ganin shi kadaine a dakin yace" tab me yakaini auranki Haleema AI iyakata dake ki kawo kanki sannan kuma ki bani kudi, ya ajiye kudin ya shiga toilet yai wanka.  
   Sannan ya shirya ya dauka wayanshi ya Kira wata tazo ta tayashi kwana
    
   Misalin 10:00pm Haleema ta kasa Bacci sai tino memories takeyi da sukai spending tare da Lukman, IPhone dinta ta dakko ta Kira taji switch off tsaki tayi aranta tace" Lukman fa nada Dan matsala bata cika kiran wayanshi ta sameshiba sedai yanada bukata ya dameta da Kira

    Sai juyi takeyi Akan gado tace" Bari na Kira mubin, shima Kira tayi Taji switch off tsaki tayi tace Ku kuka sani....Nima nai Dariya nace KO dai ke 
Kika sani ba.....lol

Aranar dai ba wani cikakken Bacci Haleema tai ba, saboda tinani barkatai da takeyi na yanda Ko da sunyi aure bazata Bari Mubin na juyataba, Kuma ta kuduran cewa duk randa ya auro Ta to se Nazeefa tabar gidan nan Dan taga Alama Mubin ne sonta sosai

   *****
     Bangaren Su Mansur kuwa, Ganin Saturday  ranar ba aiki wuni sukai suna yawo KO Allah zaisa Suga Nazeefa but unfortunately haka suka gama yawo a unguwar basu ko ga me kama da itaba
     Mansur ne ya kalle Abdallah da idanuwarshi yai kananu yace" Abdallah wallahi inason yarinyar nan Zan Iya rasa komai akanta amma Ina tsoron dai Allah yasa ba aljana bace!

    Abdallah ne yace" Abokina I'm very sure ba aljana bace, like I told you kyankune yai maku yawa kake kiranta da aljanah but calm down plz AI Dan yau bamu gantaba doesn't mean bazamu gantaba kuma

     Mansur ya kalle Abdallah kamar wani tababbe, Abdallah aranshi yace" this is serious da yaga yanayin Mansur ya chanza tuni ya tada motar suka Kara shiga unguwa, duk inda Sukaga mutane sai Su tsaya har yamma tayi

   Abdallah dayaga yanayin Mansur yaketamai Nasiha akan he should take things easy kar ya janyowa kanshi wani Lalurar

Post a Comment for "SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 7"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...