Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 3

SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 3

- - Post a Comment
SILAR GIDAN AIKICHAPTER 3


Budurwar nan tana tafe tana ta wani yanga har ta iso kofar falo, Sallama tayi a hankali taji ba wanda ya amsa Mata, dan haka ta tosa kanta cikin falon, taga Ta kowa Kara Sallama tayi faeeza ta fito tace" Waalaikumus Salaam +

Da gudu taje ta rungumeta tace" your welcome my Sister yau kace a gidan namu lalle yau munada manyan baki

Budurwar nan mai Suna Haleema tace" wallahi kuwa naji shuru to kunki zuwa har yanzu baku da zumunci wallahi

Faeeza ta Rik'e hannunta gam tace" ba haka bane Kinsan school bama zama

Haleema tace" iyayan School Ina twin Bro din naki? Tace Ya tafi masallaci, ta Kara dacewa sweet Yaya fa? Mubin kenan

Ta Kara cewa shima ya tafi masjid

Yaya Haleema Mu shiga ciki mana mun tsaya anan cewar Faeeza,

Ohh tace suka shiga suka ajiye kayanta a dakin Faeeza din sannan suka dawo falo

Suna Zaune sunata hira Saiga Nazeefa ta fito da gudu ta nufa waje, Amai takeyi Sosai Saboda Zazzabin ya dawo Mata, Typhoid dinnan ya sata a gaba ga ciwon kai

Haleema Binta da ido tayi tace" wace Yar kauyen ne wannan? Faeeza ta tabe baki tace" wai Yar aiki kenan, Kinsan ankora Wanchan shine aka samo Wannan,

Haleema gabanta yadan fadi Dan taga yarinyar so Masha Allah, dukda tana cikin wahala amma fatar Nazeefa kana ganin kasan nan gaba zai murje kuma gabobinta manyane irin na yayan boters dinnan, duk karancin shekarunsu amma zakaga fatarsu fresh

Faeez ne ya dawo daga masjid yaga tana amai da sauri ya karasa wajenta ya zauna kusa da ita yana mata sannu, Allah ya kara Sauki,

Ruwa ya ebo Mata ya wanke wajen Yana Mata sannu, Dan ta bashi tausayi sosai, Dan shi din me tausayine, kaf gidan shi daban yake

mik'ewa tayi zata nufa Daki, suka hada ido da faeez Yace Meke damunki? Ashe mubin ya Shugo yana labe yana kallonsu

Nazeefa nuni tamai da cikinta ne ke ciwo, Sai kuma ciwon Kai, Sannu Yai mata yace" idan na fita Zan samo maki magani kinji dago kai sukai tanamai murmushi alamun Tagode Dan halayen faeez na burgeta

Kamar anjefo Mutun daga sama Saiga mubin a tsakaninsu, Ya kalle Nazeefa yace" wato iskancin har ya iso cikin gida ko?

Ya juya ya kalle kaninshi yace" disappear from here kona batama rai, shashasha kawai

Tsaki yayi yai ficewarshi, Dan ya rasa me Nazeefa tai wa mubin haka, shi mugune gaskiya

Fitarshi yayi yabar mubin din yana kallon Nazeefa ido cikin ido take kallonshi but she don't have the straight da zata maidamai magana

Fitowar Su Haleema ne ya katseshi daga tinanin da yakeyi, Kusa dashi tayi sosai tace" _Yaaa muubiiin_ cikin wani irin yanayi

Smiling yayi yace dear sister kece a gidanmu

Tana magana tana wasa da yatsu tace" to bakaki zuwaba shine na biyoka *toofaaa*

Smiling yayi yace OK to Mu shiga ciki, kun gaisa da Hajiya amma ko

Tace" Hajiya na Bacci kuma faeeza tace innata Bacci baa tashinta,

Mubin Sosa keya yayi yace" Ohh hakane but hankalinshi na wajen Nazeefa balle yanda sick face dinta yayi idanuwanta yai kasa kasa kamar mejin Bacci, Tausayinta nan ya kamashi ji yake kamar ya dauketa yakaita asibiti but wata zuciyar tana karya kaita

Haleema na Lura da irin kallon Da yakema Nazeefa janyoshi tayi tace" mu shiga falo mana dear yayaaa

Ba yanda ya Iya hakanan ya shiga yabar Nazeefa a wajen

********
*"KARFI" WANI KAUYE A GABAN GARIN KANON DABO*

Wani dattijone zaune yayi tagumi duk abun duniya ya isheshi, wata matace na hango Tazo ta zauna kusa dashi kana ganinta kasan Mahaifiyar Nazeefa ce dan kamanninsu ya baci

_Hafsat farace dugowa tanada diri, fulanin yola ne amma Aure ya kawota wani kauye a garin Kano..... atakaice kenan_

Kallon malan Nalado tayi tace Alhaji kayi hakuri idan Sahura ta dawo zanje na tambayota a wani garin aka Kai Nazeefa aikatau

Kallonta yayi cikin bacin rai yace Kwata kwata bakimun adalciba, Sai kace ke kadai kika haifeta? AI kya tsaya na dawo kiyi shawara Dani

Ko ance maku Aikatau dinnan da kuke Kai yara basa shan wahalane? Kudai a kawo muku kale kalen duniya KO?

To Wallahi bazata yowuba KO ki bincika inda take adawomun da yata ko ki fuskanci bacin raina nidai na fada Maki

Nan Hafsatu mahaifiyar Nazeefa ta kasa zaune ta kasa tsaye tinaninta daya kar Malan Nalado ya saketa

********
Hajiya Asmau bacci take hankalinta kwance, Hayaniyar su Haleema ne ya tayar da hajiya daga bacci +

Fitowa falo tayi tagansu sun baje a carpet din dake falon Sai ciye ciye sukeyi, Da sauri Haleema ta tashi taje ta rungume Hajiya

Oyoyo tace" Mata sannan ta tsugunna tagaisheta, ta tambayeta ya Iyayan nata suke ta amsa da lafiya Lau suke sunce ingaisheki sosai
Tajiya tana murmushi tace Ina amsawa

Nan itama ta baje a falon Dan Uwace amma me yawan biyewa yaranta ballema faeeza Dan ita kadaice yarta mace tana bala'in sonta

Wuta aka kawo Suka kunna TV sunata kallace kallace, da hajiyar da faeeza da Haleema sai mubin din da yana tare dasune amma sam hankalinshi baya wajen, Yayi nisa Wajen tinanin Nazeefa, Har imagining yakeyi gasunan a gidansu mekyau, Nazeefa nada ciki ta haifar Mai twins, Gasunan sun fita shakatawa, yanata tinanin shirmanshi yafara smiling,

Haleemace ta kalleshi itama taji tana cikin farin ciki Dan tana bala'in Son Mubin Dan already iyayansu sunyi alkawarin zasu aura musu juna saboda shakuwar da sukai......muje zuwa

*********
*Shin wanene Mubin dinnan?*

Mubin yaron Alhaji sada ne, Alhaji Sada Haifaffan garin maidugurine, Su biyu kachal mahaifinsu ya Haifa shine babba sai kaninshi Ana cemai *BAKO* Sun taso cikin kulawar iyayansu har Allah yasa kowa ya girma ya sama abunyi, Shi Alhaji Sada Yayo KADUNA cirani saboda a Chan da suke bawani Abu sukeyiba balle shi be maida hankalinshi ba wajen karatu, Yazo kaduna yasama Gadi a wani makaranta har Allah yasa suka hadu da Matarshi Hajiya Asma'u kenan Mahaifiyar Su MUBIN

Shi kuma Dan uwan nashi da yake ya yi karatun boko da islama shi ya sama aiki da gwamnati Dan Ana damawa dashi

Hakanan sukaci gaba da rayuwarshi shi Alhaji SADA beda arziki shi kuma Dan uwanshi kaninshi (BAKO) Allah yamai arziki sosai yanzu haka yana Chan garin KANO

Cikin kankanin lokaci Alhaji Sada Yayi arzikin da kowa yake mamaki, Yayi babban gida komai nashi sai Wanda yagani, Lokacin dansu guda daya Mubin yaga soyayya Kala Kala Dan kasashen waje ansha fita dashi tun yana karami, Abokai da yan Mata kuwa a unguwa kowa so yake ace mubin Abokinshine suna magana

Hakanan mubin ya taso cikin shagwaba komai idan yanaso Ana Mai, Ya Dan girma ba laifi akai Mai kannan yan biyu faeeza & faeez, Suma ansha fita dasu kasashen waje, Haka suka taso Cikin shagwaba Ana kula dasu sosai, Faeeza ta dakko halin mubin Sak, Shi kuma Faeez cikin ikon Allah halinshi daban, Saboda yanason zuwa islamiya kuma Ana musu waazi sosai sai yasa yake tausayin talaka, Kuma Duk abunda akace bakyau yana kokarin kiyayewa that's little about them, Nan gaba zakuji yanayin siffarsu and Dangantakar dake tskaninan su da Haleema lol

*******
Ganin yamma tayi Hajiya ta shiga kitchen Dan dafawa Haleema Abinci, Dan tana bala'in Sonta ta zama sirikarta ko me yasa ohon musu

Suna Wajen shakawata da mubin da Haleema a farfajiyar gidan, Suna hiransu na Masoya ko yan uwantakane oho

Nazeefa ce ta Kara fitowa da gudu tana Amai, Haleema ta kalleta tace mtsw wai me yasa aka kawo this village and dirty girl aiki nan Gidan ai bazan iya cin abincintaba gaskiya

Mubin ne ya kalleta yanaso ya furta mata magana amma ya kasa, Dan to be frank yaji haushin maganar data fada wai village n dirty girl, a ranshi yace kuma haka nakeson abuna ba

Nazeefa Kara yunkurin wani amai tayi kamar kayan cikinta zai fito, Da sauri Mubin yazo kusa da ita yana sannu, Duk tana cikin wani hali bai hanata balla Mai harara ba

Haleema itama ta biyoshi ta yamutsa fuska tace" huh I can't stay here ai itadin ce ma abun amai, A fusace ya mik'e zai mata magana sai yaga har ta shiga pallow

Nan idanuwan Nazeefa ya fara chanzawa kamar zata mutu, mubin ne ya rude ya Shiga ya sanar Da Hajiya zekaita asibiti adubata

OK tace kuma fa ya Kamata saboda she has been sick since, yace Wallahi kuwa

Da sauri ya fito Haleema tana _yaaa Mubin_ ko sauraranta beyiba ya fita ya tada Mota

Bude Sit din gaba yayi, yazo ya sunkuce Nazeefa sai cikin mota, A idon Haleema aranta tace what am I seeing kodai mafarki nakeyi hmm

Da Sauri Ya fita ya Fara tafiya kamar ancirema Nazeefa ciwon ta tashi

Zama tayi sosai tace" Malan Ina kuma zaka kaini? Banason temakonka ka saukeni anan

Yace kiyi hakuri nasan Zafin ciwone, ta bude idonta sosai tace" wallahi ka tsaya ko na Tara maka jama'a nace kasatoni

Zare ido yayi yace Nazee.....tace don't dere call my name again, do as I say kawai

Mamakine ya cikashi wai Karamar yarinyar nan tana magana haka

Ya tsaya chak kenan ita kuma Nazeefa tana kokarin bude motar hannunshi yasa akan hannunta........ tooofaaaa Ya tsaya chak kenan ita kuma Nazeefa tana kokarin bude motar, hannunshi yasa akan hannunta Yaji wani shocking tini ya cire,

Juyawa tayi ta balla Mai harara tace" Ohh kaima Dan iskan ne ashe, inba iskanciba wani irin abune wannan, Ko ka taba ganin a musulunci inda akace Namiji ya taba hannun mace? Bakada hankaline ko meye? Sai kuma tai tsaki

Mubin kam Dan takaici kasa magana ma yayi, me yasa zai Bari wannan Yar yarinyar tana fadamai magana som ranta, yana cikin tinani ta katsemai

Kara bude bakinta tayi tace" malan Nace ka budemun kofa na fita ko

Ko sauraranta beyiba ya tada motarshi, Yaci gaba da tafiya Wani babban pharmacy suka tsaya, Kallonta yayi yace meke damunki? Batace komai ba tamai dai nuni da cikinta da kanta, Fita yayi ta bishi da kallo tai ja yar karamar tsaki

Shagon ya Shiga yai musu bayanin duk abunda da yake damunta, maganguna masu kyau da tsada yasiyo Mata sannan yadawo cikin motor ya mika Mata yace" ungo, Fuskarta na kallon waje itako ta amsa ta jefar dashi bayan sit

Kallon mamaki yake Mata aranshi yace duk Son da nake miki I'll deal with you banzan yarinyar sai wulakacin tsiya, Dariyar mugunta yayi ya tada motor yafara tafiya ahankali

Ahankali suke tafiya yasa sauti yana tashi kadan kadan, Nan jikinta ya rikice ta rik'e ciki sai kuka takeyi, tausayi ta bashi sosai, gashi yasan bataci abinciba, parking din motar yayi ya shiga wani Shago yasamo Mata kayan drinks da ciye ciye na kwalama, sannan ya samo ma Su Haleema Dan yasan sesun Mai mita inhar be siyoba

Exotic ya bata tadan sha kadan sannan ya dakko magungunan daga back sit ya mik'a Mata tasha ba'ai 10mins ba ta Fara zufa alamun Magungunan sun Mata aiki

D'ago kanta tayi ta kalleshi tace thank you ya mubin, shima yai banza da ita kamar bejiba, Nazeefa taji yayi shuru tace" nagode Still yai banza da ita

Nazeefa tsaki tayi tace wai mutun kamar kurma Ana magana yana banza da mutane

Dariyar mugunta yayi da shi kadai yasan me yake nufi

Ahaka suka Isa gida Both of them Zuciyarsu ba dadi Dan haushin juna sukeji

***********
Bangaren faeez kuwa tunda ya fita gida shima bawon Allah chemist ya nufa da yake yanada yan kudi ya siyowa Nazeefa magani, yadawo gida akace basanan Zuciyarshi sai zayyanomai abubuwa yakeyi, tsoronshi kar mubin ya wulakanta Nazeefa...
*****
Mubin ne ya Shugo gidan yasama parking space yayi, Nazeefa zata fita kenan Ya kirata cikin wani Yanayi da ita kanta seda ta tsorata, kallon juna sosai sukai, Mubin yaji wani Abu na yawo a kirjinshi, kallon labbanshi tayi taga kamar yana shirin magana, Tuni ta tina matsayinta a gidan, Tai sauri ta Sauka ta nufa fallo, Mubin kuwa Binta da ido yayi a ranshi yana Allah ya mallakamai Wannan yarinyar,

Tana sauka direct Dakin Hajiya ta nufa taje tai Mata godiya, Hajiya tace to bakomai yau ki huta abunki tunda gobe ba makaranta tace nagode

*******
Haleema daga jin mubin ya dawo tai maza taje tai wanka tai kwalliya, tazo tasameshi a falo zama kusa tai sosai tashi, adaidai lokacin ita kuma Nazeefa zata shiga kitchen ta kallesu, tsaki tayi tace wai mutane kamar yan iska Ashe sunji

Haleema ne ta tareta tace da uban wa kike? Tace da Wanda ya tsargu

Mubin ne ya taso yace"Haleema Dan soyayyar da kikemun ki saketa, wani ajiyar zuciya tayi tace dan dai kasa bakine dana balla yarinyar nan, sannan ta kalle Nazeefa tace mata village and dirty girl kawai

Nazeefa kuwa murmushi tai Mata ta shigewarta kitchen ta dauka cup ta koma dakinta

Haleema kuwa kallon mubin tayi tace kasan Dan Kai nazo KO? Yaushe zamui hirane wai

Yace Mu fita compound din gidan KO sweetheart OK tace ya mik'e ita kuma tana biye dashi

Sun fita sun kusan one hour a waje suna hiran masoya, balle yanda Haleema ta kurama mubin ido sonshi Kara shigarta takeyi,

bangaren feeez kuwa sai suntiri yake a falo, Ko zaiga ba kowa, cikin ikon Allah yana fitowa yaga ba kowa dan haka Faeez da sauri ya fada dakin Nazeefa da ma yana dan shugowa sudanyi hira idan ba kowa, Magani ya dakko mata yace" gashi nasan yan gidan nan is hardly Su siyo miki

Murmushi tayi tace" Allah sarki nagode faeez, Kagama dazu muka je da ya mubin ya siyomun

Faeez yace" Badai yai miki komai bako? Tace ah a bakomai yace" to Alhamdulillah

Nan sukaci hira sosai dashi ta farfada mai matsalarta sai bata hakuri yakeyi, sunsha hira kusan 30mins yace Bari dai na tafi Kinsan munada sa'idawa, dariya sosai tayi Dan tasan da Wanda yakeyi tace" mubin ya jika ba ruwana atoh

Shima dariya yayi yace ai gaskiyane, nidai na wuce Allah Kara sauk'i

Ya fito kenan Saiga Mubin sun Shugo da Haleema

Zare ido mubin yayi what??? Me wannan yaron yajeyi a dakin nan this is d 2nd time da naganshi

Gabanshine ke bugawa yace" Tabdijam.........

Post a Comment for "SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 3"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...