Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 18

SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 18

- - Post a Comment
SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 18
Nan Su Umma sukai Mai godiya sosai, sannan sukai Mai addu'a sukace dama basu dana chanzawa sungode! Nazeefa kuwa na tsaye a wajen tinanin kokarin da sukeyi akanta take, + Sai taji muryan Mansur yace zasu tafi tace OK Da zasu tafine Nazeefa ta rako su har bakin inda sukai parking motar Su, Abdallah ya bude site din gaba da zauna Mansur kuwa bude mazauninshi yayi ya dakko ledar wayar ya mika mata yace idan kin shiga gida sai ki bude, Tace to yalladabai tana magana tana murmushi shi kuma yana binta da kallo hade da d'aga Mata gira Tana tsaye a wajen seda suka fita sannan ta shiga cikin falo dinsu, Mansur kuwa inbanda murmushi ba abun da yakeyi Dan duk sanda suka hadu Kara kwarjini takemai sosai Tafiya suka Fara, Abdallah yace" ni harna Fara gajiya da soyayyan nan naku kawai ka fito kui aure nima na huta "Mansur wani dariya yayi yace" ai soyayya bakaga komai bama tukunna se randa na mallaketa, Abdallah yace" Mansur kenan Ana ganinka shuru shuru ni kadai nasan halinka, "Mansur ya kyalkyale da dariya Nazeefa kuwa Tana shiga falo kusa da mamanta taje ta zauna, Ta Fara bude ledar da mansur ya kawo Mata, Zare ido tayi hade da wani ihu ta dafe kirji tace nice da IPHONE 11, Kai Alhamdulillah tana maganar tana Kara kallon wayar Mamantace tace mugani, ta mika mata Tace Kai amma wannan wayar dakyau take! Masha Allah, babantama yace mugani ta mikamai, Nan take mahaifinta ya Fara tsoro yace nifa bancikason saurayi na maki kyautaba gaskiya, inda gaske yake Kawai ya fito, ta Dan hada rai tai kamar bataji me yake cewa ba Wayarta taji ta Fara ringing tana dubawa taga ansa MY LOVE Ta san ba kowa bane Mansur ne Dan haka ta tashi ta shiga daki ta amsa wayar yace, love please idan badamuwa kuzo court kaza Ina jiranku ayita ta kare kawai Tace alright gamunan zuwa ta kashe wayar tasaka a chaji, sannan tazo ta sanar da iyayanta ance suje court kaza ta fada musu, sukace to muje ke ba kinsan wajenba? Sai ki mana jagora Tace OK,
Fitowa sukai suka sama napep, sukaimai kwatancen inda zai kaisu yace badamuwa Tafiya sukai na kusan 20mins sai gasu a babban koton, Suna shiga saiga Mansur da Abdallah suna jiransu, Sallama Su Nazeefa sukai musu sannan Su kuma sukai musu jagoranci har cikin koton Suna shiga saiga Su Baban Mubeen da iyalanshi dasu Hajiya Hadiza Da yarta duk an tsaresu idon kowa kamar an musu duka Dan yayi Jajir Wani banzan Kallo Nazeefa ta jefawa Haleema, sannan ta dawo kan Mubeen shima ta balla Mai harara, kallonshi sosai takeyi sai taji idonta na shirin fitar da hawaye, a ranta Tace Mubeen Ashe Kai Dan uwanane ka wulakantar da rayuwata! Tana cikin tinanin hakan ne sai Alkali ya kirasu yace suzo yanason magana dasu...ya yanke Mata tinani Yar karamar tsaki taja, mubeen kuwa na kallon lips dinta, hanjin cikinshi ya Kada Su suna gefe a ajiyesu Su Nazeefa kuwa suna Magana da alkali, yace yau ne za yanke musu hukunci kun hakura ne KO KO kunasone a hukuntasu? Malan Nalado Yace ah'ah mun yafe wallahi kawai abunda nakeso shine Ku kwacemun dokiyoyina kuje dashi duk inda yai ajiya ya fitomun da abuna tunda hakki nane, Nidai na yafe Umma hafsatu ma Tace ta yafe itama Nazeefa kuwa yanda ta cika ta batse Tace ita Sam bata yardaba wannan ma ba yi bane, sai an wulakantasu, Dan kasheta sukaso suyi, nan take ta magana ta inda ta shiga banan take fitaba gaba daya ta rikice Da Su mubeen sun kalleta se hanjin cikinsu ya kada Dan sunsan abunda sukai Mata da wuya ta hakura Umma da babanta daka Mata tsawa sukai, nan ta fashe da kuka wai ba ai Mata adalci ba da yanzu sun kasheta fa Lauyan yace to Kawai kui hakuri yanda takeso haka za'ai ai yancinta za'a kwato Mata Abdallah da Mansur kuwa suna tsaye suna kallon ikon Allah Su Mubeen kuwa tuni ya gama tsurewa Dan wani cikinshi da yaji ya na murda mai Dan idan yai motsi da yawa zawo zai Iya zubowa, Haleema ma idonta yai zuru zuru Dan tasan today na today zasusha kashine
Umma Tace Nazeefa bake mukewa magana ba? Tace umma please kiyi hakuri suji idan da Dadi Lauya ya gama rubuce rubucenshi yace to shikkenan Ina zuwa Mansur ne ya kureta da ido yace Nazeefa zo kiji, waje suka fita, Allah yasa ba kowa yai kneel down ya roketa da Allah da annabi akan tayi hakuri, Da sauri tace huh kayi hakuri ka mik'e kar wani ya ganka, yace bazan taba mik'ewa ba har sekince kin hakura Hawayene ya zo Mata Tace bakomai na hakura, Amma kasan wahalan danasha kuwa Yace nasani kiyi hakuri, ki tuna munawa Allah laifi amma ai yana yafe mana, Tace to shikkenan Suna shiga court din sega lauyan ya fito yace meye final decision? Kanta na kasa tace na ha kura amma se sun fitar mana dakoyoyinmu Lauya yace angama Kiran Yan saida sukai aka sasu a gaba sukai gida Dan ya bata takardun komai da komai Motocin yan sanda aka kawo akace Su baban mubeen Su shiga, Jikinsu KO Ina na rawa Daka gansu kasan basu da gaskiya bare mubeen da kamar kucemai arr ya ruga + Mansur ne yace No bari ya saman musu napep ko, ai zaifi Tunda angama maganar Fita yayi ya sama napep guda biyu yace Su jirashi, court din ya shiga yace Su fito sannan yai ma lauyan godiya sosai yace idan akwai wani abun ya nemeshi yace to angama Nan ya umurce masu Napep din duk inda ya shiga Su dinga binshi zai basu kudi masu tsoka sukace angama ranka shi Dade Saboda sunsan Mansur sosai Dan commissioner ne amma ba ruwanshi ko ina sa kafa yakeyi kamar ba Dan babban gida ba sedai kalar fatarshi kawai zaka gani kasan he is from rich family Sunyi tafiya kadan suka shugo layin tun akan layin yan unguwa kamar an Kai musu rahoto suketa leke leke Daidai gidan motar Su Mansur tai parking da napep din, Suka fito suka shiga gidan dukansu!
Kowa jikinshi a sanyaye Dan alkalaminsu ya bushe, Dan sun zama abun tausayi, Hajiya Hadiza suna shiga takai gwiwoyinta kasa tana rokan Nazeefa akan ta yafe musu ita tayi nadama Wallahi bazata karaba, Nazeefa ko kallonta batai ba, Sannan ta juya wajen Mansur shima tamai godiya yace bakomai Da kafarta ta karaso wajen mahaifan Nazeefa tana musu magiya akan duk abunda sukai musu suyi hakuri dasa hannunta, Sukace Su sun yafe cos da basu yafeba bazasu taba bari Su dawo gidan ba, Tace nagode, Duk inda taje Haleema yarta na biye da ita Ta kalle Mansur Tace" akwai wani abune kuma? Yace I think tunda sun yafe bakomai Ko Umma tace hakane bakomai, komai ya wuce Ai tanajin haka riko hannun yarta tayi suka fice da gudu Dan taga tashin hankali, Mansur kamar zai kyalkyale da dariya ya fuske dai, Nazeefa kuma kasa rik'e dariyarta tayi ita KO tai dariya sosai Tace Allah ya kyauta Suna fita napep suka samo Tace yakaita tashar da za ashiga mota aje abuja yace angama Duk a tsorace suke sosai Tace" Haleema muna komawa da kwana biyu Zan saida gidan mu koma wani wajen kar azo a Kara nemanmu, Haleema Tace gaskiyane Mum Huh gaba daya jikina ba inda baya rawa mama *** Su Mansur kuwa ganin kar Su shiga hakkinsu da yawa shi da Abdallah sukace zasu wuce cos yanzu baban Nazeefa da baban mubeen da iyalanshi Kawai suka rage Yasan they need privacy bakomai ne za ai a gabansuba Dan haka sukace zasu wuce gida Su umma sukai Mai godiya sosai, Bangaren Su mahaifan Mubeen kuwa ba Wanda ya Iya cewa komai Dan a kunya ce suke sunyi budulci Nazeefa ce ta rakosu har wajen tai musu Godiya sosai yace bakomai kinfi haka a wajena Wani murmushi ta sakar mai ya dag'a mata gira yace I'll miss you my lady tace me too har zasu tafi ya juyu yace please dear SABR (be patient) please Hummm kawai tace, Mansur kallonta yayi ya girgiza kai, sukai shigewarsu mota Tana tsaye suka shigar motor sukai wucewarsu ita kuma ta shugo gida Tana shugowa gida fuskarta da walwala Dan ita tamanta ma halin da ake ciki Tozali tai da Su mubeen tuni chanza fuska ta hade rai..aranta Tace Mugu, Nifa saina rama abun dakai mun Binsu da kallo daya bayan daya tayi taji wani bakin ciki ya mamaye zuciyarta inama anmusu hukunci me tsauri Maganar mahaifinta taji yace Ku mushiga daga ciki mana
Sukace To Me gadi kuma se leke yakeyi Dan yasan akwai drama yau Su Nazeefa ne a gaba Su kuma suna bin bayansu har suka Isa falon Kowa samun waje yai ya zauna kowa yai shuruu da abun da yake sakawa a zuciyarshi Kowa samun waje yai ya zauna + Kusan minti biyar ba wanda yace wani abu kowa da abun da yake sakawa a zuciyarshi Hajiya asma'une mahaifiyar Mubeen, Ta kalla Umma Hafsatu Tace Dan Allah kuyi hakuri, Ku yafe mana Wallahi sharrin shaidan ne! Umma Tace uhm Bakomai mukam komai ya wuce a wajenmu, Allah ya Kara tsare na gaba kawai Faeeza taji duk duniyar bata Mata dadi, Ashe mugunta bakyau, Malan nalado kuwa yace to Alhamdulillah nidai abunda make so dakai duk kadarorina ka bani abuna da gidajene da duk abunda na mallaka! Baban Mubeen jikinshi na rawa ya shiga daki ya dakko Mai takardun komai da komai nashi, Harda company's dinshi na kasar waje Ya nunamai komai ga Iya riban da aka samu Malan Nalado Yace wallahi dan Kai yaya nane amma duk da haka ka cutar da rayuwata amma bakomai Nan ya eban Mai kudade da wasu company nashi yace yaci gaba da juyawa, kuma yace zasu je a chanza sunar takardon amaida Mai da sunan yarshi daya tilo, Bban Mubeen yace to Angama Sannan ya kalle Nazeefa yace yanzu Ina kikeso Mu zauna nan gidan KO Mu chanza wani? Tace No Abba bazan Iya zama a gidan nan ba ga gidajen kanan Mu koma daya kawai inyaso sai Mu bar musu nan gidan Umma hafsatu Tace kinyi tinani yata, Nan Baban mubeen da Mamansu suketa shi musu albarka kuma sukace sungode, kuma Dan Allah Kar adinga tina baya Umma hafsatu Tace ba halinmu bane ay Nandai suka sasanta, KO banza sune a kasa Da yake babban gidane Su umma Hafsatu suka zauna a dayan gefen kafin Su gama gyare gyare Su koma Chan gidan Su Su faeez da faeeza kuwa sunqi sakin jikinsu balle uwa uba kuma Mubeen Nan Baban mubeen yace yanada magana Su hudu kawai iyaye Dan haka suka kebe kome suke tattaunawa oho Nazeefa kuwa ta mik'e tabi su da kallo Tace ohh ni dama Chan bare ce a cikin Ku bare nai gaba, Faeez yace Dear sister! Tsayawa chak tayi ta waigo tace Faeez zamui magana anjuma tai shigewarta daki ta dakko wayarta a chaji taga yayi battery full, hayewa gado tayi ta Fara latsa wayarta Bayan Nazeefa ta shige daki wani hawaye mubeen ya suma zubarwa, Faeez yace yaya stop it please Yace kasan meye nakewa kuka? Ashe arzikin yarinyar da muke wulakantawa ne, me yasa Su dad da mum suka zabi wannan rayuwar? Da muntaso cikin talaucin Mu Ina zamuga wata tazo aiki gidanmu bare Mu wulaqanta ta innalillahi wa Inna ilaihir rajiun yace ni gaskiya barin gidan nan zanyi bazan Iya zama ba. Faeez ne da yake yadan fisu tinani yace Kayi hakuri yaya, duk abunda yai tsanani maganinshi Allah Mubeen yace nasan da haka, But honestly speaking sun cutar da rayuwarmu sosai Faeeza uwar iyaye Tace da wani ido Zan kalla Nazeefa nida nafi tsanarta!!! Faeez yace uhm Allah dai ya rufa asiri Suna cikin hakane sai ga iyayan sun fito kome suka tattauna Allah kadai yasani! Nagada Umma Hafsatu ta fito ranta a bace Baba Nalado ne yace Ina Nazeefa? Faeez yace tana cikin daki Kwalla Mata Kira akai saiga ta ta fito, Fitowar Da zatai suka hada ido da mubeen, Gaba daya ta rude kamar mara gaskiya Zama tayi a dakin Suka bude sabon labari, kamar ba abun daya faru Itadai tana gefe jife jife take saka bakinta a hirarsu cos gaba daya ta tsunduma tinanin Mansur

Post a Comment for "SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 18"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...