Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 16

SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 16

- - Post a Comment
SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 16
Mum tsaye take tana kallon ikon Allah, Tace Son har kayi wayon da zaka kawo wata? Yace I swear to Allah mum Is not what you think Wallahi yarinyar nan daki ka gani temakonta nake + Dad yace" ohh dama Kai sheik ne ashe bamu saniba, Son a cikin gidan nan zaka kawo mace, dad dukda yanason Mansur be hanashi wankamai Mari ba, this this d first time daya taba marin mansur, ji kake tass Yace stupid boy kawai, kabamu mamaki, Ashe wayonka na banza ne, Nazeefa kuma se kuka takeyi Mum tace" Mansur ban number Abdallah yanzun nan nasan shi kadai zai sanar damu gaskiya, kuma idan kun hada bakinema zangane
Man take ya ba mum Numbern Abdallah, hello kana Ina? Yace Ina gida tace oya kazo Ina bukatan ganinka Tana kashe wayar, Jikin Abdallah ya Fara rawa yasan be wuce zancen Nazeefa ballema yanda yaji voice dinta da fada Kallon matarshi yayi yace" Mata bari naje na dawo, Kafe shi da ido tayi Tace he will not go any where, Magana ya fara Mata cikin natsuwa, yace mum Mansur ne ke kiranshi he will be back soon Tace OK...Da sauri ya shiga toilet yai wanka, Kafin ya fito matarshi ta dakkomai kaya ta ajiye a gefen bed Yana fitowa wanka, shafamai yayi, ya kurba tea din da ta hadamai se yadanci arish da kwai
Kaya ya saka da sauri ya shafa tirare, yai Mata seda dawo, Saboda fargaba ko motarshi be daukaba, fitowa yayi ya sama napep ya Mai kwatanchan inda zekaishi Cikin 20mins ya isa gidan, cike da fargaba Part din Mum din Mansur ya wuce yaga ba kowa, Dan haka ya wuce part din Mansur Tura Yar karamar kofar gidan yayi ya sama dad din Mansur zaune a kujera a tsakar gidan mum din kuma na gefenshi, sallama yai musu suka amsa, Dad yace su Shiga daki dukansu! Abdallah duk cikinshi ya D'ura ruwa! Zama a kasa yayi Dad Mansur ya kalleshi yace ka fadamun gaskiyar al'amarin nan, a bakinka kadai zanji gaskiya, Idan ka boyemun Allah na kallonka Abdallah yace hakane Abba Mum kuwa se huci takeyi Dan ranta a bace yake sosai
Dad yace" ka fadamun gaskiyar alakar wannan yarinyar da Mansur, Mecece ita tashi Abdallah ya soma magana with confidence Dan ba karya zaiyi ba yace Wannan yarinyar sunanta Nazeefa,Mansur ya dade yana sonta itama haka, inzaku iya tuna tun wani ciwo da Mansur ya ta bayi Wanda ake tinanin KO shafar aljanune, Wanda aka kwantar dashi a Hospital yanata sumbatu, tun lokacin ya kamo da sonta amma daganan be sake ganinta ba, munyi nema har mungaji, sedai yaita cemun yana yawan mafarkinta Dan mun daukama itama aljanace Seda ga baya muka gane Mutun ce kuma ba komai me tskanin suba illa So, Intakaice maku dai se bayan kwana biyun da suka wuce Randa muka dawo daga lafiya muka ganta Nan ya kwashe labarin komai ya basu, ya dada da cewa se jiya still Mansur yazo ya fadamun yanason aurenta, ta bashi labarin ita ba Yar garin nan bane aiki aka kawota tun tana Karama, Tasha gwagwarmayar rayuwa Kala Kala, shine taba Mansur number wayar babanta Dan ta dade tana nema bata ganiba se jiya da tuni ta koma gida
Dad da mum kallonsu suka tsaya yi, Dan jin abun suke kamar a mafarki, bare Yayan yanxu sesu shirya ma karya yanzu yanzun nan kuma wasu iyayan su yarda Hmmmmm Mum tace ai Kara fure take bata yaya Ina numbern nan take tace Mansur ya bata cikin ikon Allah tana Kira aka dauka! Suka gaisa nan take wata hikama ta fado Mata "Tace malan naga numbern ne a wayana bansan wayeba kuma anyi saving da Malan so bansan wani malan bane Yace" Allah sarki, Nidai sunana Malan Nalado, Ina zaune a wani kauye KARFI a jahar kano. Ina kusa da masallacin jumma'ah, Mum din Mansur tace ohh ohh malan kamar tagane se kuma ta kashe wayar, Nazeefa kam tanajin muryan mahaifinta aranta Tace Allah me iko wallahi shine
Mum Tace ai kunji KO, Alhaji Ina tinanin dukanmu zamu tafi muje muga zahiri, Mansur kuma idan karyane sai mun bala'in saba maka Dad yace tabbas kuwa ai kaduna da kano ba nisace da itaba zamu Iya tafiya yanxu Dukkansu suka ce eh Mum kallon Nazeefa tayi se taji labarin da aka bata akanta ta tausaya Mata! Abdallah kuwa kiran matarshi yayi yace tafiya ta kamashi komun dare zaidawo Tace OK shikkenan, But zanje gida na gaishe dasu hajiyana tunda bakanan, Yace" OK ki dawo kafin magrib tace thanks hubby tamai kiss ta waya ya kashe wayar Nazeefa tarkato kayanta tayi, Kallo daya zakai mata seta baka tausayi, mum da dad sunfita part dinsu Dan dakko hijab da hula Nazeefa ta kalle Mansur da jajayen idanuwanta Tace" badan Dan iyayankaba bane se ince wulakantani kaso kayi Kasan baka da privacy na meye na kawoni gidanku? Aida kabarni na mutu a Hanya wahala ta kasheni Tsugunnawa yayi yana bata hakuri, Akan ba haka yasoba Tsaki tayi saiji sukai ance bazaku fito bane? Da sauri ta share hawayenta suka hau Hanya Tafiya sukeyi a cikin motar kowa tsit yayi kamar Wanda akai musu mutuwa, Kowa da abun da yake sak'awa a zuciyar shi, Nazeefa ce ta tsunduma cikin Tinani, Itakam tana ganin rayuwa daga wannan se wannan, magana ake Mata amma sam hankalinta be wajen, se da Hajiya Zainab (MUM mansur) tai magana da dan karfi tace mata ba nan bane garinku? 1 Dawowa daga dogon tinanin Nazeefa tayi, Bude idonta tai sosai tana cikin motar taceh eh nan ne kaman
Waje duka samu sukai parking Kowa ya firfito a cikin motor suna tsaye, Nazeefa ce ta hango wani Dan shagon da ake saida sweet, tuni tai recalling back, ta tuna nan babanta lokacin tana karama yake siyo Mata kayan dadi, Waige waige ta farayi taga kauyen duk ya sauya Mata! Duk anyi gine gine! Chan ta hango babanta a gaban masallacin yana zaune yayi tagumi! Jitai gabanta yace gham Dan wani irin yanayi da takeji Batace musu komaiba da gudu ta nufa wajen mahaifinta ta rungumeshi tana babana, babana, Alhamdulillah yace Dan tabbas yasan ba kowa bace sai Nazeefa, muryanta kawai yaji yagane Yace"Nazeefa kodai mafarki nakeyi? Rik'e hannunshi tayi Tace baba nice, ba mafarki kakeyi ba, Sukam su Mum binta da ido sukai sukace Allahu akbar wannan ba se an ce maka mahaifinta bane
Kallon babanta tayi tace bani kadai nazoba kazo muje, hannunshi ta rike da nata ya mik'e Se kallon mahaifinta takeyi shekaru sunja, yadan chanza ga halin rayuwar yau da gobe Binta yayi har inda sukai parking suka gaisa, tun a lokacin dad da Mum suka kasa magana Dan jikinsu duk yai sanyi Babane (MALAN NALADO) yace" muje ciki mana, basui musuba suka bishi har cikin gidan Mahaifiyar Nazeefa ce zaune tana tsintar wake, Taji Anyi sallama, amsawa tayi tare da kallon idonta wajen Wanda sukai Sallamar, Ganin Nazeefa tayi da sauri ta mik'e ko kallon sauran mutane batai ba, taje ta rungumeta tace ya'ta, Nazeefa kuwa tureta tayi tana kuka Mahaifiyar Nazeefa ma kuka ta Fara tana ki yafemun Dan Allah, ta sak'e rungumeta! Kuka ne yaci karfin Nazeefa sosai Dan kasama magana tayi, Samar ma bakin wajen zama sukai, Umma ta kawo musu ruwa tace sannunsu da kokari Nazeefa kuwa kafe mahaifiyarta da ido tayi, tana kokarin cewa wani Abu, Mansur ne ya fak'e idon mutane dayaga ba wanda hankalinshi ke kanshi, ya d'aga ma Nazeefa gira kuma yai Mata alamu da ido akan tayi hakuri plz, kartace komai wani ajiyar zuciya tayi kawai takai idonta Kasa
Maman Mansur ne Hajiya Zainab tace ammm bazama zamui ba, Keko Malama duk munji abunda ya faru da yarki, me yasa bakui hakuri da abunda Allah ya hore maku ba? Duk abunda kikaga bawa ya samu da sanin ubangiji kuma bawai wayonshi bane KO dubara, Ku godewa Allah ma ta fado hannun nagari daku da yarku har abada a wannan zamanin Maman Nazeefa Tace tabbas hanake kuma mungode Allah ya saka da alheri, Dama wajenku Nazeefa take aikatau? Hajiya tace ehmmm KO daya ba wajenmu bane, kinga yaron nan ta nuna Mansur Tace a hanyarsu da tafiya su Ka gamu da ita cikin wani hali badai a cewa komai kawai tunda Allah ya kawo karshen Abu Baban Mansur kuwa dukda babban mutune masu fada aji a gwammati ko kyamatarsu beyi, yaji gaba daya sun bashi tausayi, Sukace to ga yarku nan munkawo maku a kula da ita sosai dai a rage son zuciya Malan Nalado yace mungode, Sukace zasu tafi Nan Baban Nazeefa ya roka alfarma akan Dan Allah zasu bisu suje suga Inda Nazeefa tai aiki
Mum Ma Tace ba damuwa ay, muma ya kamata muje muga gidan dan Mu Kara tabbatarwa Baban Mansur kuwa yace tabbas dolema muje chan muganewa idonmu, nan suka shirya Suka kama hanya suka tafi, Su Hajiya da Alhaji motor haya suka hau dan motor ta musu kadan Alhaji suna tafe se jinjinar maganar iyayan Nazeefa sukeyi wai sun turo yarinya aikatau, a zamanin nan Hajiya Tace" wlhi Alhaji yarinyar ta shigarmun rai haka kawai naji Ina sonta Alhaji yace Allah KO? Tace wallahi daga ganinta zatai hankali Haka suketa tattaunawa Har Suka Isa gidan Koda suka gidan dare yayi, Alhaji yace suyi hakuri zuwa gobe Zasuje Chan gidan Da Nazeefa tai aikatau din Malan Nalado yace to bakomai, nan aka basu daki suka kwana, ba bacci sukai ba hira suke tayi har kusan 3 sannan suka samu suka kwanta Asuba tayi suka tashi sukai salla suka dasa hira kuma, gari na wayewa aka kawo musu breakfast sukaci sukai Hamdala Alhaji yace to Su shirya Su tafi Bangaren Su hajiya Maman mubeen da Alhaji ba wani cikekken bacci sukai ba, Saboda Alhaji se mafarkai masu ban tsoro yakeyi tun cikin Daren yake zufa 1 Hajiya itama kanta Gabanta se dukan uku uku yakeyi, Dan gaba daya a tsorace suke, tun safe suka tashi gaba daya jikinsu ba kwari, Dagasu har yaran
Misalin karfe 9AM Motoci kusan Biyar ne sukai parking a kofar gidan mahaifin mubeen tare da sodoji kewaye da wajen, Mubeen Na zaune a farfajiyar gidansu yayi tagumi gaba daya duniyar batamai dadi Sallamar muryan da ya dade baijiba yaji, Da sauri ya waiga saiga Nazeefa ta Fara shugowa da sauri ya kalleta ya furta Nazeefa! Kece a gidan nan again! Binshi da kallo tayi saiga mamanta da babanta sun shigo gidan tare da mahaifan Mansur Tsayawa tsak yayi, Mansur saboda mugun kishin daya tasomai yace" Nazeefa wannan ne Mubeen din? Dag'a Kai tayi jikinta na rawa Dan wani kibiyar son Mubeen da taji ya harbeta Iyayan har suna hada baki meye mubeen din qyayi? Da sauri Mansur yace bakomai Suna tsaye basukai ga shiga chan cikin gidan ba saiga Maman Haleema ta shugo tare da yarta ghammm ta bude kofa KO sallama batai ba, ta kalle mubeen tace Ina uwarka? Banza da ita yayi Alhaji da Hajiya asmau suna daki sukaji hayaniyar Hajiya Hadiza, Dan haka gaba dayansu suka fito harda yayansu faeez da faeeza Fitowar Da zasui sukaga gida cike da mutane, salati suke tayi Sudai Su Mansur suna gefe basuce komaiba suna kallon ikon Allah Haleema ta hango Nazeefa taga tayi kyau nan ta shiga taitayinta aranta Tace kodai masu kudin nan ne iyayanta, sai kuma ta karewa malan nalado da matar dake kusa dashi taga Sak sunyi Kama Hajiya Hadizace ta Fara yau karyanku ya kare, ni zaku sakar ma yarinya? Tau duniya sai taji Koku suwaye, Mugaye masu bin bokaye yau karyarku ta kare
Ta kara da cewa Ai nasan gidan da nalado yake a kauyen karfi, sai naje na sanar dasu komai ince Kai kamai asiri ka rabashi da dukiyarsa daidai da rigan sawa bakabar Mai ba, Hafsat mahaifiyar Nazeefa tanajin an anbato sunan mijinta tace wani naladon kodai miji na? Se a lokacin hankalin Hajiya Asmau da mahaifin mubeen da Hadiza suka Kai idonsu kanta Dan basu taba tsammanin hakan ba kwata kwata Salati kawai sukaji anayi saiga mahaifin mubeen a kasa, Ya fadi, ido hudun da sukai da nalado ya gane tabbas Dan uwanshi uwa daya uba daya Mansur da mahaifanshi suna tsaye sukace duk bamu gane wannan maganganun da kukeyiba meye asalin zance? Hafsat ta maso kusa da Maman Mubeen tace" Asmau kinyi mana budulci dama Ku kukaiwa mijina asiri? Dam ko ta tayi, dakyar Hajiya Maman mansur da Nazeefa suka bata hakuri, Sannan ta koma kan Alhaji mahaifin mubeen Tace sedai Inka mutu amma wlhi Seka Sani Hajiya tadiza tai shewa Tace Alhamdulillah aiko sedai akaimu prison gaba daya, Haleema kuwa na gafe tace yau munshiga uku Nan ta Fara bayyana sirrikan da sukai da Hajiya Asmau, tun lokacin da sukaga Malan nalado yanada arziki, gashi shine karami, sai suketa bakin ciki, Dan me zaifi yayanshi kudi Haka suketa mai asiri har seda suka rabashi da komai KO gidanshi na karfi dakyar yayi saboda shi me qashin arziki ne Hajiya Maman Mubeen da Alhaji sukace ikon Allah, Wai uwa daya uba daya! Nazeefa Ashe ke Yar gata cE, Wani murmushi tayi Ta kalle mubeen Taga ya mugun bata tausayi, Faeez da faeeza kuwa yayyafawa mahaisu ruwa sukai ya farfado suna tsugunne sunata kuka Malan nalado yazo kusa dashi yace bani ka cutaba kanka ka cuta, Allah baya zalinci, yanzu gashinan kana ganin kun tsira bazamu Kara haduwa ba, Sai gashi cikin hukucin Allah SILAR AIkin Da yarinya ta tazo gashi asirinka ya tono, Kayi budulci, halin da ka jefani da matata da yata bazan yafe maka ba, duk arzikina Ashe kake tunkaho dashi, Kuka mahaifin Mubeen ya Fara yana Neman yafiya, Makota kuwa kamar anyi sanarwa sai shugowa sukeyi, kowa se fadan albarkacin bakinsa yakeyi, sukace suma sunyi mamaki ashe kudin kaninsane ba nashiba
Mubeen kuwa yana gefe abun tausayi, jiyai kamar ya kwarma ihu, dama wacce suke wulakantawa Da arziqinsu suke tunkaho, Mansur ne ya Kira wani babban lawyer yace suzo yai musu kwatance layin, Sai gasu sunzo, Yace ya shigar da karar koto amma for now gaba dayansu akaisu prison a kulle Mahaifin Mansur yace kayi daidai abunda nake shirin yi kenan Dan wa ennan criminal din gaske ne Nazeefa kuwa tace Dan Allah kubar faeez shi ya temakeni, banda prblm dashi KO daya Mansur yace tayi hakuri zasui maganar letter nan aka kwashesu gaba sai prison Mansur yace kui zamanku a gidan ai halal dinkune, Nakune Dan da kudinku ya siya Alhaji da matarsa abun ya dauke masu Kai sukace lalle SILAR GIDAN AIKI ya zaman masu darasi sukam Sukace bari Su koma gida duk abunda ake ciki zasu tattauna letter Sukai musu godiya da kokarin da sukai musu. Lalle yau allura ta tono garma Bayan tafiyansune suka kalle gidan sukace lalle Nazeefa kinsha wuya a rayuwa, karewa gidan kallo tsab sukai suka shiga ciki suka Fara tattaunawa MUJE ZUWA

Post a Comment for "SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 16"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...