Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 13

SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 13

- - Post a Comment
SILAR GIDAN AIKI

CHAPTER 13


Nazeefa ce kwance a cikin daji jikinta duk jini, kukan zuciya takeyi dan bako digon hawaye a idanunta, rintsa ido tayi Tace a zuciyarta ya Allah see me through, Idan nama laifine ya ubangiji ka yafemun, ina ganin jarabta kalala, tadau mintina tana addu'a a zuciyarta dan Halin da take ciki Allah ne kadai zai fidda ta, Bude Idonta tayi taji karfi yazo Mata, take cewa dole nasan abunyi cos zamana anan dajin akwai matsala sai wani dabba ma yazo ya cinyeka ba Wanda ya tsani

Mik'ewa tayi dukda jikinta na mata ciwo da wani irin jiri da takeji ta tattara kayanta a Ghana most go ta Fara tafiya, though kayan ba wasu masu yawa bane bazasu wuce Kala 7 ba, tafiya take tayi tana istigfari tana neman Allah ya kawo Mata dauki

Tayi tafiya me nisa saiga wasu Fulani tashi masu tafiya da da shanuwa da karnuka harda jakuna, Ku temakeni tace masu Sannan Ta fadi kasa,

Hardo babansu yace hayya, kuzo wasshe na Neman tamako, da sauri sukazo wajen Nazeefa data fadi kasa, se nishi takeyi, Ganin jikinta duk jini suka Kara tausaya Mata suna tambayanta meya faru? Ko yan kidnapping ne suka kamata? Girgiza kai tayi ta nuna musu alamun zatasha ruwa, Ruwa suka dakko suka bata tasha tadau mintina kusan 6 sai gashi ta dawo hayyacinta amma da alamun yunwa a tare da ita, Da baba Hardo yagane haka tatso Mata fresh Nono sukai suka bata tash ta koshi sosai, Sannan suka Dan bata wani jik'e jikensu da suke tafiya dashi saiga Nazeefa Cikin ikon Allah ta dawo normal sedai Kasai jikinta da yake mata ciwo

Sannu Yar'nan Sukace mata

Nazeefa tace" yauwa baba nagode

Kowa se kallonta yak'e karamin cikinsu yace" Baba wannan dakyau take sosai

Kowa yayi murmushi yace" Hakane

Sannan suka Fara tambayarta me ya kawota nan? Ita Yar inace?

Wani hikima Nazeefa tayi aranta tace be kamata na fadawa kowa halin da nake ciki ba balle ma wa ennan ai se su tsorata Dan Fulani akwai tsoro

Shuru tayi na yan mintina, maganar Baba Hardo taji for the second time yace" meya kawoki nan? Satoni akai tace musu shine na samu na gudu Zan tafi gida!

Tsoro sukaji sosai sukace yan kidnapping kenan Bari mui maza mubar nan, Tace to Zan biko idan naje cikin gari sai in sauka suka amince suka bata jaki daya tahau dayan kayanta Suka Fara tafiya

Sunyi tafiyar kusan awa daya sannan suka shugo gari, Nazeefa kuwa tasan idan ta shiga Chan cikin garin akwai matsala, cos batasan inda zata saukaba gwanda ta sauka anan

Sunan Baba Hardo ta kira tace Zan sauka anan Zan hau babur ne dazai karasa dani kauyen Mu

Toh Hardo yace" Mata ta sauka suka sama gora mekyau suka d'ura Mata fresh Milk din, sannan sukai Mata fatan alheri, tace tagode SosaI

Nazeefa tsaye tayi bayan wani gida, kallon mutane take tayi kowa se harkan gabanshi yakeyi, Wasu na dariya wasu na shagunansu se sauraron karatun qur'ani sukeyi, Wasu zafafan hawaye suka zobo Mata tace" Allah sarki inama nine, Garin ba mutane sosai amma ya burgeta

Da yake bayan wani gida take mekyau ba mutane ta wajen tai zamanta, rufe ido tayi tana tino rayuwar da da yanzu ba daya bane, da da yake ganin tanashan wahala Ashe gwanda Chan, zataci mekyau zata kwanta a mekyau, dataga tinanin naso yai Mata yawa tace Astagfirullah, shingida tayi bacci me dadi yai awon gaba da ita

Ba ita ta tashiba se gab da magrib, jitai rayuwar se aslow amma ya zatai? Istigfari take tayi har aka kira magrib

Dukda tana cikin wani yanayi bai hanata jin sanyi a zuciyarta taba, Saboda istigfarin da takeyi yasa Mata natsuwa da walwala

Seda ta Bari gari yadanyi duhu sannan ta Dan bude Jakarta ta dakko kudi taje ta Dan kewaya a cikin garin, Shago tagani Taje tasai pure water guda 4 ta dawo ta fak'e idanuwar mutane ta shugunna tai fitsari dukda darene ba Wanda ma zai ganta

Alwala tayi tazo tai sallah ta roka Allah ya kawo Mata dauki, bayan ta idar ta Dan sha Nonon da fulanin nan suka bata tasha ruwa tajita Alhamdulillah.. tinanin inda zata kwana kawai takeyi, abubuwa take tinowa se hawaye takeyi, lallai rayuwa ba sauk'i kam, Allah yasa Mu cika dakyau da imani...AmeeenAmeeen

****
Misalin karfe 10PM hajiya Bilkisu ta kasa zama a dakinta, Se safa da Marwa takeyi a cikin dakin ta kwanta ta kasa ballema tai tinanin bacci, Kawai Nazeefa ta tino yanzu tana cikin wani haline? Meyasa bataba zuciyarta hakuriba tunda anga Gold din, da saisu barta susan yanda zasu zauna da ita, yanzu idan Bata gari suka chapketa fa? Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun tace" Kawai hawayen tausayi na fitowa a idonta,

Hussaini ya fito daga room dinshi zaije kitchen ya soya egg Dan ka'idarsu kenan duk dare sai sunsha shayi da bread sometimes harda kwai, bekai ga shiga kitchen dinba yaji alamun tafiya a room din mamanshi, Murda kofar yayi yaji is locked then yai knocking kofar, Hajiya tai sauri ta share hawayenta ta bude, 4eye's sukai da Son dinta

Kallo daya zakai mata kasan tana cikin tashin hankali, Rik'e hannunta yayi yace" Mom are you okay kuwa?

Kirkiro murmushin karya tayi tace" oh yeah I'm fine dear me ka gani!

Kara damke hannun mum dinshi yayi yace" no Mum you're not okay can you please tell me meke damunki?

Tace yeah but tomorrow yanzu dare yayi kaje ka kwanta kuma karka fadawa Hassan cewa something is wrong with me Dan nasan sani a gaba zakui

Sedai goben kawai zamui magana, Peg kiss yai Mata a kumatunta yace" OK bye Sweet Heart have a lovely might rest

Tai smiling tace" Allah ya sa yace Ameeen Tun Asuba Nazeefa sanyi ke kad'ata, Zak'olo hijab dinta tayi ta Kara rufe jikinta, idonta biyu aka kira sallar asubahi dan haka ta tashi ta dakko ruwan data siyo tai fitsari tai alwala tai sallah ta zauna tai azkar, da yake ta haddace su akanta, Ganin safiya tayine ga mutane sunfara zirga zirga a Ung ta tashi ta nannade kayanta ta zura a jakar ghana most go dinta, Ta ajiye chan karshen lungun dan bama wanda zaiyi tinanin akwai wani Abu +

Shiga cikin gari tai sosai, jitai garin na Mata dadi, Kallon al'adar garin take gwanin sha'awa Ba ruwan wani da wani, kowa abunda yasa gaba shi yakeyi, tana tsaye wasu Mata da miji sukazo wucewa ta gabanta sun burgeta sosai, kana ganinsu kasan suna tsananin son junansu, Dan hannunsu rik'e yake suna lafiya suna hira hade da murmushi a fuskarsu, A zuciyarta tace" inama nine! Inason inga Ana soyayya yana burgeni sosai, Nan take se taji tanajin haushin kanta, tace wama zai sota bare ta sama irin soyayyan nan, hawaye ne suka zobo mata Tace" Ya Allah ka kawomun dauk'I Haka taketa kallon masoyan nan har seda suka bace Mata!

Gidan Sarki
Hajiya ne zaune a fad'eden falonta, Kuyangi se tausa suke Mata, Hassan ne ya shugo ya gaisheta ta amsa, apple din dake kan plate ya dakko ya faraci, Saiga Hussani, Shima zama yayi kusa da Hassan, ya dakko Apple yanaci, Ganin yaranta biyu sun hadu ta Kora kuyangin nan tace subar wajen Sukace Angama Hajiya

Hussaini ya kureta da ido yace" Mum our promise kin tuna? Hassan yace Our promise kuwa? Wani alkawarine wannan da bansaniba? Hussain ya dafa Bro dinshi yace" Calm down sarkin jin kwakaf,

Hassan yace OK to Shikkenan, Kallon mahaifiyarsu yayi se a time din ya lura da yanayin mood dinta yace" Hajiya Lafiya kuwa KO bakijin dadine

Kafin tai magana, Hussaini yace" ai maganar zamui yanzu kenan,

A tare suka hada baki sukace to Menene Hajiyarmu?

Kallonsu tayi cik'e da tsantsan Kauna zata Fara magana kenan Sega me martaba Sarki yazo, Cos tunda Hajiya ta tashi da safe bataje sasanshiba saboda duk safe se taje, So Yajita shuru sai yasa ya biyo baya

Ya naganku anan this early morning bakuje aiki bane? Inji me martaba

Hada baki sukai sukace today is Saturday

Ohh Namanta yace" wato shine akaimun wayau wani meeting akeyi anan da ba a gayyaceni ba?

Murmushi sukai basuce komai ba, Me martaba ya kalle matarsa yace me ya sameki KO bakijin dadine? Hussain yace Dad tambayar da muke Mata Kenan, Dukansu suka kureta da ido

"Hajiya Bilkisu ta soma magana kamar haka tace" hmm Da lafiyana ne da da sauki, Kawai Ina tinanin Halin da Yar'nan Nazeefa ne zata shiga, yanzu duniya ba gaskiya, tana magana muryanta na tawa!

Me Martaba dukda yafi Hajiya saukin Kai Tsaki yayi, yace Zancen banza da wofi, Ni kunsan ban daukar raini da Wawanci, Nan a ga yarinya tai sata dumu dumu shine har zaki Tara yaranki? Sui Mata mene? Nasan be wuce kice aje a nemota to banan gidan ba Ina fada miki, Sannan ya kalle yaranshi yace" Ku bace anan KO na bata muku rai, Amma kekam baki da hankali, Mtswww yai ficewarsa, Wani Tinani Hajiya tayi tace" hakane fa banda hankali da ta tafi da gold din 3M inyi yaya, tsaki itama tayi taji ta tsana Nazeefan gaba daya

Bangaren Su Suhaila kuwa burinsu ya cika dama sun kudara sai sun sa Nazeefa tabar gidan kuma ta Bari, Sai chusa kansu suke wajensu Su Hassan amma Ikon Allah Su Hassan kamar sunsan Sune Silar barin Nazeefa gidan ko kulasu basayi,
Hassan da Hussaini ne zaune suna discussing abunda akaima Nazeefa Sam be daceba, Hussani yace kabari, Nifa ban yarda dasu Suhailan nan ba, Hassan yace" tab gaibu kenan, Bakaga sai shige mana sukeyiba ko zamuce muna sonsu? Hussaini yace" kaga psychologist kaifa akwaika da karanta mutun, Hassan yace" tuni na ankare Su ai sai yasa bana musu Wasa, Hussain yace tab Allah to yasa Mu dace Hassan yace" Ameen

Nazeefa ne Ganin jikinta na Mata ciwo tace" Bari naje chemist Ko Zan sama magani, Wani Dan madaidaicin shagon saida magani ta gani ta Shiga, tace abani maganin ciwon jiki

Me zama a chemist dinne yace na nawa? Dago kan Da zatai suka hada ido dashi, kashe Mata ido yayi Dan nan take yaji yana kaunarta

Ce Mata yayi yan Mata amma ba anan garin kikeba ko Harara takai mai tace Bansaniba nidai kabani magani inzaka bani! Miko Mata yayi tace ga kudin yace yan Mata kodan kyanki kibar kudin, tsakk tayi tace wasu dai kamar bunsuraye suke wlhi

Tafiya takeyi samari sai nunata suke wai Kai yarinyar Chan ta hadu...

****
Bangaren Mubeen kuwa Abubuwan da Haleema takeyi ya isheshi Dan ta kaishi bango, Dan haka samun mahaifiyarshi yayi yace" shi gaskiya Ya gaji da zama da ita bazai iyaba, ga kazanta gashi batamai abinci, seya tafi aiki ta taro kawayenta suzo kowa ya dafa abinda ranshi keso amma shi idan ya dawo sedai ya dafa da kanshi

MOM dinshi Tace" Alhamdulillah nima dama na gaji, aurenku getting to 4years kenan ace KO Bari bata taba ba, to gaskiya ba nan gidan ba, yanda kuke KO ukun nan munaso ku Tara mana jikoki ta KO Ina,

Kabari mugani dole nema ka saketa Dan bazamu iya zama da juya ba

Hankalin mubeen ya kwanta cos mamanshi ta goyon mai baya yace to shikkenan Mum

Part dinsu ya wuce me murna yakeyi

Yana fita Mum dinshi tace" Aiko Zaman gidanki ya kusan karewa a nan gidan, ba ansama abunda akesoba, Ji yanda Mubeen ya koma abun tausayi hmmmm

Tana ganinshi taga face dinshi dauke da fara'a, Ita kwararriyar Yar Yaudara, kusa dashi taje ta makale a jikinshi wai sanyi takeji, wani daka Mata tsawa yayi yace" wuce ki bani waje

Yau aka Fara sanyi?

Ko jiya ba'ai sanyi bane, ni ki matsamun with this your dirty mouth kazama kawai, Kalleki ko zani biki Iya daurawaba

Gabantane yai mugun fadi ta shige daki, tace kodai Mubeen Aljanu yake dashi? 2days dinnan tsorata take da al'amuranshi Haleema tunda ta shiga daki kuka ta suma, tace kayya nidai banji Dadin aure ko daya ba, Phone dinta ta zaro ta Kira mamanta tace" Mum something is wrong faa, Hubby ya chanza gaba daya ni gaskiya...... Bata gama maganar ba mahaifiyarta tace rufemun baki, what do you mean? Hakanan zakita hakuri ai inanan zuwa gidan soon, OK mum tace ta katse waya! +

 Mubeen kuwa zaune yake a bed room dinshi yana tinanin wani Abu!

***Bangaren Abdallah kuwa yayi aure, suna zaman lafiyansu gwanin sha'awa, misalin karfe 4 na yamma Mansur turaki, yaje gidansa, sallama yayi ya umurceshi da ya shugo, Zaman dayaga sunyi da matarshine gaba daya hankalin mubeen ya tashi, ya kalle abokinshi yace" Abokina kana hutawa fa! Abdallah da matarshi Fateema Suka murmusa a tare,

  Abdallah yace" fateemah this is my Frnd! 
Sunanshi Mansur turaki, dago kanta tayi ta Kara kallonshi tace" like I heard this name before, Abdallah yace" May be cos babanshi babban mutun ne amma kinganshi nan ba abun daya Dameshi, abokinane sosai, he's very simple

   Fateemah tace" shine banganshi da bikin muba? Abdallah yace" time din yaje Karo karatune China, tace Wow Masha Allah, yaushe zaka kawomun matarka Mu gaisa?

   Duka dakin shuru sukai nadan mintina

Mansur ne ya kalle abokinshi, yace baka bata labarin  na kusan aure ba? Abdallah yace" oh sorry ban fada mata ba.... Nandai sukaci gaba da hiransu

Aka kawowa Mansur abinci yace" Alhamdulillah, matar tai fushi, Abdallah yace" you shouldn't be angry, ba kowani abinci Mansur yake ciba, Tace" Ba wani zakai aure ai bazan Bari mijina yaci abincin matarka ba,

Mansur yace oohhh Gimbiya bari dai nasa miki Albarka naji ko matar Frnd ta Iya abinci, dukansu suka kwashe da dariya

Bayan mintina Mansur yace" I'm going, Abdallah yace" Bari na rakashi, Nan ta makale Abdallah wai karsu tafi su barta

Mansur juyuwa yayi yace" tab ni da nakeso ki aramunshi nan da 10days zamuje Garinmu! Uhm uhmm tace" Abdallah ya kalleta yace Ina zuwa

     Sun fito waje M.T ya kalle Abdallah yace" Ina ka samu chingum dinnan? Wannan zata barka ka huta kuwa?

Abdallah yai dariya yace" yeah sosai mai

Mansur yace to Alhamdulillah dama inasone nan da 10days ko kafin nan zanje garinmu inaso ka rakani

Abdallah yace" haba aiko inane Zan bika karka damu, Mansur yace to Masha Allah, ba wata matsala dai ko? KO kana bukatan wani abune?

Abdallah yace karka damu idan ma Ina bukata zanma magana, yace OK Nagode, sukai sallama Mansur ya tada motarshi yana tafe inajin Wani wakar soyayya Na UMAR M SHARIFF (Alherin Allah yakai maka) Har ya Isa gida

Falon mum dinshi ya wuce ya taddata tana Cin farfeson kaza

    Mum you dey enjoy yace"

Ajiye kazar tayi tace" Beloved son Ina kaje kasan banson kana fita da yawa KO? Na Kira number ka yanata ringing baka dauka ba! Tana magana fuskarta da alamun damuwa

Laluba aljihunshi yayi yace" ohh I namanta dashi a gidane Sorry mum yana magana yana taba kafarta, Murmushi tamai tace OhK Ina kaje son?

Gidan Abdallah naje namai congrats kinsan bannan akai aurenshi, Wallahi mum baki ganshi da matarshiba sun burgeni,

Kallonshi cike da tausayi tayi tace" Ayya! Tason confirm yanason auren but ta rasa dalilin qin fito da matar da zai aura

Tana cikin tinanine yace" Mum Bari na shiga gidana! Tace OK

   Mansur nada kyayataccen gidan a cikin gidan mahaifinshi, daga gidan mahaifinshi akwai wata Yar kofa dazai sadaka da gidan

   Falo ya shiga ya kulle kanshi, Tinanin wace mace zata dace dashi kawai yakeyi, Nan ya tino da Nazeefa (Aljanarsa) yaji hawaye na kwaronyowa a idanunsa, Seda yadau minti kusan 20 a haka, wata zuciya kuma tacemai meye haka, be strong mana

Karar wayarshi yaji yana dubawa yaga numbers da Wanda yai saving kusan 50 missed calls yanabi daya bayan daya yasan duka. Numbers din Mata ne, Guda dayane na. Na miji shima Abdallah ne, nan take yai calling back yamai ya yaje gida Yace Alhamdulillah

***
Bangaren Nazeefa kuwa ganin zamanta wajen nan bazaiyuba, ga yunwa na addabanta yan kudin da take dashi duk ya kusan Karewa, Gashi ko wasu sungane alamun akwai mutun ne, Samari suka Fara zirga, Tace" ina zamana. Anan bazaiyuba gaskiya Dan hka ta kwace inata inata batar wajen ta tsunduma cikin gariii

Tofaaa Nazeefa na ganin rayuwa! Bari muji mezai faru

Post a Comment for "SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 13"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...