Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 10

SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 10

- - Post a Comment
SILAR GIDAN AIKI
CHAPTER 10


Mansur Turaki tashi yayi yaji jikinshi somehow, toilet ya shiga yai wanka sannan ya dauro alwala yazo yai sallah raka'a biyu, bayan ya idar ne ya karanto wasu addu'oi sannan ya rok'a Allah duk inda aljnarshi take ya Allah ka kareta, ka tsareta Amen, A ranar nan dai wuni yayi bejin dadin jikinshi se tinanin other half dinshi yake +

Bangaren Gidansu mubeen kuwa, Tun dare basuga Nazeefa ba, kowa hankakinshi kwance banda Mubeen, se zirga zirga yakeyi a gidan KO ze ganta shuru, gabanshine yai mugun fadi har dai ya kasa hakura yaje wajen mum dinshi yace" Mum Kodai Nazeefa batada lafiyane tun jiya ban gantaba,

Mum ta taba cikinta tace" kuma yunwa nakeji muje mugani ko jikin ne, Mum na tafe, Mubin nabinta a baya har suka shugo dakinta Wayam suka gani!, ba kayanta, katifar ma ta nadeshi ta tattara gebe, Mum ne tace me nake gani haka!

Wani jiri ya kusan kwasan Mubeen ya dai daure ya jingina da bango in banda innalillahi wa Inna ilaihir rajiun da yake ambatowa!

Mum ta kalleshi tace" Ina taje yarinyar nan ta gudu kenan, innalillahi.........

Mubeen yace" daga gani Mum ta gudu tunda ga shaida nan, tun jiya ba motsinta fa, Nan take Mum taji kirjinta na bugu for no reason tinani ta shiga yi sosai ta fara Nazeefa Ina kikaje Ina kikaje, Mubeen yace Aranshi kema kenan

Suna tsaye saiga faeez da faeeza, Feeza cikin yanga da iyayi ta sako riga da wando tace" what's happening here, Mum ne tace bamuga Nazeefa bane shine abun ya tsaya mana arai, tace ohh to kuje Ku zauna mana ita taima kanta, tunda tanacin arziki ita duk me Mata ba, wani harara Mubeen ya bita dashi, Tace ohh Na tinafa Kunsan kishi takeyi saboda Mubeen bazai auretaba

Dukansu suka maida kallonsu gunta, mum tace 6ace anan Mara kunya, Faeez kuwa girgiza Kai yayi yace" Allah sarki jiyan nan fa na fito naga sekai kawo takeyi a Cikin gidan nan na tambayeta kotana da damuwa ne be gaba magana na Gaban Mubeen yace Gham tsoronshi kardai ta fada Mai abunda ya shiga tsakaninsu

Mubeen ne yace rufe mana baki, Faeez yagane ba komai bane illa kishi seya chanza magana!

Yace Bansan tafiya zataiba wallahi Dazun nan tace batada number na, in bata, Zare Ido Mubeen yayi yace" shikkenan Nazeefa ta tafi, Faeez tausayin Yayanshi ya kamashi dan yasan tabbas ba karamin Son Nazeefa yakeyi, Nan take idon Mubeen yai ja

Hajiyarsu kuma in banda faduwar gaba ba abun da takeyi

Mubeen dakyar ya shiga daki dan wani irin saramai da kanshi yaji yanayi, Shiga daki yayi ya jingina da bango in banda kuka ba abun da yakeyi

Kuka yayi sosai ma'ishinshi sannan ya dakko wayarshi ya shiga gallery, kallon pics dinta yakeyi wasu sabbin hawaye na kara zobomai

Allah Sarki Nazeefa yace a mind dinshi Ina Zan ganki, ji yayi gidan yamai zafi ya tashi ya shiga toilet ya watsa ruwa ya sako riga da wando irin track suit dinnan

Key din motarshi ya dauka Ya fita ya rasa ma Ina zaije,

Abokinshine Dr Bashir ya fado mai a rai, direct gidanshi ya wuce yana ganinshi yace Mubeen lafiya kuwa ko mutuniyarce?

Kallonshi yayi ido Cikin ido yace Dr bashir ka cuceni, ka cutar da rayuwata, yanzu ga abun da kasa nayi nan kasa SILAR abun danai ma Nazeefa tabar gidan, Ni wallahi ka cutar dani har abada

Dr bashir ne yace calm down abokina kayi hakuri, the damage has been done already Dan Allah ka yafemun

Kallonshi Yayi kamar zai rufeshi da duka Dan takaici, Gaban Dr bashir kuwa se faduwa yakeyi, shima nan take yai nadama Se lallashin Mubeen yakeyi

Yace" kayi hakuri Nazeefa takace, Wata harara yai Mai yace please stop deceiving me, ta Ina Zan ganta balle ta zama nawa

Dr bashir yace" nasan duk inda take zama ta dawone cos in ban mantaba kacemun bata da kowa, why not Mu saka gidan radio? Sannan Mu bazama nemanta?

Sake baki Mubeen yayi yace" Serious? Dr bashir yai smiling yace" hakane yace OK

Sundau lokaci suna tattauna yanda zasu bollo ma al'amarin, Mubeen yaji dadi sosai sannan ya koma gida Nazeefa ne suka sauka a wani kyayatataccen Gida, kallo daya zakaima gidan kasan Gidan sarautane ga kyau ga shi yasha ado, direct wani babban falo suka shiga aka nuna mata wani waje ta zauna, Nan take mutumin nan ya umurce yan aiki dasuka kawo Mata abinci +

Da fitarsu suka kawo Mata kayan shaye shaye, dana marmari suka ajiye a gabanta kallonsu tayi tace nagode sukace karki damu

Bayan taci ta sha tagode Allah ta sama Waje ta zauna tana Mai Kara kallon falon da take, lalle dakin ya mugun haduwa balle abunka da gidan sarakai

Wata matace ta shugo kallo daya zakai Mata kasan matar gidan ne, samun waje tayi ta zauna tana Mai kallon Nazeefa, Bude baki tayi tace baiwar Allah zo mana, Nazeefa ta mik'e taje kusa da ita ta tsugunna nan ta gaisheta, tai Mata wasu tambayoyi daga Ina take tace satota akai, Hajiya Bilkisu me gadon Zinari ta girgiza Kai tace" ki kwantar da hankalinki ki zauna nan kamar gidanku, kome kikeso Ki sanar Dani!

Nazeefa kanta na kasa tace" OK inshaa Allah, Tace ya sunanki? Tace Nazeefa tace Masha Allah nice name, hope kinci kin koshi ko? Nazeefa tace" yes I'm OK, Nan dai tai mata tambayoyi sosai ta amsa ciki ta tausaya Mata sosai

Zo muje tace" Hajiya ta mik'e tana biye da ita a baya, Wani Daki takaita sannan ta bata kayan sawa a kalla kala 4 tace zo muje, Wani daki suka wuce da yan Mata gudu 2 a ciki suna ganin Hajiya suka tsugunna suka gaisheta, tace" sannunku ga Yar uwa na muku please Ku zauna lafiya bansan hayaniya, Nazeefa na kallon yan Matan nan, Aranta tace Allah dai yasa Mu zauna lfy, cos naga take takensu, tana cikin tinanine Hajiya tace" Nazeefa ga toilet Chan Ki shiga ki wanka ki chanza kaya

OK Tace Mata sannan Hajiya ta koma Dakin Mijinta (Wanda ya kawo Nazeefa)

Nazeefa kallon yan matan nan biyu tayi kallo daya zakai masu kasan bayine daga gani y'anta Su akai Dan suna da kyau Masha Allah, sannunku tace masu sukace yauwa

Da yake Nazeefa gogaggace itama da zata shiga bayi jakanta ta bude ta dakko towel, Ta daura, direct bayi ta shiga Tasha wankanta sannan tazo ta shafe jikinta da Mai, kasancewar black beauty ce ba wani Kwalliya tai ba, Comb ta dakko tana sharshe kanta, Yan Matan nan biyu masu suna Suhaila da Jamila suka rike baki, Dan gashin Nazeefa ma abun kallone tunda asalinta Fulani ne

Kowa da abun da yake sakawa aranshi

Bayan ta gama taje kanne ta koma gefe tai zamanta, Su KO jamila Da suhaila se hiransu sukeyi

Nazeefa na zaune tinanin Mubeen ya fado Mata arai, tasan duk inda yake hankalinshi ba kwance yakeba, amma idan ta tino da duk halin da ta shiga kusan ta dalilinshine se tace Allah ya kara, Se tinanin good time that they spend together take, wani hawaye taji yana shirin kubce Mata tuni ta mike ta koma toilet ta dauro alwala tazo ta shimfida tai sallah raka'a biyu sannan ta sama sukuni


****Hajiya Bilkisune taje wajen mijinta suna hira, Hira sosai sukeyi abun se Wanda yagani Dan son junansu sukeyi sosai, Kallon Alhaji tayi tace" Wallahi wannan Yarinyar ta shigar mun Rai, Sosai jinta nake tamkar yar dana Haifa a cikina, Alhaji yai dariya yace" Hakane dama akwai yara maso shiga zuciyar mutun kaga kanajinsu tamkar Kai ka haifesu tace" tabbas hakane

Suna cikin hirane saiga Wasu Samari biyu sun shugo, Kallo daya zakai musu kasan yan biyune Dan ba abunda ya banbancesu kuma suna Kama da maihaifinsu sak

Tsugunnwa sukai sukai musu sannu da gida suka amsa cike da farin ciki

Hussaini ne ya kalle mamanshi yace meye sirrin Hajiya naga se murmushi kikeyi

Washe baki tayi tace nasama sabon yarinya

A tare suka hada baki wacece ta haihu kuma?A tare suka had'a baki sukace wacece ta haihu kuma? Hajiya bilkisu dariya tai musu tace" ba wacce ta haihu, baridai Ku ganta yanzu nayi yarinya wacce zata ebemun kewa, Alhaji dake kan kujera yanacin Apple shidai binsu da kallo yayi +

Hajiya bilkisu ne ta kwalla ma wata baiwa kira a cikin gidan tazo ta tsugunna a gabanta tace" mata kije dakin Chan na yan Mata ki kiramun Nazeefa, angama tace, Minti 2 saiga Nazeefa ta shugo dakin sanye da dogon hijab dinta, se kamshi takeyi, dukansu saukar da idonsu akanta sukai, Hajiya Bilkisu tace" kungantanan KO?

Nazeefa d'ago Kai tayi Dan kallon samarin nan biyu suma at the same time suka Kara Kai idonsu gunta, tana kallonsu taji wata muguwar faduwar gaba, lalle suna kama sosai kuma fuskarsu tai mata kama da wani! Nan take ta nema natsuwarta ta rasa se dabur dabur Takeyi

Hajiya ne ta Lura da ita tace" lafiyarki kuwa? Girgiza Kai tayi tace" kantane ke ciwo, Sannu tace Mata sannan ta kara da cawa AI dole kanki yai ciwo yanda kukasha hanya, eh tace mata but gabanta na ci gaba da faduwa

Samarin nan biyu suma ko wanne da abun da yake sakawa a ranshi, lalle yarinyar nan dakyau take, ko Ina suka samo ta oho

Nazeefa ta shiga tinani taji Hajiya Bilkisu me gadon zinari tace" ga yarana nan Su biyune kadai maza babban yayansu tayi aure, So kome kikeso Ki daukesu tamkar yayyinki kome kike so ki tambayesu, sannan ta koma gunsu tace" ga kanwa na maku Ku rik'eta amana, Sukace inshaa Allah

Sannan ta kalla Nazeefa tace kije kice Su Suhaila Su baki magani akwai achan dakin, Allah ya Kara sauki tace" Ameen, suma sukai Mata sannu tace" yauwa

Bayan Nazeefa tabar dakin ne Hassan yace" Ina Kika samo ta? Hajiyarsu ta murmusa nan ta gyara zama ta basu labarinta tsab, sun tausaya Mata sosai sannan sukace zasu rik'eta amana

Bangaren Mubeen kuwa biki nata matsowa iyayanshi sun gama shirya komai part din Da zai zauna an Kara gyarashi abun se Wanda yagani

Tun bayan tafiyar Nazeefa Mubeen be zama a gida ya rasa abun dake mai dadi, Nadama kam yayi na cutar da rayuwar nazeefa da yayi, shi tsoronshi Allah yasa ta fada hannun nagari Dan sonta da tausayinta ya mugun Kama shi

******
Kwance tashi asarar Mai rai bikin Mubeen da Haleema yau saura kwana uku. Mubeen kam in banda bakin ciki ba abun da yakeyi, dukda iyanshi sunkaishi wajen boka shi Sam har yanzu be taba jin sonta a ranshiba, kawai umurnin iyayene

Yana zaune yana tinanin Allah yasa lokacin bikin a tura shi wani course Cyprus Dan sunce Cikin week dinnan zasu turasu text din Haleema ne ya shugo kamar haka _angon kwana uku hope you're fine plz ya Kama ta kazo fa muyi maganar bikin Mu, cos inata kiran numbernka baka picking_

Ya na gama Karantawa ma yai switch off din wayar Dan shi kadai yasan abunda yakeji a zuciyarshi

Bangaren Haleema kuwa shuru shuru bataga reply ba, ta Kira numbern Taji a kashe, Hawaye ta Fara ta wuce direct wajen mamarta ta zube a gabanta tana kuka, Maman ne tace what happen Amarya

Haleema cikin Kuka tace Mum Sam Mubeen be sona kinga yaushe rabon da yazo gidan nan ni gaskiya na fasa auranshi,

Maman tane ta zare ido tace bakida hankaline zakice kin fasa auranshi? Ke kinsan tanadin da nakeyi? Kar in sakejin irin wannan maganar

Zunburo baki tayi ta tashi Cikin shagwaba ta shige dakinta ta haye gado tana kallon wayarta hawaye na zubo Mata!

Tino da saurayin da suke shakatawa tayi, number shi tai dialing taji number busy, takaici ya kara kamata

Tsaki tayi ta sake dialing for the 2nd time ya dauka muryanshi na rawa, ranki ya Dade yace" tace tare da naka ya al'amurane?

Yace se ahankali fa inanan inata missing dinki, murmushi tayi tace realy? Hararar wayar yayi ya wani tabe baki yace" da gaske nake!

Tace karka damu, inanan tare dakai, Yace OK Madam, nace ba!

Tace mene? Yace Zan sama koda 10k? I'm broke ne, tace karka damu masoyina yanzun nan zaka alert I love you ta kashe wayar

Kallon wayar yayi yace" Wahalalla kawai, da ba kudi kike bani ba kina tinanin da yanzu muna tare ne mtsww , Alamun message yaji ya Shugo Mai yana dubawa yaga alert na 30K wani ihu yayi yace yau akwai zuwa club, (Allah) ya shirya

KO thank you be ai ka mata ba yahau tsohon bike dinshi se ATM

Post a Comment for "SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 10 "

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...