Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

RAI BIYU CHAPTER 5

RAI BIYU CHAPTER 5

- - Post a Comment
RAI BIYU
CHAPTER 5


Ihun da na yi ne yasa Inna fitowa daga ɗaki da sauri tana kallona. +

“Na samu aikin Inna sun ɗauke ni”

Murmushin haukan da na ke ta yi, tana girgiza kai for first time bayan rasuwar mahaifinmu yau na ga murmushin Inna. Zuwa na yi da gudu na rumgumeta ina ta murna kamar babu abunda ke damuna. Haka na wuni cikin farinciki da jindaɗi kamar wacce aka yi ma kyautar kujerar makka. Ban san farincikina kaɗan ne har sai da Habiba ta dawo na sanar mata da labarin sai ta yi kamar zata haɗe kanta dan murna kai kace ma ita ta samu aikin ba ni ba, a ranar Habiba bata iya cin abincin rana ba dan tsananin murna, da maraici ta siye alawa da kuɗin Inna ta yi sadaka. Haka ta ke nunawa kulawarta da damuwa a duk lokacin da wani abun ya sameni, ta kan zauna ta labarta min abunda Inna bata sani ba, zata iya ɓoyewa Inna abu amman ni bata ɓoye min ba, mutune har mamakin yadda muke son junanmu suke, ganin ita take bina amman bama taɓa samun saɓani, ko ma mun samu tun anjima kaɗan zanje na rarrasheta ko kuma ita ta zo ta bani haƙuri ko da kuwa ni ce bana da gaskiya, irin tsabanin da ake samu tsakanin mabiyi da mabiyi ni ban cika samunsa da Habiba ba, muna son junanmu sosai, ko ciwo ɗayan mu yake sai ɗayan ya ji kamar ya cirewa ɗan'uwansa ya sakawa kansa.
Lokacin da Baba na da rai idan ya tashi zolayarmu har cewa yake yadda muke son junanmu bama sonsa haka, wani gurin ma idan mukaje ba dan kamanni ba da mutane za su ce Habiba ƙawata ce ba ƙanwata ba.
Ba zan iya misalta irin son da take yi ma Noor ba, tun da na haifeshi ita ce da ɗawainiyarsa har ya kawo yanzu, babu kuma wanda ya isa ya nuna masa ɗan yatsa a unguwarmu ko ma a cikin gidanmu ni kaina ban isa na hukunta Noor ba indai a kan idon Habiba ne. Ni kaina shaƙuwar ta kan ba ni mamaki, wata ƙila dan akwai tazarar shekara bakwai a tsakaninmu.

Duk farinciki da ɗaukin aikin da nake idan na tuna Baba ba ya raye sai na ji babu daɗi, na so ace na samu aikin yana da rai na san zai yi farinciki sosai, sai dai kuma ƙaddara ta riga fata abunda Allah ya rubuta dole shi zai samu bawa. A daren ranar da na samu aiki sai ga Bilal ya kirana ni a waya na yi zaton zai ce na fito ne sai ya ce na aiko masa Noor yana bakin ƙofar gida, ba musu na miƙawa Noor wayar, ban san mi suke tattaunawa ba kawai dai na ga Noor yana dariya yana ɗaga kai sai kuma ya wulgumin wayar ya tashi ya fita da gudu har yana ƙoƙarin faɗuwa.

“Falfala da gudu ɗan gidan Bilal sai in be kiraka ba”

Cewar Habiba tana dariya. Nishaɗin dake fuskarta shine a fuskar Inna da Jamila har ma Sakina da kuma ni kaina.

“Bilal ɗin nan yana son Noor kuma na tabbatar son da yake miki ne ya shafe shi”

Na ɗago na kalli Inna da furucin da ta yi.

“Ba fa so na yake ba, mutunci ne kawai a tsakaninmu, be taɓa cewa yana so na ba”

Habiba ta watsa min harara.

“Ji matar nan muna-muna munafuka, Wallahi son junansu suke amman shi ba zai iya faɗa ba ita ba zata ba shi dama ba, ai da yanzu an wuce gurin, duk alamun da yake nunawa ai na son ki ne, ke kuma kina kauce masa”

Na yi dariya ina girgiza kai.

“To ya kike son na yi?”

“Ya dai kamata ki bashi dama, zama haka ba zai yiyu ba, Allah kaɗai yasan iya gulmar da ake muku a unguwarnan, kin kore kowa kin zauna a gida gashi har mahaifinki ya rasu be ga wani auren na ki ba”

Wannan karon Inna ce ta yi maganar, kuma maganar da ta yi ta ɗan taɓani, tabbas mutuncin ƴa mace da kuma darajarta a gidan aurenta ne, sai dai ba kowa ne zai maka son tsakani da Allah ba, wasu kan zo so na saboda sha'awata da sun gwasa sun gano ni ba ƴar iskar barawarar nan ba ce sai su gudu, wasu kuma su nuna maka ba zasu yarda da je da yaron ka ba, wasu kuma basa da wani sana'ar kirkin da za su iya riƙe sauran iyalansu ma balle kuma a haɗa da ni, kowa da irin matsalarsa. Bilal ɗin ma laƙe min ya yi da sunan abota, sai dai ko da wasa ban bashi alamun da zai iya nuna min so ba, saboda na san iyayensa ba zasu yarda ya auri mace da taɓa aure har biyu ba kuma har da ɗa ma.

STORY CONTINUES BELOW


Uffan ban ce ba, Inna da Habiba kawai ke ta nanata maganar. Muna nan zaune Noor ya shigo da ƙatuwar leda a hannunsa har biyu a hannunsa baki har kunne.

“Momy kalli abubuwan da siyo min, kuma ya ce Mama Habiba kawai zan bawa kar na sammi ki, kuma ya ce yana kiranki yana ƙofar gida”

Shi da Habiba suka riƙa kokuwar buɗe ledar, ni kuma na zari Hijabina na nufi ƙofar gida. Tsaye na sameshi yana kallon ƙofar gidanmu da alama dai yana jiran fitowata ne.

“Ina ta zuba ido na ganki yau a kamfaninmu ban ganki ba”

Ban bashi amsa ba sai da na yi masa sallama ina murmushi.

“Assalamu alaikum”

Sai ya amsa min da murmushi.

“Wa'alaikissalam Nawancy, na zo na taya ki murnar samun aiki, ai na faɗa miki zasu ɗauke ki”

“Ɗazu na samu saƙon, na jidaɗi sosai”

“Mutane na ta zuwa karɓar uniform amman ke ban ganki ba”

“Uniform kuma?”

“Yes ai Uniform zaku saka, tun safe ake zuwa ƙarɓa kin ga ɗaga yau zuwa gobe ne kawai ake bada uniform ɗin, on monday zaku fara zuwa aiki, kuma idan kunje karɓar uniform ɗin za a nuna muku irin aikin da zaku yi”

“Gobe zanje Inshallah, ai ban san ana zuwa yau ba”

“Sai dai matsala ɗaya, Nawancy bana son ki saka wando, ina ganin kamar ba be dace ba”

‘Musamman ga irina masu manyan mazaunai’

Na faɗa a raina. A fili kuma sai na ce.

“Ai zan iya saka Hijabi ko abaya a sama”

“Amman baya son haka, sai idan kin tashi aikin ko kuma idan zaki shigo, shi be yarda ma ko hula a saka a gurin aikin ba balle kuma Hijabi”

Cike da mamaki na ce

“Ba musulmi ba ne hala?”

“Wallahi musulmi, amman mutumen sai a hankali, haka zaki ga tattoo a jikinsa, ina jin ya zauna waje ne”

Na taɓe baki cike da ƙyamar halin mutunen duk da ban san shi ba

“Allah ya kyauta amman abun baƙinciki ne ace musulmi ya rinjaya wani addini sama da nasa, ga shi ka ce ya cika tsanani”

“Yana da tsanani sosai, amman tsananinsa yana burge ni wani lokacin, kin ga dole kowa ya riƙe aikinsa da muhimmanci, kuma kin ga wacan da aka canja baya damuwa da duk waɗannan abubuwan shiyasa duk ƙarshen wata sai an siyo kayan abincin da cups da aikatan gurin suke aiki da su, amman zuwan wannan ya saka dokar duk wanda ya fasa masa cups za a cire cikin albashinsa, dole kowa ya riƙa taka tsantsan da abubuwan gurin”

“Amman daman ba a biyan kuɗin abincin ne?”

“No ana biya restaurant ɗin da ke cikin kamfanin ai nasa ne, amman idan ba restaurant ba kin ga ma'aikici zai buƙaci shan ruwa ko wani abun ko kuma tea musamman ga masu zuwa tun safe, ko kuma idan aka yi baƙi, to duk da wannan cups ɗin ake amfani. Bayan ma wannan kamfani suna da Sabuwar Asibiti da aka buɗe nan by pass, One-On-One Special Hospital, amman ance ta masu kuɗi ce dan katin ganin likita ma ɗari takwas da hasin ne”

Na jinjina kai ina faɗin.

“Kamfanin ma akwai girma, ni Allah yasa ma har na yi aikin na gama ba zan ganshi ba”

Sai kawai yasa min dariya.

“Kina tsoro ne Nawancy?”

“A'a ba tsoro ba ne, kawai ba zan iya jurar wulaƙanci ba ne, kaga ƙara ma ace bamu haɗu ba”

STORY CONTINUES BELOW


Mun daɗe muna fira yana ta labarta min kamfanin da kuma wasu abubuwa na cikinsa da kuma yadda aikinsa yake, kamin hirar siyasar ƙasar nan ta shigo ciki, sai tara da rabi muka yi sallama ya tafi ni koma na cikin gida.
Ko da na shiga su Habiba sun ci sun ciye an gutsura min ɗan tsiton cake da nama ƙwara ɗaya an aje min sai kuma ice cream a cibi.

“Yanzu wannan abun kawai zaku bar min?”

“Eh mana dan kin samu ma mun rage miki”

Cewar Habiba, tana bani amsar tambayar da nayi, sai Noor yasa dariya yana cin namansa ya ce

“Momy ƙyale Mama Habiba sai ta yi bachi zan ƙara miki karki kuka kinji?”

Sakin baki Habiba ta yi.

“Au ni zaka watsawa ƙasa a ido?”

Ta kai masa dudu. Inna tasa dariya, yau kan ba laifi muna cikin farinciki farincikin da muka daɗe ba mu yi ba tun bayan rasuwar Baba, sam ba zaka gan mu a yanzu ka ɗauka akwai wata damuwa a ranmu ba. Daman can talauci baya hana mu walwala ko kuma farinciki, idan ka ganmu a damuwa to muna jin yunwa ne, da kuma mun samu mun ci sai mu gode Allah da wannan ni'imar, mu kuma roƙi na anjima.

*** *** ***

Kamar yadda muka kwana cikin farinciki haka muka tashi da shi, abun ka da sabon shiga su Noor na wucewa makaranta nima na shirya muka fita tare da Habiba ita ta wuce tata makarantar ni kuma na ɗauki hanyar gurin mu a Napep.
Yau ma da na isa ban shiga ba sai da na ƙira Bilal na sanar masa ina bakin gate, shi ya fito ya shiga da ni, sai mita yake wai ya kamata ace na shigo ciki da kaina tun da Monday zan fara aiki, ni kuma ina taka tsantsan ne gudun ƙar na yi wani abun da ba daidai ba, shugaban ya ce zai hukunta tun ban fara aikin ba.
Ciki ya shiga da ni har muka isa cikin wani ƙaton haɗi inda na faɗa musu sunana suka duba sannan suka ɗauko uniform ɗin dake cikin leda suka ba ni, sai kuma wasu takalmi masu kama ta da malaman lafiya na asibiti, suka miƙa min wasu takardun na saka hannu sai suka buƙaci idan zan dawo na zo da ƙaramin hoto na guda biyu, wai zasu saka a file ɗayan kuma a kuma na saka a catin zan rayata a wuya na shedar aikina.
Ɗaya daga cikinsu ne ya yi min ja gaba har gurin da zan yi aikin nawa, kitchen zan riƙa gogewa da kuma da ake aje files kusan ɗaki biyar, sai dai ba ni zan yi sharar ba aikina Mopping ne kawai, kuma idan zamu yi mopping ɗin sai mun saka safar hannu idan mun gama mu jefar, sai kuma goge kofuna da jerasu a muhallinsu, shi ma sai mun saka safa, tsarin kamfanin kamar na turawa, lallai sai a yanzu na tabbatar da zancen Bilal na cewa Kamfanin yana takara da kamfanonin duniya. Mai nuna min aikina ya jaddada min kamin na jera kofunan sai na ƙirga ko guda nawane na rubuta a file ɗin gurin da kuma time da na fara da time ɗin da na gama, da kuma ko kofi nawa na tarar, daga ƙarshe Bilal ya kai ni reception ya nuna min gurin da zan saka sunana da kuma lokacin da na shigo, idan kuma na gama sai na saka sunana da kuma lokacin da na fita, ƙarfe bakwai zan fara aikin na ƙare tara, hakan na nufin bakwai ta yi min a can kenan.

Irin yadda tsari da dokokin kamfanin suke sai duk na ji aikin ya fara fita raina kamar ba zan iya ba, sai dai babu yadda na iya tun da nema na ke yi kuma ba anan zan dauwamaba. Har bakin titi Bilal ya rakoni, muna tsaye da shi na hango motar Zinatu ta shiga kamfanin, na tabbatar da ita ɗin ce saboda hangota da na yi ta gilashin motar da ke sauke. Bilal ya tara min Napep na hau sannan ya koma ni kuma na kama hanyar gida ciki da mamakin tsare-tsaren wannan kamfani, gaskiya ba dan ina son aikin ba da na haƙura da yinsa, a gurin da na saba sauka na ce mai Napep ɗin ya aje, sai na karɓi ragowar canjin kuɗin da Bilal ya bashi na nufi cikin unguwarmu.

A hanya na haɗu da mai gidan da muke haya, wata irin kunyace ta mamaye mu nasan yayi mana karamcin tun da be mana magana tun baya rasuwar Baba ga shi har Inna zata gama wanka takaɓan ta cikin wannan satin. Sun-sun-sun na gaisheshi ya amsa min yana murmushi tare da tambayar ya haƙuri.

“Mun gode Allah dan Allah ka yi haƙuri akan maganar kuɗin nan, inshallah za a kawo”

“Kuɗin me? Ai Bilal ya biya be faɗa muku ba ne? Tun Margayi be yi sati da rasuwa ba ya kawo kuɗin dubu arba'in cif”

Na saki baki ina mamakin ikon Allah.

“Wallahi ba mu sani ba”

“Wallahi ya biya sai dai ayi masa godiya”

Sallama na masa na wuce zuciyata cike da hauƙin Bilal, bakina kuma har rawa yake naje gida na labartawa Inna wannan labarin. A hankali wata mota da ta fito ɗaga gidansu Manjo ta doso inda na ke, mai maotar na kawowa daidai ni sai ya sauke baƙin gilashin motarsa.
  Ashe Mustapha ne, cikin shigar manyan kaya wato farar shadda da kuma barar hula sajensa na kwanta sai sheƙi yake, da alama jumma'a zai je tun da yau friday, fuskarsa cike da annuri, sai dai bana mutanen kirki ba,  na kuɗi da kuma kyawun hallita da suka nuna isa a fuskarsa. Kallona yake ba ko ƙyafta ido, ni kuma na bawa banza ajiyarsa sam babu tsoro a tare da ni saboda na shirya tarbar ko minene daga gareshi. 
  Haka nasa kai na wuce na barshi a gurin zuciyata har wani zafi take min saboda da tsanarsa. 
   Da sallama na shiga gida, Inna da dpo suka haɗa baki gurin amsa min, hakan yasa naji kamar na janyo sallamar na mayar da ita a bakina, yau ma ya taki sa'a na sauke idona cikin nasa hakan yasa ni jin kamar na ƙarasa a inda yake zaune gaban Inna na shaƙe wuyansa.

THE GAME IS ABOUT TO START...Na ɗauke kaina kamar ban san da zaman mutun a gurin da Inna take ba. +

“Har kin dawo?”

Inna ta tambaya, ni kuma na nufi ƙofar ɗakin mu ina amsa mata domin bana son na juyo idona ya haɗu da na azzalumin mutunen nan.

“Eh Inna”

Na ɗaga labulen ɗakin mu na shige zuciya cike da abubuwa guda biyu farincikin abunda Bilal ya yi mana da kuma baƙincikin ganin dpo a gidanmu. Kayan da ke hannuna ma saman katifa na jefasu, na zauna ƙasa raina a jagule.

Jidda ce ta faɗo min a rai, ya kamata ace na tabarta masa samun aikin nan da na yi, har na unƙura zan tashi na fita sai na tuna dpo yana tsakar gida, hakan yasa na koma na zauna, sai tunanin Bilal ya dawo min rai. Lokaci zuwa lokaci na kan samu kaina da murmushi tuna irin abubuwan alherin da Bilal yake mana, wanda na san har ƙasa ta naɗe ba zan taɓa saka masa da abunda ya yi min, ya sadaukarda abubuwa da dama saboda farincikina.

Kiran da Noor yake min a tsakar gida ne ya katse min tunani, ina unƙurin tashi na fita sai ya shigo ɗakin da gudu har yana ƙoƙarin faɗuwa.

“Momy duba aka raɓa mana sabon littafi a makaranta”

Na faɗaɗa fuskata da murmushi ina karɓar littafi tare da buɗewa ina dubawa, littafi rubutu ne mai hoton ciyaman, da alama ya kai musu ziyara ne, daman naji a rediyo ana cewar zai ziyarci makarantu.

“Momy da idona na ga Ciyaman yana jawabi har da godiya ya yi mana, sai aka raba mana littafai”

Na kai hannu na shafa fuskarsa ina dariya

“Amman Ciyaman ya kyauta da ya bari Noor ya ganshi”

Sai ya ƙyalƙyale da dariya ya rumgume ni. Haka ɗa na yake, masu kuɗi da ƴan siyasa suna burgeshi ko a mota ya ga mutun sai ya tsaya kallonsa har sai ya daina hangoshi sannan hankalinsa ya kwanta, a ranar kan labari sai abunda ya manta. 
  Zaunar da shi na yi saman jikina, na soma cire masa talkamin makaranta tare da safa, shi kuma yana duba littafin tare da karantawa. Habiba ce ta shigo ɗakin babu ko sallama, kana ganinta kasan a gajiye take jikar littafanta ma a bakin ƙofa ta sakesu ta kwanta kusa da ni tana ƙoƙarin cire hijabinta.

“Lafiya kike kuwa?”

Na tambaya ina kallonta, Noor kuma ya tashi da sauri ya fita waje. Ɗan guntun tsaki taja irin na wanda baya son magana kana ta ce

“Wallahi bana jindaɗi, amai na biyu makaranta kuma kaina ciwo yake sosai” 2

Dukan shida-shida gabana ya yi tsaɓanin uku-uku da na kowa keyi, a take nima na ji ciwon kan ya kamani, dafe kaina na yi na lumshe ido yana sauraren yadda zuciyata take bugawa. Ƙoƙarin kawarda abunda ke zuciyata nake, yes cikin zai iya nunawa a sati biyu amman ba ko wanne ba, cikin Noor ma a sati biyu aka gano ina da ciki balle kuma Habiba da ke da wata ɗaya har da sati ɗaya, tunda ranar litanin Inna zata cika wata ɗaya da sati biyu cikin taƙaba.

‘No ba ciki ba ne, maleriya ce inshallah ba ciki ba ne’ 2

Zancen da nake a zuci shi Habiba take a zahiri.

“Nawwara na ce ƙila maleriya ce, saboda idona har nauyi yake”

Na buɗe ido na kalleta tare da ɗaga mata kai alamar ‘Eh’

“Ita ce, bari na aika Sakina ta siyo miki Anti-Malaria shago”

“Tau”

Ta juyo min baya tana dafe da kai, hakan ya bawa hawayen da ke maƙƙale a idona saukowa zuwa kumatuna, ban taɓa tabbatar da hawaye na da zafi ba sai a wannan lokacin, gumi ne ya soma keto min ta ko ina kamar wacce ta yi rashin gaskiya. Cikin hanzari na kai hannu na share hawayena saboda motsin Sakina da na ji zata shigo ɗakin, sai na miƙe tsaye na nufi ƙofar fita. Ashe magana take min ban ji ba har sai da ta riƙoni.

STORY CONTINUES BELOW


“Anty Nawwara, wai ɗan sanda nan yana kiranki a waje”

Da kai na iya amsa mata, daman Hijabin da na shigo da shi yana jikina sai kawai na zarce ƙofar gida, har ga Allah ba dan ina cikin ruɗu ba babu abunda zai sa dpo nan ya kirani kuma har na tafi. Tsaye na yi masa idona a ƙasa ina ta tunanin makomarmu, idan har ta tabbata Habiba na da ciki mun shiga uku, lallai mutane zasu gasgata cewar Mahaifinmu ya yi sata, tun da ga ƴar'uwata da cikin shege, duk wani yabo da ganin mutuncinmu da ake a unguwarnan zai zube, ya Inna zata yi idan ta ji Habiba na da ciki? Ita kanta kanta Habiba ya zata kasance? Ni kaina da suka san na yi aure lokacin da na haifi Noor sai da suka kira shi shege balle kuma Habiba.

“Nawwara”

Kiran sunana da dpo ya yi na yasa na dawo hayyacina har na kalleshi, ashe tun da na zo gurin magana yake min amman ban fahimtaba saboda tashin hankalin da ke zuciyata.

“Ki yi haƙuri dan Allah, ki share hawayenki, duk abunda na faɗa miki zanyi ki yarda da ni”

Sai a lokacin na kula da hawayen da ke ta zuba a idona, cikin sauri na sa Hijabina na gogesu ina jan magina. Sai ya ɗora da zancen da ban gane masa ba, ba dan kuma yana min wani yaren ba sai dan hankalina baya gurin, babu komai a zuciyata sai fargaba tunani da kuma zullumin abunda zai je ya dawo, na tabbatar da za'a auna jinina a lokacin za a tarar ya haura ɗari uku da wani abu bama ɗari biyu ba. 
  A gurin na barshi tsaye na shige gida ba tare da hawayen sun tsaya min ba, haɗa ido da muka yi da Inna yasa idona ƙara cika da ƙwalla, tausayinsa ne ya kamani tabbas Mahaifiyata ba zata iya ɗaukar wannan ba, duka-duka yaushe ta rasa mahaifina kuma yanzu ta ji Habiba na da ciki.

“Lafiya?”

Tambayar da ta yi min ne yasa na share hawayena ina ƙoƙarin ƙirƙiro ƙaryar da zan mata.

“Ba komai kawai mun yi magana kan Baba ne”

“Nawwara ki yi haƙuri idan ma a duniya ba a yi komai ba, lahira za'ayi domin Allah baya zalumci kuma zai ƙwatar mana haƙƙinmu”

“Haka ne,  Inna kina da kuɗi a siyowa Habiba maganin Malaria?”

“Duba a cikin jakata ba za'a rasa ba, tace kanta ke ciwo”

Ban iya tsayawa amsa mata ba, na nufi ɗakin na ɗauko kuɗin na aiki Sakina ta je siyo mata, bata daɗe ba ta dawo da kuɗin wai sunje masallaci. 
  Kayan jikana na tuɓe na koma gaban murhu ina hura wuta domin ɗora girkin rana, har na yi girkin na gama kuka nake a boye saboda bana son Inna ta gano ina kuka hakan zai raunana mata zuciya kuma dole zata tambayeni dalilin kukan wanda ba zan iya faɗa mata ba. 
  Bayan na gama na shiga banɗaki na yi wanka tare da kuka a can, domin a nan babu wanda zai san da damuwata, bayan na fito na raba abincin na sake aikin Sakina ta je ta siyo mata maganin. Da kaina na ɓalla na bata ta sha na zuba mana abinci sai ita ta kasa ci saboda zazzaɓin ya rufeta sosai, jikinta ya yi zafi sosai. Ni kaina kasa cin abincin na yi, sai mutuwar Baba ta dawo min sabuwa, da ace ƴan sanda nan ba su masa duka ba, da be mutu ba da Habiba da ni da Inna duk ba mu shiga wannan halin ba. Bana son kowa yasan kukana hakan yasa na ɗauki buta na shiga banɗakina na ci kukana sao da na ƙoshi sannan wanke fuskata na fito, a lokacin ana kiran sallah la'asar.

Ba laifi Habiba ta samu sauƙi bayan shan maganin da ta yi, da muƙa gama sallah magariba ba har waje ta fito muna ɗan taɓa fira da ita, har ma ta ci ciwon masarar da na yi, hakan ba ƙaramin faranta min rai ya yi ba, gar na samu sakewa na labartawa Inna zancen Bilal, babu irin ruwan albakar da Inna bata sa mishi ba, Habiba ma sai yabonsa take. Inna ce ta cilasta ni kiransa a waya na sanar masa tana son ganinsa. 2

Bayan Sallah isha'i ya zo Inna tasa na shigo da shi har cikin gida ta yi masa godiya, bayan mun fito ni nake masa godiya duk da nasan cewar ba da sanin mahaifiyarsa ya yi mana wannan abun ba, da ba zata bari ba domin ta ƙi jinin ta ganmu tare ma balle kuma har kyauta ta shiga tsakaninmu, mun daɗe muna fira shi sannan muka yi sallama.

STORY CONTINUES BELOW


Bayan na dawo nake labartawa Inna yadda gurin aikin yake da kuma irin ƙa'idojinsa sai kuma zancen yadda kace min Shugaban ya ke, ta yi murna sosai ita da Habiba sun ƙarfafa min gwuiwa kuma suka min addu'ar samun nasara.
Washe gari naje na sanar da Jidda zancen samun aikina, ita ta yi murna sosai kusan sai na ce ta fini farinciki, haƙiƙa Jidda ta wuce ƙawa a gurina mun zama ƴan'uwan juna ni da ita, mun sha fira sosai yadda na ke labarta mata gurin aikinmu ita abun ma burgeta ya yi, wai ban sanar mata da wuri ba da ta kai takardunta na diploma sun ɗauke ta aiki a guri.

Sai yamma na baro gidansu bayan na haɗu ni da kwanon shinkafa da miya, abincin da na ke marmari.

***          ***            ***

MONDAY MORNING...

Hankalina ya kwanta sosai a kwanan biyu da Habiba ta yi bata sake ko da ciwon kai ba, hakan ya gamsar da ni lallai malaria ce take damunta. 
Dukan mu shiri muke bayan mun gama karyawa, ni ina shirin zuwa gurin aiki su kuma suna shirin zuwa makaranta, ban shafa hoda ba bayan na shafa mai, domin kawaliya bata dame ni ba, balle ni da zan fita tun 6:30am. Uniform ɗin na ɗauko na cire daga cikin leda, dogon wando ne ash color da farar riga, sai kuma wata ƴar ƙaramar riga marar hannu da za a ɗora saman wacan farar rigar ita ma ash, sai da na gama kallo ni da Habiba sannan na saka.
  Cas na fito kamar wata ma'aikaciyar banki musamman da na saka baƙaƙen takalmin nan masu kama da cover shoes.

“Wow Nawwara kin wanku”

Cewar Habiba tana kallona, ni kuma na yi dariya ina mai jindaɗi a raina. Ba Habiba kaɗai ba har Noor da Inna sai da suka yaba ni, ni kaona na san shigar ta yi min kamar wata ma'aikaciya, idan ba wanda ya sani ba babu wanda zai ce aikin Mopping zan yi. Wata ƴar ƙaramar baƙar hula na ɗauka na saka a kitson da ke kaina, sannan na ɗora ƙaton Hijabi yaɗi huɗu da rabi na saka, a gaggauci na fito daga gida gudun kar na yi lattti gashi yau ne farkon zuwana, duk yadda Habiba ta so na tsaya mu fito tare ƙiyawa na yi gudun kar na ɓata lokaci. Sai da na kawo bakin titi sannan na tuna da hoton da aka ce na kawo, da gudu na koma gida na ɗauko na sake fitowa ina ɗan jin kunya saboda mutane da ke kai da kawo a unguwat sun ɗan fara fitowa, duk da yake ba za'aga uniform a jikina ba amman sai na samu kaina da jin kunya saboda ban saba saka wando na fita da shi ba.

Ko da na isa kamfanin bakwai sauran minti biyar, yau kan sun tare a bakin ganin suna ɗan bincikata, sai na faɗa musu komai har ma na nuna musu uniform ɗin da ke jikina da kuma katin sheidata, sannan suka bar ni na wuce. Kamar yadda Bilal ya nuna min sai da na fara isa na saka sunana da lokacin da na shigo da kuma rana sannan suka nuna min gurin da zan aje Hijabi da wasu kaya idan na zo da su, na nufi gurin na na cire Hijabina na aje a lokar da suka ba makullinta, na samu kaina da jin kunya sosai ganin babu komai a jikina sai uniform ɗin da kuma ƴar ƙaramar hular da ke kaina, sai da na ɗan jima tsaye a gurin sannan na juyo na fara takowa, sai ɗaya ɗaga mutanen da ke reception ya ɗaga hannushi yana nuna min hular da ke kaina, a dole na juya na je na cire na aje, na juyo ina wani taku kamar wacce bata son saka ƙasa babu komai a tattare da ni sai kunya, shi kanshi ya lura da yanayina, hakan yasa ya sakar min murmushi, nima na sakar masa kaɗan idona a ware, ina kalle-kalle ala-ala na ke kar naga wanda na yasan ni har na nufi Lifted na danna ta buɗe na shiga sai na danna number 3 ta rufe ta soma tafiya da ni, zuciyata sai bugawa take da ƙarfi irin bugarwa nan na ɗoki da kuma tsoro a lokaci ɗaya. 
Muna isa number 3 ta buɗe na fito sai na samu masu irin uniform ɗina suna ta aikin gyara gurin, ganin duk mata ne yasa ni na ɗan saki jikina na nufi gurin da aka nuna min da zan ɗauki kayan aikina. A ciki na tarar da wata yarinya mai far'a da son mutane domin ita kaɗai ce ta amsa min sallamar da na yi har ta yi min kyautar murmushi.

“Da alama ke baƙuwace a nan”

“Haka ne, yau zan fara”

“Haba shiyasa”

STORY CONTINUES BELOW


“Mi kika gani hala?”

“Naga kin yi sallama ne, ai a nan ba a sallama ba a gaisuwa saboda mai Kamfanin baya buƙata, idan kika ga ana fira da juna tau angama aikine ko kuma an fita can waje” 2

“Tau shi kuma haka yake”

Ta yi dariya tana nuna min camera.

“Ki yi a hankali, Camera tana ɗaukar komai”

Security camera ce daga gabanmu tana ɗaukar komai, sai na yi saurin gumɗe bakina na ɗauki kayan aikina na yi gaba.
Na ji wuyar aikin sosai wata ƙila saboda ina farkom farawa ne, ko kuma saboda ɗakunan da aka haɗani da su suna da girma sosai, ga kuma gyara kofuna da jerawa bayan na gama ƙirgasu, sai da na gama sannan naje gurin da ake rubutawa na rubuta ko nawa na tarar sannan na nufi gurin aje kayan aikin na aje, na aje na kaiwa mutumen jiya wanda yace na kawo mashi ƙananan hotona, ɗaya ka karɓa ya saka a file sannan ya karɓi ɗayan na saka min a katin sheidata na rataya a wuya sannan ya ce min.

“Idan kina da account ki rubuta a nan, idan kuma baki da shi zan cika miki wata takarda sai ki riƙa karbar albashinki hannun kashiya”

“Gaskiya na daɗe ban yi amfani da shi ba, ina tunanin yanzu ma baya aiki”

Wata takardar ya ɗauko ya yi rubuce-rubuce sannan ya bani na saka hannu sai ya maida takardun ya aje, ya ce

“On 25 zaki riƙa zuwa gurin kashiya kina amsar kuɗin albashinki 12k”

“Tau na gode”

Na juyo duk da ban tambaye shi iya kashinyan yake ba, na fito daga gurin gaba ɗaya. A ƙaton agogon da ke reception na ga 12:14pm, lallai na daɗe ina aikin nan, sai da na saka hannu kuma na rubuta lokacin da na gama aikin sannan na nufi gurin da Hijabi yake na ɗauka, ina sakawa na ji mutun a bayana.

“Nawancy”

Da sauri na juyo na kalleshi.

“Ka ganni ne kamin na saka Hijab?”

Sai kawai ya ƙyalƙyale da dariya ya ɗora min ɗari biyar a lokar dana ɗauki Hijabina.

“Allah dai ya bar min ke, ga wannan ki hau Napep, a sauka lafiya”

Sai ya kama gabanshi ya yi tafiyarsa. Cike da kunya na fito na daga cikin kamfanin ita tunanin anya zan iya aikin nan zuwa?

“Sannu ƴar'uwar yau nima na ti latti gama aiki”

Na kalli mai min maganar da ke gefena na dama fuskarta ɗauke da murmushi, yarinyar ɗazun ce, sai dai wannan karon ita ma tana sanye da Hijabi, hakan yasa nima na yi mata murmushi.

“Da wuri kike gamawa kenan?”

“Eh gaskiya ten na ke gama aikina. Sunana Amina ke fa?”

“Nawwara”

“Suna mai daɗi”

Sai duk muka yi dariya, muna ta ɗan taɓa fira da ita kamin motar da ta wuce mu ta dawo dai-dai mu ta tsaya.

“Nawwara”

Jin muryar Zinatu yasa na yi saurin kallon motar, ita ce hakimce a motar idonta sanye da baƙin gilashi.

“Zinatu Ya kike?”

A maimakon ta amsa min sai kawai ta jefo min tambaya.

“Me kike a nan?”

“Aiki”

“Aiki aiki aiki wane irin aiki?”

“Mopping”

“Nice amman yau kika fara ko?”

“Eh”

“Good kowa zai ji muna aiki a guri ɗaya Sai dai ba level ɗaya ba, and people may not know the different, congratulations”

Ta tashi gilashin motarta ta kunna kai zuwa harabar da aje motoci. Maganar ta sosa min rai har Amina ta lura da hakan.

“Kin santa ne hala?”

“Eh tare muka yi primary school”

“Allah sarki”

Kamar ta ce wani abu sai kuma ta yi shiru, muka cigaba da tafiya. A gurin hawan Napep muka rabu ni na ɗauki hanyar gidanmu ita ma ta kama hanyar na su gidan.

Kamar kullum a inda aka sake sauke ni na sauka na ƙarɓi canjina na nufi gida, zuciyata cike da tunanin kalamin da Zinatu ta yi min, bana son fassarata da wata fuskar da kuwa da kasancewar na san halin na tsanar mutane irina da ta yi wato talakawa, haka kawai na samu kaina da faɗuwar gaba wata ƙila na tunanin da nake ne, sai da na shiga gidanmu na fahimcin faɗuwar gaban bana tunani ba ne na abunda zan tarar ne.Habiba ce kwance tsakar gida amai na gefenta da alama yanzu ta gama shi, domin Inna ta ɗauki makwashi da tsintsiya ta je ɗebo ƙasa. Da sauri na ƙarasa kusa da ita jikina a mace na dafata. 2

“Sannu Habiba mi ke damunki”

“Wallahi kaina ne ke ta ciwo ban ma iya dawowa daga makaranta ba sai da malaminmu ya kawo ni, sai faman aman na ke, kuma bakina babu daɗi”

Samun kaina na yi da kuka marar sauti, hawaye na bin fuskata kamar babu gobe. Na samu kaina cikin wani irin tashin hankali wanda ban taɓa samun kaina a ciki ba.

“Ai zata samu sauƙi ina jin malaria ce bata sake ta ba” 2

Inna ta faɗa ganin ina kuka, sai faman rufe aman take. 

“Allah yasa malaria ce, Allah yasa ta tabbata malaria ce ba ciki ba”

Maganar ta fito daga bakina kamar antseni. Hakan yasa Inna ta kalleni

“Nawwara, akwai abunda ya kamata na sani ne?”

Na yi saurin girgiza mata kaina hankalina a tashe.

“Babu babu komai”

Ta saki tsintsiyar hannunta, ta kalli Habiba da ta soma kuka daga inda take kwance.

“Akwai abunda kuke ɓoyewa ne?”

Na girgiza mata kai alamar a'a. Amman bata yarda ba. Ta soma ƙirga da hannunta.

“Tsaya dakata, Habiba tana da ciki kenan?”

Habiba ta yi saurin tashi zaune ta matsa gefena kamar zata shige jikina tana girgiwa Inna kai.

“A'a Inna”

Ta faɗa cikin kuka, kamar yadda nima na ke kuka. Sai ina ta kalleta idonta cike da hawaye ta nunata da yatsa.

“Kina da ciki Habiba, na lura da haka domin yanayinki ya canja gaba ɗaya, amman saboda karna munana zato a gareki yasa ban bari zuciyata ta ƙawata min wannan ba, ashe yaudara kuke ke da ƴar'uwarki, na shiga uku na lalace ina kika samo shi?” 2

Ta ɗora hannu saman kai ta nufi ɗaki tana kuka. Hakan yasa na cire Hijabin da ke jikina na aje a gurin tare da wayata na rufe mata baya. Safa da marwa na tarar tana yi a cikin ɗakin tana kuka, kamar jira take na shigo sai ta rufeni da maganganu marar daɗi.

“Kun cuce ni Nawwara, wannan ba tarbiyar gidan nan ba ce, ina kuka ɗaukota? Kun ƙara shafa mana baƙin fenti acewa mahaifinku ɓarawo ku kuma a kiraku ƴan iska, wayyo Allah na”

Ta faɗi tsakar ɗaki tana kusar kuka. Kusa da ita na ƙarasa na ɗafa ina kuka na ce

“Wallahi ba mu watsar ba Inna, ita ma yaudararta aka yi”

“Waya yaudareta? Faɗa min waya rusa mana ɗan farincikin da ya rage mana?”

A nan na feɗe mata daga biri har wutsiya akan abunda ya faru, sai dai ban labarta mata cewar Mustapha ne ya aikata mata haka ba, saboda bana tabbacin cikin nasa ne ko ba nasa ba ni dai abunda na sani ba shi kaɗai na ya yi lalata da ita ba, nasan kuma duk na faɗa mata cewar shi ne zata iya zuwa ta samu iyayensa wanda hakan na san ba zai mana daɗi ba, domin zasu iya ɗauka ko wane irin mataki a kan ɗan su ƙwalli ɗaya da suke ji da shi.

Can ƙasa-ƙasa na hango muryar Inna tana cewa.

“Habiba ta ci amanata kuma ta ci amanar kanta, ta zubarda ƙima da duk wani mutuncin da yake gidan nan, a yau na yi nadamar haihuwarta, baƙincikinta zai kasheni, ni ma nice na tafi ba mahaifinku ba, Allah be ƙaddara ya ga wannan abun kaico da wayyo a rayuwarsa ba sai ni, Habiba kin cuce mu...”

Duk wannan furucin da Inna take akan kunnuwan Habiba saboda tana jikin ƙofa tsaye ne, sai da Inna bata iya ganinta saboda ta bata baya ne. Muna haɗa ido da ita sai ta bar jikin ƙofar ta nufi ɗakinmu. Da sauri na tashi na bita saboda irin hawayen da na hango suna zuba a idonta.

Ko da na shiga na tarar tana ta saurin cire uniform ɗin jikinta ta saka wasu tufafin. Jin motsina yasa ta juyo da sauri ta kalleni.

“Nawwara guduwa zan yi, ba zan zama dalilin mutuwar Inna ba, ba zan rasa Baba kuma na rasa Inna ba-”

Ta juyo ta cigaba da haɗa kayanta. Ƙarasa na yi kusa da ita ya miƙar da ita tsaye na kama hannyenta da ke zafi sosai saboda zazzaɓi na riƙe gam, ina kuka kamar yadda itama take yi har ɗayanmu baya iya yiwa ɗan'uwansa magana.

Post a Comment for "RAI BIYU CHAPTER 5"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...