Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

RAI BIYU CHAPTER 19

RAI BIYU CHAPTER 19

- - Post a Comment
RAI BIYU
CHAPTER 19


Haka ya fito harabar asibitin hawaye na bin fuskarsa, babu komai a zuciyarsa na sai tausayin dan sa, kansa kuma empty har ya rasa da ina zai fara tunani akan Siraj. Be damu da tsakar dare ba ne ya shiga motar ya kamo hanyar sama road. A bakin gate dinsa ya tsaya cikin mota ya kira mai gadinsa a waya ya zo ya bude masa gate sannan ya shiga ciki ya faka motarsa ya fito jikinsa babu gwari ya shiga falonsa, saman sofa ya jefar da makulin motarsa ya shiga bedroom ya cire kayan jikinsa sannan ya daura tawul ya shiga bathroom.
Gaban madubin da ke bandakin yaje ya tsaya ya kallon still hawaye ba su daina masa zuba ba. +

"Why Siraj mi na maka?" 1

Ya tambaya kana ya fashe da kuka sosai ya fadi kasa zaune ya dafe kansa. Kuka ya yi sosai mai sauti kamar mace sannan ya tashi ya nufi shower ya sakarwa kansa ruwa, ya lumshe ido yana ra sauke ajiyar zuciya a hankali. Sai kusan hudu da rabi na asuba ya fito daga bathroom din shi ma dan wayarsa dake ta ringing ne. Gaban madubi ya karasa inda wayarsa take ya dauka ya duba, number Abbah ce yana ta kiransa cikin hanzari ya yi picking.

"Assalamu Alaikum Abbah"

"Jibril kana lafiya?"

"Lafiya kalau"

"Am sorry na kiraka da dare, na damu ne kawai and Jibril ka yi hakuri da yadda rayuwa ta zo maka dan Allah, dsp ya yi min bayanin komai nasan kana cikin tashin hankali dazu shiyasa ban kiraka ba, gobe muna nan zuwa tare da yan'uwan Rabi ka kwantarda hankalinka ka ji"

Sai kawai ya fashewa Abbah da kuka.

"Ba ni da wani sauran kwanciyar hankali Abbah, na rasa komai kuma saboda ni komai ya faru Abbah ni ne silar komai"

"Aa Jibril ba kaine ba, haka Allah ya tsara babu yadda za'a yi ka tsalleke karka sa komai a rana ka"

"Toh Abbah thank you"

Ya fada yana share hawayen idonsa, sannan ya aje wayar ya kalli kansa a madubi.

"Al-hamdulillah Allah na gode maka, komai ka yi daidai ne, Allah kai ka tsara min haka a rayuwata ban isa na tsalleke ba, Allah ka bani hakuri dauka abunda duk ka rubuto zai faru da ni, ka yafe min abunda na maka Allah, ka karbi rayuwata ina mai shauki da murnar haduwa da kai, Allah karka karbi raina ina mai bakinciki da damuwa kusantar ka" 3

Yana gama fadar hakan yaji wani irin rahama da natsuwa sun sauko masa a zuciya. Komawa ya yi bathroom din ya yi alwala ya fito ya saka jallabiyarsa ya yi nafila sannan ya tsaya jiran assalati ya dora da asuba, bayan ya gama ya zauna ya yi azkar na safiya tare da istigifari da salatin Annabi, sannan ya karanta abunda ya sauwaka a qur'ane sannan ya tashi ya nufi freezer ya dauki ruwa mai sanyi ya sha. Sannan ya dawo ya shiga bathroom ya yi wanka yana fitowa ya shirya cikin farar shadda ya dauki hanyar station.

Ya yi rashin sa a ko da ya isa ya tarar ya an wuce da shi gidan yari kai tsaye ba a station aka aje ba, a nan ya kira Dsp ya bashi hakuri akan ya yi hakuri har zuwa anjima idan Abbah ya zo. A dole ya hakuri ya koma cikin motarsa ya dauki hanyar asibitin Uduth.
Hasbiyallahu yake ta karantawa cikin mota saboda ya samu salama a zuciyarsa, a izuwa yanzu ya fawwalawa Allah komai. Yana faka motarsa ya fito ya nufi cikin asibitin, dakin da Noor yake ya nufa mai tsaron gurin ya bashi damar shiga ne saboda ya nuna masa shaidarsa ta likita mai zaman kansa.
Nawwara kawai ya samu a ciki tana zaune saman carpet tana tilawar a qur'ane da kai, ta yi matukar burgeshi hakan sai ya kara masa sonta da sha'awar zama da ita amman ya san babu wannan damar domin a yanzu ya riga ya tabbatar da cewar Nawwara ta masa nisa.

"Assalamu Alaikum"

Ya yi sallamar yana duka kofar sai ya tsaya a bakin kofar yana jiran izinin shiga. Juyowa ta yi ta kalleshi idanuwanta sun yi fari sosai fuskarta ta kode kamar ba ita ba, wani irin tausayinta ne ya kamashi har sai da ya yi daukerwa wutar seconds biyar sannan ya numfasa.

STORY CONTINUES BELOW

"Wa'alaikassalam shigo mana"

Sai ya maida kofar ya rufe sannan ya karaso ciki yana duba dansa.

"Ya jikinsa?"

"Likita ya ce da sauki ta duba shi, amman dai har yanzu be farka ba"

"Zai farka ki kwantar da hankalinki kinji?"

Ta gyada masa kai.

"Ya naki jikin"

"Na ji sauki"

"Ina Inna?"

"Taje gida"

"Ke kadai aka bari"

"Kasan asibitin ba a bari mutune su shiga sai 4pm"

Ya dan yi shiru yana kallon ta ita kuma tana kallon Noor.

"Abbah zai zo anjima tare da yan uwan Rabi"

Can kasa kasa ya sinkayo muryar Nawwara ta na cewa.

"Laifina ne, ni sakarya ce wani lokacin, na kan dora wani abu da ba muhallinsa a wani muhallin, da a ce ban yi wannan maganar ba da Rabi tana nan raye"

"No no no karki zargi kanki Nawwara, daman can haka Allah ya tsara, ba laifinki ba ne laifina ne, kuma shi Siraj din yana gidan yari yanzu haka yan sanda sun cika masa file sun turashi, kuma za a yanke masa hukuncin abunda ya aikata"

Kokarin kwantar mata da hankali yake, domin a yanzu tausayinta yake baya son abunda zai daga mata hankali ko kadan baya son damuwar Nawwara a yanzu, gani yake ta sha wahalar rayuwa a yanzu be kamata ace ta sake shiga wani halin ba.

Sun dauki lokaci a haka yana ta lallabata yana ta kokarin kwantar mata da hankali, daga baya ya dauki wayarsa ya kira Candy Restaurant ya yi order abinci da za a kawo su Nawwara. Sai sha daya da kwata ya bar asibitin a lokacin Inna ta dawo sai suka gaisa da ita sannan ya fito tare da Nawwara suka shiga mota saboda zuwa gurin Siraj, tun da suka shiga motar Nawwara bata kalli inda Jibril yake ba, shi kuma ya kasa dauke idonsa daga barin kallonta har suka isa.
Abbah kawai suka tarar sai step mother din Jibril da kuma babban yayansa da wani abokin Abbah, da dsp. Abbah ya damu sosai da ganin yadda Jibril ya koma ya rame sosai ya yi wani fari kamar marar jini.
Tare suka shiga da Nawwara da Jibril sannan dan gandireba ya fito musu da Siraj anyi handcuffed dinsa.

Da dingishi ya fito wani gurin a kansa har jini ya bushe masa, har ya zauna be daga kai ya kalli Jibril ba, Dukaninsu babu wanda ya zauna, Jibril ya matsowa kusa da shi sai Dsp din ya shiga tsakani.

"Ba sai ka taba shi, ai hukunci za a yanke masa dai dai da abunda ya aikata, abun jindadi ma ya amsa laifinsa da kansa, kuma mutane da muka kama a gidan da aka aje Noor sun fadi cewar shi ya saka su kuma be karyata ba"

"Ba komai zan masa ba tambayarsa kawai zan yi"

Jibril ya fada yana jin kamar ya kama wuyan Siraj ya shake.

"Mina hana maka Siraj? Mina maka ka aikata min haka? Me ka nema na hanaka? Mi Rabi ta maka? Me Noor ya maka?"

Ya dago kansa da idanuwansa da suka kumbure saboda duka, har baya iya gani da idon sosai gaba daya an canja masa kamani kamar ba shi ba.

"Baka min komai ba Jibril sai alheri, ni kaina ina jin rashin kyautawa a abunda na aikata, sai dai babu yadda zan yi saboda zuciya ta dibeni tun farko, abun da na ke ta kokarinyi da gani na fika Jibril, saboda ina bakincikin ace ni ne a karkashinka ba kai ne a karkashina ba, irin rufin asirin da Allah ya baka na so na samu da karfi sai ya gagara, na sa an kashe Rabi ne saboda ta tona min asiri ta ci amanata kuma na san nima kasheni za ayi, a a yayinda ita kuma za a yafe mata kuma za a yaba mata, Noor ya ganni lokacin da na yi kokarin kasheshi shiyasa na sace shi nasa a kashe shi saboda kar wata rana ya fadi sai gashi Rabi ta lalata komai" 1

STORY CONTINUES BELOW

"Hassadace ta cuce ka Siraj ka ci amanar kanka kuma daman hassada ga mai rabo taki ce, mun dauki amana mun baka sai ka cuce mu Allah ya waddaranka Siraj" 1

Cewar Abbah cike da bacin rai. Jibril ya matso kusa da shi ya chakumi wuyansa ya matse game yana kokarin aikashi lahira, daker aka kwaci Siraj a hannun Jibril har aka wuce da shi Nawwara kawai yake harara idonshi na kanta.

"Ka kwantar da hankalinka Jibril kotu za ta yi komai, litanin din nan muke son fara zaman kotu alkali zai yanke masa hukuncin ai"

Cewar Dsp yana rike da Jibril ta dake ta faman huci. Daga gidan maza station suka wuce saboda wasu statement din Nawwara da za a dauka. Sun yi awa daya a gurin sannan suka baro gurin tare da tawagar yan sanda zuwa rinjin sambo gidan wani dan'uwan Rabi da take zaune a gidansa. Ko da suka je sun tararda jama'a anyi dandazo a gurin duk kuwa da kasancewar an rufe gidan gaba daya kuma sun bar police uku da zasu yi gadin gurin.
Suna isa police din suka bude musu gidan, Nawwara ce a baya tare da Jibril, ya yinda Dsp yake can gaba tare da su Abbah da kuma wasu police din.

"Are you sure zaki iya kallon gawar Rabi? Ance fa dadsatsata suka yi"

Tsayawa ta yi cak sai ya kalleshi.

"Idan kin san zai daga miki karki kalla"

Sai kawai ta fashe da kuka.

"Duk laifina ne"

"Ba laifinki ba ne, haka Allah ya tsara"

Kamin ta kara cewa wani abu sai ga wayarta tana ringing, Baba Sulaiman ya kira ya ji inda suke ya zo, da kanta ta tsaya tana masa kwatanci sai Jibril ya shiga ciki ya bar nan waje tsaye.

Shi kansa da yaga gawar Rabi sai da hankalinsa ya tashi domin datsata aka yi aka mata guntu-guntu ko ina ya bace da jini, suna cikin gurin su Baba Sulaiman da wasu kanenn mahaifin Nawwara suka iso, isowarsu ta yi daidai da isowar yan uwan Rabi kana kallonsu zaka gane ba hausawa ba ne dukansu yanayin shigarsu da kuma tsagen da ke fuskarsu, da kuka suka shiga cikin gidan maza uku mata biyu a nan suka yi ta ihu har da mai faduwa tana tashi tana buga kasa. Daker suka tsagaita kuka har aka dauko gawarta aka fito da ita zuwa motar police. 1

NAWWARA POV.

Ana fitowa da gawarta hankalina ya tashi sosai lallai mai rai ba komai ba ne, duk kyau rabi da far'arta sun tafi kenan, a gurin na raina kaina saboda ina ganin kamar sakacina ne yasa hakan ta faru, amman Jibril ya yi kokarin dorawa kansa laifin ko kuma ya ce min haka Allah ya tsara zai faru, mahaifin Jibril ne yaso a tsaya a yi mata jina'iza a nan amman yan uwanta suka ki, a dole tasa ya hakura ya bawa police kudin mai dan su rakasu har can kogi inda iyayenta suke, a ranar yan uwanta suka juya suka koma a mota tare da gawarta da kuma rakiyar yan sanda.

Mahaifin Jibril kuma muka dawo asibiti tare da shi ya duba Noor ya yi masa addu'a tare da step mother dinsa, sannan ya yi mana bankwana akan cewar zai koma abuja a yau gobe tun da safe zai hau wani jirgin yaje kogi saboda ayi jana'iza a tare da shi, sosai ya so Jibril ya bishi amman Jibril ya ki wai sai yaga idon dansa, Abbah ya sashi gaba yana ta masa nasiha sosai akan rayuwa da kuma abubuwan da suka faru. 1

Da yamma lis Abbah ya yi mana sallama ya bar asibitin kasancewar an kira an fada masa jirginsa ya kusa tashi.
Mutane na ta zuwa ganin Noor makota da kuma yan'uwa da abokan arziki ciki har da wasu familyn Jibril da suke garin nan da kuma abokansa. Gurare takwas da rabi na dare Jibril ya bar asibitin saboda kiranshi da aka yi, ko minti goma ba ayi ba sai ga Jidda ta shigo tare da Mustapha i was very surprised dana gansu tare saboda ni na ma dauka Mustapha baya kasar nan dan tun lokacin da nayi magana da shi ban sake hada hanya da shi ba, hankalin Jidda ya tashi sosai har da kukanta Mustapha kan yana tsaye kan Noor yana masa kallon da ban san na minene ba.

"Ya aka yi aka barku kuka shigo?"

Na tambaya bayan Jidda ta zauna har yana kokarin bude abincin da ta zo da shi. Sai Mustapha ya kanne min ido daya yana murmushi

"Cin hanci na bayar"

Na sauke kaina kasa, sai ya yi yar dariya kadan ya ce.

"Allah ya kara sauki ya tsare gaba, kai gaskiya an yi arziki da mun rasa yaro mai kyau, ni da nake son na hada surukuta da ke, dan gaskiya idan na haifi ya mace sai ta auri Noor ko kuma da na ya auri yarki"

Ya fada yana dariya kamar babu abunda ya dame shi, ni dai bance masa komai ba, Jidda kuma ta kasa daga kai ta kalleni duk tabi ta tsargu.

"Ba ganin danki kawai na zo ba Nawwara, na zo na fada miki cewar na samu matar da na ke so"

Sai Jidda ta yi saurin kallonshi.

"Haba Mustapha wannan wane irin magana ne, baka ga halin da take ciki ba? Ko ma minene ai ni ya kamata na fada mata"

"Na ga kamar ba zaka iya fada mata ba ne, shiyasa ni na zabi fada mata da kaina"

"Amman dai ba a yanzu ya dace ka yi wannan maganar ba"

"Fine ba zan kara ba"

Ya fada yana daga hannunsa sama tare da yin murmushi. Ina tunanin Mustapha ya yi min haka ne saboda bakinciki ya yi min yawa a tunaninsa zan ji zafi idan ya ce ya samu wacce yake so duk da nasan ba zata wuce Jidda ba domin alamu sun nuna hakan, ko rantsuwa na yi bana kaffara Mustapha ya so Jidda ne kuma zai aureta ne saboda na ji bakinciki tun da aminiyata ce, kuma yana son bakinciki da nake ciki na rashin lafiyar Noor ya karu akan kishi ne saboda na ki shi, ni kuma na kasa damuwa saboda daman can bana son shi kuma ina ganin sonshi a idanuwan Jidda dan haka sun fi dacewa da juna duk kuwa da kasancesar ta kasa fada min ne saboda karna zargeta ko kuma na yi tunanin wani abu.

Basu wani dade sosai ba Mustapha yasa hannunsa aljihu ya dauko kudi mai dan dama ya aje mana saman gado tare da yi mana addu'ar Allah kara lafiya, sannan ya yi gaba sai na kamo hannun Jidda ya riketa har sai da ya wuce sannan na kalleta na ce

"Amintakarmu ta fi karfi mu boyewa juna abu"

"Nawwara ban yi nufin boye miki ba, kawai ban san yadda zaki kalli abun ba ne"

"Ta fuska mai kyau zan kalleshi Jidda, na san ke aminiyata ce kuma ba zaki taba cin amanata ba, Wallahi ko da Mustapha be furta da kansa yana sonki ba zan hada soyayyarku saboda dacewar da kuka yi da juna, kuma ina ta tabbacin idan har ya aureki ba zai sake wata rayuwa marar kyau ba"

"Ba a yanxurya kamata mu yi maganar nan ba Nawwara, ki kula da Noor please"

Ta fada tana dafa kafadata sannan ta wuce. Ni kuma na dawo na zauna na saka Noor a gaba ina ta kallonsa zuciyata cike da tausayinsa. Misalin goma na dare Jibril ya dawo, yana shigowa dakin Noor na farkawa da kuka yana kiran sunana.

"Momy Momy"

"Gani nan"

Na yi saurin kama hannunsa.

"Momy sun yanka ni wasu sun ce zasu kashe ni"

Sai Jibril ya yi saurin karasowa ya kama dayan hannunsa kuma ya shafa kansa.

"Shiiiiiiiiiii you're safe kana kusa da Momy da Daddy babu wanda zai taba ka"

"Daddy sun ce sai sun yanka ni sun yanka min ciki ma, kuma sun buga min kai"

Sai kawai yasa dariya.

"Ashe Noor dina ba jarumi ba ne, kadan fa suka yanka ka, kuma na sa police sun kama su"

Matsawa ya yi sosai ya kwanta gefen Noor ya rumgumeshi ya matse hannunsa cikin nasa.

"Allah ya baka lafiya ya raya min kai Noor kai kadai ka rage min sai Abbah na" 4

Tashi na yi na fita wajen kiran likita saboda ya ce idan Noor ya farka a kirashi.A GURGUJE....

Bana tunanin Bilal yana da wata hujja ko dalili na yin fushi da ni, duk kuwa da kasancesar Jibril ya sa an daureshi kuma an masa kai wulakanci da kasa guguwa a fuskar yan uwansu, amman idan har zai min adalci babu hannu a ciki balle kafata, sai dai shi ya kasa fahimtar hakan domin tun lokacin da abun ya faru zuwa yau be taba daga waya ya kirani ba, idan kuma na kirashi sai ya dinga min magana cikiciki kamar baya son magana da ni, sau uku Baba Sulaiman yana daukar mutane suna dubashi bayan sallamoshi daga asibiti, ni kan ban jeba domin Inna taje ba bata dawo da farin rai ba duk da bata fada min abunda suka mata ko suka ce mata ba, na fahimcin hakan ne a fuskarta da kuma yanayinta. +

Al-hamdulillah sauki yana ta zuwa ma Noor ta ko ina domin a farko ya firgita sosai har na dauka ko kwakwalwarsa ta tabu ne, sai dai kulawar da likitocin Uduth da kuma addu'o'in da muke sai komai ya daidaita, tiyatar da aka masa ma cikin sati biyu ya samu sauki su kansu sun yaba da irin kyau fatar Noor, yana samun kula sosai da sosai wani abun da Jibril yake masa har mamaki yake bani kamar zai dauke sa ya cinye, a dan zaman da muka yi na asibitin Noor har ya sagarce abu kadan zai fara kuka yana kiran Daddynsa. A zaman da mukayi asibiti sau biyu Jibril na aman jini a gabana abun har sai da ya bani tsoro domin na dauka zuciyarsa ko kuma hanjin cikinsa zai amayar gaba daya, sai dai shi sai ya nuna kamar be damu ba, da alama abun ya zame masa jiki.

Ana gobe za a sallamemu daga asibiti muka yi zaman kotu na karshe akan case din Baba a ranar na sha mamaki ashe matar da ta lakawa babanmu sata yayar Siraj ce daamn ina ganin alamaun haka sai dai ban tabbatar da sai yau da aka yanke hukunci na karshe, saboda yan uwan Siraj da suka zo sune wadanda aka tsaya masa a lokacin da aka yi shigar kotu ta farko case dinsa. Hukunci kazafi alkalin ya yanke mata su kuma aka yanke musu hukuncin kisa bisa ga shaidu da hujjoji kwarara da aka gabatar gaban kotu. Na yi farincikin sosai da sosai a wannan ranar daga ni har Inna da duk wani mai son ganin na kwatowa Baba hakkinsa, na yaba ma dpo daya tsaya kai da fata wajen ganin ya bi mana kadin mu. Abunda ya faru abun mamaki ne kuma abun a yabawa masa ne domin ba ko wane dan sanda bane zai kashe mutum kuma an hukunta shi kamar yadda doka ta ce, a ranar na ji kamar na zuba ruwa kasa na sha saboda farinciki mutane na ta zuwa har gida suna mana murna.

Washe garin ranar aka sallamo Noor daga asibiti, a abun mamaki sai ga Zinatu ta zo ganinsa wani sukuku da ita kamar ba ita ba, na yi mamakin ganin ta zo gida dubashi bayan bata taba zuwa asibiti ganinsa ba. Da fari jajanta mana ta farayi akan abunda ya faru sannan ta dora da bayaninta.

“Na san zaki yi mamakin rashin zuwa ganin Noor asibiti ko? Wallahi Jibril ne ya hanani, saboda na kirashi ina jajanta masa abunda ya faru sai ya gargade akan karna yarda na kusanci dansa, saboda yana ganin akwai aminci da shakuwa sosai a tsakanina da Siraj wata kila yana zargin zan masa wani abun ne”

“Ayyah kin san dole ne ya tsorata kuma ya yi taka tsantsan saboda abubuwan da suka faru”

“Amman ai ba halina daya da Siraj ba, miyasa zai yi tunanin haka”

“Ban da abinki Zinatu ai shi hali ba a fuska akae ganeshi ba, shi ma Siraj din ai bamu dauka cewar zai yi haka ba, ni kaina a yanxu ba kowa zan yarda da shi ba balle kuma shi”

“Haka ne, ni kaina da be koremu daga kamfanin ba, na kudiri aniyar aje aikin domin ba zan iya aiki inda ake ɗari ɗari da ni ba”

“Ya sa kun aje aikin ne?”

“Eh kwana biyu da faruwar hakan duka ya canja ma'aikatan kamfanin, yanxu kuma yana nan yana daukar wasu”

“Ayya abun be yi dadi ba sorry”

“Ba komai Allah kara lafiya, amman gaskiya Siraj ya bata mana suna Allah ya isar mana”

“Amin Amin shiyasa ake son ka yi taka tsantsan da mutanen duniya ai”

STORY CONTINUES BELOW

Tayi min wani kallo sai kuma ta mike tsaye tare da daukar jakarta ta yi min sallama ta fice. Inna ta zo ta zauna kusa da ni tana fadin

“Ki yi hankali da wannan ma domin kin san ba yarinyar arziki ba ce”

“Na sani Inna amman Allah ya fita kuma shi zai tsare mu”

“Haka ne”

Firar Siraj muka bijiro da ita, a nan nake labarta Inna wasu abubuwa da bata sani a lokacin da ina aiki tare da shi, mun dade muna fira mutane kuma nata shigowa suna mana barka da dawowa ga Noor a tsakar gida yana da game da dayar wayar Jibril daya bar masa ya buga game kamin ya karba.

Bayan sallah magariba Bilal ya kira ni i was very surprised da na ga kiransa domin rabon daya kirani har na manta, gabana ne ya shiga faduwa sosai sai kuma tsoro ya kamani kamar ba zan daga ba sai kuma na daure na dauka, na yi tunanin wata maganar zai fada min sai ya ce min gashi nan kofar gida na fito.

Sai da na canja Hijab din da ke jikina sannan na sanar da Inna itama kanta ta yi mamaki, ni dai jikina a sanyaye na fito. Sai na same shi a daidai inda ya saba tsayuwa yana jingine da ginin gidanmu sanye da kananan kaya.

“Assalamu Alaikum ”

Sai ya dago ya kalleni, sai kuma ya yi murmushi.

“Kin tsorata ko sarkin tsoro?”

Na yi shiru ban ce masa komai ba, sai ya sauke ajiyar zuciya ya ce

“Ki yi hakuri da duka abubuwan da suka faru, na so naje ganin Noor asibiti sai dai ban samu dama ba, saboda Mama ta furta cewar bata yafe min ba idan na taka asibiti ganin Noor ke ko waya na kira na tambaya jikinsa bata yafe min ba, wannan dalilin ne ya hanani zuwa ganinsa”

“Ba komai, Mama tana hujja ai nima kuma ban kyauta ba”

“Babu abunda kika na rashin kyautawa, face fifita son Jibril akan nawa da kika yi”

“Haba Bilal karka dauki zigar mutane mana duk wanda ya fada maka haka ya yi maka karya”

“Ba fada min aka yi ba, gani na yi da idona”

“Babu abunda ka gani Bilal kawai kana son ka yi amfani da wata damar ne ka ci min fuska”

Sai ya gyara tsayuwarsa ya kalleni

“Ki rantse min da Allah a yanzu nan babu son Jibril a zuciyarki!”

Sakin baki na yi ina kallonsa sai idanuwa suka cika da hawaye, na kasa karyata kaina balle kuma na karyata shi, Allah yake son na rantse da shi taya zan yi rantsuwa akan abunda ba ni da tabbaci ni kaina a yanzu ba zan iya cewa akwai son Jibril a zuciya ko babu abu.

“Kin gani? Kina son shi har gobe Nawwara, dan haka karki yaudari kanki, wannan dalili yasa na ke jin kamar ba zan iya aurenki ba saboda zuciyarki tana gurin Jibril ko da na aureki gangar jikinki kawai na aura”

“Wannan ne kawai dalilin?”

Na tambaya hawaye na bin fuskata.

“Ba wannan ne kawai ba, mahaifiya bata son ki Nawwara kowa ma a gidanmu baya son ki sai ni, wani lokacin abunda iyaye basa so babu alheri a cikinsa, and ko na aureki ba zamu taba jindadin zaman aure ba abubuwa za su yi ta faruwa wadanda ba zasu mana dadi ba.

Ban yarda Jibril ya fini son ki ba, amman na yarda son ki yafi yima Jibril illa sama da ni, Nawwara Jibril yana da ciwon zuciya wanda zata iya bugawa a kowa lokaci ta rasa ransa kuma ke kadaice maganin wannan ciwon nasa, na san zakiyi mamakin inda na ji ko? Na samu labarin ne ta hanyar abokan aikinmu da muka yi aiki a kamfaninsa tare, idan na aureki a yanzu na shiga tsakaninki da muradin zuciyarki kuma na shiga tsakanin Noor da Jibril na raba masa hankali gida biyu,

STORY CONTINUES BELOW

Last two weeks da suka wuce Jibril ya kirani muka hadu a Shukura Hotel da shi, kin san abunda ya yi min? Gafarata ya nema akan abubuwan da suka faru kuma ya rokeni da na rike masa dansa amana kuma na tarbiyantar da shi, da za ayi gasar son ki Nawwara da ni zan zama gwani kuma zakara, amman a wannan lokacin sai da na raina kaina saboda tausayin Jibril da ya kamani, saboda ya canja Nawwara saboda ke mutumen da baya kallon kowa da kima amman har ya nemi ya yafe masa kuma na masa alkawarin ba zan bari komai ya samu dansa ba, har ma ya yi ikirarin mayarda ni aikina, but yanzu idan baki aureshi ba kin san irin halin da zai shiga? Wata kila rayuwarsa marar kyau zai koma yi, kuma Noor ma ba zai ji dadi ba domin a yanzu ya saba da mahaifinsa, ya kamata ace shi ma yasan dadin mahaifa kamar ko wane da,

Dukan abunda Jibril ya yi miki abaya ya yi ne a cikin jahilci yanxu kuma ya dawo yana neman yafiyarki ya kamata ki yafe masa he deserved a second chance so that ya gyara duka laifin da kuskuren da ya yi, kuma shi ya fi cancanta da ya zauna da ke a yanzu saboda ya goge miki zargin da duniya take miki, kuma zaki samu ingattaciyar rayuwa ke da iyayenki wacce ni ba zan iya baki ita a yanzu ba, ko da zan iya baki sai nan gaba amman shi yana da abun duniya wanda ya kamata ace kema kin jidadi kuma kin more hakurin da kika yi,

Abu na karshe da zan fada miki shine, dukan mu ran mu a hannu Allah yake, amman masu ciwo irin na Jibril basa dadewa a duniya, kuma Jibril be da wanda zai iya tsawata masa a yanzu sai mahaifin da bashi da lokacinsa, ga jarabasar cin amanar da Siraj yayi masa wannan kadai ya isa yasa ki tausaya masa, ina son ki Nawwara amman son da nake miki na ki samu farinciki ne bana na aureki ba yan uwana da iyayena su saki a gaba, kuma ina son ki auri Jibril ko dan saboda Siraj da Zinatu, domin idan baki aureshi ba mamaki ya auri Zinatu wanda baki san iya abunda hakan zai haifar ba”

Hawaye nake babu kakkautawa kamar yadda shi ma yake.

“Kar tausayin wani yasa ka cutar da kanka kuma ka cutar da ni Wallahi ina son ka Bilal ina sonka sosai” 1

“Na san kina so na, amman ko mun yi aure zamu yi ta samun matsala ne kawai Nawwara, kuma ina da kishi sosai ba lallai ne muji dadin zaman aure ba, na san yanzu ba zaki fahimta ba, amman a nan gaba kadan zaki gane gata ne na yi miki kuma na yi ma kaina, ni dai zan bi zabin iyayena wanda ina tunanin Allah zai bani wacce zan so siye da ke saboda na yi ma iyayena biyayya, kuma in da rabon na aureki sai kiga na aure ki din gaba”

Durkusa na yi a gurin na hade hannayena ina rokonsa

“Ka yi ma Allah da annabi ka aureni Bilal zan iya jure duk wani cin fuska da wulakanci da zaka min ko na yan'uwanka Wallahi ina son ka, Bilal sauran fa sati biyu da kwana uku ayi auren nan dan Allah karka janye, kuma ko da ka fasa aurena ba zan taba auren Jibril ba, igiyar aure ba zata sake shiga tsakani na da Jibril ba” 2

“Idan har baki auri Jibril ba Nawwara to son da kike min na karya ne...!”

Ya fada a tsawace sannan ya share hawayensa ya yi tafiyarsa abunsa ya bar nan ina aikin kuka. Da kuka na shigo gida ina labartawa Inna abunda Bilal ya yi min sai tasa salati tana mamaki karfi hali irin nasa. Misalin tara da rabi Jibril ya kirani a waya wai gashi nan kofar gida ya siyowa Noor abu, a lokacin idanuwa sun kumbura kaina kuma yana mugun ciwo saboda kukan da nayi, nasan ba dan ni ya zo ba, amman ina da bukatar magana da shi saboda abunda ya faru tsakanina da Bilal hakan yasa na fito a lokacin yana tsaye shi da Noor yana bare masa ayaba.

“Noor shiga gida”

Na fada cikin muryata dake nuna na yi kuka har na gaji, ba musu Noor ya taka a hankali ya shigo cikin gida, ni kuma na kalli Jibril na ce

“Rokon Bilal ka yi ka ce karya aureni ko?” 2

“Miya kawo wannan maganar kuma?”

“Ban sani ba, duk abunda ka yi be isheka ba sai ka saka Bilal a gaba ka rokeshi” 4

“Wallahi ban rokeshi ba Nawwara, ni dai na masa magana ne akan ya rike min Noor da amana a matsayinsa na wanda zai aureki kuma na nemi yafiyarsa akan abunda ya faru daga karshe kuma na ce zan maidashi aikinsa ya ce min baya so yayi applying wani gurin sai dai idan wani abun ya fada miki daban wanda ba wannan ba”

Na dafe kaina ina kuka.

“Ki yi Hakuri Nawwara ban san haka zai bata miki rai ba da ban yi ba, nasan komai nayi a gurinki bana gwaninta” 2

Ya fada da muryarsa mai nuna tsantsan nadamarsa. Kasa ce masa komai na yi sai ya juyo na dawo cikin gida cike da zazzafan zazzabi. 1

MUSTAPHA POV.

Har yau har gobe son Nawwara na nan cikin zuciyarsa, sai dai ba kamar da ba, yana son ya auri Jidda ne kawai saboda Iayayen sun ki yarda da Nawwara kuma yana jin Jidda zata maye masa gurbin Nawwara ko ba komai hakan zai kara wanke shi a idon Nawwara ta yarda zata yarda ya canja har abada, kuma yasan hakan zai kara kusancinsa gareta, a tunaninsa idan ya auri Jidda hakan zai yi ma Nawwara zafi kasancewar aminiyarta ce, kuma yana yawan ayyanawa a ransa cewar ko Nawwara tana kasa giɗa sai ya aureta amana dai ko da ta tsufa ne dan shi har gobe be cire rai daga aurenta ba. 1

Momynsa ta yaba da Jidda ganin ita budurwa ce kuma ba a mata irin shaidar da ake yi ma Nawwara cewar ta haifi shege, mahaifinsa ma ya yaba da ita duk kuwa da kasancesar ba ita ya so ya aura ba, amman ganin ita ce zabinsa a dole ya amince da ita.
Ba zai ce baya son Jidda ba iya abunda ya sani yafi son Nawwara da Jidda sau dubu ma ba dari ba, irin soyayyar da Jidda ke nuna masa ne ma yasa yanzu ya maida hankali sosai a gurinta har manyan suka shigo cikin, duk da kasancewar ba a saka ranar auren ba iyayensa sunje sunga iyayen Jidda kuma an tsaida magana akan cewar satin sama za a yi musu engaged.
Duk irin shakuwa da so da kauna da ya shiga tsakaminsu har yau Jidda bata taba labarta Nawwara komai ba, ba dan kuma tana son boye mata din ba, sai dan tana nuna kamar ba zata kalli abun ta fuskar daya dace ba, tana ganin kamar Nawwara zata zargeta cin amanarta duk kuwa da kasancesar ta san cewar Nawwara bata son Mustapha amman bata san ta wace fuskar zata kalli alakarsu ba.Cike da bacin rai ya isa gida, abunda ya kasa ganewa miyasa Nawwara ta kasa sakewa da shi ne miyasa abu kadan zata rika ganin laifinsa, sai yaushe zata fahimci irin son da yake mata? Yaushe zata gane duk wani kalami marar dadi daga gareta yana taba masa zuciya, har sai yaushe Nawwara zata fara sanin ciwonsa? +

“O.... Ya Allah”

Ya jefar da keys dinsa ya fadi zaune saman kujera yana sauke ajiyar zuciya. Can Bilal ya fado masa a rai sai ya maida laifin a kansa daman baya son ganin laifin Nawwara, yana da bukatar jin ta bakinsa da haka dole ne ya kirashi, wayarsa dake aljihu ya ciro ya nemo number Bilal ya aika masa da kira, ta dade tana ringing kamin ya dauka.

“Hello”

“Bilal a Maganganun da muka yi a akwai wata magana dana fada maka wacce bata kamata ba ne?”

“Babu”

“Dan me zaka je ka samu Nawwara ka fada mata mun yi magana? Ba dan kowa ya sani yasa na kiraka ba sai dan ganin da na yi hakan ya dace”

“Nima dacewar na gani shiyasa na aikata abunda na aikata, na fada na fasa aurenta ne kuma gobe zan tura a karbo min kayan aurena da na kai gidansu shine kawai abunda ya tada mata hankali take ganin laifin”

Jibril yay saurin mikewa tsaye, maganar ta zo masa a baibai ya fasa aurenta as how shi ba ko dazun da Nawwara take ta kuka tana masa bala'i be tsaya ya tantance takamaimain dalilin da yasa ta haka ba, kawai abunda ya fi ji maganar sa da Bilal da yayi kuma ta ji.

“Ban fahimce ka ba?”

“Na fasa aurenta na ce, hakan yasa tayi tunanin ko kaine ka yi min wani abu sai na fada mata haduwarmu”

“Am amman miyasa ka fassa aurenta?”

“Saboda mahaifiyata bata son auren”

Yana fadar hakan ya kashe wayar be jira ya kara jin abunda Jibril zai ce ba. Farinciki ne da bakinciki suka zo masa a lokaci daya. Ya fasa aurenta yasa shi farinciki but what if shine dalilin fasa auren? Hakan zai sa Nawwara ta kara tsanarshi, bayan haka yasan Bilal yana son Nawwara idan shine yake kokarin aurenta kuma sai wani ya kwace masa ita ya zai ji?

“Amman kuma ai mahaifiyarsa yace da Bilal yana da niyar fasa auren Nawwara saboda da da tuni yayi, ina tunanin abunda ya faru ne yasa mahaifiyarsa ta hana ya aureta”

Ya furta a fili sai ya fadi zaune saman sofa ya lumshe ido.

“Wow da ace zan ganki matar nan da na miki kyauta mai tsoka”

Can kuma ya bude ido.

“I hope you're not fooling me, no he's not ai da Nawwara ba zata yi kuka ba har tana zargina”

Shi kadai yake ta maganarsa ransa fari fal ba zaka ce shine ya dawo gidan da bacin rai ba. Mikewa ya yi tsaye yana ji a ransa cewar addu'arsu ce Allah ya amsa kuma gana ganin he deserved happiness again tun da rayuwarsa ba mai tsawo ba ce. Wayarsa ce dake kan sofa ta yi ringing sai ya juyo da sauri.

“Nawwara”

Ya furta gabansa har bugawa yake da karfi, yana daukar wayar ya ga number Abbah lumshe ido ya yi.

“Oucccc am such a fool taya Nawwara zata kirani yanzu ba bayan fushi take da ni”

Bude idonsa ya yi ya danna picking ya kara a kunne.

“Hello Abbah”

“Jibril kana lafiya?”

“Lafiya kalau Abbah ya Abuja”

“Al-hamdulillah ya Noor yaushe zaka shigo”

“Da dai cikin satin nan ne amman yanzu ban sani ba gaskiya”

STORY CONTINUES BELOW

“Ya dai kamata kasa lokaci ka zo”

“Wani abun ne?”

“Akwai maganar da ya kamata mu yi”

“Ba zamu iya yi ta waya ba?”

“Magana ce mai muhimmanci zai fi kyau idan kana nan zaka fi fahimtar abun”

“Idan magana mai muhimmanci ce ka fada min a waya dan bana tunanin zuwa yanzu”

“Magana ce akan aurenka Jibril be kamata kana zaune haka nan ba, yarinyar nan da keke so aure zata yi, zama haka ba ba zai maka ba, na sha baka dama ka fitar da wacce kake so sai ka ce sai Nawwara kuma yanzu gashi yarinyar nan aure zata yi, dole ne idan ta yi aure zaka karbo dan ka dan ba zamu barshi can ba, babu yadda zaka yi ta gujeka kuma ta zauna da danka, na san ka yi kuskure kuma ka zalinceta amman ai an bata hakuri so dole ne ka nemi matar aure wacce zata rike maka yaronka”

“Haka ne Abbah amman har yanzu ba a daura mata aure ba ba lallai ne ta auri yaron da yake son ta ba”

“Wai kai ba zaka cire ranka a gareta? Yanzu dai mun yi magana da Hajiya (Step Mother din shi) akwai wata yarsa margayi Alhaji Dahiru wato Salima wacce ta fito sai kaje ka gani idan kana sonta ba zamu cilasta maka ba, amman fa bazawara ce yaranta hudu sai dai duka yaran suna hannun Babansu”

“No Abbah wanda zai auri Nawwara ya fasa aurenta saboda mahaifiyarsa ta hana just saboda abubuwan da suka faru tsakanin mu, shine sai Nawwara ta bada damar na tura nawa magabatan” 1

Abbah ya dan yi shiru kamin ya ce

“Jibril ka tabbata?”

“Yes Abba, jiya take fada min haka kuma kasan yadda na ke son ta Abbah, ni yanzu abunda na ke so da kai kasa rana cikin satin nan ka zo ku ga iyayenta”

“Jibril ka tabbata”

“Yes Abbah”

“Shikenan zan samu iyayenka na nan mu yi magana”

“Thank You”

Daga haka Abbah ya kashe wayar, sai Jibril ya yi murmushi.

“Idan ma karya ne Bilal yake ai idan Abbah ya zo dole familynta zasu fada masa gaskiya”

Ya fada kana na nufi kitchen dan hada kansa tea.

NAWWARA POV.

Na ci kuka sosai a daren nan, na kasa yarda da abunda Bilal ya fada min na san yana so na dan me mahaifiyarsa zata shiga tsakaninmu? Miyasa idanuwan wasu suke rufewa su kasa fahimtar komai sai kansu. Washe gari da asuba bayan na gama sallah na dauki qur'ane na karanta Yasin wato zuciyar qur'ane, Suratul Yasin tana da fa'idodi da yawa ga musamman ga mutumen da yake cikin matsala da damuwa ta matsalar mijin matukar ka karanta sau goma sha biyar zama daya idan ya gama ya roke Allah bukatarsa idan da hali sai mutum ya yi sadaka, ba ni da halin karanta Yasin sha biyar hakan yasa na karanta ta sau daya na karanta Ayatul Kursiyo dari domin ita ma tana da nata fa'idan sosai kuma idan Allah ya amsa maka kamar yankan wuka yake, bayan na gama na roki Allah ya zaba min abunda duk yafi zama alheri a rayuwata, sannan na aika Jamila ta siyo min kosai na yi sadaka, a lokacin Sakina har ta shirya mana abun kari sun yi breakfast ni ce kawai ban ci komai ba tun tashina.

Dakin Inna na shiga na gaishe ta a lokacin Sakina ta gama shiryawa ita da Jamila suka kama hanyar makaranta, bayan sun fice Inna ta kalleni ta ce.

“Nawwara ki yi hakuri da yadda rayuwa ta zo miki, kuma ki yarda duk abunda Allah ya zaba miki shi yafi zama alheri a gareki, ni dai ina nan ina ta yi miki addu'a, dan haka ki daina sa kanki a damuwa, tashi kije ki zuba abinci ki ci”

STORY CONTINUES BELOW

Na tada kai na kalleta idanuwa cike da hawaye.

“Amman Inna kina ganin wannan dalilin kawai ya isa yasa Mahaifiyarsa ta hana shi aurena?”

“Ya isa mana, idan kika duba daman can ai ba sonki take ba, kuma tana ganin an wulakanta mata da, ni kaina babu irin maganar da bata fada a gabana ba lokacin da na ke zuwa duba shi, amman idan har Allah ya rubuto ke matarsa ce Wallahi bata isa ta hana ba, ki sawa kanki wannan”

Na gyada mata kai na share hawayena sannan na mike tsaye ina amsa sallamar da naji wani namiji na yi a waje, bakin kofar na nufa babu mayafi a jikina hakan yasa na leka da kai na yayinda jikina yake cikin gidan, wani saurayi saman babur hannunsa rike da ledoji sai ya miko min.

“Ga sako daga Candy Restaurant Jibril ya ce a kawo ma Noor”

Kamar ba zan karba ba, sai kuma na mika hannu na karba ba tare da na ce masa komai ba, dakin Inna na dawo na aje ledodin tare da fadin.

“Wai Jibril ya aiko a kawo ma Noor, ni ban gane masa ba ya raina abincin gidan nan ko mai?”

“Ba raini ba ne, yana ganin dacewar hakan ne kawai”

“Ina Noor din?”

“Yana bandaki tun dazu ya shiga”

Cewar Inna sai gashi ya shigo dakin yana tafiya a hankali.

“Momy gurin kaikayi yake min”

“Karka sosa dai ciwon zai iya tashi”

Na fada masa, sannan na juya na koma dakinmu jin wayata na ringing. Jibril ne yake kirana katse kiran sai ya sake bugowa cikin fushi na dauka

“Wai ba zaka daina kirana ba ne?”

“Amman kin san ba ke na kira ba Noor na kira dan me zaki dauka? Na ce ina son magana da ke ne? Da na na kira kuma kin sani na ce zan siya masa waya saboda na rika kira ta nan kin hana ya kike so na yi”

“Akan me zaka aiko masa da abinci bayan kuma kasan muna da shi”

“Ta nan kika bullo kuma? Na aiko masa ne saboda na san ya saba da abincin ba zai iya cin wani abinci bayan wannan ba a yanzu, kuma ina da hakki na ciyar da dana bana son wata dogowar magana da ke dan Allah ki bashi waya na tambayi lafiyarsa ko kuma na zo gida yanzu na duba shi”

Kashe wayar na yi na koma dakin Inna sai gashi ya kira na mikawa Noor suka gaisa, sun dade suna waya daga karshe Noor ya fita daga dakin ya koma can gurin bandaki yana magana kadan-kadan da alama wani abun yake fada masa, sannan ya dawo ya kawo min wayar.

“Momy wai ya ce yana gaida Inna da kowa da kowa amman ba da ke ba”

Ya fada yana dariya, tabe baki na yi na tashi naje ya dauko kofi na zuba koko nasa suga na dawo dakin na zauna ina sha, domin shi kadai na ke jin zan iya sha kasancewar bana cikin dadin rai. Guraren goma da kwata ina yi ma Noor wanka tsakar gida sai ga Baba Sulaiman ya shigo bakinsa kumshe da sallama. Ina kallonsa nasan ba lafiya ba

“Baba ina kwana?”

“Lafiya kalau ina mahaifiyarki?”

“Tana daki. Inna fito ga Baba”

Na kwara mata kira bayan na bashi amsa. Sai ga Inna ta fito sanye da Hijabinta ta zauna bakin baranda tana gaisawa da shi.

“Na ce masa ko akwai abunda ya shiga tsakanin Bilal da Nawwara ne?”

Na tsayar da wankan da nake ma Noor na kalleshi gabana na faduwa. Sai Inna ta ce

“Miya faru”

“Ya aiko yanzu nan wai a bashi kayan aurensa ya fasa kuma wai ya yi magana da ita ya fada mata yace ta fada mana zai aiko ya karba”

“Sulaiman ai gaka ga yarka waka a bakin mai ita ta fi dadi”

STORY CONTINUES BELOW

Inna ta fada tana nuna masa ni.

“Ke Nawwara ya aka yi?”

“Jiya ne da yazo ya ce wai mahaifiyarsa ta ce bata yafe masa ya aureni ba, shine ya ce ya fasa aurena...”

Na fada ina kokarin fashewa da kuka.

“Daman Wallahi sai da muka raya a haka dukan mu sai da muka yi maganar nan, daman nasan irin rigingimun da suka faru ba zata bari ya aureki ba, Yakunbo ma sai da ta ce haka, amman matar nan ba ta yi tunani ba sam”

“Ni kaina na zargi hakan ganin irin maganganun da suke ta fada gabana”

“Ni kaina ina jin wasu abubuwan sai dai ka toshe kunnenka tun da ba a taruwa a zama daya, kuma a unguwar nan ma har a abunda ya kai unguwarmu babu abunda mutane basu fada ba, kuma kin san mutane da zuga Allah yasa haka shi ya fi alheri”

“Amin, nima haka na ce kuma in mijinta ne babu wanda ya isa ya shiga tsakaninsu”

“Tau Allah ya kyauta daman dai na ce sai na ji ta bakinta ne kamin mu bada kayan, Allah ya baki wani”

Ya fada ganin irin hawayen da nake, sannan ya mike tsaye ya fice cike da damuwa, daman kayan ba a nan suke ba, tun da aka kawo lefen aka maida shi can gurin Yakunbo kasancewar nan gidan ba Namijj kuma ina tsoron kar a biyo dare a tararda mu. A gaskiya na ji babu dadi na ji ni a cikin wani kalar yanayi mai kamar an yi min mutuwa, ban tabbatar da cewar Ina son Bilal sai a wannan lokacin, yanzu shikenan an raba mu kenan? A wunin ranar kasa sukuni na yi a cikin gidan mu, ana kiran la'asar na dauki Hijabi na nufi gidansu Jidda. Ina shiga na fashe musu da kuka daga ita har Maman Nura wato mahaifiyarta sai da hakalinsu ya tashi, sun tausaya min kuma sun nuna min rashin jidadinsu a fili lokacin da na labarta musu abunda ya faru.

“Yanzu duk soyayyar nan da kuka yi da Bilal ace be aureki ba gaskiya abun be yi dadi ba”

Cewar Jidda, sai Mahaifiyarta ta ce.

“Ni daman Wallahi ban dai fada ba ne, amman na san ba duka iyayene zasu iya bari dansu ya auri bazarawa ba, ko mai aure daya balle mai biyu kuma har da da, yanxu kuma ga abunda ya faru”

“Amman ni Wallahi da zaki min wani abu da kin auri Jibril ko dan mahaifiyarsa ta ji haushi, kuma ga Noor sannan mutumen yana son ki sosai, kin ga sai ma ya maiye gurbin kwanakin da suka rage a daura miki aure da shi”

Jidda ta fada, sai mahaifiyarta ta karba nata.

“Ni dai haka na gani, wani lokacin abunda kake so ba lallai ne ya zama alheri a gareka ba, kuma so da yawa kana kin abu ya zama shine alheri a gareka, ki baiwa Allah zabi kawai”

Wani irin abu na ji ya daki zuciyata, sam bana jin zan iya kara zaman aure da Jibril, indai har ban aure Bilal ba to be cancan na auri Jibril ba, taya ma zan yi zaman aure da mutumen da ya wulakanta ni ya nuna min ba ni muhimmanci a rayuwarsa. 16

“Na baiwa Allah zabi kuma na san zai zaba min abunda duk yafi zama alheri a gareni, amman ina jin kamar ba zan iya zaman aure da Jibril ba” 2

Jidda ta dafani.

“Zaki iya Nawwara, tunda kina son Noor kuma kina son farincikin danki, karki damu da rashin son da kike masa, abu mai muhimmanci shi yana sonki kuma so mai tsanani, kuma kinsan hausawa na cewa mai son ka be ganin ramarka, kuma kara ka auri wanda sonshi ya fi na ka yawa zaka fi jindadin zaman aure fiye da wanda ke kika fi sonshi, zan cigaba da miki addu'a kamar yadda na ke yi ma kaina Insha-Allah” 1

Hawayena na share na gyara zamana, ita kuma ta tashi ta fita saboda kiranta da aka yi a waya. Sai kusan magariba na baron gidan na dawo gida.
Bayan na yi sallama magariba na zauna ina ta karanta lahaula wala'kuwwati da carbi adadin da zan iya, saboda tana yaye damuwa kuma matukar kana cikin damuwa ka lizinci karanta ta Allah zai maka mafita.

Can kusan sallah isha'i na kira wayar Bilal sai suka nuna userbusy haka na yi ta trying suna amman na kasa samu daga karshe na gane ya saka number ta a blacklist ne. Wasa wasa aka kwana uku a haka na kasa cin abincin kirki saboda tunani, ba damuwa ce ta dame ni ba damuwar Bilal ce ta dame ni domin na san yana so na, kuma mutane da yawa zasu masa dariya idan har be aureni ba, duk na bi na rame kamar marar lafiya, jikina babu wani kuzarin kirki kasancewar bana iya cin abinci mai nauyi sai fura ko koko ko tea. 2

Ranar da aka kwana hudu da faruwar hakan ina zaune, da misalin biyar da rabi na yamma sai ga Asiya yar wajen Baba Sulaiman ta zo kiran wai na zo Baba Sulaiman da Baba Dahiru suna kirana, gabana ya fadi da farko kuma naji tsoro sai dai ance karka ji tsoron kira ka ji tsoron laifi da ka yi, kuma ina tunanin addu'a ta ce Allah ya amsa wata kila iyayen Bilal ne suka dawo a gyara maganar.

Sai da na fadawa Inna sannan na dauki Hijabi na saka muka fita tare. Muna shiga zauren gidan gabana ya fadi ganin Baba Sulaman da Baba Dahiru da kuma Baba Audi wato kanen mahaifina da yayyensa a zaune saman tabarma tare da Mahaifin Jibril da abokinsa wanda suka zo tare lokacin da wadancan abubuwan suka faru da kuma Yayan Jibril da wasu mutane maza da ban wayancin fuskarsu ba a zazzaune.

Sallama na fara yi bayan sun amsa gaishesu sai Baba Sulaiman ya nuna inda zan zauna, ba musu na zauna kaina a kasa gabana sai faduwa yake ina jiran jin dalilin kiran.

“Jibril ne ya aiko da iyayensa su nema mishi aurenki kuma ya ce kun yi magana da shi akan cewar zai aiko kin amince, amman mu baki fada mana ba, hakan yasa na ce ba za a yanke hukunci ba sai an kiraki an ji ta bakinki”

Na yi shiru ban ce komai ba, still kaina a kasa zuciyarta cike da tsanar Jibril. Sai Baba Audi ya katsa min tsawa. 1

“Ki bude baki ki yi magana mana, dukan mu ba yara balle ki tsaya yi mana wasa, da baki muke son jin amsarki ba da shiru domin ke bazawara ce ba budurwa ba, cewar kin amince shi zai tabbatar mana da cewar kin amince haka Annabi ya ce”

Dago kaina na yi na kallesu dukansu ni suke kallo amsata kawai suke son jin...

Post a Comment for "RAI BIYU CHAPTER 19"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...