Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

RAI BIYU CHAPTER 14

RAI BIYU CHAPTER 14

- - Post a Comment
RAI BIYU
CHAPTER 14

Ee kana da ɗa" +

Shine kawai abunda Jibril yake son jin ya fito daga bakin Nawwara, wani irin bugawa zuciyarsa take da sauri, ido cikin ido yake kallon Nawwara tsantsar gaskiyarta yake son ganewa, yadda ta saki baki tana kallonsa shi kansa yasan subul da baka ta yi, yadda take numfashi yake karantar da shi irin faɗuwar gaban da ke ranta.

"Kana da ɗa mana ƴaƴama zan ce, ba ka auri Aisha ba ta haifa maka ƴaƴa, na tuna ai tun kamin ka aureta ma ta samu ciki, wanda kake labarwa abokinka farinciki fal a ranka, kuma bayan ita maybe ka ƙara auren wasu matan sun mahaifa maka ƴaƴa ko kuma ka musu cikin shege"

Lumshe ido ya yi ya haɗe yawun dake bakinsa ya dunƙula hannunsa ya matse sosai kamar zai dake, har ga Allah baya jindaɗin kalamanta, duk lokacin da ya tuna rayuwarsa ta baya yana jin babu daɗi ballr kuma ace ita ce da kanta take tuna masa da wannan, hakan na karantar da shi cewar ba zata taɓa yafe masa ba kuma ba zata manta ba.

"Ina cikin da na barki da shi?"

Ya faɗa yayinda da buɗe idonsa da suka rine suka yi ja sosai.

"Cikin da ka kace ba naka ba ne? Ai na zubar domin ba zan iya ɗaukar shege a cikina ba"

"Ba zaki iya zubarwa ba, ba zaki iya kashe rai ba ko da kuwa ɗan shegen ne da gaske"

Kallonsa ta yi sai ta yi murmushi.

"Ashe kai da kanka ka san ba ɗan shege na ɗauka a cikina ba, amman ka ce ba naka ba ne ka haɗa hotona da hoton wani namiji wanda ban taɓa sanin inda ya fito ba, saboda kawai kana neman rabuwa da ni? Da na dawo da ciki sai suka kira da karuwa wannan dalili yasa na zubar da cikin"

Ta faɗa hawaye na fitowa daga idonta fuskarta kuma ɗauke da murmushi.
Wani irin ƙuna yake ji a cikin ransa, zuciyarsa zafi take kamar an kunna masa wuta, yana jin rashin kyautawa a duk lokacin da ya tuna abunda ya aikata mata, tabbas yanzu ya yarda akwai wawanci, shashanci a tare da shi, duƙursawa ya yi ƙasan guiwoyinsa ya kama Hijabinta sa gashi yana hawaye.

"Dan Allah Nawwara ki yi haƙuri dan Allah ki yafe min"

"Daman na faɗa, saboda ka riƙa neman yafiyata yasa ka cilasta min aiki a tare da kai"

"Ba dan haka ba ne Nawwara, saboda na samu kusanci da ke, ina sonki sosai Nawwara"

"Ni kuma bana son ka, bana kaunarka Jibril"

"Na sani"

Ya fada yana hade maganarta ciki da dacin rai. Zaunawa ta yi shi kuma ya mike tsaye na koma office dinsa, sam be gamsu ba shi da tsakaninsa da Nawwara ba, tabbas ya bar ta da ciki kuma ya san ba zata iya zubar da cikin ba.

'Ta haife shi, idan har babu haihuwa tsakamina da ita mi zai sa ta yi wannan maganar?'

Shine abunda zuciyarsa take ta raya masa, wayarsa ya dauka ya kira Siraj bugu biyu Siraj ya yi picking.

"Siraj ina son kasa a bincika min duk wani abu da ya shafi Nawwara, akwai da a tsakanina da ita Siraj kasa a abincika min"

"Okay"

Daga haka ya kashe wayar ya kira Abbah, sai da ta dade tana ringing sannan ya dauka yana kiran sunansa.

"Hello"

"Jibril"

"Abbah ina wuni"

"Lafiya kalau ya aiki?"

"Al-hamdilillah, Abbah akwai da tsakanina da Nawwara"

"Waya fada maka?"

"Ita ta yi subul da baka"

STORY CONTINUES BELOW


"Kaje gidansu ko? Bana fada maka karka je ba"

"Ban je ba, Abbah a nan kamfanin take aiki"

"How when?"

Ya kwashe komai ya fada ma Abbah amman be fada masa zance ya cilas mata aiki a tare da shi ba. Abbah ya yi shiru kamar mai tunanin abunda zai ce.

"Abbah we're meant to be"

"Kana son ta ka saketa? Bana son ka zama cikin irin mazan nan da ake fada Jibril ni yanzu ko wani aure ban yarda ka kara yi ba sai ka gane kuskurenka"

"Wallahi Allah Abbah na canja zan zauna da Nawwara zama na tsakani da Allah ba zan taba sakinta ba, Abbah ita kadai ce take so na tsakani da Allah"

"No ba yanzu, kuma na fada maka karka kuskura taka kafarka gidan nan"

"Tau Abbah ba zan yi ba, amman da Mahaifiyata tana da rai da ta roka min kai ka amince, rashinta ne yasa na rasa komai, ba ni da mata ba ni da ɗa sai kai kadai kai kuma ka kasa fahimta ta"

Yana fadar haka ya kashe wayar ya aje saman table, sai ya dora hannayensa saman table din ya dafe kansa ya dinga rusar kuka kamar karamin yaro.
Kuka yake sosai kuka ina zai saka kanshi, kuka neman mafita, be san mahaifiyarsa ba domin be tashi tare da ita ba, amman yana jin zafin rashinta kamar yanzu ta mutu ta barshi, ji yake ina ma tana raye da yanzu ta roka masa Nawwara ta yafe masa, ta shiga cikin lamarinsa ta gyara masa komai, be taba jin zafin rashin mahaifiya ba kamar yau.
Hannunsa yasa ya janyo aljihun table din da take zaune ya dauko hoton wata matashiyar mata mai kama da shi yana ta kallonta yana kuka kamar mace.
Kuka ya yi sosai har sai da ya soma jin kamar jiri yana dibarsa sannan ya tashi ya shiga bathroom ya wanke fuska ya dawo ya dauki ruwan freezer ya sha, sai ya dora gorar saman freezer ya nufi kofar fita.

Ko da ya fito Nawwara na zaune tana duba abubuwan da suke cikin computer, ya samu thirty seconds yana kallonta mugun burgeshi take gani yake a duk duniya babu wata mace da ta kaita daraja da kima da kuma kyau, ji ya yi kamar yaje ya rumgume kamkam a kirji, sai dai yasan ba shi da wannan damar. Karasa ya yi inda take yana kallonta da manyan idanuwansa masu kamar madara kamar zai cinyeta.

"Lokacin cin abinci ya yi, a nan zaki ci ko restaurant zamu je?"

"Ka ce min idan uku ta yi zan iya zuwa gida idan har babu aiki da yawa, kuma na ga yanzu uku sauran kwata"

Ta fada ba tare da ta kalleshi ba dan gaba daya ta tattara hankalinta ya maida kan computer.

"Ee amman a ka'ida karfe biyu da rabi zuwa uku ma'aikata suke zuwa cin abincin rana, taso muje restaurant"

Mike ta yi tsaye yana gaba tana biye har suka sauko kasa gaba daya, tare suke daga kafa kuma su aje tare har suka isa restaurant din dake cikin kamfanin, wani abun da ya bawa Nawwara mamaki suna shiga sai duk wanda ke gurin ya tashi ya fita, aka barsu su kadai daga ita sai shi. Karasa ya yi can guri wani teble wanda shi kadai yake zama akansa ya zauna ita ma ta zauna a kujerar dake fuskantar tasa.
Waiter ne ya zo da sauri yana tambayar abunda za a kawo musu.

"Fried rice and chicken soup"

"And drink?"

"Fanta"

Ya juyo gurin Jibril.

"And you Sir"

A hankali ya juyo ya kalleshi ba dan yasan a abunda yake tambaya ba sai a lokacin ya kula da shi domin gaba daya hankalinsa yana gurin Nawwara.

"And you Sir"

Ya sake maimatawa ganin kamar be ji abunda ya ce ba.

"Just water"

Nawwara ta masa wani kallo

"Ni ladai zan ci abincin kenan?"

"No"

STORY CONTINUES BELOW


Ya yi saurin amsa mata sannan ya sake kallon mutumen ya ce

"White rice and pepper soup"

"Drink?"

"Lemun juice"

"Okay"

Ya juya da sauri ya koma inda ya fito. Cikin yan seconds sai ga abincin an kawo musu, Nawwara ce ta fara dan ta nuna masa ita fa cin abincin kawai ya kawota ba komai ba, shi kan kasa taba abincin ya yi ya tsura mata ido kamar mai kirga lomomin da take, zuwa can ta dago ta kalleshi, sai ya yi saurin daukar spoon ya soma wasa da abinci dan har ga Allah baya jin cin abincin, kawai saboda ita ta samu ta ci ne yasa shi zuwa ko ba komai hakan zai kara masa kusanci da ita, yadda take cin abinci mugun burgeshi take ya tattara hankalinsa gaba daya ya mika mata, har ta gama cin abinci be yi ko da loma daya ba.

Wani abun da ya ba waiters din mamaki biya bill din abunda be taba yi ba, idan ba ya ci abinci a guri sai dai pa dinsa ya biya ko da kuwa shi da wani suka ci, amman yau shi ya biya da kansa sannan suka fita.
A lifter ma kallota yake ta yi zuciyarsa na mugun fisgarshi kamar zata fasa kirjinsa ta fito.

"Can i hug you?"

Ta juyo da sauri ta kalleshi kamar yadda yake kallonta, idanuwansa sun yi fari kal har wani ruwa ya kwanta a ciki.

"Baka da hankali Jibril, ka rumgume ni muharramarka ce? Ko dai ka dauka kamar Aisha na ke ne? Gaskiya kana bukatar komawa makaranta ka fahimci addini sosai"

"Am sorry"

Ya furta yana dauke idonsa daga kallonta so zai samu sauki zuciya, tare da danke hannunsa ya matse sosai.
Suna shiga Office ya wuce Office dinsa ya zauna saman kujera ya dora hannunsa saman goshinsa ya rufe ido yana sauraren bugun zuciyarsa.
Bayan an mintuna Nawwara ta shigo Office din rike da jakarta.

"Ni zan wuce"

Bude ido ya yi ya kalleta sai ya dauki wayarsa ya kira direbansa, yana yin picking.

"Get ready"

Yana fadar haka ya kashe wayar, da kansa ya dauki akwatinsa ya saka laptop dinsa da tardunsa sannan ya mika mata jikar.

"Aje saman teble"

Sai da ya aje sannan ta dauka suka.

"Ni fa gida zanje fa naga garin hadari ma ya hadu"

"Na sani a ka'idar kamfanin nan as you are my pa dole ni zan saukeki gida ko kuma direban kamfanin nan"

Ya yi tunanin zata musa masa ne, sai dai shi ba ya yi ba ne dan kawai ya kara kusanci da ita, haka dokar kamfanin take.
Tare suka fito duk mai son kallonsu sai idan sun bada baya sannan ake daga ido a kallesu domin sun san abunda Jibril ya fi tsana shine kallo. Ko da suka fito daga cikin kamfanin har an fara yayyafi motar da Jibril zai shiga kuma tana fake daidai bakin kamfanin, direban na ganinsa ya bude masa gidan baya da sauri yana kara masa umbrella, shi kuma sai ya zagaya ta wacan bangaren ya budewa Nawwara dan baya son ta shiga gaba, abunda ya bawa direban mamaki, ba tare da tunani komai ba ta shiga ta zauna, sai ya maida kofar ya rufe sannan ya zagayo ya shiga direban ya rufe masa, sai ta dora akwatin a tsakiyarsu ta maida hankalinta gurin gilashin motar tana kallon yadda ruwan sama ya soma sauka da karfi.

"Guiwa locos"

Ya fada yana kallonta, sai direban ya fisgi motar kamar ba ruwa sama ake ba, har aka shiga cikin unguwarsu bata juyo ta kalli inda Jibril yake ba, shi kuma idonsa na kanta, a hankali ya kai hannu zai taba hamnunta sai a ya yi dai dai da juyowarta tana fadawa direban inda zai aje ta.
Hakan yasa shi saurin janye hannunsa ya danke ya maida kallonsa gurin gidajen da suke unguwar da yadda mutanen suka fake saboda ruwa.

STORY CONTINUES BELOW


"Ya isa"

Direban na tsayawa ta bude motar zata fita sai ya yi karaf ya ce

"Akwai ruwa sosai ki dan jira a rage"

"A'a"

"Tahir kara mata lema"

"A'a"

Haka ta bude motar ta saka kafafunta cikin cabon da ke gurin tana tafiya ruwa na dukanta, sai da ya daina hangota sannan ya bude motar ya fita ya zagayo gefen da ta fito yasa hannunsa ya kwashi kasar da ta taka wacce ta fitar da sawon kafarta ya danke a hannunsa sannan ya koma cikin motar. 1

"Gida"

Kai tsaye direban ya nufi Sama road da shi, a hanyar ta tafiya ce ya fiddo wayarsa ya jira Rabi.

"Zan aiko miki da kudi duk abunda ya kamata ki siye, sai ki ka a addiren da zan turo miki yanzu amman sai kin tambaya saboda ban ga ainahin gidan ba"

Daga haka ya kashe wayar, har suka isa kasar na jinke a hannunsa ji yake kamar Nawwara ce ya rike, suna isa ya fita motar direban na tara masa lemar ya daga masa hannu alamar ya bari.
Falonsa ya shiga da hannu daya ya cire kayan jikinsa faffadan kirjinsa ya bayyana muscle din jikinsa duk suka fito real namiji, sai ga karensa ya zo da gudu yana kada masa bindi, shi kuma be kula shi ba ya nufi wata kofar ya bude ya shiga harabar gidan dake can ciki, kwantawa ya yi saman tile din ya shafa kasar a kirjinsa ya ware hannayensa ya lumshe ido ruwan saman na dukansa.


NAWWARA POV.

Sai da na tabbatar ba zasu hango ni sannan na hada da gudu ina ta tunanin subul da bakan da na yi, da yanzu ya gane ya zanyi kenan? Gaskiya ina da yauta sosai ni mi ya kaini wannan maganar ma. Kamin na isa gida komai nawa ya jike saboda ruwan da ake sosai. Inna ma ta yi mamaki ganina cikin ruwa, a bakin kofa na tsaya na cire tufafina sannan na saka wasu su kuma na rabasu gefen kofa har ruwan ya dauke. Wayana ma ruwa ya shiga ciki ya taba shi sai dai na yi sa'a be yi komai ba.
Saman kujera na zauna sai Noor yanzo kusa da ni ya zauna ya jingina kansa da jikina.

"Momy ki ara min wayarki na yi game"

"A'a kai baka da aiki sai game"

"Momy dan Allah"

Ya fada kamar zai yi kuka, ni kuma na hana shi domin wayar babu carji sosai a ciki, sosai na maida hankalina kan Sakina da ke ta rihazar din sira da zasu yi gasa a kai, Inna kuma ta dauko kur'ane tana karatu.

"Inna ki min addu'ah Allah ya sa na yi ta daya"

Cewar Sakina ganin Inna tana addu'a bayan ta gama karatun kur'anen.

"Yaushe ne ma?"

"Gobe kuma?"

"Eh daman kwana biyu aka bamu ai"

"Allah ya bada sa'a"

Na fada tare da tashi na fita waje dan yi alwalar la'asar. Bayan na gama sallah ne Inna take tambaya ya aikin na amsa mata da Al-hamdilillah, sannan na dauki wayata na kira Bilal sai ta saka min user busy, haka na yi ta har biyar na yamma ta yi amman bata shiga ba, hakan yasa na fahimce cewar na saka numberta a blacklist ne, amman mi na masa har haka ne? Ko dai yana fushi da ni ne?

Sallama muka ji da bakuwar murya, duk kokarin da na yi na rike Noor sai ya ci tura domin tuni ya kai bakin kofa shi da Jamila daman rigangan suke gurin amsa sallama ko leke aga wanene.

"Nawwara na nan?"

Na ji kamar muryar da na sani, hakan yasa na yi wuf na fita waje, Rabi ce tsanye da gown ta dora rigar sanyi sama fuskantar dauke da murmushi kamar kullum, sai dai ba ni take kallo ba Noor take kallo cike da burgewa, hakan yasa na maida shi bayana sai ta kalleni tana cigaba da fadada murmushinta, kamin ya matsa jikin kofar gidanmu ta ce

STORY CONTINUES BELOW


"Bismillah"

Sai ga wasu maza su biyu suna ta shigowa da kayan abinci da kuma manyan akwatuna guda uku suka dora saman barandar dakin Inna. Ni dai kallo na bisu da su har suka gama ganin ta juya zata fita yasa na ce

"Waya ce a akawo?"

"Ke ma ai kin sani"

"Dan Allah ki koma da kayan nan"

"Ni ba zan iya ba, amman zaki maidawa da kanki"

Inna da ke tsaye bayana ta ce

"Malama jeki abinki mun gode kinji"

"Nima na gode Mama, Handsome boy sai anjima ko"

Noor ya daga mata hannu yana murmushi da ya fitar da dimples dinsa.

"Okay Anti mun gode"

Ji na yi kamar na buge masa baki. Bayan ta fice Inna ta kalleni ta ce.

"Ba a maka alheri ka maida ko ya yake Nawwara, idan ma har kina jin ba zaki iya amfani da abunda ya baki ba, zaki iya kyautarwa, kuma idan har kika cigaba da nuna baki son abun hannunsa ba zaki karba hakan yana nufi har yanzu kina sonsa, amman idan har kika karba kika manta da komai kika nuna masa ba komai hakan zai kidimar da shi, domin zai gane cewa yanzu kina mu'ala ne da shi kawai ba ta so ba"

"Amman ai kamar ina son sa ne idan na karba"

"Ba daga nan take ba"

Sakina taje ta bude akwatin tana duba babu komai a ciki sai tufafi da abaya da kuma gowns, sai atamfa da lace wadanda ba a dinka ba,

"Amman gaskiya ba za a maida wannan kayan ba, ai ba mu muka ce ya kawo ba, mun ci banza"

Cewar Sakina tana gwada wasu tufafin a jikinta.

"Wallahi Anty ko ba zaki aureshi ba ki tatsi banza ko zafi ki rage"

Ni dai ban kulata ba balle banzan zancenta, haka na zauna cikin rashin dadin rai har dare saboda Bilal be kira ni kuma na tura masa sako be maido min da amsa ba.
Bayan sallah isha'i dpo ya zo gidanmu, ya yi wasu tambayoyi ni da Inna sannan na fada mana ya shigar da kara kotu kuma karshen watan nan ne za a fara zaman kotu, hakan ya faranta min rai sai na dan sake zuciyata ta washe.

Washe gari ba mu karya da abunda muka saba karyawa ba, saboda Indomie da aka kawo mana ita Sakina ta dafa suka ci ita da Jamila da Noor shi kan har tsalle yake yana direwa kasa yana jindadi sun ci indomie.
Inna kan kunu ta sha as usual nima shi na sha dan bana son ko warin indomie na ji balle kuma na kalleta har ya kai ni ga ci.

Bayan sun wuce makaranta, ni kuma na soma gyara gidan, sai da na gama sannan naje na samo mai ruwa ya zuba mana jalka shida Inna ta bashi dari da hansi, sai na zuba na shiga wanka.
Ina cikin bandaki na ji sallamar Baba Sulaiman da Baba Dahiru, wato kanen mahaifina da kuma yayansa, sai dai ga dukam alamu ba su kadai suke ba, domin Hayaniya ta yi yawa, ko da na fito Inna ta shimfida musu tabarma suna zaune ciki har da abokin Baba wanda ya sama masa aiki a Abuja da kuma Alhaji Bashir Makama wato mahaifin Jibril da wani dattijo tare da su.
Na ji dadin da Allah yasa na shiga wankan da Hijabi da fitowa ta yi min wuya, karasa na yi na durkusa har kasa na gaishesu, sannan na wuce dakinmu zuciyata cike da maganganu kala kala. Ina cikin saka tufafi Inna ta kira hakan yasa na yi hanzarin saka kayan na saka wani Hijabin na fito na zauna kusa da ita.

"Nawwara kin gane ni"

Na dago na kalli Alhaji Bashir da ya yi maganar sannan na daga masa kai.

"Zuwa na yi na baki hakuri akan abunda muka miki, hakika bamu kyauta ba, na sani amman dan Allah dan darajar iyayenki ki yafe mana, Wallahi har ga Allah Jibril ya canja kuma ya yi nadama, be san na zo nan ba ba shi ya turo ni ba, kuma bana son ya san na zo, na yi niyar yin haka tuntuni amman kunya da nauyinki yasa na kasa yi, yanzu ma sai da na biyo ta bangare Babanninki suka karfafa min guiwa sannan na samu na karaso ki dubi girman Allah ke da mahaifiyarki ku yi hakuri da abunda muka muku"

STORY CONTINUES BELOW


"Ba fa kai ka yi ba"

Cewar Baba Dahiru, sai ya amsa da

"Ai da na ya yi kamar ni na yi kenan"

Ni dai bance komai ba banda hawaye babu abunda na ke, Inna ce kawai take amsa masa, shi ma sai da su Baba Sulaiman suka saka baki, daga karshe ya yi magana agaisuwar rashin Baba, sai kuma ya tambaya yi Noor.

"Sun tafi makaranta"

"Amman Jibril be san yana da ba ko?"

Kai na daga masa, sai ya soma labarta mana yadda Jibril yake son da da kuma irin halin rayuwar da ya shiga bayan rabuwarmu.
Ya dauki kudi mai yawa ya bawa Baba Sulaiman da Baba Dahiru, sannan ya miko mana bandir din yan dubu daya.
Sannan ya yi mana sallama yana cewa yau ya zo kuma yanzu zai koma daman saboda ni ya zo.
Bayan sun tafi Inna ta zaunar da ni tana ta fada min maganganu akan rayuwa da kuma hakuri, ganin irin kuka da na ke.

"Na hakura Inna amman ni fa ba zan taba komawa ba"

"Babu wanda zai cilas miki komawa, amman ko dan ɗan dake tsakaminku ya kamata ace kun yafi juna"

Tashi na yi na fita na koma dakinmu na zauna na yi kuka sai da na koshi sannan na shirya na fito na yi ma Inna sallama. Gidansu Jidda na nufa da Mamanta muka fara gaisawa sannan na shiga dakinta sai ta juya min baya tana dannar wayar da ke hannunta. Ban damu ba na zauna gefen katifarta na soma mata magana.

"Jiya na yi mafarkinki Jidda, na yi mafarkin Mustapha zai cutar da ke"

Tayi banza da ni kamar bata ji ni ba, ganin hakan yasa na tashi zan fita sai ta kira sunana.

"Nawwara"

Hawaye na gani a idonta.

"Yi hakuri"

Dawowa na yi na zauna sai na dafata na fashe da kuka sosai, kwantar da ni tayi kafadarta sai da na yi kuka na gaji sannan na labarta mata abunda ya faru tsakani da Jibril da kuma iyayesa da suka zo gidanmu.

"Ki kara hakuri Nawwara ba gashi kin fara ganin sakamako ba, ni dai abunda na ke so ki yafewa Mustapha"

"Zan yafe masa"

"Amman..... Zaki iya"

Sai kuma ta yi shiru.

"Tashi kije karki makara"

Ta fada, ni kuma na tashi sai ta rakoni har kofar gida sannan na fice ita kuma ta koma. A hanya na hadu da Mustapha ina tunanin ita ta fada masa gani nan na fito, sai ya sha gabana da motarsa sannan ya bude ya fito, sai kuma ya kasa ce min komai sai kallona yake.

"Na yafe maka Mustapha ka dauka kamar komai be faru ba, amman zan gargadeka karka sake shiga hanyata, dan Allah dan Annabi ka fita hanyata"

Ina fadar hakan na kama gabana na cigaba da tafiyata na barshi nan tsaye yana ta kallona. 
Har na yi kamar na bi ta gurin gidansu Bilal duk da na san by this time yana gurin aiki, sai kuma na bi hanyar da na saba bi.

Na isa gurin aikin da misalin sha biyu saura kwata, yau ma atamfar roba ce a jikina da gyale. Kai tsaye na wuce gurin aikina zuciyata cike da son ganin Bilal, sai dai ban san takamaiman inda yake aiki ba. 
Ina isa kofar ta bude min, office dina na fara gyarawa sannan na shiga na shi Office din baya cikin hakan na nufin be shigo ba kenan, sai na na gyara komai sannan na fito, ko da na dawo nawa Office din wato office din farko wayata na ringing alamar kira ko da na duba sai na ga Number Zinatu da fari na yi mamakin da sunanta ya yi appearing a wayata sai dai tuna Rabi data karbi wayata tace za a saka min numbers mutane kuma nima a basu tawa yasa danna picking na kara a kunne.

"Nawwara dan Allah ki sauko hawa na biyu yanzu"

"Me zanyi?"

"Dan Allah dai ki sauko Bilal yake nemanki"

"Okay"

Cikin hanzari na fita na shiga lifter, a hawa na biyu na sauka komai na gurin glass ne ma'ana wani ma'aikacin yana iya hango dan uwansa, haka na rika duba sunayen da ke gurin har na kai ga wanda aka rubuta Bilal Usman na tura na shiga, sai na samu dakin cike da mutane duka tsaye wani katon cake na gaban Bilal da wuka a jiki, 
Ina shigowa sai hankalinsa ya dawo kaina kamar marar gaskiya, sam baya farinciki kamar ba shi suke yi ma wakar happy birthday ba, kasa jurewa na yi sai idanuwa suka cika da kwalla, shi kuma ya gagara karbar cake din da Zinatu take kokarin kai masa a baki.

"Happy birthday my dear"

Shi kuma hankalinsa gaba daya a tashe yake ni kawai yake kallo.Tana daf da kai masa cake din a baki sai ya yi saurin rike hannunta.

“No thanks”

“Haba Bilal sai ka ce wani abu yau ne birthday ka fa” 2

Sake kai masa a baki da karfi har tana shafa masa ragowar da yake hannunta a fuska tana dariya ita da mutane da suke cikin office din. Sannan ta juyo ta kalleni

“Karo mana Nawwara let's have fun”

“No ina da aiki a ciki, Happy birthday Bilal”

Na fada idanuwa cike da kwalla, sannan na juya na fito hawaye na bin fuskata. 
  Ban yi nisa a tafiyarba na ji muryarsa yana kirana ni kuma na kara sauri kamin ya karo inda nake har na shige lifted, ina sauka hawa na biyar na shige Office ina kuka, ko mintuna ban yi da zama ba sai gashi yazo gurin kofar, ina kallonsa ta computer na ki budewa sai kuka na ke har ga Allah na ji zafin wannan abun, da ya gaji da tsayuwa ya kirani, ban daga ba har ta yi ringing ta gaji ta katse, haka ya jera min kira har guda goma sha uku ban dauka ba, be bar gurinba sai da Jibril ya karaso sannan ya yi hanzarin barin gurin, ni kuma na yi saurin tashi na share hawayena, sai dai hakan be hana shi fahimtar kuka na yi ba. 1

“Good morning”

Na fada ina a tsaye idanuwa a kasa muryata na bayyana kukana, a maimakon ya amsa min sai kawai ya karaso gaban table dina yana kallon fuskata.

“Me kike yi ma kuka?”

“Ba komai”

Na fada idanuwa na kara cika da kwalla.

“Fada min mana waya taba ki?”

“Babu”

“Aikin ne baki so?”

Na kasa amsawa sai hawaye nake.

“Mi Bilal ya zo yi nan? Miyasa kika ki bude masa?”

“Ba komai”

Ya daki table dina.

“Dole ne ki fada min abunda yasa Gimbiyata zubar wannan hawayen mai daraja da tsada” 4

Ya fada kamar ba shi ya yi maganar fuskarsa babu alamun wasa sai ma kara hade rai da ya yi

“He's just come to apologise”

“Apologise for what?”

“Yau ya yi birthday, shine ya yi celebration tare da Zinatu”

Kallona ya tsaya yi sosai kamar mai karantar abu a fuskata, sai kuma ya kyalkyale da dariya har sai da office din ya dauka gaba yana amsa amonsa. 2

“Wow wow so that's means Zinatu ya ke so ba ke ba? Daman can ba saurayinki ba ne ko? Ko kuma...” 2

Ganin yadda na ke hawaye yasa shi saurin rufe baki yana gintse dariyar da ke cinsa.

“Okay calm down Naj-Babe i will talk to both of them”

Yana fadar hakan ya nufi office dinsa sai cigaba ya ke da dariyar, kamar cikinsa zai fashe. Ni kuma na zauna a gurin hawaye na ta min zuba zuciyata kuma na mugun zafi.

JIBRIL POV.

Be shigo office din da dadin rai ba, amman wannan labarin na ya faranta masa rai.

“Excellent”

Ya furta yana kokarin zama, abun ya fi tsaya masa a rai Zinatu da gaske tana son shi ko kuma ta yi ne kawai as a friend ita kuma Nawwara kishi ya rufeta.

“Wow”

Ya furta yana dora kafarsa daya saman daya yana lilo da kujerar. 1

“Allah ya kara raba kanku” 10

STORY CONTINUES BELOW


Bayan kamar thirty minutes Nawwara ta shigo Office din idonta a kasa.

“Kana bukatar wani abun ne?”

Kallonta yake, ya ji dadin abunda ya faru amman wannan halin da take ciki baya son shi ga hawayen da ta kasa dainawa har yanzu, yasan tana jin kwatankwacin irin zafin da yake ji a duk lokacin da ta kula wani ba shi ba. Mika hannu ya yi zai riko hannunta sai ta yanje ta yi cikinsa da masifa.

“Miyasa kake son taba hannuna ne? Miyasa kuka dauki rumgumar mace da taba hannunta a matsayin wayewa? Baka san zunubin da ke akwai a taba hannun mace da ba muharramarka ba? Baka da rayuwa mai kyau Jibril” 2

Uffan be ce mata ba har ta juya ta fita, sai dai maganganunta suna masa zafi, baya jindadin yadda duk maganar da ta zo mata a baki take fada masa, ciwon da ke damunsa ne ya taso masa har yana neman numfashinsa sai da ya dinga sauke ajiyar zuciya yana dafe zuciyar sannan ya samu sassauci har ya nufi freezer ya sha ruwa, sai kuma ya bude durowarsa ya dauko cocaine ya zo ya zauna gaban teburinsa ya soma shaka. Sai ga Nawwara ta shigo da wasu takardu a hannunta tsayawa ya yi kallonta kamar yadda ita ma take kallonsa.

“Kana da meeting da pearls global company misalin sha biyu da rabi, wannan kuma daga Dr Ishak Hacker ne zaka saka hannune a maida masa”

Ta fada tana dora masa takardun saman table dinsa, kamar be damu da ganin da tayi masa yana shan cocaine ba ya dauki pen ya saka hannu, ita kuma ta juya ta fice ba tare da ce masa komai ba. Wayarsa ya dauka ya kira Siraj.

“Ka bincika?”

“Eh amman ance bata da wani da kuma binciken ya nuna bata ma taba yin ciki ba” 2

Ya busar da iskar bakinsa dan ba abunda yake son ji kenan ba.

“Ka tabbata?”

“Yes, walimar da kasa a shirya yau za'ayi”

“Thank you Siraj ayi abunda ya dace”

Ya katse kiran yana ta tunani, sam zuciyarsa bata yarda babu da tsakaninsa da Nawwara ba, ji yake kamar dai Siraj be yi binciken daidai ba, ko kuma Nawwara tasa a boye masa ne. Rabi ya kira dan jin yadda aka yi daman tun da ta kai kayan ta kirashi be dauka ba sai ta aiko masa da sako amman be bude ba.

“Good morning Sir”

“Ina jinki!”

“Na kira wayarka baka daga ba kuma na aiko maka da sako, anyi komai yadda ya dace Sir sai dai ita kadai na yi ma siyayyar”

Ta fada da zimmar ta ji abunda zai ce tace ba tayi ma yaronta ba dan ita a zatonta Jibril ya san da shi.

“Eh daman ita kadai zaki yi ma”

Yana fadar hakan ya kashe wayar yana jin kansa kamar marar lafiya. Sha biyu saura kwata Nawwara ta sake dawowa office din.

“Akwai wani abun da ya kamata muje da shi gurin meeting din ne?”

“Ee takardun kamfanin nan, suna cikin can”

Ya nuna mata wani katon box dake lake da ginin gurin, karasawa ta yi tana kokarin budewa amman ta kasa.

“Sai kin sa password”

“Miye password din?”

“N¹¹A²³W²¹W³¹A³³R¹³A” 2

Sunanta ne zere sai mixing da aka yi da numbers, tana saka. Password din sai ya bude, farkon box din cocaine ce mai yawa, na biyu kuma zinari ne irin wanda aka ciro cikin kasa ba a sarrafashi ba, sai dollars dake binsu daga karshe ne takardun suke.

“Duka zan dauko?”

“Ki duba files din wanda aka rubutawa 001 zaki dauko”

Daki-daki ta bisu har ta wanda yake magana akai ta dauko, sannan ya maida marfin box din ta rufe ta taso ta nufo table dinsa.

STORY CONTINUES BELOW


“Miyasa kake son shan cocaine ne?”

Yaja ragowar dake hancinsa sannan ya dauke idonsa daga barin kallonta.

“Saboda na rage damuwa da bacin rai”

“Waya fada maka tana cire damuwa?”

Ya mike tsaye ya nufi gurin window ya tsaya tare da sanya hannayensa aljihu.

“A lokacin da na haukace akan tunaninki na rabu da kowa, na watsar da dukan abokaina sai Allah ya hadani da Siraj, shi ne kadai mutumen da ya taimaki rayuwata na fara dawowa mutum da wannan cocaine din, a duk lokacin na shakata ina samun sassauci akan tunaninki, musamman a lokacin da take buguna ba kamar yanzu da bata min aiki ba” 2

“Amman miyasa kake sha?”

“Saboda ta zame min jiki”

“Idan har kana son ka kore damuwa ka rika daukar kur'ane kana karatu, ina tunanin ka san illar wannan cocaine din”

Ya juyo ya kalleta.

“Ba ni da wani zabi ne saboda tunaninki na fara shanta”

NAWWARA POV.

Ban sake ce masa komai ba na juyo ya baro office din, zuciya cike da rashin jindadin halin rayuwar da jibril yake yi. Yanzu akaf a familynsa a rasa wanda zai tsaya ya fada masa gaskiya akan rayuwa? Babu mai iya bata lokacinsa ya zauna da Jibril ko dana dan lokaci ne? Abun bakiciki ne namiji kamarsa ace be san abunda ya dace ba, shikenan saboda be da mahaifiya a raye mahaifinsa ba zai iya zauna da shi ya fahimci rayuwar dansa ba? 
   Ni kadai ce zan iya canja rayuwar Jibril a yanzu, saboda ni kawai yake saurare ni ce kadai zan matsa tsawa be maida min ba, dole na taimaki rayuwarsa ko dan dana ba ni da wani zabi a yanzu da ya wuce wannan ko na ki ko na so uban Noor ne kuma dole wata rana Noor zai yi rayuwa da Ubansa, idan bashi a tafarki mai kyau taya Noor zai kalleshi? 4

Tunani kenan sai kuma wata zuciyar ta jefo min tambaya.

‘Yanzu mutumen da ya wulakanta ya nuna baki da muhimmanci a rayuwarsa  mutumen da ya kiraki da annoba? Yasa aka kiraki karuwa? Ya ce dan da kike takama da shi ba nasa ba ne? Ya wulakanta mahaifanki ya tozarta ki a idon duniya ya ce ganin bakin maciji ya fi masa ganinki, shi zaki taimaka? Irin wannan mutumen zaki tausayawa? Wanda ya kasa baki taimako daga lokacin da kike bukatarsa ya fifita karuwa akanki?’ 5

“No no ba zan iya ba”

Na furta a fili idanuwana cike da tsanarsa.

“Yaje ya yi ta yin rayuwar da yake ganin zata fidda shi ni babu ruwana a ciki”

Ina rufe bakina yana fitowa daga office, ni kuma na mike tsaye na dauki takardun.

“Naj ina ɗa na?”

Wani wawan kallo na watsa masa.

“Da kuma? Ko cocaine din ta fara bugunka?”

“Ina cikin hayyacina na san abunda na ke ina dana ko yata?”

“Mtssss kana hauka Jibril baka ma san abunda kake fada ba”

Ina yin gaba na ji an fisgoni na fado kirjinsa sai ya rumgume kamkam ya lumshe ido, ina jin yadda zuciyarsa ke mugun bugawa numfashinsa kuma na fita da sauri. Iya karfin da Allah ya bani da kuma dabara ya saka wajen ganin na kwace kaina amman na kasa ko kwakkwaran motsi, saboda karfinsa ya ninka nawa sau saba'in.

“Ka sake ni ko na maka ihu”

“Ko kin yi ihu babu wanda zai zo”

Ya fada idonsa a lumshe yana kara kwamtar da kaina a kirjinsa.

STORY CONTINUES BELOW


“Kina jin yadda zuciyata take bugawa ko Naj saboda ke”

“Idan baka sake ni ba zan sake zuwa aikin nan ba, daman saboda ka rika min haka ka tirsasani yin aiki a tare da kai ko?”

Ya dora kansa saman kaina.

“Ina ma zamu dawwama a haka”

“Ba zan sake zuwa aikin nan ba”

Ya yi saurin saki na.

“Ina son ki sosai Naj ina miki irin son da wani da namiji be taba miki ba”

“Ni kuma bana son..”

Na kasa karasa saboda hannunsa da yasa ya rufe min baki, sai kuma ya duka kasan guiwoyinsa ya hade hannayensa.

“Dan Allah dan Annabi Naj ki yafe min abunda na yi miki, dan Allah ki manta da komai” 1

“Na manta da komai saboda ka san ka zalince ni ko? Mugu bakin azzalumi” 5

“Ki kirani da ko wane irin suna zan karba miki, ki ayyanani a duk kalar mutumen da kike gani zan dauka, ki ci mutunci a gaban kowa zan jure matukar hakan zaisa ki yafe min”

“Ba zai taba sa na yafe maka ba”

“Fada min abunda zan yi ki yafe min Naj, ni kadai na san irin abunda na ke ji a zuciyana, na kan tsani kaina idan a duk lokacin da na tuna abunda na aikata miki, tunaninki ya haddasa min ciwo da damuwa, rashin kulawar nan taki ina jin kamar yana kokarin rabani da rayuwata ne, i will die soon Naj mai yuyuwa a wannan lokacin zaki tausaya min ki zo gaban gawata ki yafe min”

Hawaye yake irin hawayen nan dake nuna tsantsar abunda ke zuciyarsa, ga nadama da damuwa nan ƙarara a fuskarsa.

“Lokaci meeting yana wuce”

Na fada tare da daukar takardun na nufi kofar fita. A ranar meeting hudu muka yi uku a cikin kamfanin daya kuma a wani kamfanin da muka je tare, sai dai sam babu walwala da sakewa a fuskar Jibril da ma yadda yake maganarsa da mu'alama da mutane, dukan abunda zan yi hankalinsa yana kaina, da muka dawo na yi sallah shi kuma ya dora alwala ya fita zuwa sallah a masallacin da ke kamfanin ni kaina ban taba sanin akwai masallaci a kamfanin ba sai yau, bayan na dawo ya cilasta min zuwa cin abincin rana kamar jiya, da muka shigo office ya dauko wasu takardu ya aje min wai na yi typing dinsu a computer shi kuma ya nemi wata kujera ya aje gaban teburina yana kallona har na yi aikin na gama.

Tare da shi muka shiga mota, ya kawoni a inda ya aje jiya sannan ya mika min wata sabuwar laptop, wai da ita zan dinga zuwa office kuma na je gida ta aiki ce sai kuma na bukaci na kwashe duk abunda ke cikin wacan computer ta office na saka a laptop din, ni dai ban ce masa na gode ba balle sai anjima na fito na yi tafiyata.

Ko da na isa gida yamma ta yi lis saboda yau na dade sosai a gurin aikin, na darar da gidanmu cike da mutane suna ta mana murna wai Sakina ta ci gasa an bata gida kuma wanda yasa gasar ya dauki nauyin karatunta sannan ya yi mata kyautar dubu dari biyu da hansin, ita kanta kamar zata hade kanta dan murya.

Jibril kawai zuciyata ke raya min ya saka gasar nan, sai kuma daga baya na soma tunanin Mustapha domin shine a unguwar ya fi kowa sanin inda Sakina take karatu, har dare mutane nata shigo mana, Inna ta siye minti ta yi sadaka, bayan sallah isha'i Bilal ya kirani a waya na ki na daga sai ya aiko min da sako wai yana kofar gida, nan ma ban mayar masa da amsa ba jim kadan sai ga yaro ya shigo wai ana sallama da Nawwara, sai na yi karaf na ce

“Je ka ce ba zata zo ba”

Inna ta saki baki.

“Ba zaki zo ba? Ba kyau wulakanta dan adam fa, Wallahi ki kama kanki, ni bana son yawan zuwan da ake ama miki sallama, wallahi ko aikin nan da kike zuwa hankalina be kwance yake ba, bani da kwanciyar hankali idan ba aure kika yi ba”

STORY CONTINUES BELOW


“Inna Bilal ne fa”

“To dan me ba zaki je ba?”

“Wai birthday yayi yau shi da Zinatu suka yanka cake din kuma a gurin aikinmu wai har da kirana dan na gani”

“Kishi kike kenan, ashe ana kishin abunda ba a so?”

“Ni ina son shi”

“Kina son shi kike nuna baki son shi? Kina son shi miya hana ki aure shi? Yanzu ke kina ganin zaki samu namijin da zai so ki kamar yadda Bilal yake son ki? Babu abunda ba a fada masa ba a kanki amman ya toshe kunne ya ce yaji ya gani shi dai son ki yake, kuma kina da ɗa shi yana saurayi kuma a haka yake son ki, babu irin kulawar ta cusa kai da be nuna miki ba amman kiki bashi dama, sai yanzu dan ya kula wata zaki ji haushi har ki zo kina kishi? Wane iriin zama kike son ku yi da shi? Shi dai aure yake son ki idan baki bashi dama ba ai dole yaje inda wacce zata bashi dama,

Idan har son Bilal kike da gaske tau ki bashi dama ya ga magabatanki, sai ki yi kishi mai dalili, amman yanzu ai cin amanarsa zaki yi ki hana shi aurenki kuma ki ce ba zai kula wata ba?”

“Amman Inna ai kin san yan gidansu basa so na, ni bana son na yi aure inda zan wahala ni da Noor”

Na fada ina kuka, sai ta ce

“Zaki wahala dai ke, Noor kan ai ba zai zauna tare da ku ba, duk son da Bilal yake nunuwa Noor ana daura miki aure dole a gida zaki barsa sai dai ya rika zuwa yana ganinki, saboda Bilal Saurayi ba mai mata ba, da ma ace yana da mata da zakiniya zuwa da danki ya rika shi, amman wannan kan ai sai ya kara kiyayyar ki ga yan uwansa kuma jama'a ma sai su zageni ace na bari aka je da yaro ya takura masa, ina tunanin ba a gidansu zai aje ki ba ko da ya aureki, dan haka yan uwansa su daina damunki ba akansu zaki zauna ba, indai mijinki na son ki babu wanda ya isa ya taka ki, sai dai ki shiryar fuskantar kalubale daga garesu”

Na kara fashewa da kuka, ni dai har ga Allah ina son Bilal dina, kuma bana jin zan iya auren wani namiji bayan shi.

***     ***     ***

Washe kamar marar lafiya haka na tashi jiki babu dadi zuciya ma babu dadi, bayan mun gama karyawa suka tafi makaranta ni kuma na gyara gida sannan na shiga na yi wanka ina fitowa na shirya cikin wata bakar abaya, da mayafinta, sannan na dauki laptop din da jakata na nufi dakin Inna ina mata sallama.

“Amman dai ina tsoron ki rika wannan abun a hannu, kin san garin ne ko maza ya suka kare balle mata”

“Ai kin ga a ciki jaka take ba wanda zai san abunda ke ciki, kuma ina addu'a inshallah babu abunda zai sameni”

“Tau Allah ya tsare ya kai lafiya, ni jiya ma duk a tsoro na kwana saboda gidan nan da yan kudi da aka bamu, yau zanje na kai gidan Ya Umma na fada mata komai duk shawarar da aka yanke idan kin dawo sai kiji”

Ta karasa tana miko min dari biyar na hau Napep.

“Tau Na gode sai na dawo”

“A dawo lafiya Allah ya tsare, ga wayarki da kika bari jiya”

Nasa hannu na karba, miss call talatin da bakwai Siraj ya yi min, sai kuma kiran Jibril guda daya, da kuma wata bakuwar number  ni dai ban wani maida hankali kan wayar ba nasa kai na fice ina ta tuno abunda ya faru jiya sai na ji raina ya sosu. 
   Yau na ji da wuri sai dai duk da hakan ya rigani zuwa, a gabansa na gyara office din na jera komai yadda ya dace sannan na hada masa tea, files din da aka kawo dake kofar office din farko na dauka ina duba wanda zai saka hannu na kai masa wanda kuma ni zan yi aikin na maida hankalina ina ta yi, misalin sha biyu na shiga na fada nasa meeting din da muke da su da kuma mutane da yake da appointment da su, be samu kansa ba sai biyu daidai saboda ganawa da yake da mutane, abun mamaki sai gashi ya fito da alwalarsa ya sauka saka ya yi sallah, ni dai already na yi sallah duk da kasancewar ina jin marata tana murda min tun Shekaran jiya alamar menstruation dina na daf da zuwa, sai dai na san kamin ta zo na kan yi kurajen fuska ko da kwara daya ne ko biyu, rashin ganin kurajen yasa ban maida hankali akan tararta ba.

Bayan ya dawo ya shiga meeting, yana fitowa yasa na hada masa tea, na shiga office din ya fi a kirga ina kai masa files da documents, sannan na koma na cigaba da saka kwashe abubuwan da suke cikin computer ina sakawa a laptop, muma haka danjar nan tayi kara alamar da mutun a bakin kofar office din, a computer na ga Rabi sai na bude mata ta shigo fuskarta da murmurshi kamar kullum, wata bakar leda ta aje min saman table ta ce

“Oga ya ce a baki wannan”

Tana ajewa ya juya ya fita, ni kuma naja ledar na soma budewa, abaya ce mai dankwali green color sai dozing din pant da pad da kuma turare. Gabana ya fadi mi yake nufi ne, sauri mikewa na yi tsaye na duba baya ashe rigata ta bace, gashi abaya ce ba Hijab balle ya kare min, arzikina ma bakar abaya ce, amman ya aka yi ya zubo min ban ji ba? Wata irin kunya ce ta rufe ni tunanin daya fado min a rai shine. 2

A haka naje meeting din ko dai bayan mun dawo cikin office haka ya faru? Kaddara dai ta riga fata, bathroom na shiga na tsabtace kaina sannan na wanke rigar da karamin saket dina da ya bace da pant dina, na saka abunda ya bani, sannan na kulle wadancan kayan a ledar na fito na saka a jakata.

Ina zaune da kunyata sai gashi ya fito daga office dinsa yana fadin

“Ba zamu samu damar cin abinci a kamfanin nan ba, saboda akwai wanda zan mu magana da shi a waje, saboda haka tare zamu fita sai na shiga meeting din ke kuma ki ci abinci”

Ni dai ban ce komai ba kuma na ki na kalleshi, sai dai kijina na bani so yake na kalleshi din, na dauki jakata na rayata sannan na rika jakar dake hannunsa a dayan hannuna kuma laptop ce. 
Tare muka shiga motar ina jin kamar na natse saboda kunya, har muka isa ban kalli inda yake ba, shi kuma yana ta motsi yana son na kalleshi din.

Kamfanin da muka je kamfanin Chinese ne yan nigerian da suke aiki ciki basa da yawa, komai a tsare gwanin sha'awa. Wani bahaushe ne mai far'a da son mutane ya tare mu kuma ya yi mana iso har inda za'ayi meeting din.

Da zai shiga ya juyo yan karbi jakarsa da laptop din dake hannuna ya kalleni ya ce

“Duk kika sake kika yi fira da wani sai na yanka miki baki”

Be tsaya jiran amsar da zan bashi ba ya shigewarsa tare da mutumen, ni kuma na zauna a gurin ina kallon mutunen dake ta kai da kawo, bayan kamar minti biyar sai ga mutumen ya kawo min abinci na karba ina masa godiya ba dan ina iya ci ba, saboda mutane kowa kallona yake ba zan iya bude baki a irin wannan gurin na ci abinci ba wannan ba mutunci ba ne. 
Fira ya soma yi da ni sama sama yana danna laptop dinsa, ana nan yake labarta min cewar shi dan Zaria ne, muna haka wayata ta soma ringing, bakuwar number ce har na yi kamar karna dauka sai kuma na daga, muryar Sakina na ji tana kuka.

“Anty ki yi sauri ki zo Noor ya samu accident gashi nan za a kai shi asibiti”

“Wace asibiti?”

Na tambaya hankalina a tashe.

“Specialist Hospital”

“Gani nan zuwa”

Na kashe wayar a lokacin har na fara kuka,

“Lafiya?”

“Ɗa na ya yi haɗari” 4

“Bari a fada masa mana”

“A a”

Ina fadin haka na fita da gudu hankalina a tashe har bana iya gani da kyau.Sun samu kusan mintuna arba'in suna meeting din sannan daga karshe suka cimma matsaya daya akan kwangilar da kamfanin zai bawa kamfaninsu Jibril.  Hannu ya mikawa Jibril suka gaisa sannan ya fito, daman hankalinta yana can gurin Nawwara zuciyarsa na raya masa tana can tana fira da wannan mutumen na dazu.
  
Da ya fito sai ya samu Mutumen shi kadai yana ta aikinsa sai wasu mutun biyu da suka zauna a kujerar da ya bar Nawwara dazu, kamar ba zai tambaya a zatonsa tana can wani gurin ne ko kuma ta koma cikin mota. 1

“Mai gida matar da kuke tare ta fita wai dan ta ya yi hatsari”

Sai Jibril ya tsaya cak kana ya juyo ya kalleshi.

“Dan ta?”

Ya fada.

“Ee tun dazu ta tafi na ce bari a fada maka sai ta ce a a”

“Kasan matar da muke tare kuwa?”

“Ee wacce kuka shigo tare, ai ni na tarboku na santa wata fara doguwa ba sosai ba mai dan fadin fuska tana sanye da abaya green” 1

“Amman dan ta ka ji ta ce ko kanenta?”

“Dan ta dai ta ce indai ba rudewa ta yi ba, saboda waya aka kira aka fada mata”

“Kaji wani abu bayan wannan?”

“A a gaskiya hankalinta a tashe yake bata ce komai ba”

Da sauri Jibril ya fita daga harabar gurin direbansa na hangosa ya san a uzurce yake kuma ya san babu abunda ya tsana irin jira, tun kamin ya karaso ya janyo mota kuma ya bude masa. Har Jibril zai shiga sai kuma ya mika masa jakarsa da laptop dake hannunsa.

“Nawwara ta tafi”

“Ee naga ta fice da gudu tana kuka har wani na tambayarta a abunda ya faru bata dai kula shi ba”

Ya amsa masa yana saka Laptop din a mota, juyawa Jibril ya yi ya koma ciki gurin mutumen dazu.

“Please ko kaji inda zata je? Ko kuma inda hadarin ya faru?”

Mutumen da dan yi shiru sannan ya daga masa kai.

“Ee na ji ta ambaci Specialist Hospital gaskiya ina jin ko can aka kai yaron ko kuma can hadarin ya faru” 2

“Thank you”

Ya juyo da sauri ya nufi gurin motarsa, driver seat ya nufa ya ce direban ya fita ya hau achaba shi akwai inda zai je, @360 ya fisgi motar kamar zai tashi sama, wani irin vibration jininsa yake yana jin kamar ya runtse ido ya gansa a cikin asibitin.

“Dan ta...” 1

Yana ta maimaita hakan ya iso Abuja road sai ya dauke hanyar da zata sada shi da Specialist, gudu yake sosai kamar dan shi aka yi titi ko kuma ance masa babu ababen hawa sai nasa kadai. 
  Lokacin da zai kunna kai a gate din Specialist din sai da ya yi kamar zai buge wani magidanci da ke kokarin fitowa. 
  Ko fakin din kirki be yi ba ya fito yana ta waiwagen inda zai shiga, tsabar rude daman can sau daya ya taba shigo asibitin loacin da yake farkofarkon zuwa sokoto sika yi wata mata tiyata.

Da sauri ya nufi emergency wajen yan hatsari, har ciki ya karasa ya karasa inda Nurses suke ya muna masu id cart dinsa sannan ya soma tambayarsu ko an kawo wani.

“Eh an kawo mutun daya yanzu”

“Zai kai minti nawa?”

“Ten haka yanzu yanzu”

“Babba ne ko yaro?”

“Gaskiya dattijo ne”

“No wanda na ke nema karamin yaro ne yana tare da mamansa ina jin za ayi awa daya yanzu da kawo shi”

STORY CONTINUES BELOW


“Eh an kawo wani yaro dazu, yana ciki bayan shi ma an kawo wani”

Dayar Matar ta fada.

“Bari na duba”

Ya nufi ciki da sauri ya soma bin dakuna, sai gashi ya hadu da wani likita abokinsa. Shi ya rike Jibril dan hankalinsa gaba daya sama yake baya ganin kowa.

“Jibril”

“Dan Allah wani yaro na kr nema wanda aka kawo ya yi hatsari dazu”

“Yaro ne sosai?”

Ya dan yi shuru yana tunanin ta yadda zai amsa tunda ba sanin yaron ya yi ba.

“Yeah yeah yaro ne”

“Akwai wanda aka shiga tiyata da shi yanzu akwai kuma wanda ya rasu dazu, amman ba a fita da gawarsa ba saboda basu biya hospital bill ba”

“Wait...”

Ya fada sai ya fiddo wayarsa ya kira Nawwara duk da yasan ba zata bari ya karaso ba, ringing biyu aka daga da muryar Sakina tana masa sallama.

“Ina Nawwara?”

“Bata da lafiya”

“Wacece ke?”

“Ni kanwarta ce”

“Kuna ina ne Nawwara tana ina”

“Muna nan asibiti?”

“Wani waje?”

“Dakin Balaraba”

Ya katse wayar yana kallon likitan.

“Ina ne sashen balaraba?”

“Ta can ne, ko shine yaron da ake neman jininsa aka zo diban na uwar ta suma?”

Jibril ya rike.

“Please zan iya ganin yaron”

“Yes this way, amman an shiga tiyata da shi gaskiya ba zaka iya ganinsa yanzu ba sai dai a jira ya fito”

Tare suka karasa sashen da ake yan tiyata, jikin Jibril sai rawa yake sosai ya so ya shiga amman likitan ya hanashi saboda tiyata ake masa kuma yasan irin matsalar da zai janyo matukar ya ce zai shiga yanzu.

“Ka yi hakuri da sun fito zaka ganshi”

Safa da marwa kawai jibril ya ke yana matsar hannunsa.

“Jini ma ake nema garin bada jinin ne Mahaifiyar yaron ta yi ta amai daman da kuka ta zo, sai gashi ta sume mana dole muka kaita sashem Balaraba, kakarsa taje ta siyo”

“Please Doc Ismail muje ka gwada nawa idan zai yi”

“Okay yaron ya ji ciwo sosai gaskiya ya zubar da jini, amman yaron ka ne ko naga kuna da kaman sosai kuma yadda ka tashi hankalinka haka...”

Be gama maganar ba Jibril ya rike shi

“Da gaske muna da kama? Da gaske?”

Ya gyada masa kai cike da mamaki, ko da suka karasa lab Jibril be sani ba saboda hankalinsa yana can gurin tunani. Sai da aka dibi jininsa kadan aka gwada ya bada result iri daya da na Noor sannan Doc Ismail ya kawo masa, Jibril na ganin takardar hawaye suka fara masa zuba jikinsa ya yi mugun sanye, sai da ya karantar result din ya fi a kirga sannan ya yarda da duniya yake, fashewa ya yi da kuka sai kuma ya yi saurin guntse bakinsa tunawa da inda yake, saman table ya aje takardar ya nufi wani bangare na lab din hannayensa a baya yana jin wani irin abu marar misaltuwa.

“Doc Jibril ko ka fasa bada jinin ne?”

Sai ya juyo da sauri ya dawo yana share hawaye abunda ya bawa kowa mamaki, sai dai su abunda suke dauka saboda yaron ya ji rauni sosai ne yake hawayen, har wasu na cewa wai kamar ba namiji ba namijin ma kuma likita wanda be kamata aga yana kuka saboda sun saba ganin tashin hankali.

Dakin da ake dibar jiki ya shiga ya kwanta a saman kujerar nan mai kamar gado, aka saka masa abun diban jinin aka tasti leda biyu sannan ya tashi yana fadin.

“Doc Ismail muje yanzu ko sun fito”

“No Doc kai kansa kasan dole ka dan zauna yanzu na ga kamar a hankalinka a tashe yake”

Tashi tsaye Jibril ya yi da zimmar tafiya, ganin hakan yasa Doc Ismail ya bishi suka koma gurin tare sai suka tarar ba a fito da shi ba har yanzu. Sai kawai suka zarce inda Nawwara take domin itama yana da bukatar ganinta, basu sha wahala wajen nemanta ba saboda farko farko take. Irin dakinnan ne da ake jera masara lafiya dama da hadu, tana kwance saman gadon asibiti idanuwanta a rufe kamar tana bachi ga drip an daura mata a hannu, Sakina na zaune a kujerar da ke kusa da ita tana ta hawaye. 
  Kallonta yake sosai cike da tausayinta a nan Sakina ita ta samu damar kallonsa a take ta raya a zuciyarta cewar tabbas wannan baban Noor ne domin kamar har ta ba ce.

Zaunawa ya yi gefen gado yana ta kallon fuskar Nawwara kamar yau ya fara ganinta, can kuma ya dago ya kalli Doc Ismail dake ta faman kallonsa da mamaki ya ce

“A sama mata daki inda zata zauna ita kadai ta samu kulawa, if babu zan so ka mata transfer zuwa asibitina”

“No nan din ma akwai”

Gurin Nurses din ya nufa ya yi magana da su sai suka zo suka canja mata daki zuwa wanda take ita kadai sai dai shi kudinsa da daban ne. A nan ma ya dade yana kallonta sannan ya cire rigarsa yar sama kasancewar suit ne a jikinsa ya lulluba mata saman jiki.

“Ki kula da ita please”

Ya ce da Sakina sai kace ita Nawwara wata karamar yarinya ce. Tare suka fito da Doc Ismail har suka hadu da wani likitan Jibril dai be bi ta kansa ba dan hankalinsa yana can gurin dan da aka ce na Nawwara ne. 
Sun yi sa'a suna isa ana fitowa da shi dakin tiyata, Sai Doc Ismail ya tsayar da su saboda abokinsa ya samu ganin yaron, mutuwar tsaye Jibril ya yi a gurin idanuwansa suka cika da kwalla kamar ba namiji ba, be ankaro da nauyin da kafafunsa suka yi ba har sai da ya daga kafarsa daya ya taka zuwa gurin gadon da Noor yake kwance.

Sama yake kasa yake duniya yake lahira yake? Sai ya kasa ganewa iyakar abunda idanuwansa suke kallo kamaninsa dake zuba a fuskar Noor, yasan ba mafarki yake ba kuma idanuwan ba gizo kuke masa ba, abunda yake gani zahiri dake shiga har cikin kwakwalwarsa, faduwa ya yi a gurin yana kuka muryarsa na karkarwa.

“This is my Son, ba ko tantama wannan da na ne, he's my Son jinina da na na cikina”

Hannu ya kai zai shafa fuskarsa da ke manne da bandeji sai yaji ya rike masa hannun cak....

Post a Comment for "RAI BIYU CHAPTER 14"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...