Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

RAI BIYU CHAPTER 13

RAI BIYU CHAPTER 13

- - Post a Comment
RAI BIYU

CHAPTER 13

Ina fitowa daga banɗaki na zauna saman tabarma da na tashi sai Noor ya miƙon wayata da ke hannunsa. 10

“Momy gashi an kira na ɗauka amman ba ayi magana ba”

Ina karɓar wayar na duba sai na ga number Jibril number nan ce da ya saba kirana da ita.

“Ka yi magana?”

“Ee amman ban ce ance komai ba, sai na ce idan kin zo zan faɗa miki sai na kashe”

“Na shiga uku Noor miyasa ka yi magana?”

Hankalina ya tashi sosai zuciyata na ta raya min Jibril zai gane cewar Noor ɗansa ne.

“Momy ban ce komai ba”

Ya faɗa ganin yadda duk na bi na rikice, kai na gyaɗa masa naja shi zuwa saman ƙafafuna na zaunar da shi na rumgumeshi, muna haka wayar ta ƙara ringing ina dubawa na ga Number Jibril sai na kashe wayar gaba ɗaya, gabana sai faɗuwa yake, zuciyata na nuna min Jibril zai uya zuwa gidan nan a yanzu ko anjima saboda ɗansa.
Unƙurawa na yi na tashi sai ga Jidda ta shigo bakinta ƙumshe da sallama, sai jikina ya ƙara yin sanyi har na ke ganin kamar ita ma tare take da Jibril.

“Noor tashi kaje ɗaki yi sauri”

Sai da ya gaisheta sannan ya tashi ya nufi ɗakin, ita kuma ta zauna kusa da ni tare da dafani.

“Ki kwantar da hankalinki ba zan cuceki ba, ba kuma za a haɗa baki da ni a cuceki ba”

“Idan har ni be cuceni ke zai cuce ki”

“Mustaphan da kika sani a baya ba shi ne a yanzu ba, Wallahi ya canja Nawwara kuma saboda ke ina ganin wannan kaɗai abun farincikine ace ta dalilinka wani ya shiryu”

Na gyara zamana ina kallonta da kyau.

“Bakin san waye Mustapha ba shiyasa kika wannan maganar, baki san iya ta'asar da ya yi ba shiyasa kike ganin kamar ya canja”

“Ya canja Nawwara ko ki yarda ko karki yarda Mustapha ya canja, ganin da kika mana tare yazo gurina ne saboda yana neman yafiyarki, yana son na taimaka masa na nema masa yafiyarki”

“Kin san abunda ya aikata min kuwa?”

“Shine mutumen da ya yi fyaɗe ya bata dubu ashirin ko? Ko ba wannan ba ne?”

Kallon mamaki na yi mata.

“Ya faɗa miki kenan?”

“Ya faɗa min komai saboda kawai yana neman yafiyarki, ki dubi girman Allah Nawwara ki yafe masa ko ya samu sassaucin rayuwa” 2

“Taya kika san tuban gaskiya ya yi? Maza suna yaudararmu Jidda saboda sun san mu mata muna raunin zuciya, sukan yi amfani da wannan damar su sake cutar da mu” 1

“Ba zai taɓa cutar da kr ba Nawwara, tun daga lokacin da kika taɓa marinsa ya ƙyaleki zuciyata ta raya min Mustapha son kin yake ko kuma son wani na ki, ya isa shaidar kirki cewar Mustapha tuban kirki ya yi tun da ya biyo ki har ƙofar gidanku ya nemi yafiyarki, idan har yana son cutar da ke ba zai taɓa neman yafiyarki ba, zai iya sakawa a ɗauko masa ke ya yi miki yadda ya ke so, zan iya dafa miki ƙur'ane cewar Mustapha tuban ƙwarai ya yi kuma ya yi nadama”

“Ba zan yafe masa ba da gangan mutun zai aikata abu sai kuma ya dawo neman yafiya, da ace be mata fyaɗe ba da bata samu ciki ba da duk be kaita ga halaka ba, da yanzu ƴar'uwata tana nan raye” 9

Na faɗa zuciyata na mugun ƙuna. Sai dai abunda ya fito daga bakin Jidda ya kusa ya ruɗar da ni ko kuma ma na ce haukatarda ni gaba ɗaya.

“Ashe jahila ce ke Nawwara, karatun addininki be amfaneki da komai ba, baki da imani ko kaɗan saboda baki yarda da ƙaddara ba, kuma bari na gyara miki kalamanki da ace yar'uwarki bata je ta kai kanta gunsa ba da be samu damar yi mata fyaɗen ba, kuma ko da Mustapha ko babu Mustapha dole Habiba zata mutu kuma dole sai wani ya yi mata fyaɗe kuma dole sai ta yi ciki saboda yana rubuce cikin kundin ƙaddararta, tirr da halinki Nawwara tirr zuciyar da bata yarda da ƙaddara marar kyau ba sai mai kyau, Allah ma muna masa laifi ya yafe mana balle ke da Allah zai cewa faɗi ki mutun kuma ki faɗin ki mutu dan dolenki, zuciyarki bata da kyau Nawwara saboda babu imani babu tausayi a cikinta, bawan Allah nan ko shi da hannunsa ya kashe Habiba ya kamata ki yafe masa tun da har yace miki ya tuba, balle fyaɗen da idan aka bincika daga shi har ita suna da laifi-!” 9

STORY CONTINUES BELOW


Tun da ya fara maganar na ke kallon yadda take dantsar baki tana faɗa min duk maganar da tazo daga bakinta idonta na hawaye kamar yadda nima nawa idanuwan suke hawaye, cikin muryar kuka na ce.

“Faɗa min nawa Mustapha ya biyaki Jidda? Dala dubu nawa ya biyaki da har tasa kika goya masa baya tsaɓanin aminiyarki? Da me ya siye zuciyarki har kika ƙoƙarin ɓata abotarmu?” 1

“Da imani da tausayi ya siye zuciyata, ni na yarda da ƙaddara a yayinda ke baki yarda da ita ba”

“Saboda baki dan yadda na ke ji ba Jidda, a gaban idona yar'uwata ra rasa ranta saboda wannan azzalumin”

“Na san yadda kike ji, amman na fi jin yadda Mustapha ya ke ji saboda ƙaddara ta faɗa kansa wacce bata wuce faɗawa kowa ba”

Tana kaiwa nan ta miƙe tsaye ta fice ta barni a gurin ina ta hawaye da mamakin kalamanta. Jin ana kiran sallah isha'i yasa na tashi na wanke fuskata na yi alwala a waje na yi sallah isha'i kamar yadda na yi ta magariba.
Bayan na gama addu'o'ina na tashi na nufi ɗakin Inna, ko da na shiga na tarar tana sha'u da wutiri Noor da Jamila kuma na saman gado suna mugun wasa, ƙasa na zauna kusa da ita ina jiran ta ƙare idona suna kan ɗana da ke ta sukuwa saman gadon.

“Noor bari mana gadon Inna zaka yi sukuwa”

Da sauri ya sauko sai ya nufo inda na ke yana faɗin.

“Momy zaki ara min wayarki na yi game ko?”

Sai a lokacin na tuna da na bar wayar a wajen da na zauna har na yi a zamar tashi na fita na ɗauko wayar cike da fargaba na kunnata ina shigowa ɗaki, zan miƙawa Noor naji ƙarar shigowar saƙo, hakan yasa na tsaya dubawa.

_Matiƙar baki dawo aiki gobe ba, wannan shegen saurayin na ki zamu sallameshi kuma try me_ 5

Ba shiri na zaro ido gabana ya shiga faɗuwa na furta shiga uku da kirama kaina hallaka.

“Na shiga uku na lalace”

Da sauri duk suka kalleni har Inna dake jan carbi.

“Miya faru?”

Kallonta na yi sai kuma na rasa ta yadda zan mata bayanin ga Noor da Jamila har Sakina duka idonsu a kaina, saurin goge saƙon na yi na miƙa masa wayar.

“Ungo je kayi game ɗin”

“Momy miya faru?”

“Ba komai kuje waje da Mama Jamila sai ku yi”

Yana karɓa sai suka yi waje ni kuma na zauna kusa da Inna idona cike da ƙwalla na kama hannunta na riƙe sai na kasa yin magana hawaye suka fara yin aikinsu.

“Nawwara mi yake damunki?”

Hannuna ɗaya na kai na share hawayena yayinda wasu ke ƙara zubo min.

“Inna ko na faɗa miki ba zaki fahimce ni ba, kuma fushi zaki yi da ni”

Nan take hankalinta ya tashi ta damƙe hannayena biyu tana kallon cikin idona.

“Me kika aikata har haka ne Nawwara? Abunda ƴar'uwarki ta aikata shi kika aikata kema?”

“A'a Inna Jibril ne”

Na faɗa ina sosa kaina hawaye na sauka a fuskata.

“Wane Jibril?”

“Baban Noor”

Da sauri Sakina ta tashi zaune daga kwancen da take tana kallona, Inna kuma ta saki baki. Ni kuma na rasa ta inda zan fara mata bayani.

“Kamfanin da na samu aiki ashe na Jibril ne, ni ma ban sani ba sai daga baya....”

STORY CONTINUES BELOW


Haka na bi na zana mata komai tun daga farko har ƙarshe ban ɓoye mata komai ba, har maganar siye gidan da kuma wannan saƙon da ya aiko min yanzu.
Lunshe ido ta yi ta jingina da gado tana sauke ajiyar zuciya.

“Miyasa kika ɓoye min wannan tun farko? Da ace kin shawarce ni da duk abun be kai haka ba, har yanzu baki san ƙima da matarba uwa ba ko? Wani na waje ya ji sirrinki mahaifiyarki bata sani ba? Akwai wanda ya cancanci ki yi sirrin da shi fiye da ni?”

“Ba haka ba ne Inna, kawai ina tunanin irin halin da zaki shiga ne idan na faɗa miki, wata ƙila ma ba zaki fahimce ni ba, kuma abun zai tsaya miki a rai ki riƙa tunanin wanda ni kuma ba zan so haka, Wallahi ban ɓoye miki da wata manufa ba bayan wannan”

“Ƴaƴan mazani kenan masu yarda da ƙawaye fiye da uwaye, masu yin gaban kansu waɗanda suke ganin kamar tasu zata fisshesu” 3

“Dan Allah Inna ki yi haƙuri”

Na faɗa ina kuka.

“Amman da gaske Jibril ya baki haƙuri kuma kika mare shi ya ƙyale ki”

Sakina ta tambaya, ni kuma na ɗaga mata kai.

“Idan har yafiyarki yake nema ba zai tsaya jiran ki kawo kanki ya nemi yafiyarki ba, sai dai na nemi inda kike ya zo ya baki haƙuri kuma ya nuna miki ya yi nadama”

Cewar Inna, ni kuma na ce.

“Bana ma son ya zo dan ba zan yafe masa ba”

“Allah ma aka masa laifi aka roƙi ya yafe balle ɗan'adam? Idan baki yafe masa ba ai kya bashi ɗansa idan ya zo karɓar abunsa”

“Haba Inna duk wulaƙancin da ya yi min ya ce ɗan nan ba nasa ba ne sai kuma na bashu Noor gaskiya ba zan iya ba”

“Akwai hujjar da ta zata hana ni ganin ɗansa ne?, idan har ya dawo ya buƙaci ɗansa ki bashi kawai shine masliha a gareki da kuma mu, ku bar shi da Allah Nawwara idan har kika yi haƙuri sai ki ga kyakkyawan sakamako daga gurin Allah amman matuƙar kika ce zaki rama abunda ya yi miki Allah zai iya barinki da dabararki a ƙarshe sai ki cuci kanki, amman idan har kika barshi da Allah sai ya saka miki.

Ma a son mace da irin zuciya da halinki Nawwara, duk da zata iya ɗaga hannunta ta mari namiji ta kuma tsaya ta ci masa mutunci akan abunda zata iya kawar da ido ana mata kallon marar tarbiya kuma marar mutunci da kamun kai, raunin zuciya tausayi kawaici kunya haƙuri abubuwa da aka fi samu sun gurin ƴa mace,
Na san Jibril ya zalinceki Nawwara, amman ki barshi da Allah karki yarda ki ce zaki ɗauki fansa wannan ba halin musulmin kirki ba ne” 6

Daker na iya tsayar da kuka da na ke har na furta.

“Ni ba zan iya yafe masa ba Inna” 5

“Ban ce ki yafe masa ba, amman ki bishi a hankali kuma ki yi taka tsantsan”

“Kuma ba zan bashi Noor ba be cancanci zama ubansa ba, ni ba zan iya yafe masa ba”

“Har gobe ina faɗa miki rufin asirinki ne idan har ya dawo ya nemi ɗansa, ni kuma ban ce ki yafe masa ba”

Sakina ta dawo kusa da mu tana faɗin

“Amman gaskiya idan har aka bashi Noor ya ci riba biyu”

“Ba riba ya ci ba, Wallahi ina da tabbacin Allah ba zai barshi hakan nan ba, wata ƙila ya jarrabeshi ko zai jarrabeshi nan gaba, duk ɗa ai ƴaƴan maza ne ba na mata ba, itama wani auren zatayi ta haifi wasu ƴaƴan, ni dai abunda na ke so da ke ki yi min alkawari zaki riƙe mutuncinki kar kuɗi da ƙyaliƙyalin duniya ya yaudari zuciyarki ya kaiki ga faɗawa halaka”

“Na miki alƙawari Inna ba zan sake sakaki hawaye ba”

“Allah ya miki albarka, ki je gurin aikinki ki koma kamar yadda ya buƙata, amman karki taɓa nuna masa saboda Bilal kika dawo, kar ki nunawa Bilal saboda shi kike aikin, ko wannensu ki nuna masa saboda kanki kike yi kuma zaki iya dainawa a ko wane lokaci, idan har kika bar aikin yanzu zai kori Bilal kamar yadda ya faɗa, wanda hakan zai jefaku ciki wani halin, kuma baki san ta wace hanyar zai ƙara ɓullo miki ba”

STORY CONTINUES BELOW


“Amman Inna ina ganin kamar yana son ya yi amfani da damarsa ne ya sake cutar da ni”

“Ba zai sake cutar da ke ba, waya sani ko saboda ke ya dawo garin nan da aiki? Wanda ma yake likita miya kawo shi aikin kamfanin? Baki taɓa tambayar kanki ba?”

Na yi shiru ina nazari, sai Sakina ta yi karaf ta ce

“Wata ƙila yasan ta samu aiki a kamfanin shiyasa ya zo”

Inna ta amsa mata.

“Nima haka na ke tunani, ƴaƴan manyan masu kuɗi basa ganin irinmu talakawa da mutunci, yana ganin kamar ƙasƙanci ne a gareshi yazo neman yafiyarkin kai tsaye, bana tantama shi ne ya aiko mana da ɓarayin nan kuma ya siye gidan nan saboda ki matsu ki koma aikin a kamfanin kamar yadda yake buƙuta ta yadda zai iya kyautata miki har ya nemi yafiyarki cikin sauƙi, da ace cutar da ke yake son yi da wata hanyar zai ɗauko ba wannan ba, kuma kin ga idan har yana da wata niyar ta daban akanki babu yadda za'ayi ya ki mareshi a bayanar jama'a ya ƙyaleki har ma ya risina ƙasa yana baki haƙuri, wannan saboda yana ganin bashi wata mafita sai ita ne shiyasa ya ɓullo miki ta hanyar Bilal” 3

“Amman ina tunanin be san da Noor ba ko?”

Sakina ta tambaya. Sai Inna ta amsa ta

“Ya san ya barki da ciki, sai dai be sani ba ɗan yana raye ko baya raye, wata ƙila ma yasa an masa bincike akan haka, amman ki yi tunani Nawwara dukan mutumen da ya yi miki wannan wulaƙanci yana kunyar ya tunkareki kai tsaye ya nemi yafiyarki, kuma ta hanyar aikin nan da zaki yi a ƙarƙashinsa zaki iya fahimtar irin rayuwar da ɗan ki zai yi idan har ya zauna gunsa, ke da shi duka ƙurciya da wauta tana cinku”

Shiru na yi ina ta nazarin maganganun Inna akwai hiƙima da kuma ƙamshin gaskiya a duk abunda ya faɗa, ni kaina na san da Jibril be yi nadama ban iya na masa irin wannan cin kashin a gaban ma'aikatansa ba, kuma babu dalilin da zai ya riƙa bibiyata har yana neman na dawo aiki.
Ajiyar zuciya na sauke nasa hannu ina share hawayena, Inna kuma tana amsa sallamar da almajiri yake yi.

“Assalamu alaikum wai ance ana sallama da Nawwara a waje”

Da fari gabana ya faɗi na fara tunanin mai min sallamar.

“Waye ne?”

Na tambaya a cikin muryata mai amon kuka a cikinta.

“Haka ya ce wai bawon Allah ne”

Zan ƙara tambayarsa sai ga Noor ya shigo da gudu ya miƙa min wayar.

“Momy ga Uncle Bilal ya ce na baki”

Ina karɓa na kara a kunne already Noor ya yi picking.

“Nawancy gani nan akan hanya”

“Ka ce ma ka iso”

Sai kawai ya yi dariya ya kashe wayar, jin haka yasa na ce da almajirin ya ce ina zuwa, wayar na miƙawa Noor ni kuma na tashi na je waje na wanke fuskata na shigo na shafa mai sannan na saka Hijabi na fita.

Mustapha na tarar ƙofar gida sanye da jallabiya yana kallon ƙofar gidan, waigawa na yi gabas na duba yamma ban ga mai kirana ba hakan ya tabbatar min da cewar shi ne yaƙe kirana.

“Miya kawo ka nan kuma? Kamin nan dai bari na fara taya ka murna ka yi nasarar haɗa ni da ƙawata ta faɗa min har abunda ban zaci zata iya faɗa min ba, burinka ya cika”

“Ba burina kenan ba, burina ki yarda na tuba kuma ki yafe min”

“Akwai aiki a gabanka babba Mustapha, yafiyar Ubangiji ta fi cancanta ka nema ba tawa ba”

Sai ya kirana sunana a hankali.

“Nawwara idan na kai kaina kotu aka min hukunci zaki tafe min?”

“Allah ya rufa maka asiri karka tonawa kanka”

“Ina ma ace zan iya raba zuciyata biyu ki karanta ki ga abunda yake raina”

“Kasan zaka nemi yafiya ka aikata?”

“Ƙaddarata ce ta zo a haka, an rubutoni a cikin ƙaddarar Habiba kamar yadda aka rubutoki a cikin ƙaddararta, Wallahi da nasan Allah zai jarrabe ni da sonki da ban yarda ba kalli Habiba balle har wani abu ya shiga tsakanina da ita” 1

Ya faɗa yana ƙwalla, har na buɗe baki na sake masa wata maganar sai na hango Bilal tafe, sai na tattarahankalina na maida gurinsa gudun kar ya zargi wani abu, hakan yasa Mustapha waigaya ya kalleshi.
Tsayawa Bilal ya yi cak sai kawai ya ɗago min hannu daga can inda yake ya juya ya koma. 2

“Ka gani ko? Ka hana masoyi ya ƙaraso kusa da ni”

Na faɗa a tsawace.

“Yi haƙuri” 2

Sai ya yi saurin juyawa ya bar gurin cikin sauri, na daɗe tsaye bakin ƙofar wai ko zan hango Bilal ya dawo amman har na gaji ban dawo ba hakan yasa na juya na koma cikin gida raina a jagule.Be taɓa tattabar da cewa yana son Nawwara ba sai yanzu, wani irin abun yake jin yana dibarsa masar misaltuwa, kalamar da ta furta ga waninsa na masoyin da ta kira Bilal yake jin kamar ace shi ne.

Kai tsaye ya wuce part ɗinsa sai ya kwanta rairai ƙasan carpet ya lumshe idonsa, babu abunda yake tunani sai halin rayuwar da ya jefa kansa, da ace be kasance mazina ci ba da babu abunda zai hana Nawwara ta so shi, tunani yake abunda zai faɗawa Allah idan har ya mutu a yau ba tare da ya tuba, son nawwara yasan jarabawace Allah ya ɗoro masa gashi tana da ɗawainiya da shi ta hanashi sukuniina ga ya mutu? Tabbas zai yi ƙoƙarin juye rashin Nawwara amman azabar Allah fa zai iya jureta? Wacan azabar da za'ayi ma mazinata ba da irin wannan jarabawar ba ce da wuta mai kamar kunu za a ƙona fatarsa bayan azabar da za a gada masa cikin ƙabari.

Buɗe ido ya yi sai ya ɗaga hannunsa sama yana kallon farar fatar hannunsa, sai ga hawaye sun gangaro daga idanuwa zuwa gefen kuncinsa, unƙurawa ya yi da zimmar tashi zuwa alwala ya yi sallah ya ƙara nemi yafiyar Ubangijinsa, sai dai hango Mahaifiyarsa da yayi jikin ƙofa tana kallonsa tana hawaye yasa shi yin zaune tana share nasa hawayen.

Ƙarasowa ta yi kusa da shi ta zauna kana ta riƙa hannunsa tana kallon fuskar ɗanta cike da tausayinsa.

“Son kuka kake yi?”

Ya yi shiru be ce komai ba.

“Zan je na nema maka yafiyarta, in har hakan zai faranta maka rai, damuwarka damuwata ce a duniyar nan bana da wani farinciki sai naka, amman ina son ka sani ba kai ne ka kashe yarinyar nan ba” 3

“Ba ni na kasheta ba Mom na sani, amman ina jin rashin kyautawa a abunda na aikata, sannan Allah ya jarabeni da abunda ban taɓa tsamani ba, son yayarta, kuma kun kasa fahimtar hakan balle ku goya min baya”

“Na yi magana da mahaifinka zamu nema maka yafiyar Nawwara, da kuma aurenta matuƙar hakan zai kwantar maka da hankali” 2

Ya yi saurin kallonta kamar be yarda ba.

“Mom da gaske?”

“Kai kaɗai na ke da a duniyar idan ban faranta maka ba wa zan farantawa? Bana son na rasa ka”

Ya kwantar da kansa jikinta yana murmushi tare da sauke ajiyar zuciya.

“Thank you so much Mom i love you”

“Love you more”

Ta faɗa tana hawaye, har ga Allah ba dan tana son nawwara zata nema masa ita ba sai dan kawai ɗanta ya samu salama hankalinsa ya kwanta, amman ita har gobe gani take ɗanta be dace da nata kamar Nawwara ba. 2

Sun daɗe a haka sannan ta sake shi ta fita shi kuma ya shiga banɗaku dake falon ya wanke fuskarsa ya canja Jalabiyar da ke jikinsa ya zuwa wata jalabiyar black sannan ya fito a compound ya nufi gurin da motarsa take ya shiga horn ɗaya mai gadin ya buɗe masa gate ya ɗauki hanyar gidansu Jidda.

Tun kamin ya ƙarasa ya kirata ya faɗa mata ta fito gashi ƙofar gida, sam ba zaka ganshi a yanzu ka ce mutumen ɗazu ne ba, farinciki ya mamaye masa zuciya ji yake kamar da Momy taje ta bawa Nawwara haƙuri haƙura zata yi ta kulashi.
Yana zaune cikin motar har Jidda ta fito sanye da Hijab tana tafiya kamar marar laƙƙa, jinginawa ta yi jikin motar yana miƙa masa gaisuwa shi kuma sai ya kashe motar ya fito yana murmushi.
Gabanta ya faɗi zuciyarta ta fara bata wani tunani na daban kar dai ya cutar da ƙawarta, mutumen da tasan yana cikin damuwa yanzu kuma har da murmushi a fuskarsa. 1

“Naje na yi magana da Nawwara amman har yanzu bata fahinta ba, har na faɗa mata maganar da be kamata ba, amman na san nan gaba zata gane kuma zata yafe maka ni dai abunda na ke fata karka cutar da ita dan Allah”

STORY CONTINUES BELOW


Ya sake yin murmushi yana kallonta fuskarsa da annuri.

“Zan iya cutar da kaina ban cutar da Nawwara ba, da kin san yadda na ke sonta da baki min wannan zargin ba, amman na san duk mutumen da yasan wanene dole zai zargeni, faruncikin da kika gani a fuskata na zo ne na faɗa min cewar Mom ta yarda har ma ta ce zata taimaka min wajen neman yafiyar Nawwara” 1

“Wow amman na yi farinciki, Allah ya shiga cikin lamarin kuma ya sa ta kula ka”

“Amin nima fatana nan”

Ya faɗa yana kallon hawayen da suka zubo mata, wanda hakan yasa shi wani tunanin na daban. 1

“Hawaye kike?”

“Ni?”

Ta yi saurin kai hannu ta share hawayen, da alama bata san sun zubo mata ba. 1

“Kawai ina farinciki ne”

Ya mata murmushi as respond ba dan ya gamsu hawayen nata na farinciki bane, ita kanta bata san hawayen mi take ba, iya abunda ta sani zuciyarta na yaudararta ne da son cuta mata abunda ta san ba zai taɓa yayuwa ba.

‘i'm very stupid taya zan so mutunen da ke son ƙawata?’ 1

A fili kuma sai ta kalli Mustapha ta ce

“Zan shiga ciki”

Nan ma kai ya ɗaga mata yana murmushi da iya fatar baki kawai ya tsaya masa. Har ta juya sai ya kirata.

“Jidda...”

Ta juyo tana kallonsa

“Thank you”

“Anything for Nawwara”

Sai da ta shiga gida sannan ya juya ya shiga motarsa zuciyarsa na raya masa wani abu da baya son kawowa akansa, he's happy at first amman yanzu sai ya nemi farincikin ya rasa tunanin hawayen da Jidda take ya tsaya masa a rai. 2

Ko da ya isa gida part ɗin Mom ya fara shiga sai dai be sameta ba saboda bata gidan, Ikram ce kawai a falon tana game, yana shigowa hankalinta ya dawo kansa. 1

“Mom taje zata yi magana da Nawwara abunda ka daɗe kana jira amman kuma sai naga kamar baka farinciki”

Ya kalleta irin kallon nan na sai yanzu ya lura da maganar da take.

“Ofcourse am happy i was just thinking of something else”

“Like?”

Sai yayi murmushin da ya bayyana haƙoransa ya miƙe ya shiga kitchen yana faɗin 1

“Manta kawai ba wani abu bane mai muhimmaci”

Freezer ya buɗe ya ɗauko gorar ruwa ya kai a bakinsa ya sha sai kuma ya nufi gurin window yana ta tunani.

“Impossible”

Ya sake cika bakinsa da ruwa, sai kuma ya yi murmushi yana sauke ajiyar zuciya.

“I love you so much”

Ya daɗe a kitchen ɗin sai da yaji motsin shigowar Mom sannan ya juyo ya fito riƙe da gorar ruwan ya nufo falo.

“Mom ya kuka yi?”

Ya tambaya tun kamin ta cire mayafin da ke kanta, sai dai bata bashi amsa ba sai da ta zauna saman kujera fuskarta da murmushi.

“Sun ce ba zasu yafe ba” 1

“You must be joking Mom”

“Ka ci gidanku, ni zan maka wasa”

Ya zauna kusa da ita yana kallon murmushin da ke fuskarta.

STORY CONTINUES BELOW


“Na yi magana da su kuma sun ce sun yafe maka, baka ga yadda mahaifiyarta ta tarbeni ba kamar daman can babu komai”

“Da gaske? Amman Nawwara fa?”

Ta ɗanyi shiru sannan ta ce

“Ita ma ta yafe maka har ma tace a gaisheka” 1

“Mom da gaske”

“Sai kaje ka tambaya idan baka yarda ba”

Wani irin tsalle ya yi ya dare kamar mahaukaci.

“Mom i love you so much”

Mom ma tana farinciki ganin farincikin ɗanta, cikin zumuɗi ya fice daga falon ya nufi part ɗinsa. A ranar kasa bachi ya yi saboda farinciki, sai ya kwana yana istigifari da hamdala ga Ubangijinsa, a zatonsa da gaske Nawwara ta yafe masa har ma ta miƙo gaisuwar gunsa.
Around eight o'clock in the morning Mustapha ya fito part ɗinsa zuwa part ɗin Mom, sai dai hango motar abokinsa da ya yi yasa shi tsayawa baƙin ƙofar yana jiran ya ƙaraso.

NAWWARA POV.

Cikin rashin daɗin rai na shiga gida, Inna ma ta lura da haka sai dai bata cemin komai a zatonta tsakanina da Bilal ne wani abu ya faru. Misalin takwas da rabi na dare muka ji sallama a ƙofar gida, Inna ce ta amsa ni kuna idona na kan Noor take ta faman game baya gajiya. Sarai muryar Hajiya mahaifiyar Mustapha a ɗaki kunnena a sallamarsa ta biyu, gabana ya faɗi ba dan tsoro ba sai dan tunanin abunda yake tafe da ita. Inna ce ta unƙura ta fita sai kuma ta dawo ta ɗauki tabarma ta sake fita, sama sama nake jiyo firar da suke da dukan alamu yafiya take nemawa ɗanta abun mamaki har da su wa'azi da nuna ƙaddara, zuwa can kuma dai na ji Inna ta kirani daga inda na ke na amsa mata sannan ya miƙe na fita. 1

Hajiyar ce zaune saman tabarma yayinda Inna take zaune saman kujerar mata ta tsakar gida.

“Nawwara ce”

Hajiyar ta faɗa tare da kunna fitilar wayarta ta haska fuskata. 1

“Ina wuni?”

“Lafiya ƙalau, ayi ta haƙuri kinji haka abubuwan duniya suke zuwa” 1

“Allah ya bamu haƙuri”

Daga haka ban ƙara cewa komai ba na miƙe tsaye na dawo ɗaki. Bata ɗauki tsawon lokaci ba tayi ma Inna sallama ta fice. Inna kamar jira take tana shigowa cikin ɗaki ta hau ni da masifa.

“Wannan halin ba na ki ba ne Nawwara ba irin wannan tarbiyar muka baki ba, yafiya da afuwa ga wanda ya yi maka ba daidai shu aka fi ga musulmi, duk yadda zaki so Habiba ko ki nuna baƙincikinki akan mutuwarta be kai ni uwarta, tun da har na yafe kema ya cancancanta ki yafe, Ƙaddarace ni da ke duk ba mu wuce faɗawa a cikinta ba, yanzu da ace ɗan uwanki ne ya faɗa a wannan halin ko kuma ɗan ki Noor yaje yana neman yafiyar wata ba ta yafe masa ba zaki jidaɗi? Komai zaka yi ka riƙa kwatantawa da kanka”

Tun da take maganar na ke hawaye, Inna ta min fahimta baibai, ta kasa gane irin zafin da ɓakincikin rashin yar'uwata da nake, ko da Habiba tana raye dole na ƙyamaci Mustapha saboda ya yaga mata rigar mutunci, tana ɗora min laifi akan Jibril saboda tana ganin kamar na zufafa da yawa, ni kou na san irin zafin da na ke ji idan na tuna wulaƙancin da ya yi min ya yi min ƙazafin zina a gaban iyayensa da iyayana yasa mutane unguwa suka kira ɗa na da shege ni kuma aka kira da karuwa, irin waɗannan mutanen ne take ganin na zufafa ƙiyayyata a garesu? 3

“Ki yi haƙuri Inna, zan yi iya abunda zan iya na danne zuciya daga abunda take ji, dan Allah ki yi haƙuri kuma ki roƙa min Allah ya sassauta min abunda nake ji”

Na faɗa ina ta kuka kamar zan haɗiye zuciya na mutu, sai Inna ta zauna kusa da ni ta dafani tana lallashina. 1

Sama sama na samu bachi a daren ranar saboda kuka da na kwana ina yi ga kuma tunani ƴar uwata da ya dawo min sabo. Washe gari da wuri na farko bayan na gama raka'atayal fajir sai na jira aka tayar da sallah na masallaccin da ke kusa da mu bayan na gama na karanta azkar na safe, da ayatul kursiyu na fara

STORY CONTINUES BELOW


A 'oothu billaahi minash-Shaytaanir-rajeem. Allaahu laa 'ilaaha 'illaa Huwal-Hayyul-Qayyoom, laa ta'khuthuhu sinatun wa laa nawm, lahu maa fis-samaawaati wa maa fil-'ardh, man thai-lathee yashfa'u 'indahu 'illaa bi'ithnih, ya'lamu maa bayna 'aydeehim wa maa khalfahum, wa laa yuheetoona bishay'im-min 'ilmihi 'illaa bimaa shaa'a, wasi'a kursiyyuhus samaawaati wal'ardh, wa laa ya'ooduhu hifdhuhumaa, wa Huwal- 'Aliyyul- 'Adheem.

sannan ɗora da ƙula'uzai

Allahu ahad, Allahu assamad, Lam yalid walam yoolad, Walam yakun lahu kufuwan ahad.

Qul a'aoothu birabbi alfalaq, Min sharri ma khalaq, Wamin sharri ghasiqin ithawaqab, Wamin sharri annaffathatifee al'uqad, Wamin sharri hasidin itha hasad.

Qul a'aoothu birabbi annas, Maliki annas, Min sharri alwaswasi alkhannas, Allathee yuwaswisu fee sudoori annas, Mina aljinnati wannas.

Sai kuma na karanta hasbiya ƙara bakwai

Hasbiyallaahu laa 'ilaaha 'illaa
Huwa 'alayhi tawakkaltu wa Huwa Rabbul-'Arshil-'Adheem

Sai kuma na karanta

Bismillaahil-lathee laa yadhurru ma'as-mihi shay'un fil-'ardhi wa laa fis-samaa'i wa Huwas-Samee 'ul- 'Aleem.
Ƙafa uku.

A'oothu bikalimaatil-laahit-taammaati min sharri maa khalaqa
Sau uku

Waɗannan addu'o'i ne na neman tsari matuƙar ka karantasu babu abunda zai same ka daga iska har tsafi har ma da wasu ƙwari masu cutarwa, bayan na gama na ɗora da azkar ɗin godiya ga Allah waɗanda ake son musulmi ya karanta safe da yamma. Sannan na rufe da shugabar istigifari wato

Allaahumma 'Anta Rabbee laa 'ilaaha 'illaa 'Anta, khalaqtanee wa 'anaa 'abduka, wa 'anaa 'alaa 'ahdika wa wa'dika mas-tata'tu, 'a'oothu bika min sharri maa sana'tu, 'aboo'u laka bini'matika 'alayya, wa 'aboo'u bithanbee faghfir lee fa'innahu laa yaghfiruth-thunooba 'illaa 'Anta.

Yana na gama na yi salatin annabi ɗari istigari ba ɗari, sannan na yi hasbiyalahu sau ɗari huɗu da hansi, wacce ake karantawa a duk lokacin da mutane yake cikin matsala na halin rayuwa ko neman mafita, kamar neman aure warwarewa al'amura duk ka lamuncin karantawa zaka samu mafita cikin gaggawa. 1

Ko da na fito har Sakina ta dama kamu, Inna kuma ta aiki Jamila da Noor su siyo ƙosai da suga, bayan sun dawo muka sha kunun har Inna sannan na kama kan Noor na yi mas addu'a irin wacce Annabi yake yi ma jikokinsa Hasan da Husaini

U'eethukumaa bikalimaatil-laahit-taammati min kulli shaytaanin wa haammatin, wa min kulli 'aynin laammatin.

Bayan na gama da Noor na karantawa Jamila sannan na suka kama hanyar makaranta tare da Sakina. Ni kuma na tashi na shirya cikin wata atamfar roba na saka Hijab ɗina mai kama da atamfata, sannan na zo yi ma Inna sallama da karɓar kuɗin Napep.

“Inna zan tafi aikin”

“Allah ya tsare Nawwara Allah ya miki albarka, ban miki faɗa jiya dan wani abun ba sai dan ki gyara”

Ta faɗa tana miƙo min ɗari biyu.

“Ko babu komai kika min faɗa ba zanga laifinki ke uwace kina da damar ki yi duk yadda kike so da ni, kuma abunda kika min faɗa akai kina da gaskiya, ni kaina na san ina da buƙatar ganin na canja ta yadda zan cigaba da rayuwa na manta komai, ni dai fatana ki kasance mai min addua da kuma haƙuri da hali na miki alƙwarin zan canja”

“Addu'a ai wajibi ce ga dukan uwa ta yi ma ƴaƴanta, Allah ya miki albarka ya baki miji na gari wanda zaki ji daɗin zama mai son ki tsakani da Allah”

“Amin Inna”

Na faɗa ƙasan zuciyata na ta kira min Bilal, tun jiya be kirani ba kuma be dawo ba ni kuma ban kira ba.
Sai da na fito daga gidan sannan na soma kiran Bilal amman wayarsa a kashe, hakan yasa ni jin babu daɗi zuciyata na raya min kamar fushi yake da ni, daman na san dole sai ya zargi wani abu ganina tare da Mustapha.

STORY CONTINUES BELOW


Na yi sa'ar samun napep da wuri amman sai da ya sauke mutun biyu sannan ya ƙarasa da ni inda zai kai ni, koda na isa tara saura kwata tunda na doshi kamfanin zuciyata ta soma rayamin wasu abubuwan sai sai tunawa da maganganun Inna yasa na kawar da komai na nutsa kai cikin kamfanin, na yi mamakin yadda kowa yake kallona kamar wace suka ga baƙuwar fuska, wataƙila an faɗa musu wani abun ne akai na ko kuma dan na yi latti suke kallona oho, ban damu da cire Hijabina ba a ganina yanzu ai an canja min aiki dan haka bana buƙatar cire Hijabi duk kuwa da kasancewar ban taɓa ganin kowa da Hijabi ba a kamfanin.
Har na doshi lifter tunani na ke irin kallon da Jibril zai min da kuma irin wanda zan yi masa idan har na yi aiki a gurin. Ina dosar office ɗinsa gabana ya shiga faɗuwa, ba faɗuwar tsoro ba ko fargaba ba faɗuwa irin ta maƙiyi zai yi arba da maƙiyinsa. 
  Kamar wacan zuwan nawa na farko haka na yi saka buɗe min, yau ma sai da aka tantance ni a cikin ɗan ƙaramin gilashin nan mai bayyana komai na jikin mutun sannan aka bani damar shiga Office ɗin, ban ji ya ce na aje wayata da ƴar ƙaramar jikar da ke hannuna ba, ni kuma ban aje ba na shiga da abu ta, shi ɗin ne dai mutumen da na taɓa tararwa wacan karon.  Tun kamin na yi magana ya rigani.

“Please go in”

Ya doshi ƙofar da ya nuna min gabana na ƙara faɗuwa, ajiyar zuciya na sauke sannan na kai hannu ya tura ƙofar, ba tare da na waigo ba na maida ƙofar na rufe ina kallon bayansa, kasancewar ya bani bayana ne domin shi yana tsaye ne jikin window ya maido hannayensa baya yana kallon waje.

Har yanzu akwai tattoo ɗin taurari a bayansa, mamaki ya kamani sosai ganin sunana rubuce cikin style ɗin wasu harufa tattoo a hannunsa, nasan be san da shigowata ba ko da yake yaji an buɗe ƙofa, ni kuma na gagara kiran sunansa sai kawai na ce

“Excuse me”

Da sauri ya juyo ya kalleni, irin kallon nan na mamaki sannan ya yi hanzarin warware hannun rigarsa ya nufi ƙasaitacciyar kujerarsa ya zauna.

“Kin zo latti, ba a faɗa miki 8am zaki riƙa zuwa ba?”

Na yi shiru ban amsa masa ba. Sai ya soma kallona daga sama zuwa ƙasa.

“Ba a saka mana Hijabi a nan next time ki san irin tufafin da zaki saka”

“Ba za'a saka muku Hijab ba saboda ku ba musulmai ba ne?”

Ya yi murmushin gefen fuska sai ya taso daga inda yake ya doso ni yana faɗin.

“Aiki muke a nan ba addini ba”

“Da wannan aƙidar ka cuci kanka, kai kana ganin kamar babu ruwan addini ko Allah a cikin abunda ya shafi aikinka ko rayuwarka ko? Kana da mummunar aƙida Jibril”

“Ko?”

Ya tambaya yana ta matsowa kusa da ni ni kuma ina matsawa baya, har sai da na kai jikin ginin ɗaki, sosai ya matse ni yana kallon fuskata idanuwa cikin nasa idon, har na buɗe baki na yi magana sai ya duƙa ya kama zanen atamfata ya murja.

“Me kake ƙoƙarin yi ne?”

Ya miƙe tsaye bakinsa kusa da nawa kamar zai haɗe bakinmu.

“Dirty mind, ni ba ɗan iska ba ne”

Ya faɗa kaɗan kaɗan kamar mai raɗa, sannan juya ya doshi kujerarsa. Hakan ya bani damar lumshe ido na sauke ajiyar zuciya, jin abunda yake faɗa yasa ni buɗe idon ina kallon yadda ya haƙimce saman kujerarsa mai juyawa yana min magana cikin isa.

“Dan me za ki saka min tamfar roba?” 1

“Ba kai na sakawa ba, kaina na sakawa” 1

“Miyasa kika yi rejecting kuɗin da aka baki ki siye wasu tufafi?” 1

“Bana da buƙata, tufafin jikina sun isheni”

“Saka ƙananan tufafi marar daraja na zubarwa kamfanin da ƙima, ya kamata ki san wannan” 1

Ya faɗa fuskarsa babu alamun dariya, sannan ya danna telephone ɗin da ke kusa da shi ya yi magana da halshen nasara.

“You can go now”

Sannan ya kalleni.

“Tea please”

Tsaye na yi a gurin kamar an dasani, shi kuma ya bawa banza ajiyata yana ta aiki da system ɗin da ke gabansa. Waige-waige ɓa farayi har na hango teburin dake ɗauke da kayan tea na doshi gurin zuciyata na ta raya min maganar ɗazu, wai shi ba ɗan iska ba ne, wato ni ce ƴar iskar ko? Har na haɗa tea ya kawo masa maganar bata daina min yawo a kunne ba.

“Ƙarfe uku zaki tashi aiki, idan kuma har muna da meeting ko aiki da yawa zaki iya kaiwa har dare, kuma a shigo min office haka nan kawai, saboda karki tararda ni cikin wani yanayi, har sai idan ni na kiraki, idan wata magana ce akwai telephone a gurin dannawa kawai zaki yi ki kirani” 1

Ban ce masa komai ba na juya na fita, zuciyata na mugun ƙuna, anya zan iya jurewa na yi aiki a ƙarƙashin Jibril? 1

Sai da na ƙarewa office ɗin kallon sannan na zauna a saman kujerar mai juyawa, komai daki daki na bishi ina kallon da dubawa sannan na kula da ƴar danjar da ke ƙara a gefen teburina, sai kuma computer ta soma nuna min mutumen da ke waje, wato Bilal yana riƙe da wasu takardu. 
   Gabana ya faɗi sosai sai na soma tunani da wace fuskar zan kalli Bilal shi kuma wane irin tunani zai min.? 1

JIBRIL POV.

He's just can't believe Nawwara tana ƙarƙashinsa a yanzu, wani irin daɗi yake ji yana ta yi ma Allah hamdalla, cike da so da ƙauna yake kurɓa tea da ta haɗa masa yana wani lumshe ido. 
  Jin ya yi ba zai iya jure jin wannan farincikin shi kaɗai ba, ya ɗauki wayarsa ya danna number Siraj dan labarta masa.Ba ni da wani zaɓi face na bashi damar shiga, domin nasan komai dare daɗewa dole zai sani. Kamar yadda Rabi ta nuna a wacan karo haka na danna sai ƙofar ta buɗe masa, a ta biyu mai gilashi muka riƙa kallon kallo ni da shi. Ƴar ƙaramar danjar sai tsuwa take tana nuna min agogon hannunsa da pose ɗin kuɗinsa sai kuma takardun da ke hannunsa. 
Ban damu da ce masa ya aje ba na sake dannawa ta buɗe ya shigo yana ta kallona kamar wanda be sanni ba. Hanzarin miƙewa na yi tsaye Cikin yanayin damuwa na zan masa magana sai ya rigani

“Takardun nan zaki kai wa oga ya saka hannu”

“Na yi ta kiran wayarka ban samu ba, miyasa ka kashe wayar”

“Zamu yi maganar anjima let's do this now”

Yawun bakina na haɗe kana na ɗaga masa kai sannan na karɓi takardun kai tsaye na nufi office ɗin Jibril duk kuwa da kasancewar ya yi min gargaɗi ɗazu akan na daina shigowa ba noticing, waya na tarar yana yi fuskarsa shimfiɗe da farinciki tea da na haɗa masa yana hannunsa sai kurɓa yake, yana ganina sai ya yayi hanzarin yanke wayar ya kalleni, sai dai be ce min komai ba jira yake ni na fara masa magana.

“Hannu zaka saka a waɗannan takardun Bilal ne ya kawo”

Na faɗa kamar mai shirin yin kuka, domin har ga Allah ban jidaɗin yadda na ga fuskar Bilal kamar baya cikin farinciki. Saman tebur na aje masa takardu sai ya duba ya saka hannu sannan ya miƙa min. Ni kuma na karɓa na juyo jiki ba gwari na miƙawa Bilal takardun sai ya karɓa yana faɗin

“Congratulations”

Ni dai ban ce masa komai ba har ya juya ya isa gurin ƙofar sai ta buɗe masa da kanta ya fice. Faɗuwa na yi saman kujera da ke kusa da ƙofar ta zaman baƙi ina sauke ajiyar zuciya, har ga Allah na san dole ne sai Bilal ya zargeni amman ta yarda zan fahimtar da shi ne aiki tasowa na yi na dawo saman saman kujera ko kuma na ce kujerar office ɗin na zauna zuciyata a jagule, ina ta tunani mafita sai bachi ɓarawo ya yi gaba da ni.

Babu komai a mafarkina sai Jidda da Mustapha, wai ya mata fyaɗe kuma ya kasheta ga ƴan sanda da mutane cike a gidansu, ni kuma sai aikin kuka na ke ina kiran Mustapha, abunda ban sani ba ashe har a fili na ke kiran sunansa.

“Mustapha...”

Abunda na furta kenan daga farkowatawa, sai na ga Jibril tsaye a kaina yana kallona, hakan yasa ni saurin zabura na tashi.

“Me zaka min?”

“Me kike tunanin zan miki? Mayaudariya kina spn Mustapha kina yaudarar Bilal ko?” 1

“Ina ruwanka babu ruwanka da rayuwata”

Sai ya mire baki tare da ɗaga kafaɗunsa sama alamar abun be dame shi ba.

“Tashi muje meeting, baki da aiki sai bachi abunda ya kamata ace ke zaki faɗa min lokacin meeting ɗin ya yi amman wani ne daga can waje yake sanar da ni”

Na tashi tsaye idona kan agogon office ɗin da ke nuna ƙarfe goma sha ɗaya na safe, shi ya fara fita ni kuma ina binsa a baya har muka shiga Lifter, a nan ya miƙa min ƙaramar jakar da ke hannunsa.

“Kin duba akan me zamu yi meeting ɗin?”

Na girgiza kai alamar ban sani ba, sai kawai ta cigaba da kallona ko kunya baya ji, ni kuma na yi kamar ban ganshi ina ta kallon numbobin lifter, sai dai haka be sa ya ɗauke idonsa daga kallon da yake min ba har lifter ta tsaya a hawa na uku ta buɗe da kanta, sai na yi saurin fita duk da ban san inda zamu shiga ba, sannan shi ma ya fito sai ga Rabi ta tare mu ta karɓi layin wayata wai zaa saka min numbobin ƴan ƙamfanin ta yadda zan gane duk wanda ya kirani.

Ko da muka shiga ɗakin taron mun tarar da mutum biyar wannna abokin nasa Siraj sai kuma Zinatu da wasu ɓakin fuska uku, yana shigowa duk suka miƙe tsaye ya miƙa ma baƙin fuskar hannunsa suka gaisa sannan ya gabatar musu da ni. 
  Ɗaya daga cikinsu ne wanda na ke zaton ba musulmi ba ne ya miƙo min hannu dan mu gaisa yana faɗin sunansa.

STORY CONTINUES BELOW


“Divid Sam”

Sai Jibril ya yi saurin miƙa masa na sa hannun a ƙaro na biyu, ya kuma amsa masa kamar ni ɗin.

“Nawwara”

Ni kuma na zauna a kujerar da ya nuna min, ban maida hankalina kan abunda suke tattaunawa ba, sai dai hakan be hanani fahimtar cewa wani kamfanine yake son siye, har aka yi meeting ɗin aka gama Siraj da Zinatu idonsu na kaina duk wani motsi da nake suna kallona har na soma jin babu daɗi.

Tare muka fito daga ɗakin taron sai ya koma daga bayana yana kallon tafiyata, hakan yasa ni ƙara sauri na shiga tifter, sai da tana daf da rufewa sannan ya ƙaraso ya shigo, still yanzu ma idonsa na kai, da alama dai kallona daɗi yake masa, ko kuma yana min ne dan kawai na tsargu, sau ɗaya na ɗago na kalleshi sai yayi min kwarjini sosai na yi saurin sadda kaina ƙasa ban sake kallonsa ba har Lifter ta sauke mu a hawa na biyar, har na miƙa jiki na fita sai ya riga fita. 1

“Baki iya competition da ni”

Ya furta daidai lokacin da zai fice, a nan na kalli bayan kansa sannan na fito muka doshi office ɗin, da fari na tsaya tunanin wa zai buɗe mana tun da ba mu bar kowa a ciki ba, muna isa sai kawai naga wata ƙaramar na'ura tana ɗaukar fuskarsa, sai ƙofar ta buɗe masa ya shiga, ina zuwa na shiga sai wani jan layi ya shata yana ta ƙara.

“Ki tsaya a nan karki raunata kanki, ba zaki iya shiga yanzu ba saboda bata tantance fuskarki ba”

Bayan ya shiga ciki da kamar minti biyu sai ƙofar ta buɗe min. Ina shiga ya jawo ni gaban computer ta ɗauki hotona ya saka sunana sannan ya juya ya shige Office ɗinsa. 
Ina zaunawa idanuwa suka kai kan agogon Office ɗin na ga ɗaya da kwata, lokacin Sallah azahar ya yi, wata ƙofar da ke cikin Office ɗin na nufa ina taɓawa sai ta soma ƙara tana nuna min na saka password, ta biyu kuma ina turawa na ga toilet, daman shi na ke nema, alwala na yi na fito na d8ba ko'ina na gurin babu carpet ɗin Sallah sai na shimfiɗa ɗankwalina na yi dashi bayan na gama, na nufi Office ɗinsa dan tunatar da shi lokacin Sallah ya yi.

Zaune na sameshi yana ta aiki a system ɗinsa, kamar jira yake na shigo mayun idanuwansa suka dawo kaina har na ƙaraso kusa da teburinsa.

“Lokacin Sallah ya yi”

Iskarka bakinsa ya busar sannan ya kalli tsadadden agogon hannunsa.

“Idan na gama aikin nan zan yi”

“Har sai ka gama aikin? Jibril mi ka ɗauki sallah ne? Sallah ita ce rukuni na biyu daga cikin rukunan addinin musulunci, kuma ita ce gimshiken addinin musulunci. Barinta kafirci ne da yake fitar da mutun daga cikin addini, babu addini babu musulunci ga wanda ya bar sallah namiji ko mace!”

“Ba fa kafiri ba ne ni, ina sallah”

“Na san ai kana sallah, amman ba akan lokacinta ba, ina mamakin avunda zai ɗaukewa mutun hankali har ya watsar da bautar Ubangijinsa, kasan irin azabar da Allah ya tanadarwa masu wulaƙanta sallah kuwa? Jinkira sallah lokacin ya fita ba tare da wani uzuri na shari'a ba, wannan tozarta sallah ne kamar yadda Allah ya faɗa a suratul Maryam aya ta hansi da tara zuwa sitti : Sai mutanen banza suka maye bayansu, suka tozarta sallah, suka bi sha'awace-sha'awace na saɓo; to ba da daɗewa ba zasu haɗu da gayyu wato wani gwalolon azaba a cikin wutar jahannama, sai fa wanda ya tuba.

Farkon abunda za a maka hisabi da shi a cikin ƙabarinka sallah ce, kuma ita ce zata tayaka zaman ƙabari (Allah ka bamu ikon tsaida Allah akan lokaci 🙏😭)” 2

Tun da na soma maganar yake kallona fuska a sake, da alama na burgeshi ne ko kuma mamakina yake oho, but to my surprise sai na ji ya ce

“Thank you, da kika tunatar da ni, babu wanda ya taɓa faɗa min wannan, inshallah zan gyara ko dan na samu damar rayuwa da ke a aljanna” 1

STORY CONTINUES BELOW


“Aljanna kowa gidansa daban, na Jibril daban haka ma na Nawwara daban”

Dariya ya yi kamar ba shiba ya miƙe tsaye ya nufi wata ƙofar da nake zaton banɗakine a ciki. Ni kuma na juyo na fito, sai na samu computer tana nuna min Rabi da ke waje, sai da na zauna sannan na buɗe mata sai ta shigo fuskarta a sake kamar ko yaushe.

“Ga sim ɗinki anyi miki dukan abunda ya dace”

“Thank you, amman yanzu idan ina son na kira general meeting a madadin Jibril ya zanyi?”

“Sir Jibril zaki ce ko kuma mai gida”

Ta faɗa sannan ya buɗe wani ɗan ƙaramin littafi dake gefen teburin ta soma nuna min

“Wannan number zaki kira, idan an ɗaga ba sai kin tsaya gaisuwa ba, kawai ki ce Sir Jibril ya ce haɗa masa general meeting, idan emergency ne sai ki faɗa, idan kuma meeting ɗin yana da date da time sai ki faɗa, zasu haɗu a hawa na biyu room 24 domin shi ne kawai ɗakin da yake iya ɗaukar yawan ma'aikatan da ke kamfanin nan, idan har ya yarda ki yi magana a madadinsa zaki iya zuwa kiyi idan kuma shi zaiyi da kansa sai ki raka shi”

“Thank you so much”

“Your welcome”

Sannan ta juya ta fita, ni kuma na saka number da ta nuna min a telephone zuciyata na ta raya min kar na yi, idan har na yi haka na yi karanbani, wata zuciyar kuma na nuna min idan har na yi haka na taimaiki Jibril da rayuwarsa har da da sauran ma'aikatan. 
Sai kawai na dannan kiran na ce ina buƙatar a haɗa min meeting ɗin gagawa, ni kuma na tashi na fita riƙe da wayata na nufi lifter, ina sauka hawa na biyu na soma ƙirga ɗaki, har na hango ɗakin da mutane suke shiga. Tsayawa na yi sai na kasa ƙarasawa ina ta tunanin ma yadda zan ce musu abunka da wanda be saba ba, sai kawai na juya na koma lifter, na yi mamakin yadda ina isowa bakin ƙofar office ɗin sai kawai ta buɗe min.

Ina shigowa na samu Jibril tsaye yana jiran shigowata.

“Akan mi kika kira general meeting kuma emergency?”

“Am sorry”

“Ba hakuri na ce ki ba ni ba, dalili zaki faɗa min”

“Da na yi ƙoƙarin na faɗa musu idan lokacin sallah ya yi kowa yaje ya yi sallah, sai kuma na ga kamar na maka karanbani”

“Karabanni ne mana, ba yau yau kika kama aikin ba?”

“Am sorry”

Na faɗa cike da nadama sai ya matso kusa da ni.

“Is okay, zan faɗa musu da kaina indai har haka kike so, follow me”

Yana faɗar hakan ya nufi ƙofar fita na bishi, tare muka isa da kansa ya faɗa musu cewar a yanzu da lokacin sallah ya yi kowa ya aje aikin da yake yaje ya yi sallah, daman akwai masallaci a cikin kamfanin. A yanayin yadda fuskokin musulmin ma'aikatan suka nuna sun yi farinciki sosai kuma sun nuna jindaɗinsu har ma da yin godiya.
   Ina tsaye gefen Jibril Bilal na kallona kamar zai cinye ni, irin kallon nan da mutum zai kasa gane manufarsa sai hakan yasa duk na bi na tsargu, mu muka fara fita sannan sauran suka fito. A bayan na tsaya ina amsa waya shi kan gogan na ku tuni ya yi nisa tare da Siraj.

Dpo ne ya kirani wai an bashi number ta daga gida, saboda ya zo be sameni ba kuma yana son magana da ni, a ina nake ya zo ya tafi da ni.

“Na kusa dawowa aiki, idan na dawo zan kira ka”

“Okay”

Daga haka na kashe wayar, na cigaba da tafiyata. Ko da na shiga office ɗin ƙpfar Office ɗin Jibril tana buɗe ina hango abokinsa sai dai ban san mi suke tattaunawa a akai ba har sai da na zauna sannan na soma jiyo muryar abokin nasa.

“Be kamata ka sake mata har haka ba, so ai ba hauka ba ne....”

Sai kawai na ji an ba ƙofar gam an rufe, bayan wani ɗan lokaci sai abokin nasa wato Siraj ya fito kamar cikin ɓacin rai ya fice ba tare da ya kalli inda na ke ba. 
  Takardar da ke gabana na ɗauka na duba sai na ga lokacin meeting ɗinsa da wani Hon Usman Dahiru ya yi, a maimakon na kira sai kawai na tura ƙofar na shiga.

Saurin saka bayan hannunsa ya yi ya kare hancinsa, sai dai abunda be sani ba abunda ke gabansa a farar takarda mai kamar hoda ya taɓa masa hannu, juyawa na yi zan fita sai ya kira ni.

“Naj”

Ina juyowa ya ce

“Madarace na ke sha ina fama da ulcer” 2

Ni dai ban ce masa komai ba na juya na fita, ina shirin zama sai gashi na fito daga office ɗinsa ya biyoni.

“Madara ce Naj”

Nan ma kallonsa kawai na tsaya yi, sai ya ɗaga hannayenasa sama domin shi ma yasan ban yarda da shi ba.

“Fine cocaine ce shikenan?”

“Allah ya wadaranka Jibril, kullum abunka gaba yake ba baya ba, har yanzu akwai tattoo a jikinka, yanzu kuma cocaine kake sha bayan neman matan da kake? A haka iyeyenka za su nuna ka a matsayin ɗansu ɗan ka kuma ya nuna ka a matsayin uba? Iya yau kawai na zauna da kai, amman na ga halaye masu marar kyau a tare da kai, wasu baka canja ba wasu kuma sabbi ne, na yi nadamar da na taɓa saninka a rayuwata Jibril...”

Na faɗa cikin hawaye da kuka na ɓakinciki da jin zafi, yanzu irin wannan mutunen ne na haihu da shi? Ina baƙincikin da ya kasance uban Noor sam, ɗa na be yi dacen uba ba, dan haka ban zan nuna masa ko kuma faɗa masa cewar Jibril ne ubansa na gaskiya ba.

“Bana neman mata Naj, Aisha ce kawai na ke taraiya da ita ma kuma na daina na tuba, cocaine ɗin ma akwai dalili shanta da na ke, amman na ji kamar kin yi wata magana, na ji kin ce ɗa me kike nufi akwai abunda ya kamata na sani ne?”

Ganin yadda yake matsowa yasa na yi hanzarin miƙewa tsaye har ina ɗauke numfashi, shi kuma yana ta kallona kamar mai karantar abu a fuskata, sai takowa yake har sai da ya kowa daf da ni...!

“Ina da ɗa ko Nawwara...?”

Post a Comment for "RAI BIYU CHAPTER 13"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...