Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

MAKOTAN JUNA CHAPTER 8

MAKOTAN JUNA CHAPTER 8

- - Post a Comment
MAKOTAN JUNA

CHAPTER 8


Mommy Hauwa kallonta kawai take hawaye na zubo mata kukan Zara na karya mata zuciya babu abinda yafi d'aga mata hankali kamar Dr da batasan ya zasu kwashe dashi ba idan yaga Zara.
+

Zara kuwa ganin Mommy Hauwa a tsaye tak'i motsawa ballantana tayi magana yasa ta rarrafa ta k'arasa wajen Mommy Hauwa ta rik'e mata k'afa tana k'ara fashewa da kuka tana "Dan Allah Mommy kiyi magana ki yafemin nasan ban cancanci yafiyarki ba sabida abubuwan da nayi miki banida sama dake Mommy dan Allah ki yafemin nasha wahala bayan da Ameer ya sakeni da ciki Mommy maganar da nake ma Yanzu ko abinci banci ba tun safe"

Mommy Hauwa da sauri ta durk'usa agaban Zara hankalin ta a tashe ta ruk'o kafad'ar Zara tana "Zara dama da ciki Ameer ya sakeki? Meyesa tsawon lokacin nan baki zo gida ba?

Zara katseta tayi tana " Mommy da ciki Ameer ya sakeni babu irin zuwan da banyi wajensa ba ina rokonsa akan ya maidani d'akina ko dan cikin dake jikina yak'i ina tsoron zuwa gidane sabida nasan korata zakuyi duk tsawon lokacin nan awajen wata mata mai siyar da abinci nake kwana nake tayata wanke wanke jiya ta koreni akan zata koma garinsu jiya ma abakin titi na kwana shine nace yau bari nazo gida na nemi yafiyarku dan banida sama daku Mommy dan Allah kubani Abu naci yunwa nakeji"?

Mommy Hauwa hankalin ta a tashe ta mik'e tare da rik'e hannun Zara ta taimaka mata ta mik'e tana "Amma Ameer bai kyauta ba ya za'ayi ya sake ki da ciki ko tausayi babu kuma nayita kiransa a waya yana raina min hankali duk abinda kika masa ai ko dan cikinsa dake jikinki bai kamata yayi ta korarki ba duk da nasan Zara bakida gaskiya haka kawai bazai sakeki ba tare da kin masa laifi ba muje kici abincin Na kira shi awaya"

Ciki suka Nufa Khaleed da tunda suka fara magana yana daga gefe yana kallon Zara cikin tsananin tausayi kamar ba Zara 'yar gayun da ya sani ba.

Mommy Hauwa shap ta manta da Dr Na zaune a Palo suka nufi cikin palon.

A bakin k'ofa sukayi kicibis dashi shima zai fito waje dan tunda khaleed yazo yayiwa Mommy Hauwa rad'a a kunne suka fice a tare yake ta tunanin mai tafi ta waje yi ganin basu dawo yasa ya fito dan yaga ina taje.

Mommy Hauwa da Zara a tare gabansu yayi mummunan fad'uwa Zara tayi sauri ta koma bayan Mommy Hauwa da sauri tana b'oye fuskarta.

Dr kuwa take annurin fuskarsa ta b'ace b'acin rai ya bayyana a fuskarsa.

Ko khaleed dake bayansu sai da hantar cikinsa ya kad'a.

Mommy Hauwa kallon Dr kawai take itama tana tattaro duk wani k'arfin halin da ya rage mata dan yau zata mishi tijara bai isa ya kori Zara daga gidan nan ba.

Dr cikin tsananin b'acin rai yace "Hauwa mai wannan yarinyar take nema a gidanan  bana ce kar ta sake ta k'ara tako k'afarta ta shigo min cikin gida ba"

"Mai kuwa zata nema a gidanan Dr karka manta bata da sama da gidanan bata da inda zata zauna daya wuce gidanan kayi hakuri ka yayafawa zuciyarka ruwan sanyi hannunka bai rub'ewa ka yanke ka yar Zara ta zama dolenmu bata da sama da mu duk lalacewa bazaka so rayuwarta ta tagayara ba kama dubi halin da take ciki tsakanin mutuwa da rayuwa Na cikin da take d'auke dashi  kayi hakuri ka yafe mata karka manta sau d'aya tayi maka rashin kunya Nikuwa tun suna yara suke min rashin Kunya har zuwa lokacin da tayi ma ni Dana tsugunna Na haifeta nasan zafin nakudarta nikuma nace me? Dan haka kayi hakuri yanzu Zara na bukatar taimakon mu"

STORY CONTINUES BELOW


Dr wani irin mummunan kallo ya fara bin mommy Hauwa dashi idonsa ya kad'a yayi jajir

Zara kuwa kafafunta in banda rawa babu abinda suke d'an cikinta kamar ya fad'o sabida fargaba haka ma kirjinta lab'ewa ta k'ara yi abayan Mommy Hauwa zufa na keto mata bayan taga irin kallon da Dr keyiwa Mommy Hauwan

Mommy Hauwa duk da a mugun tsorace take gabanta na fad'uwa hakan bai sa ta yarda ya nuna a fuskarta ba illa ma d'aura fuska da ta kuma yi sabida Dr yasan wanan karon babu wasa a maganarta.

Cikin wani irin murya Dr yace "Hauwa gidanki ko gidana kafin na kirga uku yarinya nan ta bar gidanan idan ba haka ba bazakiji dadin abinda zan miki ke da ita ba har gobe zagin da tayimin yana amsaa kuwa a kunenna *Allah ya isa bak'in mugu azzalumi* wai yarinya Dana fifita ta akan sauran 'ya'yana nake mata duk abinda takeso  itace yau ta bud'i baki ta zageni yanzu haka danake kallonta agabana tamkar a yanzu take min wanan zagin yarinya nan  bata cancanci yafiyata ba ko wane irin hali kuwa zata shiga bazan yafe mata ba abinda yayi daga yayarta har 'yayy'en nata da kaninta babu wanda ya tab'a zagina duk da akwai 'yan shaye shaye a cikinsu ko da sun sha ya gaya musu karya hakan bai sa sun tab'a zuwa sun zageni ba dan sun san ni mahaifinsu ne dan haka  *Bak'in mugu azzalumi* bashida gidan da zata zauna aciki dan haka ta fitar min daga gida yanzu nan kafin Na fitar da ita da kaina"

Zara zub'ewa tayi a k'asa sabida kafafunta daya k'asa rik'eta ta fashe da wani irin kuka tana "Daddy dan Allah kayi hakuri Na tuba bazan kara ba wlh Sharrin shaidan ne yanzu idan ka koreni banida inda zanje Daddy dan Allah kayi hakuri"

A tsawace Dr yace "Ba damuwata bace kije duk inda zakije kibar min gidana yanzu nan kafin Na fitar dake"


Wajen Zara ya nufa gadan gadan

Mommy Hauwa ta  sha gabansa da sauri cikin d'aurewar fuska tace "Dr babu inda Zara zata je domin abinda kayiwa naka mahaifiyar Zara tayi maka karka manta duk abinda ka shuka sai ka girbeshi banso nayi wanan maganar agaban 'yayanka ba amma naga ya zama dole Na tunatar dakai abinda ka manta abinda kayiwa Hajiya shi 'yarka tayi ma kaji idan da dadi ina da labarin duk abinda kayiwa Hajiya Na rashin kyautatawa Ina da labari har ta mutu baka samu ka nemi yafiyarta ba dan haka ba wai gori nake ma ba nasan yau da zaka maida hannun agogo baya da sai ka nemi yafiyar Hajiya da ka gyara kurakurenka dan haka karka wani ga laifin da Zara tayi ma abinda kayi akayi maka Allah ne ya sakawa Hajiya ta hanyar nuna maka ishara akan abinda ka Haifa sabida haka Zara ta cancanci ka yafe mata tunda har ta gane ta kuma zo akan ka yafe mata"
1

Tunda ta fara magana hawaye suka hau zubowa Dr zuciyarsa Na sama da k'asa kamar ba namiji ba

Mommy Hauwa duk da hawayen da ta ga yana yi ya bala'in karya mata zuciya har itama taji hawayen Na Neman zubo mata hakan bai sa ta nuna a fuskarta ba in banda ma kau da kanta da tayi dan taga alamar idan ba haka tayi mishi ba ba zai shiga hankalinsa ya gane shine silar rashin tarbiyyar 'ya'yansu ba.

Dr kuwa jikinsa wani irin rawa ya ringa yi ya zubawa   Mommy Hauwa ido dan ta tona mishi b'oyayyen sirrinsa agaban 'ya'yansa

Sai da suka kwashi minti goma ahaka in banda sheshek'ar kukan Zara babu abinda yake tashi.

Dr da k'yar ya bud'e bakinsa yace "Hauwa ai bansan abun naki ya kai har kimin gori akan ban kyautatawa mahaifiyata  ba karki manta rashin kyautatawar da ban manta ba bai wuce Dana fara aiki bata ci kudina ba bayan wahalar da ta sha dan taga Na kai wanan matsayin amma idan kika d'auke hakan ban tab'a mata rashin kunya ba ban tab'a zaginta ba ina bata girmanta Na mahaifiyata shima kudin da ban kashe mata ba  sharrin matan Dana ringa mu'amalla dasu ne a lokacin  Hauwa ngd da abinda kika min kuma tuna min da kikayi da rashin kyautatawa mahaifiyata da banyi ba ba shi zai hana Na kori Zara ba dan gidana ne ba naki ba Idan kinga bazaki iya ba zaki iya binta Na sauwake miki kije tayi ta miki rashin Kunya amma ba a gidana ba" 1

STORY CONTINUES BELOW


Mommy Hauwa ido ta zubawa Dr hawaye na zubo mata dan bata tab'a ganin Mai irin halin Dr ba

Dr kuwa tsaki yayi ya juya ya koma ciki bayan ya zubawa Zara mugun harara.

Khaleed wajen Mommy Hauwa ya nufa ya rik'e hannunta yana

"Mommy kiyi hakuri karki wani d'aga hankalinki yanzu Daddy yayi fushi sosai wanda sai an d'auki lokaci zai sauko idan ba haka ba  a yanzu ba zai wani saurareki ba tunda kinga akan Zara har yana ambatar zai sauwake miki"

Mommy Hauwa kukan bak'in ciki da takaici ta fashe dashi Tana "Haba khaleed Meyesa daddynku baya yafiya Meyesa zai d'auki irin wannan matakin akan Zara Ina yake so Zara ta tafi da wanan uban cikin Allah ma muna masa laifi mu nemi yafiyarsa ya yafe mana ballantana mu 'yan Adam Meyesa yake haka"

Zara cikinta ta rik'e sakamakon zillon da yake mata ga wani irin jiri dake kwasarta sunan Mommy Hauwa ta kira da k'arfi tana

"Mommy kibani abinci zan mutu"

Khaleed a guje ya shiga palon Mommy Hauwa kuwa ta tare Zara sabida kar ta fad'i k'asa.


Kular dake dining Khaleed ya kinkima yayi waje dagudu

Ya ajiye agaban Zara.

Zara bata wani tsaya jiran plate ba ta bud'e kular hannunta Na rawa taga tuwon shinkafa ne da aka mulmula a farin Leda ko jiran khaleed daya koma d'auko miya batayi ba ta warware guda d'aya ta fara cusawa a bakinta kafin Khaleed ya dawo har ta kusa cinye mulmule d'aya.

Mommy Hauwa ido kawai ta zubawa Zara hawaye Na cigaba da zubo mata dan ba k'aramin tausayin Zara taji ba.

Khaleed miyan agushin da yaji namomi ya zubo a cikin plate ya kawowa Zara.

Cikin minti biyar Zara ta ci tuwo wajen mulmule uku ta ringa lashe kwanu wanda hakan yasa Khaleed zubar da hawaye dan tamkar wacce bata tab'a cin abinci ba haka ta ringa lasar kwanun.

Mommy Hauwa kuwa kallonta kawai take Tana tunanin mafita dan Sam bazata iya barin a kori Zara ba sai dai idan itama barin gidan zatayi.

Sai da Zara tasha ruwa ta koshi har da gyatsa ta kalli Mommy Hauwa Tana "Mommy kiyi hakuri nasan Daddy yayi fushi ne sosai shiyasa ya fadi haka akaina bazan bari aurenki ya mutu ba ki kira Aunty khadija awaya ki roketa akan zan zauna a gidanta na d'an lokaci kafin Daddy ya huce nidai fatana ki kara yafemin abinda nayi miki ki tayani rok'on Daddy"

Mommy Hauwa mik'ewa tayi tace "Ba kiranta zanyi a waya ba zuwa zanyi da kaina bari na d'auko Hijabina"

Daga haka ta shige ciki Zara kuwa ta kalli Khaleed tace "Khaleed dan Allah d'auko min leda  na juye abincin nan anjima nasan zanji yunwa sai naci"

Khaleed girgiza kansa yayi cikin tausayawa yace "Haba Aunty mai yayi Zafi haka ai akwai abinci a gidan Aunty khadija har sai kinci kin ture ba sai an juye miki a leda ba"

Mommy Hauwa kuwa fuska a d'aure ta shige d'akinta Dr kuwa da tunda ya zauna a Palo yake tuna irin rayuwar da yayi abaya na rashin kyautatawa mahaifiyarsa inda tunanin hakan yasa yayi ta zubar da hawaye yana nadama dan Mahaifiyarsa babu abinda bata siyar ba sabida shi amma wai ya rasa wacce zai yiwa rowa idan ta tambayeshi kudi sai ita ayau duk abinda ya mallaka ta silarta ne Inama hannun agogo ya koma baya da sai ya bata duk abinda ya mallaka a cikin wanan halin yake Mommy Hauwa tazo ta wuce shi ya bita da kallo har ta kuma fitowa sanye da Hijabinta. 

Gabansa ne ya fad'i a lokacin daya ga Tayi hanyar waje da Hijabi a jikinta cikin tashin hankali ya mik'e tsaye yace "Hauwa ina zakije"?

Mommy Hauwa juyowa Tayi fuska a d'aure tace " ba kace nabi Zara ba  binta zanyi sai ka zauna kai kad'ai tunda haka kakeso".

STORY CONTINUES BELOW


Daga haka Mommy Hauwa ta fice daga palon duk kiran da Dr ke mata ko juyawa batayi ta kalleshi ba.

Hannun Zara ta rik'e sukayi waje Khaleed yabisu abaya sai da ya tsayar musu da tricycle yaga tafiyarsu kafin ya koma ciki inda yana komawa ciki Dr ya rufeshi da Fad'a yana akan me bai hana Mommy Hauwa tafiya ba ya barta ta tafi tamkar ya rufe Khaleed da duka haka ya ringa zuba masa fad'a.

k'arfe 9 dai-dai suka isa gidan Kanwar Mommy Hauwa Aunty khadija.

Aunty khadijar kuwa tana ganinsu ta dafe kirjinta dan kana ganin idon Mommy Hauwa kasan taci kuka ta gode Allah a rud'e ta fara tambayarsu abinda ya faru sai da Mommy Hauwa ta samu guri ta zauna ta bawa Aunty khadija labarin duk abinda ya faru babu abinda ta b'oye mata dan bata da sama da khadijar babu sirrinta da bata sani ba.

Aunty khadija Zaran dake ta gyangyadi ta bi da kallo tace "Tashi kishiga d'akina ki kwanta gobe sai muyi magana dan naga agajiye kike ki kuma shirya fad'amin gaskiyar abinda ya faru dan nasan halin ki Zara Ameer haka kawai bazai miki kazafi ya sakeki ba"

Zara bata wani tsaya jin mai take cewa ba ta nufi d'akin tana Hamma sabida mugun baccin da takeji tana kuwa zubewa a shimfidaddiyar gadon bacci mai nauyi tare da nutsuwa yayi awon gaba da ita.

Mommy Hauwa kuwa tana shigewa ta Ciro wayarta daga jakarta ta latso lambar Ameer ta saka a handsfree tana girgiza k'afa tamkar agabanta yake.

Adai dai lokacin  Ameer ke  waya da Aliya yana janta da hira dan k'arfi da yaji yakeso ya cusa kansa awajen Aliya har ya samu ta saki jiki dashi  .

Kiran dake ta shigowa wayarsa ne yasa ya cire wayar daga kunnensa dan yaga wanda yake ta kira haka ganin Mommy Hauwa ke kiransa yasa ya d'an waro ido yana mamakin kiran da take masa ganin har lokacin kiran na shigowa yasa yacewa Aliya bari ya d'aga wani waya yanzu zai kirata.

Yana katse kiran ya d'aga na Mommy Hauwa tare da sallama

Inda Mommy Hauwa ta fara zabgawa wayar harara kafin ta amsa sallamar ko gaisuwar da yake mata bata tsaya amsawa ba tace "Ameer yau Zara ta dawo gida da tsohon ciki Ashe da ciki ka saketa haba Ameer ban tab'a tunanin haka daga wajenka ba duk da nasan Zara bata da Hali ban tsammaci zaka mata haka ba duk da rokonka da naringa yi akan ka dubi girman Allah ka ringa hakuri da ita amma koda daka kamata da wanin ka kuma ga da cikinka ajikinta ai sai ka sausauta mata kabari ta haihu kafin ka koreta"

Ameer bai iya bari Mommy Hauwa ta cigaba da magana ba yace "Innnalillahi wa inna ilahi rajiun Mommy wlh wlh ba cikina bane kinga na rantse miki sai dai idan cikin Adnan ne dan rabona da Zara kafin na saketa kusan wata uku ban kara kusantar ta ba   idan ma tana d'auke da cikina yaci ace ta haihu zuwa yanzu wlh Mommy ba cikina bane kuma zan iya rantsuwa da Al Qurani ina Zaran take kibani ita ta rantse tace cikina ne"

Mommy Hauwa jikin ita da Aunty khadija ne yabi yayi sanyi aka rasa wanda zai iya magana acikinsu

Sai da Ameer ya kara cewa Hello

Mommy Hauwa Tayi k'arfin halin cewa "Zara bata kusa Tayi bacci"

Ameer da sauri Yace "Mommy zanzo dakaina gobe nazo da Qurani indafa ta dafa indai ta dafa tace cikina ne wlh zan amshi cikin"

Mommy Hauwa magana takeso Tayi Ameer yayi sauri ya katse dan ransa ya bala'in b'aci jefar da wayar yayi yana wani irin huci dan bai tab'a tunanin Rainin hankalin Zara ya kai haka ba shi zata bawa cikin Adnan k'arfi da yaji lailai batasan waye shi ba dan indai akan wannan cikin ne har kotu sai suje.

Ameer kiran da bai kara yiwa Aliya ba kenan sabida b'acin rai inda Aliya duk tabi ta damu da rashin kiran nasa kamar ta kirashi haka ta ringa ji.

Mommy Hauwa kuwa Ameer yana katse wayar ta zuba uban tagumi hawaye na zubo mata Aunty khadija kuwa ajiyar zuciya ta sauke cikin tsananin tausayin jarrabawar da yayarta ke tagani akan y'ay'yanta tace "Kiyi hakuri Aunty Hauwa watarana komai mai wucewa ne insha Allahu dan Allah karkisa tunani aranki ki kamu da hawan jini"

Hawaye Mommy Hauwa ta share tace "na nawa kuma khadija sai dai kuma hawan ruwa khadija ina ganin jarrabawa akan yaran nan daga yan shaye shaye sai mai bin maza wanan wane irin rayuwa ne khadija ke shaida ce banyi wa iyayenmu haka ba bansan ya nawa yaran suke min haka ba"

Aunty khadija da sauri tace "ki daina fad'ar haka Aunty Hauwa kiringa musu addu'ar shiriya insha Allahu Allah zai shirya miki su kizo muje na rakaki naga dare yanayi"

"Murtala ya dawo ne"?

Aunty khadija da sauri tace " aaa har yanzu ai bai dawo daga Ghana ba shi da zuwa ma sai wata mai kamawa"

"To babu inda zani Anan zan kwana dan naga abinda banyi ba tun lokacin yarinta na sai Nayi yanzu Dr zai shiga hankalinsa"

Aunty khadija murmushi Tayi tace "Aunty Hauwa ba dai Yaji kike nufin zakiyi ba"

"Gashi kuwa kin fad'a Khadija yanzu ya zanyi idan dai wannan yaron Ameer dagaske yake cikin Zara ba nasa bane ina zan kai wannan kayan kunyar innalillahi wa inna ilahi rajiun Khadija ban tab'a kusantar zina ba amma gashi 'yar cikina harda ribar zina"

Khadija da sauri tace "aaa aunty kima kwantar da hankalinki cikin Ameer ne b'acin rai ne yasa ya fad'i haka"

Mommy Hauwa badan ta yarda ba tace to ameen

Daga nan suka cigaba da hira Aunty khadija na kwantar mata da hankali

B'angaren Adnan kuwa Zara na tafiya yaga gidan ya k'ara masa fad'i da Zafi haka ya ringa shiga d'aki yana dawowa Palo  har a lokacin yana gwada wayar Ajjidde ganin idan baiji muryarta ko yaganta ba bacci bazai yi gigin d'aukarsa ba yasa ya d'auki mukullin motarsa  ya nufi gidan Ajjidde a lokacin da ya isa mai gadi bai hana shi shiga ciki ba dan yariga da yasan Ajjidde ta san shi.

Adnan kuwa kansa tsaye ya shiga cikin gidan tare da nufar palon gabansa na d'an fad'uwa.

A k'asan carpet yaga Ajjidde a zaune da wani narkakken mutum tumbinsa kamar mai cikin wata Tara Ajjidde sanye take da bom shot da wani farin vest shi kuma mutumin sanye yake da gajeran wando nononsa kamar na kirjin wata buduruwar (meela)πŸ˜›πŸ˜› kansa sai kyalli yake sabida sanko tukunyar shisha ce a tsakiyarsu suna ta zuka ga kwalaban cordien nan a zuzube a k'asa da can d'in coke.

Adnan wani irin zufa ne ya hau keto masa gabansa ya ringa fad'uwa jikinsa kuwa sai rawa yake cikin kinkina yace "Ajjidde"

Ajjidde juyowa Tayi da rinannun idonta da suka kad'a sukayi jajjir cikin muryar mayye tace "uban me kazo yimin a gida zanci uwarka fa dan bana san naci dan shegiya kai ka kiyayeni fa  zan ci ubanka yaseen"
3

Lukutin mutumin dake gefenta shima d'agowa yayi cikin muryar mayyen yace "Ajjidde waye wanan mai kama da maigadinki"

Adnan sallati yasaka da k'arfi yana kallon Ajjidde zuciyarsa kuwa kamar ta fado k'asa wai matar da yake so ya aura ta zama uwar 'ya'yansa ce a cikin wannan halin wai ma tukuna waye wanan katon dake gefenta???.........Adnan kamar wanda aka dasa haka ya tsaya yana kallon su jikinsa na rawa +

Ajjidde kuwa cikin mayye ta cigaba da surfa mishi ashar tare da mik'ewa tana tangal tangal

Wajen Adnan ta nufa dake tsaye a bakin k'ofa ta fad'i yafi a kirga tana mik'ewa.

Adnan cikin buguwar zuciya ya  cigaba da kallonta har ta k'araso gabansa ta d'aga hannunta daya mata nauyi zata mari Adnan.

Adnan yayi sauri ya rik'e hannunta yace "Ajjidde wai me haka mai yake damunki"? 2

Cikin muryar mayye Ajjidde tace "ubanka ne yake damuna mai yasa kake damuna ne ka fitar min daga gida"

Adnan  a zuciye yafara gigirza ta yana "Ki dawo hankalinki Ajjidde Nine fa Adnan ko"""

Aman data fara shek'a mishi ajikinsa ne ya katse masa maganar da yake

Adnan cikin tsananin takaici ya rik'eta har ta gama kwara aman ta zube a k'asa idonta a rufe tana maida numfashi. 2

Adnan kayan jikinsa yabi da kallo cikin kyankyami ya zare rigar daga jikinsa.

Ya ajiye a gefe ya kinkimi Ajjidde yayi hanyar wajen da yake kyautata zaton d'aki ne.

Akan k'aton Royal bed d'in dake d'akin ya kwantar da ita.

ya zauna  a gefenta ya zuba mata ido santa na gudun tsere a zuciyarsa ahankali yafara bin ko'ina na jikinta da kallo yana hadiyar yawu dan Ajjidde ta bala'in haduwa fatar jikinta glowing kawai yake yana kyalli kirjinta dake tsaye yafi ko'ina d'aga masa hankali tuni ya ma manta da wani b'acin ran daya tsinci kansa a ciki na halin da ya zo ya riskesu.
2

Ya kai hannunsa a hankali yafara shafo kirjinta yana lumshe ido 2

Ajjidde kuwa baccinta kawai take Adnan a hankali ya cigaba da shafata hankalinsa na tashi daga zaunen  dayake. 1

Ganin idan ba controlling kansa yayi ba zai iya aika aika kuma bashida wanan intention d'in Aurenta kawai yake so yayi d'auke hannunsa yayi a hankali yana mai sauke nannauyan ajiyar zuciya ya mik'e ya shiga band'akin ya d'ebo ruwa Dan ya goge mata jikinta da aman ya b'ata. 1

K'aramin towels d'in dake Jere a band'akin ya d'auko d'aya ya tsoma acikin ruwan ya goge mata jikinta dashi ganin vest d'inta ya jike yasa ya cire mata.

Adnan kamewa yayi a lokacin daya cire mata vest d'in yasha huld'a da 'en mata iri iri amma Ajjidde ta daban ce numfashinsa ke fita Sauri da Sauri sai da yayi dagaske ya iya saisaita kansa bayan ya k'ara shafo kirjin nata da kai musu wani irin zazzafan kiss kamar ya haye kanta haka yake ji. 1

Farin lallausan bargon dake gefen gadon ya janyo ya rufeta ya bar fuskarta awaje ya cigaba da kallonta sai a lokacin ya tuna da k'aton daya zo ya tarar dasu a tare take Yaji ransa ya baci wani irin bak'in kishi ya rufe shi da Sauri ya mik'e yayi palon inda ya tarar dashi da shirgegen cikinsa ya baje yana ta munshari.

STORY CONTINUES BELOW


Adnan ji yake kamar ya rufe shi da duka inda kuma yafara tunanin mai had'in Ajjidde da mutum irin wanan da ya kusa haifarta wanda ko kyan gani bashi dashi sai wani zuciyar nasan rayya masa Ajjidde zaman kanta take kila saurayinta ne lura da dukansu biyun babu suturar arziki a jikinsu sai kuma yayi Sauri ya kau da tunanin haka a ransa dan sam bayasan wani abun da zai sa yayi mummunan tunani akan Ajjidde yanda yake jinsa duk aibun halin Ajjidde bazai iya rabuwa da ita ba dama yasan hardly mace ta zauna ita kad'ai batare da ta samu wani tangarda a tarbiyyarta ba fatansa dai Allah yasa a iya shaye shayen ta tsaya kuma wanan katon daya gansu taren Allah yasa d'an uwanta ne da sannu zai hanata shaye shayen da wanan tunanin hankalinsa ya d'an kwanta bayan ya kaiwa katon mutumin naushi a ciki amma ko gezau mutumin baiyi ba.
4

Adnan haka ya zauna a palon yana duba agogo akai akai yana lek'o d'akin Ajjidde yaga ko ta farka dan Sam bazai iya tafiya yabarta da wanan shirgegen mutumin ba.
1

Ajjidde ba ita ta tashi ba sai wajen ukun dare a lokacin Adnan Yana rik'e da rigarsa da amai ya b'ata yana gyangyadi.

Ajjidde sai da ta samu minti goma sha biyar a zaune tana karewa kanta kallo sannan ta tuna kamar Adnan yazo gidan tana cikin mayye zata iya tuna a Palo ta zauna ita da Alhaji  Al gazaru suna shaye shayen su to waye ya kawo ta d'aki ina Alhaji Gazarun"

Da wannan tunanin ta duro daga kan gadon ta d'auki k'aramin towel ta kare kirjinta dashi ta nufi palon.

Mamakine ya rufeta a lokacin data ga Adnan a zaune akan kujera yana gyangyadi Alhaji Al gazaru a baje a k'asa yana ta zuba munshari.

A take tunanin ta ya bata Adnan ne ya maidata d'aki ya dawo Palo ya zauna.

Juyawa tayi ta kalli agogon palon taga uku har da rabi wajen Adnan ta nufa tana rik'e da towel d'inta a kirjinta  tana tab'a shi yayi Sauri ya bud'e idonsa.

Ajjidde fuska a d'aure tace "Ya akayi baka tafi gida ba"?

Adnan zuba mata ido kawai yayi yana kallonta take Yaji hankalinsa ya tashi dayaga yanda ta d'aura fuska.

Ajjidde kau da kanta tayi daga kallonsa tace " Adnan kana crossing limitation d'inka zan iya fasa auranka tunda ka kirani kaga ban d'aga ba ya kamata ka san takura ne banaso ga d'aki can kaje ka kwanta idan gari ya waye sai ka tafi dan dare ya Riga da yayi zamuyi magana gobe kafin ka tafi"
1

Daga haka ta juya ta nufi d'akinta
1

Adnan bin bayanta yayi da kallo har ta shige ya hadiyi wani irin yawu mai tauri dan yasan tabbas ya d'ebo ruwan dafa kansa dan Sam bai Samu fuska a wajenta ba ballantana har yayi  mata tambaya wani irin takaici da bak'in ciki ne suka rufeshi dan ba dan mugun kaunarta dayake ba da ya mata dan banzan duka na raina masa hankalin da tayi. 1

Ahaka ya cigaba da zama bayan bacci ya mishi k'aura tunane tunane kawai yake na yanda zai iya juya Ajjidde idan ya aureta dan tafi k'arfinsa ko ta ina  da yana da Hali da ana kiran asuba zai bar gidan amma ina bazai iya ba tunda har tace ya tsaya haka zai tsaya yaji wane maganar zasuyi duk da yana so yasan matsayin wannan katon iska dake kwance a wajenta.
1

K'arfe hudu dai-dai Alhaji Al Gazaru ya farka inda suka had'a ido da Adnan dake  zabga mishi mugun harara da sauri ya mik'e zaune yana kalle kalle dan yama manta inda yake sai da ya dawo dai dai ya maida kallonsa kan Adnan da idonsa ke Neman fadowa.

Alhaji Gazaru kau da kansa yayi yana tunanin k'ila daya daga cikin customers d'in Ajjidde ne shima yazo rage dare shine yazo ya tarar dashi bai kara kallon inda Adnan yake ba ya nufi d'akin dake kusa Dana Ajjidde dan ya kimtsa jikinsa yazo ya dau hanya dan bai isa ya soma zuwa d'akin Ajjidde a yanzu ba dan ta Riga da ta sallame shi ya kuma san rules d'inta indai ba kudi Mai bala'in tsoka ka biyata ba baka isa ka kwana da ita d'aki d'aya ba.

STORY CONTINUES BELOW


Adnan kansa ne ya d'aure da yaga ya shige d'aya d'akin inda take yaji hankalinsa ya kwanta dan ayanzu yafi kyautata  zaton d'an uwanta ne ba Saurayinta ba take ya nemi bacin ran sa ya rasa baccin daya Dade yanaji yayi awon gaba dashi.
1

K'arfe goma Adnan ya farka daga baccin daya d'aukeshi inda ya mik'e da sauri yana mamakin yanda ya Dade yana baccin d'akin dake kusa Dana Ajjidde ya shiga ya d'auro alwala a bandakin yana tunanin inda Alhaji Al Gazarun yayi dan bai ganshi a d'akin ba sai da yayi sallah ya kuma fitowa palon ya zauna yana jiran Ajjidde tafito duk da yana so ya tafi gida amma haka zai jira har ta fito.

Haka Adnan ya cigaba da zama a Palon sai wajen sha biyu Ajjidde ta fito daga d'akin sanye da wani arnen less taci uban kwalliya in banda kamshi babu abinda take yi.

adnan kuwa ya hadiyi yawu yafi a kirga tamkar mudubi haka ya maidata yana kallonta.

Ajjidde kuwa kujerar dake fuskantarsa ta zauna bata ko kalli inda yake ba ta hau kwallawa 'yar aikinta kira.

Aguje 'yar aikin nata tafito daga d'akinta tazo ta zube agabanta ta gaisheta ta gaida Adnan

Ajjidde  umarni tayi mata data  kawo musu abun karyawa.

Cikin minti biyar ta jera kulolli agaban Adnan da Ajjidde.

Ajjidde kuwa ganin taki kallonsa ne yasa ya d'aure ya hadiyi bak'in cikin dake cin ransa ya gaisheta.

Da mamakin sa amsawa tayi batare da taji nauyinsa ba amatsayinta Na wacce ya kamata ta fara gaishe shi inda take ya k'ara jin ransa ya b'aci. 2

Ji yake kamar ya bud'e zuciyarsa ya Ciro santa yayi ta kwallo dashi dan ba laifi Ajjidde Na wulakanta shi.

Ajjidde kuwa serving kanta tayi ta fara cin abincin ta hankalinta kwance bata d'ago ba sai data koshi ta ture table d'in gefe ta kalli Adnan tana "kai bazaka ci abincin bane kafasan bazan maka wata magana ba har sai kaci abinci tukuna"

Murmushin data sakar masa ne yayi melting duk wani b'acin ran dayake ciki ya maida mata martanin murmushin data masa daga haka ya debi dankali da kwan dai dai yanda zai iya ci ya ya koshi ya sha shayin kad'an shima ya ture tebur d'in gefe tare da Hamdala.
1

Sai da yace mata yagama ta ajiye wayar da take ta dannawa ta kalleshi tace "Yauwa maganar da zanyi ma shine banasan takura arayuwata idan aka takura min tsanar mutum nake idan dai ka shirya aurena kazo a d'aura mana aure kawai idan baka shirya ba ka daina takuramin da waya har ka ringa nado k'afa kana zuwa ka bari idan ka shirya Sai kazo karkuma ka manta sharrud'an Dana gindaya maka kafin ka aureni dama maganar da nakeso nayi maka kenan"

Adnan da sauri yace "Na shirya Ajjidde ko a gobe ne ma a d'aura mana aure dan wlh bana iya bacci idan banji muryarki ba.

Ajjidde Sai data kare mishi kallo tundaga sama har k'asa tace " Are sure u are ready"?

Adnan da sauri ya gyad'a mata kai

Ajjidde kuwa ta sauke ajiyar zuciya tace "to shikenan gobe zan kira Wanda zaiyimin walliyi a d'aura Auren a palon gidana kaima ka taho da naka walliyin karka manta nace maka aurenka bazai hanani sana'ata ba babu ruwanka da samun ido abinda naga dama shi zanyi aurena bashi yake nufin zaka nade k'afa ka zauna ba zuwa zakayi ka cigaba da Neman kudinka a kuma gidana zaka zauna ka yarda"

Adnan tsabar farincikin zai mallaki Ajjidde a gobe da sauri ya washe bakinsa yace ya yarda"
1

Ajjidde ta girgiza kai tace "kamar yanda Na fad'a maka ba Sai kayi min komai ba sadaki kawai nakeso kuma ni zan yanke maka sadakin da zaka bani miliyan d'aya zaka min sadaki dashi lura da bakada kudi yasa bazan ce kayimin akwatin gold ba idan dai fa ka shirya aurena kenan"

STORY CONTINUES BELOW


Take murmushin dake fuskar Adnan ya b'ace gumi ya hau tsatsafo masa babu abinda yake nanatawa sai Miliyan d'aya inda Ajjidde ta zuba mishi ido cikin mamakin yanda yabi ya rude yana wani nanata miliyan d'aya.

"Ko dai Miliyan d'ayan yamaka kad'an ne idan kuma baka dashine kaje ka Tara idan ka samu sai kazo a d'aura mana Auren dan bazai yiwu ka aureni a sadaka ba"

Ajjidde tace tana w'ulawa Adnan harara

Adnan wani irin yawu ya hadiye bayan ya hararo dubu Dari hud'u da hamsin d'in  daya rage masa a account yafara lissafin inda zai nemo  cikon Dari biyar da hamsin dan bashida ita ballantana ya kai ga ya bawa wani ajiya gabansa wani irin fad'uwa ya fara yi hankalinsa yayi mummunan tashi dan bazai iya jure rasa Ajjidde ba.

Ajjidde kuwa  wayarta ta d'auka ta mik'e tana "Ni zan shiga daga ciki idan ka gama tunanin kamin magana"

Adnan da sauri ya tsayar da ita yace "Allah ya kaimu goben insha Allahu zan kawo walliyina da Sadakin"

Ajjidde murmushi ta sakar masa tana "sai goben kenan k'arfe hudu za'a d'aura mana Auren ka d'an zo da shirinka akwai wani k'aramin liyafa da zan had'a mana ka kuma kwaso komai naka tunda Anan zaka zauna"


Adnan murmushin yak'en ya sakar mata dan hankalinsa a tashe yake yace "pls zan iya miki waya kafin goben"?

" eee zaka iya kirana idan kayimin kira uku ban d'aga ba karka sake kira kila ina wani uzurin ne ko banasan d'aga waya"

Adnan girgiza mata kai yayi yace "to shikenan Na tafi sai goben"

Daga haka ya juya ya bar palon Ajjidde kuwa ta bishi da kallo tana murmushin mugunta.


Adnan kuwa da rawar k'afafu da jiki ya k'arasa cikin motar hankalin sa a mugun tashe dan bai san daga ina zai fara neman kudi ba waye zai yarda ya bashi rancen dubu Dari biyar har da hamsin alhalin an san bawani aiki gare shi ba.

Adnan dafe kansa yayi dake Sara mishi yana tunanin ma fita inda a karshe ya nufi wajen Safwan dan ya gwada sa'arsa.

Abun mamaki a lokacin daya gayawa Safwan abinda ke tafe dashi Dariya ya ringa kyakyata masa yana cewa a ina zai samu kudin da zai biya shi da Biyar biyar d'in da ake lik'awa awajen biki zai biya shi ko da me zai biya shi a takaice Baram baram suka rabu da Safwan inda ya cigaba da karad'e sauran abokanan nasa ko zai dace sai dai ina dukansu rashin mutunci suke masa tunani ya fara yi na ya hakura da Ajjidde kawai ya huta amma me kamar kara rura masa wutan santa ake akan dole ya yanke hukuncin siyar da motarsa sabida shi kad'ai ne abinda zai iya siyarwa ya samu kudin da zai cika ya biya sadakin Ajjidde Inda can k'asan zuciyarsa murnar Mallakar Ajjidde kawai yake dubu Dari takwas da ashirin ya  siyar da  motarsa yayi banking kudin ya dawo gida yafara had'a kan kayansa dan a gobe zai koma gidan Ajjidde da zama yana kyautata zaton da sannu zai koyawa Ajjidde yanda zata so shi har ya juyata san ransa da dukiyarta.


1

B'angaren Ameer kuwa tunda yayi sallar asuba bai koma barci ba wanka yayi ya shirya yana jiran gari ya k'ara sa wayewa ya nufi gidansu Zara dan ko kad'an bacci bai ziyarci idonsa ba sabida b'acin rai.

K'arfe bakwai dai-dai ya d'auki hanyar gidansu Zara da Quraninsa izzu sittin dan sai Zara ta rantse da Qurani akan cikin jikinta nashi ne hankalin sa zai kwanta.

K'arfe bakwai da minti ashirin yayi parking a k'ofar gidansu Zara fuskar Nan tashi a had'e

Yana k'ok'arin fitowa daga cikin mota  Khaleed yafito daga gidan da kayan ball zai fita training d'in safe mamakine ya rufe khaleed a lokacin daya ga Ameer yafito daga motarsa ya nufo wajensa hannunsa rik'e da Qurani 

Khaleed gaishe shi yayi a lokacin daya k'araso Ameer kuwa ya mik'a masa hannu sukayi musabiha.

Ameer bai tsaya b'ata lokaci ba yace yacewa Mommy Hauwa yazo yana waje.

Khaleed ce masa yayi  ba'a gida suka kwana ba suna gidan Aunty khadija ita da Zara.

Ameer kasancewar yasan Aunty khadijar ya kuma san gidanta  juyawa yayi ya koma  motarsa ya d'auki hanyar gidan Aunty khadijar cikin 'yan mintuna ya k'arasa gidan Ameer bai sha wahala ba aka masa iso har cikin palon gidan sabida a gidan suka fi zance da Zara kafin suyi aure.

Aunty khadija dake kitchen  tana had'a breakfast ba k'aramin mamaki tayi ba a lokacin data ga Ameer a gidansu da sassafe gaisawa sukayi bayan yan tambaye tambaye Ameer yace mata wajen Mommy Hauwa yazo yaje can gidan ance suna nan da Zara.

Aunty khadija mik'ewa tayi jiki a sanyaye tace bari ta taso ta Dan bacci take.

A lokacin data shiga d'akin a zaune ta tarar da Mommy Hauwa ta zubawa waje d'aya ido tana tunani ita kuwa Zara ta baje tana ta baccinta cikin kwanciyar hankali dan ko juyi batayi ba tunda ta kwanta sabida yanda take jin dadin baccin.

Mamakine ya rufe Mommy Hauwa a lokacin da Aunty khadija tace mata Ameer yazo yana Palo yace wajenta yazo.

Mommy Hauwa take jikinta ya k'ara sanyi dan tasan idan Ameer bashida gaskiya babu yanda za'ayi ya bugo wannan samakon cikin tsananin takaici ta d'akawa Zara duka a cinya.

Zara kuwa tayi sauri ta bud'e idonta tana Sosa cinyarta.

Mommy Hauwa Harara ta galla mata tana "ki tashi ki wanke fuskarki kizo ki samemu a Palo dan ga Ameer can yazo yace ki rantse agabansa akan cikinsa ne ajikinki"

Zara kwalalo ido tayi take dan cikinta ya motsa ta dafe kirjinta tana "Mommy yanzu haka Ameer Na gidanan"

"Kwarai kuwa yana gidanan ba dai kince da ciki ya sake ki ba kizo muje yana Palo yana jiranmu"

Daga haka Mommy Hauwa ta mik'e tayi waje dan Aunty khadija ta Dade da yin waje dan ta duba abinda ta d'ora.

Zara kuwa hankalinta ne yayi bala'in tashi ta hau gumin k'arfi da yaji dan bata isa ta kalli idon Ameer tace cikinsa bane jikinta ne ya hau rawa gabanta Na fad'uwa a lokacin data jiyo Mommy Hauwa Na kwalla mata kira sabida gigicewa daga ita sai doguwar rigar jikinta ta fita babu ko dankwalli.

Mommy Hauwa kuwa tunda suka gaisa da Ameer ta sunkuyar da kanta tana hawaye ganin Zara ta shanyasu yasa tafara kwalla mata kira dan Ameer yace bazai yi magana ba sai Zara tafito.

Karar bud'e k'ofar d'akin ne yasa Ameer d'agowa inda suka yi ido hud'u da Zara da turtsetsen cikin ta.

Jikin Zara ne ya fara bala'in rawa kamar zata fad'i sakamakon tozali da tayi da Ameer daya zama bature sabida kyau da ya kara yi ga wani mugun kallon da yake binta dashi........Zara a kusa da k'afar Mommy Hauwa ta zub'e ta sunkuyar da kanta dan   bazata iya jure kallon da Ameer ke mata ba dan wani mugun tsanarta take hangowa a kwayar idonsa cikinta murd'awa kawai yake gumi Na tsatsafo mata.
+

Mommy Hauwa ganin Ameer yak'i magana in banda mugun kallon da yake bin Zara dashi kamar ya tashi ya rufe Zara da duka yasa tace

"Ameer ga Zaran nan agabanka jiya ta dawo daddare tace min da ciki ka saketa babu irin wuyan da bata sha ba dan wata mata mai siyar da abinci take tayawa aiki take bata abinci to a jiyan ta koreta sabida zata tafi garinsu ganin babu yace
1

zata je yasa ta dawo gida inda shima Mahaifinta yace baza ta zauna masa a gida ba akan dole na biyota nan jiya na kuma kira ka awaya dan na tambayeka gaskiyar lamarin dan nayi mamaki da tace min da ciki ka saketa"

Ameer cije lebb'ensa yayi cikin tsananin takaici nan take idonsa ya kad'a yayi ja Zara dake rawar d'ari kawai yake kallo sai da ya kwashi minti biyar kafin yace "Mommy wlh wlh wanan ba cikina bane cikin Adnan ne dan tunda na kawo Zara gida akan kuyi mata fad'a na kuma maidata babu abinda ya k'ara shiga tsakanina da ita har muka rabu kuma NA fad'a miki dalilin da yasa na saketa Mommy Zara cin amanata take da mak'ocina wlh da idona na gansu Bawai gayamin akayi ba  idan kuma tace cikina ne yanzu zan d'auko Qurani acikin motata ta rantse akan cikina ne ni kuma zan k'arbi cikin"

Ameer sai da ya numfasa yace "Zara"

Zara d'agowa tayi hawaye na zubo mata jikinta na rawa suka had'a ido

"Tsakaninki da Allah cikin dake jikinki cikina ne"?

Ameer yace yana jifanta da wani irin kallo

Zara k'asa magana tayi ta cigaba da kallonsa ta na jin wani tsohon san Ameer na taso mata

Ameer sai da ya maimaita tambayar sau uku Amma Zara ta k'asa magana.

Mommy Hauwa a Zuciye ta kai mata duka tana " bakiji mai yace bane yace ki rantse da girman Allah akan cikinsa ne"

Zara sunkuyar da kanta tayi ta fashe da kuka tana tunanin Halin da Adnan ya jefata ya za'ayi ta soma cewa cikin Adnan ne agaban Mommy Hauwa fad'ar hakan na nufin d'an tausayinta da take ji ta daina itama ta gujeta Ameer ya k'ara tsanar ta gwara kawai ta dage akan cikin Ameer ne shine kawai ma fita agareta inyaso idan ta haihu sai ta fad'a musu gaskiya.
1

Zara kukan ta cigaba da yi sai da Mommy Hauwa ta k'ara kai mata duka ta d'ago cikin sheshek'ar kuka tace "Ameer wlh cikinka ne"

Ameer sakin baki yayi yana kallon Zara cikin tsananin mamaki wani irin bak'in ciki ya k'ara rufe shi dama wacce ma take jahila ta keta alfarmar Aure ya ma za'ayi tak'i rantsuwa akan karya kad'an da aikinta kenan.

STORY CONTINUES BELOW


Mommy Hauwa itama kallon Zara take dan haka kawai taji bata yarda da Zara ba.

Ameer kuwa mik'ewa yayi yacewa Mommy Hauwa yana zuwa yana fita waje Mommy Hauwa ta rufe Zara da fad'a akan gwara ta fito ta fad'i gaskiya tunda har taje tana muamalla da wani namijin al halin da aurenta to cikin jikinta bana Ameer bane dan da nashine bazai karyata har yazo musu da sassafe ba.

Zara ita dai kuka kawai take tana cewa cikin Ameer ne.

Ameer kuwa yana fita waje ruwan faron daya sha ya rage ya d'auko daga cikin motarsa yayi alwala ya d'auko Quraninsa ya koma ciki.

Zama ya k'ara yi daga inda ya tashi yacewa Mommy Hauwa nayi alwala a waje ga Qurani nan izzu sittin Zara itama taje tayo alwalar zan rantse akan ba cikina bane idan cikina ne Quranin nan ya tozartani itama ta rantse kamar yanda NA rantse akan cikin jikinta nawane idan ba nawa bane Quranin nan ya tozarta ta nikuma idan ta rantse haka wlh Mommy zan k'arbi cikin"
3

Mommy Hauwa da sauri tace  "Haba Ameer mai yayi Zafi haka har za'a rantse da Qurani ai abun be kai haka ba wlh ma  yarda da kai dan nariga da nasan halin Zara nasan kuma mai zata iya aikatawa"
1

Ameer da sauri ya katseta yace "aa Mommy ki bari dan Allah mu rantse sai hankalina yafi kwanciya ke Zara tashi kije kiyo alwalar ina jiranki"
1

Zara tunda ya shigo da Qurani hankalinta yayi bala'in tashi dan ko giyan wake tasha bata isa ta soma rantsuwa da Al Qurani ba kallon Ameer kawai take jikinta na rawa" 2

Mommy Hauwa kuwa dan ta gwada hankalin Zaran tsawa ta daka mata tana "ki tashi mana kije kiyo alwalar kizo ki rantse tunda kince cikinsa ne"

Zara kuka ta fashe dashi tana "mommy bazan iya rantsewa ba wlh ba cikinsa bane na Adnan ne dan Allah Mommy ki yafemin wlh sharrin shaidan ne nayi nadamar biyewa san zuciyata tun ba'aje ko'ina ba na fara girbar abinda na shuka Mommy dan babu irin wulak'anci da Adnan bai yimin ba har dukana yake  shine ma ya koroni yace nadawo gida nace cikin Ameer ne"
2

Kuka Zara ke yi sosai tana rik'e k'afafuwan Mommy Hauwa

Inda mommy Hauwa ta ringa zabga sallati tana girgiza kai

Ameer kuwa runtse idonsa yayi wani mummunan Tsanar Zara na kuma tsirga mishi tabbas had'uwarsa da Zara da Auren mace irin Zara yana cikin kundun kaddararsa idan ba haka ba ina shi ina Auren watsatsiya Mara kamun kai irin Zara.

Babu abinda ke tashi a palon sai kukan Zara Dana Mommy Hauwa inda Zara ta kankame k'afar Mommy Hauwa ta na ta Neman yafiyarta 

Mommy Hauwa fusge k'afarta tayi ta ture Zara tana 'kinyi Asara Zara wlh kin bani kunya da aurenki kika ringa aikata zina hardasu ciki dame Ameer ya rage ki Zara? Irin tarbiyyar Dana miki kenan Zara ooo ni Hauwa ina zan sa kaina sabida kunya wlh banyiwa iyayena haka ba Zara dawane ido kike so na kalli mutane da wane ido zan kalli Mijinki innalillahi wa inna ilahi rajuin"

Kuka mommy Hauwa takeyi sosai inda tausayin Mommy Hauwa ya rufe Ameer yace

"Mommy ki bar fad'in haka Allah ne ya jarrabceki kiyi addu'a Allah ya baki ikon cinye jarrabawarki Alhamdulillahi naji dadi data fito ta fad'i gaskiya dan banaso kuringa mun kallon mugu ko Mara mutunci danace cikin ta ba nawa bane aganina ta kai Ku wajen Adnan d'in yasan cewar kunsan ba cikina bane nasa ne nima sai yanzu hankalina ya kwanta dan wlh jiya ko runtsawa banyi ba Allah ya rabamu da san Zuciya Mommy ni zan wuce dan yau ko Hajiya ta ban gaisheta ba na taho nan.

Ameer mik'ewa yayi yana kallon Zara dake ta kuka numfashinta na Neman d'aukewa

Mommy Hauwa kuwa ta tsagaita kukan da take tace " Ameer dan Allah kayi hakuri ka haifi d'ana baka haifi Halinsa ba wlh bansan a ina ta d'ebo wanan halin nata ba wlh kunyarka nakeji"

STORY CONTINUES BELOW


Ameer da sauri yace "Haba mommy dan Allah me na bani hakuri wlh ba komai Allah dai ya shiryeta ki cigaba da mata addu'a Akan Allah ya shiryeta kuma ku tabbata kun d'au mataki akan Adnan dan kar ya barku da hidimar cikinsa"

Ameer hanyar waje yayi mommy Hauwa kuwa ta  dakawa Zara tsawa tana "dan ubanki ki tashi ki bishi ki nemi yafiyarsa ko zaki samu saukin masifar da kika janyowa kanki dan idan bai yafe miki ba bazaki tab'a ganin dai-dai a rayuwarki ba dan kin cutar dashi"

Zara mik'ewa tayi da turtsetsen cikinta tabi bayan Ameer da saurinta a lokacin har ya kusa isa gate.

Sunansa ta fara kira sabida duk saurinta bazata iya tado shi ba

Ameer kuwa ya juyo fuskarsa a had'e dan yana raga mata ne kawai dan yanajin kunyar Mommy Hauwa.

Da mugun kallo ya ringa jifanta har ta k'araso wajensa tana share hawaye.

Zara zub'ewa tayi akan gwiwarta tace "Ameer dan Allah Dan annabi ka yafemin cin amanar ka da nayi nasan nayi maka ba dai dai ba na cutar da kai ban kyauta maka ba wlh Ameer nayi dana sanin biyewa san zuciyata Ina zaman zamana Adnan ya kawo kansa wajena lokacin dayake shaidan yana ingiza ni nima sai na biye masa Ameer dan Allah ka yafemin ko zanga haske a rayuwata bansani ba ma agarin haihuwar ko rai yayi halinsa kaga idan baka yafemin ba na shiga uku"

Ameer kallon Zara kawai yake yana tuno yanda yaganta da Adnan take yaji zuciyarsa na masa zafi cikin wani irin murya mai nuna tsantsan b'acin ran da yake ciki yace "Zara kenan ai ba yanzu ya kamata kizo ki nemi yafiyata ba dan bakiga komai ba tukuna zaki nemeni a lokacin dana  iya manta  abinda kikayi min Wanda kema kinsan har na koma ga mahallicina bazan iya manta abinda kika min ba hoton yanda na ganki da Adnan yana nan a manne a idona ko mai irin sunanki naji sai yanda na ganku ya fado min Zara zan yafe miki a lokacin da zan iya manta abinda kika min  idan kuwa na kasa mantawa hoton yanda naganku namin yawo a zuciya to bazan tab'a iya yafe miki ba dan Zara kinci amanata kin ha'inceni al halin ban rageki da komai ba bakiyi nadama ba tunda Dan iskan kwarton naki na iya cewa kizo ki lankaya min cikinsa ki kuma zo ki lankayamin alhalin banji ba ban gani ba abinda ma kika min yau ya saka min mugun tsanarki Wanda nake tunanin bazan iya yafe mikin ba ki haifi shege lafiya" 16

Daga haka Ameer ya fice daga Gidan Zara tabi Sawun k'afar sa da kallo hawaye na zubo mata.

Sai data samu minti goma a zaune ta mik'e ta koma ciki.

Gabanta ne yayi mummunan fad'uwa a lokacin data ga Aunty  Khadija na rik'e mommy Hauwa akan kar ta tafi  Mommy Hauwa na tirjewa shigowarta palon yasa Mommy Hauwa ta watso mata wani irin kallo tana "Zara gwara kisan inda dare ya miki dan nima bazan iya tayaki rainon cikin shege ba Allah ya rufa miki asiri ya miki sutura kika tonawa kanki Zara kinsan hukuncin Wanda yayi zina da Aure kuwa jifansa za'ayi tayi har ya mutu ina tausayinki ne sabida na d'auka da Ciki Ameer ya sake ki Ashe ba nashi bane na shege ne tsinannan kuma yasa kika dawo gida akan ki lanka yawa Ameer cikin dayake ke jahila ce sai kika biye mishi kenan duk tsawon lokacin nan da Ameer ya sake ki kina wajen sa nabi na d'aga hankalina jinina na hawa sai daya gaji dake ya koroki kika dawo gida kenan da bai koreki ba bazaki tab'a dawowa ba ya miki kyau ni kinga tafiyata na Zare hannuna a al amuranki  Khadija kema idan kinga bazaki iya ba ki koreta ta san nayi dan yanzu gidana zan koma bazan biye Mata ba Allah yasan babu irin k'ok'arin da banyi akanta ba"

Zara wani mugun ihu ta fasa taje ta kankame Mommy Hauwa tana "Dan Allah karki min haka mommy banida sama dake karki juyamin baya a lokacin danake bukatarki gurin wa kikeso naje idan kema kin gujeni dan Allah ki rufamin asiri kiyi hakuri wlh na gane kuskurena"

Mommy Hauwa bata wani bari maganganun Zara sunyi tasiri akanta ba ta fusge jikinta tayi waje da sauri.

Aunty khadija kuwa ta dafe kanta tare da zubewa akan kujera.

STORY CONTINUES BELOW


Zara rarrafawa tayi taje ta kama k'afar Aunty khadija tana rokonta akan itama kar ta juya mata baya Aunty khadija kuwa ta fusge k'afarta tare da zuba mata harara tana "kad'an da biyewa san zuciya kenan ai ga irin ta nan kin kai Aunty Hauwa bango ta Zare hannunta akanki sai kije ki karata ke kad'ai dan idan Abban Ummi ya dawo dole kisan nayi Dan bazaki goga min kashin kaza ba"

Daga haka ta mik'e tabar Zara nata kuka tana ihun ayafe mata.


Ameer kuwa yana barin gidansu Zara kafin ya k'arasa gida yaga misscall d'in Aliya guda biyu har da text message dan hankalinta ba k'aramin tashi yayi ba  data ga da asuba bai kirata tayi sallah kamar yanda ya saba ba har wayewar gari bata ga kiransa ba Wanda hakan yasa hankalinta kasa kwanciya dan tun kafin ma ya furta Santa yakeyi yake tashinta da asuba rashin ganin kiransa yasa hankalinta tashi sai da ta kira shi ganin bai daga ba yasa tayi mishi message dan take ta rasa mai ke mata dadi.

Wani irin farinciki ne ya rufe Ameer take ya manta da wani b'acin ran da Zara ta saka mishi bayan ya karanta message d'in da Aliya tayi mishi ya juyar da kan motarsa ya nufi gidansu Aliyan yana isa ya kirata a waya.

A lokacin Aliya na kudundune a d'aki tana rik'e da wayarta a hannu ta kurawa wayar ido ko kiran Ameer zai shigo wayarta aikuwa wani irin mik'ewa tayi jiki na rawa ta d'aga wayar Ameer.

Ameer kuwa yace mata yana waje.

Durowa tayi daga kan gadon ta fad'a bandaki da sauri ta wanke fuskarta ta saka farin hijabinta tayi waje ita kanta har mamakin yanda ta kamu da san Ameer take lokaci guda.

Ameer kuwa tunda ta fito yake ta washe baki dan ko ba'a fad'a masa ba yasan yasamu karb'uwa awajen Aliya tunda har ta damu dashi haka.

Aliya kanta a sunkuye ta k'araso wajensa tana d'an kare fuskarta da Hijabinta tare da gaishe shi.

Cikin fara'a ya amsa ya ringa tsokanarta da Ashe haka itama ta damu dashi bai sani ba.

Aliya ita dai murmushi kawai take tana k'ara sunkuyar da kai sai da Ameer ya gama tsokanarta ya gyara tsayuwarsa ya kwashe duk abinda ya faru ya gaya mata babu abinda ya b'oye mata.

Aliya ba ta tab'a kallon Ameer cikin ido na minti biyar ba sai gashi ta zuba mishi ido tana kallon shi tsananin mamakin labarin daya gama bata dan bata tab'a tunanin shaidancin Zara da Adnan ya kai haka ba kullum acikin godewa Allah take daya kawo sanadin rabuwarta da Adnan da Yanzu tana nan tana kunsar bak'in cikinsa sai da Ameer ya tafa hannuwansa tayi sauri ta kau da kanta tana Allah ya shirya.

Ce mishi Tayi tana zuwa ta koma ciki ta had'a mishi abun karyawa ta kai palon saukar baki.

Ta koma wajensa tace yazo su shiga daga ciki.

Ameer bai ce komai ba yabi bayanta suna shiga ta fara zuba mishi soyayyan dankali da kwan ta zuba mishi kunun gyad'a tace ya karya kafin ta dawo ta mik'e tana k'ok'arin barin palon

Ameer da sauri ya tsayar da ita yace bazai ci ba indai ta tafi gwara ta tsaya yaci agabanta akan dole Aliya ta koma ta zauna kanta a sunkuye Ameer yafara ci yana janta da hira.

Ameer ba shi ya bar gidan ba sai wajen Sha biyun rana dan badan anata kiransa a office ba da babu inda zaije da Aliya ta saki jikinta dashi sosai suna hira inda a hirar tasu yace ta gayawa Alhaji Abubakar akan zai turo manyansa  a satin nan asa ranarsu dai-dai dana kanwarta Sumayya.

B'angaren Adnan kuwa yana tashi da sassafe yaje ya nemo masu siyan kayan gidan.

Inda yayi gwanjon  komai na gidan ya siyar ko cokali bai bari ba kayansa na sawa kawai ya zuba a cikin sabon akwatinsa da siyo sai wajen k'arfe biyu na rana ya kira Ajjidde a waya shima sai daya mata misscall uku kafin ta d'aga yace mata k'arfe hud'u zai taho da walliyinsa.

STORY CONTINUES BELOW


Ajjidde kuwa tace masa sai yazo dan itama tana nan tana shirye shiryenta ta ma tanada masa kayan da zai sa daga haka ta kashe wayarta.

Adnan wani irin farinciki ne ya ringa ratsa shi dan kamar a mafarki wai shi ne zai mallaki Ajjidde.

Waya ya buga wani  Dauda da ba shi da aikin da ya wuce zaman majalisa duk da ya manyanta babu Wanda yake huld'a dashi acikin unguwar sai shi yana d'agawa Adnan ya kora mishi jawabi akan yanaso yazama walliyinsa zai bashi dubu ashirin ya shirya k'arfe uku da rabi zai biyo su tafi.

Dauda kuwa jiki na rawa yace bari ya shirya tun yanzu ya taho sai su wuce daga nan Adnan yace to sai yazo yana jiranshi.

Dama tun safe ya Ciro kudin Sadakin Ajjidde  ya saka a wani sabon k'aramin  akwatin daya siya sabo lokaci kawai yake jira ya tafi dan har wanka yayi ya kuma saka yar tsadaddiyar shaddarsa light blue bakin takalmi da agogo ba k'aramin kyau yayi ba dan har sabon waya ya siya babu abinda yake sai murmushi yana hango yanda zai sarrafa lallausan jikin Ajjidde.

K'arfe hud'u dai-dai suka iso gidan Ajjidde acikin adai daita sahu shi da Dauda.

Mamakine ya rufe Adnan dayaga manya manyan motoci a k'ofar gidan Ajjidde kid'a nata tashi daga gidan dan tun daga nesa suka fara jiyo kid'a gate d'in gidan ma a bud'e yake cikin gidan yasha decoration har waje.

Adnan k'asa saukowa yayi daga cikin adaidaita sahun Dauda kuwa ya saki baki da hanci yana kallon gidan .

Adnan wayarsa ya zaro daga Aljihunsa ya kira layin Ajjidde bugu d'aya ta d'auka tace yana ina

Adnan yace gashi awaje

Ajjidde da sauri tace ya tsaya kar ya shigo ya bata kunya agaban kawayenta ya koma ta bayan gidan zata turo wani da kaya ya saka za'a tuko shi har cikin gidan daga haka ta kashe wayar.

Adnan yabi wayar da kallo yana hadiyar yawu tare da kara kallon jibga jibgan jeep din dake pake a k'ofar gidan.

Mai adai-dai ta sahun yacewa su koma ta bayan gidan ya sauke su yana ajiyesu ya sallameshi ya tafi ya tsaya shi da Daudu da akwatin kayan Adnan agaba.

Tsayuwarsu da minti biyar sai ga wata katuwar Jeep ruwan toka  yaji decoration din flowers da balloons ya parker agabansu.

Daudu jikinsa ne ya fara rawa Adnan kuwa yawun bakinsa ya k'afe

Zubawa motar ido sukayi bayan k'ofar motar ta  zugee a hankali wani matashi yafito daga cikin motar yace su shiga ciki.

Jiki ba kwari suka  shiga cikin motar jikinsu na rawa matashin saurayin nan kuwa ya saka musu akwatin a bayan motar  Adnan Lumshe ido  yayi sakamakon sanyi Ac da kamshin daya d'aki hancinsa.

A hankali ya dofana duwawunsa akan kujerar daudu kuwa ya zubawa plasmar dake cikin motar ido yana had'iyar yawu.

Matashin mutumin wani Leda ya janyo daga gefensa ya mik'awa Adnan akan ya saka ya d'auki d'aya ledar ya mik'awa Daudu shima akan ya sa

Cikin minti biyar matashin Saurayin nan ya taya Adnan shiryawa a cikin wani arnen gezner mai kyalli kamar mudubi ash colour hula takalmi da agogo ma Ash kana ganin shirgar jikin Adnan zaka san naira tayi kuka tsaf kayan suka masa kamar telan yasan measurement d'insa ba k'aramin kyau da had'uwa Adnan yayi ba inda Adnan ya ringa shafa kayan sabida kyaun da suka masa turarruka masu mugun tsada matashin ya fito dashi ya fara fesawa Adnan Inda Dauda da shima aka hada shi da farin shadda mai kyau da tsada har da babbar Riga hular kuwa tayiwa kansa yawa sabida k'aramin kai gareshi washe hakora kawai yake yana kallon jikinsa  yana addu'a Allah yasa su bar mishi kayan.

Adnan ji yayi kansa yayi wani irin girma a lokacin da matashin ya koma gaba yana jansu shi da Daudu daga baya.

Adnan dayake yasan komai na gayu tuni ya d'ora k'afarsa d'aya kan d'aya yana wani yatsine yatsinen fuska ala dole irin mai kudinan.

STORY CONTINUES BELOW


A hankali motar ta shiga harabar gidan Adnan kuwa ya fara kallon yanda akayi decorating wajen da za'ayi walimar ga masu serving abinci a gefe ga manya manyan Alhazawa masu ji da kansu kid'an 'yan shu'uwa kawai ke tashi.

Matashin saurayin nan yana parking ya fita daga motar yaje ya fad'awa Ajjidde akan sun k'araso tace masa ya shigo da Adnan da walliyinsa.

Inda Matashin Saurayin yayiwa Adnan da Daudu iso har wani Palon da Adnan bai san dashi ba.

Wani mutum suka tarar a palon da wata matashiyar buduruwa tana zaune a cinyarsa tayi shigar lafayya itama kanta kyakyawa ce ba laifi.

Adnan kansa ne ya d'an daure dayaga mutumin ahaife zai haifeshi amma katuwar buduruwa a cinyarsa.

Haka ya maze ya samu waje ya zauna shi da Dauda zamansu da minti goma sai ga Ajjidde ta fito da wani irin shiga kamar ta indiyawa kayan sai kyalli suke rigar iya kirjinta ya rufe sai bud'edd'en skirt d'inta da bai kai k'asa ba wajen kugunta da duwawunta kuwa wani irin jigida ne mai kyallin gaske kamar mudubi ta jerashi tunda ga wajen cibiyarta har zuwa duwawunta duk taku d'ayan da tayi sai yayi k'ara.

Gashinta kuwa yasha gyara ta baje shi a kafadarta sai kyalli yake ba ko mayafi ajikinta.

Adnan zuba mata ido kawai yayi numfashinsa na shirin d'aukewa har ta k'araso wajen Adnan ta zauna a cinyarsa tare da sakar masa murmushin dake narkar da zuciya.

Adnan k'asa maida mata martanin murmushin yayi sabida mazaunanta da yaji ajikinsa da kamshin dake fita ajikinta ido kawai ya zuba mata yana kallon ta.

Ajjidde kuwa ta d'auke kanta ta kalli wanan mutumin da har yanzu buduruwar nan na cinyarsa bata d'aga shi ba tace "Mamman nur gashi ya k'araso a d'aura mana Auren lokaci yana tafiya kasan yau kwana zamuyi muna chasu"

Adnan mamakine ya rufeshi ya zubawa sarautar Allah ido yana kallon ikon Allah inda Wanda aka kira da Mamman Nur ya ya d'aga buduruwar daka kansa ta zauna a gefensa yace to "Bismillah"

Ajjidde cikin murmushi ta juya ta kalli Adnan tace "ina Sadakin"?

Adnan cikin 'inina yace " yana cikin mota"

Ajjidde kuwa ta kalli matashin da tunda suka shigo ya kame a bakin k'ofa kamar wani soja tace " jeka kwaso  duk abinda yazo dashi "

Cikin minti biyar ya dawo d'auke da akwatin kayan Adnan dana sadakin Ajjidde Inda Ajjidde tace ya mik'o mata k'aramin akwatin dan tana kyautata zaton aciki kudin sadakinta suke.

Matashin ne ya bud'e akwatin Ajjidde ta sauko daga kan cinyar Adnan ta fara kirga rafar dubu dubu dake ciki akwatin.

Adnan shi dai sakin baki yayi yana kallon ta inda Daudu shima ya bud'e baki da hanci yana kallon sabon salo.

Ajjidde murmushi Tayi ta rufe akwatin ta kalli Mamman nur tace "kudin sun cika zaka iya daurawa ka matsa kusa dashi ku d'aura muna kallonku"

Ajjidde tacewa Daudun da yawu ke neman zubo masa sabida kallo da saurinsa ya matsa kusa da Mamman nur yana kallon sabon salon daurin aure.

Ajjidde kuwa ta koma kan cinyar Adnan tana shafa mishi Saje tana sakar masa murmushi.

Abun mamaki Mamman Nur sai da yafara gindaya sharrud'an da Ajjidde ta gindayawa Adnan tace ya zama shaida sannan  yayi sallati ya  karanta fatiha yace shima daudu yayi sallati ya karanta fatiha Daudu kuwa ya karanta kamar yanda ya umarce shi Mamman Nur kuwa ya shafa fatiha yace shikenan an d'aura Auren  Ajjidde da Adnan sun zama miji da mata
3

Daudu mamakine ya rufe shi ya juya ya kalli Adnan da shima ko ba'a fad'a ba mamakin sabon salon da suka zo dashi yake inda take wannan buduruwar dake gefen Mamman Nur ta saki wani irin gud'a Ajjidde kuwa ta rungume Adnan tana murmushi.

Adnan kamar soko haka ya zama yana kallon ikon Allah Dan Ajjidde tana cika shi ta mik'e ta fara wani irin rawa tana kad'a kugunta tare da ruk'o hannun Adnan suyi waje.


Adnan binta kawai yake abaya kamar soko ganin sun nufi wajen da akayi decoration inda manyan manyan Alhazawan ke zaune yayi sauri ya rik'e hannunta yana "Haba Ajjidde ba dai haka zakije wajen Mazan can ahaka ba kinga fa komai na jikinki awaje ko kin manta ke matar aure ce dan Allah muje ki canja kaya"
3

Wani irin kallo Ajjidde tayiwa Adnan tace "ka biyoni"?

Daga haka Tayi gaba Adnan ya fara binta abaya.

Tundaga nesa da mai kid'an garinsu ya hango Ajjidde ta taho ya saki wani irin kid'a yana zabga gud'a kamar mace.

Ajjidde kuwa da rawa ta k'arasa tsakiyar filin ta fara wani irin rawa tana gantsaro kirjinta tana kad'a kugunta.

Aikuwa Alhazawan nan d'aya bayan d'aya suka fara tasowa suna mata liki inda Hankalin Adnan yayi balainy tashi dan duwawun Ajjidde suke kaiwa duka suna matsewa da hannu suna zuba mata ruwan kudi ita kuwa sai tura musu duwawun take Inda wasu kuma suka ringa zubawa kirjinta shafa da liki wasu har da d'an rungumeta.
Wai ahaka da sunan sun zo tayata murna Auren da tayi suke

Wasu mata goma ne suka fito daga wani k'ofa sun sha shigar lafayya da manya manyan jakankuna suka zo suka zagaye Ajjidde suka tsugunna suna kwasar kud'in da ake likawa Ajjidde.

Ajjidde kuwa kamar zata balle ta cigaba da taka rawa dan likin da suke mata shine tamkar gudunmawarsu 


Adnan cikin tsananin tashin hankali yashiga tsakiyar filin yajawo Ajjidde  da k'arfinsa sabida wani mugun kishi daya rufe masa ido Ajjidde kuwa ta juyo ta zabga mishi mari........

Post a Comment for "MAKOTAN JUNA CHAPTER 8"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...