Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

MAKOTAN JUNA CHAPTER 7

MAKOTAN JUNA CHAPTER 7

- - Post a Comment
MAKOTAN JUNACHAPTER 7First class olosho tankwarariyar karuwa datayi gadon karuwanci a wajen Mahaifiyarta Nura inda itama Nuran gadonsa tayi wajen Mahaifiyarta Kanzel asalinsu 'yan shu'uwa ne Neman kudi ne ya fara kawo kanzel Nigeria inda a lokacin babu Wanda ya kaita kyau da diri hakan yasa manyan masu kudi da siyasa suke ringa rububinta suna kashe mata kudi a ciki wani Wanda bata San kowaye ba sabida yawan mutanen da take mua'amalla dasu ya mata ciki ta haifi Nura Inda itama Nura ta yo gadon kyaunta babu inda ta barta ahaka ta taso a hannun Kanzel inda tana da shekara 12 customers d'in Kanzel suka fara komawa kan Nura inda ita kuma Kanzel tayi retire sabida cutar sanyin data kwasa awajen wani bature sai ta d'ora Nura akan harkar tana samun mahaukatan kudi dan sai ka dire manyan kudi zata sallama maka Nura.
+

Nura itama sai data zo ta ninka Kanzel a karuwanci dan ita har k'asar Saudiya take zuwa Anan ta had'u da wani Balarabe da ya biya ta mahaukatan kudi akan ta huta dashi har na tsawon shekara d'aya batare da ta kula wani ba a cikin shekara d'ayan ta haifo 'yarta Ajjidde datayi gadon kyau da kyau wajen uwa da uba inda Balarabe da Nura ta gama shekara d'ayarta ya mata babban sallama ta k'ara gaba ahaka ta cigaba da zama a saudiya tana kula da Ajjidde.

Ajjidde tun tana da shekara shidda a duniya zaka ga irin baiwar kyau da diri da Allah ya mata Wanda ya kai ya kawo Nura sai da ta koma Sanya mata hijab sabida gudun kar ayi mata fyad'e.

Tun Ajjide nada shekara goma Nura ta fara mata wani irin gyara da tsumi sabida yanda Manyan alhazawa suka fara kai mata hari suna rokonta akan zasu bata ko nawa takeso indai zata basu Ajjidde

Nura kuwa hakane yasa itama ta fara tunanin lokacin ritayanta yayi sabida itama tana fama da cutar sanyi yanzu bata da kwarin da zata iya cigaba da hark'ar.

Ajjidde nada shekara goma sha biyu Nura ta bada ita ga wani Alhaji da ya dire mata makudan kudade da gwalagwalai inda shi ya fara amshewa Ajjidde budurci daga nan kuma Ajjidde ta zame mata source of income dan tamkar ita kad'ai ce mace duk da kankantar ta rububinta ake yi dan har su Dubai England Nura tura ta take yi ta samo musu kudi.
2

Ajjidde nada shekara goma sha shidda Nura ta rasu bayan rasuwarta da shekara d'aya Ajjidde ta tattara duka dukiyar da suka mallaka ta dawo gida Nigeria wajen Kanzel a lokacin Kanzel ta tsufa sosai tana fama da wani irin cuta sabida kudin da suke dashi yasa ake mata kula na musamman ana siya mata magunguna.


Kanzel kamar jiran dawowar jikarta take itama ta amsa kiran Mahallici bayan ta damkawa Ajjidde dukan dukiyarta.

Tunda Ajjide ta duro Nigeria 'yan bariki da Manyan Alhazawa suka kyallara ido suka ganta suka fara layi akanta.

Ajjidde ba kowa take kulawa ba sai Wanda ya tada Kai sosai dan wayayya ce ta tashin hankali.

Shekarata hud'u kenan da dawowa Nigeria inda take buga runs d'inta da isassu kudi ne da ita kamar su kasheta banda dukiyar da Nura da kanzel suka bar mata.

STORY CONTINUES BELOW


Ita kad'ai ke zaune a wani makekken gidan data gina da kudinta bata yarda tabi kowa sai dai ka biyota har gidanta kayi abunda ya kawoka ka bata kudinta.wanan kenan

*ADNAN*


Adnan sai k'arfe d'ayan dare ya koma gida Ajjidde na masa gizo duk fitar numfashinsa sai San Ajjidde ya linku a ransa koyaya ya d'an runtse idonsa sai ya hango yanda ta zuba masa lumsassun idonta tana kashe shi da murmushi Allah Allah kawai yake gari ya waye ya kirata yaji zazzakar muryarta can k'asan ransa kuma yana fargabar rasata dan ko fatar ta da suturar jikinta kawai da ya kalla yasan kudi sun zauna mata Allah yasa kar ta k'i Aurensa.

A lokacin da ya isa gida a palo ya tarar da Zara da turtsetsen cikinta kamar wacce zata haifi 'yan biyu a cikin irin rigunan da ya siya mata ta saka wani doguwar Riga mai zubin buba kana ganinta kasan kwalliya Tayi dan tunda ta daina laulayi ta dage da kwalliya ko zata karkato da hankalin Adnan ya daina mata wulak'anci dan tasan bata da sama dashi dan bata isa ta soma dosar gidansu ba idan ya koreta.

Adnan kallo d'aya ya mata ya d'auke kansa.

Zara da bacci ke dan kwasarta ta mik'e da sauri tana masa sannu da zuwa.

Adnan Hannu kawai ya daga mata ya shige d'akinsa.

Zara kuwa ta mik'e ta bi bayansa.

Bandaki ta shige ta had'a masa ruwa ta fito ta same shi yana cire kayan jikinsa ko kallonta baiyi ba.

Murya na d'an rawa tace "Ad ga ruwa can na had'a maka"

Adnan juyowa yayi ya watsa mata wani mummunan kallo yace "na rokeki ki zuba min ruwane wai ni mai hadina dake ne bana hanaki shigo min d'aki ba"

Zara idonta ne ya ciko da hawaye tace "ka hanani Adnan amma aganina bai kamata ka d'auki irin wanan matakin akaina ba dan ban cancanci haka daga wajenka ba karka manta duk halin da muke ciki Kaine silar komai bai kamata ka ringa gwada min kiyayya haka ba Adnan ayanzu banida Sama dakai dan Allah ka dubi girman Allah ko Dan cikin danake dashi ka ringa sasautamin"
Tace hawaye na zubo mata

Adnan zama yayi akan katifar yace "zo nan ki zauna magana zamuyi"

Zara da sauri ta nufi wajensa tana goge hawayen dake zubo mata ta zauna a gefensa tana dan murmushi dan a tunaninta maganar ta ya shige shi shiyasa yakeso suyi sulhu.

"Saura wata nawane ki haihu"Adnan yace yana kallon cikin ta

" Saura wata biyu na haihu yanzu cikina wata bakwai"

"Yauwa kina jina Zara kinaso idan kin haihu na Aureki ko"?

Zara da sauri ta girgiza masa kanta yace " yauwa shawara gareni zan kuma baki Idan kin dauka to idan baki dauka ba ruwanki idan kin haihu inaso mu kai abinda kika Haifa gidan rainon yara basai kinsha wahalar wani shayarwa ba idan yaso sai ki koma gida ni kuma zan roki yafiyar iyayenki daga nan sai na nemi aurenki awajensu kinga bai kamata ki je musu da dan shege ba bazasu ji dadi ba kuma bai kamata mu cigaba da zama ahaka babu aure ba amma idan aure mukayi sai hankalinki da hankali na Sai yafi kwanciya"

Tunda ya fara magana Zara ta zuba masa ido tana kallonsa har ya kai aya sai data kwashi kusan minti Biyar kafin tace "Adnan na kai abinda na Haifa gidan rainon yara fa kace idan har zan iya jure duk wahalar dana sha akan cikin nan sai na haifo shi kuma sai na wani kai shi gidan marayu a gaskiya bazan iya ba Adnan inasan abunda ke cikina karka damu indai iyayena ne nasan yanda zan bi dasu.


Adnan d'aura fuskarsa yayi yace "toh tunda kince haka ke bakya gudun abun kunya bari kiji na fad'a miki kina haihuwa ki koma gidanku da abinda kika Haifa dan kinsan dai wanan gidan gidan haya ne ba nawa bane yanzu ba wani Sana'a gareni ba ballantana inta dawainiya dake da shegen da zaki Haifa kina kallo sai da yunwa yakusa kasheki a gidanan kafin nasamu na kuma siyo miki kayan abinci dan ke kadai kike ci banda ni Dan kina haihuwa zan koma Maiduguri na nemi aiki acan k'ila na samu kinga kuma babu yanda zan iya tafiya dake da shegen da zaki Haifa dan 'yan uwana sun San bake ce mata ta ba kuma dole zasu tambayeni mai hadina dake kinga da kunya ince zaman daduro mukayi dake har kika haihu dani dan haka ki fara shiri kina haihuwa zaki koma gidanku"

STORY CONTINUES BELOW


Adnan yace yana kau da fuskarsa daga kallonta dan so yake ya yakice Zara daga Rayuwarsa k'arfi da yaji dan da ta bashi had'in kai ahaka zai lallabata ta koma gidansu yaje ya Auri Ajjidde hankalinsa a kwance.

Zara kallon Adnan kawai take hawaye na zubo mata bata tab'a nadama kamar irin yau da take zaune a kusa da Adnan ba tabi San zuciyarta da rudin shedan ta biyewa Adnan gashi yau ita take shan wahala shi kuwa burinsa ya yakice ta ya huta tunda gashi har yana cewa zai korata gida ya koma Maiduguri da zama.

Adnan kuwa ganin tana koke koke yasa ya mik'e yayi shigewarsa band'aki yabar ta a wajen.


Zara itama mik'ewa tayi ta koma d'akin ta inda ta kwana tana kuka da nadama abinda tayi da ace da waya a hannunta da babu abinda zai hana ta kira Mommy Hauwa ta fara Neman yafiyar ta dan tasan hakkinta ke dawainiya da ita Ameer da ta tuna ne yasa ta kara volume din kukanta dan tasan shima alhakinsa ne ya kamata Adnan ke wulakantata haka babu abinda yake d'aga mata hankali kamar idan ya koreta ina zata koma dan tasan Mommy Hauwa bata da wani matsala zata iya yafe mata Dr fa korarta zaiyi idan bai biyota da duka ba.

Aranar Zara Sam bata runtsa ba in banda kuka da ta ringa yi Wanda hakan ya haddasa mata ciwon kai.

Adnan kuwa yana fitowa daga wanka sallah yayi shap shap ya zube akan katifa ya fara aikin tunanin Ajjidde idonsa akan agogo dan gani yake lokaci baya tafiya yayi dailing number ta yafi a kirga dan ji yayi sai yama ji muryarta zai iya bacci amma kash wayarta a kashe take haka yayi ta juyi akan katifa San Ajjidde na huda ilharin jikinsa sai wajen k'arfe hud'u bacci yayi awon gaba da ita cike da mafarkin Ajjidde.

Washegari tunda safe Adnan ya ringa gwada wayar Ajjidde amma a kashe hankalinsa idan yayi dubu ya gama tashi zirga zirga kawai yake yi a palon dan ji yake kamar zai iya mutuwa idan baiji muryarta ko yaganta ba ahaka ya rik'e waya a hannunsa yana aikin gwada kiranta duk da bak'ar yunwar da yake ji hakan bai sa yayi tunanin ya nemi abunda zai sa a cikinsa ba.

Zara kuwa tun kafin Adnan ya farka ta dafa taliya mai da yaji ta juye a kula ta koma d'akinta dan Adnan wani zubin ce mata yake tafiye ci yayi ta mata wulak'anci iri iri shiyasa take rigashi tashi ta dafa abinda zata ci wani zubin sai yafita take fitowa daga d'aki kid'an da ya ware a gidan ne yasa ta k'asa komawa bacci tayi zamanta tana tunanin Halin da take ciki idan ka d'auke cikin daya rufa mata asiri ta d'an murmure da ba k'aramin rama zatayi ba.


Adnan haka ya cigaba da gwada wayar Ajjidde mintuna mintuna sai k'arfe goma sha biyu na rana yaji wayar ta shiga

Mik'ewa yayi da sauri yana jin wani sanyi aransa dan ji yake kamar har ta d'aga wayar.

Sai da yayi mata 10 misscal kafin ta d'aga

Adnan gabansa na d'an fad'uwa yace cikin kwantar da murya "Hello ranki ya Dade ina kwana"

Ajjidde da bud'e idonta kenan ta bud'e wayarta kiran Adnan ya shigo wayarta sai da bacci ya d'an saketa ta d'aga wayar tana d'aga wayar tayi shiru sai da Adnan ya k'ara gaisheta tace "Lafiya"

Adnan da sauri yace "am so sorry for disturbing u Ajjidde Allah ya jarrabceni da mugun kaunar ki wlh jiya ban runtsa ba tunaninki kawai na ringa yi daga jiya zuwa yau ji nake idan bake bazan iya rayuwa ba dan Allah Ajjidde ki taimaka ki saurareni Aurenki nakeso nayi"

Ajjidde waro ido tayi kamar yana gabanta tace "Aure"???

Adnan da sauri ya gyad'a kansa yace " eee Aurenki nakeso nayi tunda nake ban tab'a yiwa mace irin San danaji ina yi miki ba pls kibani chance nazo gidanku yanzu muyi magana "

Ajjidde shiru Tayi tana tunanin abinda ya dace tayi dan itama haka kawai jiya da ta dawo gida Adnan ya ringa fad'o mata duk da ta had'u da mazan da suka ninke Adnan a kyau had'uwa da komai Haka kawai taji Adnan ya kwanta mata

STORY CONTINUES BELOW


Ajiyar zuciya ta sauke tace "sultan road gida mai lamba shidda kazo ka sameni k'arfe hud'u na yamma"

Kafin Adnan yace wani abu har ta kashe wayar

Adnan bin wayar hannunsa yayi da kallo fuskarsa d'auke da murmushi wani irin kiss ya kaiwa wayar tamkar Ajjidden yake yiwa kiss ya daka tsalle yana "yes"

Dan ji yake kamar Ajjidde har ta amince zata Aure shi.

Adnan volume din kid'a ya k'ara warewa sai da yayi rawa San ransa dan tsabar murna kafin ya zube akan kujera ji yayi yama daina jin yunwar a koshe yake.

Sai da ya huta yayi hanyar waje bayan ya cika bokitai biyu da ruwa

Wanke motarsa yayi sosai ya gogeta daga nan ya shige cikin gida ya nufi d'akinsa ya ringa zaro goggagun kananan kayansa yana duba Wanda ya kamata ya sa idan zaije wajen Ajjidde dan so yake ya burgeta sosai duk da can k'asan zuciyarsa yana tunanin Ajjidde tafi k'arfinsa dan tunda tace Sultan road yasan ba k'aramin yar gidan masu kudi bace.

Wani farin Riga ya d'auko mai bak'in rubutu Wanda ya siye shi kwanan nan sai bak'in wandonsa ya d'auko wani bak'in agogonsa da ya siya dubu goma sha biyar tun lokacin dayake aiki a company sai wani cover shoe d'insa baki da shima dubu goma sha biyu ya siye shi tun lokacin da yake aiki.

Polishing d'in takalmin yayi sosai ya ringa kyalli.

Sai da yagama had'a kan kayan waje d'aya ya koma Palo ya zauna ya cigaba da kamo tashoshin wake wake ko sau d'aya baiyi tunanin duba Zara ba lura da tunda ya tashi baiji motsinta ba.

Ahaka ya rage lokaci yana kallo karfe 3:30 ya fad'a wanka ya dirje jikinsa kamar zai canza fatar jikinsa.

Yanda mace ke d'aukan lokaci agaban mudubi tayi ta kwalliya haka Adnan ya tsaya agaban k'aramin mudubi dake d'akinsa ya ringa kallon kansa dan har hod'a ya shafa duk Dan ya burge Ajjidde.

Brushing kansa yayi sosai ya k'ara gyara sajensa Wanda hakan ya k'ara fido da zahirin kyaunsa turarruka wajen kala shidda ya fesa.

Gyara tsayuwarsa ya ringa yi ya ringa practising irin maganganun da zaiyi wa Ajjidde tamkar yana gabanta sai daya d'ago yaga hud'u saura minti goma ya d'auki mukullin motarsa yayi waje.

Zaran da yunwar rana yasa ta fito daga d'akin dan ta samawa kanta abinda zata ci.

Sakin baki tayi tana kallon Adnan kirjinta na wani irin harbawa dan wani irin kyau Adnan yayi kamar bashi ba gyaran da yayiwa gashinsa yafi tafiya da imaninta ga wani irin kamshi da ya bad'e palon.

Adnan ganin ta zuba masa ido kamar bata tab'a ganinsa ba yasa ya sakar mata murmushi tare da kanne mata ido d'aya

Zara Saura kiris numfashinta ya d'auke

Adnan gabanta ta k'arasa ya tsaya ya k'ara gyara zaman goggagen rigarsa yace "nayi kyau"?

Zara ji take kamar ta fad'a jikinsa ta rungume shi da sauri tace " kayi kyau Ad sosai kamar ba kai ba"

"Haka nakeso bari na tafi sai na dawo idan dai na samu abinda naje nema Yau zan siyo miki nama kici ki ture"

Zara da sauri ta fara zabga masa addu'a kamar wacce bata tab'a cin nama ba dan ta manta rabonta da taci"
2

Adnan cool music ya saki a motarsa ya ringa tuki a hankali yana jin wani irin dadi na shigarsa duk minti d'aya sai ya d'aga kansa ya kalli kansa a mudubi.

Karfe hud'u da minti shidda ya k'ara so k'ofar gidan inda gabansa ya ringa wani irin fad'uwa sabida kyau da haduwar gidan haka kawai yaji jikinsa yayi bala'in sanyi dan a gaskiya Ajjidde dak'yar ta yarda ta aure shi dan Sam bashida kudin ma da zai iya aurenta.

STORY CONTINUES BELOW


Sai da ya samu minti goma a bakin gate yana karewa gidan kallo kafin ya tattaro d'an sauran kwarin gwiwar data rage masa yafito daga motar dan Sam bama zai shiga da motarsa ba.

Kwankwasa gate d'in ya fara yi mai wani buzu ya leko yana tambayarsa wa yake nema"

Cikin rawar baki yace masa Ajjidde yake nema mai gadin kuwa yabisa da kallo tundaga Sama har k'asa dan Sam baiyi kala da Wanda zai nemi hajiyar tasa ba dan manyan Alhazawa ke zuwa wajenta amma kuwa wnan dayazo nementa bai wuce mai mata wankin kayanta ba.

Adnan kuwa ransa ne ya baci dayaga irin kallon da yake masa hakane yasa ya zaro wayarsa daga Aljihunsa yayi dailing number Ajjidde  sai da yayi ringing sau hud'u kafin ta d'aga.

Adnan ce mata yayi gashi nan a bakin gate maigadi ya hana shi shigowa.

Ajjidde dake kwance  da wani Alhaji daya shigo gari wajenta kashe wayar tayi ta kira mai gadin tace ya barshi ya shigo daga haka ta kashe wayar ta kalli Alhajin tace "lokacin tafiyar ka yayi  dan bakona ya iso"

Alhajin kallon Ajjidde yayi kamar zaiyi kuka yace "Dan Allah kibari na kwana zan kara miki kudi wlh ban gaji dake ba"

Ajjide mik'ewa tayi tace "aaa sai wani lokacin kuma yanzu inada bako"

Daga haka ta mik'e ta saka doguwar rigarta ta mik'a masa hannunta.

Ya mika mata d'an k'aramin akwatin dake cike da kudi.
Ta bud'e drawer dinta ta saka a ciki ta juyo tana jiran ya gama saka kayansa ta raka shi.

Adnan tunda ya shiga cikin gidan jikinsa ya d'au rawa yana kallon makeken gidan da manya manya jeeps d'in dake pake a gefe tuni yaji makoshinsa ya bushe ya cigaba da bin gidan da kallo.

Acikin wanan halin Ajjide suka fito da Alhajin zata raka shi ya tafi.

Inda Adnan Sam bai lura da fitowarsu ba sabida shagala da yayi yana kallon gidan.

Alhajin kuwa da sauri ya juya ya kalli Ajjidde yace "kar dai kice min wanan Almajirin ne bakon naki haba Ajjide wlh wnan ba girmanki bane yanzu akan wanan da bai wuce ya goge min takalmi ba zaki koreni"

Ajjidde murmushi tayi tace "eee fa akansa zan koreka ko nawa zaka bani bazan ki sauraransa ba kaje kawai sai munyi waya"

Daga haka tabar shi a tsaye ta nufi wajen Adnan daya zama soko yana kalle kalle.

"Bismillah zomu shiga daga ciki"

Adnan yaji muryar Ajjidde ya doki dodon kunnensa

A firgice ya dawo da kallonsa kanta inda numfashinsa ya kusa barin gangan jikinsa dan gani yayi Ashe kallon dare yayiwa Ajjidde kyaunta yafi ganin da ya mata jiya dan doguwar Riga ce ajikinta babu dankwalli gashinta na reto a baya babu bra ajikinta da alama babu komai a jikinta idan ka d'auke doguwar Riga dake jikinta.

Tamkar soko haka Adnan ya ringa binta abaya yana karewa bayanta dake sittin saba'in Dari da hamsin kallo karar tada mota ne yasa ya juya ya kalli parking space inda ha had'a ido da wanan Alhajin ya zabga masa wani mugun harara.

Adnan da sauri ya d'auke idonsa yana tunanin waye wanan da ya masa irin wanan kallon ko dai yayanta ne.

Ahaka ya Ringa tunane tunane har suka shiga palon gidan daya kusa sawa ya zube a k'asa sabida haduwarsa.

Ajjidde kujera ta nuna masa tace ya zauna ta hau kwallawa 'yar aikinta kira.

Da sauri yar aikin tazo gabanta ta tsaya

Ajjidde tace ta kawo masa abun motsa baki kafin ta fito daga haka ta juya ta shige cikin d'akinta.


Adnan kuwa tunda ya zauna yaji gabansa na balain fad'uwa dan yasan Ajjidde Sam ba class d'insa bace kyaunta ma kawai yasa yasan ta wuce ajinsa tuni hankalinsa ya tashi yafara tunanin yanda zai soma rayuwa idan tace bazata aure shi ba duk da yasan ma yaudarar kansa yake bazata aure shi ba dan bashida arzikin da zai aureta.

Abun motsa baki yar aikinta ta cika masa agabansa  dashi Wanda kamshin ferfesun kazan dake tashi yasa yawunsa tsinkewa  tuni yaji tsohon yunwar sa ta tashi amma tsoro yasa ko ruwa ya k'asa d'auka ya sha.

Manyan  Hotunan Ajjidde dake jikin bangon palon kawai yake bi da kallo cikinsa na tsurewa.

Yana nan a zaune har karfe biyar Ajjide bata fito ba 

Adnan kuwa sai muskute muskute yake ga wani mugun yunwa dayake ji kamar ya sa hannu ya fara cin abubuwan dake gabansa.

Biyar da minti goma sha biyar Ajjide ta fito daga d'akinta taci kwalliya da wani Riga da skirt baki da ja tayi parking gashinta kamshi turarenta ya cika palon.

Adnan bai San lokacin da ya mik'e ya tsaya ba sabida yanda kyaunta ya Kara girgiza shi murmushin data sakar masa ne yasa ya k'ara zubewa akan kujerar.

Ajjidde kuwa tazo kusa dashi ta zauna tana "sorry for keeping u waiting nayi wanka ne"

Adnan kamar soko kallonta kawai yake ko kiftawa bayayi.

Kallon abunda aka jera masa agabansa tayi taga ko tab'awa baiyi ba tace "Idan kanaso muyi magana ka tabbata kaci abinda aka baka dan ba'a zuwa gidana batare da anci wani abu ba"

Adnan gidana gidana kawai ya ringa nanatawa aransa ya hau tambayar kansa me take nufi da gidanta ko dai zaman kanta takeyi gabansa ne yayi wani irin fad'uwa a lokacin da ya zuba mata ido adai dai lokacin da ta dauki remote tana k'unna katon plasma dake jikin Bangon palon........Sai da ta kamo tashar da take so ta juyo taga har lokacin Adnan kallonta yake yi +

Murmushi tayi tace "Ya dai wanan kallo haka ko dai na canja maka ne dan Allah kasa hannu kaci idan ka gama muyi magana in kuma in koma d'aki idan ka gama ci sai na fito"

Ajjidde tace tana mik'ewa

Adnan murmushi yayi yace "yi zamanki zanfi jin dadin ci idan ina kallonki"

Murmushi tayi ta d'auke kanta ta maida kanta kan TV

Adnan kuma ya fara cin abincin da aka jera masa agabansa yana ci yana kallonta ji yake kamar ya tashi yaje ya rungume ta sabida yanda wani irin shaukin  santa ke dibarsa babu abinda yafi tafiya da imaninsa kamar  kwantacen gashin  dake  gefen wuyanta da bak'in  tattoo  dake kwance a wajen.

Ganin ta maida hankalinta kan kallon da take bata kara juyowa ta kalleshi ba yasa ya saki jiki yaci ya koshi.

Sai da ya goge bakinsa da handkerchief d'in dake hannunsa ya d'an ture glass table d'in dake gabansa yace mata "Am done"

Ajjidde juyowa Tayi da murmushi a fuskarta tace "yauwa to zamu iya magana yanzu wats ur intention towards me"?

Adnan murmushi ya sakar mata dayake narkar da zuciyar ' yan mata yace " Ajjidde kamar yanda nafad'a miki a waya am madly in love with u so nake miki irin Wanda ban tab'a yiwa wata 'ya mace ba wlh daga jiya zuwa yau d'inan ni kad'ai nasan mai nakeji akanki Ajjidde sanki nake da Aure ina so ki zamo uwar 'ya'yana duk da nasan I don't wort u but pls ki soni ki ceci rayuwata cos I cant live without u"

Ajjidde ido kawai ta zuba masa tana kallonsa har yayi shiru yana sauraran abinda zata ce

Sai da suka kwashi minti goma ahaka inda Adnan yafara shan jinin jikinsa kirjinsa na d'an bugawa dan Sam bai gane kallon da take masa ba tundaga sama har k'asa.

Ajjidde ajiyar zuciya ta sauke ta kau da kanta tana "wat do u do for a living wane irin Sana'a kake"?

Adnan kirijinsa ne ya hau bugawa take zufa ya hau keto masa dan bai San ya zai iya bud'e baki yace mata shi DJ bane bashida wani Sana'a shima yasan ya yaudari kansa idan yana tunanin Ajjidde zata so shi ta kuma aureshi a matsayinsa na DJ gashi ba dama ya mata karyar wani abun tunda bashida abinda zai mata karyar jiki a sanyaye ya bud'e bakinsa da ya masa nauyi can k'asan mak'oshi yace "banida wani Sana'a da nake yi Ajjide ni DJ ne but pls kar hakan yasa ki k'i saurarana am still looking for Job insha Allahu nasan zan samu"

Ajjidde tunda ta kau da kanta bata juyo ta kalleshi ba har ya gama maganarsa tambaya ta K'ara jefo mishi tana "nawa kake samu idan aka kiraka "?

Adnan jikinsa ne ya fara rawa kirjinsa na bugawa dan yasan Ajjidde tafi k'arfinsa bazata wani saurareshi ba cikin rawar murya yace " bana samun sama da 10k idan anyi liki sosai shine nakesamun 15 aciki na sallami yarana"

STORY CONTINUES BELOW


Ajjidde sai a lokacin ta juyo tana kallonsa

Adnan kuwa Sam bai gane expression d'in fuskarta ba hakane yasa jikinsa balain sanyi hankalinsa ya tashi dan Allah ya jarrabace shi da mugun kaunarta

Haka suka kuma kwasar wani minti goma kafin Ajjidde ta sauke ajiyar zuciya tace " And a hakan kake so ka aureni"?

Adnan cikin rawar baki yace "am sorry nasan kinfi k'arfina ba laifina bane laifin zuciyata ne daya kamu da San wacce tafi k'arfinta but pls ki taimaka ki ringa kulani ahaka kila na samu space a zuciyarki har ya kai da kiji kina kaunata"

Ajjidde murmushi tayi for d first time da ta kira sunansa inda Adnan yaji Ashe haka sunansa keda dan banzan dadi sabida yanda ta kira sunansa cikin zakin muryarta

"Adnan u knw wat I dont love u but I like u ba wai na rainawa samunka bane ina ganin u can not meet my needs gaskiya and apart from that bani da intention din Aure yanzu but zan iya auranka on one condition"

Adnan da sauri yace "What condition"?

" Take me out"

Adnan gabansa ne ya yanke ya fadi hankalinsa ya tashi amma bai bari tagane hankalinsa ya tashi ba ya maze ya kirkiro murmushi yace "Any thing for u princess"

Ajjidde murmushi ta sakar masa ta mik'e ta nufi d'akinta

Tana shigewa Adnan ya dafe kansa dan yasan bashida kudin da zai iya kashewa Ajjidde  ya burgeta amma ya zaiyi haka zai Ciro ko da 50k ne ya kashe mata palon ya ringa bi da kallo yana ganin irin dukiyar da aka narka aciki tunani ya fara yi na inda iyayen Ajjidde suke dan yasan ba ita kad'ai ce a cikin irin wanan tamfatsetsen gidan ba bari ta fito yace mata zai gaida iyayenta"
2

Ahaka ya zauna yana kalle kalle har Ajjidde ta fito ta same shi

Numfashin Adnan ne ya kusa d'aukewa dayaga wani irin hadaddiyar doguwar Rigar da tasa Wanda ko ba'a fad'a masa ba yasan naira tayi kuka wajen siyan ta

Har ta k'ara so kusa dashi bai d'auke idonsa ba kallonta kawai yake.

Murmushin da ya zama tamkar dab'iarta ta sakar mishi tace "mutafi ko"

Adnan murmushi shima ya sakar mata yana sauke ajiyar zuciya yace "inaso na gaida mom dinki kafin mu  tafi dan nasan Dad dinki baya nan"

"They are late I leave alone"

Ajjidde tace tana kashe kayan kallon tare da kwashe wayoyinta dake kan kujerar ta zubasu cikin tsadaddiyar Jakarta"

Adnan da sauri yace "eyya am sorry Allah ya jikansu da rahama"

Ajjide ameen kawai tace Tayi gaba Adnan ya bita abaya yana tunanin irin kudin da iyayenta suke dashi kafin su mutu haka kawai yaji wani irin farinciki na ratsa shi daya tuna idan har Ajjidde ta amince zata Aure shi yasan yayi hanun Riga da talauci.

Maganar Ajjidde ne ya katse masa tunanin da yake "where is your car"

Adnan da sauri yace "is outside Allah yasa ki iya hawa"

Ajjidde bata ce komai ba har suka fita waje inda Adnan yayi saurin bud'e mata motar ya rufe shima ya zagaya ya hau ya k'unna Ac yaja motar suka tafi.

Ita da kanta ta gaya masa Mall d'in da zai kaita

Inda Cikin Adnan ya duru ruwa dan yasan sai Wanda ya isa ya tada kai ke iya zuwa wajen

So yake yace mata bashida kudin da zai iya mata siyyaya awajen amma ya kasa dan kau da kanta tayi tana kallon waje tunda suka fara tafiya.

A banki ya fara tsayawa ya cire 50k kafin suka K'arasa mall d'in.

Adnan shi kansa duk wayewarsa bai tab'a zuwa wajen ba tamkar Dan kauye haka ya koma Ajjidde kuwa dayake ta saba zuwa bata wani tsaya kalle kalle ba ta hau zabar abubuwan da takeso.

STORY CONTINUES BELOW


Abu biyu kawai da ta d'auka 100k ne .

Hankalin Adnan idan yayi dari ya tashi matsawa yayi kusa da ita da sauri ya kankantar da muryarsa yana cewa bashida kudi 50k ne kawai a Aljihunsa.

Ajjidde ko dagowa batayi ta kalleshi ba har ta gama kwasar abinda zata kwasa ta nufi inda ake biya bayan tace Adnan ya biyota.

Adnan kamar ya saki fitsari ya d'iba da gudu dan yasan ya gama shan kunya Ajjidde bai kamata tayi masa haka ba tunda tasan bashida da kudi.

Cikinsa ne yayi wani irin kullewa dayaji bill d'in kayan da ta siya dubu dari biyar da hamsin.
Wani irin gumi ne ya hau keto masa.

Ajjidde kuwa ta juya fuskarta d'auke da murmushi tace yayi settling bill d'in

Adnan ido ya gwagwalo yana kallonta ya kasa ko motsawa.

Ajjidde kuwa ganin yanda Adnan ya tsure ya gigice yana narka gumi yasa ta saki murmushi duk hakoranta suka fito ta sa hannu a Jakarta ta Ciro ATM card d'inta ta mik'a musu suka ciri kudin.

Ta kwashi ledoji biyun da aka saka mata kayan a ciki tayi gaba Adnan ya bita abaya jiki asanyaye yana tunanin meyesa tayi mishi haka  ko Dan ta nuna masa bazai iya aurenta bane tafi k'arfinsa 

Ahaka ya ringa binta abaya har suka karasa inda yayi parking motarsa ta ajiye kayan akan motarsa ta juyo tana kallonsa  da wanan murmushin nata.

Adnan shima kallon nata yake yi jiki ba kwari dan yasan zaginsa zatayi sabida ya kasa biya mata idan ba ganganci irin nasa ba ina shi ina Ajjidde.

Ajjidde ce ta katse masa tunanin da yake yi tace "nace ka fita dani ne  sabida idonka ya gane maka irin luxurious life danakeyi this is how I spend money on perf and cream I used a rana bana kashe k'asa da dubu dari can u still marry me"?

Adnan yawu ya hadiye mai kauri dan ya jika makoshinsa daya bushe  jikinsa ya fara rawa

Ajjidde kara tambayarsa tayi tace " zaka iya aurena ka cigaba da hidimanta min kamar yanda na saba"?

Adnan shiru yayi ya cigaba da kallonta sai da ta k'ara tambayarsa  akaro na uku Adnan ya bud'e bakinsa dak'yar yace 2

"Ajjidde ba laifina bane dan na kamu da matsanacin sanki nasan nima na yaudari kaina idan nace zan iya aurenki dan nasan kinfi k'arfina am no body I have nothing but ya zanyi zuciyata bata min adalci ba with wat u just said nasan nasan bazan iya auranki ba banida kudin da zan iya meeting need dinki"

Adnan yace muryarsa na cracking kana ganin Cikin idonsa zaka hango tsantsar tashin hankalin da yake ciki na rasa Ajjidde.

Ajjidde murmusawa tayi tana tunanin hukuncin kawai da ta yanke na Auren Adnan at least bai kamata ace rayuwar da kanzel da Nura sukayi ba aure ace itama tayi irin wanan rayuwar ba kamata yayi ita  kuma ta Auri irin Adnan ta ringa juya shi San ranta tana cigaba da barikinta dan dama auran mai kudi zai hanata tayi abubuwan da takeso but auren Adnan da bashida komai zai sa ta cigaba da abubuwanta dan bashida powern da zai hanata cigaba da sana'arta da wanan tunanin  tace "I know nafi karfin aurenka na girmi ajinka but ba hakane zai sa naki auranka ba but on just on one more condition".

Adnan jiki na rawa da d'an hope d'in bazai rasa Ajjidde dayake jinta tamkar fitar numfashinsa ba yace " am ready for any condition indai bazai sa ki k'i aurena ba"

Ajjidde girgiza kanta tayi tace "inka Aureni zan cigaba da sana'ar danakeyi cos da sana'ar da nake yi kagani a Wanan stage d'in kuma har na baka sha'awa kaji kana sha'awar aurena  2 aurena bashi yake nufin zaka mik'a k'afa kayi tunanin ka samu inda zaka huta ba Sam kaje ka cigaba da Neman kudinka kuma idan anyi Auren  gidana zaka zauna sabida bakada gidan da zaka iya ajiyeni lastly babu ruwanka da samun ido acikin al amurana i do wat Eva I want idan ka yarda fine zan yarda ka aureni idan baka yarda ba zaka iya hakura da aurena"
3

Adnan duk da dokokin sun mishi tsauri amma tunda dai ta yarda zata Aure shi bai tsaya wani dogon tunani ba ballantana har yayi tunanin irin sana'ar da take nufi yace mata ya amince jiki na rawa.

"Duk lokacin da ka shirya zaka iya zuwa a d'aura mana Auren I dont need anything from u"

Daga haka ta kwashi ledojinta ta shige cikin mota Adnan ya zagaya ya shige Cikin tsantsar farincikin aurensa da Ajjidde tace zatayi.

Sai da ya sauketa a gida yana jera mata godiya inda ita kuma tayi shigewarta ta bar shi awajen.

Adnan tsabar murnar cikar burinsa da dubu hamsin dinsa  da baiyi ciwon kai ba sai da ya tsaya a hanya ya siyi kaji da tsire har dasu yoghurt ya nufi hanyar gida.

Karfe goma dai dai ya k'ara so gida da wake wakensa ya shiga gidan sabida murnar dayake ciki inda ya Tarar da Zara a zaune a Palo ta had'a manja da yaji tana ta lassa sabida kawai kwadayin da takeji.

Adnan kusa da ita ya zauna yana ta murmushi ya ajiye ledar agabanta yace "yarinya gashi kici ki ture burina ya cika na samu abinda nakeso"

Zara da kamshin da tajiyo yasa taji tsohon yunwar da takeji ya taso mata wani irin damka ta kaiwa ledar ta Ciro takardar kazar ta bud'e ta fara yaga tana kallon Adnan tana zabga murmushi Adnan kuwa kallonta kawai yana kallon yanda jikinta ke rawa kamar bata tab'a cin kaza ba.

Sai da taci iya cinta har ta rasa wajen turawa ta hakura ta ture takadar gefe ta fara zabgawa Adnan godiya tana Allah ya k'ara cika masa burinsa.

Ameen Adnan yace ya kira sunanta yace "Zara aikin da nake nema a Maiduguri na samu nan da wata da zai kama zan koma can da zama gabadaya dan haka kafin watan ya kama kisan yanda zakiyi ki koma gidanku Ki daidaita da iyayenki zan baki kudin da zaki kula da abinda zaki Haifa kafin na yi balancing na dawo inyaso idan nazo sai muyi Auren amma idan kuma kika k'i to babu ruwana dan babu abinda zai hanani tafiya ta idan kuma kudin hayan ya kare sai kisan yanda zakiyi amma dai ki kara shawara da zuciyarki kigani ya kamata kije ki sami iyayenki ki nemi yafiyarsu tun lokaci bai kure miki ba"

Wani irin zufa ne ya hau ketowa  Zara hankalinta yayi mugun tashi cikinta yayi wani irin dunkulewa.Kallon Adnan kawai take hawaye na zubo mata

Adnan  kuwa tab'e baki yayi yafara k'ok'arin mik'ewa dan bashida wani  matsala yanzu tunda zai Auri sanyin idaniyarsa Ajjidde. +

Zara da Sauri ta ruk'o hannunsa adai-dai lokacin data fashe da wani irin kuka tace "Haba Adnan ya za'ayi ka tafi ka barni a cikin wanan halin da nake ciki ina ma laifin ka tsaya na haihu kafin ka tafi Maidugurin daga ina zan fara idan ka tafi karka manta cikinka ne ajikina duk halin danake ciki a yau Kaine sila bazan iya zuwa gida da cikin nan ba  idan naje da ciki nace musu me ince musu cikin waye ajikina"

Zara tace tana sakin hannunsa tare da kara fashewa da kuka

Adnan da sauri ya koma ya zauna a gefenta da wani tunani ya fad'o masa   da Sauri yace  "na samo shawara indai kika koma  gida iyayenki zasu k'arbeki da hannu biyu kuma zamuyi Auren mu cikin kwanciyar hankali ba tare da mun fuskanci wani matsala ba kinaji "

Zara da sauri ta gyad'a masa kai

Adnan kuwa ya K'ara gyara zamansa yana tunanin mai yasa duk wanan tsawon lokacin wanan tunanin bai fad'o masa ba sai yanzu.

"Gobe ki shirya da magriba na kai ki gidanku da kaina idan kinje karki shiga gidan kai tsaye kisa ayi miki magana da Mahaifiyarki idan ta fito ki fad'a jikinta ki fashe mata da kuka sai kin yi kuka mai isarki kin tabbata da hankalinta ya tashi sai kice mata tunda Ameer ya sakeki kike tsoron zuwa gida sabida kinsan korarki zasu yi  wajen wata mata mai siyar da abinci kika zauna kike tayata aikace aikace take baki abinci kike ci kina kwana a gidanta babu waya a hannunki ballantana ki kirata ki gaya mata halin da kike ciki Sanan ga wahalar da kika ringa sha sabida sakinki da Ameer yayi da ciki ahaka kika ringa shan wahala kinje gidan Ameer yafi a kirga amma yana korarki shine jiya wacce kike yiwa aiki tace miki zata koma garinsu da zama yau babu Yanda bakiyi da ita ba akan ta barki ki zauna tace aa sai kin bar mata gidanta ahaka ta koreki yau dinan kika ringa Neman wajen da zaki koma ki zauna amma babu shine kikace bari ki gwada zuwa gida ko zasu amsheki kinsan kinyi kuskure dan Allah ta yafe miki bakida wajen zuwa karta manta bakida   sama da ita  Kinga sai ki lanka yawa Ameer cikin kice da ciki ya sake ki ni nasan zasu karbeki kinga idan kin haihu zasu d'auka d'an Ameer ne nan kuwa nasan d'ana ne bakida wani tashin hankali kinga idan naje na samu abinda nakeso sai na dawo na aureki cikin kwanciyar hankali na nuna musu zan rik'e abinda kika Haifa Kinga shikenan d'anmu ya dawo gabanmu" Adnan yace yana sakin murmushi rabuwa da k'aya ya huta

STORY CONTINUES BELOW


Zara kallon  Adnan kawai take dan tasan wayo kawai yake so ya mata guduwa zai yi ya barta amma ya zata yi hakan shine kawai zai zame mata ma fita idan ba haka ba idan bata koma gidansu ba ya zata fara rayuwa idan ya koma garinsu idan dai iyayenta suka amsheta basu Koreta ba zata zauna ta haifi abinda ke cikinta ta kuma raineshi ta bar Adnan da Allah.

Adnan ne ya katse mata tunanin da take yi yace "ya kika yi shiru ko shawarar bata yi ba Nifa tausayinki nakeji Zara dan wlh idan na tafi zan Dade ban dawo ba kuma kinga zaki shiga gararin rayuwa sabida haka gwara kawai kibi shawarata"

"Idan kuma suka kira Ameer suka tambayeshi fa akan dagaske cikinsa ne ajikina yace ba cikinsa bane bafa"? 


Adnan da Sauri yace "haba sai kace ba mace ba ai tub'urewa zakiyi kice wlh cikinsa ne zarginki kawai yake ke baki tab'a sanin wani d'a namiji ba ni nasan idan kika dage da kuka da komai dole zasu yarda"

Zara ajiyar zuciya kawai ta sauke ta mik'e Hawaye na zubo mata  magana ta fara yi cikin karyayar murya tana  "Adnan nasan so kake na koma gida kawai dan nabar rayuwarka nasan so kake ka gudu kabarni Bawai dan ka samu aiki a Maiduguri ba nasan nid'in ce baka so Karka damu Adnan zanje gida zan kuma bar rayuwarka zan lanka yawa Ameer cikin dake jikina duk da nida kai munsan cikin ba nashi bane nakane amma inaso ka sani zan raini abinda muka Haifa har ya girma inaso duk inda ma zaka gudu kaje ka tuna kana da d'a awajena idan baka neme shi ba ni zan sa ya neme ka wlh nayi dana sanin biye wa san zuciyata nayi dana sanin biye maka yanzu gashi tun ba'aje ko'ina ba ina girb'ar abinda na shuka Allah ya rufa min asiri na tonawa kaina Allah ya min niima ya bani salihin miji mai kaunata amma dayake banida rabo shaidan na kad'an min ganga haka na biye maka muka ringa watsewa babu komai idan na koma gida iyayena suka yafemin bayan na haihu zan nemi Ameer in nemi yafiyarsa  Adnan ngd da irin sakayyar da kayimin Insha Allahu tun a gidan duniya Allah zai sakamin abinda kayi min Allah ya kaimu goben zanje gida da kaina ba sai ka kaini ba"

Zara tace ta juya tare da nufar d'akinta

Adnan duk maganganun da tayi babu Wanda ya tab'a shi ko kad'an hasali shi Allah Allah yake gari ya waye Zara ta k'ara gaba yana ganin babu Wanda zai kai shi jin dadi.

Ido kawai ya zuba mata har ta shige d'aki tana zubar da hawaye tab'e baki yayi ya shige d'akinsa yana kiran Layin Ajjidde ya mata misscall yafi a kirga amma bata d'aga ba ahaka ya kwana yana kiran layinta inda a karshe yaji ta kashe wayan gabad'aya da tunanin Ajjidde yayi bacci har dasu mafarkinta.

Zara kuwa fargaba ne yabi ya cikata dan batasan mai zata tarar ba goben idan taje gida.

B'angaren su Ameer kuwa washegarin ranar da yamma yana barin office gidansu Aliya ya nufa da d'an confidence d'in shawarwarin da Hajiya Ameena ta bashi.

A k'ofar gidansu yayi parking ya d'auko wayarsa yana k'ok'arin kiran Aliya.

Adai-dai lokacin motar Alhaji Abubakar yayi parking a k'ofar gidan inda Adnan yayi Sauri ya maida wayarsa cikin Aljihunsa ya mik'e yana sunkuyar dakai daya hango Alhaji Abubakar ya fito daga motarsa fuskarsa d'auke da fara'a.

Ameer da Sauri ya k'arasa ya tare shi kafin ya iso wajensa ya zub'e a k'asa yana gaishe shi.

Alhaji Abubakar cikin fara'a ya amsa gaisuwarsa tare da cewa ya taso su shiga daga ciki akan me zai tsaya a waje ai shi na gidane.

Ameer cikin tsananin farinciki ya mik'e yabi bayansa wani irin farinciki na ratsa shi  dan ji yake tamkar har an bashi auren Aliya.

A palon saukar baki Alhaji Abubakar ya sauke shi suka kara gaisawa dashi yana tambayarshi mutanen gidan inda bayan sun gaisa Alhaji Abubakar ya mik'e da zumar ya shiga daga ciki dan yaga Ameer din kunyarsa yake ji.

STORY CONTINUES BELOW


Ameer da Sauri ya d'ago yana Sosa kai ya fara magana cikin 'in'ina yana Cewa dama wajensa yazo.

Alhaji Abubakar komawa yayi ya zauna yace Allah yasa lafiya duk da yariga da yasan abinda ke tafe dashi amma gwara yaji dai daga bakinsa.

Ameer kara sunkuyar da kansa yayi a hankali ya fara gayawa Alhaji Abubakar abinda ke tafe dashi akan san Aliyar da yake  da kuma Aurenta da yakeso yayi ba wasane  ya kawoshi ba.

Tun kafin ya gama magana Alhaji Abubakar ya washara baki yana Mai jin wani irin farinciki dan kowane uba zai so yarsa ta samu miji irin Ameer.

Alhaji Abubakar ce masa yayi babu komai Allah ya tabbatar musu da alheri su fahimci juna shi da Aliyar duk lokacin daya shirya yazo kawai a tsaida magana.

Ameer godiya ya fara zabga masa tamkar har an d'aura masa aure da Aliyar inda Alhaji Abubakar ya mik'e yace masa bari ya turo masa Aliyar daga haka ya fice daga palon fuskarsa d'auke da fara'a.

A Palo ya Tarar da Hajiya Rukayya da Aliya da Sumayya suna kallon tashar Arewa 24

Shigowarsa palon yasa suka mik'e suna masa sannu  da zuwa

Alhaji Abubakar amsawa yayi ya dakatar da Aliya dake   k'ok'arin barin palon yace ta dawo ta zauna.

Aliya cikin fad'uwar gaba ta koma ta zauna tana kallonsa dan ta d'auka wani laifin Tayi.

Gyaran murya yayi yafara magana yana "Aliya yanzu dana dawo na tarar da Ameer a k'ofar gidanan yazo nemana akan yana sanki da aure yana neman izinina akan zai fara zuwa wajenki dan Ku fahimci juna dashi ya kuma ce ba wasa ya kawo shi ba ban tsaya naji ta bakinki ba sabida munriga da munyi magana dake na kuma baki shawara nace mishi na amince mishi akan ya ringa zuwa kuna fahimtar juna kafin magana Tayi k'arfi Aliya ga Ameer can ban yarda ki wulakanta Shi ba dan godiya ya kamata  kiyi wa Allah daya baki Wanda yafi wanan tsohon mijin naki dan haka gashi can a palon bak'i yana jiranki maza kije ki same shi.

Aliya mik'ewa tayi jikin ta asanyaye ta nufi d'akinsu taje ta saka hijabinta ta nufi palon bak'i gabanta na d'an fad'uwa bazata iya cewa ga abinda take ji ba game da Ameer ita dai tasan zata ringa kula shi kawai dan tayiwa iyayenta biyayya amma idan ba haka ba ta Dade da kulle zuciyarta bata jin akwai wani d'a namiji da zata bud'ewa Zuciyarta.

Ahaka ta k'arasa wajensa fuskarta babu yabo babu fallasa.

Ameer kuwa shigowarta yasa ya mik'e ya tsaya sai da ta zauna  ya koma ya zauna shima.

Aliya gaishe shi Tayi kanta a sunkuye.

Ameer ya amsa yana lek'a fuskarta sai dai suka samu minti biyar ahaka kafin yace "Aliya kiyi hakuri nasan na takura miki ba laifina bane zuciyata ce ta kamu da mugun kaunarki da har nake ganin bazan iya rayuwa  batare dake ba nasan u would find it difficult to trust and love again but ina rokonki ki bani dama  nashiga rayuwarki na zama abokin rayuwarki I promise u bazaki tab'a Dana sani akaina ba"

Aliya ita dai kanta a sunkuye yake bata d'ago ba ballantana Tayi yunkurin magana

Sai da Ameer yace "kinyi shiru baki ce komai ba Aliya i don't want to false u idan dai kina ganin bazaki iya samar min waje a zuciyar ki ba pls ki fad'a min bazan ji haushi ba dan komai yin Allah ne duk inda nakai da kaunarki idan Allah yayi bazan aureki ba dole na hakura"

Aliya sai a lokacin ta d'ago suka had'a ido tayi Sauri ta maida kanta k'asa tace murya na rawa "Allah ya zaba mana abinda yafi alheri"

Ameer cikin tsananin farinciki yace "meaning am accepted kenan"?

Aliya kai kawai ya gyad'a masa

Ameer ya saki ajiyar zuciya yana ta zabga hamdala a filli hakane yasa Aliya d'an sakin murmushi dan ba k'aramin Dariya ya bata ba.

Ameer hira ya ringa janta dashi duk dan ta saki jiki dashi duk da amsarta ee ko aa ne bashi ya bar gidan ba sai da Magriba bayan ya dire mata siyayyan da ya mata da sakon da Hajiya Ameena ta bashi ya bata da bai samu ya bata a jiyan ba.

Washegari da sassafe Adnan ya kara dira kan wayarsa yana kiran Ajjidde dan kwana yayi yana mafarki da ita shi kansa har tsoron irin san da yake yiwa Ajjidde yake  haka  ya ringa kiran wayar Ajjidde har sai da yagaji dan yana ta ringing taki d'auka tagumi ya buga kamar Wanda akayiwa rasuwa dan ji yake idan baiji muryarta ba zai iya mutuwa wanan wane irin azababben so ne haka yake yiwa Ajjidde haka ya wuni a gidan tamkar Mara lafiya wayarsa rik'e a hannunsa yana san zuwa gidan Ajjidden yana tsoron zuwa.

Zara kuwa a ranar da sassafe ta had'a kan kayanta da basu fi kala biyar ba bayan kukan dataci ta koshi har wani fad'awa Tayi sabida fargaba aranar ko abinci ta k'asa ci a d'aki ta wuni tana jiran magriba tayi ta tafi gidansu.

Ana kiran sallar magriba tafito daga d'akinta da turtsetsen cikinta hannunta rik'e da ledar kayanta.

Ko kallon inda Adnan daya buga tagumi yana kallon waje d'aya batayi ba ta nufi hanyar waje.

Adnan wucewarta ne yasa ya dawo daga tunanin da ya tafi tun safe bai sata a idonsa ba sai yanzu da sauri ya mik'e yabi bayanta yana "Ki tsaya nazo na kai ki mana"

Zara ko tsayawa batayi ba ta fice daga gidan.

Adnan kuwa ya tab'e bakinsa ya koma ciki dan shi wani zazzabi zazzabi ma yakeji sabida rashin jin muryar Ajjidde.

Zara kuwa bata sha wahalar samun tricycle ba ta nufi gidansu gabanta na balain fad'uwa hawaye kawai take sharewa.

Daga nesa da gidan tace a sauketa ana sauketa ta tsaya cak tana kallon gidan gabanta kamar ya fad'o dan cikin ta kuwa sai motsi yake sabida abincin da bata ci ba tun safe.

Sai da ta samu kusan minti talatin tana tunanin abinda ya kamata tayi dan wani irin tsoro takeji.

Ahaka ta d'aure jikinta na rawa ta nufi k'ofar gidan ta fara kwankwasa wa kirjinta kamar zai fado k'asa sabida fargaba

Takun takalmi ta jiyo alamar za'a zo a bud'e k'ofar ta ja da baya da sauri tana dafe cikinta dan ji take kamar dan zai fad'o.

Ana bud'e k'ofar ta maida hannunta kirjinta ta dafe ta gwalalo ido.

Khaleed da k'arfi yace "Aunty Zara kece ko mafarki nake"

Zara cikin rawar baki da jiki hawaye na zubo mata tace "Khaleed nice dan Allah jeka kirawo min Mommy"

Khaleed a 360 ya koma ciki da gudu dan yasan burin Mommy Hauwa da mafarkinta kenan taga Zara.

Zara kuwa zubewa tayi a k'asa sabida k'afarta dake rawa wani irin kuka ta fashe dashi.

Adai-dai lokacin da Mommy Hauwa ta fito kamar wacce aka hankad'o daga gidan tabi ta rame kamar ba ita ba.

Ido kawai ta zubawa Zara hawaye na zubo mata inda Zara itama ta zuba mata nata idon tana sheshek'ar kuka.

Mommy Hauwa cikin rawar murya tace "Zara kece"?

Zara cikin matsanacin kuka da numfashinta dake seizing tace " Nice Mommy Dan Allah ki yafemin...........

Post a Comment for "MAKOTAN JUNA CHAPTER 7"