Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

MAKOTAN JUNA CHAPTER 5

MAKOTAN JUNA CHAPTER 5

- - Post a Comment
MAKOTAN JUNA
CHAPTER 5Ameer kuwa yana gama waya da Mommy Hauwa ya tari Abun hawa ya nufi company su dan ya d'auko motarsa yaje gidansu ya fad'awa mahaifiyarsa duk abinda ke faruwa.
+

Zara kuwa tana ganin Ameer ya tafi ta mik'e da k'yar ta koma ciki ko damuwa batayi da kayanta dake watse a k'asa ba direct ta nufi b'angarensu Adnan hannunta rik'e da kanta dan kanta wani irin azababben ciwo yake mata sanadiyar fitar hak'oranta guda biyu.

K'ofar d'akin Adnan ta fara kwankwasa tana kiran sunan sa.

Adnan dake kwance cikin matsanacin Hali yana juye juyen azaba da sauri ya tsaya cak dayaji Zara na kiransa cikin rawar murya.

K'asa kunnensa ya k'ara yi dan ya tabbatar da itace kuwa ya kuwa ji ta k'ara kiran sunansa da k'arfi tana k'ara kwankwasa k'ofar.

Shima cikin rawar murya yace "Zara kece"

"Nice Adnan ka bud'emin"

Adnan k'ofar ya nufa da zungureren lebb'ensa na sama da yayi suntum ko hango idonsa ba kayi sabida kumburar da yayi.
2

Yana bud'e k'ofar ya tsaya yana kallon Zaran da itama fuskar nata ya canja kamani mamakin ganin yanda lebb'ensa ya kumbura yasa ta bud'e baki tana mamakin irin raunin da Ameer yajiwa Adnan adnan shi kuma bakinta ya zubawa ido yana mamakin hak'oranta biyu na gaba da suka zub'e tabi ta canza kamar ba ita ba 1

"Ad ya akayi ka tsaya Ameer yayi maka irin wanan dukan idan ni yafi k'arfina amatsayina na mace ai bai kamata yafi k'arfinka ba tunda kai namiji ne"

Zara tace muryarta na rawa

Adnan da k'ananun idonsa yafara harararta yana " tayaya zan rama dukan da yamin Alhalin kamani yayi da matarsa Duk bake kika jawo min ba ina zaman zamana kin janyo min mugun duka nasha fad'a miki ki iya takunki kar mijinki ya zarge mu kika k'i saurarata ai ga irinta nan kema ya miki asaran hakora biyu nidai Allah yasa iya dukan da yayi ya huce kenan kar ya d'ebo min 'yan hisba"

Zara cije lebb'e tayi sabida mugun ciwon kan daya cigaba da damunta

Tace "Ad Ameer ya sakeni saki uku ga kayana can ya watsa min a bakin gate tayaya zan soma komawa gida Alhalin Daddy yace kar na sake na k'ara zuwa gidansa ina zan nufa"?

" Ya zakiyi Zara haka zaki koma gidan naku ki bashi hakuri idan ba haka ba a ina zaki zauna ko awajena kike tunanin zaki zauna In k'ara tabbatar masa da cewa ina nemanki"

Zara cikin tsananin mamaki tace "in koma gidanmu fa kace kasan kuwa duk halin Dana shiga sabida Kaine akan wane dalili zan koma gidan da akace kar na k'ara zuwa Ad babu inda zani ina nan tare dakai ai yariga da ya sakeni babu abinda ya dame shi dani"

"Inaga dukan da Ameer ya miki ya sa kinsamu tab'in hankali ya za'ayi ki zauna dani alhalin mijinki ya sake ki Zara ki barni naji da damuwar Dana ke ciki dan ko ni yanzu barin gidanan zanyi sai bayan kwana biyu zan dawo dan bansani ba ko Ameer ya bar maganar haka kije gidanku idan an kwana biyu zamuyi waya Idan kin gama idda sai naje gidan naku a d'aura mana Aure"

STORY CONTINUES BELOW


Zara duk da halin da take ciki sai da ta watsa masa wani mummunan kallo tana "wane idda zanyi bayan da Auren ma muke Neman juna babu wani iddar da zanyi Ad ina tare dakai dan ko naje gida koroni za'ayi dan haka duk inda zakaje sai na bika Idan yaso bayan kwana biyu sai a d'aura mana Auren"

Adnan babu yanda bai yi da Zara ba akan ta tafi gidansu zai nemeta tak'i a k'arshe ma daya takura mata bangajeshi tayi ta wuce ciki ta kwanta tana zaginsa da shi matsoraci ne Idan ba haka ba tsoron kuma mai yake ji tunda Ameer ya Riga da ya saketa maganganu ta k'wak'wab'awa Mishi san ranta.

Adnan kuwa ya saki baki yana mamakin yanda take zuba mishi rashin kunya.

Akan dole ya rarrasheta da ta tashi su tafi ko hotel ne su kama bai kamata Ameer yasan ta kwana a b'angarensa ba dan hakan na iya tunzura shi ya d'ebo masa 'yan hisba.

Ahaka suka fito da kumburarrun fuskarsu Adnan ya kwashi kayan Zara ya kai ciki dan Zara dagewa tayi bazata kwashe kayan ba.

Sai da ya tsaya a banki ya Ciro musu ishashen kud'i suka fara biyawa chemist aka rubuta musu magunguna aka yi musu allurar rage Zafi suka nufi wani hotel mai saukin kud'i Adnan ya kama musu na kwana ukuHajiya Ameena sallati kawai take tana tafa hannuwa a lokacin da Ameer ya gama bata labarin abinda Zara da Adnan suka ringa aikatawa ba tare da saninsa ba.

Ameer kuwa girgiza k'afa kawai yake yanajin wani irin bak'inciki a zuciyarsa har yanzu yana hango yanda yaga Adnan da Zara dazu babu Kunya babu tsoron Allah ko tun yaushe suka fara Neman juna suka jefa Kansu a cikin irin wanan bala'in oho babu wacce yake tausayawa sama da Aliya dan ko da bai shiga zuciyarta ba yasan irin bak'inciki da takeji a zuciyarta shi Allah ya jarrabce shi da mace mazinaciya ita kuma Allah ya jarrabce ta da mazinacin miji duk su biyun babu Wanda ya dace da abokin arziki na kwarai tunanin da ya darsu a zuciyarsa ne yasa ya bud'e idonsa ya kalli Hajiya Ameena dake ta surutu ita kad'ai tana mamakin halin Zara da Adnan

"Hajiya idan Aliya matar Adnan ta gama idda zan Aureta dan Aliya irin macen danake fata da mafarkin samu ne mun dace da juna 2

Hajiya Zara da Adnan sunfi dacewa Allah ne ya kaddara zamu Auri wayanda basu dace damu ba dan mazinaci sai da mazinaciya mazinaciya sai da mazinaci"

"Ina goyon bayanka Ameer wlh ka aureta ko Dan ka k'unsawa wanan Dan iska Wanda bashi da rabon duniya da lahira in banda iskanci kana da mata kana Neman matar wani indai ka yaba da hankalin matarsa wlh ina goyon bayanka ka aureta ni nasan sai ya kusa haukacewa Idan yaji labari"

"Hajiya masifa ce kawai irin ta d'a namiji fa amma Idan ba haka ba wlh matar sa ma tafi Zaran dayake nema kyau ki dai tayani da addu'a kawai"

"Insha Allahu Ameer ai kullum acikinta kake"

"Yauwa Hajiya nifa goben nan zan samo mota a kwashe kayan Zara dan nima a gobe zan bar gidan zan koma sabon gidana dan bazan iya cigaba da zama da fasiki mazinaci da babu tsoron Allah a zuciyarsa ba dan Idan ina kallonsa wallahi zan iya aika shi lahira"

"Duk abinda kayi Ameer ina goyon bayanka wlh ka bar gidan dama idan ba yanayin aikinku ba mai zai kai ka zama da irin sa ka bar mishi gidan ya cigaba da iskancinsa wlh watarana za'a jera masa matan ya k'asa tab'asu kuma kana ganin babu matsala zaka iya zama a gidan naka kai kad'ai"?

" Hajiya mai zai hana zan zauna mana ni kad'ai da can da banida aure bani kad'ai ke kwana ba"

"Aaa Ameer aganina ka bari Idan zaka yi wani Auren sai ka tare da matarka a yanzu dai ka dawo nan ka zauna tunda ga d'akinka can babu kowa aciki"

"To shikenan Hajiya duk yanda kikace haka za'ayi amma"

Ringing d'in wayarsa ne ya katse masa maganar da yake ganin Mommy Hauwa ke kiransa yasa ya d'ago ya kalli Hajiya Ameena da itama shi take kallo tana jiran Karin bayani"

STORY CONTINUES BELOW


Ameer ajiye wayar yayi yace "Hajiya kingani ko Mahaifiyar Zara ke kirana ni Wlh tausayin ta nakeji yanzu bansan kiran da take min ba"

"Dalla d'aga kai kace 'yarta taje ta ringa bin maza da Aurenta ka d'aga kaji mai zatace Idan kuma ta gaya maka ba sukari tana goyon bayan mazinaciyar 'yar tata yanzu nan nima na kirata na warware mata"

Ameer d'aga wayar yayi jiki a sanyaye dan yasan Mommy Hauwa tana cikin matsanacin hali tunda ya gaya mata sakin da yayiwa Zara to ya zai yi dole ya saketa bazai iya cigaba da zama da ita ba

"Assalamu alaikum"

Mommy Hauwa tace cikin rawar murya hawaye nata wanke mata fuska

Ameer amsa sallamar yayi tare da gaisheta tamkar yana gabanta muryarta dayaji ya k'ara karyar masa da zuciya

Mommy Hauwa cewa tayi "Ameer yanzu ina Zaran take dan har yanzu bata zo gida ba"

"Mommy wlh bansan inda take ba dan ni tafiya ta nayi nabarta awajen amma bansani ba ko ta koma wajen saurayin nata "

Mommy Hauwa runtse idonta tayi da k'arfi dataji mai yace wai saurayinta kukan da take ta dannewa ne ya kwace mata tace "Ameer wlh Idan Zara tazo Sai babanta ya koreta dan kullum sai yace min koda mutuwa yayi bai yarda Zara tazo mishi cikin gida ba

babu waya a hannunta ne na kirata nace taje gidan kanwata gobe naje na sameta"


"Nidai tunda na k'arb'e wayar hannunta ban siya mata wani ba amma naga wani waya a hannunta da saurayin nata ya siya mata suke wayar banida lambar ballantana na baki"

Mommy Hauwa ajiyar zuciya ta sauke tace "to shikenan Ameer ngd"

Ameer shima godiya yayi mata ya kashe wayarsa yana mai tausayin Mommy Hauwa duk da rashin kunyar da Zara tayi mata ranan hakan bai sa tayi fushi da ita ba.

Aliya kuwa tunda ta koma gida wani zazzafan zazzabin mai had'e da ciwon kai ya k'ara rufeta Wanda har sai da aka kuma maidata asibiti.

Alhaji Abubakar kuwa ji yake kamar ya tsinci kansa agaban Adnan dan duk shi yake d'orawa laifin Halin da Aliya take ciki wani abokinsa d'an sanda ya kira awaya yace masa zai zo gobe zasuje su kama wani dan iskan yaro yana so akoya masa hankali.

Yana gama wayar Hajiya Rukkayya tace dan Allah yayi hakuri ya rabu da Adnan su bar shi da Allah kawai tana cikin zuba mishi bayani Alhaji Abubakar ya daka mata wani mummunan tsawan daya sa hantar cikinta kad'awa yace mata babu abinda zai hana shi d'aure Adnan sai dai tayi abinda zatayi

Hajiya Rukayya tuni taja bakinta tayi shiru dan tasan Alhaji Abubakar ya zuciya.

Adnan da Zara kuwa tunda suka shiga d'akin hotel d'in da suka kama Zara ta nemi guri ta kwanta dan ita kad'ai tasan mai takeji a jikinta duk da ta sha magani anyi mata allura hakan bai hana taji azabar ciwo a jikinta ba hak'oranta biyun da suka fita ya taimaka wajen sa kanta wani irin ciwon na daban.

Adnan kuwa  sai da yayi wanka da ruwa mai zafi ya gaggasa jikinsa ya shafe jikinsa da ointment kafin shima ya kwanta a gefen Zara yana mai balain jin haushin ta Dan duk a ganinsa ita ta jawo masa duk halin da yake ciki ciki kuwa har da aikinsa da bashi da tabbacin ba korarsa akayi ba ahaka shima wahalallen bacci yayi awon gaba dashi.

B'angaren Ameer kuwa sai da ya kai kusan k'arfe goman dare ya koma gida.

Shima baccin bai d'auke shi da wuri ba sabida tunane tunanen da yaringa yi inda Rabin tunaninsa na Aliya ne dan wani ikon Allah haka kawai yau ya tsinci kansa da balain kaunarta idan ya tuno yanda take hawaye dazun sai ya rasa mai ke masa dadi idan kuwa ya tuna Zara da Adnan sai yayi ta tsine musu ahaka har bacci ya d'auke shi.

*7am*

Ameer da bacci ya d'auke shi akan sallaya tunda ya dawo daga Massallaci bud'e idonsa yayi da sauri a lokacin da yaji ana kwankwasa gate d'in kamar za'a b'alla shi.


Da sauri ya mik'e tare da nufar waje hannunsa d'auke da carbin dayake ja bacci ya d'auke shi

"Waye" ya k'ara cewa akaro na uku a lokacin dayake k'ok'arin bud'e gate d'in

Aikuwa yana bud'ewa yaga 'yan sanda uku a tsaye da Angry Alhaji Abubakar dake ta vibrating kamar idan ya damki Adnan ba zai bar shi da rai ba.

Gaisawa sukayi da Ameer suka fad'a mishi Adnan suke nema Alhaji Abubakar bai ma bari sun gama yiwa Ameer bayani ba ya shige 'yan sandan suka bi bayan shi anan Ameer ya gane Mahaifin Aliya ne.

Alhaji Abubakar buga k'ofar b'angarensu  Adnan ya ringa yi da k'arfi yana jijjigawa kamar zai b'alla bai ko juya ya kalli Ameer dake ta gaishe shi ba har sai da Ameer yace mishi yana jin Adnan baya nan ya daina buga k'ofar yana huci.

Ameer cikin kwantar da murya da ladabi da biyayya ya fara bawa Alhaji Abubakar hakuri yana kwantar masa da hankali Alhaji Abubakar kuwa sai huci yake idon nan nasa jawur

Cikin tsananin b'acin rai Alhaji Abubakar yace "wlh wlh sai na d'auki fansar wulak'anta min 'ya da yayi asanadin abinda yayi mata gata can a gadon asibiti tun jiya bata san inda kanta yake ba shikenan dan yaga tana da hakuri sai ya taka ta yanda ransa keso ni ba shashashan uba bane da zan tsaya wani Dan iska can ya ciwa 'yata mutunci"

Tunda Alhaji Abubakar yace Aliya na asibiti gaban Ameer yayi wani irin fad'uwa take hankalinsa ya tashi.

Maganar Alhaji Abubakar ne ya dawo dashi hankalinsa "idan yama gudune kace masa ina nan dawowa wlh bai isa ya wulak'anta min 'ya ba"

Ameer ganin Alhaji Abubakar ya hau dayawa yasa ya ringa bashi hakuri yana cigaba da kwantar masa da hankali har ya kai shi ga bashi labarin ai matarsa Adnan d'in ke nema shima bai san Adnan bashida hali ba sai jiya"

Alhaji Abubakar jin abinda Ameer yace ne ya saka ya gyara tsayuwarsa  yana "kuma bazaka kai kararsa hisba ba haka zaka bar shi"?

Ameer murmushi yayi yace babu wani hisba da zai kai shi 
shi dai ya bar shi da Allah

Acikin hikima da dabara Ameer ya ringa Jan Alhaji Abubakar da hira har ya saki jikinsa dashi ya ringa bashi hakuri akan ya rabu da Adnan kawai tunda Allah ya rufa asiri tun ba'aje ko ina ba Allah ya tona musu asiri.

Alhaji Abubakar tuni yaji Ameer ya burge shi da kyawawan lafazinsa inda har Ameer ya raka shi bakin motarsa da zai tafi cikin dabara ya bugi cikinsa yaji asibitin da aka kwantar Aliya.


B'angarensu Zara kuwa ita ta fara Riga Adnan tashi jikinta duk yabi yayi tsami bakinta kuwa a d'an kumbure mik'ewa tayi ta nufi mudubin dake jikin bangon d'akin tana tattab'a fuskarta da jini ke kwance tana ganin Yanda Ameer ya canja mata kamani ta zama wata iri kamar ba ita ba.

Bud'e bakinta tayi a hankali tayi tozali da katon wawulon dake tsakiyar hak'oranta gabanta fad'uwa yayi data ga yanda tayi masifar muni kamar cewa akayi ta waiga taga Adnan na kallonta ta mudubin fuskar nan tashi a had'e da sauri Zara ta rufe bakinta tana nufar band'akin.

Adnan kuwa yace turkashi "ina zai kai Zara da wanan katon wawulon bakin nata........Zara wajen Adnan ta nufi dake mata wani irin kallon da bata gane ko na k'yamarta ne ko kuwa na kiyayya.

Zama tayi a gefensa ta k'au da fuskarta sabida kar yaga wawulon nata tace cikin sanyin murya

"Ad wlh Ameer ya cuceni dan Allah dubi yanda ya cire min hak'oran gaba kamar wata tsohuwa Pls ka shirya anjima ka kaini asaka min hakoran roba bazai yiwu na zauna haka ba kai kanka nasan zaka iya tsanata"

Ta juyo tana kallonsa dan taga yanda ya k'arbi maganarta

Adnan mik'ewa yayi ya nufi hanyar band'aki yana "banida kud'in da zan kai ki asaka miki hakoran Roba yanzu duk ke kika jawo mana halin da muke ciki yanzu ciki kuwa har da aikina danake Neman rasawa dan a sanadinki na fara wasa da aikina ni ayanzu mafita kawai nake nema da zaki taimakawa kanki da kin tafi gidanku k'illa su taimaka miki su kaiki asibiti asaka miki hakoran robar inyaso nima idan nasamu nutsuwa sai mu san nayi"

"Ad u must be joking idan ana magana ka daina cewa in tafi gidanmu domin mahaifina ya Riga da ya haramta min zuwa gidansa ko da kake cewa laifina  ne Ad all I did is because of d love I have for u ka daina blaming d'ina and babu yanda za'ayi kace min bakada kud'in da za'a samun hakoran roba sai dai kawai idan rashin mutunci ka taka" 1

Adnan wani irin kallo ya watsa mata yace "Ke kiringa tauna magana kafin ki fad'a min ita idan ba haka ba wlh ubanki zanci dan naga alamar bakida kunya kowace irin magana ta fito bakinki fad'inta kawai kike tunda nake da Aliya bata tab'a min rashin kunya ba so ki kama kanki inada kudin bazan biya bane kuma wlh idan kika isheni korarki zanyi dan kina neman zame min masifa ko ma nace kiringa kin zame min" 3

"Ad ni kake gayawa magana san ranka? ina san daka ce kana yimin tun ba'aje ko'ina ba kana neman juya min baya"

Tsaki Adnan yayi ya shige band'aki wani irin haushin Zara na rufe shi dan kamar yaje ya rufeta da duka da take magana dan tamkar ba ita ba dan Tayi wani irin muni.

Ameer kuwa su Alhaji Abubakar na tafiya ya koma ciki yayi wanka ya shirya ya fita.

Minti goma da fitarsa sai gashi ya  dawo da  katon akori kura da wasu maza majiya k'arfi suka shiga gidan suka hau fito da kayan Zara suna lodawa aciki sai da suka kwashe komai daya kasance na Zara ne ko cokali basu bari ba.

Ameer ya basu kud'i ya musu kwatancen gidansu Zara yace su kai kayan gidan.

Suna tafiya shima ya hau fiddo da kayansa masu mahimmanci yana lodawa acikin motarsa sai da ya kwashe komai nasa sai gadonsa da rage bai d'auka ba.

STORY CONTINUES BELOW


Ya  kulle gidan ya hau motarsa ya nufi gidansu dan ya kai kayan nasa.

Dangin tuni suka zagaye Aliya kowa nasan nuna bajintarsa ta hanyar kula da ita dan Mahaifinta mutumin kirki ne gashi dan dangi kowa sai tofa albarkacin bakinsa yake ana la'antar Adnan dan duk anfad'a musu abinda Adnan yayi mata.

Aliya kuwa d'auriya kawai take ta na nuna musu hankalinta akwance yake amma can k'asan zuciyarta ita kad'ai tasan mai take ji.

Mommy Hauwa tunda aka fara shigo da kayan Zara hankalinta ya k'ara tashi ta rasa mai ke mata dadi jiya ko kad'an batayi bacci ba sabida batasan inda Zara take ba ballantana ta san halin da take ciki.

Tana tsaye suka gama shigo da kayan suka tafi.

Zama Tayi a tsakar gidan tare da zubawa kayan ido hawaye suka hau zubo mata.

Sunanta da Dr ya kira ne yasa ta d'ago tana kallon shi

Sai da ya k'arewa kayan dake zub'e a harabar gidan kallo ya maida kallonsa kan Mommy Hauwa da ta zuba masa ido tsoro ya bayyana a fuskarta.

Dr wani irin murmushi dayafi kuka ciwo yayi yace "Zara ta kaso Auren nata kenan to yayi kyau amma inaga kinada masaniyar nace kar Zara ta sake ta k'ara taka k'afarta tazo gidanan ko da mutuwa nayi banyarda abarta tazo cikin gidanan ba idan kuwa kika barta wlh bazan tab'a yafe miki ba kuma yanzu na kara jadadda miki ko ayanzu data kaso Aurenta ban yarda tasa k'afarta ta tako gidanan ba taje duniya ce ta ishi kowa Riga da wando insha Allahu sai  ta kwashi dashin da ta zuba da hannunta" 6

"Haba Dr bai kamata kace haka ba karka manta Zara bata da sama damu ina zata je Indan kace kar tazo gidanan  dan Allah kayi hakuri ka yafe mata matakin daka d'auka akanta yayi tsauri duk lalacewa 'yarmu ce bazaka so ta tagayyara ba dan Allah ka yafe mata abinda tayi ma"

"Hauwa yarinyar da ta bud'i baki tace min bak'in mugu azzalumi Allah ya isa bazata yafe ba ita kike cewa na yafe mata kema kinzo da ganganci wlh bazan tab'a yafe miki ba idan kika bari ta shigo min gida kaf cikin 'ya'yana babu Wanda ya tab'a min abinda Zara Tayi min dan har dangina zan kira akan ban yarda su saurari Zara ba idan taje musu ban kuma yarda su taimake ta ba"

"Haba Dr dan Allah ka daina cewa haka hannunka baya rub'ewa ka yanke ka 'yar kayi hakuri yarinta ne"

Mommy Hauwa tace cikin matsanacin kuka tana Jan majina

Dr Tsaki yayi ya shige ya barta awajen.

Mommy Hauwa ta k'ara fashewa da kuka ta d'auki wayarta tana kiran layin Ameer.

A lokacin Ameer har ya sauke kayansa a gida ana gyara masa d'akinsa shi kuma ya tafi office yana kan aiki kiran Mommy Hauwa ya shigo wayarsa.

D'agawa yayi da sallamarsa kukan da mommy ke yasa jikinsa yayi sanyi

Ba tare da b'ata lokaci ba mommy Hauwa tace "Ameer kaga har yanzu Banga Zara ba bata zo gida ba gashi har an kawo mata kayanta"

Ameer shiru yayi ya rasa mai zai cewa Mommy Hauwa sai data k'ara cewa hello yayi sauri yace

"Mommy wlh bansan inda Zara take amma ni nasan duk inda take hankalinta a kwance yake amma zan duba miki wajen saurayin nata dan k'ila tana wajensa".


Mommy Hauwa runtse idonta tayi sbd  wani irin d'aci ta take ji a mak'ogaranta idan  dataji Ameer  yace saurayin Zara tana bala'in jin haushin kalmar  bata iya cewa Ameer komai ba ta kashe wayar.

Ameer kuwa yabi wayar da kallo yana girgiza kai dan yana bala'in jin tausayin Mommy Hauwa.

Tunanin ya fara yi inda Zara zata tafi tunda ba gidansu taje ba

STORY CONTINUES BELOW


take Adnan ya fad'o masa arai

Zai kuwa yi mamaki idan Zara na wajen Adnan amma dan ya tabbatar anjima zai lek'a gidan yaga ko Adnan ya dawo dan idan Zara bata wajensa dole  zai iya sanin inda Zara taje.

Adnan da Zara kuwa kamar wasu tom en Jerry dan in banda hararar juna babu abinda suka ringa yi abinci ma daban daban suka ci haushin juna kawai suke ji

K'arshe ma Adnan ficewa yayi ya barta a d'akin ita kad'ai dan wani mugun haushin ta yake ji idan ya tuna halin da yake ciki na aikinsa dake rawa sai hankalinsa ya tashi gida yake so yaje dan yasan by now Ameer baya nan

Bai tsaya b'ata lokaci ba ya hau motarsa ya nufi gidan nasu.

Yana parking a k'ofar gidan

k'aton motan company su na parking gabansa ne ya yanke ya fad'i a lokacin dayaga ma'aikatansu su uku  sun fito daga motar  mataimakin ogansa shima ya fito daga bayan motar  sun nufi cikin gidan.

Adnan jiki na rawa ya fito daga motar yabi bayansu a zuciyarsa ya ringa tunanin k'ila zuwa sukayi suce ya koma bakin aikinsa.

Suna k'ok'arin k'wank'wasa k'ofar suka lura da Adnan dake tsaye abayansu jikinsa na d'an rawa.

Cikin d'aurewar fuska mataimakin ogansa yace

"Dama wajenka muka zo"

Hannu ya zura a Aljihunsa ya d'auko wani farin envelope mai d'an nauyi ya mik'awa Adnan.

Adnan kuwa k'asa k'arba yayi gumi na tsatsafo masa cikin rawar murya yace "takardar me wannan"?

" ka k'arba takadar sallama ce oga yace mu kawo maka dan har ya Samu Wanda zai maye gurbinka takardunsa ma yafi naka kyau dama idan baka manta ba sabida Alhaji haruna yayi maka alfarma ya k'arbeka Bawai dan ka cancanci ya d'auke kan ba  yace ka kwashe kayan ka gabad'aya daga cikin gidan gobe wancan zai dawo cikin gidan amma kar ka damu akwai dubu d'ari biyu dake Cikin takadar zai isheka ka d'an rage Zafi kasan oga akwai shi da mutunci da tausayi"

Adnan wani razanan ihu ya k'wala yana zub'ewa ak'asa tare da kamo k'afar mataimakin ogansa nasa "ka taimaka kayimin rai ka roki oga kar ya koreni daga wajen aiki wlh dashi na dogara yanzu daga ina zan fara wlh ko fili bani dashi ballantana gida nashiga uku na lalace a ina zan zauna idan ya koreni daga gidanan"

Mataimakin ogansa fusge k'afarsa yayi yace "kayi hakuri Adnan aikin da aka samu muke yi yanzu ma haka wadanan da muke tare dasu cewa akayi su tayaka fito da kayan dan ayau zasu kwaso kayan wancan d'in su dawo dashi nan ka tashi ka bud'e mana k'ofa su shiga su fara fito da kayan"

Adnan ihu ya k'ara sawa ba sallati ba komai ya fara birgima a k'asa kamar wani k'aramin yaro yana cewa suyi mishi rai suje su rok'i ogansu daga ina zai fara.

Mataimakin ogan nasa yana ganin Adnan na b'ata musu lokaci ya basu umarni su b'alle k'ofar su shiga su fara fito da kayan.

Aikuwa cikin minti uku suka lalata mukullin suka fara fito da kayan daga cikin gidan.

Adnan kuwa sai ihu yake yana birgima.

Ana cikin fito da gadon Aliya suka ji k'aran bud'e gate d'in gidan

Adnan da sauri ya waiga tare da tashi daga k'asa aikuwa sai ga yan gidansu Aliya sun shigo fuskarnan tasu a d'aure mamakine ya rufesu dasu ga Ana fito da kayan Aliya tamkar sun san zuwa suka yi su kwashe kayan dan Alhaji Abubakar tuni ya azalzale su akan su zo su kwashe kayan Aliya ko cokali karsu barwa Adnan ballantana ya mora.


Gaban Adnan ne ya k'ara fad'uwa a lokacin dayaga sun bud'e gate d'in gidan gabad'aya a kori kurar da zasu kwashe kayan dashi ya shigo cikin gidan ko kallon inda yake basu yi ba suka fara kwasar kayan Aliyan suna sawa a mota 

STORY CONTINUES BELOW


Adnan Hannu ya k'ara d'orawa aka dan inka d'auke kayan sawa komai na cikin gidan na Aliya ne .

Cikin minti Arbain danginsu Aliya suka gama kwashe kayan suka k'ara komawa ciki dan su tabbatar da babu abinda ya rage a cikin gidan ganin babu abinda ya rage yasa suka je suka hau motarsu suka tafi  bayan sun  zubawa Adnan wani mugun kallo.

Adnan kuwa helplessly ya zauna kawai yana bin suturunsa dake watse a k'asa da kallo adai-dai lokacin da suma 'yan company nasu suka rufe gidan da sabon kwad'o suka bar shi azauna awajen da kayansa agaba da takadar sallamarsa daga aiki.

Adnan yafi k'arfin minti arbain a zaune a k'asa yana tunanin daga inda zai fara ina zai dosa a cikin kwana biyu ya had'u da iftilai haka na farko ya rabu da Aliya matarsa saliha mai kaunarsa na biyu ya rasa aikinsa na uku bai san daga ina zai fara ba"

A hankali ya d'aga kansa ya kalli k'ofar b'angarensu da aka kulle da sabon mukulli wani irin bak'inciki da danasanin abinda yayi ya rufe shi tabbas Aliya rahama ce a gare shi gashi daga rabuwa da ita ya rasa aikinsa ya rasa komai nasa.

Zara kuwa masiface agare shi dan sai daya fara muamalla da ita ya ringa had'uwa da masifu iri iri dan sabida ita ya ringa wasa da aikinsa har aka sallame shi ga mugun dukan dayaci a hannun Ameer duk asanadiyar ta wani mugun tsanar Zara ne ya darsu a ransa yaji inama ya ganshi a gabanta da shi ma sai ya cire mata sauran hakoran dan duk ita ta jawo masa wanan masifar.

Ganin ya zaune lokaci nata tafiya yasa ya mik'e ya fara tattara kayansa yana cusawa a katon jakarsa sai da ya gama saka kayansa ya zuge jakar da k'yar ya d'auko envelope d'in da suka ajiye masa a k'asa yasaka a cikin Aljihunsa  yafara Jan jakar dan bazai iya d'aukar jakar ba sabida nauyi.

Bai sha wahala samun abun hawa ba ya hau nufi hotel d'in da ya kama.

Tunda ya fita Zara wani irin Zazzabi ya rufeta Wanda sai da ta shige cikin bargon sabida sanyin da take ji d' Tayi amai ya kai sau uku tunda take bata tab'a irin wanan zazzabin ba sai baccin zazzabi ya fara kwasarta sai taji zuciyarta na tashi sai ta nufi band'aki da gudu.

A cikin wanan halin Adnan yazo ya sameta tabi Tayi zuru zuru.

Ko sallama bai yi mata ba inbanda mugun hararar daya watsa mata ya ajiye jakar da ya shigo dashi gefe ya nufi band'aki dan ya watsa ruwa ko zai ji sanyi a zuciyarsa.

Zara binsa kawai ta ringa yi da ido sabida bazata iya magana ba sabida halin da take ciki.

Tana kallo ya fito daga wanka yazo ya canja kayan jikinsa ya Ciro envelope d'in daga cikin kayan daya cire ya Ciro wrapper dubu dubu guda biyu ya ajiye agaban mudubin d'akin ya fice daga d'akin yana watsa mata harara.

Zara kuwa mik'ewa Tayi da sauri duk da bata jin dadin jikinta ta nufi gaban mudubin ta d'auki wrapper d'aya na kud'in ta koma ta kwanta dan ta samu kud'in da zata saka hakorin roba abakinta sai dai duk abinda Adnan zai yi yayi.

Tana kwanciya Adnan ya shigo da plate d'in abinci a hannunsa

Ya zauna akan kujerar dake d'akin ya fara cin abincinsa batare da kalli inda Zaran ke kwance ba fried rice ne dayaji kayan had'i da luk'a luk'an cinyar kaza ga maltina a gefe yana korawa idan ya had'a ido da Zara sai dai ya zabga mata harara dan gabad'aya gani yake itace matsalarsa .

Zara kuwa duk da bata tabbacin zata iya cin abincin sabida rashin appetite mik'ewa Tayi daga kwancen da take tace

"Ad ina nawa abincin nima fa yunwa nakeji ga wani irin zazzabin dake damuna"

Adnan ko d'agowa baiyi ba ya cigaba da cin abincinsa

Zara k'ara nanata maganar tayi

Adnan ya d'ago a fusace yana "idan yunwa kike ji ki tafi gidanku mana mai hadina dake naga dai ba hakkina bane na baki abincin Zara inda kin san tsanar Dana miki da baki tsaya kina min magana ba da kin tashi kin tafi gidanku dan babu abinda zanyi dake dan zama dake masifane a gareni kin janyo min asarar da bazan iya mayar ba asanadiyarki na rabu da matar da har na koma ga Allah bazan tab'a samun irinta ba asanadiyarki na rasa hanyar cin abincina asanadiyarki na rasa inda zan zauna babu abinda kika janyo min sai asarori Zara if u knw wat is good for u wlh ki tafi gidanku idan kuwa kika dage akan zaki zauna dani wlh sai na lahira yafiki jin dadi I would make your life a living hell ki daina kallona da wanan katon wawulon bakin naki I hate u"

STORY CONTINUES BELOW


Zara da kalmomin sa suka masifar girgiza ta hawaye ne ya hau wanke mata fuska take wani irin ciwon kai ya rufeta babu tunanin da take da ya wuce idan Adnan ya koreta ina zata nufa mai ta jawo wa kanta ne ita tana tunanin rabuwarta da Ameer shi zai sa Adnan ya aureta cikin sauki sai gashi tun ba'aje ko'ina ba yana gwada mata irin tsanar daya yi mata"

Zuba masa ido Kawai tayi tana sheshek'ar kuka

Adnan kuwa ya cigaba da cin abincinsa hankali sa kwance sai daya gama ci tsaf yayi gyatsa ya mik'e ya nufi gaban mudubin daya ajiye kud'i dan fita zaiyi ya nemi gidan da zai kama haya dan bai ga ta zama ba gobe kudin hotel d'in Zai yi expire.

Turus yayi daya ga babu wrapper d'aya ya juyo yana kallon Zara data zama statue tana kallonsa hawaye na zubo mata

"Ke ina kudin Dana ajiye Anan yake"?

Adnan yace cikin mugun d'aurewar fuska dan Zara tasan ba wasa yake da ita ba.

Zara wani irin d'auriya da k'arfin hali ne yazo mata ta koma ta kwanta tace " kabani ajiyar kudinka ne ka tambayi gaban mudubin ya gaya maka inda ya kai kudinka"

"Zaraaaa kina hauka ne kina san naci ubanki na k'arasa cire miki ragowan hakoran da suka miki Saura ko  zaki bani kudina ko kuwa ashe bayan iskancin ke barauniya ce ya daga ni sai ke a d'aki zan nemi kudin Dana ajiye na rasa Zara don't try my patient wlh zan sauke duk haushina akanki na miki dan bazan duka na kakaryaki kifito min da kudina"

Zara duk da ta tsorata sabida yanda Adnan ya koma tamkar wani zaki d'aurewa tayi dan Sam bazata iya bashi kudin ba bashi kudin na nufin ta cigaba da zama ahaka ba hakora ko ita da take da kanta bata sha'awar kallon kanta a mudubi sabida munin da tayi inaga kuma wani ya ganta ahaka ita tasan rashin hakoran ne ma yasa ya tsaneta tashi d'aya.

Cikin fad'uwar gaba ta juyar da kanta tace "sai kayi kuma ni ban d'aukar maka kud.."

Adnan bai bari ta k'arasa ba ya fuzgota daga kan gadon ya hau kwallo da ita yana cewa ta fito masa da kudinsa

Zara kuwa sai ihu take tana neman taimako

Ganin Adnan na dukanta cikin fitar hayyaci yana neman aikata lahira yasa tayi sauri tace "ka tsaya zan baka wallahi kar ka kasheni"

Adnan tsayawa yayi yana maida numfashi yace "maza bani barauniyar  Banza barauniyar wofi"

Zara da sauri ta d'aga katifar ta d'auko kudin tana mik'a mishi tare da tare jinin dake zubowa cikin hancinta wani irin jiri na d'ibarta yana k'arbar kud'in ta zube a k'asa ta sume awajen.

Adnan kuwa ya k'ara hamb'areta yana d'aukan kudin dake gaban mudubin ya had'a da Wanda ya k'arba a hannunta ya fice yana Allah yasa ta mutu kafin ya dawo.

Yana barin hotel d'in ya hau motarsa ya fari bin unguwa unguwa yana neman gidan haya sai daya samu awa biyu yana nema daga Wanda yayi mishi tsada sai Wanda gidan yayi mishi kad'an ahaka dai har ya samu wani d'an madaidaci mai saukin kudi d'akuna biyu Palo band'aki da kitchen.

A take ya bada dubu d'ari da ashirin ya biya ya samu wasu Almajirai suka share masa gidan suka mopper shi.

Sai da ya siyo sabon katifa da zanin gado ya kai cikin gidan ya baro gidan da zummar yaje ya kwaso kayansa.


Gabansa ne ya d'an fad'i a lokacin dayaga Zara na kwance ayanda ya barta dazun.

Da sauri ya nufi wajenta yana jijjiga ta amma ina ko motsawa batayi ba take hankalinsa ya tashi ya d'ebo ruwa yazo ya watsa mata amma abanza ko motsawa batayi ba.

Cikin tsananin tashin hankali ya kinkimeta yayi waje da ita da sauri bai tsaya sauraran wayanda suka ringa tambayar shi mai ya sameta ba ya saka ta a motarsa da sauri ya nufi wani k'aramin private hospital dake can k'asan hotel d'in 

Zirga zirga kawai ya ringa yi a harabar asibitin hankalinsa a tashe wani b'angare na zuciyarsa na addu'ar Allah yasa Zara ta mutu ya huta wani b'angare na zuciyarsa na addu'ar Allah yasa kar ta mutu.

Sai da aka samu awa d'aya da rabi kafin likitan dake duba Zara yafito yace ya zo ya same shi a office.

Adnan kamar zai hantsila sabida saurin da ya ringa yi a lokacin dayabi bayan likita dan duk ya matsu yaji halin da Zara take ciki.

Likita sai daya gama rubuce rubucensa ya d'ago yace masa "matarka na cikin critical condition amma alhamdulillah mun samu mun shawo kan matsalar  dan har Karin jini akayi mata pls ga wanan tana bukatarsu sosai sabida cikin dake jikinta"

"What"?

Adnan yace yana dukan tebur d'in dake gabansa "

"Mai kace likita ciki fa kace"?

Likitan a d'an mamakince yace "ee ciki nace dama bakasan tana da ciki ba tana d'auke da ciki har wata biyu da sati d'aya"

"Innalillahi wa inna ilahi rajiun  Dr dan Allah ka cire cikin nan ban shirya zama uba ba yanzu ko nawa ne zan baka dan Allah ka cire cikin nan"

Likita da sauri yace "am sorry to say bama zubar da ciki a asibitin nan kuma a condition d'in matarka wlh idan kace zaka zubar mata da cikin zata iya rasa ranta mai yayi zafi haka kai kuwa bawan Allah cikin da wasu suke nema ido rufe wasu har da kudinsu basu samu ba kai ka samu kana so ka zubar."

Adnan kallon likita kawai yake hankalinsa a tashe tunani kawai yake inda zai kai Zara da cikinta shi da yake so ya korata gidansu kuma sai ga ciki ya b'ullo Anya ba guduwa zaiyi daga asibitin ba Idan sun gaji da rik'eta su koreta ta tafi gidansu tunda dama Zara batasan gidan daya koma ba........"I advise u idan haihuwane baka so kabari idan ta haifi abun cikin nata sai ka d'orata akan family planing I think that's d best solution"
+

Likitan ya k'ara cewa  yana kallon Adnan dayayi zurfi a tunanin

Likitan dukan teburin yayi Adnan yayi sauri ya dawo daga tunanin daya tafi

"Inata maka magana kana tunanin"

Adnan ajiyar zuciya ya sauke yace

"Sorry banji bane bani takardar na amso  mata magungunan"

Likitan mik'a masa takadar yayi

Adnan yafice daga office d'in.

Adnan kuwa yana fita ya hau motarsa ya bar harabar asibitin sai da yayi tafiya mai d'an nisa ya tsayar da motar ya k'ifar da kansa a steering d'in yana tunanin abinda ya dace yayi

Tunaninsa ne  ya rabu gida biyu wani nacewa daga nan kar ya k'ara komawa asibitin wani nacewa ya koma inyaso idan an sallamo Zara sai ya samo maganin zubar da cikin ya d'ura mata har sai cikin ya zub'e dan yanzu ma ko ya gudu Zara zata haifi abun cikinta kuma dole Wataran a nemo shi.

Da wanan tunanin Adnan ya tada motarsa yaje wani pharmacist ya siyo magungunan daga nan ya tamb'ayesu ko suna da maganin zubar da ciki ko allura idan suna dashi su bashi ko nawane zai basu.

Aikuwa mutumin da tsada ya bashi wasu kwayoyi guda shidda yace ta shanye guda hud'u tasaka biyu agabanta cikin zai b'are.

Adnan da saurinsa yasaka kwayoyin a aljihunsa yana d'an jin relief d'in tashin hankalin da yake ciki.

Sai da ya kai musu magungunan ya koma gida dan Sam bazai iya wani kwana a asibitin ba.


A takaice sai da Zara ta samu kwana uku a asibiti kafin a sallamota duk da lokacin Tana azababben laulayi duk da magungunan da allurai da ake mata.

Adnan kuwa duk zuwan da yake bai wani nuna mata komai ba in banda d'an tattalinta dayake yi dan so yake ya samu ya shawo kanta tasha maganin zubar da cikin.

Tun da suka baro asibiti suka d'auki hanyar hotoro danmarke suka fara kutsawa cikin unguwani 

Zara ta gyara zamanta akan kujerar Tana bin unguwar da kallo dan bata ma san unguwar ba.

K'asa hakura tayi sai da tace "Adnan wai ina zamuje ne"?

Adnan bai juyo ya kalleta ba yace "gidana zamuje mana"

"Gidanka kuma a unguwar nan"?

Zara tace Tana kallonsa cikin mamaki

" Adnan tsaki yayi yace  "idan bazakije gidan nawa ba ai zaki iya sauka ki tafi gidanku dake G.R.A"

Zara girgiza kanta kawai tayi ta cigaba da kallon unguwar Tana mamakin Yanda zata yi rayuwa a cikin  irin unguwar nan

Ganin Adnan yayi parking  ne yasa tayi sauri ta juya Tana kallon k'ofar gidan da sukayi parking bata gama tunanin da zatayi ba Adnan yafito daga motar ya nufi gidan Tare da zaro mukulli a aljihunsa ya bud'e gidan.

STORY CONTINUES BELOW


Ko kallon Zara dake zaune a cikin motar bai yi ba yayi shigewarsa

Zara kuwa jiki a sanyaye tafito daga motar ta rufe ta tsallaka k'aton kwatan dake k'ofar gidan ta shige ciki Tana kalle kalle

Sai da ta karewa tsakar gidan kallo Wanda rijiya ke gefe ta nufi wajen da take kyautata zaton Palo ne.

Bud'e baki tayi a lokacin da taga babu komai a palon ko labule babu in banda tiles d'in dake k'asan palon ga palon k'ararrami.

D'akuna biyun dake palon tabi da kallo ta nufi d'aya daga ciki nan ma ta bud'e taga babu komai a ciki 

Jikinta ne ya k'ara bala'in sanyi ta nufi d'akin da take kyautata zaton Adnan na ciki.

A kwance ta ganshi akan katifar yana danne danne a wayarsa gefe kuma kayansa ne a zub'e birjik.


A hankali ta k'arasa wajensa ta zauna a gefensa Tana cigaba da kallon d'akin dan shima in banda katifa babu labule a d'akin.

"Adnan wai mai ke faruwa ne kanaso kacemin ka baro wancan gidan ka dawo nan da zama kenan"?

"Gashi kuwa idonki ya gane miki an koroni daga wancan gidan a dalilin ki Na rasa komai nawa adalilinki so nan ma da kike gani haya ne idan zaki iya zama ruwanki idan bazaki iya zama ba zaki iya kama gabanki dan nikam zamanki awajena ma takura ne dan bansan kalar asarorin da zaki kuma janyo min ba"

Adnan yace yana mai zabga mata harara 

Zara sakin baki tayi tana kallon shi ganin Adnan ya juya mata baya yana zuba tsaki yasa tace

"Haba Ad wai meyesa kake d'oramin laifin duk abunda ya sameka kar fa ka manta ina da laifi kana da laifi nakan ma yafi yawa dan kai kafara nuna interest d'inka akaina kafin nima nafad'a kogin sanka har na k'asa controlling kaina  gida da  aikin da ka rasa can be replaced iyaye fa bazan tab'a iya replacing d'insu ba  akanka nayiwa iyayena rashin mutunci na zab'eka akansu na rabu da  mijin aurena akanka  karshe ma har wani b'ari na jikina na rasa duk sabida kai amma kuma tun ba'aje ko'ina ba gashi kana neman juya min baya haba Ad wlh ban cancanci haka daga wajenka ba"

"Ai ke mahaukaciya ce shiyasa kika zabi namiji  akan iyayen da suka kawoki duniya ni bance miki kiyi zurfi a sona haka ba d way u dress attract me har yasa naji ina mugun sha'awarki amma bawai wani sonki  nake ba I lost everything I have ciki kuwa harda salihar matata dan ni nasan Wlh Aliya koda babu aure a kanta bazata yarda wani ya rik'e mata hannu ba ballantana akai ga ya santa 'ya mace wlh  not even in my dream idan aka rantse min zanyi rayuwa a irin gidanan na yarda amma gashi a dalilin ki dole na fara rayuwa aciki u have cost me a lot of damages"
1

"Enoughhhh Ad  lokaci yayi da zaka daina d'oramin laifin duk abunda ya sameka d time u are riding and raining love on me meyesa baka hango zaka shiga irin wanan matsalar ba sai yanzu koda abaya sha'awata kake bawani sona kake ba kamar Yanda ka sha fad'a abaya to yanzu kuwa ya zama dole ka koyi sona tunda zama dani ya zama dole dan ga cikinka a jikina"

Adnan wani mummunan kallo ya watsa mata yace "Sai kin cire wanan shegen cikin dake jikinki dan nariga da nasan ke ba Kunya gareki ba tunda kika iya neman wani mijin da aurenki Auren naki ma ya mutu kika k'asa tafiya gidanku ko iddan nan da ake yi kika k'i yi dan ki raini cikin shege ki haife shi ba wahala zai miki ba  amma kisani ni da sauran kunyata bazan iya k'arbar shege a d'a ba dan haka ki zubar da cikin nan ki koma gidanku idan kinyi jini uku sai nazo na aureki asan ke mata ta ce"

"Adnan a kalmominka Nagano cewar kai katon jahili ne ina aka tab'a idda da ciki sai dai idan na haihu na koma gidanmu sai ka zo ka aureni bani zakayi wa wayo kace na zubar da cikin jikina  ba daga nan ka gujeni"

Tunda Zara tacewa Adnan jahili jikinsa ya fara rawa ransa yayi bala'in b'aci ita kuwa Zara itama harararsa take ta mik'e gabanta na d'an fad'uwa sabida rawar data ga jikinsa nayi tasan zai iya kawo mata duka 

Adnan mik'ewa yayi  yana nuna kirjinsa yace "ni kike cewa jahili"?

Zara baya ta fara yi tana cigaba da harararsa ganin ya nufota yasa ta kwasa aguje ta bar d'akin ya kuwa rufa mata baya ya damkota ya fara kwallo da ita 

Zara kuwa sai ihu take sai da yagaji da jibgarta ya koma d'akin da sauri ya kwaso k'wayoyin da ya siyo na zubar da cikin ya nufi wajenta bayan ya d'auko pure water guda d'aya

Zara kuwa kuka kawai take tana birgima 

Adnan kuwa ya d'urk'usa agabanta ya janyo ta jikinsa ya danneta da k'afafunsa ya  matse bakinta sosai Zara kuwa tsananin azaba yasa ta bud'e bakin ya kuwa watsa mata tablet hud'un a bakin ta ya bud'e ledar ruwan ya dura mata aciki.

Zara kuwa da sauri ta had'iye tana zaro idonta waje sabida Yanda ya matse mata baki.

Bai saketa ba ya k'ara matseta tare da raba k'afarta gida biyu ya cusa hannunsa k'asan ta ya tura sauran guda biyun aciki.

Zara kuwa ido kawai take zarowa sabida tsaya mata da magungunan sukayi a makogaro

Adnan kuwa ya rik'eta gam dan kar ta tashi tayi yunkurin amai.

Zara kuwa mutsu mutsu ta fara yi dan ya cikata sabida aman daya taho mata amma ina Adnan kara riketa yayi

Aikuwa Zara ta sakar masa aman ajikinsa sai ga tabs d'in kuwa guda hud'u ta amayo su ko alamar narkewa bai yi ba

Adnan wani irin kullutun bak'inciki ne ya taso ya tokare masa makagaro a lokacin dayake bin tabs d'in da kallo

Zara kuwa ta ringa sauka ajiyar zuciya sabida wahalar da tasha

Adnan tureta yayi daga jikinsa ya mik'e a fusace.

Yace "kwanciyar hankalinki shine ki zubar da cikin jikin nan idan kuwa kika k'i wlh sai na ringa gana miki azaba iri iri har sai cikin ya b'are"

Zara ita dai ajiyar zuciya kawai ta ringa saukewa tana binsa da ido dan yanzu wani irin tsoron Adnan take ji.

Adnan d'akin ya koma ransa a mutuk'ar b'ace ya shige band'aki dan yayi wanka

Zara kuwa yana shigewa ta mik'e a hankali ta nufi band'akin d'aya d'akin ta cire wandonta ta sa hannu ta Ciro tabs d'in daya sa mata dan har wani tokareta yayi ta wanke jikinta ta fito ta kwanta a k'asan tiles d'in d'akin ta lumshe ido tana jin kanta dake Sara mata tsoro take ji ta fita Adnan ya kara jibgarta ko kuma ya k'ara d'ura mata maganin zubar da cikin.

Adnan kuwa yana fitowa daga wanka ya shirya ya d'auki ATM d'insa ya fice daga gidan dan so yake yayo siyayya daga nan ya k'ara samo wani maganin dan sai cikin jikin Zara ya zub'e hankalinsa zai kwanta.

Post a Comment for "MAKOTAN JUNA CHAPTER 5"